Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Farwa tayi tunanin wani abu, roƙon Allah take Allah yasa Aunty Farwa ta fita ta samu ta tafi.

  Abinci ya kai bakinshi, wani daɗi ya bugi kunnenshi, yace “ummmm wannan abinci haka waya dafa", Aunty Farwa dake iya jiyo su tace “aikin Hajna ne", gaɗa kai yayi yace “kin iya abinci gaskiya " abinci ya shiga ci hankalin shi kwance, Aunty Farwa kuma ta ɗauki jaks tace “ni zan fita, sai anjima, Aisha ki ɗaura abincin rana, Hajna tayi na dare, kice ma Monica zata iya tafiya gida idan ta gama aikinta sai gobe kuma", “to mommy a dawo lafiya "Aisha ta faɗa.

  Wayar Farween ce ta shiga ringing, kallon sunan da ke yawo kan wayar Hajna tayi, Baby taga an rubuta, wani zafi taji ranta, da sauri ya ɗaga “hello baby sai yanzu kika tashi", “eh se yanzu "ta faɗa, murmushi yayi yace “to ki ci abinci kin ji, take care" ya faɗa yana kashe wayar, tashi Hajna tayi zata wuce, taki biyu yayi ya kama hannunta, “me yake damunki ne, duk lokacin da nayi waya da Halia sai kin yi fushi ", shiru tayi, “ki faɗa min miyasa", hannunta tasa ta ture shi, sake riƙe mata hannu yayi yace “ faɗa min miyasa", “ ina sonka! "ta faɗa da ƙarfi ba tare da ta san ta furta, da sauri ta rufe bakinta, cike da mamaki Farween ke kallonta, “nima ina sonki Hajna, ina sonki" ya faɗa yana murmushi, Aisha da ke zaune tana kallon ikon Allah ta tashi daga inda take tace “kuna son juna tun yaushe ", “na ɗauki tsawon lokaci ina sonta, a taƙaice ma shekaru" Farween ya faɗa, Hajna kuwa cikin sauri ta shige ɗaki, ko kaɗan bata da niyyar faɗar haka, a taƙaice ma bata san ta faɗa ba, murmushi tayi, sai kuma ta ɓata rai da tuna da Halia, yanzu ya zata yi, tana kishin Farween sosai, fiye da tunaninku.

“ Uncle Farween miyasa take fushi da kai " Aisha ta faɗa, Farween yace “saboda Halia", Aisha tace “miyasa baka faɗa mata wacece ita ba", Farween yace “saboda bansan tana sona ba, kuma yanzu bazata saurare ni ba", Aisha tace “zan faɗa ma mommy, nasan zata mata bayani yadda zata gane, ka kwantar da hankalinka, zata haƙuri, indai akan aunty Halia ne "murmushi yayi yace “to Allah yasa, nima zan yi farinciki", Aisha tace “ni zan fika farinciki, sannan ka je gobe ka ɗauko Aunty Halia yadda Aunty Hajna zata fahimta, yanzu bazan faɗa ma mommy ba sai ka ɗauko ta ", Farween yace “har Abuja kike so naje", “eh mana ke hau jirgi zuwa da dawowa zaka yi sauri", Farween yace “gobe da safe zan je insha Allah ", Aisha tace “Allah ya kaimu", “ashe kina da hankali "Farween ya faɗa yana jan kunnenta, “hmmm naji, ni dama nayi missing Aunty Halia gashi baka barin ta yawo" , “eh so kike ta dinga yawo kamar ke, ai ƙarƙashin Farween take ba ke ba sarkin" yawo" Farween ya faɗa yana murmushi, “hmmmm amma ai kai kana yi ", yace “ni namiji ne ita mace".

Anan zan dasa aya........... ✍️
Queen ɗinku a ko yaushe.

Kar ku manta kuyi following account ɗina na Wattpad ta link ɗin da ke sama.

Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️♻️♻️♻️💃🏻
[8/17, 10:00] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNA

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
PAGE 77-78
**********************

Da rana Aisha ta dafa abinci rana kamar yadda momy ta bada umurni, Hajna kuwa bata fito ba, dan kunya duk ta gama rufe ta, gani take bazata sake bari ta haɗa ido da Farween ko wani daga ahalinshi ba, a ɗayan ɓangaren kuma haushin Farween ta ke ji, saboda Halia. Sai misalin ƙarfe 4:00 ta fito, ta yi sa'a Farween yana compound ɗin gidan, dan haka ta yi saurin shigewa kitchen.

    Tunanin abunda za ta dafa ta ke yi, kafin daga baya ta yanke hukuncin dafa macaroni da hanta, dan haka ta buɗe fridge ta ɗauko kayan miya da ɗanyar hanta, wanke kayan miyan tayi sannan ta wanke hanta, kayan miyan ta jajjaga a turmi, sannan ta zuba a cikin tukunya, bayan ta tanadi duk abunda ta ke buƙatar a gabanta, sannan ta fara dafa abincin, kasancewar macaroni ne yasa bata ɗauki lokaci ba ta gama, tun kafin ta gama ƙamshin abincin ya gauraye ko ina na gidan, Aisha da fitowar ta kenan, duk ta ƙagara Hajna ta gama abincin ta ci .

    Pepper soup ɗin naman rago tayi, wanda ƙasusuwa su ka fi yawa, shi ma ɗin tun a ido zaka tabbatar ya yi daɗi, komai na kitchen ɗin ta gyara, sannan ta fito da abinci ta jera a dinning, lokacin ƙarfe 5:30, ɗaki ta koma ta cire kayan jikinta, dan duk zafin kitchen ya ishe ta, wanka tayi sannan ta shirya cikin wata doguwar rigar atampha, tayi matuƙar yin kyau.

A ɓangaren Farween kuwa video call yake yi da Halia, sai labari ta ke ba shi yana dariya, da alama akwai shaƙuwa me ƙarfi tsakanin shi da Halia, “yauwa baby ki shirya zan zo gobe mu taho tare da ke ", zare ido tayi “ina za mu?", “sayar da ke zan yi gurin buzaye, su je da ke niger kowa ya huta", turo baki ta yi, tace “ai da kai da kanka zaka je ka karɓo ni ", “haka kike gani, idan fa na canza sabuwar baby", Halia tace “ko wacece ita bazata kai ni ji da kai ba, ni dai ƙyale ni ma" ta faɗa tana juyar da fuska, dariya ya fara yi, dan yadda ta yi ya ba shi dariya, “au ni na ɗauka ai baza ki yi fushi ba " ya faɗa, juyowa tayi tace “to nayi a rarrashe ni", murmushi yayi yace “am sorry baby ", “ni bazan haƙura ba sai idan bazaka canza baby ba" murmushi yayi yace “I promise u bazan canza baby ba, kece baby har abada ", “to shikenan, idan ka yi baby ba zamu sake magana ba", gaɗa kai yayi alamar ya yadda, “to ina zaka kai ni", “gurin Aunty Farwa zamu zo fa ", “Ohhhh god, wai da gaske" ta tambaya cikin farin ciki, Farween yace “eh ba wasa ba", ɓata rai tayi dan ta san Farween zai iya cewa su fita amma ganin tana zumuɗi sai ya fasa, kallonta yayi yace “ki fara shiri, insha Allah zaki zo ", yanzu da yace insha Allah, sai ta ɗan yadda, dan haka sai ta saki rai su ka cigaba da labari da shi, sai da aka kira magrib sannan ya mata sallama.

   Arwala yayi ya nufi masallaci gurin sallah, tunda ya fito hankalinshi na kan Hajna, ko kaɗan baya so ya ga ranta ya ɓaci, cikin gida ya shigo inda ya samu Aunty Farwa zaune da alama itama bata daɗe da dawowa ba, duk da dai ta canza kayan jikinta, “har kin dawo kenan ", aunty Farwa tace “tun 6 na dawo, ai na wuce ka kana ta waya", rassss! Gaban Hajna ya faɗi, dan jikinta ya bata Halia ce, amma sai ta dake, “Aisha ɗauko mishi abinci "Aunty Farwa ta faɗa, “a'a ni Hajna zata kawo min" ya faɗa, Aisha da ke ƙoƙari tashi tace “ka hutar da ni ", Hajna bata ce komai, tashi tayi ta kawo mishi, kamar ko yaushe, yau ma santi ya ke yi, tun Hajna na haɗe rai har ta fara dariya, wani bin har da riƙe ciki, shi kuwa sakin baki yayi yana kallon ikon Allah, gurin a gurin shi be ga abun dariya ba, amma kalli yadda Hajna ke yi, har da riƙe ciki, jin ana kallon ta yasa tayi saurin dakatawa, nan take suka haɗa ido da shi, da ƙyar ta samu ta ja dogon numfashi, sannan tace “aunty Farwa ni zan shiga daga ciki, saboda zan yi karatu, ina so da anyi isha'i na kwanta ", Aunty Farwa tace “to shikenan ki kula kinji", tashi tayi ta wuce, har tana haɗe ƙafa.

Girgiza kai kawai Farween yayi yace “Hajnata", ni kuwa nace Hajno ba Hajna ba. Yana gama cin abinci ya wuce masallaci dan an kira sallah, sallah yayi, sannan ya dawo ya kwanta, dan gobe so ya ke ya wuce tun bayan asuba.

Kiran fari kawai aka yi Farween ya tashi yayi wanka, sannan ya shirya cikin riga da wando, sannan ya fita, masallaci ya shiga ya bi jam'in sallah sannan ya wuce airport, dan yana zuwa zai juyo, so ya ke 9:00 ta mishi cikin Lagos.

Aisha ko barci ta ta sha bata tashi ba sai ƙarfe  8:30, dan yau da ƙyar ta samu ta yi asuba, cake  aunty Farwa ta musu baking suka haɗa da tea, Hajna ta fara gamawa dan ita ba wani cin abinci take yi ba, Aunty Farwa tace “je ki tada min Farween sarkin kwaɗayi yau anyi favorite snack ɗin shi "Aisha tayi ƙasa da murya tace “Mommy baya nan fa", “to ina ya je " Aunty Farwa ta tambaya, Aisha tace “ya je ɗauko Aunty Halia ne", “da gaske? "Aunty Farwa ta tambaya, Aisha tace “eh, saboda Aunty Hajna ne, ita da Uncle Farween ne su ke son juna, amma tana fushi da shi saboda Aunty Halia", “shi ne dan shirme ya je ya ɗauko ta, lallai Farween ", Aisha tace “ni ce fa nace ya zo da ita, saboda zata fi fahimta", shiru aunty Farwa tayi, ita bata ga abun wahalar da kai nan ba, miye na zuwa ɗauko ta, ko da baki ai za'a iya ma mutum baya ni kuma ya fahimta.

Suna zaune Farween ya shigo riƙe da hannu wata yarinya da a ƙalla zata girmi Hajna da shekara ɗaya ko kuma su zo tsara da juna, kanta a ƙasa dan ita bata cika ɗaga kai ba idan tana tafiya, da gudu Aisha ta zo ta rungume ta, “oyoyo my best aunty I miss u bad "Aisha ta faɗa, Aunty Farwa ta ƙaraso tace “har ka taho da Halia ɗin ko" gaɗa kai yayi dan yasan Aisha har ta faɗa mata, Hajna da ke shirin barin gurin ba tare da ta kalli ko ɗayan su ba ya ke kallo, zata wuce yace “Halia ga auntyn ki, je ki mata magana ", da sauri ta tari gaban Hajna, murmushi ta mata tace “ki kalle ni ko sau ɗaya ne", Hajna da bata yi niyyar kallonta ba ta ɗago  ta kalle, kamar ta da Aunty Farwa kamar an tsaga kara, bambanci kawai ita Halia fara ce, Aunty Farwa kuma ba fara ba ce sosai, Aunty Farwa tace “yanzu sai ka mata bayani da kanka ", Halia tace “ni zan yi", Auny Farwa tace “to ƴar a yi, jikan na saba, maza ki faɗa mata ", Hajna kuwa kallon su ta ke yi da mamaki.

“ yaya Farween ya bani labarin komai da komai a hanya, to ni ba budurwar shi bace, hasali ma an kusa aure na, ni ƙanwar shi ce, kawai dai shi kamar aboki ne a gurina", Hajna da idonta ya ciko da ƙwalla da sauri ta wuce ɗaki tana kuka, me tayi ne haka, bata ma tsaya ta tambayi Farween wacece Halia ba, amma ta hau fushi.

A ɓangaren Farween yace “Aisha ki bi ta dan Allah ki rarrashe ta " bata yi musu ba ta wuce, Aunty Farwa tace “ Halia ki ji daɗinki, da badan Hajna ba ke da gidan nan sai sallah, ko kuma in kin yi aure mijinki ya dinga bari kina zuwa", Halia tace “wallahi ", Farween yace “to minene amfanin yawo ke da aka sa ma ranar aure", Aunty Farwa tace “ina ruwanka to ba mijinta ya yadda ba ", Farween yace “oho dai, ki fara shirin tafiya gobe kinji ni ai", Aunty Farwa tace “ka yi kaɗan kuma, dan yadda ka biya buƙatarka haka mu ma yanzu za ka saka mana na mujiya har mu gama ", dariya Halia tace “ai nasan inda zan ɓullo, in be yi a hankali ba ina nan har bayan biki", Farween yace “ki mutu a nan in kin iya, mara ji kawai ".

Anan zan dasa aya............ ✍️

Ku min afuwa, daga yau zan je hutu har bayan sallah saboda aiki ya min yawa, gashi muna shirye-shiryen biki, bana so ina raba hankali, ina buƙatar natsuwa gurin rubutu, dan haka sallah da sati insha Allah zaku jini, taku har abada Queen Nasmerh.

Karku manta kuyi following Wattpad account ɗina, sannan ku bibiye littafaina tun daga kan Ayisherh har zuwa SAQAR SO.

Haɗin guiwar Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️♻️♻️♻️💃🏻💃🏻
[8/19, 11:40] Queen Nasmah✍️:     ♻️♻️HAJNA ♻️♻️

Mallakin :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAGE 79-80
************************

ALHAMDULILLAH ALA KULLI HAL🙏🤲
KAMAR YADDA NAYI ALƘAWARI BAYAN SALLAH ZAN DAWO GAREKU, YAU GASHI NA DAWO GAREKU, DUK DA BAN DAWO AKAN LOKACI BA, SABODA AKASIN DA AKA SAMU, AMMA ALHAMDULILLAH KOMAI YA DAIDAITA, INA MATUƘAR FARINCIKI DA ALLAH YA ƘADDARA YAU NA DAWO GARE KU ❤️❤️❤️❤️❤️I MISS YOU. QUEEN ✍️


*****************************'******

Ɗakin Hajna ta shiga, murmushi ɗauke a fuskarta, zaune ta sami HAJNA akan sallaya, da alama sallah ta gama dan na ji ana sallame sallar isha'i, murmushi ne ya bayyana a fuskar Hajna, “ina wuni Aunty "Halia ta faɗa tana ƙoƙarin zama kan gado, “lafiya ƙalau, Halia ya kike?", Halia tace“ina lafiya Alhamdulillahi", “masha Allah " Hajna ta faɗa tana ƙoƙarin karantar yanayin Halia, da ta duƙar da kai da alama akwai abunda take so, “Halia ina fatan dai babu wata damuwa" Hajna ta faɗa, Halia tace “Aunty Hajna dama, ummm..... " sai kuma ta yi shiru, Hajna tace “feel free Halia, duk lokacin da kike tare da ni ki ɗauka Farween ne", murmushi Halia tayi, sannan tace “dama akan maganar tafiya ta ne, Yaya Farween ya ƙi yadda na zauna nan, shi ne nake so ki mishi magana ya bari na zauna nan har ayi aure na, wallahi can ɗin babu daɗi, kuma kinga aurena saura sati uku, idan na koma ba zai bari na dawo ba, kinga nan kaɗai nake da ƴar uwa bazan ji daɗi ace bata kusa da ni fa, Aunty Farwa da yaya Farween kawai nake da a duniya "ta ƙarasa magana hawaye na bin kuncinta, rungume ta Hajna tayi, a hankali ta shiga bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi, tace “shhhh! Ki kuka insha Allah zan mishi magana", maganar Hajna ba ƙaramin daɗi ta mata ba “na gode Aunty Hajna, Allah ya bar miki yaya ", murmushi Hajna tayi tace “ke kamar ƙanwata kike to kar ki damu kin wuce haka a gare ni", sun jima suna fira, sai ƙarfe 11:00 na dare Halia ta yi ma Hajna sallama.


A ɓangaren Farween kuwa ya gagara barci, saboda yana ta kiran Hajna amma bata ɗaga ba, haka kuwa ba ƙaramin ɗaga mishi hankali yayi ba, ba dai Hajna bata huce ba, har yanzu fushi ta ke yi da shi, be wani samu issashen barci ba, gashi ya bar mata text messages har guda uku yana me ƙara bata haƙuri.


Washe gari da safe Hajna ta fito ta ɗaura breakfast, bata wani ɗauki lokaci ba ta soya doya da ƙwai, sannan ta zuba a kula, Farween ne ya fito daga ɗaki, a dinning area ya ganta, ba tare da ta gani ba ta ji tsayuwar mutum a gabanta, da sauri ta ɗago, karaf suka haɗa ido da shi, murmushi ya sakar mata, amma sai ta haɗe fuska, “haba Hajna kiyi haƙuri mana, saboda ke fa har Abuja na je ɗauko Halia ", “ni fa bazan haƙura ba" ta faɗa tana ƙara haɗe rai, kallonta yayi yace “me kike so na miki ki haƙura, plss Hajna bazan iya jurar rashin magana da ke ba " Farween ya faɗa, kallon shi tayi tace “ka tabbata?" , “eh na tabbata "ya faɗa cike da ƙwarin guiwa, har yanzu bata saki fuskarta ba tace “ so nake ka bar Halia ta zauna da mu har ayi aurenta", “shi kenan abunda kike so? " ya tambaya, “eh shi ne kawai" Hajna ta faɗa, murmushi yayi yace “to my jewel ki saki ran haka, in dai Halia ce ta zauna an gama ", murmushi ta yi tace “ har haka kake so na", Farween yace “ fiye ma da tunaninki Hajna ", murmushi tayi tace“ ka kyautata min", “tukunna dai Hajna, ni ɗinnan zan baki rayuwata gaba ɗaya idan ta kama ", da ido ta tsare shi tana me jin sonshi a kowace gaɓa ta jikinta, wani lokacin har mamakin yadda take son Farween take yi.


Zaunawa yayi, “ya da kallon?" ya tambaya, HAJNA tace “ni ba kallon ka nake ba ", dariya yayi yace “ji idonta, ko kyau", turo baki tayi, Farween yace “ ƙarya bata miki kyau ", “ni yaushe na yi ƙarya", HAJNA ta faɗa, Farween yace “to wa kike kallo "rufe ido ta yi, dai-dai lokacin Aunty Farwa da Halia suka iso, zaunawa suka yi sannan suka fara cin abinci, dan Aisha ta tashi da zazzaɓi, dan haka ɗakinta za'a kai mata, Aunty Farwa ce tace “masoya, idan an gama a kaiwa Aisha abinci ɗaki bata da lafiya ", Murmushi HAJNA tayi tace “bari na kai mata", Farween yace “zan jira ki ", bata kula shi ba ta wuce.


Kwance ta sami Aisha cikin bargo, da alama tana jin jiki, taɓa jikinta tayi ta ji yayi zafi sosai, da ƙyar ta samu Maryam ta ci abinci, shi ma kaɗan ta ci ba da yawa ba, tattara kwanonin tayi, ta kai su kitchen sannan ta dawo suka ci abinci ita da Farween, Halia na ta tsokanar su, wai da haka me zai hana su ci a plate ɗaya, Farween yace “ai wata rana zamu ci a plate ɗaya ", Hajna kuwa bata iya furta komai ba.


Likitan da Momy ta kira ne ya zo, dan haka suka nufi ɗakin Aisha da shi, duba ta yayi, sannan ya mata allura tare da bata wasu magunguna da zata sha, biyan shi Momy ta yi, sannan ya wuce.

ANAN ZAN DASA AYA.
Manage plsss, yau aka fara😂🥰🥰

Shin ya kuke tunanin auren Hajna zai faru, naga kamar bata da niyar komawa gida ❓




KAR KU MANTA KUYI FOLLOWING WATTPAD ACCOUNT ƊINA TA LINK ƊIN DA KE SAMA.

SAI MUN HA ƊU A NEXT CHAPTER
COMMENT & AND SHARE.

ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️
[8/20, 08:52] Queen Nasmah✍️: ♻️♻️HAJNA♻️♻️

Mallakin : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
https://www.wattpad.com/user/QUEENNASMERH08?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

PAGE 81-82
********************
Bayan kwana biyu

Aunty Farwa ce zaune, tare da Farween, kallon shi ta ke yi yadda ya ke kallo, hankalinshi kwance, da sauri ya juyo jin kallon yayi yawa, “wai Aunty Farwa minene, tun ɗazu sai kallona kike yi ", dariya ta yi, sannan tace “ magana nake so mu yi ni da kai", “ina jin ki", ya faɗa yana juyowa dan su kalli juna da kyau, “ akan Hajna ne " Aunty Farwa ta faɗa, Farween yace “me ya faru da ita", Aunty Farwa tace “ ganin yadda kuke son junanku yasa na ga ya kamata ta koma gurin iyayenta, daga can sai ka nemi aurenta ", “haka ne, nima na yi irin tunaninki, ya kamata ace na nemi aurenta a gidansu, tunda tana da iyaye, ya kamata mu je can, bayan haka ma bata san halin da suke ba" ya faɗa, Aunty Farwa tace “ abunda na ke gani kenan, ina tunanin mu shirya gobe mu je, dan ni so nake ayi aurenku da wuri ", murmushi ya yi sannan yace “baki kai ni zumuɗi ba, amma ki mata magana da kanki ina tunanin zata fi fahimtar ki", “to yayi bari na tashi na shiga ciki ka ga dare ya soma yi, idan nayi isha'i zan same ta a ɗaki "Aunty Farwa ta faɗa tana tashi tsaye, “ohk bari na wuce masallaci"ya faɗa, Aunty Farwa tace “to yayi ka kula", bata jira me zai faɗa ba ta nufi ɗakinta.




********************
SHINKAFI LOCAL GOVERNMENT (AJIYAWA)

“ Umman Hajna tashi ki kawo min abinci " Baffa ya faɗa yana zaune kan wata tabarma, Umma ta tashi, kitchen ta nufa, bata jima ba ta fito da kula a hannuta ta aje mishi tare da cokali, “ yauwa Allah ya miki albarka", “ameen Baffan Hajna " ta faɗa, “gobe kayan nan zasu shigo fa" Baffa ya faɗa, “ahh lallai, masha Allah, Allah ya sanya ma kasuwanci albarka ", “ameen" ya faɗa, shiru ta yi tana tunani, dan yanzu duk inda Umma ta ke idan ta yi shiru na minti biyar zata fara tunanin Hajna, da tunanin halin da take a yanzu, ba ta ankara ba ta ji saukar hawaye a kuncinta, jin shirun yayi yawa yasa Baffa ya ɗago, “Amina kuka kike yi, har yanzu bazaki daina kukan rashin Hajna ba,bayan ta zaɓi zaman can akan mu" Baffa ya ƙarasa maganar yana me jin zafi a ranshi, ya fi kowa son Hajna ta dawo, yana tsoron Allah ya tambaye shi haƙƙin kula da ita, “amma ai ƴarmu ce, ni bazan iya mantawa da ita ba, duk inda take nasan zata dawo gare mu, na yadda cewa ƙaddararmu ce ta zo ta haka, amma ban yadda na rasa Hajna ba " Umma ta ƙarasa maganar tana jin wasu hawaye masu zafi a kuncinta, Baffa yace “Amina bani da buri da ya wuce na ga Hajna tun kafin ƙasa ta rufe min idona, dan haka ba ke kaɗai ce a halinnan ba, saboda wannan tunanin na ki yasa kika samu hawan jini, so kike sai kin kashe kanki a kanta? " ya faɗa, shiru ta yi, “kiyi haƙuri ki daina damuwa kinji" ya ƙara faɗa cikin murya me sanyi, shiru tayi tana me ji a ranta duk inda Hajna ta ke zata dawo gare su.



______:::_______:::________

Bayan an gama sallah ne Aunty Farwa ta nufi ɗakin Hajna, inda ta same ta kwance akan gado ta lulluɓe kanta a bargo, da sauri ta ƙarasa jin shash-shekar kuka, buɗe bargo ta yi tace “Hajna kukan me kike yi ", da sauri Hajna ta tashi, idonta sun yi ja, tace “Aunty Farwa bansan me na aikata ba, na guji iyayena, ba tare da nayi tunani ba", hannunta tasa ta sharewa Hajna fuska, sannan tace “ko kaɗan Hajna karki yi tunanin lokacin tuba ya wuce, ki koma gurinsu, nasan zasu karɓe ki hannu biyu ",Hajna tace “Aunty abunda nake son yi kenan, amma da wane ido zan kalle su", Aunty Farwa tace “ shi ne amfanin abun, ki gode ma Allah da yake sonki da rahama, har yasa kike jin kunya idan kika yi laifi, wani baya damuwa da kurakuranshi, kina jin kunya, haka ya nuna bazaki sake yin kuskuren da kika yi a baya ba, kuma abunda Allah ke so kenan, kayi tuba irin wadda bazaka maimaita wannan kuskuren da ka tuba a kai ba, wannan dama ce a rayuwarki, wannan abun ya faru da ke ne domin ya zama darasi a gare ki da ƴan baya, da ma masu hali irin naki, ki sani komai yana da dalili, kuma rayuwa ta baki dama, Hajna zaki iya farawa daga farko, ki koma gurin iyayenki shi ne samun sauƙinki, nasan suna jiran ki, kuma sun jira na tsawon shekaru, ki shirya karɓar sabuwar rayuwa, ki watsar da waɗanda kika yi a baya, har yanzu kina da lokaci ", maganar da Aunty Farwa ta yi ba ƙaramin kwantar mata da hankali ya yi ba, “nagode Aunty Farwa, ke kamar yaya kike a gare ni", Aunty Farwa tace “ki ɗauka ba kama ba ce, ita ce! Ni yayarki ce har abada, ki shirya kayanki gobe zamu je Zamfara, dole ki koma ga iyayenki akan lokaci ", “ bazan misalta farincikin da kika saka ni ba, nagode miki sosai" Hajna ta faɗa, Aunty Farwa tace “kin wuce godiya a gare ni, duk abunda na miki ki ɗauka kaina na yi ma ", murmushi tayi, sannan ta fita.


Halia da Aisha suka haɗa mata kayanta, ita kuma tana tare da Farween a gaban gida, kallon ta ya ke yi, yayin da wasu hawaye suka zubo mata a kunci, “Hajna kukan ya isa haka", shiru tayi dan a yanzu abu biyu

Please Login or Register in order to submit comment