Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shirya ya nufi dajin da suke tsubbace _tsubbacensu.......

Nan ya bi duk dokar dajin da suke kamar yanda suka saba, Kafin daga bisani ya ganshi a cikin gida tsafin......

Ko bayan ya isa sauran abokan tafiyarsa sumw suna ciki suna jiran zuwan shi domin zuwa yanzu shi suke jira......

Batare da sun ce mishi komai, Alhaji tanim gamji ya zauna yayi Shuru kafin daga bisani ya miƙe ya nufi ɗayan ɗakin ......

Kayan tsafinshi ya saka , daga bisani yawo ɗayan ɗakin ya zauna ya sami sauran ........

Shuru gurin yayi kafin daga bisani babban wato Azarfakinzu yafara magana da kakkausar murya yana faɗin," to kowa ya hallata , sannan kowa yazo , sabida haka yanzu inaso naji kyakyawan labari daga kowanne ku ........

Alhaji tanko ne ya fara magana yace," an gaisheka Azarfakinzu, nidai ta ɓangare na komai yayi daidai domin na riga na sadaukar da ita yanzu aiki ya rage naku .......


Wata shu'umin dariya Azarfakinzu ya yi kafin daga bisani yace," aiki ka yayi , kayi aiki mai kyau , yau ɗinan za' a ziyarceta ba sai gobe ba , matuƙar kaga tana ciwo to kasani aikin mune, daganan kuma zamu zuƙe jininta kaga sai mutuwa......

Shuru yayi ,yaɗan sunkuyar da kanshi kafin daga bisani yaɗago kai jiki a sanyaye yace," shikenan .......

Alhaji mato ne yaɗan Numfasa daga bisani yace," to nima dai ta ɓangare na babu wata matsala domin ,yanzu haka na Ajiye kayuka guda biyu suna ɗakin ajiya ɗaya na yaro ɗaya kuma na babba, za'a iya fara aiki .......

Wata shu'umar dariya Azarfakinzu ya ƙara tuntsurewa dashi abun tsoro ,kafin daga bisani yayi Shuru ,ya dake tamkar bashi yayi dariyar ba ,yace," Dakyau angama .........

Nuna Alhaji salim yayi da yatsa yace," kaima ina jinka , tsoro ne matuƙa ya baiyyana a fuskar Alhaji salim , jikinshi na rawa muryarshi na rawa yace," Azarfakinzu Taimaka, taimaka Amun uzuri Ni nawa aikin bai samu ba , a ɗan ƙara bani wai lokaci ......

Wani huci Azarfakinzu yayi mai matuƙar tsoro, idonshi yayi ja wani hayaƙi ne ke fita daga bakinshi yace," kasani a wannan harka babu tausayi babu tausayawa babu uzuri, sannan babu yafiya , sannan baza'a taɓa fita ba, kasan wannan shine dokar ƙungiyar mu , sannan kai kayi Alƙawarin ka yarda da haka shine yanzu zaka kawomun wasa ,to baka isa ba ,tunda bakasamu ba dole zamu amfani da naka ai.......

Cikin matsanancin tashin hankali Alhaji salim ke faɗin," kayi haƙuri Azarfakinzu ,tuba nake baza'a sake ba wannan alƙawarin nayi maka , wata irin tsawa yada kamishi kafin daga bisani yace," ina ai kasan dokar wannan kungiyar sabida haka yanzu kai zamuyi amfani da naka , take yafara wasu irin maganganu , inda Alhaji salim yafaɗi a gurin a sume bakinshi na fita da wani kumfa , cikin ƴan mintuna rai yayi halinshi , jikinshi yayi wani irin fari kamar takarda , nan suka ɗagashi suka ɗauke shi suka kaishi cikin ɗakin duhu ....,..

Na aka zo gurin Alhaji tanim , nan Azarfakinzu yace," kai kuma fa ? Ina jinka , ya ake ciki ?

Gyaran murya Alhaji tanim yayi daga bisani ya ɗan numafasa yace," ehh na riga da na auri yarinyar ma , me ya rage yanzu? Wata shu'umar dariya Azarfakinzu yayi daga bisani yace," zamuyi amfani da jininta ,bayan ƴan watanni , cikeda gamsuwa ALHAJI TANIM yace," babu matsala .......

Nan suka cigaba da tsubbace tsubbace su daga bisani kowannensu yatafi kamar yanda suka saba ........


A ɓangaren Ammi murna sossai takeyi matuƙa , bata damu da sanin halin da Hamdiyyah ke ciki ba , ita dai abun da ta sani tasan ƴar ta na cikin daula , hakan yasa bata damu sai ta kira taji lafiyarta ba ........


Bayan sati ɗaya shaƙuwa mai ƙarfi ce ta ƙullu tsakanin Su Hibba da Hamdiyyah , suna matuƙar ƙaunarta , domin Hamdiyyah bata taɓa musu mugunta , tana bala'in don yaran Kasancewa ita ɗin mai son yara ce matuƙa .......

Sossai suke jin daɗin zaman gida , sun daina zaman takura , kullum cikin hira suke , ga jansu a jiki da take sossai , hakan yasa suka shaƙu matuƙar gaske .......

*Pls manage this*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 29 & 30*

Bayan sati biyu Alhaji tanim gamji yawo daga ƙasar Indiya .......

Tun da ya kira waya yace yana dawowa gaban su ke ta faɗuwa kamar me , dukkansu jikinsu a sanyaye musamman ma Hamdiyyah ,da duk ta rasa nutsuwarta tamkar an faɗa mata ranar mutuwar ta ........

Wunin ranar gaba ɗayan su babu wani walwala a tattare dasu , musamman Hamdiyyah ......

Ƙarfin hali sossai sukayi suka girka musu abinci , domin Hamdiyyah jikinta a sanyaye yake ga matsanancin tashin hankali , tana me tunanin dawo warshi ,tana me matuƙar tausayin kanta......

Baya sun gama girka abincin nan ta zuba ma dukkanin su Batare da ita taci ba.......

Zama tayi ta rafka uban tagumi tane me matuƙar tashin hankali .....

Shuru Hibba tayi tana kallonta kafin daga bisani tace," Anti , meke damunki ne? naga kinƙi cin abinci ,meyasa ? dan Allah ki sauƙƙo muci , tafaɗa cikin sanyin murya .......

Murmishin yaƙe Hamdiyyah tayi tace,"Hibbatu na zanci kinji banajin yunwa yanzu ne.......

Cikin rashin yarda da magana ta tace,"A'a ba haka bane , ai naga tunda daddynmu yace yana hanyar dawowa shine duk jikinki yayi sanyi ko, bakyaso yadawo ko? yaƙen dole Hamdiyyah tayi tace,"A'a ba haka bane kai na ne yake ɗan ciwo kaɗan fa , Shuru Hibba tayi batare da yarda da abun da ta faɗa ba taɗan Numfasa tace,"Hmmm to kiyi haƙuri in Allah ya yarda bazaki sha wahala , kidinga yin Addu'a kinji , amma kinsan miye? Ki daina damuwa mudaina jin tsoronshi kinji? tunda ai kina sanshi tunda kika aureshi ......

Hawayene ke ƙoƙarin zuboma Hamdiyyah a fuskar ta, tayi saurin jan dogon numfashinta , gamida da sa hannu ta goge fuskarta tace," Hibba mun riga munzama ƙawaye , kuma Abokiyar shawarata , sannan ƴata ,duk da ke ɗin yarinya ƙaramar ce amma tunanin ki na manya ne , Maganar gaskiya Hibba banason mahaifinku , auren dole mahaifiyata tayi mun tur sasani akayi, inada wanda nakeso ,wanda muke soyaiyya amma Ammi ta batasanshi saboda bashi da kuɗi , shine ta sa na auri mahaifinku, ta ƙara sa maganar gamida fashewa da kuka .......

Shuru Hibba tayi kafin daga bisani tace," Anti nima ban miki murnar auren daddynmu ba , sabida kina da kirki sossai, kuma nima nayi mamakin yanda kika auri daddynmu , kinsan meyasa ? Kaɗai kai Hamdiyyah tayi Alamar A'a ,Hibba taci gaba da faɗin," kece mace ta biyar da daddynmu ya aura a shekara ɗaya , bayan iyayenmu da suka rarrasu,......

Zaro ido Hamdiyyah tayi gamida buɗe baki tace," da gaske Hibbah? Ehhh da gaske Anti , rabuwa dasu yakeyi ? Hamdiyya ta tambayi Hibba ,A'a Hibba tace," ta cigaba da faɗin," ba rabuwa dasu yake ba ,in ya ɗauke su yayi tafiya da su to bazai ƙara dawo da su ba sai dai yadawo shi kaɗai kuma bamu taɓa tambayarshi ina suke ba , saurin dafa hannun Hamdiyyah hibba tayi tace," Dan Allah Anti in yace ku tafi kar ki bishi ko ina kinji? banaso mu rabu dake ,duk cikin matan ke kaɗai ce mai kirki ,ke kaɗai ce kike tausayin mu,kike son mu , muna sanki sossai , banaso ki tafi dan Allah kar ki bishi kinji banaso mu rasaki ........

Sossai Hibba taba Hamdiyyah tausayi ,hakan yasa wasu ƙwalla suka zuboma Hamdiyyah tace," Hibba bazan tafi ba bazan tafi na barki ba ina tare da ku har ƙarshen rayuwata ko da kuwa hakan zai sa na rasa raina baza'a taɓa barinku ba kinji Hibba ta , sossai Hibba taji daɗin maganar cikeda da farin ciki tace," yauwa Anti nagode sossai ,dan Allah ki ci abinci ki daina damuwa kinji? To Hamdiyyah tace gamida sakin murmishin yaƙe tace," to muje muci abincin ko ? murmishi sukayi daga bisani suka ci abincin.......

Duk wani dokokinshi na gidan sai da Hibba ta tabbatar ta kiyayeshi, duk abun da bataso ta tabbatar bai gani ba, sossai ta yi duk abun da tasan bazai yi mata faɗa ba in yazo yagani, hakan yasa ta faɗa ma Hamdiyyah cewa ta gyara mishi ɗakinshi gamida bata turaren wutar da zata saka mishi a ɗakin .......

Babu musu Hamdiyya ta karɓa batare da damuwa ba tayi duk abun da Hibba tace mata , wuni sukayi suna aiki .......

Girke sossai suka fara ƙoƙarin shirya mishi , sanin cewa da karuwanshi zai dawo gidan yasa Hibba faɗin," Anti kinsan Abincin da yawa zamuyi , cike da mamaki Hamdiyyah tace," da yawa kuma Hibba?ehh da yawa ba shi kaɗai yake dawowa ba da wasu mata yake dawowa kuma abincin dasu ake yi.......

Dogon numfashi Hibba taja tace," kuma duk ke kaɗai kike girke girken nan? Ehhh Hibba tafaɗa......

Mamaki sossai Hamdiyyah tayi gami da faɗin,"To su matan su waye? budurwayenshi ne Hibba tafaɗa batare da nuna wata damuwa ba ......

Nan danan Hamdiyyah ta fahimta inda zancen ya dosa , hakan yasa tayi shiru bata ƙara magana ba , sai cewa tayi , okay to shikenan Bari mu ƙara sanwa.....

Nan suka cigaba da aikinsu suna yi suna ɗan taɓa hira gwanin ban sha'awa.........

Misalin ƙarfe tara na dare su Hamdiyyah da Hibba sunyi jigun jigun suna jiran dawowarshi .....

Goma da minti biyar Motar Alhaji tanim gamji ya faka a katafaren gidanshi........

Sossai gaban Hamdiyyah ya faɗi jikin ta ya fara rawa ,bakinta na karanta innalillahi wa'inna illaihir raju'un shine abun da bakinta ɗa zuciyarta ke iya furtawa.........

Jiki a matuƙar sanyaye suke jiran shigowar shi....

Kamar yanda ya saba , dama da mata huɗu yake shigowa cikin gidan......

Batare da damuwar komai ba kai tsaye ya shigo cikin gidan matan suna ta shewa abinsu.....

Sossai Hamdiyyah tayi mamaki matuƙar gaske ganinshi tare da mata......

Mamaki sossai tadinga yi tana jiran ganin ikon Allah.......

Bayan sun shiga ɗakin ne sukayi wanka daga bisani kai saye suka nufi dining dan cin abinci .........

Da kakkausar murya ya ƙwalla ma Hamdiyyah kira , ganin bata fito ta gaisheshi ba ......

Jin kiran shi yasa gabbanta ya kara faɗuwa matuƙa , kallan Hibba tayi batare da tace komai ba , jikinta na rawa ta fita , gaban ta na mugun faɗuwa ,wutar tsoronshi na ƙara ruruwa cikin ranta.......

Daƙyar ta iya ƙarasawa gurinsu, wani kallo karuwan nashi suka wurgamata gamida yatsine fuska......

Bakinta na rawa ta kalleshi tace,"sannu da dawowa , wani kallon raini yayi mata gamida da sakar mata wata harara batareda ya kulata ba ......

Wata tsawa ya daka mata gamida faɗin,"ke Ni kaɗai kika gani a gurin nan? bakya ganin baƙi ne bazaki tsugunna ki gaisheshi ba ?

Da sauri Hamdiyyah ta ɗan risina tace,"kayi haƙuri , sannunku da zuwa ina wunin ku ......

Wata harara suka galla mata tare kafin daga bisani su amsa cikeda isa.....

Juyawa tayi tafara ƙoƙarin tafiya , wata tsawa ya daka mata gamida faɗin," how dear you Zaki tafi batareda na baki izinin ba ,Ni ne nace ki tafi ? Wawiya common kizo ki serving ɗin mu ......

Batare da tace komai ba tayi sauri jikinta na rawa tace,"to ......

Dasauri ta fara ƙoƙarin serving ɗin su ,duk da rawa da jikinta keyi , tana yi suna daka mata tsawa duk tabi ta rikice, daƙyar ta iya serving ɗinsu , duk ta ƙosa tayi ta bar musu gurin ko zata samu nutsuwa.......

Sai da ta tabbatar da ta gama musu komai kafin daga bisani ta juya ta tafi ........

Ko bayan sun gama cin abincin ,nan suka tashi suka nufi ɗaki suka fara aikata Alfashansu ,wa iya zubillahi ........

Dakinsu Hibba Hamdiyyah sukayi tayi uban tagumu tana me tunanin yanda zasu wanye dashi a daren yau ko zai nemeta ohoo? ,duk da dai cewa ga karuwan shi , hakan yasa take ta Addu'ar kar Allah yasa ma ya nemeta ya ƙare can da karuwanshi .......

Ganin har ƙarfe sha biyu na dare bai kirata ba yasa hankalinta ya kwanta matuƙa ,hakan yasa ta yanke shawarar barci a ɗakin su Hibba hankalinta kwance ......

Ita ma Hibba daɗi taji da Hamdiyyah zata kwana a ɗakin nasu ......

Washe gari da Asuba su Hamdiyyah da Hibba suka tashi kamar yanda suka saba.......

Nan Suka fara ƙoƙarin shirya break fast da shirin school ɗin su Nihal ........

Misalin karfe bakwai suka kammala komai , suka jera komai akan dining ɗaga bisani suka fara ƙoƙarin shirya su Nihal suka tafi school.......

Bayan sun gama ne suka gyara gidan tas, daga bisani suma suka karya suka kwanta suna ɗan taɓa hirar su jifa jifa......

Misalin ƙarfe sha ɗaya suka fito bayan sunyi wanka sun fito ne daga bisani suka nufin dining suka fara ƙoƙarin ƙaryawa.........

Baya sun gana suka shirya suka fita hutawansu hankali kwance ........

Batareda Alhaji tanim gamji ya damu da halin da suke ciki ba yayi tafiyarshi hankali kwance......

Ganin sun fita yasa su Hamdiyyah sakewa sossai a gidan , hankalin Hamdiyyah ma ya ɗan kwanta kaɗan ........


Misalin ƙarfe shaɗa na dare Alhaji tanim gamji yadawo , kai tsaye ya nufi ɗakin shi , ganin Hamdiyyah bata ɗakin yasa shi ɓata rai gamida faɗin," wai me yarinya nan take nufi ne? Ko ta manta a matar aure take ja ne , shine zata barni ni kaɗai , tsaki yaja daga bisani ya ɗaya murya ya ƙwala mata kira yana faɗin," ke!ke! Hamdiyyah? jikin Hamdiyyah na rawa ta miƙe tace ," Hibba yana Kirani barin je , jiki a sanyaye hibba tace," to Anti sai da safe , gaban Hamdiyyah na mugun faɗuwa jikinta na rawa ta nufi ɗakinshi....

Ko data shigaiga ɗakin da sallama ɗauke a bakinta , tace," sannu , batareda ya kulata ba yace," ki zo mu kwanta bakya ganin dare yayi ne?.......

Jin ya ambaci haka yasa gaban Hamdiyyah mumunan faɗuwa,muryarta na rawa tace," me kace?bansani ba common kizo mu kwanta ,ke bakisan hakkin mata akan mijinta bane?yafaɗa kamar yaro ƙarami.....

Bakinta na rawa tace," nasani kayi haƙuri ........

Batareda yace mata komai ba ya jawo ta ya wur gata kan gado ,shima ya hau gadon ya Nufeta gadan_ gadan , ya biya buƙatarshi kamar yanda yayi a wancan lokacin.......

Sossai Hamdiyyah take kuka tsabar azabar da ta ƙara ji , sai dai bata kai ta ranarr farko ba,kasancewar bai daɗe akanta ba sosai a wannan karan , amma hakan baisa ta daina jin zafin ba........

Ko da ya gama ya tashi ya koma ya kwanta hankalinshi kwance batareda da damuwa da halin da take ciki ba ,daƙyar ta iya miƙewa ta gyara jikinta ta shiga ruwan zafi da kanta, ta yi wankan tsarki, ta gyara jikinta tana kuka tana cizan leɓe, tana me ƙara jinjina rashin imani irin na Alhaji tanin....

Kuka sosai takeyi tana me ƙara danasanin haihuwar ta da akayi har tazo duniya da duk hakan bai faru da ita ba .........

Ganin ba sarki sai Allah yasa ta ɗan tsagaita kukanta tacigaba da addu'ar mafita ..............


*To nasan zakuso kuji wanene shi Alhaji tanim gamji , sannan wacece kuma Hamdiyyah,ku biyoni danjin labarin ALHAJI TANIN GAMJI.........*

*To Alhamdulillah ƴan uwa ana zan tsaya sai kuma bayan sallah inshallahu rai da lafiya zamu ɗaura daga inda muka tsaya inshallahu.......*.

*Watan Ramadan wata ne dazamu mai da hankali wajan yin ibada , hakan yasa bazan cigaba da posting ba , kuyi haƙuri, mu duƙufa wajan bautar Allah*

*Inshallahu bayan sallah zamu ɗora daga inda muka tsaya*

*To inayima kowa fatan Alkhairi ƴan uwa Allah yasa muyi ibada karɓaɓɓiya , Ameen ya Rabbil Alamina,*


*Story & written by mum fu'ad*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 31 & 32*

*Alhamdulillah , Allah mungode maka da ka sa mukaga har ƙarshen Ramadana , Allah ya maimaita ma, Allah kuma ya karɓi ibadunnun mu Ameen*


Shin wacece?????? Hamdiyyah!!!!!

Hamdiyya muhammad lawal shine cikakken sunanta .......

Mallam lawal shine mahaifinta ,Sai Baba Ramatu mudi itace mahaifiyarta......

Hamdiyyah ita kaɗai Allah ya Bama Mallam lawal da Ramatu , sun ɗauki lokaci mai tsawo kafin Allah ya sa su haifi Hamdiyyah , inda tunda suka haifeta Allah bai sake basu haihuwa ba ......

Mallam lawal mutun ne shi mai sauƙin kai da kauda kai , mutun ne wanda magana ma ba cika son yinta yake ba , duk abun da zai gani sai dai ya bishi da ido, hakan ne yasa Ramatu ,wato mahaifiyar Hamdiyyah take yi mishi duk abun da taga dama , wulaƙancin yau daban na gobe daban , babu irin rashin mutuncin da bata mishi ........

Kullum goron take mishi cewa shi talaka ne bashi da ko sisi......

Mallam lawal talaka ne amma yanada wadatar zuci matuƙa , saɓanin matarshi da take da son abun duniya , hakan yasa rashin mutuncin yake ƙara ƙaruwa dalilin halin talaucin dayake ciki ......

Tun Hamdiyyah nada shekaru takwas zuwa goma A lokacin tafara waiyyo sossai ,hakan yasa take lura da halin mahaifiyarta inda sam bata jin daɗin yanda take yi ma mahaifinta .......

Sossai Mallam lawal yake haƙuri da halin Ramatu , duk abun da takeyi baya taɓa mata maganar , haka yaje barin abun a cikin shi duk da cewar abun na ɗamunshi matuƙa.......

Babu Abun da zai kawo mata da bazata kushe ba , sam baya burgeta duk abun da zai mata sai ta rai , bata taɓa mai godiya akan duk abinda yakawo yayi mata gwaninta .........

Hakan yasa Ciwo yafara ƙamashi da kaɗan_ kaɗan , ko dayaje Asibiti gwaji ɗaya likita ya tabbatar mishi da cewa yana ɗauke da ciwon zuciya......

Sossai abun ,ya dameshi matuƙa, hakan yasa likita ya gindaya mishi sharuɗa akan ya kiyaye abun da zai ɓata mishi rai , sannan kuma ya kiyaye saka abu arai , da to ya amsa , daga bisani ya tafi gida cike da damuwa da tashin hankali ........

Ko da yaje gida jiki a sanyaye ya tsugunna yana rokon matartashi akan cewa tadaina ɓata mishi domin ance yana fama da ciwon zuciya, kuma yasan damuwarta ce ya janyo mishi wannan ciwon ......

Ko da yake faɗa mata bai abun da ya dameta ,sai cewa ma tayi matuƙar yana so zaman lafiya yaje ya nemi kuɗi ko ma a ina yake sai su zauna lafiya ......

Ganin zata ƙara bata mishi rai ne yasa ya tashi ya bar ta tana ta bibininin masifa......

Da sauri Hamdiyyah ta bi mahaifin ta da gudu tana bashi haƙuri, wata ƴar ƙwalla ce ta zubo mishi, Hamdiyyah tayi saurin share mishi tace," Abba kayi haƙuri kaji ??

Murmushin yaƙe yayi yace," babu Komai Hamdiyyatu , kinsan me nake so dake ?kaɗa ka tayi Alamar A'a nan ya ɗan numfasa yace," ina son ki zama mai wadatar zuci kinji ? Kar ki dinga san abun duniya , kar ki zama mai son kuɗi ,Ki nemo farin ciki a rayuwarki ba daula ka mulki , ko muƙamin ba kinji , to tace gamida kaɗa kanta , nan ya cigaba da faɗin," kar ki zama mai roƙon ko maula ko Bara , ki dogaro da Allah sai Allah yataimakeki , kar ki bi ruɗin zuciya ,kiyi abin da kikasan zai sanyaka farin ciki kinji ? yaƙarasa maganar ɗauke da murmishi a fuskarshi ......

To Abba , Hamdiyyah ta faɗa gamida rungume shi gwanin ba tausayi.........



Bayan shekaru uku , A lokacin Hamdiyyah nada shekaru goma a duniya......

Rashin mutuncin Ammin Hamdiyyah kullum ƙara yawa yakeyi , hakan yasa ciwon Mahaifin ta ya ƙara tsananta matuƙa......

Jinya sossai ya farayi,kafin har rai yayi halinshi ......

Sossai Hamdiyyah tayi kukan rashin Abbanta Saɓanin Ammi da take faɗa dama dashi da babun duk ɗaya hakan yasa mutuwar bata wani ratsa ta sossai ba ........

Tunda Abban Hamdiyyah ya rasu , Ammi ta miƙe tsaye fafur da neman kuɗi, a cewarta sai tai kuɗi ko ta yaya ......

Ƴan uwan Mallam lawal sun so su karɓi Hamdiyyah amma sam Ammi taƙi yarda da hakan a cewarta ita zata kula da ƴarta kar su goga mata talauci irin ma ubanta , talaucin irin dangin su ne.......

Badan sun so hakan ba suka haƙura dan kansu .....

Tunda Hamdiyyah ta fara girma Amminta ta ɗauki buri matuƙa a kanta a cewarta Hamdiyyanta sai mai kuɗi , hakan yasa duk kuɗin da ta samu akan Hamdiyyah yake ƙare wa ita ala dole tana so ta dallo miji mai kuɗi ........

Hamdiyya na J.S.S 3 suka haɗu da Faisal, ba yanda Ammi ta iya haka ta haƙura ta barsu suke tare Amman badan taso ba , ganin

Please Login or Register in order to submit comment