Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakon son ka", “to ni na taɓa cewa ki so ni ne? " Qaseem ya tambaya, Hajna tace “a'a", “to ki cire rai, ni ɗin nan bazan aure ki ba ", riƙe mishi riga tayi tana kuka tace“miyasa Qaseem", zuwa yanzu ta fara ƙular da shi, dan haka yasa hannun shi ya ture ta, sai ƙasa ta faɗi, belt ɗin jikin shi ya cire ya fara dukan ta kamar Allah ya aiko shi, ihu take yi tana kuka, tana roƙon shi, amma sai da ya mata liƙis, zuwa yanzu Hajna ta saba da dukan da Qaseem ke mata, fita yayi ya barta nan.

   Office ya nufa, yau suna da taro da  Qaseem da Farween sai shugaban su kawai, kamar yadda shugaban ya faɗa.

Office ɗin shugaban su ya nufa, zaune ya sami Farween, zaunawa yayi, gyaran murya shugaban yayi yace “Qaseem da Farween, kuna ji na? ", tare suka amsa da eh, shugaban yace “zan naɗa ɗaya daga cikin ku matsayin shugaba, amma na lura da rashin jituwar da ke tsakanin ku, saboda haka na yanke hukunci zan ba ɗayan ku, amma sai wanda yayi aure", dummmmnn gaban Qaseem ya buga, “dan haka ku je na baku sati uku duk wanda yayi aure kafin lokacin, shi zai zama shugaban wannan ma'aikatar "shugaban ya faɗa.

Anan zan dasa aya............ ✍️

To masu karatu kunji dai wata chakwakiya, shin a tunanin ku wa zai hau shugabancin nan?


Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️
[8/17, 09:43] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya


QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 37-38
************************

Gida Qaseem ya nufa cike da takaicin shugaban su, shi yanzu ya zai yi aure, bayan ko wacce yake so be samu ba, parking motar yayi cikin gida, sannan ya nufi cikin gida, ɗaki ya wuce kai tsaye.

  A ɓangaren Hajna kuwa har yanzu kuka take yi,  duk jikin ta ya kumbura kamar ba bata ba.

Qaseem kuwa wanka yayi, ya kwanta tunanin yadda zai yi yake yi, wayar shi ya ɗauka kiran yayar shi yayi bugu biyu zuwa uku tayi ta ɗauka, “hello Qaseem "ta faɗa cikin sakin rai, dogon numfashi ya ja wanda har ita tana iya jiyo haka, “Qaseem ina fatan dai lafiya?" ta faɗa cikin nuna damuwa, “Aunty, kin san na daɗe da faɗa miki ina son na mallaki ma'aikatar mu ko? ", “eh Qaseem me ya faru", “lokaci yayi da zan mallake ta "ya faɗa , “masha Allah...., bata ƙarasa maganar ta ba Qaseem ya katse ta, “Amma akwai sharaɗi", “sharaɗin mi kenan? "ta tambaya, shugaban mu ya buƙaci ɗaya daga cikin mu nida Farween akan duk wanda yayi aure nan da sati uku, shi zai hau shugabancin" Qaseem ya ƙarasa maganar cikin takaice, “to ai wannan ba matsala bace, me zai hana ka auri Hajna" ta faɗa, da sauri ya tashi tsaye yace “Hajna fa kika ce, ni bazan auri Hajna ba ", Aunty Qaseem tace “to Qaseem saboda mi, miye abun Hajna? Ni ban ga wata matsala a tare da ita ba", “to ni naga aibun ta, dan ni bazan auri macen da ta baro iyayen ta ba saboda namiji, so kike yarana su tashi da irin wannan halin, su barmu da damuwa irin yadda ta bar iyayen ta", shiru momyn Elizabeth tayi, can tace “to ya kake so ayi? ", Qaseem yace “ki samomin wacce zan aura a Lagos", “to shikenan kar ka damu, an gama ɗan uwa na"ta faɗa tana kashe, “Qaseem aure zaka yi? " Hajna ta faɗa, duk zancen nan da Qaseem ke yi akan kunnen ta, kunnuwan ta sun kasa gaskata mata, “eh Hajna, kamar yadda kika ji" ya faɗa, juyawa tayi da sauri zata bar ɗakin amma sai ji tayi ya jawo ta a jikin shi, sannan yace “kuma ki sani, yin aure na baya nufin zan dena kusantar ki, dan haka kisani ke dadiro na ce har abada ", bakin shi ya haɗa da na ta, dan kar ta samu yin magana, hannun ta tasa iya ƙarfin ta tace, “Qaseem na gaji, na gaji! Wallahi" ta faɗa tana buɗe ƙofar ɗakin da ƙarfi ta turo ƙofar ɗakin ta wuce, ɗakin ta, ta shiga karo na farko da taji ta tsani kasancewar ta duniya, kallon kanta take a madubi, ba abunda ta rasa, amma Qaseem ya ƙi ya aure ta, sai yanzu ta tuna da saurayin ta na ƙauye yana son ta har ranshi amma wulaƙanci take mishi, saboda Fahna kullum tana faɗa mata ba kalar namijin da ya dace ta aura bane, kuka take yi sosai.

Ni kuwa Nasmerh nace Hajna baki zubar da hawaye ba ma.
__________________

  Haka aka yi sati biyu Hajna bata wa Qaseem magana, ko ɗakin shi bata zuwa, idan yazo ƙofar ɗakin ta kullum a rufe, Hajna ta rame tayi baƙi, ita gurin ta kuɗin da take samu basu da amfani, dan ta tara kuɗi sosai, amma ita basu take buƙata ba, Qaseem kawai take so, yanzu da ta san zai yi aure bata jin zata iya jurar wannan wulaƙanci, bazai yuyu ba auren ta zai yi ba sannan ya cigaba da taɓa mata ciki.

A ɓangaren Qaseem kuwa, sati biyun da yayi baya magana da Hajna kuma baya ganin ta haka baƙaramin damun shi yake yi ba, shi ya rasa dalili amma yana jin Hajna a ranshi, ya kasa yadda shi ɗinnan yana son Hajna, yana cikin tunanin wayar shi ta fara ringing, ganin auntyn shi na kiran shi yasa yayi saurin ɗagawa, “hello Aunty ", “Qaseem ya kake?", “ina lafiya "Qaseem ya faɗa, “na kira ka ne dan na sanarda kai cewa na samo maka mata", murmushi ya saki, sannan yace “to ya kuka yi da ita", Aunty tace “iyayen ta sun ce nan da kwana shida za'a maka aure da ita ", farinciki fal ranshi dan yasan yasamu shugabanci ya gama, ni kuma a raina nace idan fa Farween har yayi auren shi, ta wani ɓangare kuwa Qaseem ba daɗi yake ji.

Bayan kwana huɗu, wanda ya kasance saura kwana biyu auren Qaseem , yau Hajna ta zaɓi ta fito ta zaga gida, wando ta saka baƙi, sannan ta sanya white half vest, sannan tayi parking kanta, duk wanda yaga Hajna zai san tana cikin damuwa, fitowa tayi, ƙofar parlor ta buɗe ta fita compound ɗin gidan, za gayawa tayi ta bayan gidan, inda suke yawan zama ita da Trisha, kallon wurin tayi, maganar da Trisha ta mata na ƙarshe a gurin ta tuna “Hajna watarana zaki tsane Qaseem, kar ki manta da wannan zancen ", rufe ido tayi, dan a yanzu tana tsakanin so da ƙiyayya, har aka yi magrib tana gurin, cikin gida ta shigo inda ta samu ana shigowa da kaya kala daban-daban, kallon  ko ina take da mamaki, dai-dai lokacin Qaseem ya shigo “Hajna, wannan kayan fitar biki ne, jibi za'a kawo amarya, ɗakin ki zata zauna, dan haka ki zauna ɗakin Trisha na da, ki fara kwashe kayan ki, gobe zan sa a canza kayan ɗakin, anjima kaɗan za'a canza kayan Parlorn nan", Hajna kuwa yana gama zance ta juya ta wuce bata amsa shi ba, kallon ta yake yadda take tafiya, da sauri ya tari gaban ta yace “Hajna wai wannan duk na minene, saboda naƙi auren ki shine kike fushi dani ", “ni ba matar ka bace, ba buƙatar sai ka kawo min wasu kayan biki, sannan kuma ka fita a hanya ta Qaseem, buri na auren ka, yanzu ka ruguza min shi, dan Allah Qaseem ka barni" ta faɗa hawayen da take riƙewa suka zubo, da gudu ta juya ta fita, shi kuwa Qaseem girgiza kai kawai yayi ya wuce.


Anan zan dasa aya............. ✍️

Haɗin guiwar : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️😍❤️❤️❤️❤️
[8/17, 09:44] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya


QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 39-40
***********************
Ɗaki ta shiga, inda ta shiga haɗa kayan ta kamar yadda Qaseem ya faɗa mata ta koma ɗakin da Trisha ta bari, cikin kuka ta kwashi kayan ta fara kaiwa, tare da taimakon Adaku suka kwashe kayan duka, sannan suka gyara ɗakin, dan ɗakin tun bayan rasuwar Trisha ba mai shiga ciki, zaunawa tayi tana tunani, yanzu Trisha ta sake faɗo mata a rai, “ Hajna idan kika ga Qaseem ya aure ki, to dama a ƙaddarar shi an rubuta haka, nasan wanene Qaseem, haka nan bazai aure ki ba " hawaye suka zubo mata, tun daren ranar aka canza kujerun gidan.

     Washe gari da safe aka kwashe kayan ɗakin da Hajna ta bari, wasu haɗaɗɗin kaya ne, sai ɗakin ya ƙara kyau kamar bashi ba, har dare ana ta hada-hadar biki, Hajna kuwa bata fito tana ɗaki zazzaɓi mai nauyi ya rufe ta saboda kukan da ta kwana tana yi, Adaku ce ta shigo ɗauke da kofin ruwan tea, tashin Hajna tayi zaune, “kisha wannan zai warware miki hanjin ciki ", karɓa Hajna tayi tasha, sannan Adaku ta mata allura kasancewar Adaku nurse ce, wayar ta, ta ɗauka ta kunna data, status ɗin Qaseem ta duba, inda taga hoton kamun da ake yi yau, shiyasa tun da safe ya hau jirgi zuwa Lagos, amaryar kyakkyawa ce sosai, da alama zama ya kai su Lagos dan jikin ta ya nuna bafulatana ce, bata shiri wasu hawayen suka zubo mata masu zafi.

NI KUWA NASMERH NACE HAJNA KAƊAN KIKA GANI, SAI TA SHIGO GIDAN MA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.

Qaseem taron bikin kawai ake amma shi amaryar bata mishi ba ko kaɗan, kawai shi da buƙatar shi ta biya zai kora ta gida, dan shinta mishi ƙaranta.

Hajna tana ganin kiran Fahna amma bata ɗauka ba, dan ta san maganar auren da Qaseem yayi zata mata magana, ita kuma bata da abun cewa, tana zaune taji shigowar Qaseem, agogon ɗakin ta kalla taga har ƙarfe 3:30,a ranta kuwa tunanin me ya dawo dashi gida yanzu tayi, miyasa ya dawo gida a irin lokacin nan.

Kiran Fahna ne ya shigo cikin wayar ta, ɗagawa tayi tace “Hello Fahna ya kike", Fahna tace “ke ni ba shi na kira ki in ji ba, wai da gaske Qaseem aure zai yi? ", “hmmmm" Hajna ta fa&a tare da jan dogon numfashi, “Hajna amma an yi sakaryar mace, ki biyo namiji kuma ki bari yana miki iskan ci, da nice tuni ban ci uwar shi ba! ", Hajna tace “Fahna ke kika ce, ni ba ke bace", dariya Fahna tayi tace “gobe zan zo ai, sai mun koyawa amarya hankali ", Hajna tace “ni bana son tashin hankali, ai ba laifin ta bane, tunda ita bata ma san da zama na gidan ba", Fahna tace “kai amma anyi ɗan tsiya, wallahi Qaseem ya raina hankalin mutane, ke wallahi dole gobe na zo, dama jiya na dawo daga Jigawa gurin oga, ina Abuja yanzu hakab, shine fa Alhaji musa yake faɗa, da yake ɗazu muna tare ", Hajna tace “au wai ke dama baki sani ba", “to Hajna ina zan sani, sati na biyu Jigawa, kuma kafin na je Jigawa kin san na gaya miki zan je sokoto sati biyu nayi can, na biya gida naga inna sannan na wuce Jigawa ", Hajna tace “wayyo Allah sarki, kin ga Umma", Fahna tace “ke ni rufa min asiri, so kike a kama ni, kinsan kowa ya san ni kika bi, shigar dare nake yi ai ", murmushi Hajna tayi wanda yafi kuka ciwo tace “Allah sarki Baffa", Fahna tace “Hajna kinsan dai ba yadda za ayi ki koma ajiyawa sai da Qaseem ko, to kima daina tunanin su Baffa, kiyi tunanin yadda za muyi maganin Qaseem ", “Fahna ba wata hanya, ni buri na shine na bar mishi gidan shi, dan zuwa yanzu na gane Qaseem bazai taɓa sona ba", Fahna tace “ke kullum sai kace ba mace ba, za ki iya jan ra'ayin shi har ya aure ki", Hajna tace “jawo hankali nawa, Fahna tabon dukan da Qaseem ke min nasan har abada bazai ɓace ba, na bauta ma soyayyar shib, ta ko wace hanya, ciki har da barin gidan mu da nayi, to miyayi saura banda wulaƙanci da gori da nake fuskanta a gurin shi, Fahna a idon Qaseem kare ma ya fini ", kuka Hajna ta fara, Fahna tace “Allah ya saka miki, Allah ya bi miki haƙinki, wallahi ya cuce ki, kiyi haƙuri, gobe za muyi cin uwa ni da shi", sun jima suna waya sannan suka yi sallama da junan su, akan gobe tun da safe zata zo.

Qaseem kuwa yana kwance da misalin ƙarfe 4:00 dai-dai aka kira shi a waya, da sauri ganin me kiran shi yasa ya ɗauka, mi zai sa a kira shi yanzu, “Hello Qaseem", “hello aunty "ya faɗa cike da zumuɗin son jin me ya faru take kiran shi yanzu, “kayi haƙuri na tashe ka" ta faɗa, murmushi yayi yace “babu komai yasu Elizabeth ", “suna lafiya" ta faɗa, Qaseem yace “me ya faru kika kira ni ", shiru tayi rasa yadda zata kama, can tace “Qaseem kayi haƙuri da ƙaddara ko wace iri ce", cikin rikicewa yace “me ya faru? ", “Fateema ta rasu"ta faɗa, “wace Fateemar" Qaseem ya tambaya cikin rikicewa, “wacce zaka aura "Aunty ta faɗa, Qaseem yace “amma me ya same ta, lafiya ƙalau fa na barta", Aunty tace “a cewar iyayen ta suna komawa gida ta fara ciwon ciki, ƙarfe 3:00 na dare suka nufi asibiti da ita, yanzun nan aka faɗa musu ta rasu", dafe kai yayi yace “ohh my god, yanzu ya zan yi, kwana biyu kawai nake da yau da gobe, kuma gobe yace mu dawo da misalin ƙarfe bakwai da rabi, aunty yau fa ya kamata a ɗaura auren", Aunty tace “ ka auri Hajna kawai, dan yanzu ba wanda zai aurar da ƴar shi nan da kwana biyu ", dafe kai yayi yace “ni bazan auri Hajna ba fa", Aunty tace “Qaseem ka saurare ni da kyau, babu ƴar da zata aure ka nan da kwana biyu, sai karuwa, dan gidan su ba'a shirya ba, sannan kuma indai budurwa ce zata so tayi wani party, to ko wannan Fateemar da ƙyar aka samu gidan su suka yadda, zaka iya auren Hajna bayan bikin da wata biyu haka komai ya daidaita zaka iya sakin ta, sai ka kama gaban ka", “ohhhh yes kin kawo shawara haka za'a yi ma" ya faɗa.

Anan zan dasa aya................ ✍️

Haɗin guiwa :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
[8/17, 09:44] Queen Nasmah✍️: ♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 41-42
**********************
Tana kwance kan gado Fahna ta shigo, ɗakin Hajna ta nufa inda ta samu an canza kayan ɗakin, "kan uba, badai yana nufin ya canza wa Hajna ɗaki ba", fitowa tayi kai tsaye ta nufi ɗakunan da ke ƙasa, wani ɗaki ta leƙa inda taga Hajna kwance, "ke dallah tashi" Fahna ta faɗa, da sauri Hajna ta tashi, idon nan nata duk sun kumbura, "ke wace irin yarinya ce, ya za'a yi ki zauna kina wa namiji kuka, ke da ya kamata ku gwabza, gobe ko ance yayi wa wata bazai yi ba" Fahna ta faɗa, Hajna tace "ni Hajna bana son tashin hankali", Fahna tace "tashi dai kiyi wanka, fita za muyi yawo ", Hajna tace "ba inda zani wallahi", Fahna tace "ki zauna baƙin ciki ya kashe ki ", Hajna tace "Fahna ai na daɗe da mutuwa ni, kawai gangar jiki na kike gani", Fahna tace "to ki dai tashi kiyi wanka", tashi Hajna tayi, toilet ta shiga tayi wanka, ta fito, wata atamfa ta saka wadda tasha ɗinki da wani net mai shegen ƙyali-ƙyali, wanda yayi matuƙar ƙarawa ɗinkin kyau, ɗauri Fahna ta mata kamar ture kaga tsiya, jan baki kawai ta ƙara kan kwalliyar fuskar ta, tayi kyau kamar ba ita ba, parlor suka fito suka ci abinci, har yanzu Hajna bata ga Qaseem ba, wanda haka yayi mugun ɗaga mata hankali, suna zaune a parlor har ƙarfe 12:30

A ɓangaren Qaseem kuwa yaje a ɗaura mishi aure da Hajna, inda ya nemo waliyan amarya na ƙarya, sannan aka ɗaura auren ta akan sadaki mafiƙanƙanta a cewar shi, naira dubu 20.

Cikin gida ya shigo inda ko ina ya hargitse da hayaniya, kowa yana so yayi hoto da amarya, shi ya fara shigowa yace "Hajna ki biyo ni muje ɗaki ", Fahna tace "ba inda zata macuci, azzalumi ka raba ta da gidan iyayen ta sannan kazo kana ci mata fuska, yanzu me zata maka in ta bi ka ɗaki" ta faɗa tana watsa mishi mugun kallo, da kallon yake binta kafin yace "ni da ke waye ya ɗauko ta daga gidan su ", Fahna tace "da nasan sakarai ne kai da bazan bari ta zo ba, kai kafi dabba ma", hannun shi ya ɗaga zai mare ta, ta riƙe hannun tare da yarfarwa, "ni ba Hajna bace da zaka sa ma hannu, duk ranar da hannun ka ya hau jikina wallahi shari'a zata rabani da kai, ba ruwana da ko kai waye, dan doka ce zata yi aiki akan ka, wawa kawai ", shiru yayi yana mai jin taƙaici yau shi Qaseem ake zagi, juyowa yayi kan Hajna yace "ki saurare ni plss", ba musu ta tashi ta bishi, Fahna ta ja tsaki tace "kinji haushi wallahi, dan ni bana son sakarci ", komawa tayi ta zauna.

Ɗaki suka shiga yace "Hajna yanzu kin zama matata, abokanai na suna waje zasu shigo ayi hoto, ina buƙatar haɗin kanki", "bangane matar ka ba", "eh Hajna burin ki ya cika an ɗaura auren mu" Qaseem ya faɗa, Hajna tace "ita fa waccan? ", "ta mutu yanzu ba lokacin tambaya bane, ni na dakatar da su dan Allah kar ki bani kunya", fitowa yayi ita ta biyo bayan shi, Fahna na zaune taga sun fito"kin dawo daga gurin ƙanin uban naki ko", Fahna ta faɗa, Hajna tace "Fahna wai auren mu aka ɗaura", Fahna tayi sauri buga ƙirji tace "ke da waya", Hajna tace "Qaseem mana ", Fahna tace "ke kiji ɗan akuya miyasa ya aure ki bayan wata zai aura?", Hajna tace "wai ta rasu ", "shine ya aure ki ko, matsiyaci kawai", Hajna za tayi magana kenan Qaseem da abokanan shi suka shigo, nan suka dinga tsokanar shi wai ya ɗauke wacce tafi kowa kyau ko, shi dai kawai bin su yake da ido, hotuna aka dinga yi, har da su Fahna 😂babbar aminiya.

Bayan an gama ne Qaseem ya bisu suka fita, Fahna kuwa itama tafiya tayi, a cewar ta ta zazzage abunda ke cikin ta dan haka bata ga ta zama ba.

Hajna kuwa ɗaƙin Trisha ta koma ta kwanta, Qaseem ne ya shigo, ɗakin ya nufa inda ya tashe ta suka fito parlor, kallon ta yayi yace "Hajna kin dai san munyi aure ne badan na so ba ko ", shiru tayi bata ce komai ba, yace "to ki shirya zaman ƙunci a gidan nan har ƙarshen rayuwar ki, sannan ki sani aure na da ke ba me ɗaurewa bane, na ɗan lokaci ne, nan da wata uku zan sake ki, kuma ki sani watan nan uku yadda nake jin ƙuna na auren ki sai kin ji abinda yafi haka ", hawaye kawai ke zubo mata, yace "gara ki fara kuka dan kuka za ki yi shi ne har ƙarshen rayuwar ki, baki da daraja a ido na, Hajna darajar ki ta zube tun daga ranar da nasan ki a matsayin a mace, wato tun daga ranar da na karɓi budurcin ki", tashi tayi tace "ba sai ka cimin mutunci ba, nagode da ka faɗa min matsayi na a gidan nan", tashi yayi ya mare ta, faɗuwa tayi ta buge fuskar ta da center table, sai jini, amma be ma lura ba, ya cire belt ɗin shi ya hau dukan ta, tashi tayi tana bin bango ta wuce zuwa ɗaki, "keeee"ya daka mata tsawa, da sauri ta juyo cikin firgici, "ki kuma tsohon ɗakin ki ", shiru kawai tayi ta juya zuwa ɗakin da aka gyara domin amarya, kwanciya tayi tana kuka, tayi nadamar abunda ta aikata, yau take nadamar barin su Umma da tayi, masoyan da bata da kamar su, Allah sarki Baffan ta, yana ji da ita yadda ba'a tunanin, son ta ne yasa kullum yake mata nisaha akan rayuwa, amma yau gashi ta ƙare a gaban mutum wanda be san minene so ba,"Baffa na, ina fatan wata rana ka samu guri a zuciyar ka ka yafe min, Umma kema haka, bana tunanin zan iya dawowa gare ku, saboda na aikata babban zunubi, bani da ƙwarin guiwar da zan fuskance ku" ta faɗa tana kuka.

Washe gari tun da safe Qaseem ya shigo ɗakin ta, kwance ya ganta ƙasan carpet, da alama bayan tayi sallar asuba ta kwanta, dan har da hijab a jikin ta, toilet ɗin ta ya shiga, ruwa ya ɗebo bokiti ɗaya, ya shiga kwarara mata a jiki, tashi tayi firgice, amma haka be sa ya daina ba, har sai da ruwa suka ƙare ƙaf, da ƙyar take fitar da numfashi, saboda dama lokacin sanyi ne

Please Login or Register in order to submit comment