Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tangaɗi ta tashi zata fita, amma ina ta gagara tashi, wani saurayi da ke zaune gurin ya taso ya zo gaban ta “ƴam mata kina buƙatar wani ne ", bata amsa shi ba, domin maganin ya buge ta sosai, kamata yayi su ka nufi wani ɗaki dake cikin shagon, kan gado ya jefa ta, tare da faɗawa kanta, romancing ɗin ta ya fara yi, yana jagwalgwala ta ko ina, har yayi nasarar raba ta da kayan jikinta.

Ni kuwa ƙofar ɗakin na rufe, duk tsoron Allah ya kama ni.

Fahna kuwa hankalinta ya tashi ganin har ƙarfe 9:00 na dare Hajna ba ta dawo ba, gashi ita tana so ta fita, wayar ta ɗauka ta kira wani saurayinta “hello Muhsin kana ina kazo ka ɗauke ni, kasan yau muna da night party a shagon nan na giya ", Muhsin yace“an yi haka fa, to ina motar ki?", “ina ruwan ka, kai dai kawai ka zo ka ɗauke ni ", be yi musu ba yace “to ganinan zuwa, nan da minti talatin", bai ɗauki wani lokacin ba ya iso, kiranta yayi “hello baby ina ƙofar gidanki ", “to ka shigo mana, ina ɗan canza kaya ne"Fahna ta faɗa, “to baby bari na shigo na taya ki sa kayan" , dariya tayi tace “wallahi bazaka ɓata min lokaci ba, kasan 11:00 za'a fara, gashi yanzu har 10:30 tayi ", murmushi yayi yace “bari dai in shigo ki gani" kashe wayar yayi, umurni yayi ma mai gadi akan ya buɗe mishi gate, buɗe mishi aka yi ya shigo.

    Bai same Fahna a parlor ba, haka ya tabbatar mishi da tana ɗaki, kai tsaye ɗakin ya wuce, mai take shafawa gaban dressing mirror, sai ji tayi ana shafa jikinta a hankali, cikin muryar dariya tace “Muhsin ka bari mana, za ka, ɓata min lokacin ", Muhsin yace “Baby minti 20 ya min yawa, plsss" ya ƙarasa maganar yana mannata a jikin shi, “a nawa to? "ta tambaya, “dubu ɗari biyu" ya faɗa yana haɗa bakin shi da na ta, basu wani ɗauki lokaci ba ya biya buƙatar shi, tare da shi su ka  yin wanka ta sa kaya, sannan su ka wuce.

   Ba su ɗauki lokaci ba su ka isa gurin, mamaki ya kama Fahna lokacin da taga motar ta a gurin, Muhsin ne yace “Baby can gurin ba motar ki bace ", gaɗa kai tayi alamar eh, “to me ya kawo ta nan" Muhsin ya tambaya, Fahna tace “kasan fa ni bana son yawan tambaya, ƙawata ta zo da ita ", fitowa su ka yi daga motar, itama Hajna ta san nan gurin kenan, cikin su ka nufa.

   A ɓangaren Hajna kuwa ko da ta farka, kwance ta ganta kan jikin wani, tashi tayi, tana kallon kanta ba kaya a jikinta, haka shima, da sauri ta yaye zanen da ke lulluɓe a jikinsu, da sauri ta samo tuna duk abunda ya faru da ita ɗazu, wasu hawayene masu zafi ke bin kuncinta, dai-dai lokacin shima ya tashi, agogon wayar shi ya duba ya ga ƙarfe 8:00 na dare, “ kiyi haƙuri na ganki cikin damuwa ne shiyasaa na rage miki zafi ", bata ce komai ba sai kukan da ta cigaba da yi, wata zuciyar na tambayar ta anya Hajna kin zaɓarwa kanki rayuwa me kyau, ji tayi ya rungumeta ta baya, “a zahirin gaskiya, ban taɓa kusantar wata ƴa mace ba sai ke, na fi shekara ina zuwa nan guri, amma banga macen da ta min ba sai ke ", shiru tayi banda hawaye ba abunda ke bin kuncinta, “kina da duk abunda ba kowace mace ke da shi ba, zan so mu rayu tare", tashi tayi tace “nagode da ka faɗa min abunda wani be taɓa gaya min ba", ta faɗa tana sa kayanta, shirin barin ɗakin ta ke yi, da sauri ya riƙe mata hannu, “ina zaki "ya tambaya, Hajna tace “gida zani", yace “ki jira ƙarfe 11:00 za'a yi night party ki tsaya plssss " ya faɗa yana marairaice fuska, ba dan ta so ba ta haƙura, fita suka yi ya kai ta boutique su ka siye kaya, ta canza, a can yake faɗa mata sunan shi Mubarak, sosai taji daɗi kasancewa da shi, dan Mubarak mutum ne mai son barkwanci, da raha, basu dawo ba sai ƙarfe 11:40.

  Fahna kuwa tunda ta shiga gurin take sa ido ko zata ga Hajna amma bata shigo ba, can ta hango ta tana shigowa tare da Mubarak, sanye ta ke da jar riga, Iya guiwa, ta kama ta sosai, daga gefen rigar ta wurin cinyarta an tsaga rigar, hannun shi a kan ƙugunta, Fahna mamaki take yi yadda taga Hajna, da sauri ta nufi gurinta, “Hajna ashe kina nan"Fahna ta faɗa, “eh ina nan tare da Mubarak ", Fahna tace “kai ɗan gari daga ƙarshe ka samu macen da ta maka", Hajna tace “dama kin san shi ne ", Fahna tace “tambaye shi kiji, babban aminin Muhsin ne", dai-dai lokacin Muhsin ya ƙaraso, da wani mayen kallo yake bin Hajna , Mubarak ya daki kafaɗun shi yace “ka shiga taitayinka fa, wannan beb ɗita ce ", dariya Muhsin yayi yace “kace yanzu za ka rage shaye-shayen da ka ke yi", Mubarak yace “ai bazan iya bari ba ", Fahna tace “ai Hajna bata yi", Mubarak yace “Injiwa ya faɗa miki, abunda na ke yi ai dole zata yi ", kama hannunta yayi yace “ beb muje daga can mu samu abun korawa", wucewa suka yi, giya aka bashi, Hajna kuwa ƙwayar magani ta kora dan a cewarta giya ta mata ƙarfi, cikin maye Fahna ta kamata su ka je gida, lokacin ƙarfe 3:57 na dare, Fahna ta ja motar, Mubarak ya musu rakiya, tare da faɗa ma Fahna zai zo gobe gurin Hajna.

Anan zan dasa aya................. ✍️

Da masu karatu kun ji wata rayuwa da Hajna tazo da ita, bari muga inda zata kai ta.

Karku manta kuyi following Wattpad account ɗina, dan wata rana zan iya daina chart, amma zaku samu labaraina a Wattpad insha Allah.
QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
[8/17, 09:52] Queen Nasmah✍️: ♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAGE 57-58
***********************
Kamar yadda Mubarak yayi alƙawari, yau da misalin ƙarfe goma na dare ya zo, tana zaune, su na labari da Fahna a hankali maganin da tasha na bugunta, sai wani luuuuu take yi da ido, da alama ƙwayar tana bugunta, jin ƙarar buɗe ƙofa yasa Fahna ta juya, “oh Mubarak har ka iso? "Fahna ta faɗa, “eh wallahi" ya faɗa yana zama kusa da Hajna, mutumiyar ta mu sai wani mashalo take, “kaiiii harrr ka isoooo"ta faɗa cikin maye, kallon Fahna yayi yace “wai ita ko yaushe a buge ta ke? ", Fahna tace “yau ma yini tayi a buge, yanzu muka samu ta dawo dai-dai shine fa ta sake shan wata ƙwayar", “amma tana da damuwa ne ko? "Mubarak ya faɗa hannun shi cikin na Hajna, Fahna tace “eh mana mijin ta ne ya sake ta", Mubarak yace“ahh haba nima dai ina mamakin mi yake yawan sata cikin maye ", Fahna tace“ to ka dai ji", “kuuu me kuke cewa haka neeeeeee"Hajna ta faɗa, Fahna tace “kaga dan Allah ka ɗauke ta daga nan, ni fa ban cika son irin abun nan ba, nifa duk iskanci na ban iya shan ƙwaya ", Mubarak yace “iskancin ki a iya shisha ya tsaya ai", dariya Fahna tayi tace “na ji, ja ta dan Allah ku je "ta faɗa tana nuni da ɗakin Hajna.

    A ɓangaren Umma kuwa, ta cire rai akan Hajna, Baffa ma haka harkar gaban su su ke yi, kuma yanzu dai-dai gwargwado suna da arziki, kuma Baffa yana tafiye-tafiye, domin haɓɓaka kasuwancin shi, dai-dai gwargwado su na ci mai kyau, su sha mai kyau, Baffa ya gyara gidan shi, dan ɗakin Hajna ma an mishi rufi, yadda ruwa bazasu iya shiga ba, Umma ta fara sana'ar abinci siyarwa, inda su ka yi magana da wani ɗan maƙotan su cewa zai riƙa kai mata talla, ita kuma kullum zata bashi hamsin da abinci ya ci, kuma haka aka yi ko yaushe yana zuwa ya fitar mata da kaya gurin talla, ita kuma abincin safe da rana da dare take bashi, da hamsin ya siye alawa.

    ************************************************************

Bayan wata biyu.

Wata danƙareriyar mota ce naga tayi parking a harabar gidan Fahna, buɗe ƙofar aka yi, da mamaki na naga Hajna ta fito daga cikin motar , sanye da wani wando three quarter da riga half vest, ta naɗe gashinta ta gefe ɗaya, da kallo na bi ta tsabar mamaki, Hajna tayi fresh tayi kyau sosai, tafiya take yi tana mashalo kamar zata faɗi, kan kujera ta faɗa, Fahna da fitowar ta kenan tace “kin bani wallahi kullum a buge, ke baki san daɗi duniya ba, ƴar wahala kawai "ta faɗa tana bin gefen ta ta fita, Hajna kuwa tana kwance a gurin, wani Alhaji ya shigo, kamata yayi su ka shige ɗaki da alama sunyi da shi zasu haɗu.

   A ɓangaren Qaseem kuwa neman Hajna yake yi ruwa a jallo amma bai samu ganinta ba, Meenat kuwa satin da ya wuce ta dawo, gasa mishi aya take a hannu, yanzu idan ku ka ga Qaseem zaku tausaya mishi, yau zasu yi tafiya zuwa London gurin wani aiki, inda aikin zai ɗauke su wata biyu acan, badan yaso ba haka ya haɗa kayan shi, fitowa yayi zai tafi inda ya tarar da Meenat zaune akan kujera “ni zan wuce, sai na dawo "ya faɗa, ko kallon shi bata yi ba, tace “a dawo lafiya", be sake cewa komai ba ya fita abin shi yana mai takaicin sakin Hajna da yayi, da ace be sake ta ba duk da haka bata faru ba.

    Meenat kuwa tunda Qaseem yayi tafiya ta kama harkar bin maza, ba abunda ta saka gaba, kuɗin Qaseem kam suna shan kashi, dan kusan kullum sai ta ɗibi kuɗi a ƙalla 2 billion, ita duk burinta be wuce tayi kuɗi ba, dan ta aure shi ne dan kuɗin shi, sannan yanzu atm card ɗin shi yana hannunta, tasan password da komai na shi, idan tana gida ta taɓa na ɗakin kuɗin shi, idan tana waje ta taɓa na asusun bankin shi, shi kuwa bawan Allah yana can aiki tuƙuru dan ya samu kuɗi.

    *************************************************
Rayuwa sai cigaba da gudu take yi a lokacin da wasu suke sheƙe ayar su, sun manta da duniya zamanta na lokacin ne, zamu koma lahira madawwamar kowa, Hajna ta zama shahararriyar ƴar iska, mai faɗa aji a ko ina indai fanni bin maza ne, maganar kuɗi kuma Hajna ta tara kuɗin da har ta mutu baza su ƙare ba, wannan dalilin ne yasa Fahna ke ƙara ingiza Hajna akan shaye-shaye da bin maza, saboda ta kwashi kuɗin Hajna.

  Yau Qaseem ya dawo daga London, bai nufi ko ina ba sai gidan Fahna inda Hajna ke zama, dan Fahna ta bata shawarar kar ta siye gida kawai ta zauna nan, Hajna gani take duk soyayya ce Fahna ke nuna mata, bata san Fahna nayi ne da manufar cin kuɗin da ta tara ba.

    Tafiya ta ke yi tana tangaɗi, dan yanzu baka taɓa ganin Hajna dai-dai kullum a buge take ko yaushe, Qaseem ne ya ƙaraso gabanta, shigowar shi kenan ya ganta tana shirin fita, “Hajna " ya faɗa, a wani ɗage take kallon shi, “Hajna ni ne mijin ki Qaseem" ya faɗa yana riƙe hannunta, da ƙarfi ta fizgi hannun tare da watsa mishi mari, tasssssssss! Kake ji ƙarar saukar mari a fuskar shi, hawaye ne ki bin kuncinta, tace “na tsane ka Qaseem bana son ganin ka, kar ka sake taɓa ni ", Qaseem yace “yanzu Hajna wannan rayuwar kika zaɓar ma kanki?", kallon shi take har ya gama maganar sannan tace “bani na zaɓi rayuwar nan ba, rayuwar ce ta zaɓe ni, kai ne nan wanda ya ruguza min rayuwata, ya sauya ni, ya jefa ni a wannan rayuwar, na tsane ka" ta faɗa tana shigewa mota, a 260 ta bar gidan, Qaseem kuwa juyawa yayi jikin shi ba ƙwari ya nufi motar shi, shi ma a 260 ya bar unguwar cikin ƙunci da ciwo, tabbas idan akwai wanda ya ɓata ma Hajna rayuwa shine, amma akan Hajna ya san minene so! .

😴😴😴😴
Anan zan dasa aya........... ✍️

Haɗin guiwar: Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ♻️♻️✍️✍️
[8/17, 09:53] Queen Nasmah✍️: HAJNA♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 59-60
***********************

Rayuwar Hajna kullum ƙara ɓata kanta take yi, a lokacin hanyar arziki ke ƙara buɗe mata, yanzu kam ta wuce tunanin ku, saboda tsabar maye ko tsayuwa bata yi dai-dai, can na hango cinkoson mutane akan hanya da alama wani abu ke faruwa, matsawa nayi domin ganin abunda ke faruwa, can naga Hajna ta fito, sai wani lulu take da ido, “wai taron me kuke yi haka neeee"Hajna ta tambaya cikin maye, wani mutumi dake tsaye yace “me za kiyi, bayan kin riga kin bugu, dallah koma mota ", da wani mugun kallo take bin shi tace“kai dallah matsa can, sakaran banzaaaaa", faɗa ya hautsine tsakanin su, Hajna ba ji ba gani ta yiwa mutumin rashin mutunci.

    A ɓangaren Meenat kuwa kwasar kuɗin Qaseem ta ke kamar ba gobe, ita abunda ke bata mamaki ba komai bane, illa yadda kuɗin basa jin duka, zaune take ɗaki tana faman taɓa waya, Qaseem ya shigo ɗakin daga shi sai boxers, zaunawa yayi kusa da ita, a hankali ya shiga shafa ta, “kai wai miye haka, maye kawai ni matsa min can "Meenat ta faɗa tana goge inda ya taɓa, “haba Meenat miyasa kike min wulaƙanci ne, miye amfanin auren ki indai bazaki bani haƙƙina ba" ya faɗa, tace“oho kaje ka dawo da wannan karuwar matar ta ka ", Qaseem be ce komai ba ya tashi ya koma gefen gado ya kwanta, ba tare da ta damu ba ta juya ta cigaba da chat, sai masifa ta ke mishi jefi-jefi, shi kuwa be kulata ba, sai ma rufe idon shi da yayi, bai ɗauki lokaci ba barci yayi awon gaba da shi.

    HAJNA kuwa night party taje, inda suka sha rawa har su ka gaji, yau kam tasha tayi maƙil, tafiya take yi bata ma ganin gabanta, motarta ta nufa tare da sa mata key, ta hau kan titi, Allah ya so dare yayi sosai ba mutane a titin, da yau Allah kaɗai yasan adadin waɗanda Hajna zata kaɗe, dan bata gani kawai tafiya take yi, da ƙyar ta samu ta gane gidan Fahna dan ta kusa yawace garin, buɗe mata gate aka yi, ko parking bata tsaya yi ba, ta aje motar ta shiga gida tana jin kanta yana matuƙar mata ciwo, ga wani jiri da ke ɗibar ta, a parlor ta yadda wayar ta da jakar ta, sannan ta faɗa kan wata kujera, kanta mugun ciwo ya ke yi, da ƙyar ta samu barci yayi awon gaba da ita, sai dare sosai Fahna ta shigo cikin gidan, ganin jakar Hajna a yashe yasa ta ɗauka tare da kwashe duk kuɗin da ke ciki, sannan ta jefar da jakar, kallon Hajna tayi tace“ƴar wahala "wucewa tayi ta nufi ɗakinta.

    Washe gari da sassafe Fahna ta fito da alama za tayi baƙi, inda ta bar Hajna jiya nan ta same ta, kallo ta ƙare mata sannan ta fita, bata dawo ba sai bayan azahar har yanzu kwance take agurin, dan haka ta shiga tada ita, “Hajna ki tashi "amma bata tashi ba, taɓa jikinta tayi taji da zafi, ɗaukar ta tayi su ka nufi asibiti, dubata aka yi sannan aka mata allurai, akan cewar tana fama da zazzaɓi ne mai nauyi.

    Kwanan Hajna biyu a asibiti amma bata san yanayin da take ciki ba, abun ban haushin ma, yanzu ta yawaita yin dariya, da yawan kuka, an ɗibi jininta kuma an mata hoto a kai, domin kwajin ƙwaƙwalwa da kuma wata cutar, dan alamu suna nuna tana da matsala a kai.

   “keeee kin san meeee , hhhhhhhhhh"Hajna ta faɗa tana nuna Fahna, Fahna tace “ina kyautata zaton baki da hankali, in ba hauka ba me zai sa mutum yayi ta yawan dariya, nifa nan kin ganni ba so nake ana min dariya ba kin sani sarai kuma " ta ƙarasa maganar a hasale, dan tun jiya Hajna ke mata dariya, (nima Nasmerh dariyar na fara yi gani yadda Fahna ta hasala🤣😂), Hajna kuwa dariya kawai take yi kamar wata zararra, can kuma sai ta ɓata rai, tana wasu maganganu waɗanda basu da kai, “kin ba ni, a'a baki ba ni ba, hhhhhh", sai dariya ta ke yi, Fahna kuwa tsura mata ido tayi, dai-dai lokacin likita ya shigo, “ke ce kika kawo me jinyar nan ko "ya tambayi Fahna da ke zaune, Fahna tace “eh ni ce", “me jinyar ki na shaye-shaye? "ya tambaya, “eh likita" Fahna ta faɗa, “to maganar gaskiya ya taɓa mata ƙwaƙwalwa "likitan ya faɗa, Fahna tace “subahanallahi, kana nufin ta haukace?", likitan yace “kusan dai haka, domin yanzu zata riƙa yin abubuwa kamar ba ita ba", Fahna tace“ minene mafita ", likita yace “za a iya mata aiki amma fa zata ci kuɗi sosai", jin an ambaci kuɗi sosai yasa Fahna saurin cewa “likita bari zan yi shawara, yanzu ka bamu takardar sallama ", ba tare da likitan ya kawo komai ba ya rubuta ma Fahna maganin da Hajna zata sha da allurai, “insha Allah indai ana mata su zata samu sauƙi ki siya mata", “to likita "Fahna ta faɗa, takardar sallama aka rubuta musu sannan su ka wuce gida.

A mota Hajna sai surutu take zuba muta marasa ma'ana, “ke dallah ni yimin shiru, wallahi bazan zauna da mahaukaciya ba, ribar me zanci, ke wahalalliya ce, kin ji haushi wallahi", buɗe ƙofa tayi tare da tura ta waje, faɗawa tayi ƙasa tana ta mulmula a ƙasa, sai kuka take yi, Fahna kuwa ta ƙarawa motar ta gudu, tana mai jin daɗi yanzu duk dukiyar da Hajna ta tara ta zama tata, ta fara lissafin abubuwan da zata siye.

    Hajna kuwa tafiya take yi, duk abunda ta gani sai ta tsinta ta sa a baki, tana dariya, kafin ki ce me, yaran gari suka yi caaaaa kan ta suna bin ta suna waƙa, “mahaukaciya, mahaukaciya "Hajna kuwa sai tiƙar rawa take, kwance ɗankwalin kanta tayi ta ɗaura a ƙugu tana rawa, (abun takaici abun dariya), su kuwa yara sai dariya su ke yi, ganin suna dariya yasa ta zauna tana dariyar ita ma, “kuuuu ku tsaya na gaji" ta faɗa tana tashi, sai tangaɗi take yi, biyo ta yaran su kayi, ai kuwa ta kwasa a guje sai cikin tashar mota, wata mota ta loda mangwaro, da alama wani gari zata kai, ai kuwa ta shige cike, yaran su ka zo suna ta neman ta basu ganta ba, su ka yi tafiyar su, cika motar aka yi taƙil da mangwaro, motar ta tashi.


Ni kuwa nace su Hajna sai ina 🤣🤣😂.

Anan zan dasa aya................. ✍️

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya.


ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️♻️
[8/17, 09:55] Queen Nasmah✍️: ♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 61-62
*********************
Tafiya ce mai ɗan tsayi amma ba wani sosai ba, daga Abuja zuwa wani gari, idan naga a wani symbol an rubuta Lagos, haka ya tabbatar da nan Lagos ne, a tashar mota suka tsaya, inda aka fara saukar da buhuhuwan mangwaro zuwa ƙasa, daga can ciki na hango Hajna sai barci take yi da alama wahalar hanya ce, gashi duk bakinta ya ɓaci da alama taci mangwaro har ta ƙoshi, dan ƙwallon mangwaron da na gani sun fi 10, mutumin da ya jaye wani buhun mangwaro yayi saurin sakin buhun tare da watsa ihu, dan sosai ya firgita, ina su ka samu wannan kyakkyawar yarinyar, ɗaya daga cikin masu fitar da mangwaron ne ya shigo cikin motar yana tambayar lafiya, Hajna kuwa jin ihu yasa tayi firgigit ta tashi, da kallo su ke binta, “ke baiwar Allah me ya kawo ki nan? ", bata kula su ba sai ma tashi tayi, ta diro daga kan motar, da tsalle-tsalle ta bar gurin, shi kuwa mutumin girgiza kai yayi, dan da gani kasan wannan mahaukaciya ce.

   A ɓangaren Fahna kuwa kayanta ta shiga kwashewa, dan yau zata tattara ta komai Zamfara, kuma tayi alƙawarin zata koma gida ta ɗauko Inna, dan har ta kirata ta faɗa mata, an gama gina mata gida a Gusau, kuma insha Allah nan zasu zauna, akwatin ta jawo wanda ta gama loda wa kaya, wata ƙatuwar Jeep ce, kuɗi ta loda mata, buhan American dollars Har huɗu , da buhu biyu na naira, sauran kuɗin ma bata kwasa ba a cewar ta, waɗannan ma sun ishe ta rayuwa.

    Tafiya ce me nisa daga Abuja zuwa Zamfara, dan haka take shara guda akan titi, dan kar a duba motar ta har hayar ƴan sanda tayi dan su mata rakiya, saboda haka duk checking point ɗin da ta zo ba'a duba ta.

   A ɓangaren Hajna kuwa, yara sai binta su ke yi suna waƙa, “mahaukaciyar bola ", Hajna kuwa ko a jikinta sai kwasar rawa take yi, da ƙyar ta samu wani tsoho ya kora mata su, sannan ta samu wuri anan cikin tashar mota tayi kwanciyar ta, dan dare yayi.

    Shigarta garin Zamfara kenan yayi dai-dai da tahowar wata mota tirela, bata yi auni ba ta faɗa musu, nan take motar da Fahna ke ciki ta ƙone da wuta, ita ma Fahna da ke ciki ƙonewa tayi, nan take ƴan sandan da ke bayan ta suka fito, da ƙyar aka jawota daga cikin motar, duk jikinta ya kware, sai ihu take yi, wayarta da bata yi komai ba aka ɗauka, kiran Inna aka yi ana shaida mata Fahna tayi hatsari za'a je asibiti da ita, “wane irin asibiti ni bani ma da kuɗi, ku dawo min da ita gida kawai ",“to shikenan" ɗan sandan ya faɗa yana kashe wayar, bayan boot suka saka ta dan a cewar su basu da gurin saka ta a cikin su, ni kuwa nace duniya kenan, yau Fahna da ke iko, ake sawa a boot, yau kai ne gobe ba kai ne ba, yanzu take cikin mota ita kaɗai amma ta dawo cikin boot, Fahna kuwa bata iya cewa komai.

    Garin Shinkafi su ka nufa da ita, kai tsaye unguwar ajiyawa su ka wuce, gidan su Fahna be musu wuyar nema ba, tambaya ɗaya su ka yi su ka gane gurin, a ƙofar gidansu su ka tsaya inda su ka shiga cikin giɗan ɗauke da Fahna, da yanzu ko motsi bata yi, Inna da ke tsaye da sauri ta matso, “Fahna haka ta faru da ke, me ya same ki ", aje ta suka yi suka ce “mu zamu wuce", bata samu damar amsa su ba tsabar tashin hankali, fita tayi da gudu, kai tsaye gidan wata mata ta nufa likitan gargajiya ce, tare suka dawo da Inna cikin gidan.

    Taɓa Fahna matar ta shiga yi, hannunta ta kai kan hancinta dan jin yadda numfashin ta ke fita, da sauri ta jaye hannun tare da ɗaga hannun Fahna, amma sai ya sulale ya faɗi, zani ta tashi ta ɗauko Inna sai magana take mata amma ta kasa bata amsa, rufe Fahna tayi a cikin zanen har fuskarta, “mikike nufi da zaki rufe min fuskar ƴa ", Baba Jummai tace “ta hanyar nan kawai zaki iya fahimta, Fahna ta riga mu gidan gaskiya" ta faɗa tana ɗaukar kayan aikin ta, Inna faɗuwa tayi gaban gawar, ita kuwa baba Jummai gidanta ta koma, Inna da kanta ta fita domin neman waɗanda za su yiwa Fahna sallah, wannan shine karo na farko a rayuwar Inna da tayi nadamar abunda tayi a rayuwar, yanzu me Fahna zata ce tace a gaban ubangiji, zata ce Mamarta da kanta ta ɗaura ta akan turbar bin maza, yanzu me zata ce ma ubangiji idan ya tambaye ta amanar

Please Login or Register in order to submit comment