Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inna furairah ba mutum bace Aljana ce?shine na zauna zauna tare da ita .......?

Ƙawarai kuwa Hamdiyyatu ba mutum bace Aljana ce shine ya ɗaukeki yakaiki gurinta , ya ajiyeki har zuwa wanan lokacin, kuma ba dan komai yayi hakan ba sai dan kyawawa ɗabi'unki da kyawawan halayen ki sune dalilin da yasa ya taimakeki , domin kuwa badan haka ba da yanzu an mata dake a babin rayuwa , da yanzu mun rasa ki , Alhaji tanim mijinki bda ya sadaukar da jininki wa ƙungiyar su , to ki godewa Allah ƙarfin Addu'armu da kuma tausayi da kyakkyawar zuciyarki sune suka ceceki.....

Nan Mallam Musa ya labarta na Hamdiyyah komai da harɗo ya faɗa musu akan Rayuwar Alhaji tanim , da kuma irin abubuwan da ya aikata ........

Tunda Mallam Musa yafara magana hawaye masu zafi ne suke fita daga cikin idon Hamdiyyah , rama rasa me zatayi , ƙwaƙwalwar ta ta gagara ɗaukan wasu maganganun , bakinta yaka iya furta komai , sai yanzu take tuna wasu abubuwa akan zamantakewan ta da Alhaji tanim , da kuma Rayuwar ta da Inna furairah , haƙiƙa ita kam taga rayuwa ,ta yarda kam Inna furairah ba mutum bace , domin dayawa wasu abubuwan ba na mutane takeba , musamman ta bangaren abincin ci , domin sai yanzu ta sake tunani in har zata dafa abinci bata taɓa fita cefane , saidai taga abincin kawai ta kawo mata , ta bangare guda kuma wanda shi ne abun da yafi ɗamunta bakomai bane illa takaici da bakin ciki da kuma danasanin haɗa jiki da Alhaji tanim da tayi , da kuma ƙyamatar shi , ƙyamar shi ce takamata sossai tana me takaici da danasanin sanin Alhaji tanim a rayuwarta, ba ma iya ɓata rayuwar yaranshi ba ita karan kanta ya cutar da ita ya ɓata mata Tata rayuwar da ta daɗe tana tattalinta , Shuru tayi tana ta tunani iri_iri , hawaye na cigaba da zubo mata , babu wanda ya ce ƙala ,babu wnada ya hanata kuka da takeyi , domin su kansu sun san cewa dole zatayi kuka ,kuma dole abun zai yi mata wani iri , tunda har tasan da irin kazamin kuma marar imanin mutumin da take tare dashi , hakika dole abun ya dameta , hakan yasa babu wanda yace mata komai sai haƙuri da suke bata da kuma maganganun kwantar da hankali, Mallam Musa ne ya ce sai dai kuma ta wani ɓangaren shiga gidan Alhaji tanim da Hamdiyyah tayi Alkhairi ne, domin ko ba komai an kuɓutar da wa'innan yaran daga halin damuwa da uƙuba da tashin hankali da suke cikin, da wannan muke ƙara godewa Allah , ya cigaba da faɗin," kuma dole muje Asibiti mu tabbatar da cewar lafiyarta kalau , kar wannan tsinannen mutumin ya saka mata wanan ciwon na zamani,Allah ya tsare nan kowa yayi na'am da zancen Mallam Musa , suka yanke shawarar gobe su tafi asibiti .......

Sai da suka tabbatar da ta daina kukan ,hankalinta ya ɗan kwanta Kafin suka fara neman hanyar da zasu bi dan raba auren ta da Alhaji tanimu gamji......

Washegari suka je Asibiti da Hamdiyyah da Mallam Musa , gwajin farko aka tabbatar mata da cewar bata da cutar kanjamau , amma duk da haka sun ɗaurata akan magunguna , saboda gudun matsala .......


Dogon na miji ne Sanye da fararen kaya , riga da wando half janfa , kanshi sanye yake da hular zanna bukar Mai kalar design ɗin rigar shi , fuskarshi sanye da farin gilashi mai matuƙar tsadar gaske , hannunshi sanye da tsadadden agogo ƙurar rolex , hannuwanshi biyu sanye da lafiyaiyyun zobuna na azurfa , ƙafarshi sanye da farin half shoes , sai ƙyalli sole ɗin takalmin yake, fuskar nan black Beauty , mai kwantaccen saje sai murmishin da ya baiyyana farin haƙorin makanshi yake sakarwa , fitowa yai daga cikin tsaddaddiyar motarshi ƙirar Camry silver Ash , cikin Takun ƙasaita ya nufi cikin gidansu ,uhmmmm tabarakallah Masha Allah shine Abun da bakina ya iya furtawa,Young Alaji, Faisal kenan , masoyin Hamdiyyah na gaskiya, shine yadawo cikin garin Jos , bayan doguwar tafiya da yayi ,wato garin Lagos , inda kawunshi yasashi akan harkokinshi, na mining , gashi kuwa cikin yardar Allah sai Allah ya sanya mishi Albarka harma yafi kawun nashi Arziƙi , Hmmm Allah kenan .......

Da murna Mahaifiyarshi ta tarbeshi ,tana me matuƙar jin daɗin ganinshi , ganin yanda ya koma young Alhaji yasata murna matuka da farin ciki .......

Hira sukayi sossai na yaushe gamo ,amma duk abun da mahaifiyar shi take tayi mishi sam ba jinta yake dan hankalin shi ba agun yake ba , so yake yayi mata maganar Hamdiyyah yaji halin da take ciki ..........

Ɗan gyaran murya yayi kafin daga bisani yace," amma nikuwa mama ya maganar Hamdiyyah kuwa , ko kina jin labarin ta ......?

Taɓe baki mahaifiyarshi tayi gamida faɗin," Hmmm labari kam ina ji , ai anyi mata aure , bayan anyi auren ashe ma wai miji nata wai dai ɗan shan jini ne , to yanzu bansan halin dai da ake ciki ba , naji ance ma tana gidan kawunta ......

Ikon Allah *Wa'iyazubillah* toh fah !!!, To Allah ya bada mafita , Ameen mahaifiyar shi tace , tunda yafaɗi haka bai sake cewa komai ba sai daki da ya shiga ya kwanta dan ya huta , tunani iri_iri ya shigayi ,barcin da yake ji sam tunani ya hanashi zuwa ,sai juyi dayake ta faman yi ..........

Bayan kwana biyu , Mallam Musa ne zaune a ɗakin Baba mariya , gyaran murya Mallam Musa yayi gamida fadin," Ni ya kike gani zamiyi ne aka Yarinyar nan , dan gaskiya bazaiyuyu a bar yarinya da dakwan aure ba , domin kema ki san ko ban faɗa ba ai aure bazai yuyu tsakanin Hamdiyyah da wannan la'anannen ba , kuma Ni bazan so tayi ta zama da aure ba , Ni babban damuwa ta in samu in San inda yaje , wallahi da ko ina ne ma sai na je gurinshi ya bata takardar ta , to rashin sani takamaime inda zan sameshi shine matsalar yaƙarasa maganar gamida jan dogon tsaki , to ko magabatan shi za' a nema ne cewar Baba mariya.....?

Wani kallo Mallam Musa yayi mata gamida jan dogon tsaki yace," mstttt kinji da wata magana a ina zamu sami magabatan nashi ,kin manta magabatan nashi na ƙaryane ????
Ai hakane Mallam wallahi shaf na manta , kai wannan mutumin akwai tsinanne matsiyaci , Allah dai ya sakama Yarinyar nan kawai , Amma inshallahu zamu samu mafita , kasamu sauran mutane kuyi magana kaɗan nemi shawarwari mugani , cikeda gamsuwa Mallam Musa ya fita gamida yi mata sallama.......

Zaune suke suna ɗan taɓa hira , mufeeda na jikin Hamdiyyah , ba laifi a kwana biyun nan jikinsu yayi sauki sossai , jikinsu yaɗanyi ƙarfi kuma , sai dai a hankali suke tafiya kasancewar har yanzu gurin bai gama warkewa ba ,kuma yanayi musu zafi gwanin ban tausayi .....

Kulawa sossai yaran suke samu gurin Mallam Musa , ta ɗayan ɓangaren kuma Human right na kawo musu ɗauki sossai , domin da zaran sun gama jin sauki duk za'a maida su makaranta su cigaba da karatunsu.......
Sossai Hamdiyyah take jan yaran a jikinta, ƙwaƙwaran tari inda ɗaya yayi toh da sauri zataje ta duba shi , kullum yaran ƙara shiga ranta suke da tsananin tausayinsu da take ji, hakan yasa take ƙara kaunarsu cikin zuciyarta ,suma kuma yaran suke tsananin ƙaunarta.......

ƙaton guda Faisal ya siya ma mahaifiyarshi , yakuma zuba mata dukkanin wani abun buƙata a cikin gida , Albarka tasa mishi sossai takuma yi mishi fatan Alhakiiri haɗe da Addu'a irin ta iyaye akan ƴaƴansu ..........

Tunda Faisal yadawo zuciyarshi da idanuwanshi suke tsananin son ganin Hamdiyyah, hankalinshi duk ya karkata gurinta, a kowanne minti sai Hamdiyyah ta faɗo mishi cikin ranshi hakan yasa yakasa sukuni , yana matuƙar muradin ganinta, sai dai kuma yana Tsoron abun da zai iya zuwa ya dawo , yana kuma tsoron zuwa amma tabbas har zuciyarshi yana matuƙar kaunar ganinta, sai dai idan ya tuna da cewar auren wani na kanta yana matuƙar jin haushi da takaici dakuma damuwa,da shiga cikin ƙunci da takaici , da kuma jin haushin dawowa da yayi , hakan yasa yafara tunanin komawa Lagos , sai dai kuma bazai taɓa iya komawa Lagos batare da ya ganta ba ,ganin bashi da wata mafita yasa ya barma Allah komai ,zai kuma ci gaba da zuba ma sarautar Allah ido yagani ...........

A ɓangaren Alhaji tanim kuwa!!zuwa yanzu yazama zaburarre , baya fita ko ina, ko ƙungiyar su baya shiga ,yama kasa kai jinin da suka umarceshi banda zabura babu abun da yakeyi , kullum cikin yi mishi gizo su Hibba sukeyi , yarasa sukuni kwata_kwata, duk ya rame ya lalace yayi bakin ƙirin , baya cin abinci , gawani irin zazzaɓi da yake damunshi , uwa uba kuma yawan gudawa da yakeyi da ciwon ciki , ganin haka ne yasa ya kira likitanshi , ko da likitan yazo duba shi gwaji daya aka tabbatar mishi da cewar yana ɗauke da cutar kanjamau wato H I V , ko da likitan ya faɗa mishi bai damu ba dan yasan hakan tabbas zai iya faruwa , zabura ya dinga yana faɗin gasu Hibba da Hamdiyyah yan nuni da bango , can kuma sai hankalinshi ya dawo jikinshi, ganin haka yasa likitann ya tabbatar da cewa ba kanshi ɗaya ba , ba shiri likitan ya tattara inashi inashi ya tafi.....


A ɓangaren kungiyar su Kuwa!! sun yanke shawarar haukata Alhaji tanim, zasu tura mishi baƙin Aljani kafin daga baya kuma su zuƙe jininshi suyi amfani dashi ..........

Washe gari Alhaji tanim ne kwance barcin wahala yayi dan yi awun gaba dashi , a razane ya farka ya tsala wani gigitacen ihu , yafara cire kayan jikinshi , yarage ba komai a jikinshi haihuwar uwarshi a tsirara , da gudu ya fito waje yana ihu yana tsikarar gashin jikinshi yana ci, cikin ƙanƙanin lokaci yajima kanshi ciwo mai munin gaske da ƙyamatarwa ......

kasana cewar ƙasar Indiya ne, babu wanda ya kula da halin da yake ciki , duk wanda ya kalleshi iya kaci ya kauda kanshi shi , hauka yake me matuƙar tsoro da ƙazanta , duk ya fita haiyyacinshi , ya rame ya lalace , matuƙar ka ganshi to zaka iya rantse wa cewar bashi bane , tun haukar nasakashi sambatu yayi ta faɗin munanan Aiyyukan da ya aikata har ya zamanto ba ya ma iya magana ,sai kallo , idonshi daya ma ya canka mishi tsinke a ciki ya tsiyaye , sai da guda ɗaya yake gani .........

Masu kaman mahaukatane na kasar suka kamashi suka tafi dashi, ko da suka tafi dashi kai tsaye sukayi bincike aka gane cewa ba dan kasar bane , babu shiri suka nemi kaya suka sa mishi, aka hada shi da mutane uku suka dawo dashi Nigeria , da taimakon ma'aikatan airport ɗin suka samu addireshin shi suka ajiye shi a daidai ƙofar gidanshi suka juya suka fita ........

Haka Alhaji tanim ya ci-gaba da haukar shi tuburan batare da yana magana ba .......

Haukarshi ta munana kuma ta ƙazanta , domin kuwa abubuwan sunyi mishi yawa , dole haukar tayi yawa, haƙiƙa da irin haukar shi gara mutwar shi tafi mishi Alkhairi , tsabar tsananin warin dayake duk layin da ya shiga da duwatsu suke koranshi tsabar ɗoyi da yakeyi ,saɓanin sauran mahaukatan da ba'a yi musu haka ..........
Hmmmmmm Alhaji tanim.........



*Muje zuwa a last page*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 59 & 60*

*The last page*

*End !!!End !!!End!!! End!! End!!*

Bayan kwanaki biyu zuwa yanzu haukar Alhaji tanim ta matuƙar ƙazanta matuƙa, domin babu marabarshi da Aljani domin ganinshi sai ya matuƙar tsorata mutum matuƙa ......


Zaune Mallam Musa yake yana ta tunanin ta yanda zai ɓullowa Al_ amarin Hamdiyyah, kamar an zungureshi ya miƙe cikin ranshi yake faɗin," kai barinje gidan Wannan tsinannen koh Allah zai sa mu haɗu dashi , dan ko ma menene sai ya ba Hamdiyyah takardarta .......

"A fusace Mallam Musa ya fita kai tsaye ya nufi gidan Alhaji tanim , ko da ya je gidan ga mamaki Alhaji tanim ne kwance a ƙasa saɓa cin ciyayi tamkar akuyar.........

"Ga mamaki Mallam Musa tsaye yayi yana son ganin ikon Allah shin Alhaji tanim ɗin ne ko kuwa ??ƙara murza ido Mallam Musa yayi ya sake tabbatar da abun da idanuwanshi ke nunar mishi , domin babu shakka Mallam Musa bazai manta da fuskar nan ba .......

Ƙarasawa gurinshi yayi yafara ƙare mishi kallo ,ɗagowa Alhaji tanim yayi yana kallon Mallam Musa , wani kukan kura yasa ya miƙa a fusace ya zura da mugun gudu , binshi mallam Musa ta farayi a baya , shikuwa Alhaji tanim na ci-gaba da zura guda , ganin hakan yasa Mallam Musa tsayawa dan ganin inda zai nufa , ci gaba yayi da gudu , titi ya shiga gadan-gadan , wata ƙatuwar tirela ce ta shigo da gudu ta hau kanshi ta takeshi.......

Duk da cewar Mallam musa yayi nesa dashi hakan bai hanashi ganin shi ba , sossai ya tsorata da ta ka shin da motar tayi , jikinshi na rawa ya nufi gurin ya ga Alhaji tanim kwance mutane sun fara taruwa akanshi , sossai ya raunana , domin ko ba'a faɗa ba da ganinshi kasan cewa tabbas ranshi baya jikinshi , wani irin wari sossai yakeyi , hakan yasa Mutanen gurin suka fara toshe hancinsu suna tufar da yawu , maganganu suka farayi kowa na faɗan Albarkacin bakinshi , har suka tsaida matsayar kan cewa a wurgar dashi kawai , Mallam Musa na tsaye ta gefe yana jinsu ba tare da ya ce komai ba , haka kuwa sukayi suka cicciɓeshi suka wurgashi gefe suka barshi a gurin kowa ya watse ciki kuwa harda Mallam Musa ........

Jikin Mallam Musa a sanyaye ya dawo gida cikin ranshi yake faɗin," haƙiƙa karshen alawa kasa , ko da ya koma gida nan ya labarta ma baba mariya Komai ya bata labari duk yanda akayi , sossai baba mariya tayi Allah wadai da hakan , nan Mallam Musa ya kira Hamdiyyah ya faɗa mata duk yanda akayi , sossai itama bata ji daɗi ba, cikin dabara Mallam musa ya faɗa ma su Hibba cewar mahaifinsu ya rasu , hakan bai wani damesu ba , sai binshi da sukayi da Allah ya jiƙanshi ......


Duk yanda Faisal yaso ganin Hibba sam abun yaƙi , yana tsoro da tunanin zuwa ganinta hakan yasa yafara bibiyar dukkanin lamarinta , cikin bibiyar lamarin nata ne ya ji labarin cewa mijin da ta aura ya rasu , ko da yaji labarin bai yarda ba sai da ya tabbatar yaji a majiya mai ƙarfi kafin nan ya yarda .......

Su Hibba sun samu sauƙi sossai ba laifi , Kasancewa kulawar da suke samu ta kowanne ɓangare ............

A ɓangaren Ammi kuwa zama kaɗai ci ya dameta , hakan yasa Mallam Musa ya umarceta da ta dawo gidanshi kawai da zama sai su haɗu su kula da su Hibba , haka kuwa akayi Ammi ta dawo cikin gidan , kulawa sossai sossai su Hibba suke samu daga garesu , shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin su , sun zama tamkar yaran cikin gidan , sun zama kamar Mallam Musa ne ya haifesu , babu abun da suka nema suka rasa , suna samun kulawa sossai da gaske , sai dai kewar Ilhama da suke matukar yi.......

Bayan Wasu kwanaki Mallam Musa ya kirawo Mallamai da kuma Alƙalai akan Maganar gidan Alhaji tanim da gadon su Hibba, ganin shaidu masu karfi yasa batareda wani ɓata lokaci ba aka sa gidan a kasuwa , aka kuma fito da ɗumbin kuɗaɗe masu yawa a cikin gidan , aka danƙasu a hannun mallam Musa kan cewa ya riƙe ma marayu yadinga juyamusu har Allah yasa su girma ya ɗan ka musu abunsu , badan Mallam Musa yaso ba ya karɓi dukiyar ,a cewar shi bayason rikon dukiyar marayu , sai dai kawai ya amince dan babu yanda zaiyi ne Kawai ya karɓa ya kuma yi fatan cewa Allah ya tayashi ruƙo ........

A gurguje

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kammaluwar takaba da kuma iddar Hamdiyyah wata huɗu da kwana goma........

"Ba laifi hankalinta yakwanta sossai , kyawunta da ƙibarta sun fara dawowa , sai dai tunani da ba'arasata da su ba jifa_jifa' musamman tunani Faisal masoyinta , takanyi tunani wani lokacin kan cewa ko a wani hali Faisal yake ciki?? A kullum in ta tuna hankalinta na tashi , dan kuwa har yanzu soyaiyyar faisal kullum sabuwa take ƙara zama cikin ranta , domin kuwa duk wani abu da takeyi soyaiyyar faisal tana maƙale cikin ranta ........

Bayan kammaluwar takaba da kuma iddar Hamdiyyah da sati ɗaya , Faisal yafara shirye shiryen zuwa gidan Mallam Musa gurin Hamdiyyah ..........

Faka motarshi yayi daidai ƙodar gidan mallam Musa , yaro yagani a ƙofar gidan yace, yaje ya kira mishi Hamdiyyah , nan take yaron ya shiga cikin gidan , ko da ya shiga da sallama yace," wai Hamdiyyah tazo , ga mamaki Ammi da baba mariya da ita kanta Hamdiyyah da take wanke wanke suke kallon juna , cike da mamaki Baba mariya tace yaro wai inji wa ??? Bansani ba inji wani ne dai a waje , to jekace tana zuwa baba mariya ta faɗa .........

Murmishi baba mariya tayi gamida faɗin," kai ni mariya , to fa Hamdiyyah sai ki shirya , da alama dai wannan mai sallamar dai yagama ƙirga kwanakin takabarki da kuma iddar ki ne , gashi kin fara kasuwa , maza tashi ki bar wanke_ wanken nan ki leƙa kigani ko waye ,yarinya mai farin jini Baba mariya ta ƙara sa maganar gamida da sakin murmishi a fuskarta , itama murmishi Ammi tayi tace," kai Baba mariya kinjiki da wata magana .........

Cuno baki Hamdiyyah tayi gamida da faɗin," uhm nidai baba mariya bazanyi aure ba babu inda zani , nikam na haƙura da aure kwata_ kwata bazan fita ba tsoron aure nakeji nikam , a je kawai ace bazanzo ba Hamdiyyah tafaɗa kamar me shirin yin kuka ........

Kinji yarinya da shegantaka , idan bakiyi aure ba zama zakiyi mu tasa ki gaba muna kallo ? Ai birikiji ko yau miji ya fito miki aurarki zamuyi mu huta kin ji na faɗa miki, maza bar wanke_ wanke nan ki tashi kije cewar Baba mariya........

Batareda Hamdiyyah ta kara cewa komai tashiga daƙi taɗauki hijabinta ta fita kamar zata fashe , gamida cuno ɗan ƙaramin bakinta ta fita cikin ɓacin rai........

Tsaye yake a jikin motarshi hannunshi rike da waya yana dannawa , jikinshi sanye da ƙananan kayan da suka matuƙar amsar jikinshi.......

Turus tayi ta tsaya tana kallonshi , zaro ido tayi dan tabbatar da cewa Faisal ɗin ne ko kuwa??

Murmishin da ya baiyyana fararen haƙwaranshi ya sakar mata gamida da faɗin," kina mamakin gani na ne , ki ƙaraso mana zaki fi yarda da cewa Faisal ɗinkin ne dai , shine dai yadawo gareki Hamdiyyah ...........

Wasu ƙwalla masu sanyi ne suka zubo daga cikin idanuwanta , haɗe da sakin murmushin jin daɗi da farin cikin da bata san dashi ba ........

A hankali ta tako ta ƙarasa kusa dashi ta cigaba da ƙare mishi kallo , a hankali ta buɗe ɗan ƙaramin bakinta tace," Faisal tafaɗa da tattausar murya , na'am Hamdiyyah ! Faisal ya faɗa cike da farin ciki da murmishi baiyyane akan fuskarshi.......

Cikin rawar murya Hamdiyyah tafara faɗin,"faisal ka tafi kabarni!! kabar ni cikin damuwa da baƙin ciki da takaici , faisal yanzu kayi mun alƙawari kadawo gareni na har abada dan Allah , wallahi nakasa mantawa dakai a cikin raina , kullum soyaiyyar ka sake ƙaruwa take a raina , Faisal kacemun kadawo gareni dan Allah ........

"Cikin ƙarfin hali bakinshi ya iya furta , Hamdiyyah karki manta tun da can ba nine na tafi na barki ba , kece kika tafi kika barni, kece kikayi mun nisa yanzu gashi na dawo gareki , dawowar da bazamu taɓa rabuwa ba har ƙarshen rayuwarmu Hamdiyyah ina sonki ina tsananin ƙaunarki ƙaunar da bazan ita misaltashi da komai ba.........
Cikin kuka Hamdiyyah tafara girgiza kanta ta sauƙar da kanta ƙasa kafin daga bisani ta ɗago tace,"Faisal kamanta yanzu fa ni ba budurwa bace , an not a virgin any more , kana ganin zaka iya rayuwa dani a haka , zaka iya auren bazawara??tafaɗa gamida fashewa da matsanancin kuka.........

Dariyar yaƙe yayi ya danne zuciyarshi , cikin ƙarfin hali yace," Hamdiyyah ba budurcin ki nakeso ba , Ashe har in ban aureki ba soyaiyyar da nake miki ta ƙarya ce ,ƙaunar da nake miki ta yaudara ce kenan , yanzu a tunanin ki ni zan iya ƙin yarda da aurenki ne , wallahi tallahi Hamdiyyah in kinyi aure sunkai goma , kuma kin haifi yara dayawa , matuƙar nasamu damar kika dawo gareni wallahi babu wani abu dazai hanani aurenki Hamdiyyah , wannan Alƙawari na ne , yanzu idan nine haka ta faru dani nayi aure bazaki iya aurena ba kenan , dan Allah kidaina wannan tunanin hardai iyayenmu sun aminta wallahi babu wani abu dazai hanani aurenki Hamdiyyah , ke tawace bi'iznillahi ......

"Wani murmishin daya baiyyana fararen hakwaranta ta sake ,wasu hawaye masu sanyi suka ƙara fita daga cikin indonta tace,"Faisal bansan da wani irin baki zanyi maka godiya ba , bansan da wani abu zan saka maka ba , Faisal Nagode ƙwarai da gaske , Allah yasaka maka da Alkhairi.......
murmishi yayi gamida faɗin,"babu komai Hamdiyyah ina matuƙar girmama soyaiyyar ki a koda yaushe , dariya tasa ta ƙura mishi ido daga bisani tace", Nagode sossai masoyina , amma Faisal naga duk ka canza ka sake kyau ina katafi bayan rabuwar mu ne ? Ko labarinka ma ba'aji banyi tunanin zaka dawo gareni ba .......

Dariya yayi yace," to nidai saidai nace Alhamdulillah , nan Faisal ya labarta mata

Please Login or Register in order to submit comment