Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, ya ɗauki jini ya kaima Azarfakinzu .......

Ba tare da ɓata lokaci ba Azarfakinzu ya karɓi jinin , ganin jini yasa Azarfakinzu faɗin," to babu tabbas ko jinin zaiyyi aikin da mukeso , har in baiyyi ba , to dole mu sake nemo wata mafita, kuma dole ka aikata abin da mukace......

Sossai hankalin Alhaji tanim ya tashi matuƙa , cikin tsananin tsoro da fargaba yace,"Azarfakinzu badamuwa ko me kace a shirye nake da duk abun da kace a aiwatar .........

Nan Azarfakinzu ya shaida mishi cewa duk yanda ake ciki zai faɗa mishi bayan kwana biyu .........


Washe gari da safe, Ammi ce zaune cikin ɗakin Asibitin ta rafka uban tugumi , Abubuwa da dama sun taru sun yi mata yawa , ta ɓangare ɗaya na zuciyarta fal take da tunanin halin da Hamdiyyah take ciki shin ko a mace ko a raye Allah masani , ta wani ɓangare kuma tana matuƙar tausayama yaran , domin har yanzu basu farfaɗo ba, dukkanninsu ,hakika Lallai suna jinjiki sossai ........

Washe gari da safe Inna furairah ce zaune , tana son taga Hamdiyyah tayi barci , amma sam barci yaƙi zuwa mata , tsabar ɗoki da zumunɗin zuwa gida, domin inna furairah na so tayi barci .........

Ganin har yanzu Hamdiyyah batayi barci ba yasa inna furairah zuwa gurin Hamdiyyah gamida shafata haɗe da maganganun kwantar da hankali, nan take wani dadaɗɗan barci yayi awun gaba da ita, cikin ƙanƙanin lokaci ........

Ganin tayi barci yasa Inna furairah saurin kiran harɗo cikin harshen su irin na Aljanu, nan harɗo yayi mata umarnin kan cewa su tafi kawai , take Inna furairah ta dafata gamida runtse ido , nan take suka ɓace ɓat a gurin .........

*Kuyi haƙuri , na rashin update Kullum , wallahi abubuwa ne sai a hankali , ni kaina ina o nayi nagama na huta na fara sabo , abubuwan ne sai a hankali*

*Muje zuwa*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 45 & 46*

*Kuyi haƙuri rashin jina kwana biyu wallahi tallahi bukukuwa ne suka sani a gaba , kwata kwata bana zama ,kumun uzuri dan Allah , ga matsanancin ciwon kai , yau ɗin ma daurewa nayi zan muku kuyi haƙuri .........*

Washe gari farkawa Hamdiyyah kawai tayi ta ganta a daidai bakin layin su ...........
Sossai tayi mamakin ganin haka, dube_dube tafarayi ta ko ina ko zata ga inna furairah , amma sam babu ita babu kamarta .......

Sossai kan Hamdiyyah ya kulle tana me cike da mamaki matuƙa , jikinta na rawa ta fara ƙoƙarin tafiya , zuciyar ta cike take fal da tunanin abun da zata tarar a cikin gidansu........

Kalle_kalle take ko ta ina tana ganin unguwa duk ta canza mata , tazama kamar wata doluwa ,domin kanta ya matuƙar ɗaurewa......

Tunanin su Hibba ne ya shigeta ta tana tunani a halin da suke ciki ........

Kai tsaye cikin layin ta shiga ,domin a cewar ta in taje taga Ammi zata koma gidan su Hibba taga halin dasu ke ciki , dan jinsu take tamkar yaran ta da ta haifa da cikinta , ko ƙannenta ciki ɗaya ........

Ga mamaki ta tsaya daidai ƙofar gidan , ganin gidan maƙale da tsohon kwaɗo yasa Hamdiyyah tsaya turus tana kallon mamaki , juya_juye ta farayi ko zata ganta .......

Neman guri tayi ta zauna a dakalin gidansu , ta rafka uban tagumi abubuwa duk sun taro sunyi mata yawa a ƙwaƙwalwa , wasu hawaye Masu zafi ne suka gangaro a fuskarta , cikin ranta take faɗin," wannan wacce irin jarabawar rayuwace, wani irin kaddara ce wannan, haƙika ita kam taga rayuwa , sossai kuka ya kuɓce mata , tana mai tsanani tausayin kanta .........

Takai a ƙalla Awa ɗaya tana zaune ,tana tunani iri_iri cikin ranta , har barci yafara barazanar ɗaukar ta .........


Ammi ce zaune ta rafka uban tagumi tana kallon su Hibba da mufeeda da Nihal , hawayene suka zuba a idonta tausayin yaran duk ya cika mata rai , gashi ta ɓangare ɗaya kuma tausayin halin da Hamdiyyah take ciki ne fal a ranta ........

A hankali Hibba tafara ɓude idonta .......

Wani nauyi taji kanta yayi mata , dusu_dusu tafara gani, ɗakin na juya mata .......

Hannu ta takai ta dafe kanta dashi , jikinta yayi mata wani irin nauyi , daidai da dan yatsanta ma ciwo yakeyi mata, ta kasa ɗagawa, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata a gefen idonta........

Sa sauri Ammi ta nufi gurinta , ta zauna ta gefen gadon ta matso kusa da ita , gamida dafe kanta tace," Sannu ko ? Kin farka .........

Da kallo Hibba take bin Ammi ,duk da dusu_dusun da take gani .......

hannun ta Ammi takai kan Hibba ta ɗan dafa mata kanta , taji yayi zafi kamar wuta ......

Sannu Ammi tafara yi mata.......

Duk yanda Hibba taso yin magana kasawa tayi ,kasancewar nauyin da bakinta yayi mata......

Da kallo take bin Ammi dashi , ita kuma Ammi ta kalleta tace," ki kwantar da hankalinki kinji , sannu ko , itadai Hibba hawaye ne kawai suke fita a idonta ..........

Da sallama baba mariya tashiga ɗakin Asibitin , wato Matar Mallam Musa kenan, da murmishi Ammi ta tarbe ta tace," sannu da zuwa mariya, murmishi baba mariya tayi tace," yauwa sannu Ramatu , nan suka gaisa , Baba mariya ta tambayeta masu jiki , Ammi ta amsa da sauƙi..........

Shuru ne ya biyo baya, bayan baba mariya ta dudduba jikinsu, dukkaninsu da suke ta sharar barcin Azaba saɓanin Hibba da take kallonsu kamar mutum mutumi.........

Shuru ne ya biyo baya kafin daga bisani Ammi tace," yauwa mariya dan Allah ko zaki ɗan zauna dasu ne na je gida naɗan watsa ruwa nadawo , banyi wanka ba wallahi .......

Da murmishi baba mariya tace," to shikenan babu damuwa Ramatu jekiyi wanka ki dawo , ina na , dama shi Mallam ɗin cewa yayi ko yau na kwana ke ki huta a guda , shine kuma naga kwana idan na kwana a nan babu me Kula da su Ajamal ɗin ,shiyasa ko ya kike gani ?

A babu komai barinyi wankan nadawo kawai , indan nayi wankan za dawo zan kwana babu damuwa ,ke kije gidan tunda ga sauran yaran,Ammi tafaɗa cikin sakin fuska , to shikenan ba damuwa sai kin dawo ,baba mariya tafaɗa .......

Tashi Ammi tayi ta fita gamida da yima baba mariya sallama , ta tafi ..........

Zaune take tana ta sharar barcinta ta jingina da bango , daidai lokacin Ammi ta ƙaraso bakin layin .......

Hango mace zaune a daidai dakalin ƙofar gidansu tayi, ga mamaki take kallon gurin gamida faɗin," wacece wannan kuma????

Ganin Bata da amsar yasa tayi saurin nufan gurin dan ganin ko wacece ........

Ga mamaki Hamdiyyah tagani zaune tana ta sharar barcinta hankali kwance ........

Mutssika idanuwanta Ammi tayi ko sune basu gwada mata dai_dai ba , cikin tsananin damuwa ta tashin hankali da mamaki Ammi ta ƙara buɗe idonta , taga ehh tabbas Hamdiyyah ce .........

Kai tsaye gurinta ta nufa , ta ɗan taɓata a tunaninta ko fatalwa ce .......

Ganin har ta taɓata yasa ta tabbatar da cewar eh haƙiƙa Hamdiyyah ce ........

Tashinta tayi tace," Hamdiyyah!! Hamdiyyah!!! Firgit Hamdiyyah ta buɗe ido , ta sauƙe su akan Amminta da take tsaye a gabanta ..........

Da sauri Hamdiyyah ta miƙe ta rungume Ammi, wani kuka mai tsuma zuciyar masu saurararo , ya kuɓuce mata........

Itama Ammi kuka tafarayi gamida faɗin," Hamdiyyah !!! Hamdiyyah!!! ina kika je ? Ina kika tafi ? Mun nemeki mun rasa Hamdiyyah ........

Cikin muryar kuka Hamdiyyah tace," Ammi bansani ba , bansan inda nake ba, Nima kawai na tsinceni a wani irin gurine .........

Juyawa Anmi tayi taga mutane sun ɗan fara taruwa a gurin , hannun ta ta kama tace uhm mushiga guda , idanuwan mutane sun fara dawowa kan mu , nan Ammi ta curo ɗan mukulin taa gefen zaninta ta buɗe gidan suka shiga ciki da Hamdiyyah , kowa ya watse ..........

Ko da suka shiga cikin gidan , kuka Ammi ta cigaba dayi tace," Hamdiyyah bamu ga tazama ba , kinsan miye maza tashi mutafi gidan Mallam Musa kawai , domin ni yanzu na sallama mishi komai wallahi , na bar mishi komai a hannunshi ..........

Cikeda damuwa Hamdiyyah tace," Ammi wallahi tallahi ko da ace zan rasa rayuwata yau dinan sai na je naga halin da su Hibba suke ciki, Ammi ina kaunar su ina kaunar su Hibba , nayi kewarsu , Ni so nake naje na gansu da idonsa , naji daɗi a rayuwata,In har ban gansu ba bazan taɓa samun nutsuwa ba wallahi , dan Allah ki kaini na nagansu kinji Ammi .......

Shuru Ammi tayi cike da jimamin ta yanda zata fara faɗa ma Hamdiyyah halin da ake ciki ,kafin daga bisani tace,"Hamdiyyah ki kwantar da hankalinki , yanzu nasan yunwa kikeji , barin fita na Nemo yaro a waje ya siyo miki ko dan_wake ne kici ko ?

Hawaye ne suka fara fita daga idanuwan ta tace," Ammi ki fahimta , na faɗa miki bazan iya komai ba in banga su Hibba ba , dan Allah ki tamaka ki Kaini na gansu kinji .........

Shuru Ammi tayi hawaye Masu zafi suka fara fita daga idonta , gamida sunkuyar da kanta ƙasa tana tunanin ta inda zata fara faɗama Hamdiyyah halin da su Hibba suke ciki .........

Ganin halin da Ammi take ciki yasa Hankalin Hamdiyyah tashi matuƙa tace," Ammi lafiya kuwa menene?? Me yafaru Kuma kike kuka ,akwai damuwa ne?????

Shuru Ammi tayi kafin daga bisani tace," Hamdiyyah tunda kin dage barin faɗa miki halin da ake ciki kawai , da sauri Hamdiyyah ta tari numfashinta ta hanyar faɗin," Ammi meke faruwa dasu me yasa mesu,kinsamu labarinsu ne??

Numfasa Ammi tayi kafin daga bisani ta ɗago ta kalli Hamdiyyah tace," Hamdiyyah yaran suna Asibiti........

Zaro ido Hamdiyyah tayi kafin daga bisani tace," Asibiti kuma Ammi!!, meyasa mesu ????

Hmmmm Hamdiyyah mahaifinsu ne yayi musu fyade gaba ki ɗayan su.......

Take Hamdiyyah tasa ihu tace fyade Ammi!!!!

Take tunanin ranar daren farkon su ta Alhaji tanim ya faɗo mata a rai , tunawa da Azabar da tasha tayi , hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya tace," Ammi Babansu shi yayi musu fyaɗe ?????

Ehh Ammi tabbata amsa jiki a sanyaye tacigaba da fadin," ai har Ihlam ma tarasu .......

Wani ihu Hamdiyyah tasa tace," Ilhama ta rasu , nan take ta zube a ƙasa ta fadi sumammiya........

Kuka Ammi ta fashe dashi tafara jijjiga ta tana faɗin," Hamdiyyah !!! Hamdiyyah!!! Ki tashi na shiga uku na , da sauri ta tashi ta mike jikinta na rawa ta ɗebo ruwa a buta ta yaiyyafa mata a fuska .........

Take taja wani dogon numfashi haɗe da ajiyar zuciya tafara ɓude idonta a hankali ta sauƙesu akan Ammi , da take tsaye a kanta ........

Ɗagota Ammi tayi tace,"Hamdiyyah sannu ko??

*Muje zuwa*

*Muhadu a next page*


*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 47 & 48*

"Bayan ta ɓude idon ne ta fashe da matsanancin kuka mai matuƙar tausayi da tsuma zuciya .........

Cikin muryar kuka haɗe da tashin hankali da kiɗimewa Hamdiyyah itace,"Ammii dan Allah kice abun da kika faɗa ba gaskiya bane , Ammi dagaske Ihamana ta rasu , yanzu bazan sake ganinta ba , bazan sake sanyata a idanuwanaba?? me suka mishi zai musu irin wannan aika_aika , wannan wanii irin Azzalumin mutum ne maras Imani, kuka sossai Hamdiyyah take mai cin rai da tausayawa .........

"Itama Ammin kuka tafara yi gamida faɗin," kiyi Shuru Hamdiyyah ki ƙaddara lokaci ta ne yayi , ita kam ma ai ta huta , tunda bata ɗauki zunubin kowa ba, Addu'a Kawai zaku biya dashi ko ..........

" Cikin kuka Hamdiyyah tafa girgiza kanta gamida faɗin," Ammi, Ammi dole inyi kuka , dole nayi kuka Ammi , bazan ɓoye miki ba , a lokacin da kikace anyi musu fyaɗe , a lokacin ne na tuno da dare na farko a gidan, Ammi har ɗinki sai da akayimun nasha wahala bansan inda kaina yake ba , Ammi nasha wahala Ni karan kaina , na ji jiki , Ammi wannan Azabar na tuna da har tasa nake cikin ruɗani da tsananin tausaya ma yarannan , Ni karan kaina bala'in Azaba nasha ballan tana kuma su Hibba musamman ma Ilhama , kai *innalillahi wa'inna illaihir raju'un* Hamdiyyah ta faɗa ta sake fashewa da wani irin kuka mai matuƙar tausayi da takai ci haɗe da tashin hankali.........

" Kuka sossai Hamdiyyah take haɗe da hawaye da majina , cikin lokaci ƙanƙani fuskarta ta canza tayi jajawur, idanuwanta ma suka kaɗa suka jajir kuka , take ba ɗan kaɗan ba .........

"Duk yanda Ammi taso rarrashinta ta kasa , domin Hamdiyyah tayi kukan da ko mahaifiyar ta ce ta mutu iyakaci kenan........

" Ganin bata da niyyar yin Shuru ne yasa Ammi ta haƙura tadaina rarrashinta ........

"A gigice Hamdiyyah ta miƙe ta dauki hijabinta ta miyar dashi , ta mike , ga mamaki Ammi take kallonta cikin rashin fahimta tace," ina zakije kuma ???

" Cikin kuka tace," Ammi tashi ,Ammi tashi mu tafi muje ki Kaini naga su Hibba dan Allah tafaɗa cikeda tausayawa da matsananciyar damuwa .........

Zaunar da ita Ammi tayi gamida faɗin," haba Hamdiyyah kiyi haƙuri mana ki kwantar da hankalin ki ,yanzu ki bari in nemo yaro ya siyo miki abinci kici ,nima inyi wanka kinga yanzu daga Asibitin nake fa wanka nadawo yi , kiyi haƙuri nayi wankan tunkunna sai mu je kinji ko ?

"Ammi !!Ammi!! bazan iya ba wallahi bazan iya cin komai ba wallahi matuƙar banga yaranan ba , dan Allah Ammi kitaso mu tafi dan Allah ........

"Cikin faɗa Ammi tace," wai ke meyasa kike haka ne? Nace miki zamuje zamuje , wanka nadawo yi fa , kiyi haƙuri mana , haba kinfiye taurin kai wallahi , na ce miki ki kwantar da hankalinka yanzun kici abinci nayi wanka mutafi kinƙi ,ni dai wallahi bazan koma ba sai nayi wanka .........

"Badan Hamdiyyah taso ba tace," to shikenan Ammi nayarda , ki je kiyi wankan sai mu tafi Amma wallahi bazan iya cin abinci ba kiyi haƙuri .......

" Tsaki Ammi taja tace," to tunda bazaki ci abinci ba sai kijirani nayi waka ai mutafi , kuma kinsan ruwan wankan ma sai na daura tukunna ko??........

Kai Ammi dan Allah ki kawo naje na siyo miki kawai tsayawa dafawa ma ɓata lokaci ne wallahi , Hamdiyyah ta faɗa cikin ɓacin rai.......

Zaro ido Ammi tayi tace," kije ina?? Lallai bakida hankali , amfaɗamiki yanzu ni zan sake barin ki ki fita ne , wallahi baza kije ki siyo wani ruwan wanka ba Ah to ........

Haɗe rai Hamdiyyah tayi gamida faɗin," kai Ammi to miye dan Allah dan na fitan????

Uhm barin leƙa in dubo yaro in aikeshi ya siyo to kawai sai nayi na watsa mutafi , Ammi tafaɗa badan ranta yaso ba , cikin ƙaguwa Hamdiyyah tace,"to shikenan Ammi .......

Cikin ƙankanin lokaci Ammi ta aika akayi siyo mata ruwan wanka tayi sauri tashiga wankan......

" Sossai Hamdiyyah take Azazzalarta akan suyi su tafi , cikin sauri Ammi ta shirya suka tashi suka tafi cikin ƙaguwa da son ganin halin da su Hibba suke ciki, Hamdiyyah ji take kamar tayi tsuntsuwa ta tashi sama dan ta gansu ........

" Cikin mintuna ishirin suka iso asibitin, ko da suka iso Asibitin gaban Hamdiyyah ne ya fara faɗuwa , tana me tsoro da fargabar halin da zataje ta tarar da su Hibba ........

Tsayawa tayi tayi turus a ƙofar asibitin,ganin ta tsaya yasa Ammi yi mata kallon rashin fahimta tace," Hamdiyyah ya kika tsaya mu shiga ciki mana ........

"Hawaye Masu zafi ne suka fara fita daga idonta cikin kuka tafara faɗin," Ammi ina fargabar shiga ne ,ina tausayin halin da zan shiga naga yaranan......

Lallaɓata Ammi tayi gamida nunar mata cewar babu komai ta dai musu fatan samun sauki kawai haɗe da Addu'a cikin ranta , haka kuwa akayi Hamdiyyah ta danne zuciyarta ta shiga amma gabanta na ta faɗuwa.........

Kai tsaye ɗakin da su Hibba suke suka shiga......

"Zaune baba mariya take tana lazimi, da sallama suka shiga , nan baba mariya ta tashi ganin Hamdiyyah yasata figita haɗe da mamaki......

"Da sauri Hamdiyyah ta ƙarasa gadon Nihal da take ta sharar barcin Azaba kasancewar Allurar da akayi musu tana da ƙarfi sossai , ganin halin da Nihal take ciki yasa Hamdiyyah ta fashe da matsanancin kuka tana taɓata cike da tausayi, ba tare da ta kula baba mariya ba........

"Haka ta nufi gaɗon mufeeda ,ta ganta kwance tana barci haɗe da ɗan numfarfashi ........

Nan Ta dawo ta nufi gaɗon Hibba , tafara girgiza kanta , ta tabbatar da abun da Ammi take faɗa mata , sossai take kuka kamar ranta zai fita , duk yanda baba mariya da Ammi suka so rarrashinta sam abun yaƙi , sai da tayi mai isarta kafin dan Kanta tayi shiru ..........

"Neman guri tayi ta gefen gadon Hibba ta zauna ta rafka uban tagumi , tunani iri_iri take yi cikin ranta ..........

Bayan ƴan mintuna kaɗan Hibba ta sake farkawa, a hankali ta buɗe idonta , da sauri Hamdiyyah ta kalleta , Hibba ta buɗe idanuwanta ta sauƙesu akan Hamdiyyah........

"Ganin ta bude idonta yasa Hamdiyyah rike mata hannu , wasu hawaye suka zubo daga idonta , suka sauƙa a kan hannun Hibba........

"Wani irin kallo Hibba take bin Hamdiyyah dashi, a tunaninta gizo Hamdiyyah take yi mata , lura da kallon da Hibbn takeyi ma Hamdiyyah ne yasa Hamdiyyah shafa hannu Hibba gamida sakar mata da murmushin yaƙe tace," Hibba nice , Hibba nasan kina tunani ko gizo nake miki ko ? To ba gizo nake miki ba Hibba nice Anti Hamdiyyanki na dawo gareku kunji taƙarasa maganar gamida fashewa da matsanancin kuka .........

" Ƙoƙarin miƙewa Hibba tayi amma sam ta kasa , sai wasu hawaye masu zafi ne suka zobo mata ta gefen idonta ........

"A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe bakinta tana son yin magana , daƙyar ta ƙarfin hali ta ce," Anti......

Murmishi Hamdiyyah tayi tace," ki kwanta kinji kar ki tashi ki kwantar da hankalinki ina tare dake kinji Hibba na .........

Su dai baba mariya da Ammi tsaye sukayi kamar Mutum mutumin suna kallon ikon Allah tsakannin Hibba da Hamdiyyah , lallai sun sake tabbatar da cewar shakuwarsu ba ɗan kaɗan bane, haka yasa su mamaki matuƙa .......

Nan Ammi ta labartama baba mariya duk yanda akayi tsakaninta da Hamdiyyah , sossai baba mariya ta yi mamaki.........

Lalubo wayar ta tayi ta daliling lambar Mallam Musa ta faɗa mishi duk halin da ake ciki , sossai Mallam Musa yayi mamaki yankuma yi ma Allah godiya matuƙa da ya baiyyana musu ƴar tasu.........

Cikin sauri da zumuɗi yashaida musu cewar yana zuwa daga bisani ya kashe wayar .......

Cikin ƴan mintuna ƙalilan Mallam Musa yazo Asibitin........

Sossai shima yayi mamaki ganin Hamdiyyah, ganin halin damuwar da take ciki ne yasa bai yi ma Hamdiyyah ko wace irin tambaya ba , yabari sai ta dan nutsu tukunna, bayan ya ganta ne ya dudduba lafiyar yaran daga bisani ya tafi office ɗin woman right Kasancewar suna nemanshi cikin gaggawa ........

"Da yamma baba mariya tayi musu sallama tace," zata tafi tayi ma yara girki , Hibba taso Binta dan don ganin halin da su Ajamal suke ciki , kasancewar Ammi ta faɗa mata cewa suna gun baba mariya , ganin baza ta iya tafiya ta bar su Hibba ba yasa ta fasa bin baba mariya, nan baba mariya tayi musu sallama daga bisani ta tafi , bayan ta shaida musu cewa zata aiko musu da abinci in ta koma , da haka tayi musu sallama ta tafi........

Washe gari su Nihal da mufeeda suma su ka farka , sai dai ido da suke bin kowa dashi batare da sunyi magana ba.......

" Tunda Hamdiyyah tazo Asibitin bata fita ko nan da can ba tana nan tare da su.......

"Daƙyar da ɓacin rai Ammi tasa ta ta ci abinci , badan ta so ba taɗan ci abincin amma ba sosai taci ba........

Da daddare ma haka Hamdiyyah ta kwana batare da ta runtsa ba ,inda Ammi ta dinga bata labarin duk abun da yafaru , har zuwa kawo su Hibba Asibiti .........

Sossai Hibba ta sake yin mamaki da Kuma jinjina rashin imani irin na Alhaji tanim , zuciyarta na kara ruruwar wutan tsanarshi a ranta, haɗe da sake jin tausayin su Hibba , Aɗdu'ar wulakatan ta bishi dashi haɗe da binshi da mumunan zagin da har sai da Ammi tayi mata magana ,

Please Login or Register in order to submit comment