Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaga ko da ɗan yatsan ta tayi , sai hawaye ne dake fita a gefen idonta , ƙirjinta na yimataa wani irin zafi , ga wani azaba da takeji a ƙasanta........

Tunda Alhaji tanim ya fita hibba take tsaye a jikin window take kallanshi...

Ganinshi ɗauke da trolley yasa ta mamaki matuƙa , tana me tunanin inda zai je ......

Bayan ya tafi ne ta koma ta cigaba da barcinta , kasancewar ranar Lahadi ne babu school balle ta shirya ƙannen nata su tafi school ......

Misalin ƙarfe shaɗaya Hamdiyyah ta ƙara farka daga barci wahala da yayi awun gaba da ita .....

Kwance take a kan gadon kamar mutum_ mutumin , hawayen kawai ke fita a fuskarta, ƙarfin hali tayi taɗan Jawo bargo ta rufe jikinta dashi ......

Ganin shuru_shuru bata fito ba yasa Hibba ta fara tunani ko lafiya ? bata fito ba har tayi break fast ta ajiye, ƙanne ta har sun karya suna zaune suna wasa .......

Tashi tayi ta nufi ɗakinta kai tsaye ....
Da Sallama ta shiga , sallama ta dinga yi amma shiru ba'a amsa ba , jin ba'a amsa ba yasa Hibba tunani ko tana barci ne , hakan yasa ta koma ɗakinsu, tana jiran fitowar ta .......

Ganin har ƙarfe ɗaya bata fito ba yasa Hibba ta ƙara komawa ta duba .....

Sallama ta ƙara rafkawa , amma shiru ba ta amsa ba , jin ba'a amsa ba yasa ta kutsa kanta kai tsaye cikin uwar ɗakin......

Ga mamakin Hibba ganin Hamdiyyah tayi kwance cikin jini, lulluɓe da bargo......

Tunda ta ganta Hibba ta tsorata , saurin hawa gadon tayi ta ɗan ɗagota tace," Anti ,Anti me ya sameki .....

Da kallo kawai Hamdiyyah take Binta dashi tana tunani ko wacece ita ?

Ƙara tallafo ta Hibba tayi ta ƙara faɗin," Anti ! Anti kiyi magana me ya sameki ?

Hawayen kawai ke gangaro wa a fuskar Hamdiyyah , amma babu halin magana , domin duk yanda taso yin magana ta kasa domin bakin ta yayi mata nauyi matuƙa ......

Dakyar Hamdiyyah ta iya tattaro dukkanin ƙarfin ta, ta ɗaga hannunta tayi ma Hamdiyyah nuni da wayar ta dake kan dressing mirron ɗakinta......

Nan da nan Hibba ta fahimta , cikin hanzari ta miƙe ta je kan dress mirror ɗin ta ɗauki wayar ......

Cikin ikon Allah Hibba ta miƙa mata wayar tana faɗin," gashi kiyi sauri ki nemi wanda za'a kira ......

Kasa karɓar wayar tayi , domin duk yanda taso ɗaga hannunta ta kasa .....

Ganin haka yasa Hibba ta fara daliling gurin call logs ɗin wayar.....

Last call ɗin ,suna ƙawarta ne ya bayyana , batareda da sanin me aka rubuta a gurin ba yasa Hibba tunanin kiran wayar ......

Ganin bata da zaɓi sai hakan yasa ta fara daliling number , ringing wayar ta farayi , bugu uku aka ɗauki wayar, cike da murna tace," ƙawata Amarya ganin zuwa ma ina hanya yanzunnan ......
To Hibba ta faɗa, tana faɗin haka ta kashe wayar , gamida tashi tayi saurin fita gurin gare din dan jiran isowar ta .....

Misalin ƙarfe ɗaya da rabi ƙawar Hamdiyyah ta ƙara so ......

Knocking ɗin ƙofar tafara .....
Ganin ƙofar a rufe yasa Hibba tace," ina zuwa gamida yin sauri ta koma ta fara neman extra key ɗin gidan, kasancewar Babansa ya kulle su ta waje ......

Ganinshi tayi a can ƙasan akwatin Kuɗinsu , ɗauka tayi da saurin jikinta na rawa ,tayi sauri ta koma ta fara ƙoƙarin buɗe gate ɗin .....

Jikinta na rawa tace," sannu da zuwa muje na nuna miki ɗakin Antin.....
Ganin Hibba a rikice yasa zulaiha zaro ido tace," yarinya lafiya kuwa ? na ganki a rikice ina Hamdiyyah ?
Bakinta na rawa tace," tana cikin ɗaki muje , da sauri zulaiha tabi bayanta dan zuwa....

Ɗakinta suka nufa kai tsaye , ganin Hamdiyyah cikin jini yasa zulaiha tsorabta matuƙa tace,"wa iya zubillah lafiya make faruwa haka ? Hamdiyyah mai ya sameki?



Kasa magana Hamdiyyah tayi sai Binta da kallo da tayi , bargon dake jikinta ta ɗan ɗaga taga jini ya ɓata kafarta .......

Cike da tashin hankali zulaiha ta ɗauki wayar ta tafara ƙoƙarin kiran lambar Nurse halima .....

Bayan Nurse halima ta ɗauka wayar cikin sauri zulaiha tace,"Nurse Dan Allah kina asibiti ne ki kina gida?

Ina gida yau bani da duty amma lafiya?

A kiɗime Hamdiyyah tace," pls ki kijirani ina zuwa yanzun nan zan zo na ɗaukeki akwai wata ƴar ƙaramar matsala ne wallahi, okay to shikenan babu damuwa sai kinzo ina jiranki , cewar Nurse halima .....


*Muke zuwa*

*Kuyi manage da wannan pls*



*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 23 & 24*

Cikin sauri zulaiha ta je gidansu Nurse halima ....

Batare da ɓata lokaci ba Nurse halima da zulaiha suka taho tare ......

Ko da suka zo ganin halin da Hamdiyyah take ciki yasa Nurse ɗin tsorata matuƙa.....

Kallan Hibba tayi tace," ke yarinya anan gidan kike? Kaɗa kai tayi Alamar ehh , ina Babanki? Nurse ta tambayi Hibba , Shuru Hibba tayi kafin daga bisani tace," bayanan yau da safe naga ya ɗauki jakan tafiyanshi inaga yayi tafiya ne ....

Shuru Nurse tayi kafin daga bisani tace," okay to shikenan ɗan jeki ban bamu guri kaɗan kinji , to Hibba tace gamida juyawa ta fita zuciyarta cike fal da tausayin Hamdiyyah tana me mamakin abun da ya sameta ......

Zani zulaiha ta ɗauka mata daga bisani ta ɗagata suka riƙe ta suka nufi toilet da ita....

heatern bayan gida suka kunna , bayan sun kunna suka zuba mata ruwan zafin a ƙaton baf daga bisani suka ɗan ɗebo gishiri suka zuba mata a ciki ......

Wani marayan ihu Hamdiyyah tasa tana runtse idonta , duk da jikinta babu ƙarfi , Amma hakan bai hanata ƙoƙarin miƙewa ba , da sauri zulaiha da Nurse suka dannata a cikin ruwan , ihu sossai Hamdiyyah take yi tsabar azabtar da takeji ......

Sai da takai a ƙalla minti goma sha biyar a ruwan kafin suka fitar da ita a ciki , zufa sossai ta haɗa tsabar Asabar da takeji ......

Dubawa Nurse tayi taga yanda ta ɗan yage, hakan yasa Nurse ta yanke shawarar yi mata stitches wato ɗinki ......

Cikin sauri Nurse ta koma ta ɗauki duk abun buƙata , cikin ƙanƙanin lokaci ta dawo da kayan aiki ,batare da ɓata lokaci ba tafara ƙoƙarin yi mata ɗinkin .....

Haƙiƙa dan Azaba Hamdiyyah tasha Azaba dan kuwa sai da taji inama Allah zai ɗauki ranta ko zata huta ......

Cikin ƴan mintuna Nurse ta gama mata, suka samata kaya , daga bisani suka haɗa mata ruwan tea, da indomie ta ɗan ci ,sossai taci abincin duk da cewar bakinta babu daɗi domin da ƙyar take iya cin abincin,batare da ta ji daɗin shi ba ......

Bayan ta gama cin abincin sukayi sauri suka bata magani tasha , bayan tasha ne wani wahalalen barci ya ƙara awun gaba da ita ......

Bayan sun tabbatar tayi barci , nan Nurse ta kalli zulaiha tace," zulaiha!wacece wannan shuru zulaiha tayi daga bisani ta kalleta ta ɗan numfasa tace," hmm wallahi Nurse halima ƙawatace , bikita ya rage saura kwana uku takira ni tana kuka tana faɗa mun , nayi mamaki matuƙa jin yanda auren nata yazo , nan zulaiha ta kwashe ta faɗa ma Nurse duk abun dah Hamdiyyah ta faɗa mata.......

Shuru Nurse tayi hawayen tausayi na fita a idonta tace," zulaiha yarinyar nan ta bani tausayi , wallahi baƙaramun wahala tasha a daren jiya ba , Ni abun Ma mamaki yabani ya za'ayi ace miji yayi mata haka kuma ace ya tafi ya bartab a haka gaskiya baida imani kuwa , Kai wa iyazubillahi, Nurse tafaɗa gamida dafa kanta da hannunta.....

Hango Hibba a tsakar gida sukayi suna san ganin abun da zatayi , ganin ta ɗebo wanki zayati yasa su matuƙar mamaki , dukkanninsu suna mamakin yanda za'ayi ƴar yarinya ƙaramar tayi wankinann .......

Tsayawa sukayi dan ganin ikon Allah , cikin ƙanƙanin lokaci Hibba ta kammala wankin.....

Bayan tagama ne ta kirawo ƙannenta tafara ƙoƙarin musu kitso kasancewar ranar Lahadi ne , take musu kitso , tunda Monday school ....

Mamaki ne baiyyane a fuskarsu , tashi sukayi suka fita , Nurse tace," ke me sunanki ? murya a sanyaye tace," Hibba, ina mamanki zulaiha ta tambayeta.....

Shuru Hibba tayi idonta yafara kawo ƙwalla tace ," ta rasu , ɗayar mamanmu ta rasu , cikeda mamaki Nurse tace,"to ke dawa kuke zaune ? mu kaɗai Hibba ta bata amsa , numfasawa sukayi daga bisani zulaiha tace," kitso zakiyi ma ƙannena naƙi? Ehh Hibba ta bada amsa , cikeda da tausayawa zulaiha tace," kawo nayi muku kitson kinji , da murna Hibba tace," to mungode , tafaɗa gamida umarta ƙannenata akan suje ayi musu , babu musu sukaje, Nihal ta zauna aka Fara yi mata ......

Kallan Hibba Nurse ɗin tayi tace," Hibba to ke waye yake miki? ni da kaina nake kamawa , Hibba tafaɗa gwanin ba tausayi ......

Tsefe kema zatayi miki Nurse tafaɗa, da murna Hibba tace," to tafaɗa gamida cire hular kanta ta fara tsefe kitson guda huɗu da suka tsufa har ba'a ganin tsagun .....

Duba Hamdiyyah Nurse ɗin tayi ,ganin ta tashi yasa ta ɗan taɓa kanta tace," Hamdiyyah sannu? Da mamaki take kallan ta tace," yauwa , Amma yakike jin jikin naki ? da sauki Hamdiyyah ta ƙara bada amsa ......

Haƙiƙa duk wanda ya kalli Hamdiyyah yasan ta ji jiki domin tayi rama matuƙa tamkar wacce ta tashi daga doguwar jinya ......
Shuru Hamdiyyah tayi , kafin daga bisani ta kalli Nurse ɗin tace," Nagode sossai Allah saka da Alkhairi , Ameen Nurse ta faɗa gamida sakin murmishi......

Zaki iya tashi Nurse ta tambayi Hamdiyyah? Kaɗai kai Hamdiyyah tayi alamar ehh, okay ɗan tashi ki jingina akan filon kar ki gaji da kwanciyar.....

To Hamdiyyah tace gamida ƙoƙarin miƙewa, da ƙyar tana cizon leɓe ......

Misalin ƙarfe shida na Yammah zulaiha tagama musu kitso su , godiya sossai Hibbah ta yi musu......

Shirin tafiya gida suka farayi ....

Idon Hamdiyyah ne ya kawo ruwa ƙwalla fal ciki tace," zulaiha dan Allah kar ku tafi yau ma zaizo ya ƙaramin tsoro nakeji kar ku barni Ni kadai dan Allah ......

Shuru Nurse da zulaiha sukayi kafin daga bisani suce, Hamdiyyah kiyi haƙuri kinji inshallahu zamu dawo ,kuma ma ai mijin naƙi bayanan yayi tafiya fa ,ki kwantar da hankalinki kinji , to Hamdiyyah tace, murya a sanyaye Hamdiyyah tace," amm dan Allah zulaiha ki riƙe mun wannan sirrin banaso kowa yaji hatta mahaifiyata kinji dan Allah , karki faɗawa kowa , domin Alƙawarin nayi ma Kaina Babu me jin halin da nake ciki koda kuwa hakan zaiyyi sanadiyar rasa rayuwata .......

Cike da rashin fahimta zulaiha tace, Ah haba Hamdiyyah yazakice haka? yanzu haka za'a zuba ido kita zama a wahala kenan ke kin yarda da haka? ehh nayarda Hamdiyyah taɗaga kanta , Alamar ehh cikin sanyin murya , okay shikenan tunda haka kikace Allah ya taƙaita ,Allah kuma ya kiyaye na gaba mu zamu tafi sai anjima, to Nagode sossai Hamdiyyah tafaɗa ......

Tafiya sukayi suna me matuƙar tausayinta ......

Tashi Hamdiyyah tayi a daddafe tashiga toilet tayi wankan tsarki , bayan ta gama ta ɗauro alwala , da ƙyaar ta miƙe tayi salolin da ake Binta , bayan ta idar ta kwantar da kanta a jikin gadonta, tana tunanin yanayi ta a jiya , wasu hawaye Masu zafi suka sauƙa akan fuskarta , ji takeyi inama Allah zai karɓi rayuwata , domin ta tsani rayuwarta , wani kuka ta fashe dashi da ta tuna rayuwarta ta baya , dakuma hali irin na Amminta , ji takeyi ma ta tsani Ammin sai dai dan kawai mahaifiyarta ce , wani zafi taji ƙirjinta na yi mata ,zuciyarta da bakinta sunayi mata zafi , idonta na sake fitar da wasu zafafawa hawaye , tana me jin tsanar Alhaji tanim na ƙara dirar mata, lokaci ɗaya , Take soyaiyyar Faisal ta sake zama sabuwa fal cikin ranta ,murya a dashe tafara faɗin," faisal! Faisal! Ka tafi Faisal ka tafi ka barni cikin azababbiyar rayuwa , naso ace mutuwa ce ta ɗaukeni da wannan wulakantaccen rayuwa da take fuskanta........

Jin sallamar Hibba yasata saurin share hawayenta ta amsa , tashi tayi da ƙyar ta fara ƙoƙarin buɗe kofar , ganin Hibba tsaye da kular Abinci yasata mamaki matuƙa tace," Shigo mana , kai tsaye Hibba tashiga , gamida ajiye kullar Abinci tace," Anti ga Abinci na dafa mana , kici , da kallon mamaki Hamdiyyah ta bita tace," to Nagode sossai ,me ma sunanki? Hibba tace," Hibba sunana , ke kike dafa muku abinci ? Ehh Hibba ta bada amsa , mamaki sossai Hamdiyyah taji ganin yarinya ƙarama wai ita take yin girki , murmishi tayi tace," to Hibba nagode sosai , zan iya banki ɗakinku mu zauna miyi hira ?

Da murna Hibba tace," ehh Anti Dan Allah muje , tafaɗa gamida Jan hannunta suka nufi ɗakin su ..........


*Muje zuwa*

*Take note , wallahi labarin nan da gaske ya faru , ba ƙagaggen labari bane*


*Story & written by mum fu'ad*



*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 25 & 26*

Daƙyar Hamdiyyah take ɗingiwasa , kasancewar zafin da ƙasanta keyi mata ....,

Ɗakin su Hibba suka shiga , ganin Hibba da Hamdiyyah yasa ƴan uwan mamaki matuƙa suka ce," Anti Hibba kin zo mana da Antin ne?

Dariyar ƙarfin hali Hamdiyyah tayi tace,"ehh yazo muku dani ,ko ina koma ne? taƙarasa maganar cikin sigar wasa .....

A'a suka faɗa a tare , murmishi tayi daga bisani ta nemi guri ta zauna da ƙyar ta gefe a karkace ......

Murmishi Hamdiyyah tayi tace," yanzu abun da za'ayi ko wa ya faɗamun sunanshi , da sauri nihal ta buɗe baki tace," Sunana Nihal , nan kowa ya faɗa mishi sunanshi , har akazo kan Ihlam , da ɗan tsamin bakinta tace," sunana ilhaman Anti Hibba , dariya sossai Hamdiyyah tai tace," to ilhaman Anti Hibba , yanzu kin zama ilhaman anti Hamdiyyah ko?

Dariya ilham ɗin tayi daga bisani ta ɗaga kanta Alamar ehhh , dariya sukayi sossai.......

Cikin ɗan lokacin nan Hamdiyyah taji soyaiyyar yaran na ratsa ta matuƙa , kasancewar Hamdiyyah mai san yara ce , hakan yasa suka ƙara shiga ranta .......

Nan suka ci abinci tare suna ta hirar su gwanin ban sha'awa ,.....

Nan Hibba tafara ba Hamdiyyah labarin cewa mahaifiyarsu ta rasu suka kaɗai suke zama a gidan , tausayin su sossai Hamdiyyah taji gamida kudirar cewa zata zauna da su har ƙarshen rayuwarta......

Bayan sun gama cin abinci ne suka cigaba da hirar su .....

Da haka ne har barci ya fara ƙoƙarin ɗaukansu , tashi Hibba tayi ta tafara ƙoƙarin kashe wutacen, ganin Hibba ta kashe wutar gidan yasa Hamdiyya faɗin," Hibba yanaga kina kashe wutar gidan ?

Eh Anti Babanmu ne yace kullum mu dinga kashe wutar gidan ,Bama barci da wuta ya hanamu ,mamaki sossai Hamdiyyah taƙayi tace," okay to shikenan........

Ɗaga kai Hamdiyyah tayi , ganin hoto a juye yasa ta faɗin," Hibba ya kika juya hotonan ?

Hoton maman mune , Babanmu ne yace in juya wai bayason gani tana bashi tsoro, Hibba tafaɗa cikin sanyin murya ......

Cikin tsantsan mamaki Hamdiyyah tace," tsoro kuma? ehh Hibba zafaɗa , okay Hamdiyyah tace cikeda tsananin mamaki ......

Shuru ne ya biyo baya daga bisani Hamdiyyah tace," nima barin tafi in kwanta sai da safe ko? toh Hibba tafaɗa ......

Lallaɓawa Hamdiyyah tayi da ƙyar ta tafi ɗakinta , daga bisani ta kwanta a kan gadon ,bayan tasha maganin ta.......

Tunda ta kwanta take ta tunani iri_iri cikin ranta , ta ɓangare ɗaya kuma na zuciyarta tana me tsananin tsoro.....

Da haka barci ɓarawo yayi awun gaba da ita , tunda barci ya ɗauki Hamdiyyah ta kwanta take mugaye mafarkai iri_iri , firgita tayi ta tashi tsoro ya ƙara ɗarsuwa cikin ranta ,bakinta na rawa take furta *la'ilaha'illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin,* shine abun da bakinta ke furta wa , a hankali ta sake jin wani barcin na neman ɗaukar ta amma tana tsoron yi gudun kar ta sake yin wani mafarkin ......

Da haka dai wani barci ya ƙara ɗaukar ta......

Misalin ƙarfe biyar Hamdiyyah tafarka jin motsin Hibba a tsakar gida ......

Fitowa tayi a hankali ta buɗe ƙofarta , ganin Hibba na ɗiban ruwa yasata mamaki matuƙa tana faɗin," Hibba me kikeyi a nan a wannan lokacin?

Ruwan wanka zan sakama su Nihal kinsan akwai school yau , kuma in ba da wuri na tashi ba latti zasuyi , shiru Hibba tayi tana me ƙara mamakin wahalar da Hibba takeyi, cikeda tausayawa Hamdiyyah tace," barinyi sallah ina zuwa, to Hibba tace .......

Bayan Hamdiyyah ta yi Sallah ta fito , nan ta nufi gurin su Hibba ,ganin Hibba tayi tana ta firan doya, da sauri Hamdiyyah ta karɓa tace," kawo inyi firan ko , to Hibba tace cike da farin ciki......

Cikin ƙanƙanin lokaci suka gama komai , Hibba ta tashi ƙannennata tayi musu wanka , Hamdiyyah kuma na soya musu doya da ƙwai , nan danan suka gama suka shiryay, zuwa bakwai suka gama komai , Hibba ta rakasu suka tafi school......

Kafin Hibba ta dawo har Hamdiyyah tafara rage aikin gidan , gyara ɗakina nasu tafarayi ......

Ganin wani ƙaton akwati yasata sha'awar buɗe wa tace," barin buɗe nagani ko me a ciki? buɗe wa tayi , ganin maƙudan kuɗaɗɗe yasata zaro idontace," nashiga uku ji kuɗi , jin motsi da sallamar Hibba yasata saurin rufewa ta cigaba da aikin dake ganta .......

Bayan Hibba ta shiga nan Hamdiyyah tace," Amm Hibba wai miye a akwatin nan ne?

Kuɗi ne Hibba ta faɗa cikin alamar ko in kula , ta cigaba da faɗin," Babanmu ne ya ajiye mana , wai in munaso sai mu ɗeba, kuna ɗiba? Hamdiyyah tafaɗa , kaɗai kai Hibba tayi tace," A'a Bama ɗeba saboda ba abun da zamuyi dasu Bama fita ko ina shiyasa ma ba ma ɗiba bama zuwai ko ina sai school kawai da nake rakasu , bayan nan ba inda muka sani......

Tsabar ruwan mamakin da Hamdiyyah taji yasata kasa magana tace," to Allah ya kyauta ,.......

Na suka cigaba da yin aikinsu a daddafe sai Hamdiyyah take komai da ƙarfin hali har suka gama.......

Bayan sun gamma suka fara hira sossai,inda Hibba take ta faɗa mata komai na cikin gida batare da ta ɓoye mata komai ba , har halin da suke ciki da mahaifin su , sossai Hamdiyyah taƙara tausaya musu , hakan yasata ƙara ɗaukar aniyar zama dasu ko dan tausayin halin da suke ciki .......

Misalin ƙarfe shaɗaya sukafara ƙoƙarin ɗaura abincin rana .......

Haƙiƙa Hamdiyyah ta matuƙar jinjina ma ƙauzon Hibba ganin yarinya ƙaramar yan da take aiki kamar babbar mata, ita dai duk abun da suke kallan Hibba kawai Hamdiyyan take cike da mamaki .......

*ƘASAR INDIYA..........*


*DAN ALLAH KUYI MANAGE DA WANAN PLS*



*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 27 & 28*

*ƘASAR INDIYA........*

Bayan Alhaji tanim gamji ya tafi kasar ndiya, kai tsaye masuƙinshi ya nufa, Kasancewar yamai da indiya tamkar gida , babu inda bai sani a ƙasar ba ba .......


Bayan ya sauƙa ya huta ,washe gari ya

Please Login or Register in order to submit comment