Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake damunta, tsoro da fargaba, tsoron haɗuwa da iyayenta da fargaban hukuncin da zasu mata, “Hajna ba abunda zai sameki, ki kwantar da hankalinki, su Umma zasu yi farin cikin zuwanki ", kallonshi tayi tace “ ina kunyar haɗa ido da umma, Umma ta yadda da ni fiye da tunaninka", “karki damu love, komai zai dai-daita, kuma zasu karɓe ki hannu biyu ", da haka suka yi sallama dan ganin dare yayi.

Asuba ta gari.


Sai mun haɗu a AJIYAWA.



HAƊIN GUIWAR
Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya


ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️🌎🌎♻️♻️
[8/20, 10:16] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
,
🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAGE 83-84
**********************
WASHE GARI DA SAFE

Tun da asubar Aunty Farwa da Hajna suka kama hanyar Zamfara, wanda Farween yake tuƙa su, tafiya ce me tsayin gaske, jirgi suka hau zuwa Abuja, inda suka hau mota daga Abuja zuwa Zamfara, a cewar Farween tafiyar zata ƙara musu sani idan suka yi a mota, Hajna kuwa ta kasa sukuni, tunanin yadda zata tunkari su Baffa take yi, Aunty Farwa ce ta dafa kafaɗarta, “Hajna tunanin me kike yi", shiru ta yi dan bazata iya cewa komai ba, faɗuwar da gabanta ke yi ba ƙarami damunta yake yi ba, Farween yace “ki bar min mata, kin san ba magana ta fiye yi ba ", Aunty Farwa tace “ to masu mata waya ɗaura auren", Farween yace “yoo masu ɗaurawa mana ", “ba sai an baka ba" Aunty Farwa ta faɗa, Farween ya ɓata fuska “kinga Aunty Farwa ki ƙara min ƙarfin guiwa shine zaki sare min guiwa ", murmushi ta mishi, sannan tace “ ni ina ji a jikina an baka Hajna an gama", murmushi yayi shi ma, sannan yace “wannan ita ce ƙwarin guiwar da ta fi ko wace ", fira su ke yi sama-sama, wanda Hajna bata ma san me su ke faɗa ba.

    Basu isa Zamfara ba sai ƙarfe 8:30 na dare, ganin dare yayi gashi duk sun gaji yasa suka tsaya gusau, suka nemi masaukin baƙi, Aunty Farwa ce ta tashi Hajna lokacin da motarsu ta tsaya a gaban Maryam hotel, ɗaga idonta ta yi, gabanta ne ya faɗi lokacin da ta sauke idonta a hotel ɗin, ba wadda ta zo mata a rai irin Fahna, da sauri ta dafe ƙirjinta, bata son wani abu ya sake tuna mata da rayuwar baya, Farween ne ya matso dab da ita, “ki cire komai a ranki baby, zamu kwana nan, amma gobe da safe zamu bar nan, ki sani komai zai zo da safe, ke dai kawai ki yawaita maimaita hasbunallah wani'imal wakeem, la'ilaha illa antas-subahanaka inni kuntu minaz-zalimin, insha Allah tsoronki da fargabanki zai gushe, kuma ko minene zai zo miki da sauƙi insha Allah, ki tuna ina gefenki a kowane yanayi, kuma zan so ki a ko wane hali ",murmushi kawai ta mishi, dan ita a yanzu bata fahimtar komai.

     Hannunta ya kama su ka shiga cikin, wani yanayi ya ke ji, dan wannan shi ne karo na farko da ya taɓa hannun mace, ita ma Hajna akwai dalili, dan baya da wani zaɓi da ya wuce ya tallafa mata, ita ma ɗin yadda ya ke ji haka ta ke ji, runtse idonta ta yi, yanzu ta tabbar tana son Farween, dan bata taɓa jin irin haka akan Qaseem ba,  ɗaki ɗaya su ka kama, shi zai kwanta a parlor, Aunty Farwa da Hajna kuma a ɗaki, wanka Farween ya shiga yayi, lokacin su Hajna na parlor, bayan ya fito ne ya dawo parlor, ɗaki su Aunty Farwa su ka nufa, dan dama Hajna barci ta ke ji, a daddafe tayi wanka dan kanta yana mata ciwo, wanda Aunty Farwa ta alaƙanta da kukan da ta ke yi.


WASHE GARI

Tun da asuba kayan Baffa su ka iso, wani shago na gani kusa da gida, ba laifi shagon babba ne, takalmin maza da mata ne, dan haka aka zuba su a ciki da alama sabon kasuwanci da Baffa zai fara kenan, Umma ya shiga kira dan ta zo ta saka ma kayan albarka, tare su ka fito, farincikin da ke fuskantar ya bayyana sosai, amma ta wani ɓangare tana jin ciwo, da su ke farinciki amma Hajna bata nan, “masha Allah, kaya sun yi, Allah ya sa alkhairi, kuma ya Allah ya ɗaga darajarka, ya sa nan abincinmu ya ke "Umma ta faɗa, Baffa yace “ameen Amina, Allah ya haɗa mu har gidan aljanna", “ ameen" ta faɗa, juyawa ta yi, dai-dai lokacin wata ƙatuwar mota ta danno kai cikin unguwar, hakanan Umma ta ji murmushi ya bayyana a fuskarta, Baffa ma idonshi na kan motar, motar tinted glass gare ta, dan haka baza su iya ganin wanda ke ciki ba, Hajna da ke cikin mota, bata san lokacin da hawaye su ka sauko a kuncinta ba, tayi kewar komai da ke gurin, duk da su Umma sun ƙara tsufa, amma bazata taɓa mantawa da su ba.

Ba tare da ta jira Farween ya gama parking ba ta buɗe ƙofar, gudu ta ke yi, dan akwai tazara sosai daga inda su ke zuwa inda take, su Umma sun riga sun juya za su shiga gida, sai jin mutum suka yi a bayansu, ta rungume su, wani sanyi Umma ta ji, wannan sanyi a gurin Hajna kawai ta ke jin shi, duk lokacin da Hajna ta rungume ta to haka take ji, “Hajna! " umma ta faɗa tana juyowa, baffa ma juyowa yayi, gaɗa mata kai Hajna ke yi, alamar eh ita ce, rungume juna su ka yi, sai kuka su ke yi, dai-dai lokacin Farween da Aunty Farwa su ka ƙaraso, Baffa ne ya lura da su, dan haka ya musu iso zuwa cikin gida, Umma da Hajna kuwa sai kuka su ke yi, da ƙyar Baffa ya ja su zuwa ciki, zama su ka yi kan tabarma, cikin nadama Hajna ta ɗago idonta tana kallon gidan, gidan ya canza, ɗakinta ma an gyara shi, kallon Baffa ta yi tace “Baffa! " sai kuma tayi shiru, kallon Umma tayi, cikin muryar kuka tace “Umma!" amma ta gagara ƙarasa maganar sai hawaye, Aunty Farwa ce ta dafa kafaɗarta tace “Hajna ki fara daga farko, zasu saurare ki, su ɗin iyayenki ne ", hawayen da ke kuncinta ba ƙaramin damun Farween su ke yi ba, da sauri ya tashi ya matso kusa da ita idonshi sun cika da ƙwalla, cikin sanyin murya yace “ Hajna bazan jure ganin kukanki ba, kukan ya isa haka" ya faɗa yana miƙa mata handkerchief, karɓa tayi, sannan ta ƙaƙalo murmushi ta mishi “na gode " ta faɗa, tana jan dogon numfashi, “Umma, Baffa, kuyi haƙuri, nayi kuskure kuma na shirya karɓar hukuncin da zaku min, amma bazan jure fushinku a kaina ba, na share shekaru ina so na dawo gare ku, amma bansan da wane ido zan kalle ku ba", Baffa yace “ba laifinki bane ke kaɗai har da nawa, na tsananta miki sosai, wanda haka yana janyo matsala sosai, kiyi haƙuri" da sauri ta riƙe ƙafarshi, “baffa ba laifinka, nawa ne, na ɗauki muguwar huɗu ba, Umma dan Allah ki yafe min, na karya yardarku " ta ƙarasa tana kallon Umma, “Hajna na daɗe da yafe miki, dan nasan ƙaddara ce, ina fatan karki maimaita irin wannan kuskuren wata rana" Umma ta faɗa, “Baffa baka ce komai ba "Hajna ta faɗa hawaye na bin kuncinta, “Hajna ni me zan, bani da abunda zance sai dai na gode ma Allah da ya dawo min da ke hanyar dai-dai, wannan abun da ya same ki ya faɗa min tsanani bazai gyara komai ba, na yafe miki duniya da lahira, amma da sharaɗi akai ", Hajna tace“ a shirye na ke da na yi duk abunda kake so", Baffa yace “ zaki auri wanda na zaɓa miki a matsayin miji, sannan za'a yi auren sati me zuwa ", da sauri ta ɗago jin yadda gabanta ke faɗuwa, sosai hankalinta ya tashi, Farween ma haka yake a ɓangarenshi, kallon Hajna yayi ya mata alama da kai, akan ta amince da zaɓin mahaifinta, da ƙyar ta natsar da kanta, cikin sarƙewar za ce tace “eh, Baf..fa na yar.......da", “to shi kenan, waɗannan su waye? "ya faɗa yana nuni da su Farween, nan Hajna ta kwashe duk abunda ya faru da ita, tun daga ranar da ta bar Ajiyawa, har zuwa yau da take nan, amma banda labarin soyayyarsu da Farween, sosai hankalin Baffa ya tashi, yanzu wannan mummunar rayuwa ƴar shi tayi, Umma ma haka yake a ɓangaren Umma, godiya Umma ta yi tace “muna godiya Farwa, abunda kika yi wa Hajna shi ne abunda ya kamata ace mun yi, muna godiya da kika maye gurbin mu a lokacin da bama nan ", “ba komai, ai Hajna ƙanwa ce a gareni" Aunty Farwa ta faɗa, ɗakin Baffa Farween ya sauka, sai Hajna da Aunty Farwa ɗakin umma, dan a cewar Umma yau tare da ƴarta zata kwana, sosai Hajna ta ji daɗi, yanzu take jin rayuwarta ta cika, amma idan ta tuna Farween sai ta ji ina ma rayuwa ta basu damar zama tare har abada, ita abunda ya fi damunta shi ne bata san wa za'a aura mata ba.


To masu karatu, ana wata ga wata in ji bahaushe
KO WAYE MIJIN DA BAFFA ZAI AURA MATA?, NI DAI NACE ALLAH YASA BA QASEEM BA NE.


ANAN ZAN DAKATA.



KARKU MANTA KU YI FOLLOWING ACCOUNT ƊINA TA LINK ƊIN DA KE SAMA.



ALQALAMI YAFI TAKOBI✍️
[8/21, 16:55] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
,
🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAGE 85-86
***********************

Barci Aunty Farwa ke yi, saɓanin Hajna da ta zauna a ɗakin zugum, kallon Umma ta ke yi, yadda ta ke barci hankalinta kwance, yanzu da gaske Baffa ne zai mata zaɓin wanda zata aura, hawaye ne suka zubo daga kuncinta, Umma da ke kwance a gefen Hajna a hankali ta shiga buɗe ido, mamaki ne ya kamata lokacin da ta sauke idonta akan Hajna, da ko alamar barci babu a tare da ita, “Hajna " Umma ta faɗa cikin muryar barci, zubur ta juyo dan bata yi tunanin Umma zata farka a irin lokacin nan ba, kallon Umma take yi ba tare da ta amsa kiran da ta mata ba, “mi kike yi a irin lokacin nan baki yi barci ba" Umma ta faɗa tana tashi zaune, “babu komai " Hajna faɗa a taƙaice, Umma tace “na lura tunda Baffanki yayi maganar aure ki canza", shiru Hajna tayi, ko kaɗan bata yi mamaki ba da Umma ta fahimce halin da ta ke ciki, dan tun tana ƙarama Umma ke fahimtarta, kuma har yanzu haka be canza ba, “kina da wani zaɓi ne na mijin aure? " Umma ta katse mata tunanin da take yi, idonta su ka ciko da hawaye, tana kallon Umma, a yanayin da ta ke bazata iya furta komai ba, “Hajna ni mahaifayarki ce, kuma har abada bazaki samu kamata ba, ina sauraren kowace damuwa ta ki, ki faɗa min ko minene, zan nema miki mafita " Umma ta ƙarasa maganar tana me tausayin ƴarta, Hajna tace “Umma, Farween shi ne zaɓina, bazan juri rasa shi ba, amma kuma bazan juri fushin Baffana ba, dole na karɓi hukuncinshi, duk irin tsananin da hukuncin zai zama, amma kuma hukuncin da Baffa ya ɗauka Umma zai iya kashe ni ", Umma tace “na fahimci hakan, tun bayan shigowarku, amma kuma Qaseem ya zo neman aurenki tun bakya nan, Hajna kiyi haƙuri ina tunanin Qaseem shi ne zaɓin mahaifinki", da sauri Hajna ta zabura “Umma, Qaseem fa kika ce, bazan auri Qaseem ba, bana sonshi, Umma zan iya mutuwa idan na auri Qaseem, Umma ki faɗawa Baffa ya aura min ko wane irin mutum, kuturu, musaki, gurgu ko makaho, wallahi zan aure shi, ko ya nakasarshi take ni zan aure shi, amma Umma bazan auri wanda ya ruguza min rayuwa ba, Umma ki cewa Baffa ya kashe ni zai fi, amma kar ya aura min Qaseem "cikin kuka take maganar, dan a yanzu ji take dama ta mutu tun tana yarinya, dama bata ga irin yau ba, cikin tsawa Umma ta dakatar da ita “Hajna! Yi min shiru, baki ji, bansan me ya ke damunki ba", hawaye ne ke bin kuncinta ɗaya bayan ɗaya, “Umma to ni zan kashe kaina", da sauri Aunty Farwa ta miƙe, wanda hayaniyar su Umma ya tashe ta,“Hajna kina hauka ne? Ya za'a yi ki kashe kanki, miye matsalarki? ", “Aunty Farwa, Qaseem za'a aura min fa" Hajna ta faɗa tana runtse idonta, wani zafi ya ziyarci zuciyar Aunty Farwa, ita ba Farween take ji ma ba, Hajna take ji ma, be kamata a aura mata mijin da baya girmamata ba, “Hajna ki natsu, ki zuba wa sarautar Allah ido, haƙuri shi ne matakin nasara gare ki, gobe insha Allah ni da Farween zamu wuce, na miki alƙawari zamu dawo ɗaurin aurenki tare da su Halia, amma bazamu tsaya ba " Aunty Farwa ta faɗa, Hajna tace “ Aunty Farwa dan Allah kar ku tafi, abun zai min yawa yadda baki yi tunani ba", Umma zata yi magana kenan sautin kiran sallah ya daki kunnensu, dan haka, kowa ya fito domin yin arwala.


Bayan sun yi sallar asuba, Hajna ta gyara gidan, sannan ta shiga kitchen ta ɗaura abinci, ƙarfe 8:30 ta kammala aikin gida, lokacin kowa ya tashi, zaku iya ganin yadda hankalinta yake a tashi, domin kuwa idonta ya bayyana haka, Baffa ne ya fito tare da Farween, wanda idan ka kalli Farween zaka ga tsantsar tashin hankali a idonshi, wani zafi yake ji a ranshi, ya share shekaru da dama yana ɗawainiya da son Hajna, tun bata sani ba, har ta zo ta san yana sonta, yanzu da yake ganin damar mallakar ta, ya rasa ta, runtse idonshi yayi dai-dai lokacin da ya zauna, dan shi tun jiya ya gama haɗa kayanshi, bazai jira ba zai tafi kawai, dan bazai iya ganin Hajna a irin halin nan ba.


Zama suka yi kan tabarma, Umma ma tana zaune daga gefen Baffa, Farween da Aunty Farwa a gefe ɗaya, abinci Hajna ta kawo, sannan ta zauna, sakwara ce da miyar ja, ita ta zuba ma kowa, amma banda kanta, “ke fa, bazaki ci ba? " Baffa ya tambaya yana kallonta, “a'a ni na ci tun ɗazu" ta faɗa cikin dakiya, duk da ba abunda ta ci, Baffa na lura da yanayin Farween , tunda ya zauna be ci komai ba, gashi har abincin ya huce, Aunty Farwa ce tace “Farween bake ci komai ba fa, miyasa?", Farween yace “na ƙoshi, kiyi sauri ina so zamu wuce ne, wani aiki ya taso min na gaggawa", Umma tace “wane aiki ne wannan? ", shiru yayi da bashi da abun cewa, Baffa yace “ kafin ka tafi ina so na tambaye ka", Farween yace “kai mahaifi ne a gare ni dan haka ka yi kowace tambaya ni zan amsa maka ita ", Baffa yace “ya kwatankwacin yadda yake son Hajna", rads! Gabanshi ya faɗi, sosai tambayar Baffa ta zo mishi a matsayin bazata, “ina sonta fiye da yadda zuciyata zata ɗauka ", Farween ya faɗa wasu hawaye na bin kuncinshi, Baffa yace “daga jiya zuwa yau na lura da yanayinku kai da Hajna, dan haka na yadda da aurenku, nasan ba wanda zai riƙeta kamar yadda zaka yi", zare ido yayi irin ni?, gaɗa mishi kai baffa yayi alamar eh, shi, Aunty Farwa ta yi sauri cewa “kai masha Allah ina taya ku murna, Baffa kayi ceton rai, muna godiya sosai ", Umma tace “ to ƴar leleta, sai gode ma Allah", rufe fuska Hajna tayi, a ranta tace Alhamdulillah, Farween yace “Baffa bani da bakin gode maka, kyautar da ka min a yau ita ce kyauta mafi girma da na taɓa samu a rayuwata, nagode da babbar kyautar da ka min, kuma na maka alƙawari ahalina su ne ahali na biyu a gurin ƴarku ".


Anan zan da sa aya.


Iya yawan comments ɗin ku, iya yadda zan yi update kun san mun shiga satin karatu, dan haka idan baku comment zan maida hankalina can makaranta, idan kuma kuna yi zaku ji ni on time.

TO READERS YA KUKE TUNANIN QASEEM ZAI YI BAYAN YA NEMI AUREN HAJNA, GASHI YANZU BAFFA YA BA FARWEEN.

ƘARA-ƘARA-ƘARA, GA AKUYA GA KURA.


love u all fans.


INA MATUƘAR SONKU.


ALQALAMIN QUEEN ❤️❤️

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💖
[8/25, 18:31] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
,
🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

HAPPY BIRTHDAY TO ME
YAU NA CIKA SHEKARA, INA ROƘON ALLAH DA YA BANI IKON GANIN RANAR YAU YA ALBARKACI RAYUWATA TA GABA, KUSKUREN DA NAYI A CIKIN SHEKARUN NAN RABBI YA YAFE MIN, WAƊANDA ZAN AIKATA ALLAH YA HANA NI.
DEARIES UR QUEEN IS PLUS ONE KU SAKA NI A ADDU'ARKU 💞💞💞 MUAH 🎂👑🎂🎂🎂🎈💐🎊🎉


PAGE 87-88
**********************

Sosai Farween yayi farinciki da hukuncin Baffa, basu wani jima ba su ka wuce, da niyyar zasu dawo wani sati, tun a Airport Aunty Farween da Farween su ka rabu, dan ita daga nan Dubai zata je, haɗo kayan ɗakin Halia, da kuma kayan lefen Hajna, tafiya ce mai ɗan nisa.

Cikin gida ya shiga, inda ya tarar da su Halia a parlor da alama jiransu su ke yi, da gudu Halia ta rungume shi, “baby I miss you " ta faɗa, murmushi yayi yace “I miss you more baby", Aisha ta matso tace “Uncle ina Mommy ", Farween yace “na siyar da ita na ci ƙuli-ƙuli a hanya", turo baki tayi, “ta wuce Dubai "ya faɗa, zaro ido tayi “Dubai kuma, gurin me?", “haba Aisha, duk na gaji kin zo kina min tambayoyi kamar ƴar jarida " ya faɗa yana rufe ido, “to Uncle, ruwan zafinka na toilet, ka je kayi wanka, idan ka ci abinci sai ka faɗa min", be kula ta ba ya wuce abun shi, toilet ya shiga yayi wanka, ya jima sosai a toilet, dan sai da ya huce gajiya, yana fitowa ya ji wani iska na ratsa shi, murmushi yayi, jin yadda yake jin wani sanyi na ratsa ko ina na jikinshi, ya ɗauki 30 minutes yana shiryawa, sannan ya fito, har yanzu su Aisha na inda ya bar su Aisha nan ya same su, dama shi su ke jira, dan haka dinning area su ka nufa.

“waya dafa abincin nan? "Farween ya tambaya lokacin da ya kai abinci bakinsa, Halia tayi saurin cewa “ni na dafa shi", Aisha tace “hmmmm", Farween yace “minene hmmmm ", Halia tace “ƙyale ta dan ta daka min kayan ƙamshin miya shi ne tace wai ita ta dafa", Aisha tace “Uncle wallahi tare mu ka dafa", Farween yace “ na yadda da ku duka, ni ku barni na ci abinci, abincin ma da ba daɗi yayi ba shi ne kuke rigima ", Halia tace “lallai ma baby, yanzu abincin ne be yi daɗi ba", Farween yace “ki bari matata ta zo, idan ta dafa mu ku abinci sai kun cije ɗan yatsa ", Aisha tace “ai abincin matar taka sananne ne, dan haka ba wani cije hannu da zamu yi", Farween yace “ to yayi bari ta zo ɗin, mommynki zata wuce da ku Ajiyawa idan ta dawo daga Dubai ", Aisha tace “wai me ta je yi can", Farween yace “ta je haɗa kayan ɗakin Halia ne, da kuma kayan lefen matata ", ihu Aisha ta fara yi tana rungume su, farincikin da ke fuskarsu daga ita har Halia bazai ɓoyu ba.


AJIYAWA
“Umma wai ina labarin Fahna" Hajna ta faɗa tana kwance a cinyar Umma, “wai baki da labari dama? " Umma ta tambaya, Hajna tace “labarin me, ai ni na jima ban ga Fahna ba, tun ranar da ta turo ni kan titi tayi tafiyarta", Umma tace “ai Fahna ta riga mu gidan gaskiya ", wani rasssss! Taji, gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗago daga cinyar Umma, “innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!" ta ke maimaitawa da ƙarfi yafi sau uku, wasu hawaye ne su ka fara ambaliya a fuskarta, “Hajna ki natsu mana"Umma ta faɗa tana dafa ta, ganin ta ratsa natsuwa, “Umma Fahna ta mutu....." bata ƙarasa maganar ba wani kukan ya ci ƙarfinta, Umma tace “to minene, ko ke baki wuce mutuwa ba, Hajna ki natsu mana", Hajna tace “ Umma Fahna ta mutu kuma kike tunanin na natsu, Umma ita kaɗai ce ƙawata, duk abunda zata min bazan manta da cewa ta tsaya min a lokacin da muna yara " hawaye su ka zubo mata, umma ta share mata hawaye “Hajna na sani, yanzu addu'a kawai zaki bita da shi, sannan babbar kyautar da zaki mata shi ne ki yafe mata duk abunda ta miki, dan kinsan ta mutu da haƙƙinki a kanta", “Umma ni na yafe mata, kuma tun dama can ban riƙeta a raina ba " Hajna ta faɗa, Umma tace “to yayi bari na shiga daga ciki.


Zaune Umma ta bar Hajna, tunanin Fahna take yi, ko kaɗan bata so Fahna ta mutu a irin yanayin nan ba, ta mutu a lokacin da bata tuba ba, ta tuna yadda Fahna ke tsaya mata lokacin da ake tsokanarta, kasancewar ita tun tashinta yarinya ce da bata fiye magana ba, sannan bata da hayaniya, ƴan ajinsu suna yawan tsokanarta, Fahna ita ke tsaya mata a kowane lokaci, duk lokacin da bata da wani abu Fahna zata raba nata biyu su yi amfani da shi, idan bata manta ba Inna ce ta fara ɗaura Fahna akan harkar bin maza, lokacin su na da shekara 14 a duniya, “kin gan ki Fahna maza zasu yi ribibinki, saboda dirinki " kullum maganar Inna kenan, tun Fahna bata fahimta ba har ta zo ta fara tunanin minene diri da Inna ke faɗa a ko yaushe, sai ranar a makaranta suka ji wata na magana tana cewa “da ni ke da irin dirin Hajna da Fahna, da na yi kuɗi da surata" yarinyar ta faɗa, Fahna tace “wai Hajna minene diri, kuma ya ake samun da diri ", Hajna tace “ke yanzu idan kika san miye diri hala kuɗin zaki nema?", Fahna tace “da gudu ma, ai wallahi yadda na ke son kuɗi ba wata matsala ba ce dan na nema, ai ina da abun kuɗin shiyasa ake faɗa ", Hajna tace “to Allah ya kyauta", guri su ka samu su ka zauna, dai-dai lokacin wata yarinya ta zo, dai-dai tsararsu, “ku manyan gari me kuke yi nan? "yarinyar ta faɗa tana zama gefensu, Fahna tace “yauwa dama ina son ganinki, wai minene diri", “ni a yadda na fahimta diri shi ne kina da komai, ke dirarrar mace ce, jikinki ya cika ", Fahna tace “to miyasa maza zasu yi ribibin me diro?", Yarinyar tace “ai maza suna son dirarrar mace", Fahna tace “me zasu yi ", yarinyar tace “idan maza basu bin macen da bata da diri, kuma ta wannan hanyar an fi samun kuɗi", tun daga wannan ranar Fahna ta fahimce me Inna ke nufi, dan haka ta fara bin maza da kanta tana masu tayin kanta, duk abunda ta yi Inna na goya mata baya, tun Hajna na faɗa mata gaskiya tana cewa “wallahi Hajna ƙaddara ce amma zan bari ", har ya kai Fahna ta riƙa bata jin maganar kowa, tana da shekara 16 tayi ciki, inna da kanta ta nemo magani cikin ya zube, da baba ya ga tana kwance kullum sai ya fara tambayar minene matsalar, Inna ta fake da zazzaɓi Fahna ke yi, da ta ga Baba zai iya gano wani abu , sai ta haɗa ma Fahna kayanta ta tura ta gusau gurin Aunty Kareema, a can Aunty Kareema ta buɗewa Fahna ido, daga lokacin Fahna ta zama riƙaƙƙiya a harkar bin maza, gashi ta mutu a tafarkin da ba dai-dai.


“Ke Hajna! "Umma ta faɗa da ƙarfi, firgigit Hajna ta dawo daga tunanin da ta ke yi, “me kike yi har yanzu baki tashi ba?", “Umma wallahi nazarin duniya nake yi, yanzu duk abun

Please Login or Register in order to submit comment