Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da furta.

"hibba me yasa kike son sakawa kanki damuwa akan abinda gba dayan mu muma ita mukejira? Wannan abinda kikeyi sam ba shine cikakken masoyi ya kamata yayiwa masoyinsa ba, abu daya ynz mahir ke bukata har gaban abada a gare shine addu'a matukar zaki dinga takura rayuwarki kina sawa kanki damu da iyayenki da yan uwanki to mahir baze ta6a alfahari da ke ba, hibba wanda ya rasu ya rasu baze dawoba kinsan da wannan mahir ya rigamu zuwa gidan gaskiya kuma alhmdllh sae dea muyi masa murna domin muna kyautata masa zaton dacewa da rahmar ubangiji domin annabi yace duk wanda ya cika da kalimatush shahada to tabbas ze samu cetona! To hibba anan wata makoma kike tunanin mahir ze tafi tabbas duk wata alama ta rahamar ubangiji tna tare da mahir ko dan kyakkyawar shedar mutane da yake samu tare kyakkyawan karshe da yasamu domin ajalinsa yazone a hanyarsa ta zuwa ceto dumbin rayukan talakawa da ake rasawa saka makon yajin aikin da asibitoci keyi, toh ynz dan Allah hibba ko wannan bazesa muyiwa mahir kyakkyawan zato ba? Mu tayashi murna da farincikin dacewa ba sannan muyiwa junanmu muma addu'ar samu babban rabo irin nasa ba?"

shiru yayi yana kallo yarda ta kife kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka kamar ranta ze fita, tabbas duk cikin kalaman anwar babu karya a ciki domin itace babbar sheda kancewa mahir ya rasu da ambaton Allah a bakinsa, tabbas babu amfanin wannan damuwa ta ta sai dea har gaban abada bazata Iya kankare digon soyayyar mahir daga cikin zuciyarta da magudanar jini da numfashinta ba, gsky tayi babban rashin da bazata Iya samun madadinsa ba, domin mahir haskene a rayuwarta kuma babban bangon dafawa a rayuwarta.

Sae da tayi kukanta me isarta yayin da anwar begaza wajen kwantar mata da hankali ba ta hanyar nasiharsa da lallashinta.


har sae da yaga ta dan Saki kadan, yana dan janta da hira ta amsa mishi sama sama har ya tashi ze tafi sukayi sallama da umma ita kuma ta rakoshi soro ya tsaya tare da dafa kofa yana kallonta, cikin sanyi yace.

"plz ki cire duk wani damuwa mahir addu'a ke so a gurinmu kawai Allah ya gafarta masa yasa idan tamu tazo mu cika da imani."

"amin."

Ta fada kanta a kasa.

Ya danyi murmushi dake fito da zallar kyawunsa yace.

"gobe zaki koma gurin aiki ko?"

Ta dago dasauri ta kalleshi tare dayin narai narai da ido zatayi kuka tace.

"na hkr da aikin nabari bazan Iya ba."

"karkice haka hibba aikin kine kawai ze rage miki damuwar da kike ciki kuma kinga...."

"bazan cigaba da zuwa inda zan dinga saka ran ganin hub ba."

Daga haka tabar wajen tare da komawa ciki abinta.




*YOLA*

Mum ta zauna gefan bed din feena dake kwance amma ba barci take ba.

A hnkl Mum tace.

"feena ki tashi kici abinci kiyi sallah ki samu kisha magani ai bazaki ta zama da ciwo a jiki ba, mahir ya rasu kuma kinsan ba dawowa zeyiba har abada tabbas ansan mutuwar miji da daci amma wannan abinda kike babu inda ze kaiki ace kiki ci kiki sha sallahr ma sae anyi ta fama kiyita ga ciwo kinki shan magani ya kike abu kamar wadda baki da ilimin Islam."

Feena ta Mike zaune idanuwane kawai a fuskarta tsabar rama ga wani baki da tayi ashe daman ana hadawa da bliching, ta kalli Mum tare da turo baki tace.

"shi isa nace ku mayar dani wajen uwa da ubana tunda ku ba kaunata kuke ba ya za'ayi mijina ya mutu kuma kiyi tunanin sake ganin walwalata ko dan ke....."

Wata tsawa najwa ta daka mata dai dai shigowarta dakin tare da unty fareeda.

Najwa tace.

"ashe har ynz baki da mutunci to kiji da kyau daman wanda ya hada ya raba albarkacin takabar dan uwanmu kikeci kawai dan da tuni mun manta dake wace a wajenmu karki kuskura ki zagar mana uwa diyar mararsa tarbiya."

Ran feena yayi mugun 6aci ta Mike zaune tare da dura wata uwar ashar kai bakace mai takaba bace suka fara musayar baki da najwa da fareeda Mum tayi iyakar ta su bari suka ki kuka Mum ta fashe da shi Tana fadin.

"yau wata dana guda a kabarinsa amma gashi kun zauna kuna debe albarka akan shi duk cikinku babu wanda na isa nace yabari yaji maganata yabari shikkenan kuyi duniya taji ta zagemu burinku ya cika ai."

Ta karasa mgnr cikin kuka tana barin dakin, su najwa sukabi bayanta suna lallashi feena kuwa tsaki taja tare da janyo wayarta da ta 6oye karkashin pillow jin motsin Mum din dazu ta cigaba da chatting dinta.πŸ€”feena ba ilimin Islam fa.






Haka dai aka cigaba da fadi tashi a lamarin duniya, yayin da ynz kusan kullum anwar yana tare da hibba yana sake kwantar mata da hankali hakama yan uwnta dana mahir duk babu wanda aka bari a baya wajen jan hibba a jiki duk dan ta cire damuwar da take ciki.

Rayuwa haka ta cigaba da ja da dadi ba dadi, har feena ta fita daga takaba, ta koma gidansu tare da fitar mata tuminin takaba daga gadon mahir.



Yau hibba tana dakinta barci rana ya dauketa bayan ta gama shan kukanta da ta saba, cikin barci tayi mafarkin mahir sanye da wasu kaya na alhariri kansa dauke da wata hula ta tattacen gold yana cikin wani irin katon pool mai girmn gaske ga wasu kyawawan furanne a cikin ruwa.

Daga can nesa ta farajin karar wata sarkar kafa ta zinare nan taga ta iso itama cikin wani ado a nutsu yna fitar mata da kyakkyawan murmushinsa ya fita daga ruwan ya isa gabanta, kneeling down yayi gabanta yana murmushi wanda itama shi take masa, kalmar karshe da ya fada mta lkcn mutuwarsa ya sake maimaita mata sae kuma ya saketa tare da mikewa ya koma cikin ruwan yana tafiya yana waiwayenta yana daga mata hannu yana murmushi har ya kure mata.

Zumbur ta Mike gumi jargab ya jikata dakin nata ta farabi da kallo sae taga kmr zata ganshi mikewa tayi tafara neme neme.........








More comments plzπŸ˜ƒπŸ˜ƒ







Oum Afaf✍🏻
[10/23, 10:30 PM] +234 812 554 4850: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*





*_Ikon Allah kenan wai na zaune ya fadiπŸ€”to inbanda hankali na wasu jama'a mutuwa nawa ce tabbas mutuwa daya ce kuma babu wanda ze guje mata, wannan labarin bawai da ka nake komai ba, kafin na fara rubuta labarin nan sai da nayi nazari da tunanin yadda zan tafi da farko da kuma karshe, to sbd me wasu keson na change idea ta na dauki tasu, wasu na zagina suna aibatani har wasu na kushe basirata wadda dasu ne na tabbata ko read more guda basa Iya yi, tor alhmdllh nagodewa lillahi da yasa bana nema gurin kowa bare a bani umarnin abinda zan rubuta....Kuma kusani yana daga cikin rashin yarda da Allah kinyin imani da mutuwa, Allah (SWT) da kansa ya fada cewa:"dukkanin mai rai mamaci ne." to ku ba'a mutuwa a garinku? Mutane nawa kuka sani naku da suka mutu? A social media sau nawa a rana ko wata ko shekara kuke ganin ana posting Allah ya jikan kaza?...Dan Allah dan annabi ku zama masu uziri tare da tsayawa kuga inda gudun ruwan mutum ze tsaya...._*





*πŸ…Ώ 30*

Har parlour ta fito kamar mahaukaciya tana zazzare ido tana dube dube kmr me neman wani abu, umma ta dubeta tace.

"ke hibba mekike nema?"

"umma mahir wllh umma mahir yana raye be mutuba umma wllh jikina ya bani mahir dina yana raye be mutu ba, dan Allah umma ki kaini na ganshi."

Ta fada cikin kuka sosai, umma ta Mike tare da janyota ta fuzge ta fita tsakar gida da gudu tana dube dube har toilet ta leka da kitchen, umma duk ta rude gashi babu kowa gidan ga hibba dake abu kmr hauka ta janyo hijjab dinta tayi waje umma tabi bayanta da gudu cikin ikon Allah sae ga Baba, dakyar suka Iya shigo da hibba ke wani irin ihu tana fuzge fuzge.

Umma in banda kuka babu abinda take baba ransa ya gama 6aci da lamarin hibbar ya daka mata wata irin tsawa tare da kwada mata wani irin Mari wanda har sae da wata farar wuta ta fito daga kuncinta, jikin umma ta fada tare da rungumeta tana wani irin kuka da dukkan jikinta ke rawa.

Umma sake rukun kumeta tayi itama tana wani irin kuka dajin zafin Marin da baban yayiwa hibbar.

Cikin 6acin rai Baba ya fara cewa.

"Ashe ke jahilace da baki yarda zecewa rayuwa gaskiya bace kuma mutuwa ma gaskiya ce? Munyi lallashin munyi ban baki amma kinki ji sbd wani banzan son da kike tunanin kinayiwa mahir wanda karya kike ba sonshi kike ba tunda har kullum kukan da kike masa yafi nema masa gafarar da kikeyi waya, to ki tsaya kiji mahir ya mutu domin ni shedani dan har dani aka bunneshi a turakarsa, sbd hka mahir ya tafi har abada kuma baze dawoba idan kema zaki bishi to ga hanya nan, gargadi na karshe da nason yi miki shine Karna sake ganin kina mana irin wannan hauka a gida."

hibba cikin kuka tace.

"baba wllh mahir be mutuba."

Baba ya tsura mata ido yana tsinkewa da lamarinta ya tausasa murya yace.

"hibba mahir ya mutu."

kukan hibba ya tsananta Baba rasa abin yafa yayi ya Mike ya shige daki jiki sanyaye.



Bayan sati

Lamarin hibba sae gaba yake da kullum cikin mafarkin mahir take ta sake lalacewa sosai duk ta zama wata irin lokacin hatta da Mum da unty fareeda sunzo sunga halin da hibbar take, shawara suka yanke akan kawai ayi mata aure wata kila hakan zesa ta samu sassaucin damuwar da take ciki.


Sati daya aka tsayar da auren hibba anwar, wanda hibba ko da ta samu wannan labarin kusan kwana tayi tana kuka nan fa ta sake bude wani sabon shafin damuwa.

Anwar kuwa farinciki ba'a misiltawa daman ma hakurci mawadaci, Ashe duk hakurin da yayi shine alkhairin hibba rabonsace bata mahir ba lallai ikon Allah ba me Iya ja da shi.

Ba'ayi wani biki ba domin anwar yace duk bayaso sbd halin da amaryar tasa take ciki yace daga baya Idan ta saki akayi duk abinda ya kamata, daga kasar Paris kuwa 6angaren dangin mamyn sa kyakkyawan biki suka shirya na musamman bayan daurin aure da zasuyi a can.

Hibba duk ta gama shiga damuwa domin ita gani take kmr batayiwa mahir adalci ba kuma taci amanarsa, ranar juma'a dumbin Al'umar musulmai suka sheda daurin auren *HIBBATULLAH MUKTAR AMMANI DA BARR SALIHU BASHIR LAMIDO* akan sadaki dubu Dari uku kudi hannu ba bashi ba.

Lokaci guda gari ya dauki kuwa ana ta sanarwa, hibba na kwance jikinta in banda rawa babu abinda yake.

Ango anwar kuwa ya dauki wanka Iya wanka yayi kyau Iya kyau tare da manyan yaran abokansa suka gabatar da walima mai kyau a meenat event center.



Kwana uku da daura auren hibba wadda ta kama lahadi kuma a daren zasu wuce Paris tana zaune a parlour kan kujera tana kallon laccar Dr umar rijiyar lemo mai taken imanin mutum baze cika ba....gaba daya ta mika attention dinta kan laccar tana sauraro, wani kamshi ne taji ya gaurare parlourn gaba daya Wanda bazata ta6a manta da kamshin nan ba har abada kuwa, a hankali taji kamshi ya dosota tare da tuku zuwa gabanta, tsaye ta Mike da sauri tare da dafe kirjinta da hannu idawunata duk finto jikinta duk ya dauki rawa cikin rawar baki tana nuna gurin da hannu tace.........








share
vote
commentS








Oum Afaf✍🏻
[10/23, 10:30 PM] +234 812 554 4850: *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S✍🏻*

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
*NI DA DR MAHIR*
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Writing by
*HAFSAT BELLO*

_Follow me on instagram:_
*hapc20*





_Allahu ya Qara girma da daukaka hajiya Hindu goya marayu Sudan...nagaisheki uwar dakin uwar dakinaπŸ˜ƒjazakillahu be jannatul firdaus....hafsah love you shaaaβ€πŸ’ž_





*πŸ…Ώ 31*

"Meya kawoki gidan mu?"

Hibba ta fada fuskarta cike da tsoro.

Wani shi'umin murmushi feena tayi tana zare bakin spec din fuskarta, parlourn tabi da kallo a shekeke sannan ta ta6e baki tare da furta.

"no wonder aka nacewa gidan arziki mana Ashe anan ake rayuwa."

Hibba ta katseta da cewa.

"Nace mekikazo yi gidan nan nakejin wanda ya hada ya raba to me kikazo nema kuma gurina?"

Feena tayi taku daya zuwa gaban hibbar ta dafata fuska dauke da murmushin raini sannan tace.

"kwantar da hankalinki hajia nazo na tuna miki da alkawarin mu, tare da tuna miki yarjejeniyar da muka kulla tsaka....."

"Karki rainawa kanki hankali Nafisa dan baiwa inaji alkawarin munkulashine kan mijinki ko? To ynz yana ina yatafi yabar mana duniyar da babu komai cikinta sae wahala da tarin bakin cikin rayuwa, dan girman Allah ki fita a rayuwata dan banson sake ganin ko me irin kamanninki a duniyar nan, bari kiji ko ynz asa misali mahir ze dawo duniyar nan bani da damar auren shi sbd daman can Allah ya qaddara ba mijina bane, feena ki kyaleni plz I begging you. "

wata irin dariya hibba ta fashe da ita.

"Gaskiya ke matsoraciya ce, haba hibba ae komai ya wuce, sae dea da ace kinyi gigin bari an daura aurenki da mahir to da wllh ynz jimamin mutuwar iyayenki ake bata mahir ba, but Allah ya qaddara faruwan hakan ne kawai, ni abinda ya kawoni nazone na tayaki murnar aurenki, happy marriage life wish you all the best and zuri'ah dayyaba, I hope first born za'ayi mini namesake?"

Ta fada tana dariya tare da dauke mata gira alamar rainin hankali.

Hibba ta girgiza kai cike da tarin tsanar feena, ba tare da ta kuma cemata komai ba ta nemi waje tayi zamanta tana cigaba da kallonta.

Feena kuwa Jakarta ta zuge tare da fito da rapper na dubu dubu bandir guda ta mika mata tana fadin.

"Ga wannan asiyi gado da kujera dan nasan ba'a shirya musu ba da anajiran na bati."

Hibba tayi murmushi tace.

"Talaucin mu be kai nan ba, dazaki rike kudinki meybe sae kinfini bukatarsu wajen siyan kayan shafe na zawarci, idan kin gama abinda ya kawoki zaki Iya tafiya sannam ki janyo mana kofar gida."

Daga haka ta Mike tayi shigewarta daki tabar feena tsaye, feena kuwa wata muguwar dariya ta saki tare da furta.

"shashasha."





karfe uku na rana, unty ramla tazo dame kunshi wanda zatayiwa hibbar, dakyar hibba ta yarda aka saka mata ja kawai a kafa da hannu karfe biyar aka cire yayi kyau sosai a farar fatar kafarta ta.

Ana cire lallen suka tafi Indian saloon dake zoo road da yake matar indiyace shi isa manyan masu kudi ne suke zuwa gyaran gashi wajen.

gyaran gashi na musamman akayi mata nan take duk wata martaba ta gashinta ta fito basu dawo gida ba sae bayan magriba, suna dawowa suka baje tsakar Gida suna hutawa Allah yasa sunyi sallar magriba a wajen, umma ta fito daga kitchen rike da food flacks da plate da spoon ta zauna tare da bude plate din farfesun tattabara ne a ciki wanda akayi masa hadin kankana da fresh milk sae magunguna da ake sawa, ta zuba mata cikin plate tare da romo da yawa ta tura gaban hibbar tace.

"maza hibbatullah cinye du har kashin ki taune kafin ruwanki yayi zafi na daura miki ynz."

Hibba ta ta6e baki sannan ta kalli farfesun ta saka danyantsanta ta dandana tayi saurin furzarwa.

"gaskiya umma ni ban Iya cin wannan abu shiba tsami ba shi ba zaki ba shiba gishiriba."

Ta fada tana ture plate din a gabanta.

Umma tayi dariya tace

"kiji mini mutuniyar kurum zaki dauka kici ko sai na miki dura."

"me za'a dauka aci ni abani naci."

Unty ramla ta fada lkcn da ta fito tsakar gidan.

"wannan hadin tattabaran ne wae bazataci ba."

"kutu bazakici ba? Tab wannan yarinyar naki aziman ni da nasan darajar sa bani naci umma rabu da ita."

Ta fada tana jan plate din gabanta, umma ta kar6a sannan ta harareta tace.

"bani ae bada sunanki aka dafaba mara kunya, ke hibba dauki kici kafin ki 6atan rai."

umma ta fada ba wasa hibba hawaye ta fara amma haka ta dinga dannawa sae da ta cinye tas ta shanye roman, tanayi tana kakarin a mai wani hadin ta sake bata a cup shima haka ta shanye tas, ruwan wanka unty ramla ta hada mata tashiga tayi.


Karfe 9 na dare dukkan yayyun hibba da umma da Baba da granny suna zaune dakin baba gefe kuma Anwar ne zaune ya hade cikin wata dakakkiyar vuwa shadda fara da bakin aiki ya saka hula baka, sae hibba dake sanye da Arabian gown mai manyan stone masu walwali sae kyalli suke ta yane kanta da mayafin rigar.

Nasiha mai tsuma zuciya da shiga jikin gaske akayi masu duk taurin zuciyar mutun sae wannan nasiha ta shigeshi nan kukan da hibba takeyi ya sake tsananta har yana fitowa filo kowa naji, a yau da zata bi anwar wata kasar a matsayin matarsa ta riga ta gama saddakarwa mahir ya tafi har abada kuma baze ta6a dawowa ba.

umma kasa mgn tayi sai kukan rabuwa da yartata da tafi soyuwa a wajenta fiye da sauran yayan nata, dakyar da Iya damka amanarta a hannun anwar din tare da sanya masu albarka.



Har airport suka rakosu lkcm da hibba zata shiga jirgi dakyar aka rabata da umma da rayyan tsabar kukan da take kamar ranta ze fita anwar shima har hawaye yayi tare da jan hannunta tana waiwayen su umman suka shige jirgi sai Paris.




Sun jima a sararin samaniya suna lulawa kafin jirginsu ya sauka a babban birnin qasar Paris.

Hibba lkcn bacci take, a hnkl ya daura lips dinshi kan nata tare da zura harshensa cikin bakinta, a hnkl take bude kumburarren idawunta suka sauka a smile face dinshi tayi saurin zabuwa ta Mike yayi dariya a daidai kunnenta yace.

"welcome to Paris my wife. "

sae a lkcn hibba ta kula da mutanen jirgin dake fita kokarin mikewa tayi ya dagata tare da janyo wata jacket ya rufa mata sbd sanyin garin ya riko hannunta ta zare ya dubeta a mareraice yace.

"plz baby mamy zata gane wani abun matukar bata ganmu a haka ba."

Baki hibba ta dan turo shi kuma yayi murmushi yaja hannunta suka fito.


Tun daga nesa nake hango dalleliyar baturiyar wadda color ta yayi yanayi da Arabs tana sanye da wasu hadaddun riga da skirt na flowy ta yane kanta da vail, with a smile face ta karaso gaban couple.
Anwar har ya tafi zeyi hug nata ta tureshi tare da janyo hibbar tana murmushin farinciki ta rugumeta tight kafin ta saketa ta dagota tana jin son ranta har cikin ranta tace.

"Masha Allah finally nima gani da daughter in-law alhmdllh, welcome to me Looking so beautiful and good girl my God bless you now and always."

ta karasa mgnr tana kissing forheArd dinta..

Hibba ta dukar da kanta tana murmushin yake tare da tuno haduwarta ta farko da Mum din mahir wajen dinner yarda itama ta nuna mata zallar kauna, hawayen da ke shirin zubo mata ta danne.

Katafaren gidan mamy suka nufa cike yake da yan uwan mamy haka sukayi ta masu welcoming tare da yaba kyawun hibbar kasan cewarta Nigerian girl.

Wani katon apartment ta Kai hibba tayi wanka sannan tayi feeding nata abinci ta matsa ta danci sosai sannan ta dauko mata wata nighty cotton tace tasaka ta kwanta ta huta.

Anwar ya shiga apartment mamy tana zaune tare da fam dinta anwar yshigo dauke da sallamar da mamy ce kawai ta amsa kasan cewarta itace kawai Muslim a cikinsu, hannu ta bude mishi ai kuwa ya tafi tare da fadawa jikinta kmr Annour ne mai goge typing idan nayiπŸ˜ƒ.

Hannunshi ta riko suka nufi dinning tana fadin.

"Cwthart you look so tired."

"yes mamy and I miss you more."

murmushi tayi tana bude manYAn warmers abinci ta zuba masa sannan ta fara feeding nashi kmr yarda ta saba.

Sae da ya koshi sannan tace.

"son kaje kayi warm bath ka kwanta."

ta fada cikin hausarta dabe fita sosai.

Kai ya gyada mata tare da kissing kumatunta yace.

"good night mamy."

"night habeby."

Daya apartment din ya nufa tare da shiga bathroom din ciki ransa fal farincikin mallakar hibba kmr a mafarki.

"Alhmdllh yh rabbul'alamin, am married to hibbatullah wow mahakurci mawadaci I thank God wllh."

Ya fada yana rawa sosai tsaye kan shower daga haka ya gama wankan ya fito tare da shiryawa a gurguje ya nufi part din da hibbar take.

Chan tsakiyar katon gadon ya hangota kwance ta kudundune jikinta da bargo sai dea fuskarta a bude take baccinta take hankalinta kwance, a hankali ya zauna gefan bed din ya kurawa fuskarta ido da rame sosai duk tausayinta ya kamashi, cikin bacci hibba ta fara jin kamshin turarensa, a hnkl ta bude fararen idanunta ta sauke kanshi, murmushi yasakar mata.

"hello."

ya fada cikin sanyin murya.

A hankali ta Mike zaune tana sunkuyar da kanta kasa.

"kinci abinci? "

ya fada yana riko hannunta, kai ta daga masa ba tare da tace masa uffan ba.

Matsowa yayi kusa da ita sosai sannan ya kuma cewa.

"yah gajiyarki? "

Cikin rawar muyarta tace.

"lafiya."

"need a massage?"

Kallonshi tayi for few seconds.

"ah ah."

ta fada muryanta na dancing sosai.

Sake matsowa daf da ita yayi har suna jiyo numfashin juna cikin whisper yace.

" I insist."

Kwantar da ita yayi ba musu ta koma ta kwanta ya dan birkitata ta kwanta kan cikinta gabanta in banda rawa babu abnd yakeyi.

Sauka yayi daga gadon ya nufi gaban mirror ya dauki nitrogena sasemi oil sannan ya rage wutar dakin ya kunna Heather ya haura saman gadon.

hibba cikin ranta take addu'ar Allah ya taimaketa kar anwar yayi mata wani abun, rigar jikinta ya Fara zamewa a hankula nan beautiful skin nata ta bayyana, oil din ya zuba a hannunshi ya fara shafa mata a hankula.

Kankame pillow hibba tayi da kyau dan yarda taji hannunshi a gadon bayanta feel so great, wani irin sensitive massage ya dinga yi mata, a hankali cike da dabara ya rabata da duk kayan jikinta ya zamana daga ita sae pant da bra, jikin hibba sae rawa yake so skemπŸ‘―πŸ»πŸ€ͺhannu yasa ze 6alle bra din tayi saurin riko hannunshi murya qasan makoshinta tace.

"kabari yah anwar plz."

Hannunta ya mayar tare da idda zare brezia din, rintse ido hibba tayi da sauri hawaye na zubo mata, anwar kuwa shoke ya shiga ganin manyan hallitun jikin hibba so sexy shape, a nutse ya birkito da ita gaba ya hade kirjinta da nashi nan take wani electric bolt ya sokesu.

"precious look at me. "

Ta fada IN sexy voice.

Kara runtse eyes hibba tayi, yayi murmushi tare da zare rigar jikinshi, yayi hugging nata tight kmr ze tsaga kirjinsa ya saka a hankali ya ja bargo ya rufesu.


The following days.

Hadaddiyar dinner da mamy ta shirya masu aka gabatar a wani tsadadden hotel an kashe kudi sosai hibba da anwar sunyi kyau har sungaji.

Satinsu guda a Paris suka wuce European har da mamy sunyi yawon bude ido Sosai a kasashe da dama kafin nan suka wuce saudia nan ma sunyi ziyara da umarah sae da sukayi wata uku a yawon bude Idon da sukaje kafin su dawo Paris, hibba ta sake kyau sosai fatarta tayi wani irin luwai luwai na Hutu sai dea har ynz da ramar nan sbd ta kasa dena damuwar da take.

Ta shaku da mamy sosai fiye da anwar domin mamy tana da wayewa sosai kuma tana janta a jiki tana nuna mata soyayya da kulawa fiye da zaton mai tunani.

Anawar kullum addu'arsa Allah ya karkato da hnklnta kanshi ko zasu samu su shimfidar rayuwar auren su yarda ya kamata, wannan damuwar ta hibba itace ke damun anwar shima domin wataran ciwonsa har kokarin tashi yake idan ya ga hibba cikin damuwa.



paris

Yana zaune a parlo daga shi sae farar singlet da 3quater,yana aiki a system dinshi kallo daya zakayi masa kasan yana cikin damuwa sbd yadda fuskanshi ta nuna.

hibba ce ta fito daga kitchen sanye da pincil jeans blue da armless pink tayi parking dogon gashinta da pink ribbom babu dan kwali, coffee din da ta hado masa ta ajiye, tare da neman kujera ta zauna tana kallonshi.

Dagowa yayi tare da kafeta da ido dan ba kadanba yau tayi masa kyau, murmushi yayi mata yace.

"thank you."

Kai kawai ta gyada masa can kuma tace.

"umm nace ba inason mgn da Kai."

yadda tayi mgnr yasa anwar rufe laptop din ya dan kur6e coffee din ya ajiye sannan ya sake dubanta da kyau yace.

"ina jinki."

dan jim hibba tayi sannan ta dago kanta

Please Login or Register in order to submit comment