Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

da ya bata na kula da tarbiyar yarinyar ta, hawaye masu zafi suka sauko mata.

   Bayan an kawar da Fahna ne Umma ta shigo domin yin gaisuwa, dama shi Baffa da shi aka yiwa Fahna sallah, kuma da hannun shi ya saka ta cikin ƙabari, yana mai jin ciwo da ta mutu akan turbar karuwanci, roƙon Allah yake kar Hajna ta mutu a irin yanayin nan, da sallama Umma ta shiga gidan, amsa mata aka yi, sannan ta shiga ciki inda ta samu Inna zaune tana kuka sai rarrashin ta ake yi, “ya aka ji da haƙuri ", Umma ta faɗa, Inna tace “haƙuri an gode Allah", Umma tace “to Allah ya sanyaya, Allah ya sada ta da mala'ikun rahama ", da ameen ta amsa, sannan tace “Amina kiyi haƙuri da abunda ya faru", Umma tace “be kamata muyi maganar nan ba, kar ki manta rasuwa aka miki kuma akwai mutane, ni na yafe miki duniya da lahira, har ita Fahna ɗin " fita umma tayi, da shigar ta cikin gida ta fara kuka, wai ina Hajna take, ko ita ma ta mutu, ko kuwa dai da sauran ranta Allah kaɗai ya sani, addu'a tayi akan Allah ya bayyana mata Hajna, ya dawo mata da ita gida tun lokaci be ƙure ba.

   Anan zan dasa aya............ ✍️

Muna gab da ƙarshen labarin wanda yake ɗauke da hargitsi da kuma farinciki daga ƙarshe.

HAJNA NA MUKU BA KWANA NAN KUSA ZAI ZO ƘARSHE.

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
[8/17, 09:55] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAGE 63-64
***********************
   Yau aka yi kwana uku da rasuwar Fahna dan haka yau aka yi addu'ar uku, mutane sai shiga da fita su ke yi cikin gidan Inna, bayan anyi sallar la'asar Baffa ne ya shigo yayi addu'ar uku kamar yadda ake yi a al'adance, Inna sai kuka take yi, Baffa duk yaji ba daɗi, idan bai manta ba ranar da aka haifi Hajna da daddare aka haifi Fahna, baba da kanshi yayiwa Baffa sallama har gida yana sanar da shi cewa shima Inna ta haifar mishi mace, Baffa ne, yace to a naɗa mata suna Fareeda amma ana kiranta Fahna, wanda Fahna ya bi ta, ita kuma Hajna aka sama ta  suna Hafsat amma ana ce mata Hajna, lokaci na tafiya har sunayen su suka ɓata, idan ba an faɗa ba ma bazaka san sunan su ba, gashi har lokaci yazo da Fahna ta bar duniya, sosai Baffa ya tausaya ma inna, gashi baba bayanan a duniya yanzu ma Fahna ta bar duniya.

    ****************** LAGOS ***************

Tafiya take yi tana tsalle-tsalle, sai tsince tsince take yi, wata ƙatuwar mota ce ta zo BMW fara ce sol, gudu take yi akan titi, da alama sauri take yi, da sauri ta cije burki,dai-dai lokacin da mahaukaciyar nan ta hau kan titi, ƙiiiiiiiii kake ji, da sauri ta tsaya, Fitowa tayi sanye da wata doguwar riga, gashin kanta da gani kasan gashin doki ne, kyakkyawa ce, da alama ba musulma bace, gaban yarinya tazo da sauri, Hajna ta ɗago dan  tsoratar da tayi ne yasa ta faɗi ƙasa, kallonta matar ke yi, nima ɗin kallonta nake yi, mata duk tausayi ya kamata, ganin Hajna da tayi ba ƙaramin imani ya shiga ranta ba, da ganin Hajna zaka gane bata hayyacinta, gashi tayi baƙi sosai in ba ka santa ba sai ka rantse iffiritu ne, kama hannunta tayi suka shiga mota, wannan karon Hajna bata damu ba dan ta gaji.

    Kai tsaye gidanta ta nufa da Hajna, mai gadi ne ya buɗe mata gate, parking tayi a gurin da aka tanada domin parking, gidan ya haɗu sosai da sosai, Hajna kuwa sai kalle-kalle take yi, matar kuwa sai jan hannunta take yi, cikin gida suka shiga da Hajna, parlor wani irin babban ne, ni a ganina zai iya ɗaukar mutum yafi dubu tsabar girman shi, kujerun dake parlorn manya-manya ne, maganar gaskiya duk kujera ɗaya zata iya ɗaukar mutum sha biyar, kujerun black da white ne, sunyi matuƙar yin kyau, ban ƙara tabbatar da haɗuwar gujerun ba sai da na zauna ciki, tsabar laushi ji nake kamar ina kan mage, ban san lokacin da na fara jin barci ba (masu karatu saura ku ce Nasmerh ƴar ƙyauye ce 😂). TV ma abun kallo ce, dan girmanta sai kayi tunanin zata iya haɗiye mutum, kayan ɗakin basu da hayaniya haka yasa nayi tunanin ina turai.

    “Eli ! " naji wannan matar ta kira sunan Elizabeth , “yes mom, am coming" (na'am mama, ganinan zuwa), fitowa tayi, matar da Elizabeth ta, kira Momy tace “ kullum kina zaune a ɗaki tun bayan hatsarin su twins da yayan ku ", hawaye ne suka zubo a kuncinta, hannunta ta saka ta share hawayen sannan tace “Mommy ki daina tuna min da ƴan uwa na, in ba haka nima zan kashe kaina", Mommy tace “to naji, shiga da wannan ɗaki, ki tabbatar kin saka ta yin wanka, sannan ki bata kaya zamu fita da ita asibiti ", Eli tace “momy kisa Monica ta mata wanka, da ganinta bata da hankali", murmushi kawai momy tayi tace “kira min Monica ", zuwa Monica tayi, umurni momy ta bata akan ta shirya Hajna tsaf .

   Be wani ɗauki lokaci ba gurin yi mata wanka, tass Monica ta mata, asalin farin fatarta ta bayyana, masha Allah, idan ba an faɗa maka ba bazaka ce mahaukaciya ce ba, bayan haka ma bawani hauka can take yi ba, kawai dai ƙwaƙwalwar ce ta juye.

    Wata riga Monica ta saka mata sannan su ka fito, a parlor su ka sami momy da Eli suna shan grapes, da sauri Hajna ta ɗauki grape ɗin ta hau turawa cikin bakinta da ba ƙaramar yunwa take ji ba, rabon ta da abinci tun ranar da ta zo Lagos yau kwana uku kenan, murmushi momy tayi sannan tace “Monica ki zubo mata abinci ", “ohk ma" Monica ta amsa tare da wucewa kitchen, bayan minti biyar Monica ta dawo da abinci a plate tare da ruwa da lemu, ita Hajna ba ta lemu take yi ba, da sauri ta ƙwace plate ɗin a hannun Monica ta fara tura da sauri, hannu baka hannu akushi.

    Sai da taci ta ƙoshi sannan ta tashi tana dariya tana tsalle-tsalle, sai waƙa take yi kamar yadda yara ke kiranta “mahaukaciya, mahaukaciya "ta shiga rerawa tana rawa, Monica da Eli kuwa me zasu yi in ba dariya ba, Mommy tace “dariyar me kuke yi kuma, bana son shirme fa", “yi haƙuri " su ka faɗa a tare, Hajna ko a jikinta, rawa take kwasa iya ƙarfinta  tana wani karkaɗa ƙugu, sai taɓi take yi ita a dole rawa take yi, Eli tace “momy ba kince zaku asibiti ba", mommy tace “eh amma ina jiran doctor Mahmood ne, sai ya fara dubata, idan akwai buƙatar zuwa asibiti gobe sai muje kinga marece ya fara yi ", ta ƙarasa maganar tana kallon Hajna dake zaune ƙasa sai nishi take yi, da alama har ta gaji da rawar da take yi, dai-dai lokacin likita ya shigo, gaisawa ya fara yi da Mommy sannan ya zauna, nan take mishi bayanin ta haɗu da wata, amma alama na nuna ƙwaƙwalwarta ta samu matsala, nuna mashi Hajna tayi, da kamar an tsikare ta ta miƙi tsaye ta cigaba da rawa tana cewa “mahaukaciya, mahaukaciya "ita har cikin zuciyar ta wannan kirarin daɗi yake mata, girgiza kai likitan yayi yace “tana da brain disorder ne ai", Mommy tace “me ya kawo haka? ", likitan yace “nima ban sani ba, amma gobe da safe zan zo sai muje da ita asibiti ayi gwaje-gwajen da za'a yi", Mommy tace“ to shikenan Allah ya kai mu ", “ameen" likitan ya faɗa tare da haɗa kayan shi ya fita.

. Anan zan dasa aya............... ✍️

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
[8/17, 09:57] Queen Nasmah✍️: HAJNA♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAGE 65-66
*********************
Washe gari da safe likita ya zo kamar yadda yayi alƙawari, Mommy da Hajna suka tafi zuwa asibiti, idan aka shiga kwaje-kwaje, likita ya tabbatar ma da Mommy cewa shaye-shaye ne ya taɓa ƙwaƙwalwar Hajna, “to likita har wane lokaci zata ɗauka a irin yanayin nan", Likitan yace “idan zaki iya ɗaukar nauyin kula da lafiyarta bazata jima a yanayin nan ba, sati ɗaya zai isa ace ta samu sauƙi ", Mommy tace “eh zan ɗauka", Likitan yace “to shikenan zaki biya million ɗaya domin lafiyarta ", transfer ta mishi ta account akan cewa a fara aikin yau tana so Hajna ta warke da wuri.

A ɓangaren Umma kuwa tun ranar da Fahna ta rasu tana yawan mafarkin Hajna a cikin bola, haka kuma ba ƙaramin tada mata hankali yake yi ba, haka yasa kullum take addu'a akan ko a wane hali take Allah ya fitar da ita, tana zaune a tsakar gida Baffa ya shigo, “sannun da zuwa Baffan Hajna ", murmushi yayi “yauwa, tunanin me kike yi" ya faɗa yana zaunawa, “wallahi Baffan Hajna kwanan nan ina yawan mafarkin Hajna a bola ", Baffa yace“bola kuma a na zaune lafiya", “eh wallahi kuma jikina na bani ba lafiya ba "Umma ta faɗa, Baffa yace “to koma minene Allah ya sauwaƙa mata, ni kaina ina damuwa da rashin Hajna, ko ba komai ita ƴar mu ce, ina fatan ta dawo gida tun wuri be ƙure mata ba", Umma tace “nima haka nake roƙo ko yaushe ".

   Washe gari da safe Qaseem yana kwance akan kujera abun duniya duk ya dame shi, Meenat ta fito da gajeren wando da wata riga, tafiya take yi a hankali tana karkaɗa ƙugu, kallon ta yake yi har ta kai gaban ƙofar fita “ke ina zaki" ya faɗa. Meenat tace “inda ka aike ni ", Qaseem yace “da wannan shigar?", Meenat tace “eh ko kana da ja ne ", Qaseem yace “kina da aure fa", “ai rawa yake "ta faɗa tare da buɗe   ƙofar zata fita, tashi yayi da iya ƙarfin shi ya fizgo ta, juyowa tayi cike da mamaki tana kallon shi, “yaushe kayi matsayin shiga harka ta?", “Meenat na gaji da abunda kike min ", Meenat tace “to kayi abunda zaka yi" ta faɗa tare da ture shi ta fita abunta, shi kuwa cikin takaici ya faɗa kan kujera tare da rufe idon shi, yana jin ciwon rashin Hajna, gashi yanzu duk sha'awa ta gama mishi yawa, amma duk yadda yaga mace baya iya kusantar ta, dan gani yake kamar Meenat na ganin shi ta ko ina, shi da kanshi yana mamakin yadda yake tsoron Meenat.

     Yau sati ɗaya kenan, wanda yayi dai-dai da gama aikin da aka mata, tsaye Mommy take kanta, a hankali ta shiga buɗe idonta da “Umma dan Allah ku yafe min, nayi kuskure amma ku yafe min " Hajna ta faɗa tana mai takaicin rayuwarta ta baya, wasu hawaye ne ke bin kuncinta, Mommy tace “yarinya ya sunanki?", “Hajna sunana, dan Allah ina su Baffa " Hajna ta faɗa, Mommy ta rungume ta tace “sunana Farwa, amma saboda wasu dalili kice min aunty kawai yadda ƙanina ke kira na", gaɗa kai Hajna tayi irin na fahimta ɗin nan, kwanan su biyu a asibiti aka sallama su, dan Hajna ta samu sauƙi sosai.

   Yau ya kasance ranar Sunday, dan haka suka fita dan al'adar Mommy ce fita every Sunday shopping domin haka yana tuna mata da yaranta, sosai Hajna taji daɗin fitar, sai ta ji kamar ita ce rana ta farko a rayuwarta da ta fita.

   Basu dawo daga shopping ba sai dare, Hajna ta gaji liƙis dan haka tana gama kwashe kayan da suka siyo, sannan ta nufi ɗakin da aka gyara mata, dan yanzu jin kanta take kamar ƴar gidan, wanka tayi sannan ta saka rigar barci, sallar da aka bita ta magrib tayi, sannan tayi isha'i, tunda dare ya fara yi sai ta nemi tayi barci abunta, kwanciya tayi ko minti uku ba'a yi ba barci ɓarawo yayi awon gaba da ita.

    Bata farka ba sai da ta ji kiran sallar asuba, da addu'a a bakinta ta tashi, ɗaura ƙafarta tayi ta sauko daga kan gado, toilet ta shiga kasancewar kiran sallar farko ne yasa tayi wanka, ta saka wata doguwar riga, wadda Mommy ta siya  mata, dai dai-dai lokacin taji kiran sallah, zaunawa tayi tana addu'a tana istigifari, har ranta taso ace ta tsaya tayi ilimin addinin amma ina bata yi ba,  wasu hawaye ne masu zafi suka sauko mata a fuskarta, tunawa da zaman ƙuncin da tayi a gidan Qaseem tayi , da yanzu ace ta tsaya gida bata baro Iyayenta ba da yanzu tayi nisa a karatunta na islamiya, tana cikin wannan tunanin taji an shirin tada sallah da sauri ta tashi, ta fara sallah , a cikin sujjadar ta tana mai ƙasƙantar da kanta ga ubangiji tare da neman yafiyar shi akan ƙaddarar da ta faɗa mata, cikin da nasani kowane lokaci da ta ɓata tare da Qaseem tun daga farkon haɗuwarta da shi har ila yau, a cikin sujjadar ta roƙi Allah ya bata wadda yake alkhairi a gareta, dan ita bata da zaɓi sai na shi, ta ƙara da “ya Allah ka yafe min haƙƙin Iyaye na dana ɗauka, bayan ta gama sallah ma bata tashi ba, sai addu'a take yi har haske ya fito tana miƙa wuya gurin Ubangijin ta, tare da yin tuba wadda take ɗauke da nadama da dana sani akan ko wani hali na ta, masu karatu zan so kuga tsantsar nadama a idon Hajna, yanzu kam tasan tayi laifi kuma ta shirya ƙarbar laifin da tayi.

  Allah yasa mu dace, taku Queen Nasmerh har abada.

Kar ku manta dai, nice dai wannan ɗin nan a ko yaushe, buƙatar ɗaya ce kawai kuyi following account ɗina na Wattpad ta link ɗin da ke sama 😴😭😘

Ina sonku har abada masoyan gaskiya 😘😘😘💗

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️✍️✍️✍️
[8/17, 09:59] Queen Nasmah✍️: HAJNA♻️♻️

[8/17, 09:59] Queen Nasmah✍️: ♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 69-70
**********************
  Washe gari da safe Hajna ta tashi, wanka tayi a gaggauce dan ta riga tayi sallah da asuba, gashi ta makara, wata ƙila dan jiya ta daɗe bata yi barci ba, shiryawa tayi cikin wata atampha skirt ne da riga, ɗinki yayi matuƙar yi mata kyau, kayan basu kamata ba, powder kawai ta shafa da jan jam baki, sai jan bakin ya haska fuskarta, murmushi tayi yadda na ƙara ganin fuskarta.

     Parlor ta fito, Aunty Farwa ta sama a parlor tana jera ma Farween abinci a kan centre table, dan shi baya cin abinci a dinning, “Yauwa Hajna zo ki haɗa mi shi, yanzu zai fito ya ci abinci ",, da to ta amsa, sannan suka jera, dkula uku ce, da flask, sai plate da cup, juyawa tayi zata wuce, wanda dai-dai da fitowar Farween, murmushi ɗauke a fuskar shi ya ce “Auntyna ta kaina har kin kammala aikin kenan", Aunty Farwa ta ce “Hajna ce ta taya ni kammalawa, da ka fita baka karya ba ", “Ohhh Hajna ina godiya" ya faɗa yana haɗa hannu biyu tare da duƙar da kai alamar jinjina, cikin jin kunya Hajna ta ce “ina  wuni", “ina lafiya " ya faɗa yana zama, Aunty Farwa ta ce “ Hajna kiyi serving ɗin shi, ni zan shiga ciki nayi wanka", Farween ya ce “ta dai jira har in gama ta kwashe, ai ni ba yaro ba ne da za'a zuba min abinci", ya ƙarasa maganar yana kashe ma Aunty Farwa ido, “hmmmm, kai dai ka sani, ka ce dai me ta ya ka fira ka ke so, ai wanda zai iya zuba ma kanshi abinci, ai zai iya kwashewa, bari na turo maka Aisha ta zo kuyi fira ", Farween ya ce “kar kiyi zata ja na ɓata lokaci ban tafi ba", wucewa tayi ba tare da ta kula shi ba.

Hajna kuwa abinci ta shiga zuba mishi, doya ce a ciki kula, ɗaya kular kuma miyar ƙwai, wani ƙaramin bowl ta ɗauka ta zuba mishi pepper soup ɗin da ke cikin ɗayar kular, sannan ta zuba mishi kunun alkama da ya ji madara a cup, tana gamawa ta tashi zata wuce, ji tayi ya kira sunanta “Hajna" ya faɗa, juyowa ta yi, “ki dawo ina so na tambaye ki", zaunawa tayi, gabanta na duka uku-uku, murmushi yayi ganin yadda duk ta firgita, fork yasa a cikin plate ɗin tare da wata ƴar ƙaramar wuƙa ya yanki doyar, sannan ya haɗo da miyar yasa a baki, “ya kika ji a ranki lokacin da kika ganni ", zaro ido tayi cikin rashin fahimta ta ce “na'am", Farween ya ce “kin jini da kyau, alama sun nuna min kamar kina tsoron kar nace ba za ki zauna a nan ba ", shiru tayi dan maganar shi haka take, abun da take tsoro kenan, Farween ya ce “ko ba haka ba ne?", gaɗa kai tayi alamar eh, Farween ya ce “to ki cire wannan a rai, dan ba zan taɓa cire ki daga gidan nan ba sai idan kin gaji da gidan ", gaɗa kai kawai take yi duk tsoro ya cika ranta, Farween ya ce “amma miyasa baki tunanin zuwa gurin iyayen ki", ina ma ace zan iya faɗa maka, da na faɗa maka bani da ƙwarin guiwar da zan tunkari su Baffa, dole sai nayi aure, ta faɗa ranta, amma a zahiri ta gagara furta ko kalma ɗaya, Farween ya ce “da alama kina jin kunya ta, zan tafi Kwara, idan na dawo nan zan tsaya, zamu tattauna akai, lokacin kin ƙara yin tunani ",“to nagode" ta faɗa, “za ki iya tafiya "ya faɗa yana aje plate ɗin doyar da ya gama ci, sannan ya ɗauki pepper soup na kaji ya fara ci, yana shan kunun, yana jin daɗin girkin Aunty Farwa,

Please Login or Register in order to submit comment