Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita muke aiki , cire hotonta a gidan matsala ne , sai dai zamuyi abu ɗaya , kasa a kwakule ido ta na cikin hoton kaga daganan bazata ƙara razanaka ba , wanan shine kaɗai mafita .......

Durkisawa yayi yasa kanshi bisa kwaryar yace," a gama godiya nake la'anannen Allah , sai kuma matsala ta biyu , duk da dai ba za'a kirashi matsala ba sai dai buƙata .....

Inaji!! Azarfakinzu ya faɗa," dama akan maganar auren da kuka saka nayi ne , kuma inason zan kashe kuɗi sossai da sossai , kuma naga kamar kuɗi na sunyi ƙasa saboda haka ina da buƙatar wasu in badamuwa ........

Wata shu'umar dariya ya tuntsure dashi yace," an gama ai wannan buƙatar har mu zamu amfana dole muyi maka ruwan daloli , kaduba ma'ajiyar zakagani, yana faɗa haka ya ɓace ɓat a cikin kwaryar ........

Take Alhaji tanim gamji ya miƙe ya buɗe wata ƴar ƙaramar ƙofa ......

yaye wani baƙin ƙyalle yayi ,take wani irin halitta ta bayyana ,halittar da baza'a ce mishi mutum ba ba kuma baza'ace Aljani ba ....

Daloli ne suka fara fita ta bakin halittar , suna zuba cikin wani ƙaton akwati , sai da suka cika akwatin daga bisani suka daina fita ......

Ɗauka yayi ya dawo ɗayan ɗakin nashi, inda ya canza kayanshi ya ɗauki akwatin ya sha tafi ɗakinshi dashi .......

Cikeda farin ciki ya fito yana ƙara tuntsurewa da wata matsananciyar dariya.......

Fitowa yayi a ɗakin ya shiga ɗakin shi hankali kwance ,daga bisani ya canza kaya ya saka kayan barci ya kwanta .......


Washe gari misalin ƙarfe uku na yamma Alhaji tamim gamji ya shirya cikin manyan kaya .......


Wata rantsasiyar shaddar buwa ya saka kalan bulu, anyi mata baƙin design sai takalmin shi baƙi hula baƙi , da agogo da zobuna , glass ɗin idonshi ma baƙi ne, haƙorin makamashi na basaja ya ɗauka ya maƙala ,carbi ya ɗauki ya riƙe , yafi to kamar yana ja da gaske .......

Kuɗi ya ɗiba masu yawan gaske wa' inda aƙalla zasu kai dubu ɗari bakwai ya fita dasu ......

Haƙika duk wanda yasa idonshi akan na Alhaji sai kaji ya burgeka , zaka rantse ma da Allah mutumin arziƙi ne .......

Kai tsaye ya fito ya nufi motarshi, ya shiga sai rikos are'a......


A ɓangaren hibba kuwa a daren jiya da zazzaɓi sossai ta kwana , sai ƙarfin hali kawai tayi ta musu abinci da taimakon nihal ........

Da safe ma daƙyar ta iya shirya su suka tafi school , tana gamawa ta ƙara shan paracetamol ta kwanta .......

Duk halin da suke ciki bai ko damu ba ,bai ma san halin da suke ciki ba bare ya san bata da lafiya domin kuwa ba zuwa dubasu yake ba ........

Haka ta ɗaura musu abincin rana daƙyar , da ƙarfin hali , duk da dai taɗanji dama_dama a jikinta ......

Dadai ƙofar gidansu Hamdiyyah Alhaji tamim gamji ya faka.......

Sallama ya rafka da kanshi a ƙofar gidan, inda Ammi ta amsa......

Da sauri Ammi ta miƙe ta shiga ɗakin Hamdiyyah......

Kwance take tana kallon sama fuskarta duk ta kumbura da idanuwanta tsabar kukan da ta wuni ta kwana tanayi ........

Cikin faɗa Ammi tace," in kin ga dama ki tashi kije ana sallama inaga mutumin jiya ne ......

Shuru Hamdiyyah tayi Cikin ranta take faɗin," uhmm to miye amfanin zuwanshi , tunda aikin gama ya riga ya gama faisal ya tafi ,ni da me bai zo ba ,dan bai da amfani , domin ma zuwanshi gida Ammi ta ƙara tsanar Faisal.......

Cikin tsawa Ammi tace," wai ba magana nake miki bane? Maza ki tashi kije mana .......

Tashi Hamdiyyah tayi ta zari hijabi ta fita fuuuuu kamar zata fashe .......

Zaune yake a mota gani shi yasa shi sauri fitowa ya tsaya ......

Ganin yanayin ta yasashi faɗin ," subhanallahi , Hamdiyyah mai ya faru haka da alama kuka kikayi tabbas .......

Batasan sanda kuka ya kuɓuce mata ba tace," Faisal Faisal ta taƙarasa maganar gamida fashewa da kuka .......

Dan Allah kiyi shiru kimun bayani kinji banaso abun da za'a ɓata miki rai ki daina kukannan.......

Tsagaita kukan tayi tace," Faisal ya tafi bazan sake gani shi ba .......

Jin haka yasa farin ciki ya ƙara bayyana cikin zuciyar Alhaji tanim gamji , inda cikin ranshi yake aiyya a cewa ba sai yasha wahala ba kenan komai zai tafi dai_daii.....

Cikin sigar tausayi yace," to ina Faisal ɗin yaje?ban sani ba bansan inda yaje ba yadai rubutomin wasiƙa wai ya tafi bazai dawo ba.....

To kiyi shiru kinji yanzu muje inga mahaifiyar taki in yaso zan mata bayani ,sannan na miki alƙawarin nemo miki Faisal a duk faɗin duniyar nan kinji ko ?

Cikeda gamsuwa Hamdiyyah tace to Nagode sossai ,barin je ina faɗa mata sai ka shigo , okay yafaɗa ,ita kuma ta koma ciki .......

Ammi wai zai shigo yanzu in badamuwa , Hamdiyyah tafaɗa jiki a sanyaye .......

Jiki na rawa Ammi tace,"Ahh yashigo kai badamuwa kice ya shigo , Ammi tafaɗa gamida shiga ɗaki ta ɗaukko tsohuwar tarburmarta ta shinfiɗa mishi .........

Gurinshi ta koma tace," wai ka shigo, zamu iya shiga yanzu ......
Cikeda farin ciki yace okay nagode , yafaɗa gamida shiga cikin gidan .......

Ganin yanayin gidan yasashi taɓe fuska , cikin ranshi yake faɗin," Ni banda akwai abun da nake da buƙata a gidan nan mai zai kawo Ni ,ƙazamin gida haka,ai ko inda zan ajiye karnuka zaifi nan haɗuwa , yafaɗa cikin zuciyarshi inda a fuskarshi kuma yana me murmishin yaƙe..........


*MUJE ZUWA*

*NOTE LABARIN NAN TRUE LIFE NE KARKUMANTA*

*ZAKU IYA FARA BIYAN KUƊI KU DAN NASA KU A PAID GROUP*

*DAN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAU IYA TUNTUƁATA AKA LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386347*


*COMMENTS*
*&*
*SHARE*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*

*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 17 &18*

Da fara'a fal a fuska Ammi ta tarbeshi , tana faɗin sannu, sannu da zuwa shigo ƙaraso, tana mishi nuni da tsohuwar ta burman su .......

Cigaba da murmishin yaƙe yayi yace," yauwa sannu mama.....

Daƙyar ya iya zama a tsohuwar tarburman yana ɗan yatsine fuska , cikin ranshi yana faɗin," in badan yana da bukatar wani abu ba, ace wai kamar shi ya zauna a wulakantaccen guri irin wannan kai tirr, saɓanin a zahirance da yake ta washare baki........

Zama yayi cikin ladabi,haɗe da sunkuyar da kai yace," sannu Mama ina wuni......

washe baki Ammi tayi tace," lafiya kalau , ka wuni lafiya ya gajiya ya gidan da kowa da kowa ......

Cikin girmamawa yace," lafiya kalau duk suke,to sannu da zuwa Ammi ta faɗa , yauwa Nagode ya faɗa a takaice ......

Cikin mai da hankali Alhaji tanim gamji ya fara faɗin," to da farko dai Ni sunana Alhaji tanim gamji , ina zaune a ringroad Are'a ,sannan iyayena suna zaune a rayfield, sannan Ni ma,aikacin gaumnati ne , sannan ina wasu harkokina ƙasar Indiya....
Tunda Ammi taji ya ambaci ƙasar india'a hakan yasa ta ɗan zaro ido , cikin ranta take faɗin," Ah Lallai Hamdiyyah ta samu mijin aure .....

Nan ya cigaba da faɗin," sanan kuma inada yara , amma bani da iyali a halin yanzu , domin Allah yayi mata rasuwa , to tsakanina da Allah ina da buƙatar ƙarin aure tun ba yanzu ba , amma ina tsananin tsoron mata a wannan zamanin domin ba kowacce mace bace takeda tsoron Allah a cikin ranta , mata dayawa sukan kawo kansu gareni da sunan so na auresu Amma Sam ni na nuna bana ra'ayinsu , saboda kwata_kwata tarbiyyar su batamin ba, haƙiƙa na nema mata a garin dama wasu gari amma ko wacce na samu sai na sameta da wani banzan hali , sabida Ni nafison naga na auri mace wacce zata riƙeni amana sannan kuma ta riƙe mun ƴaƴana tamkar ita ta tsugunna ta haifesu, numfasawa yayi gamida sunkuyar da kanshi ya cigaba da faɗin," tsakani na da Allah , tunda na sauƙe idanuwana akan Hamdiyyah , nan take naji in ƙaunarta , sannan jinin jikina ya bani ta fito daga gidan tarbiyya , hakan yasa na ji ina tsananin buƙatar aurenta , to gaskiya banyi ƙasa a gwiwa ba na yi sauri nayi mata magana amma sam bata bani haɗin kai ba , hakan bai sa na karaya ba shine na ƙara dawowa jiya dan na ƙara jaddada buƙata ta a gare ta , to A lokacin shine ta zomin da wata magana da tasa na matuƙar tausayama ta ......

Jin haka yasa Ammi ƙara gyara zamanta gamida zaro ido tace," to fa wacce irin magana tafaɗa maka? Hankalin Ammi duk ya tashi matuƙa tana me tunanin abun da hamdiyyah ta faɗa mishi ......

Eh to ba komai ta faɗa mun ba illa tafaɗamun cewa akwai wanda take soyaiyya dashi ......

Saurin dakatar dashi Ammi tayi ta hanyar faɗin," wallahi Alhaji ƙarya take Ni bansan wannan zance ba sai dai in ita dashi ne suka haɗa kansu .......

Hamdiyyah da take ɗaki tana ji tasa kuka ta na me jajjada hali irin na mahaifiyarta .......

Murmushi yayi cikin ranshi yana me murnan samun nasara yaci gaba da faɗin," A'a mama ba haka bane ki saurareni kiji yanda muka yi da ita ......

Cikin ɓacin rai Ammi tace," kaga Alhaji banaso inji wanan banzar maganar da wannan shashashar yarinyar ta faɗa maka , kasan Allah wallahi ƙarya take babu wani wanda na san dashi da yake zuwa gurinta ƙarya kawai takeyi, cigaba tayi da faɗin ," kasan Allah Alhaji in ka shirya ko yau a ɗaura muku aure kai da ita a shirye muke , dan ta haka ne kaɗai zaka ƙara tabbatar dacewa ba bu wani wanda yake san Hamdiyyah,uhmmmm kaga Alhaji nifa in ma kanaso yanzu sai muje dakai gidan kawun ta ku gama magana dasu sai ma kawai ka kai sadaki a saka rana a ɗaura muku aure !! .......

Jin kalaman Ammi yasa Hamdiyya ta shiga cikin matsananciyar fargaba da tashin hankali , take taji ƙijinta yafara mata zafi , bakinta yafara ɗaci ,kuka da takesonyi ma ko zaji daɗi amma ta kasa , lallaɓawa tayi daƙyar ta zauna a kan gadonta , tana ta aiyya na abubuwa iri_iri cikin ranta.......

Cikeda murna da gamsuwa Alhaji tanim yace," Amma Ummah , dan Allah in kinsan anyi mata miji wallahi na haƙura babu damuwa , banaso tazo ta shiga damuwa .......

Haɗe rai Ammi tayi tace,"to Alhaji in Banda abunka shin dani zaka yarda ko da ita , inji dai nice mahaifiyarta , kuma Ni nace na baka ita halak malak kaji ko ?

Cikeda jin daɗi Alhaji tanim yace," okay to shikenan Nagode sossai , Allah ya ƙara girma ,Ni zan tafi , gobe inshallahu zan dawo sai a kwatanta mun gidan kawun nata inje in sameshi sai muyi magana Nagode sossai yafaɗa gamida ƙoƙarin tashi ya fara ƙokàrin fita ,ya ɗauki kuɗi a aljihunshi , dubu ɗari biyar ya miƙa mata yace," ga wannan Ammi a siya goro ba yawa .......

Ganin kuɗi yasa Ammi zaro ido tace," Alhaji duka wannan ? Murmishi yayi yace,"Ah haba mama ba komai wallahi , ai kinfi ƙarfin haka a gurina.......

Duƙawa Ammi tayi tana ta godiya cike da farin ciki, tace,"barin in kira wo maka Hamdiyyah , cewar Ammi jikinta na rawa......

Fita yayi ya tsaya a jikin motarshi , gamida sakin wani shu'umin murmishin da shi kaɗai yasan abun da yake nufi......

Bayan fitar Ammi ta shiga ɗakin Hamdiyyah cikin sauri tace, ke maza maza tashi ki fita ki rakashi yana waje a ƙofar gida yana jiranki.......

Tsabar takaici da baƙin ciki yasa Hamdiyya ta kasa ma Ammi magana sai ido data ƙura mata wasu hawaye Masu zafi suna fita a fuskarta .......

Wai dan ubanki Ni ba magana nake miki ba ne, Zaki tashi ki fita ko sai na wanka miki mari?

Ba musu Hamdiyya ta tashi ta ɗauki hijabinta ta fita.....

Murna Ammi ta dingayi harda ɗan rawar ta da waƙa tana faɗin, Alhamdulillah , Alhamdulillah , Allah ya kashe ya bamu , kai kai , Allah Nagode maka burina zai cika , Hamdiyyah zata samu gidan daula , harnima na zama hajiya waiyyo Allah ,murna ta dingayi sossai tanayi tana ƙirga kuɗin......

Koda Hamdiyyah ta fita sallama kawai tayi tana harararshi ......

Buɗe baki yayi zaiyi magana , Hamdiyyah tayi saurin dakatar dashi ta hanyar faɗin," naji komai basai kace komai ba , Amma kasani tunda Ammi ta faɗa maka haka har ka yarda to kasani bana sanka bana ƙaunarka kuma wallahi bazan taɓa sonka ba , gara ma tun wuri ka je ka janye kace ka haƙura dani , in ba haka ba zakayi da nasani , ina da ace kana da niyyar taimako na ai da bazaka yarda da kuɗirin Ammi ba ai , nuna shi da yatsa tayi taci gaba da faɗin,"kasani in kasiya mahaifiyata da kudi , to Ni bazaka siyeni ba domin in zaka ɗauki duk duniyar nan ka bani wallahi bazan taɓa sonka ba , taƙarashe maganar gamida galla masa wata harara ......

Duk da maganganun ta da ta faɗa mishi ya taɓa shi hakan bai sa ya nuna ba sai dannewa da yayi ta hanyar yin dariya yace," shikenan ,kingama?

Harara ta gallamishi tace," oho bansani ba.....

Numfasawa yayi yace," Amma Hamdiyyah Yakamata ace kin fahimci gaskiya , ai ni ba da maganar aurenki najema da mahaifiyarki ba , faɗa mata gaskiyar abun da ke raina nayi , hasali ma ita ta musaki tace babu wani wanda kuke tare dashi , to Kinga da maganar wa zanyarda a cikinku, Kinga ai ita tace mun baki da wani tsayyaiyye , hakan yasa nikuma na shigar da buƙata ta na auranki, saboda haka ki taimaka ki amince da soyaiyya ta kinji , yafaɗa cikin sigar tausayi .......

Wata uwar harara ta galla mishi ta ja uban tsaki tace," sai kayi ai da Alama kai daƙiƙi ne kai ,baka iya fahimta , ta ƙarasa maganar gamida jan uban tsaki ta shiga cikin gidan.......

Wani shu'umin murmishi yayi yace," yarinya duk ki gama na ɗan lokaci kaɗan ne muje zuwa,yafaɗa gamida buɗe motarshi ya shiga yaja motarshi ,bai zarce ko ina sai gidan hutawanshi , bayan ya biya ya ɗauki karuwai biyu......

Bayan hibba ta shiga gida , nan Ammi tace," ke miye kike ta haɗe rai , fatan baki ɓata mishi rai ba ko?

Kuka Hamdiyyah ta fashe dashi ta tsugunna a ƙasa cikeda da magiya tace," Ammi dan Allah ki fahimce ni wallahi banasan mutumin bana ƙaunarahi ko kaɗan, Kar azo ana dana sani akan wannan auren ,Ammi dan Allah ki taimakemu karkimun auren dole kinji......

Kallon Hamdiyyah Ammi takeyi ta ƙura mata ido Ammi tace," ɗago ki kalleni , babu musu Hamdiyya ta ɗago kai ta kalleta.....

Cikin mai da hankali Ammi tace," wallahi tallahi ki saurareni da kyau kiji maganar da zan faɗa miki babu wasa ko ƙarya a cikinta , ina dai ni na haife ki na ci kashi ki na ci fitsarinki ,sannan kuma na cigaba da kula dake duk da kasancewarki marainiya ko, to bari kiji matuƙar baki amince da wannan auren ba ,to kisani a matsayina na wacce na tsugunna na haifeki to wallahi sai na tsine miki , kuma nono na da kika sha Allah ya isa ban yafe ba ......

Jin kalaman Ammi yasa Hamdiyya ta ɗago rinannun idon ta ta kalleta , kukan da takeyi ta tsagaita shi , wani tashin hankali ta shiga ciki , kasa magana tayi tana ƙoƙarin tattaro nutsuwarta .....

Tashi Ammi tayi ta fita cikin tsantsan ɓaci rai.....

Wani gigitaccen kuka Hamdiyyah ta fashe dashi mai matuƙar tausayi da tashin hankali a ciki ......

Cikin muryar kuka Hamdiyyah ta fara faɗin," waiyyo Allah nashiga uku , meyasa ,meyasa meyasa na fita ƙofar gida har wanan ƙaddara ta sameni , ya akayi har ya ganni, Allah ka kawomun mafita , in Ammi na ta yi fushi dani nashiga uku na lalace .....

Kuka ta ɗan tsagaita ta share haway e ta , gamida miƙewa ta nufi ɗakin Ammi ......

Da sallama tashi ga,Amma Ammi taƙi kulata ......
Dadai gabanta Hamdiyyah tazo ta tsugunna tace," Ammi kiyi haƙuri dan Allah karkiyi fushi dani ,fushi ki zai iya jefa ni cikin tashin hankali, ni nayarda na Amince zan aureshi , matuƙar hakan zai saki farin ciki, na yarda na amince da shi , taƙarasa gamida fashewa da kuka gwanin ban tausayi ......

Murmishin Ammi tayi ta washare baki tace," yauwa Hamdiyyatuna to ko kefa ,ai garama da kika amince ɗin , ai da tun farko kin amince da baza'akai ga haka ba , Amma tunda yanzu kin Amince shikenan , Allah yayi miki Albarka kinji ko ,maza ki daina kuka haka .....

Shuru tayi batare da tace komai ba , ta tashi ta fita, ta shiga ɗakinta, tana shiga taƙara fashewa da wani matsanancin kuka , tana me tunani iri_iri cikin ranta , musamman soyaiyyarta da Faisal, Haƙiƙa in ta tuna Faisal tana ji kamar ta bar duniyar ma ko zata huta , da wannan tunanin har barcin wahala yayi awun gaba da ita ..........


Ba laifi jikin hibba yafara yin sauƙi sai dai komai ƙarfin hali takeyi dan babu yanda zata yi ne , amma yanda take ciwon nan kamata yayi ace ta huta sossai , amma sai dai ba hali......


Washe gari misalin ƙarfe huɗu na yamma Alhaji tanim gamji ya zo gidansu Hamdiyyah.....

Fitowa tayi cikin sakin fuska ta gaisheshi , cikin fara'a duk da cewa cikin zuciyarta na cikin baƙin ciki , amma tayi ƙoƙarin dannewa gudun saɓa alƙawarin da tayi ma mahaifiyarta ........

Da murmishi ya amsa , yana me mamakin sauyawanta , kasa barin abun yayi a ciki ranshi yace," Amma Hamdiyyah ya naga kin sauya yau ɗinan ko meyasa?

Na amince da auranka tafaɗa a taƙaice , cikin ranshi yake faɗin," shegiya dan ubanki ba dole ma ki amince ba inda nine , saɓanin a zahiri yace," wow Alhamdulillah ,gaskiya naji daɗi sossai Nagode ƙwarai da soyaiyyarki a gareni , murmishin yaƙe tayi daga bisani yadinga janta da hira ,ita sai dai tace," ehh ko a'a maganar ta kenan ,domin tasawa ranta bazata taɓa sakin jiki da shi ba.......

Da haka bayan ya gaji dan kanshi yayi mata sallama ya tafi itama ta shiga gida ..........

*MUJE ZUWA*

*ZAKU IYA FARA BIYAN KUƊIN KU DAN NASAKA KU A PAID GROUP*

*DA NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁATA AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386347*

*COMMENTS*
*&*
*SHARE*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*
*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 19 &20*

*ENDING OF FREE PAGES*

*Wannan page ɗin shine ƙarshen free page, zaku iya tuntuɓata akan lambar waya kamar haka ,09066386347 ku tuntuntuɓeni dan ci gaba da karatun littafin guguwar Annoba,*


A gurguje,Abubuwa da dama sun faru , ciki kuwa harda sauyawar Hamdiyyah , duk ta danganawa Allah lamuranta , duk da tasa damuwa matuƙa a ranta , domin duk ta rame ta lalace, ganinta a hakan bai sa Ammi ta damu ba , ko zata janye ƙudirinta , acewarta in ta aureshi komai zaiyyi daidai in tafara ɗanɗanan daɗin daula......

Cikin haka ne aka fara maganar auren Hamdiyyah, inda Ammi ta mishi jagora wajan zuwa gidan kawun Hamdiyyah dan fara maganar aure .......

A satin da ya wuce ne Alhaji tanim gamji ya nufi gidan kawun hamdiyyah , inda kawunta ya shaida mishi cewar zaiyyi magana da mahaifiyar Hamdiyyah in sun gama magana zai neme shi , da haka sukayi sallama.........

Bayan Alhaji tanim ya ɗauki kuɗi mai yawa ya bashi , inda kawun hamdiyyah ya ƙi karɓa , kasancewar shi ba mai son abun duniya bane......

Batare da nuna damuwa ba Alhaji tanim gamji ya tafi cikin ranshi yana me faɗin," koma dai menene kai kasani , dama ban damu ka karɓa ba aure ne dai bazaka hanani ba duk bala'in da za'ayi , da haka ya fita yaja motarshi ya tafi .......

Washe gari kawun Hamdiyya ya kira mahaifiyar Hamdiyyah da Hamdiyyah ......

Batare da ɓata lokaci ba suka zo dukkansu .....

Bayan sun zauna sun huta

Please Login or Register in order to submit comment