Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamata suka nufi wajen da motarsa take, ya bud'e mata Hajna ta kallesa ta ce "Yaya ina zamuje??" Farween ya ce "Asibiti" Ya bata amsa a takaice, Hajna tayi raurau da ido ta ce "Noorul Qalbi ba na so" Da sauri ya kalleta ya ce "Bakya so kuma?? Me ki ke nufi da bakya so kina nufin zan zuba ido nayi ta kallonki kina cikin ciwo ba zan kai ki asibiti ba" Hajna ta yi shuru idonta yana zubar da hawaye bata iya cewa komai ba, Farween ya ce "Shiga mota muje" Hajna ta shiga motar tana goge hawayen fuskarta, Farween ya kulle kofar motar ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya ja motar suka nufi asibiti, babban asibiti ne wanda ya amsa sunansa ko ina tsaf-tsaf yake fita sukayi office d'in babban likita suka huce bayan gwaje-gwajen da akayi mata aka tabbatar tana d'auke da ciki tsawon sati uku kenan, doctor ya kalli Farween yana murmushi ya ce "Congratulations Matarka tana d'auke da ciki tsawon sati uku".

Anan zan dasa aya............................👩🏼‍🦯😂♻️

ALQALAMI YAFI TAKOBI⚔️
[8/31, 18:50] Queen Nasmah✍️: *♻️♻️HAJNA♻️♻️*

Mallakin: Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Page 95-96
**********************'
Ya kalli Farween yana murmushi yace “Congratulations matarka tana ɗauke da ciki na tsawon sati uku ", ware ido yayi with much surprise yace “Alhamdulillahi ala kulli hal", likita yace “amma akwai matsala, cikin bai zauna da kyau ba, kasancewar a da can baya tana amfani da ƙwayoyin hana haihuwa, wannan ne yasa cikin zai matuƙar bata wahala, fiye da tunaninku ", “yanzu likita ya zamu yi?" Farween ya faɗa yana ɓata fuska, “ zamu ɗaura ta a kan magunguna, sannan kuma zata riƙa zuwa asibiti duk bayan kwana huɗu ɗomin a duba lafiyar abunda ke cikinta" likitan ya faɗa, wanda haka yayi dai-dai da fitowar Hajna daga ɗakin da aka duba ta, alamu sun nuna ta ji duk abunda suka faɗa, da sauri Farween ya iso gabanta ganin hawaye a idonta, faɗawa tayi jikinshi tare da fashewa da kuka me tsuma rai, maida hannunshi yayi ya kan bayanta, tare da bubbuga bayanta alamar rarrashi, “Hajna ba kuka zaki yi ba ", ɗagowa tayi tace “dole na yi kuka, duk abunda mutum yayi zai girbi abunshi, lokacin da ina shan maganin ban hango ranar yau ba, amma yanzu na fahimta" ta ƙarasa maganar hawaye na bin kuncinta, hannunshi yasa ya share mata hawayen “ki yi shiru kinji, ni zan tsaya miki a kowa ne hali, kinyi kuskure amma kin gyara, dan haka ki manta baya ki fuskanci rayuwarki ta gaba, tare da yaranmu ", idonta da suka cika da ƙwalla ta zuba mishi ta fi minti uku tana kallonshi, be hanata ba, sai ma ƙura mata ido da yayi shi ma, “kai ɗinnan kullum kana sa rai a kaina, amma bana jin na cancanci haka" ta faɗa tana ƙoƙarin haɗe hawayen fuskarta, hannunshi guda biyu ya ɗaura akan ƙugunta, sannan yace “ina sa rai ne, saboda ina sonki, wanda yake sonka, Hajna ki sani bazai taɓa cire rai ba, zai baka dama ne har ka gane gaskiya, dan haka kar kiyi tunanin zan cire rai a kanki, ki saka a ranki, zamu raini wannan cikin kuma insha Allah zamu ga ɗanmu a duniya ", cikin yanayin mutuwar jiki ta ɗaura hannunta a fuskarshi “ka cika min rayuwata, wani bai taɓa sona ba kamar yadda kai ɗinnan kayi, ka bani asalin farincikin da nake nema, bazan rayu in baba kai ba, duniyata zata cika da duhu idan na rasa ka", rungume ta yayi, sun ɗauki kusan minti goma (10) a hakan, sannan ya sake ta suka nufi hanyar gida.


---------------------------------------
A Ɓangarenshi Inna kuwa komai ya rikice mata, musamman in ta tuna da Fahna, nadama da ƙunci duk ya cika ta, gashi kwanan nan tsufa duk ya rufe ta, ko tashi bata iya yi, a inda take zaune nan take kashi, tayi fitsari, ga yunwa ta kusan kashe ta, gashi tun bayan auren Hajna Farween ya ɗauke su Inna daga wannan gidan, Baffa be so barin ajiyawa ba, amma baya da zaɓi, saboda haka su ka wuce, wani babban gida Farween ya siya musu a cikin garin gusau, sannan ya buɗewa Baffa babban shago, yanzu arzikin Baffa ya haɓɓaka sosai.


Hawaye su ka zubo Inna, ta san ita ce alhakin duk abunda ya samu Fahna, gashi yanzu tana girbar abunda ta shuka, yau da ace ta reni Fahna yadda baba ya so, kuma ta mata tarbiya, da yanzu tana raye wataƙila ma tayi aure, mijinta ne zai ɗauki nauyin ciwon da take yi, amma yanzu da ta biyewa son duniya gashi ta rasa Fahna kuma ta rasa komai nata, bata da komai yanzu sai rai, ga tsufa ya kamata, sanadiyyar son zucuyarta Baba ya mutu.

***********'******************************************************************
Rayuwar Hajna ta canza sosai samun Farween a matsayin ciki, kwanaki sai tafiya suke yi, yau wata huɗu kenan, cikin Hajna ya fito sosai in ka gani sai ka rantse yau zata haihu, dan cikinta ya girma sosai, wata huɗu ba masu sauƙi ba ne a gurin Hajna, dan yanzu tana da ƙarancin jini, saboda yawan zubar jinin da take yi, yau zasu koma asibiti, dan haka ta shirya tsaf cikin wata dakakkiyar shadda doguwar riga, yanzu bata aikin komai a gidan Farween ya maye gurbin duk wani aiki nata a gidan.


Mota suka shiga tare, tafiyar minti talatin suka yi zuwa National hospital Abuja, office ɗin ganin likita su ka nufi, sunyi sa'a ba layi, dan haka suka yi knocking aka basu umurnin shiga, guri suka samu suka zaune , “kun dawo kenan" likitan ya faɗa, Farween yace “eh doctor mun dawo ", kallon Hajna likitan yayi, ganin yadda tayi fari ta kumbura yasa shi gyara murya yace “gaskiya in zan baku shawara ku yi haƙuri a zubar da cikin nan, idan ba haka ba zaka iya rasa matarka, dan jinin nan bazai daina zuba ba", “a'a likita bazan sake aikata wani kuskuren ba, idan har ƙaddarata ce na mutu na yadda, amma bazan goyi bayan kisan kai ba "Hajna ta faɗa, Farween yace “doctor ba wata hanya", Likita yace “hanyar biyu ce, ko dai ku bari a cire cikin yanzu, ko kuma ku dawo nan da wata uku a mata tiyata a fidda yaron ", Hajna tace “sai dai ayi min tiyata, amma bazaka cire min ciki ba", hannunta Farween ya riƙe “calm down Hajna, babu wanda zai zubar da cikinnan, insha Allah zaki haife koma minene ", likita yace “Allah yasa, muma muna fatan haka ai, kuma kun ƙi bari a mata scanning ballanta a san lafiyar jaririn, sannan asan ko nawa ne, dan girman cikinki bana tunanin ɗaya ne", “idan na haihu zaka gani, yanzu bana son sanin abunda ke cikina ku bar ubangiji yayi hukuncinshi ", Farween yace “doctor mun gode", wasu allurai aka mata, sannan ya ƙara rubuta wasu magunguna yace “ki aje shan waɗancan lokacinsu ya wuce, ki farada wannan ", “to na gode" ta faɗa tana fitowa.



Tana shika mota ta kifa kanta a cinyarta, ta shiga kuka. “wifey kukan ne minene ", ɗagowa tayi da idonta da suka yi ja tace “kalli yadda nake wahala akan abunda nayi", “baki yarda da ƙaddara ba kenan "Farween ya faɗa, “na yarda" ta amsa mishi, “to bana son matata ta sake zubar da hawaye indai akan wannan ne", gaɗa mishi kai tayi, murmushi yayi yace “yauwa shalelen Farween, yi murmushi ", dariya ta ɗanyi saboda yadda ya marai-raice fuska kamar marayan jaki.


*********************************************************************************

Bayan wata uku

“Baffan Hajna, magana nake ta yi amma kayi shiru, ina fatan dai lafiya" Umma ta tambaya taba zama gefenshi, “tunanin Hajna nake yi, ɗazu mijinta ya kira ni suna asibiti, wai za'a mata aiki a ciro abunda ke cikinta ", Umma tace “Allah dai ya bata lafiya, abun ba daɗi, ni so nake ka bar na je can", girgiza kai Baffa yayi yace “idan tayi kwana arba'in za'a kawo miki ita ki ga jikinki ko jakarki", badan umma ta so ba haka ta haƙura dan ta san Baffa bazai bari ba.


*****************************

Wasu allurai aka mata, cikin lokaci ƙalilan ta ɗauke wuta, dan haka aka shiga yi mata aiki, inda suka ciro yara huɗu, masu kyau, mata biyu, maza biyu, likitocin sun matuƙar mamaki, ɗinki aka mata sannan suka yima jariran wanka, murmushi likitan yayi ganin yadda yaran ke wasa da hannayensu a hankali yace “yaran yanzu da wayau ake haihuwarsu ". Farween dake tsaye gaban ɗakin yana jira fitowar likita, wata nurse ta sama, “Congratulations an ciro ma matarka yara huɗu, mata biyu maza biyu", cikin rashin yadda da zancenta ya wuce ta tare da shiga ɗakin da sauri, “ barka da arziki Farween "likitan ya faɗa yana nuna mishi yaranshi, da sauri ya isa gabansu, idonsu har yanzu a rufe yake amma suna wasa da hannayensu, ɗaukar su yayi yayi musu kiran sallah da huɗuba a kunne.


“Za a dakatar da haihuwar matarka, saboda rayuwarta na cikin hatsari, idan haka ta sake faruwa, kuyi imani, sannan ku yi tawakkali, waɗannan da kuka samu ina fatan Allah ya raya muku su ", “Ameen" Farween ya faɗa, dan gaskiya bazai juri ganinta cikin ciwo haka ba, juyar da mahaifar aka yi, akan bayan shekarar biyar za'a juyo da ita dai-dai, kiransu Umma yayi ya faɗa masu abunda ke faruwa, addu'a suka yi akan Allah ya raya waɗanda aka samu, a cewar Baffa ai ko su sun isa wasu suna neman yaran Allah be basu ba, wasu ma ɗaya gare su, ballantana ita da Allah ya albarkace ta da yara ɗai-ɗai hur huɗu.



Bata farka sai dare, lokacin Farween ya gama sallah, yunƙurin tashi take yi, Farween yayi saurin tashi ya riƙeta, “ki kwanta ki huta " ya faɗa, “ina babyn?" ta tambaya tana rufe ido, murmushi yayi yace “rufe idonki ", bata yi musu ba ta rufe, gadon yaran ya turo har zuwa gabanta yace “yanzu zaki iya buɗewa", buɗe idonta tayi a hankali ta sauke su a kan yara guda huɗu, wanda yaran sai faman barci suke yi abunsu, kasa ɗauke idonta tayi akan yaran, wani sonsu take ji yana rasa zuciyarta, “ki faɗi sunan da kike so a saka musu ", “duk abunda kake so ni shi nake so" ta faɗa, murmushi yayi, sannan yace “zaɓinki nake so ", murmushi ta mayar mishi tace “wannan Hajja, wannan Ummeed, wannann kuma Muffadal, da Mahfuz"ta ƙarasa maganar tana nuni da kowannen su , murmushi yayi yace “ashe kin iya zaɓen suna har haka", “hmmm kai ko "ta faɗa tana shafa gefen fuskarshi.


Ranar suna ba'a yi wani taro ba saboda Hajna na asibiti, har yanzu, sannan yaran an saka su a kwalba, kasancewar bakwaini ne su. Watan ɗaya a asibiti, Farween ma nan yake kwana, yau za'a sallame su dan yanzu ta samu sauƙi sosai, dan haka daga nan kai tsaye Zamfara zasu gurin su Umma.



A mota Farween sai tsokanarta yake yi, “ni fa, ka daina "ta faɗa, “anƙi ɗin lokacin da kina da ciki ba haka kike yi ba", Hajna tace “to ai ya wuce ko ", Farween yace “ni kuma ai tunawa na yi", kallon Ummeed da Mahfuz da ke jikinshi yayi yace “kin gansu sai sauraren mu suke yi ", Hajna tace “ba ruwan yarana, inda me Hajja da Muffadal kace wannan kam" ta faɗa tana shafa fuskarsu, dan rabawa suka yi, kowa ya ɗauki biyu, Farween yace “su da kika raina ko ", Hajna tace “ai irin kunnen Abeeynsu gare su", haɗe fuska yayi kamar zai yi kuka, Hajna ta fara dariya tana tsokanar shi, wai me kunnen zomo.


-----------------
“Gaskiya ni ajiyawa zan tafi, nayi kewar can ", Umma ta faɗa, Baffa yace “to ki shirya mana sai mu je, kinga sai muyi shigar marece can", “haka za'a yi ko zuwa bayan isha'i sai mu dawo ", Baffa yace “mu dai kwana can", Umma dace “ni wayata bata ma da caji ", “idan mu je can zai kiyi caji ai" ya faɗa, bata ɗauki kaya ba dan tana da kaya a can. Ko da su Hajna su ka iso Umma da Baffa sun wuce, da suka tambayi maƙociyarsu, sai tace musu Umma ta kawo masu mukulli sun wuce ajiyawa. Juya mota suka yi zuwa ajiyawa.


Gidan Innar Fahna su ka shiga, tun a ƙofar gida suka fara rufe hanci, dan gidan duk wari yake yi, kwance take bakinta duk ya juye, gashi kuturta ta kamata saboda ƙazanta, ko ina na gidan wari yake, “subahanallah "Baffa ya faɗa ganinta haka, kuka Inna ta fara yi, itama Umma kuka take yi, duk imani ya cika su, “kikkk ki yafe min" Inna ta faɗa daƙyar, Umma tace “har so nawa zaki roƙe mu gafara ", Inna bata sake cewa komai ba sai kuka da take ta faman yi, magana wahala take mata, dan wani mugun ciwo take ji a moƙoshinta.


Isowar su Hajna kenan, wani yazo da gudu ya duƙa gabansu “Allah ya ƙara maka nasara, ɗan girma", Ameen suka faɗa a tare, Hajna tace “Halle kana nan baka canza ba, Allah ya shirye ka", “ameen Hajnono "ya faɗa, Hajna tace “ina su Umma suka shiga", Halle yace “sun shiga gani tsohuwar, kinsan tun bayan aurenku da sati biyu ta fara wani mugun ciwo, ba me shiga gidan, dan wari ", “Subahanallah, shi ne baka kira ni ba na faɗa maka ka kira ni idan da matsala ba" Farween ya faɗa, Halle yace “Ina fa zan kira ka tunda ba ƴar uwarka bace, matar can ƴarta na so kamar hauka, Hajna sheda ce, amma taƙi amincewa wai ni bani da maiƙo, to ai gashi nan ta janyo ruwa sun ci ta, yanzu wa gari ya waya ", Hajna tace “Allah dai ya kyauta", “waɗannan yaran fa "Halle ya faɗa,Farween yace “ina zaka lura surutu ya saka ka gaba", “yarana ne"Hajna ta faɗa, Farween yace “yarana dai ", “kai masha Allah yara, duɓul-duɓul da su" Halle ya faɗa yana kallon yaran, Kuɗi Farween ya dunƙule ya ba Halle, “Allah ya ƙara buɗi, kin gani Alhaji ya bani dubu biyar "ya ƙarasa maganar yana ƙirga su, “ka gode Halle" ta faɗa, sannan su ka shige cikin gidan Inna.


Da sallama suka shiga, inna na gani Hajna ta fashe da kuka me tsuma zuciya, ita kanta Hajna bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba, Umma ta karɓi yaran tana nuna na inna da ɗaɗɗaya, “yaran Hajna ne" ta faɗa, “Allah ya raya mikkk ki suu" Inna ta faɗa daƙyar, sun jima gurin inna sannan suka fito gaba ɗaya, inda Farween yayi da wani likita akan ya zo ya dubata, anan Shinkafi.


******************************************

BAYAN SHEKARA HUƊU


Inna ta samu sauƙi sosai, dan ta samu kulawa sosai yadda baku tunani, yanzu ta koma zama tare da su Umma, yanzu kam baffa ya zama shahararren ɗan kasuwa, Allah ya buɗe mishi hanyoyin arziki ta ko ina.


A ɗayan ɓangaren kuma

Yara ne tsaye a gaban madubi “waya fi wani dogon hanci? "Farween ya faɗa yana ɗauke da wata ƴar ƙaramar yarinya da bazata wuce shekara ɗaya ba, Hajna daga gefe tace “ni dai bani Maryam na mata wanka, kaga Faheem har yayi barci" ta faɗa tana nuni da ɗan yaron da ke kwance kan gode, kamarshi da yarinyar da ke hannun Farween ta ɓace, kuma bada kowa su ke kama sai Hajna, miƙa mata yarinyar yayi yace“ni bari na sauka da su Hajja down stairs in yaso sai ki zo da su Maryam daga baya, nasan Faheem sarkin rigima ne bazai yi minti biyar yana barci ba in dai irin yanzu ne ", Farween yace “kamar ga sani" ta faɗa tana buɗe ƙofar toilet, Mahfuz yace “Abeey na fi su hanci fa ", Farween yace “ai lokacin wasa ya wuce mu je down stairs mu jira Maminku ta zo", Ummeed tace “to " a tare su ka ruga da gudu, “ku bi a hankali kar ku ji ciwo", Hajja tace “a'a fa ba zamu ji ciwo ba", Muffadal yace “Abeey ai ka ce kana mana addu'a ko ", “to na ji mu je".


Down stairs suka sauka tare, abinci suka jera a kan dinning table, suna zaune Hajna ta fito, ɗauke da yaranta guda biyu, Farween ya tashi ya karɓi Faheem hannunta, sannan su ka zauna suna cin abinci, ƙa'ida ce idan suna cin abinci ba'a magana. Bayan sun kammala ne suka kwashe kayan zuwa kitchen, tv'n da ke kunne ce ta fara magana kamar haka “A yau ne muka samu labarin rasuwar wani attajirin mai kuɗi da aka kama shekaru huɗu da suka wuce, mai suna Qaseem, a rahoton da muka samu mun samu labarin cewa Allah yayi mishi rasuwa ne sanadiyyar doguwar jinya da yayi a gidan yari, inda muka samu labarin cewa ya mutu ne sanadiyyar cutar nan ta zamani, wato HIV, ya rasu ne da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar yau, tare da ni da ɗauko muku rahoto Sumayya Al-mustapha na ke muku sallama" dummmm! Gaban Hajna ya faɗa, Faheem ya fahimci yanayinta, dan haka ya juyo da ita ta fuskance shi, shafa fuskarta yayi yace “ki kwantar da hankali, na samu bayanai akan Qaseem, a taƙaice ma ni na ɗauko mishi likitan da ke duba shi, ya kamu da cutar ne shekaru biyar da suka wuce, lokacin baku tare ", “ni nasan bani da cutar ai, dan na je asibiti tare da Umma kafin aurena, kawai dai ina tunanin yadda duniya ta ke, duk iya abunda kayi zai dawo maka, duk yadda ka daɗe zai dawo maka", murmushi yayi yace “ina sonki matata", kwantawa tayi a ƙirjinshi tace “ina sonka mijina ", su Ummeed da ke zaune suka ce “ muna sonku mu ma", “Abeey da mami na sonku "Hajna ta faɗa tana share hawayenta, Farween yace “kuka ba naki ba ne, kina da yara kuma kina da ni, kukan me zaki yi" murmushi ta mishi, shi ma mayar mata yayi.




ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!

DUKKAN YABO SUN TABBATA GA ALLAH ME KOWA ME KOMAI DAYA BANI IKON GANIN NA KAMMALA SHI, INA GODIYA GARE KU, BADAN SOYAYYARKU GARE NI BA DA BAN KAMMALA SHI BA.


RABI'ATU NAYI KEWARKI SOSAI, READER'S KUYI HAƘURI KAMAR YADDA KUKA JI HAƊIN GUIWARMU NE AMMA MATSALA TA FARU WANDA ALLAH BE BATA IKON YIN TYPING BA.


NOTE: NA FUSKANCI ƘALUBALE GURIN RUBUTA LITTAFIN NAN , AMMA SONDA KUKE MA LITTAFIN SHI YA ƘARA MIN ƘARFI HAR NA SAMU NA KAMMALA.

BAYANI : A WANI ƁANGARE KUN JI HAUSHI A LABARIN NAN SABODA ABUBUWAN DA SUKA SAMI HAJNA.

HAJNA TA BAR GIDA NE BADAN KOMAI BA SAI DAN SOBODA SO, SOYAYYAR QASEEM ITA TA RUFE MATA IDO HAR TA JEFA KANTA GA HALAKA.

KUYI HAƘURI DA MUTUWAR TRISHA A LABARIN NAN, NA CIRE TRISHA NE SABODA IDAN TRISHA NA DUNIYA BAZATA BARI HAJNA TA BAR GIDAN QASEEM BA HAR TA FARA SHAYE-SHAYE, DOLE NE NA KAWAR DA ITA DAN NA CIMMA ABUNDA NAKE SO A LABARIN.


WASU DAGA CIKIN KUN SUN JI HAUSHI DA HAJNA TA FARA SHAYE-SHAYE, TO ƘUNCI YANA SA SHAYE-SHAYE, A INDA HAJNA TAKE NA TURBAR SHAIƊAN BATA WANI ZAƁI DA YA WUCE SHAYE-SHAYE, KUMA HAKA TSARIN LABARIN YA ZO DAN YANZU HAKA NA FARUWA A DUNIYA SOSAI, DAGA BIN MAZA SAI HARKAR SHAYE-SHAYE, WANDA NAKE SO NA NUNA MUKU EFFECT ƊINSHI, KUMA KUN GA ABUNDA YA JA HAJNA TA HAUKACE.

SHAYE-SHAYE BABBAR ILLA CE GA AL'UMMA, KUMA YANA TAƁA ƘWAƘWALWA, INA KIRA GA MATA DA KU GUJI SHAYE-SHAYE.


WASU BASU JI DAƊI BA DA HAJNA TA HAUKACE, AMMA KU SANI DA BATA HAUKACE BA DA BAZATA HAƊU DA AUNTY FARWA HAR TA KAITA GIDANTA BA, ANAN INA NUNA MUKU KOMAI DA ZAI SAMU ƊAN ADAM YANA DA DALILI KAMAR YADDA KUKA GANI, DALILIN HAKA FARWEEN YA SAKE GANIN HAJNA.


FAHNA TA MUTU NE SABODA BA ITA CE TAURARUWAR BA, AMMA IDAN KUN LURA TANA TAKA RAWAR JARUMAI, KUMA SUNAN LITTAFIN HAJNA BA FAHNA BA, SANNAN MUTUWARTA AYA CE GA INNA DOMIN MUTUWAR FAHNA ZATA TAƁA RAUNINTA, BUGU DA ƘARI MUTUWAR FAHNA DARASI GARE KU, DAN KU SANI CEWA DUK ABUNDA KA DAƊE KANA YI WATA RANA ƘASA ZATA RUFE MAKA IDO.


YAWAN SHAN MAGANIN HANA HAIHUWA NA JANYO MATSALOLI, KUN DAI GA YADDA HAJNA TA SO RASA RAYUWARTA, KO DAI KI ƘI HAIHUWA HAR ABADA, KO KUMA IDAN KIKA SAMU CIKI YA ƁARE KO KUMA YA HANAKI ZAMAN LAFIYA KI RASA RANKI KO KUMA IDAN ALLAH YASO KI, KI SHA DAƘYAR.


HAJNA TA BIYA LAIFUKANTA TUN A DUNIYA, KUMA SU BAFFA SUN CI RIBAR HAƘURI DAGA ƘARSHE, UBANGIJI YA RABA MU DA TALAUCI.


DAGA ƘARSHE INA SO KU SANI WANNAN LITTAFIN DARASI NE GA IYAYE MASU ƊAURA YARANSU AKAN TURBAR DA BA DAI-DAI BA, WANI LOKACIN WATA KALMA DA KAKE MA ƊANKA ZATA IYA SAUYAWA ƊANKA TUNANIN KAMAR DAI YADDA INNA TAYI, HAKA YAWAN TSANANI IDAN YAYI YAWA YANA ƁATA YARO, KAMAR YADDA BAFFA YAYI, DA ACE LOKACIN DA BAFFA YA FAHIMCI AKWAI ALAƘA TSAKANIN HAJNA DA QASEEM YA BINCIKE MINENE DA BA'A KAI GA HAKA BA, BE TAMBAYI ƳARSHI KO TANA SONSHI BANE, KAWAI SAI YA DAKATAR DA QASEEM DAGA ZUWA GIDAN WANDA HAKA YASA QASEEM YIN FUSHI DA HAJNA HAR YASA TAYI TUNANIN BINSHI. SANNAN GARE KU MASU AMINTA DA MUGAYEN ƘAWAYE, KU NISANCI GURƁATACCIN MUTANE DA ZAKU IYA ƁATA MUKU RAYUWA KAMAR YADDA FAHNA TA YI WA HAJNA. SANNAN KUMA KAR MU ƘYAMACE WANI, KUNGA YADDA FARWEEN YAYI BE GUJI HAJNA BA DUK DA ABUNDA TAYI WANI LOKACI WASU NA LALACEWA SABODA WANI DALILI, KUMA DALILIN NUNA MUSU SO ZAI JAWO HANKALINSU GA SHIRIYA KAMAR YADDA AUNTY FARWA TAYI, KOWA YANA DA DALILIN AIKATA WANI ABU KO MAI KYAU KO MARA KYAU.


DA WANNAN NI QUEEN NASMERH NAKE MUKU SALLAMA, ZAN MATUƘAR KEWARKU MU HAƊU A SABON LITTAFINA ME SU DUNIYAR ASMA'U, DA KUMA CIGAN 🔱🔱ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱.



ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💞💞💞💞💞

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that

Please Login or Register in order to submit comment