Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aka bata zata karɓa ta saka mishi albarka, a cewar ta kaɗan me albarka yafi dawa mara sa albarka, “Umma na tambaye ki zaki amsa min " Hajna ta faɗa, Umma tace “eh ƴa ta me zai hana", murmushi Hajna tayi tace “me zan yi duniya ki juya min baya ", Umma tace “babu abunda zaki yi na juya miki baya, Hajna in na juya miki baya wa zai so ki, hannun ka baya ruɓewa ka yanke ka yadda shi",, hawaye suka zubo daga idon Hajna tace “Umma duk abunda rayuwa ta canza, a kowane hali ni ɗinnan zan so da dukkannin rayuwa ta ", rugume ta Umma tayi suka sha kukan su, Umma na kukan son da take wa ƴar ta, ita kuma Hajna na kukan rabuwa da Umma.

Anan zan dasa aya........

Sai munji yadda Hajna zata gudu daga gidan su kuma ya zata yi da Qaseem, shi zai haƙura ko a'a.

Muhaɗu a next chapter.

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
[8/17, 09:36] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya


QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT KU NUNA MIN SOYAYYA KUYI FOLLOWING
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 21-22
***********************
Fira suka taɓa ita da Umma, sannan ta tashi ta koma ɗaki, tabbas zata yi kewar Umma, cikin dare da misalin ƙarfe 10:30 ta ji Baffa ya shige ɗaki, dama shine lokacin da yake kwanciya , har ƙarfe  12:30 sannan ta fito, bata ɗauki komai ba, hijab kawai ta saka, a hankali take tafiya har ta kai ƙofar gida, Alhamdulillah dama Baffa baya rufe ƙofar gida da sakata, kawai addu'a yake, dan yayi imani ba wanda zai iya shigo masa gida, amma be taɓa tunanin watarana wani a gidan sa zai fita ba, kamar yadda Hajna tayi yau.

     Ta lugun dake tsakanin gidan su, dana Fahna tabi ta wuce, a bayan gidan su ta  ga wata mota baƙa mai tinted black, fitowa Fahna tayi daga cikin motar, suka shiga, direct gusau suka nufa kai tsaye.


********************************
Washe gari da safe.

Baffa yayi sallah ya fita, ƙofar gida, har ƙarfe 10:30 Hajna bata fito ba, shigowa yayi yace “Aminatu! "Baffa ya kira sunan Umma, “na'am malam"umma ta faɗa, Baffa yace “wai kin duba Hajna kuwa?", “a'a malam, me ya faru", Baffa yace “duba ta dan Allah duk yau bata fito ɗakin ta ba ", murmushi Umma tayi tace “to kai kasani ko bata tashi ba, kasan fa bata sallah", Baffa yace “to shikenan, ki barta wataƙila a gajiye take ", Umma tace “to shikenan".

**************GUSAU*************

Hajna ce zaune duk abun duniya ya dame ta, Qaseem ɗin da ta gudu saboda shi baya ɗaukar wayar ta, gashi tun da safe Fahna ta fita, ita bata ma san inda Fahna ta nufa ba.

    Da misalin ƙarfe 12:00,Fahna ta shigo ɗaki ta sami Hajna zaune tayi taguma, “ke banza tashi dan Allah muje parlor "Fahna ta faɗa, Hajna bata musa mata na ta bita, Hajna tayi matuƙar mamaki da taga Qaseem, zaune ta same shi  wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba, nuɗe hannun shi yayi ta faɗa jikin, ya mayar ya rufe, a tare suka sauke wata ajiyar zuciya, Qaseem yaji daɗi ba kaɗan ba, ganin Hajna dan be yi tunanin ganin ta ba, ko Fahna bata faɗa mishi ba, kawai ce mishi tayi yazo gidan ta zasu yi wata magana akan Hajna, “Favorite one, am so happy to see u ", murmushi tayi amma bata ce komai ba, ita bata da ta cewa, dan ta san duk yadda zata faɗa bazai gane ba, har yanzu tana kwance a jikin sa ita bata ce komai ba, kuma bata tashi daga jikin sa ba, kallon Fahna yayi yace “ya aka yi tazo nan", Fahna tace “kirana tayi wai baka ɗaga wayar ta saboda Baffa ya hanata fita, shine na je na ɗauko maka ita ", murmushi yayi yace “ gaskiya kin kyauta", kallon Hajna yayi yace “dama haka kike so na? "
, “hmmmmm" kawai ta iya furtawa, wayar shi ya zaro daga aljihu, nan take Fahna taji alert ɗin 2million, sai jin ƙarar alert tayi, zare ido tayi ta kalli Qaseem tace “ 2million duk nawa ", murmushi yayi yace “a'a na kawo Hajna da kika yi ne, yanzu zan wuce sokoto na hau jirgi, yau zan koma abuja, saboda kira na da kika yi shiyasa ban wuce ba, kinga bazan bar Hajna nan ba tare za muje", Fahna tace “to shikenan Allah ya tsare hanya ", “ameen ya rabbi" ya faɗa, Fahna tace“to ke hajiya sai ki tashi ku tafi", tashi tayi suka wuce.

     A ɓangaren su Umma kuwa har aka yi azahar Hajna bata fito ba, Umma tace “ni kam bari in shiga ɗakin yarinyar nan, nasan dai ciwon nan ne ya matsa mata", ɗakin ta  nufa, ta buɗe mamaki ya kamata lokacin da ta kalli ko ina na ɗakin amma bata ganta ba, gashi ɗakin ba wani guri da za'a ce mutum ya ɓoye, gashi komai nata lafiya ƙalau ba'a taɓa, fitowa tayi tana salati, Baffa da shigowar  sa kenan, a firgice yace “ lafiya dai Umman Hajna, me ya faru ", Umma tace “banga Hajna ba", Baffa yace “wace Hajna? ", Umma tace “wace Hajna  kasani, bayan ƴar ka" ta faɗa cikin ruɗani, Baffa yace “duba ta dai ko ta shiga banɗaki ", Umma tace “ina waje fa tun ɗazu ban motsa ba, yaushe ta fito da bangani ba", Baffa yace “ke dai ki duba ta, ki gani ko kina gyangyaɗi ta shiga ", Umma tace “hmmm, gyangyaɗin me zan yi, bari dai na duba", Baffa yace “ke dai ake ji, nace ki duba ta kin tsaya wani zance", toilet Umma ta nufa, ta duba bata ganta ba, kuka Umma ta saka “Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, an sace min yarinya ", Baffa cikin ruɗani yace “wai da gaske baki ganta ba", “to na taɓa maka irin wasan nan ne? "Umma ta faɗa, tare suka dinga duba gidan amma ba Hajna ba labarin ta, kuka Umma ke yi Baffa na kwantar mata da hankali, “ki zauna bari na fita waje naji ko wani ya ganta", Umma tace “ni ba zaka barni nan ba ", dole suka fita tare suna tambaya ko wani yaga Hajna, amma ba wanda ya ganta, Umma sai mita take yi wai laifin Baffa ne da yake barin ƙofar gida buɗe, gashi nan an shigo an sace mata ƴa, har aka yi la'asar suna yawon neman Hajna, Baffa ne yace “Aminatu muje na raka ki gida, ni zan dawo na cigaba da ciyar ta, har Allah yasa a dace, ko wani ya ganta ", a hanyar su ta komawa gida suka haɗu da wani, gaisawa suka yi da Baffa, yace “Malam lafiya ku ka fito", Baffa yace “lafiya dai, wallahi Hajna ce muka nema muka rasa, bata gida ", mutumen da suke magana dashi wanda ake cewa Audi yace “to jiya cikin dare ba ita bace naga ta fito daga gidan ka ba", “ina? "baffa ya faɗa, Umma tace “ba dai Hajna ba kam, ƴata bata yawon dare", Malam Audi yace “to wataƙila ban gani da kyau ba, amma jiya naga wata ta fito daga gidan ku, ta lugun dake tsakanin gidan ka dana marigayi Habu naga tabi ta wuce, nayi jiran in ga dawowar ta ban gani ba, na gaji na tafiya ta gida ", Baffa da yake jin ƙamshi gaskiya a maganar yace “ to shikenan Allah ya bayyana ta", wucewa suka yi, a ƙofar gida suka haɗu da wani mutum “kaine Mahaifin Hajna"mutumin ya faɗa, Baffa yace “eh nine", yace “ni da farko ina da shago ne bayan gidan ku, yanzu labari ya same ni kana neman Hajna, shine nazo na faɗa maka, jiya cikin dare na ganta, ita da ɗiyar aminin ka Marigayi Habu, sun shiga wata mota ", Baffa yace “ina suka nufa?", mutumin yace “labari ya same ni cewa wata mota ta wuce gusau cikin dare ana tunanin ko ƴan fashi ne, ta nufi gusau, ni kuma da yake nasan su waye sai nace musu ba ɓarayi bane, ƴar malam Ibrahim ce da marigayi Habu", Baffa ya dafe kai yace “nagode sosai", Umma ma, mutuwar tsaye tayi, kuka kawai take, dan yanzu kam ta yadda Hajna ta gudu ta bar gari, kuma ita Umma bata ganin laifin kowa sai na Baffa, “duk da baka tsananta mata ba, har ka hana ta fita, duk da baka hanata fita ba, ai da yanzu tana gidan nan, shi yaro ba'a tsananta mishi ", Baffa yace“ko kuma sakaci irin naki ba, da kina sa mata ido ai da bata gudu ba, Allah ya gani nayi iya yina, amma tunda ta zaɓi irin rayuwar Fahna, taje ga duniya nan, duniya zata koya mata darasi", Umma kuka kawai take yi.

Anan zan dasa aya........ ✍️

Haɗin guiwar : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

   
[8/17, 09:39] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT KU NUNA MIN SOYAYYA KUYI FOLLOWING
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 23-24
***********************
Tunda suka shiga mota, take barci, har suka isa Abuja, kasancewar jikin da suka hau Sokoto Kaduna ya aje su, gidan shi ya nufa kai tsaye da ita, tada ita yayi, buɗe tayi tace “Umma dan Allah ki barni, a gajiye nake ", Qaseem yayi murmushi, a ranshi yace Allah sarki tana tunanin gida take, dan haka kawai ya ɗauke ta a hannun shi zuwa cikin gida, ma'aikatan shi na mamakin inda ya samo Hajna.

     Ɗakin dake kusa da nashi ya aje ta, kwantar da ita yayi sannan ya ja ƙofar ɗakin, ɗakin shi ya shiga sa fara rage kayan jikin shi, wanka ya shiga ya fito, maimakon ya kira mai shirya shi ta shirya shi, sai ya saka kayan shi da kanshi, already asuba tayi dan haka sallah yayi dan ya riga yayi arwala a toilet, sallah yayi sannan ya dawo ya kwanta don a gajiye yake, murmushi yayi lokacin da ya tuna da Hajna, yanzu dama ce gare shi, zai samu abunda yake so, amma fa bazai aure ta ba, tunawa yayi da jibi zai je gurin yayar shi dake zaune garin Lagos, wadda yake cewa love, kasancewar ba musulma bace shiyasa be wani cika so yana zuwa gurin ta ba.

     Da addu'a a bakin ta, ta tashi, ƙoƙarin buɗe idon ya take yi har ta samu ta sauke su a kan fankar ɗaki, da sauri ta tashi a firgice, tana mamakin ina take, da kallo take bin ɗakin yadda komai yaji, da alama mai gidan nan babban mai kuɗi ne, kallon ko ina take, sai yanzu ta tuna ta biyu Qaseem zuwa Abuja, to nan ina ne ma, tashi tayi ta shiga toilet, komai na toilet ɗin ya mata,kayan jikin ta cire, cikin bathtub ta shiga tare da sakar ma jikin ta ruwa, yadda ruwa ke sauka tana jin wani sanyi sai take jin son Qaseem yana ratsa gaɓoɓin jikin ta, she admit it, she really love Qaseem, ta shirya bada rayuwar ta akan soyayyar Qaseem.

NI KUWA NASMERH NACE ISKA NA WAHALAR DA MAI KARA.

Wanka tayi sannan ta fito, tayi matuƙar yin mamaki da ta buɗe wardrobe ɗin ɗakin taga kayan sawa, kuma na mata, ko da yake ba abun mamaki bane, saboda Qaseem womanizer ne shi, zaɓar wata riga tayi mara nauyi ta saka, sannan ta fesa turare kala-kala, sai yanzu take ganin irin kyan da Allah ya mata, asalin farin fatar ta ya fito, sannan pink lips ɗin ta ya bayyana, ƙugun ta ta kalla yadda ya zauna a jikin ta gashi ɗan ƙarami hakan ya ba shape ɗinta damar fitowa da kyau, shafa bakin ta tayi, dogon gashin kanta ta gyara, sannan ta tattara shi ta gefe ɗaya, wanda hakan yayi matuƙar ƙara mata kyau, murmushi tayi wanda ya fito da fararen haƙoran ta, wow masha Allah, masu karatu Hajna kyakkyawa ce ajin ƙarshe, tsayawa bayyana muku hakan ɓata lokaci ne, sallah tayi sannan ta fito zuwa parlor, lokacin ƙarfe 9:30.

   A parlor ta same she kwance akan kujera, ɗaya daga cikin masu aikin shi na shafa mishi jiki da sunan tausa, idon ta suka ciko da hawaye lokacin da taga yadda yake wani lumshi ido, guri ta samu ta zauna nesa dasu, buɗe idon shi yayi yace“favorite one zoki mana"ya faɗa yana buɗe mata hannun shi, ba musu tazo, rungume ta yayi yace “kin tashi lafiya ", “Alhamdulillah" ta faɗa, murmushi ya sakar mata yace “ miye kike wani haɗe rai ", “hmmmm" kawai ta iya furtawa tana tashi daga jikin shi, ya fahimci saboda wannan yarinyar dake gaban shi take fushi, “favorite one, kin cika rigima waɗannan fa ƴan aiki na ne, ke kuma fa, ke tawa ce, su kuma kawai biyan su nake, banga abun fushi nan ba "ya faɗa, turo baki tayi tace “amma ai ba gaba na ya kamata kuyi wannan ba", “to ai bansan zaki zo ba"ya faɗa, “amma ai kasan ina gidan nan", kallon ta yake da mamaki yace “kina nufin bazan hole ba dan kina gidan nan, inaaa Hajna bazai yuyu ba, da halina kika ganni in kina iyawa ki zauna dani, idan kuma bazaki iya ba ban miki dole ba ki haɗa kayan ki ki koma", shiru tayi tana bin shi da kallo, tabbas in dai kai kake son namiji ka bani, murmushi tayi duk da abun ya mata ciwo amma sai ta ɓoye, tashi tayi ta bar gurin, ɗayan parlorn ta shiga in da ta tadda sauran matan su haɗu, kowa da cup wanda ita bata san menene ba, “sannun ku"ta faɗa tare da zaunawa, gaisawa suka yi, trisha ta mata tayi kunun gyaɗa wanda dama shine abunda suka fiye sha, murmushi tayi tace musu ta gode, kwanciya tayi kan ɗayar kujerar, rufe idon ta tayi, maganar da Qaseem ya mata ke yawo a cikin ƙwaƙwalwar ta, hawaye suka zubo mata, saurin sharewa tayi, tana kwance har suka watse daga parlor saura ita da trisha kawai suka rage, “ke sister boss ce" Trisha ta faɗa, Hajna tace “a'a ni matar da zai aura ce", Trisha tace “aure, shine yace miki zai aure ki ", Hajna ta girgiza kai alamar a'a, Trisha tace “in dai boss ne kina da aiki tabbas, dan marriage is not his card", Trisha ta ƙara da “i have been working here for almost 15 years tun ina yarinya, mata da yawa sun zo sun zauna da Qaseem, kuma duka da sunan waɗanda zai aura, amma basu san Qaseem is very smart ba, shi be yadda da aure ba, rayuwar shi be yadda akwai aure ba ", da ta fahimce Trisha da kyau, tace “kina nufin duk abunda zan yi bazai aure ni ba", Trisha tace “idan ƙaddarar ki ce ki aure shi za kiyi amma ni bana miki fatan ki aure shi, dan bazai fasa halin shi ba", Hajna tace “amma me yasa kike faɗa min", Trisha tace “na faɗa miki ne saboda nasan Qaseem, kuma mutum ne da baya gajiya da mace in dai karuwa ce, kuma kin bani tausayi ne, dan tunda na ganki nasan kina cikin damuwa saboda na bar Qaseem da Easter a parlor, nasan duk mai son shi zata ji haushi, kuma kece kawai musulma a cikin yaran da Qaseem ke mu'amala da su", Hajna tace “kina nufin baya harka da musulmai? ", Trisha tace “ai shima ɗin be wani jima da karɓar musulunci ba, bazai wuce shekara biyu ba, kuma yayar shi na nan, har yanzu bata musulunta ba, ita ce ma ta kawo ni nan", Hajna tace ya sunan ki? ", Trisha tace “, Trisha David Cameron, kefa ya sunan ki", “Hajna Ibrahim Shinkafi "ta faɗa cikin murmushi, “wow nice name, Hajna! Nice to meet you" Trisha ta faɗa, Hajna tace “ thank you ", nan suka dinga labarin Qaseem, har take faɗa mata jibi Qaseem zai je gurin yayar shi, wanda duk bayan wata ɗaya yake zuwa, Hajna kuwa duk abunda Trisha ta faɗa mata yana shiga, a cikin labarin ta fahimci abubuwa da yawa da Qaseem yake so, da waɗanda baya so, Trisha ta yiwa Hajna alƙawarin ciwa idan Qaseem yayi tafiya zata taya ta gyara jikin ta kafin ya dawo,kuma zata koya mata yadda ake karairaya, da dai sauran su.

Anan zan dasa aya..............

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️😍😍😍😍😍😍😍😍💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

       

    
[8/17, 09:40] Queen Nasmah✍️:    ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️
Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

QUEEN NASMERH'S WATTPAD ACCOUNT

Show me love and follow
https://www.wattpad.com/user/AsmaunanaLawalliman?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.


*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 25-26
**********************
A ɓangaren su Umma kuwa, Baffa ya yanke hukuncin ko Hajna ta dawo ba gidan sa ba, Umma kuwa ta ja bakin ta tayi shiru, saboda itama ɗin bata da ta cewa, kuma addu'ar ta Ita ce Allah ya shirye Hajna.

     ABUJA ************
A ɗaki take tayi wanka tayi kyau kamar ba ita ba, Qaseem ne ya shigo yace “Favorite one ki same ni ɗaki ", be tsaya yaji me zata ce ba ya juya, ya fita, bayan ya fita Hajna ta zauna tana tunanin yadda Qaseem ya canza, dan ta mishi magana akan  Easter shiyasa yake ɓata rai ko minene, ɗakin shi ta nufa, kwance ta same shi, zaunawa tayi, yafi ƙarfin minti uku be juyo ya kalle ta ba, daga baya kuma ya juyo, duk da haka be yi mata magana ba, sunfi minti talatin a haka, kafin Hajna tace “kayi haƙuri idan nayi maka laifi, ba da njyya nayi ba, kuma in dai akan ma'aikatan ka ne bazan sake maka magana ba", har ranshi yaji daɗi, amma sai be nuna mata ba, sai ma rufe idon shi da yayi, hannun ta, ta kai kan goshin shi, a hankali tana shafa mishi kai, cikin salon da ita kanta bata san tana da shi ba, a hankali har ta rikita shi, bata yi auni ba ta ji ya jawo ta jikin shi ta faɗo masa a jiki, lumshe ido tayi jin ta a jikin shi, wani farinciki ya cika ta, ina ma ace suna da aure, “ka haƙura? "ta tambaya tana kallon cikin idon shi, be amsa ta ba kawai ya haɗa bakin shi da nata, in a romantic mood ya fara wasa da ita, wani sound take sake duk ta rikice, ƙoƙarin haɗa jikin ta da nashi take yi duk ta rikice, ture ta yayi yace “ke miye haka, wannan salon naki be min ba, ki tashi ki bar min ɗaki, ko yadda ake sa namiji yaji daɗi baki iya ba, fitar min daga ɗaki, kuma ki kira min Trisha nasan zata min abunda nake so "ya faɗa cikin faɗa, tashi tayi ta fita, Trisha ta kira mishi kamar yadda ya ce tayi, sannan ta wuce ɗakin ta, kwanciya tayi tana me jin tsanani ciwon mara, dan dama tana da matsalar ciwon mara, gashi yanzu Qaseem yana tada mata da shi, juyi take yi kamar ranta zai fita haka take ji, ko tafiya ma bata iya yi, yadda taga dare haka taga safiya, a daddafe ta shiga toilet tayi arwala, sallah ma a zaune tayi ta, tana matuƙar buƙatar Qaseem amma miyasa zai mata haka, tana nan domin shi, bata samu soyayyar shi ba, kuma ga wulaƙanci tana fuskanta gurin shi, wasu hawaye masu zafi su ka zubo mata a kunci, kuka taci ta ƙoshi, a gurin barci ya ɗauke ta.

Misalin ƙarfe 12:30 na rana
Trisha ce ta fito daga ɗakin Qaseem, dan dama Qaseem yana jin daɗi harka da Trisha, sannan tasan yadda zata bi da Qaseem cikin sauƙi, shiyasa in ta shiga ɗakin shi tana daɗewa bata fito ba, saukowa tayi downstairs ta gyara ko ina, sannan tayi wanka, ganin har yanzu bata ga Hajna ba yasa ta shiga ɗakin ta domin duba ta, kwance ta same ta akan sallayar ta, da alama ko sallar azahar ba'a ta yi ba, dan yanzu ake kiran sallah, tada ita ta shiga yi, a hankali ta shiga buɗe idon ta, tashi take ƙoƙarin yi amma ta gagara saboda marar ta na mata tsananin ciwo, kama ta Trisha tayi ta tashi wanka tayi sannan ta dawo ɗakin, inda ta bar Trisha ɗazu nan ta same ta, shiryawa tayi, nan ta zauna tana gayawa Trisha abunda ya faru jiya, dariya Trisha tayi tace “ashe baki gama sanin halin boss ba, muddun kina nuna mishi so to kin gama wulaƙanta, kina basar dashi, yanzu kar ki bari ku sake haɗuwa har sai ya neme ki, kuma ko ya zo ɗakin ki karki kula shi har sai anyi kwana uku yana bin ki, yanzu nasan bazai neme ki ba, sai nan da kwana biyu, haka yake wa Favor, har yanzu wulaƙanci yake mata, tun tana kuka har ta saba, wai bata da daɗi ", Hajna tace “amma ni bazan iya fushi da Qaseem ba", Trisha tace “ke kuma baki daina fuskantar baƙinciki ba", shiru Hajna tayi tace “to ita Favor miyasa yake mata wulaƙanci ", Trisha tace “saboda tana son kwanciya da shi, da ya gane haka, sai ya riƙa mata wulaƙanci", Hajna tace “amma ni baki ganin da bambanci, shi

Please Login or Register in order to submit comment