Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/17, 09:27] Queen Nasmah✍️:        ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin:- Queen Nasmerh ; Marubuciyar & Rabiatul Adawiyya; Marubuciyar


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 1-2
*******
Shigowa ta Ajiyawa kenan, wata unguwa ce da ke garin shinkafi, kallon unguwar nayi da kyau, da alama ba masu kuɗi a unguwar duk talakawa ne sai ɗai-ɗaiku zaka gani da rufin asirin Allah, wani gida na gani, ginin gidan ya tsufa, ko fenti babu, shiga nayi inda naga wata doguwar hanya da zata sada ni da cikin gidan, ko ina na gidan an share shi, kuma komai na aje inda ya dace, duk da talakawa ne hakan be hana su gyara gidan su ba.
   Wani tsoho nagani sanye da jallabiya fara ta koɗe sosai, zaune yake akan wata tabarma, daga gefe kuma wata tsohuwa ce zaune sanye da zani daban, riga daban, “Hajna! "Umma ta faɗa,  tana kiran Hajna dake cikin wani ɗaki, wanda ni banyi tunanin mutum zai iya zama gurin ba, rufin ɗakin ma na kara ne, sannan da alama ko ruwan sama aka yi ruwa zasu iya kaiwa gurin.
   Zuwa tayi ta durƙusa gaban su,“ ina wuni Baffa " ta faɗa tana gaida tsohon da ke zaune, ɗagowa yayi yace “lafiya ƙalau", Umma tace “dama Baffan ki ne ke tambayar me ya hanaki zuwa makaranta ", sosa kanta ta shiga yi kamar wata mara gaskiya, duniya ta tsani zuwa islamiya, wata ƙarya ta faɗo mata, “ummm Baffa dama malamin mu ne......" bata samu damar ƙarasawa saboda Baffa ya dakatar da ita “Hajna kiji tsoron Allah, yanzu na haɗu da malamin ku yace min lafiyar shi ƙalau, yau kwananki huɗu baki je makaranta ba, kullum sai kice Malamin ku bashi da lafiya", shuru tayi dan yanzu bata da ta cewa, Umma tace “kayi haƙuri wataƙila ko bata son zuwa ne", Baffa da mamaki ya gama cika shi yace “ke fa na lura baki damu da tarbiyar yarinyar nan ba ", Umma tace “Allah ya baka haƙuri" tashi tayi ta shige ɗayan ɗakin.

   Faɗa yayi wa Hajna sosai dan Baffa mutum ne da yake da tsaurarren ra'ayi, bayan ya gama mata faɗa ne, ta tashi ta ɗauki bokiti ta fita zuwa ɗibar ruwa.

   A ɗayan ɓangaren kuwa wani gidan ne kusa da gidan su Hajna, wata yarinya ce kwance akan wata katifa ƴar ƙarama, waya take yi “yau ina zamu haɗu, wallahi ina mugun kewar ka" ta faɗa tana ƙara gyara kwanciyar ta, daga ɗayan ɓangaren aka ce “ wallahi nima baby nayi missing ɗin lallausar fatar ki ", “ta yayi amma sai ka biya", yarinyar ta faɗa, kallo na ƙare mata, fara ce amma da alama farin bana Allah bane, ina ganin ta haɗa dana bleaching,  “kut, dubu ɗari?, wallahi sunyi kaɗan " ta faɗa, “haba Fahna ki tausaya min kina gani fa wata ya kora ba'a biya mu albashi ba", shiru tayi kamar bata jin shi, “kinji baby ", nan ma shiru bata amsa ba, “ Baby Fahna, na ƙara, zan baki dubu ɗari uku, amma zaki kwana fa", juya ido tayi kamar yana ganin ta tace “ a'a dubu ɗari huɗu, idan ba haka ba malam sai anjima ", “ a'a baby na yadda" murmushi ta saki tace “to shikenan mu haɗu a  maryam hotel " kashe wayar tayi.

     Ɗakin inna ta shiga zaune take tayi tagumi, zuwa tayi ta zauna tace “inna Alhaji Musa yana so mu haɗu yau, kuma wai kwana zan mishi" kallon ta inna tayi a gwatsine tace “ a nawa? " “dubu ɗari huɗu" Fahna ta faɗa, jin an faɗi dubu ɗari huɗu inna ta washe baki tace “to shikenan, kije zan san yadda zanyi da baban ki ", tashi tayi ta shirya cikin wata atamfa mai kyau wanda Alhaji Musa ya ɗinka mata, gyalen ta ta saka cikin jaka, sannan ta rataya, sannan ta kawo hijabi dogo ta saka, fitar ta waje kenan ta haɗu da Hajna ta ɗauko bokiti da ruwa a cikin, alama ya nuna daga gurin ɗibar ruwa take, “ke kalar manya "Fahna ta faɗa, Hajna tace “ƴan matan duniya sai ina?" Fahna tace “gurin samo naira ", Hajna tace “Allah ya shirya min ke", “yo ke Hajna ina zan yadda talauci ya kashe ni, wannan kasadar sai ku ai ", murmushi Hajna tayi tace“a dawo lafiya" , shigewa tayi cikin gida tana mamakin irin wannan rayuwar ta Fahna.

     Tashar mota Fahna ta shiga zuwa Maryam Hotel dake gusau, kiran Alhaji Musa tayi, ya faɗa mata ɗakin da ya kama, guri ta samu ta cire hijabin ta sannan ta yafa gyale, ɗakin shi ta wuce kai tsaye, Kwance yake daga shi sai gajeren wando, tun daga ƙofar ɗaki Fahna ta fara rage kayan jikin ta, dan Fahna in dai karuwanci ne ta shahara, wani girgiza jikin ta take yi tana ƙarawa, na take Alhaji yaji desire shi ta tashi, jawo ta yayi ta faɗa jikin sa, ƙoƙarin raba ta da rigar nonon ta yake yi, yana wani lumshe ido, saurin barin ɗakin nayi.

   Ɓangaren Hajna kuwa kwance take akan katifa tana tunanin rayuwa, yau ko Abinci bata samu ta sa a baki ba, dan ko ruwa ba'a ɗaura a gidan su ba, rufe idon ta tayi lokacin da taji cikin ta na ƙugi alamar yunwa, hawaye ne suka zubo mata, tana zaune taji Baffa ya dawo ranshi a ɓace, fitowar Hajna ya ƙara sa shi jin ba daɗi, tabbas shi zai iya jurar yunwa amma Hajna shekarar ta nawa?, duka-duka shekarar ta 19, ya zata yi da yunwa.
     Umma ce ta fito, “Baffan Hajna ka dawo?, “Eh wallahi, amma yanzu ma ban samo komai ba ", Umma tace “to Allah ya mana mafita, kowa ya sha ruwa, ai marece yayi, gobe Allah zai mana mafita", Hajna kuwa juyawa tayi Zuwa ɗakin ta, ta kwanta, dan an riga anyi isha, rufe  ido tayi, ta furta “yaushe wannan yanayin zai wuce ", zuciyar ta tace ba rana Hajna sai kinyi aure wataƙila, Hajna shiru tayi tace wa zai aure ni, a wannan zamanin, masu kuɗi sai masu kuɗi, talaka ma sai talaka ɗan uwan shi kawai da talauci zan mutu.

  A ɓangaren Fahna kuwa Alhaji yayi aiki, duk ya jijjiga ta, dan duk sha'awar da yake ji sai da ya sauke ta akan Fahna, ita kuwa banda daɗi ba abunda take ji.

Masu karatu ina fatan zaku fahimci labarin mu, saboda zai zo muku a hanyar da bakuyi tunani ba, fatan mu ku yi amfani da darasin da labarin zai koyar. 🤗🤗

    Haɗin guiwar mu ce.

QUEEN NASMERH & RABI'ATUL ADAWIYYA

ALQALAMI YAFI TAKOBI

📚🖊️ *ZAMWA* 🖊️📚
( _Zamfara writters_ )

COMMENTS ƊINKU NA DA MATUƘAR MAHIMMANCI, HAKAN ZAI ƊAURA MU A HANYA. 😂😂😂.

Comments please 🙏🤕
[8/17, 09:27] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin :- Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 3-4
****************
Washe gari da safe wanka Hajna tayi, cikin shirin ta na islamiya, hijabi daga saman shi ya yage dan haka sai da ta sa allura da zare ta ɗinke sannan ta fito, a zauren gidan su ta sami Baffa, gaida shi tayi sannan ya mata nasiha kamar yadda ya saba sannan ta wuce makaranta, a hanya ta haɗu da umma taje samo musu abunda zasu sa baki, gaida ta tayi sannan tace “Umma ko da na tashi ban ganki ba, ina kika je ", “Hajna naje samo kuɗi ne, da ƙyar aka ara min ɗari biyar" umma ta faɗa tana kwance haɓar zanin ta, nuna na Hajna tayi, murmushin ƙarfin hali sannan tace “umma ai da ba kiyi haka ba", “Hajna ina zan yadda yunwa ta kashe ki, zuwa zanyi na siyo mana dawa ko ta ɗari biyu ce, na siyo mana garin kuka ta ɗari, sai na siye magi da icce da sauran kuɗin, na mana tuwo muci, ko ya abinci yake ai yafi babu", “to shikenan Umma ni zan wuce "Hajna ta faɗa tana wuce.

   A ɓangaren Fahna kuwa tun kiran farko ta dawo gida, saboda tasan baban ta shi yake tashin ta da asuba, inna kuwa tunda Fahna ta fita tasa aka kira mata wata yarinya ta kwanta a gadon Fahna, da mahaifin ta ya dawo sai tace mishi ai tayi barci ciwon kai take yi, shi kuma be kawo komai aranshi ba, yanzu ma da asuba shi ne ya tashe ta, da miƙa ta tashi kamar me barci, tana cikin sallah Inna ta shigo ta same ta, bayan ta gama ne ta nunawa inna kuɗin, aikuwa suka ɓoye kuɗin,da safiya ta waye Baba da kanshi ya sa ƙeyar Fahna gaba har makaranta.

Shigowar Hajna kenan ta hango Fahna zaune a gindin wata bishiya, ƙarasawa tayi gurin ta, Fahna tace “Kalar manya har kin ƙarso kenan", Hajna tace “haka dai kika ce ƴan matan duniya ", Fahna tace “wallahi ni Hajna kina bani mamaki, wallahi da kinsan yadda kika dace da irin harkar nan duk da bakiyi ba", hararar wasa Hajna ta mata tace “ke ni ba wannan ba yunwa nake ji banci komai ba tun shekaran jiya", Fahna tace“ baga irin ta nan ba, nace miki kizo ki fara bin maza kin ƙi", “haba Fahna ni fa kinsan iskanci na be kai nan ba, ni ban iya baɗala irin taki ba, kuma bayan haka ma kinsan ni da shegen tsoro, kuma Baffa zai iya kashe ni duk ranar da ya samu labari", Fahna tace “nima ɗin ai Baba zai iya kashe ni na keyi, minene a ciki, ni wallahi bazan mutu da talauci ba", Hajna tace “ke kika ji zaki iya ni bazan iya kasada da mutunci na ba", Fahna tace “ai ke komai mutunci ke kika sani ", Hajna tace “naji dai, kema Allah ya shirye ki".

    Haka suka cinye lokacin karatun su a waje suna surutu, a hanya Fahna ke gayawa Hajna kuɗin da ta samu yanzu, dubu goma taba Hajna, murmushi Hajna tayi tace“ nagode ", gidan su Fahna suka fara shiga, inna ta dafa musu tuwon shinkafa da miyar kuɓewa suka ci sannan inna ta zubawa Hajna a wani kwano tace “gashi Hajna ki kaiwa mahaifiyar ki", Fahna ta rakata har gida, Umma na ta godiya taji daɗi sosai, ɗakin Hajna suka shige, dawani kallo Fahna ke bin ɗakin, “Hajna wannan ba rayuwa bace, me kika rasa a jikin ki da namiji zai ƙi, kawai kiba maza haɗin kai ki biya buƙatar ki, yanzu kalli ɗakin ki, dubi kayan jikin ki, ki kalli cikin kwali kike aje kayan ki, duba kiga takalmin ki ma duk sun tsufa", Hajna tace “to se me Fahna haka Allah ke son ganina ", Fahna tace “bawani barda son ranki rayuwa ta baki dama, kuma Umma macece da ba ruwanta da tarbiyar yaranta, bata takura miki zaki iya yin duk abunda kike so" Hajna tace “to shi Baffa fa ina zan kai shi, kinga Fahna ki bar maganar nan kawai ke bazaki taɓa ganewa ba ", Fahna tace “to shikenan kanki ki yiwa bani ba", dagan kuma sai suka canza fira akan wani da yake son Hajna  “ke Hajna inda ma yana da kuɗi minene ciki dan kin kula shi ", Hajna tace “nifa bama maganar kuɗi ba ni kwata-kwata be min ba", dariya suka sa, Fahna tace “wani ƙolo da shi ko kaya yasa basa masa kyau", “ashe kema ki lura"Hajna ta faɗa, haka suka dinga gulmar ganyen nan har aka yi ƙarfe 9:00 sannan Fahna ta wuce gida.

Ƙarfe 12:30 na dare, Hajna na kwance har yanzu bata yi barci ba, abunda Fahna ta faɗa mata ɗazu shi yake mata yawo akai, tabbas tana da duk abunda maza suke so, amma bazata iya ba, a haka har barci ya ɗauke ta.

   ABUJA........

  Kwance yake akan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, da alama wayar da yakw yi ta mishi daɗi, kallo na ƙarewa gidan ya haɗu, iya haɗuwa, zagaya ko ina na gidan nake yi saboda naga wayar tashi ba mai ƙarewa bace gashi bana ma jin me yake cewa, mamaki fal raina lokacin dana fahimci ba kowa a gidan sai masu aiki ƴan mata guda biyar, masu karatu idan kuka gansu zaku rantse ba ma'aikata bane uniform ɗinsu zai nuna miki su ma'aikata ne, wata riga ce mai wutsiya gefe da gefe ajikin su, a bayan ko wacce an rubuta aikin ta, (cooker, cleaner, washer, dresser, da kuma gardener) abin ya matuƙar bani mamaki dana ga rigar su kamar kayan barci, kowa aikin gaban shi yake.

   Dawowa nayi parlor inda nasamu ya gama waya, fuskar shi na ƙarewa kallo bashi da makusa, dan kyakkyawa ne fiye da tunanin ku, sajen fuskar shi ya kwanta sosai, latsa wani abu yayi ba'a yi minti uku ba sai ga cooker ta shigo ɗauke da abinci, ita tayi feeding ɗinshi da kanta sannan ta bashi lemu yasha ta bashi ruwa sai ta wuce, ni kuwa nace wanene wannan mutumin mai ji ji da kai.

   Wayar shi naji tayi ƙara sakw ɗauka yayi daga ɗaya ɓangaren naji ance “Qaseem kana ina shugaba na neman mu "tashi yayi da sauri ya shiga ɗaki, wanka yayi sannan dannan wani abu sai ga dresser ta shigo, ita ta taimaka mishi ya shirya ta fita, ohhh ni ina ganin ikon Allah namiji da suna ummi 😂.

Masu karatu nasan zaku so sanin wanene wannan ɗan faɗin ran 💃kusance damu dan jin yadda zata kasance.

I love u so much my fans, muna godiya da comment ɗinku tabbas kun nuna mana so 💕❤️❤️❤️

Haɗin guiwar QUEEN NASMERH & RABIATUL ADAWIYYA.

ALQALAMI YAFI TAKOBI.

📚🖊️ *ZAMWA* 🖊️📚
( _Zamfara writters_ )

https://www.facebook.com/Zamfara-Writers-Association-zamwa-110643447448245/

  COMMENTS PLSS🙏🙏❤️❤️💕💕🤕😑.
   
[8/17, 09:29] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 5-6
***************'
Office ya nufa inda oga ke kiran sa, a ƙofar shiga meeting ɗin ya haɗu da Farween, kallon wulaƙanci yake ma Farween dan a duniya ba wanda ya tsana irin Farween, a ran Farween murmushi kawai yayi yace Qaseem kenan Allah ya maka magani, to masu karatu kunji dai wannan sarkin faɗin ran sunan shi Qaseem.
      A meeting hall ɗin suka zauna inda kowa yayi shiru yana jiran abunda za'a ce, kallon kallo ake yi tsakanin Qaseem da Farween, jin gyaran muryar ogan su ne yasa suka maida hankalin su, bayani yayi akan cigaban da za'a kawo a company ɗin da kuma ƙarin salary ma kowane ma'aikaci.
 
  Meeting ɗin yayi kyau sosai, kamar dai ɗazu a ƙofar fita hall ɗin yayi karo da Farween, wani jawo shi yayi yace “kai wani irin mutum ne, taya zaka na bibiya ta, nasha faɗa maka ni ko hanya bana fatan ta haɗani da kai ", murmushi Farween yayi ma kashe zuciyar maƙiyi sannan yace “ni bani da lokacin kula sakarai irin ka, idan baka son ganina ka kashe ni mana", maganar da Farween yayi tayi matuƙar ɓatawa Qaseem rai, amma sai ya haɗe rai ya wuce da kallo Farween ya bi bayan Qaseem, cikin kallo irin na natsane ka, shi kanshi ya tsane Qaseem saboda mugun halin shi.

     Kai tsaye gida Qaseem ya wuce, already anyi magrib, wanka yayi sannan ya ɗauro arwala ya zo yayi sallah, parlor ya dawo ya zauna, yana kallo, har yanzu ma'aikata na kai-kawo a gidan, kowa sai aiki yake yi.

**********
AJIYAWA
  Kwance take akan katifar ta, kasancewar daren jiya anyi ruwa duk sun jiƙata, dan karan ta aka rufe samman ɗakin ta bazai hana ruwa kaiwa ba, zazzaɓi ya rufe ta, Umma na gani zaune daga gefen ta tana jiƙa mata maganin gargajiya, bayan ta gama ne ta bata sannan tace “Hajna bari naje na ɗebo miki yanɗori, a dafa miki, insha Allah zazzaɓin ki zai sauka", gaɗa kai tayi dan bazata iya yin magana ba.


Fita Umma tayi, bayan gidan su naga ta zagaya gurin daji ne, ɗibar yanɗori tayi sannan ta koma cikin gida, tukunya ta ɗaura a wuta sannan ta dafa maganin, Hajna na kwance a ɗaki Umma ta shigo da maganin ta bata, sauran tuwon jiya Umma ta ɗauko ta miƙa mata “karɓi maza ki cinye, yanzu zazzaɓi zai sauka bari na je na gyara ɗaki na duk ruwa sun ɓata shi.

Ɗakin ta tashiga, masu karatu kar ku so kuga ɗakin su Umma ashe ɗakin Hajna Aljannar duniya ce akan na su umma, duk saman gurin ya hude, ɗakin duk ruwa sun ɓata shi, idon Umma ya cika da hawaye tace “ya Allah ka mana sassauci " gyara ɗakin tayi sannan ta gyara ɗakin Hajna, lokacin barci mai nauyi ya ɗauki Hajna.

   Bata farka ba sai da aka yi sallar azahar, wanka tayi sannan tayi sallah, tana saune a tsakar gidan su Baffa ya dawo da leda a hannun shi, ya miƙawa Umma sannan yayi wa Hajna ya jiki, abinci Umma ta ɗaura, suka dawo suna fira, Hajna kam shiru tayi dan bata magana in dai su Baffa na magana.

    Suna zaune Umma ta zuba musu abinci suna ci, Fahna ta shigo, zaunawa tayi ta gaida Baffa, “Lafiya ƙalau Fahna ina iro", cewa da mahaifin ta wanda ya kasance babban aminin Baffa, “yana gida "Fahna ta faɗa, Baffa yace “to ki gaida shi", “insha Allah "Fahna ta faɗa tana kama hannun Hajna suka shige ɗaki, da kallo Hajna ke bin ta, “wai minene kika wani jawo ni ɗaki" Hajna ta faɗa tana haɗe rai, Fahna tace “nifa wuya ta dake kenan ba'a miki abun arziki ", Hajna tace “wane abun arziki, ke kina da maganar da ta wuce ta maza ne", Fahna ta ɓata rai tace “to ai hanyar da ake yin kuɗi kenan, Hajna sai in baki son gaskiya amma kinsan dole sai an bi maza za'a yi kuɗi "Hajna tace “ke kike ganin haka ni ban gani ba, kuma hanyar arziki zata zo ta inda banyi tsammani ba, kar ki sake min maganar nan", Fahna tace “ni bazan gaji da jan ra'ayin ki ba, tabbas watarana zaki fahimta", Hajna yi tayi kamar bata ji me Fahna ke cewa ba, ganin Hajna bata karɓi zancen ta ba yasa suka canza labari.

    A ɓangaren Qaseem kuwa bayan yayi sallar isha ɗaki ya wuce ya latsa wayar shi, da misakin ƙarfe 9:30 na dare naga ya danna wani abu cikin minti 5 sai ma'aikatan nan nashi su biyar sun shigo, kallon su nake yi a raina nace su kuma waɗannan me ya kawo su nan cikin dare, kallon su naga yana yi, lokaci ɗaya naga ya nuna mutum biyu daga cikin su, sauran suka fita,

Please Login or Register in order to submit comment