Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gashi ya zuba mata ruwa, idon ta ta ɗago ta kalle shi, wanda hawaye suka fara ambaliya a fuskar ta, yace "na baki minti 10 ki shirya zamu fita", kallon agogon shi yayi sannan yace "ƙarfe 6:30 zaki fito daga ɗakin nan, yanzu 6:20" juyawa yayi ba tare da ya ji me zata ce ba, wanka tayi a gurguje, shirya tayi cikin wata shadda lemon green, tayi matuƙar yi mata kyau, gyale baƙi ta sa da takalmi baƙi, sannan ta fito, agogon shi ya duba gani ta fito, yaga 6:29,bata ma yi minti 10 ba, zaunawa tayi, amma be ce da ita komai ba, sai da 7:00 tayi daidai sannan yace "tashi muje", bin shi kawai tayi, fuskar ta kuwa duk ta kumbura saboda kuka, gashi daga gefen goshin ta kana ganin alamar buguwa, da inda ya fashe, tafiyar ta ɗauke su tsawon minti talatin sannan suka isa offishin, fitowa yayi ya buɗe mata gida gaba, kasancewar ya hango ogan su a bakin ƙofar shiga, hannun ta ya kama suka nufi, inda yake, Farween da zuwan sa kenan yaga Hajna, mamaki ya cika shi, idan be manta ba wannan yarinyar dadiron shi ce, ai tana zuwa office ɗin shi ta kowa mishi abinci, a ranshi yace oho dai, ni ba auren da zanyi ba shiri nan take ace nayi aure, ai ba dole bane sai nayi mulki.

Zuwa suka yi suka gaisa, sannan suka shiga cikin ma'aikatar, offishin shugaban suka shiga, inda yace "kai Farween ina matar ka "dummmm zuciyar Qaseem ta buga, tsoro da fargaba suka cika shi kar ace Farween ya riga shi yin aure, Farween yace "ranka ya daɗe ban yi aure ba", gaɗa kai ogan yayi yace "kai fa Qaseem ", "ga ta nan ranka ya daɗe", murmushi yayi yace" to Farween zaka iya tafiya na gama da kai, kai kuma Qaseem gobe zaka fara aiki matsayin shugaba, zan sanar da kowane ma'aikaci anan ", murmushi Qaseem yayi, Farween tashi yayi ya fita, Hajna ce tayi ƙoƙarin tashi amma sai idon oga ya sauka a kan fuskar ta da goshin ta, "amma Qaseem ne ya sami amaryar ka", Hajna zata yi magana, Qaseem yayi saurin cewa "jiya da za'a kawo ta ne aljanun ta suka tashi shine ta jima kanta ciwo", ogan yace "eyya Allah sarki, rabuwa da ƴan gida ba daɗi", ai kuwa kamar ya sosa mata inda ke ƙaiƙayi ta fita, cikin mota ta shiga ta fara kuka 😭😭😭😭😭.

NIMA NASMERH KUKAN NA FARA SABODA HAJNA TA BANI TAUSAYI.

Anan zan dasa aya......... ✍️

Haɗin guiwar : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️♻️♻️❤️❤️❤️❤️👑
[8/17, 09:44] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️
Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

PAGE 43-44
***********************
Fita yayi daga office ɗin, inda ya samu Hajna zaune a mota sai faman kuka take yi, shiga yayi cikin motar, tare da danna key ɗin, tada motar yayi zuwa gida, kuka kawai take yi, parking yayi gefen titi yace “malama ki min shiru wallahi ko na fito da ke na zane ki ", shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, har suka isa gida ba ta sake cewa komai ba.

Parking motar yayi, fita tayi da gudu ta shige ɗakin ta, Kwanciya tayi ta fara kuka, Allah sarki Umma da tana nan ita ce zata share mata hawaye.

A ɓangaren Qaseem kuwa wanka ya sake yi ya fito, ɗakin da Hajna take ya shiga. “Ke munafuka, wa zai dafa min abinci bayan gaki? ", kallon shi tayi cikin taƙaici tace “ban iya ba, kuma bazan dafa ba", buɗe baki yayi tare da ɗaura hannun shi a baki irin mamakin nan ya gama cika shi, “lalala, Hajna ni kike wa magana haka", shiru tayi hannun ta na rawa ganin yana shirin zare charger daga jikin socket ɗin da ke ɗakin, “kayi haƙuri kuskure ne zan dafa" ta faɗa cikin muryar kuka, amma ko sauraren ta beyi ba ya shiga dukan ta ko ta ina ta jikin ta, ihu kawai take yi, sai da ya mata liƙis sannan ya duba fita daga ɗakin yana huci, har ya kai ƙofar ɗaki yace “na baki 20 minute ki dafa min abinci idan ba haka ba, zan miƙa ki gurin karnukan gidan nan su cinye min ke, kowa ya huta"ya faɗa ba tare da ya juyo ba, fita yayi. Tashi tayi daga kan gado, jikin ta yana mata mugun zafi da ciwo, fita tayi zuwa kitchen, ga shi kitchen ɗin babu wani abu da zata dafa cikin 20 minutes kamar yadda Qaseem ya faɗa, kuma tukunyar da zata ɗaura sanwar Adaku ta ɓata ta, kuma bata wanke ba, dole sai ta wanke, wanke tukunyar tayi cikin tsoro da fargaba tace “Allah ka dube halin da nake ciki ka min mafita "ta faɗa hawaye na zubo mata, agogon dake liƙe a bango ta kalla taga har taci minti biyar cikin lokacin da ya bata, kayan miya ta soya, sannan ta tsayar da ruwa, tare da saka maggi da sauran kayan ƙamshi, doya ta fere, sannan ta zuba ta cikin haɗin ta, idon ta ta sauke akan agogo, inda taga saura minti uku lokaci yayi, gashi ita kanta doyar ƙarfi gare ta, ba zai yuyu ta gama ta cikin minti uku ba, zaunawa tayi, ta rafka uban tagumi dan tasan kashin ta ya bushe, shigowa yayi cikin kitchen ɗin inda yayi dai-dai da lokacin da ya bata, “ina abinci na? "ya tambaya, shiru tayi bata ce komai ba, “ina abinci na, nace!" ya sake tambaya da ƙarfi, jikin ta na rawa tace “ban gama ba, da saura ", “what! Baki gama ba fa kika ce" ya faɗa, tare da fita, biyo shi tayi zuwa parlor, extension wire ya zare daga socket, zare ido tayi ganin kaurin da extension wire ɗin ke da shi, watsa mata ita yayi a jiki da iya ƙarfin sa, ihu ta sa, tare da fashewa da kuka, dukan ta yake ta ko ina, duk jikin ta ya fashe, amma ba tausayi ba tsoron Allah ya mata duka, ranta kamar zai fita dan kuka, ƙaddara ta kai ta son mutumin da bai san darajar mata ba, tashi ma gagarar ta yayi, dan haka tayi kwanciyar ta gurin har Adaku ta dawo daga kasuwa da misalin ƙarfe 1:00 na rana.
    A parlor ta sami Hajna kwance, jikin ta, ta taɓa taji zafi kamar garwashi, ga shi ko ina ya faffashe na jikin ta, kama ta tayi suka shiga ɗaki, first aid box ta ɗauko ta gyara mata ciwon ta, sannan ta fita, allurai ta siyo da kuma ruwa da canular ta dawo gida, allurai ta mata sannan ta saka mata drip, dan ta ɗan samu ƙarfi, kiran sallah aka yi, amma ba dama ta tashi tayi sallah saboda bata lafiya, Qaseem kuwa yana gama sallah ya fita, ɗakin Hajna ya nufa, yana shiga yaga an saka mata drip, kuma ta samu barci, matsawa yayi yana kallon ta, hannun shi ya kai kan hannun ta da aka sawa canular, da ƙarfi ya fizgi hannu, wanda haka yasa ruwan zubowa a fuskar ta, kuma canular ta kwaɓe daga gurin da aka saka ta, kasancewar canular a buɗe take, ya sa jini zubowa daga hannun ta, juyawa yayi ya fita tare da rufe ɗakin, jini yake zuba kasancewar canular tana da connection da jijiya, Hajna kuwa bata ma san ana yi ba, dan allurar barci Adaku ta mata dan ta samu barci, sosai jinin ta ke zuba, har ya gangaro kan tiles, Adaku tana kitchen sai faman aiki take Qaseem yazo yace “Adaku je ki ɗaki na ki ɗauko min files ", “to boss" ta faɗa , wucewa tayi zuwa ɗakin, wanda tana shiga Qaseem ya bi bayan ta, ya kulle ta a ciki, yayi tafiyar shi.

Parlour ya dawo ya zauna yana mai jin farinciki har ranshi dan shi yafi so ace mutuwa Hajna tayi, yadda yake jin tsanar ta, kallo ya kunna abun shi, tare da ƙule volume ɗin tv, wayar shi ce tayi riging, murmushi yayi ganin me kiran shi, gani nayi an rubuta NURUL HAYAT da manyan haruffa, ɗauka yayi ya kara a kunne shi, wani dogon numfashi yaja jin muryar ta “hello baby ", “Meenat hasken rayuwa ta" ya faɗa, “shine duk yau baka kira ni ba", murmushi yayi yace “ ni na isa, wallahi abubuwa suka min yawa", “hmmmm ko dai wannan shegiyar matar ta ka ce ta hana ka kira na ba" ta faɗa, “laaaa baby waya isa ya hanani kiran amarya ta kuma abokiyar rayuwata ta har abada" Qaseem ya faɗa yana wani lumshe ido, “wai amaryar ka, amaryar me rabo dai " Meenat ta faɗa, da sauri Qaseem ya tashi daga kwanciyar da yayi kan gado yace, “ Meenat ya kina min irin maganar nan", “saboda ba ka aure ni ba, kuma ina da labarin ka shahara gurin cin amana, dan haka duk abunda zaka faɗa ba yadda zan yi ba, sai ka aure ni", numfashi ya ja, yana jin sonta na ƙara shiga zuciyar shi, yana jin son ta har ranshi Meenat ita ce macen da ya fara so har ranshi, zai iya bada komai dan ya mallake ta , “zan tabbatar miki da wannan ba gaskiya bane, kuma nan kusa zan aure ki", wani shu'umin murmushi Meenat tayi tabbas ta samu kan Qaseem, asiri yayi aiki sosai, yanzu zata koya mishi hankali.

A ɓangaren Fahna wanka tayi, ta shirya cikin riga da wando, wando iyakacin shi gurin guiwa, taje kanta tayi sannan ta ɗaure shi da band, motar ta, ta shiga ta nufi gidan su Hajna, dan gobe da asuba zata bar Abuja, zata je birnin kebi gurin wani Alhaji, dan haka zata je taga ya kwanan su Hajna yake, ta kuma mata bankwana, gudu take sharawa kan hanya kamar zata tashi sama, har ta isa ƙofar gidan, buɗe mata gate aka yi ta shiga, fitowa tayi kamar wata arniya, tana tafiya tana karkaɗa jikin ta har ta shiga cikin parlor, zaune ta sami Qaseem sai waya yake yi, saboda tsabar soyayyar da suke zubuwa shida Meenat be lura da Fahna ba, ita kuwa ɗakin Hajna ta nufa, cikin isa ta dannan mabuɗin ƙofar ...........

Anan zan dasa aya............ ✍️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Haɗin guiwar: Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻♻️♻️♻️♻️
[8/17, 09:48] Queen Nasmah✍️:   ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
PAGE :45-46
************************

Cikin isa ta dannan mabuɗin ƙofar ɗakin, zare ido tayi lokacin da taga jini yana bin ko ina na ɗakin, kallon Hajna tayi, da sauri ta isa gabanta ta fara girgiza ta, tana ƙoƙarin tashin ta amma ina, cikin zafin rai ta fito, inda ta bar Qaseem nan ta same shi “kai ɗin banza har ka isa"ta faɗa tana fizge wayar shi tare da watsar da wayar, ji kake tarassss wayar ta watse, tashi yayi a firgice yace “minene zaki shigo min gida ko sallama, ki fita Hajna bata nan", da wani mugun kallon ta bishi, sannan ta kama kwalar rigar shi, da hannunta ɗaya ta watsa mishi mari, tassss! “munafuki, macuci, azzalumi, kisan kai zaka yi ", “ni bangane me kike nufi ba", “dama ina zaka gane annamimi kawai " ta faɗa, da ƙyar ta samu ta ɗauki Hajna, waje suka nufa sai asibiti, inda aka karɓe ta cikin gaggawa, gwaje-gwaje aka shiga yi, inda aka gano jininta ne ya zuba sosai shiyasa, kuɗi Fahna ta bada aka siyo jini, nan take aka saka mata, gora biyu aka sa mata ta jini, sannan aka saka mata gorar ruwa, tare da mata wasu allurai, text Fahna ta ma Qaseem.

Qaseem yana tsaye a parlor yana kai da kawo a parlor, sai ƙara yaji na shigowar text a wayarshi , 'wallahi Qaseem duk abunda ya sami Hajna kaine, kuma ana buƙatar million ɗaya, ko ka turo, ko kuma na kaika offishin ƴan sanda, kaji me na faɗa maka, sakarai kawai ' sa. Sai da ya karanta text ɗin yafi sau biyar, jikin shi na rawa ya mata transfer.

Fahna na zaune taji alert na 1million, murmushi tayi a ranta tace, haka kawai zan yi in ci kuɗin shege, tana zaune har Hajna ta farka, kallon ta tayi tace “har kin farka? ", gaɗa mata kai tayi tace “meya kawo ni nan" Hajna ta faɗa, Fahna tace “wannan sakaran ne ya so kashe ki, Allah ya so ki naje", Hajna tace “me ya min kuma banda dukan da ya min ", “zuwa nayi na same ki cikin jini, an fizge miki ruwan da ake ƙara miki, jini sai zuba yake yi" Fahna ta faɗa, Hajna tace “amma Fahna waye ya faɗa miki shine ", Fahna tace “ke fa baki da hankali, wallahi shine, ai ina zuwa gurin shi, shi munafuki sai yace min wai baki nan, ni ko na ɗage shi mari, ni zai raina ma hankali, shi fa be san na shigo ba, yana can yana waya, shine da ya ganni ya rikice sai rawar jiki yake yi ", shiru Hajna tayi, akwai alamun gaskiya a fuskar Fahna, Fahna tace “wallahi Hajna ki tashi tsaye, bazai yuyu ya rabaki da gidan iyayen ki ba, sannan ya kashe ki, akwai maza da yawa bariki, kawai ki kama ɗaya, kinsan dai ba wanda zai aure ki ko", maganar da Fahna tayi  ba ƙaramin ci mata rai yayi ba, tabbas maganar Fahna gaskiya ce, kenan haka na nufin a dadiro zata mutu, dafe kai tayi, ta furta “Ohhh ni Allah me nayi wa kaina ne haka " bata ɗaga murya ba, haka yasa Fahna bata ji abunda take faɗi ba, ba'a sallami Hajna ba sai da tayi kwana uku a asibiti, saboda kumburin da tayi, kuma Qaseem kullum sai ya aiko da dubu dari, ana siya mata kayan ƙarin jini, dan Fahna ta tsorata shi, shi kuma tsoro yake ta zubar mishi da mutunci a idon jama'a.

     Yau aka rubutawa Hajna takaddar sallama, Fahna ce ke driving zuwa gida, “wallahi Hajna kin ɓatamin lokaci, da yanzu ina birnin kebbi", Hajna tace“yi haƙuri", “haƙuri fa kika ce, ai baki isa ba, dole sai kin biya ni ladar jinya "ta faɗa, Hajna tace “to mikike so?", Fahna tace “dubu ɗari biyar ", Hajna tace “kar ki damu", dai-dai lokacin suka iso gaban gate ɗin, buɗe musu aka yi suka shiga, fitowa suka yi tare, a parlor suka sami Qaseem zaune shida amaryar shi, da kallon mamaki Fahna tabi yarinyar da ke kwance a ƙirjin shi, ta san yarinyar farin sani, Meenat ce, shugabar ƴan dadiro, a garin sokoto, ta shahara sosai gurin bin maza, kuma Meenat tasan Fahna sosai, dan so da yawa sukan haɗu da ita gurin night parties, “wacece wannan? "Fahna ta tambaya kamar bata santa ba, “mamata ce" dariya Fahna tayi tace “kana cikin mata ", Meenat kuwa duk ta rikice tsoro take kar Fahna ta tona mata asiri, dan tasan Fahna ciki da waje, tsaf ta tona mata asiri.

Masu karatu nasan zaku ce Qaseem yayi aure baku sani ba, nima yanzu nake ji, kasncewar muna gurin jinyar Hajna, amma nan gaba zaku ji yadda aka yi auren.

Hajna kuwa tunda taji Qaseem yace matarshi ce sai taji kamar an daɓa mata wuƙa, lokaci ɗaya jikin ta ya shiga rawa, zufa na bin kuncin ta, Fahna ce ta ja ta zuwa ɗaki, “ke banza kukan me za kiyi ", Hajna tace “ ji ba fa ki ga, ni ina nan ina wahala da son shi amma wai aure yayi", Fahna tace “da hankalin Qaseem ai bazai auri karuwa ba, yafi son sabuwa, dan haka ki karkaɗe kunnen ki kiji, Qaseem ba a hankalin shi ya auri Meenat ba, dan ta shahara gurin bin malamai da bokaye, kuma babbar karuwa ce, ki bari zan binciko komai, idan na dawo daga birnin kebbi, zan biya Sokoto na samo miki bayanai", Hajna tace “to shikenan ", Fahna tace “wallahi kar ki ɗauki raini ko na minti ɗaya, tana gaya miki magana ki nuna mata ke renon ƙyauye ce, wallahi ki naɗa mata na jaki", shiru Hajna tayi, Fahna tace “ke matsala ta da ke tun muna yara baki iya faɗa ba, ke kika sani, ki zauna baƙinciki ya kashe ki, ni kinga tafiya ta, tashi Fahna tayi, “kuma kimin transfer kuɗina ta account kinji ni ko", “Hajna tace “tsaya ma in baki, ina dasu ƙasa ai ", buɗe bedside drawer tayi ta ɗauko su, ta miƙa mata tace“Fahna kin maida kuɗi kamar abinci", Fahna tace “ai su na fito nema", “hmmmmm ke dai kika sani ", ta faɗa tare da gyara kwanciyar ta, fita Fahna tayi, nan su kayi karo da Meenat, wuce ta Meenat tayi, sai ji tayi Fahna ta riƙo hannunta, “nawa zaki biya ni?" Fahna ta faɗa, Meenat tace “da kika min aikin me? ", “da zan rufa miki asiri, idan ba haka ba zan faɗawa Qaseem ki karuwa ce, kuma kin mishi asiri ne shiyasa ya aure ki, ke kinsan ba ƙaramin aikina bane naje har gidan bokan naci mishi mutunci ", Meenat tasan halin Fahna dan haka tace “nawa kike so, ki faɗa ni kuma zan baki", Fahna tace “10 million zaki bani ", zare ido Meenat tayi, sannan tace “amma sun yi yawa", Fahna tace “ya rage naki, ni kinsan aikin kuɗi nake ", juyawa Fahna tayi zata wuce, Meenat tace “ na yarda zan baki", murmushi Fahna tayi tace yauwa, wannan ita ce account number na, sai na jiki, ta miƙa mata wani card, sannan ta wuce, da sauri Meenat ta shiga ɗaki, mota kawai Fahna ta shiga taji alert ɗin shi, wani shu'umin Fahna tayi, sannan tace “shegiya ni Fahna, me gyara ɗan iska, duk tsiyar mutum Fahna ce dai-dai shi ", mota ta shiga kai tsaye sai airport, nan take tayi booking flight zuwa sokoto, mota ta shiga ta nufi birnin kebbi.



Anan zan dasa aya........... ✍️

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

INA WAƊANDA SUKE SON SU FARA RUBUTA LITTAFI INA MASU RUBUTU DA BA SU DA ƘUNGIYA, MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION TA SHIRYA TSAF DOMIN TAIMAKA MUKU

MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION 🌙🌙💫💫💫
----------------
Wannan ƙungiyar an buɗe shi ne saboda marubuta da basu da ƙungiya, da kuma waɗanda suke so su fara rubuta littafi, both Hausa and English novel duka zamu yi guiding ɗinku.

Domin neman ƙarin bayani, ka tuntuɓe wannan number
08078302446
Sai kun zo 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💋💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
[8/17, 09:48] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
PAGE 47-48
*************************
Hajna bata fito ba sai da dare yayi, lokacin ta san Qaseem da Meenat sun kwanta, kitchen ta nufa kai tsaye, bread ta soya da ƙwai, sannan ta kawo lemu, saboda yunwa ta ke ji, gashi dare yayi, ɗakinta ta koma, bayan ta ci biredin ta ƙoshi, kwanciya tayi tare da rufe idonta, Allah sarki Umma, nayi kewar ku, ta faɗa a ranta, daren ranar bata yi barci ba, tunanin Umma da Baffa kawai take yi.

     A ɓangaren Qaseem kuwa kwance yake, da mamaki na ba Meenat akan gadon, tana zaune akan wata kujera tana waya, shi kuwa sai kallonta yake yi, a matse yake da ita, amma ita ko a jikinta, aje warya tayi alama ta gama, tashi tayi wanda hakan ya bani damar ƙare mata kallo, riga ce a jikinta dai-dai guiwa, gaban rigar duka a buɗe yake, sannan rigar tana nuna komai na jikinta, kwanciya tayi kan gadon tare da juya mishi baya, hannunshi ya ɗaura kan bayanta a hankali yana mata tafiyar tsutsa, amma ko juyowa ba tayi ba, ballantana yayi tunanin zata maida martani, hannun shi ya zagayo dashi zuwa kan ƙirjinta, a hankali ya shiga matsa boobs ɗinta, tare da ɗaura bakin shi akan bayan ta, yana goga harshen shi in a sexy tune, hannunta ta sa ta ture shi, “wai miye haka ne, kai kullum kamar maye kake, abu kaɗan mace haba" ta ƙarasa maganar a tsawace, “ haba Meenat, tun ranar da aka kawo ki baki sake bari na kusance ki ba, kuma kin san ina mutaƙar buƙatar ki", “to ni bani da ra'ayi akan haka, dan Allah ka barni, ni nan duk na gaji wallahi " ta faɗa tana juwa, rufe idonta tayi ko minti biyar ba'a yi ba, barci yayi awon gaba da ita, Qaseem kuwa kallon ta yake yi, duk takaice ya cika shi, miyasa take mishi haka, to miye amfanin auren idan buƙata bazata biya ba, tashi yayi ɗauki ruwa, buɗe bedside drawer yayi ya ɗauki ƙwayar magani, sha yayi domin ya samu sassauci abunda yake ji, idan ba haka ba zai iya mutuwa akan sha'awa.

Washe gari da safe, Hajna ta tashi, toilet ta shiga tayi wanka, tana fitowa ta shirya cikin doguwa rigar shadda, kwalliya tayi sannan ta feshe jikin ta da turare, kitchen ta nufa, inda ta ɗaura ruwan zafi, domin ta dama kunu, bayan sun tafasa ne ta ɗauko ƙullun kunun da ta kwaɓa ta aje, tafasasshin ruwan zafi ta zuba akai, dama kunun tayi, sannan ta zuba a flask, dankalin da Adaku ta fere, ta dafa, miyar ƙwai tayi sannan ta jera a kan dinning table, zaunawa tayi sannan ta zuba abinci, zata kai baki taji an riƙe mata hannu, ɗaga kan da zata yi taga Meenat a tsaye, “ke har kin isa ki ci abinci ban ci ba " Meenat ta faɗa, Hajna kuwa da kallo ta bita, “zaki tashi ki bar gurin nan ko sai na mare ki", ba shiri Hajna ta tashi ta koma parlor, Meenat kuwa guri ta samu ta zauna, ta fara cin abinci, cup ta ɗauka ta zuba kunun da yaji kayan ƙamshi da madara, sha ta fara yi, wani daɗi ya daki kunnen ta, domin kuwa kunu ma iyawa ne, tana cin dankali tana shan kunu, har sai da ta kusa gamawa da abincin kular, kunun ma kasancewar bada yawa Hajna ta dama ba, duka Meenat ta shanye shi, Qaseem ne ya fito yana cin wata muguwar yunwa, sauran abincin da ke cikin kular ya zube ya cinye, “ki miƙo min ruwa cikin fridge "Qaseem ya faɗa, Meenat tace “ni ƴar aikin ka ce da zaka ce na ɗauko maka ruwa", “yi haƙuri "ya faɗa, “ke! Zo nan" Meenat ta faɗa tana nuni da Hajna dake zaune tana kallonsu, tasowa Hajna tayi tana tafiya kamar wata sakarya har ta iso inda su ke, “ɗauko mana ruwa " Meenat ta faɗa cikin yanayin wulaƙanci, fridge ta buɗe ta ɗauko musu ruwa ta kawo musu, “ke baƙauyar ina ce, baki san in aka ce ki kawo ruwa ki haɗa da lemu ba" Qaseem ya faɗa, jikinta na rawa ta juya, lemu ta kawo, sannan ta wuce ɗaki, da ƙarfi ta rufe ƙofar, faɗawa tayi kan gado, kuka ta fara yi kamar ranta zai fita, wannan wani irin wulaƙanci ne, tana ji tana gani yake ci mata fuska a gaban Meenat.

   “Ka bani million 10" Meenat ta faɗa, Qaseem yace “ ina zaki kai kuɗi jiya ma kin karɓi million 20,yau 10" ,Meenat da ke kallon shi irin a ɗage ɗin nan tace “yo kana nufin gori zaka min", Qaseem yace “a'a ni ba haka nake nufi ba, amma abun ne yayi yawa ", “to kar Allah yasa ka bayar, kai kuma kaga tashin hankali da masifa a gurina" Meenat ta faɗa tana shirin fita daga ɗakin, da sauri ya jawota, ƙasa yayi da murya yace “ yi haƙuri zan baki 30 million, amma da sharaɗi", “sharaɗin me "ta faɗa, “dan Allah ki bari na kusance ki" ya faɗa yana haɗa bakinshi da nata, ba yadda ta iya dole ta fara biye mishi kan gado su ka faɗa, ni kuwa da naga abun nasu yayi yawa sai naja ƙofar ɗakin na fito.

*************************''
Yau Fahna tayi sati ɗaya a Birnin kebbi, dan haka ta haɗa kayan ta zuwa Sokoto, in da zata yi bincike akan auren Qaseem da Meenat, Alhaji kuwa ya bata kyautar mota, tun a garin ta saka motar kasuwa ta saida ta, Sokoto ta nufa, ba wata tafiya bace a gurin Fahna, dan haka tana isa masaukinta wanka kawai tayi ta shirya cikin wando da riga, naɗe gashinta tayi sannan ta ɗauki jaka ta rataya, fita tayi, tafiya take yi, har ta isa gaban wani gida, gaban gidan an rubuta, MASU ƳANCI da babban harafi, parking motarta tayi wajen gate ɗin, sannan ta buɗe ƙofar gate ɗin ta shiga cikin gidan, ƙato ne sosai fiye

Please Login or Register in order to submit comment