Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da haka har Ammi ta kamala bata labari duk yanda akayi ..........

Motsi kaɗan in sukayi sai ta duba su , da haka har gari ya waye ........

*Mu hadu a next page*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*

*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 49 & 50*

"A Ɓangaren Alhaji tanim kuwa !!!!
Ko bayan ya tafi ƙasar Indiya kai tsaye masauƙin shi ya nufa kamar yanda ya saba.......

"Karo na farko kenan da ya zo ƙasar Indiya bai nemi ko wacce ƙaruwa da zata kwana dashi ba, jinshi yake tamkar bashi da lafiya, tunani yake iri_iri cikin ranshi.........

"Zaune yake a bakin gado, dafe kanshi yayi ya runtse idanuwanshi , yana tunanin irin aika_ aikar da ya aikata ma yaran shi , a razane ya miƙe ya firgita , abun nayi mishi tamkar a mafarki, yana jujjuya kanshi kamar ɗan bori haɗe da cizar leɓe, idanuwanshi na hasko mishi abun da ya aikata .........

"Shuru Yayi yana tunanin abubuwa da yawa cikin ranshi , tsaki yaja gamida faɗin," mstt aikin banza , to ina ruwana ma naje ina tunani akan wani ƙaramar damuwa , naje ina wani irin banzayen tunani, numfasa yayi gamida cigaba da faɗin," da na wulakanta gara ko ma menene na aikata, babu abun da ya dameni ,da ace na rasa kudi na gara na aikata koma miye, da wannan tunanin ne yasamu zuciyarshi tayi sanyi , yayi wanka daga bisani ya kira karuwanshi guda biyu da zasu kwana dashi .........

"Misalin ƙarfe sha biyu na dare Alhaji tanim ne kwance da karuwanshi bayan sun gama aikata fasiƙanci da aka saba , barci ne mai nauyi yayi awun gaba da shi ...........

"Ko da yake barcin wani mummunan mafarki yafarayi , su Hibba da Nihal da mufeeda da kuma Ilhama ne suke zagaye dashi suna ta kuka , shi kuma yana tsakiyar su , can kuma sai suka ɓace ,sai kuma akafara yi mishi wata irin Azaba, ruwan wuta ake mishi , ta ɗayan bangaren kuma ana ta yayaiyyanka namanshi , ga kuma wuta da ake kona shi dashi .........

"Da wani razanannen ihu ya farka yana numfarfashi haɗe da wani irin haki , ga zufa duk ta jikashi sharkaf .........

"A tsorace karuwanshi suka tashi haɗe da firgita , cikin tsoro suka ce Lafiya?? Meke faruwa ........

Cikin numfarfashi haɗe da goge zufar jikinshi yace," babu komai ku kwanta kawai ........

Tsaki suka ja gamida faɗin," to tunda ba komai mu kar ka sake mana ihu in ba haka ba zamu koma ɗayan ɗakin bazamu iya ba ..........

"Da sauri ɗayar tace," uhmm tashi ma kawai mu koma mu barshi ya ƙarata da ihun shi......

Tashi sukayi da niyyar tafiya , da sauri ya dakatar da su ta hanyar faɗin," dan Allah ku zauna kar ku tafi , kunsan kune kuke ɗan ɗebemin kewa kar ku barni ni kaɗai kunji !!

Harara suka bishi dashi gamida jan tsaki suka fita suka bar shi a ɗakin batare da sun ce mishi komai ba ..........

" Ko da suka fita suka tafi ɗayan dakin Alfashansu suka yi su biyu, wato less *wa'iyazubillah*.......

"Cikin tsoro da tashin hankali Alhaji tanim ya sake komawa barcin , ko da ya koma ma abun da yagani a cikin mafarki yafi na farkon muni , sossai ya sake firgita , ko da ya buɗe ido ya farka a zahiri , gizo suka farayi mishi kunnuwanshi na jiyo mishi muryoyinsu suna faɗin," Daddy!!! Daddy!!! Daddy!!!! Ka cucemu , me mukayi maka haka? Allah bazai Barka ba ka cutar da rayuwarmu .........

"Ihu sossai yake yi yana yin juyi hannuwanshi manne da kunnuwanshi yana juyi haɗe da yin zufa.........

"Wannan halin Alhaji tanim ya shiga har garin Allah ya waye batare da ya sake rintsawa basai razana da tsoro .......

"Washe gari da safe karuwanshi duk suka tafi batare da sunyi mishi sallama ba, kasancewar ya biya su kafin su fara ,tunda ya farka ya rasa sukuni ,sai gizo su Hamdiyyah suke yi mishi , hakan yasa duk ya fita haiyyacinshi , ko fita a cikin ɗakin yakasa , sai rawa da jikinshi yake ........

"Ta bangaren su Azarfakinzu kuwa zazzaune suke suna jiran Alhaji tanim ɗin ya kawo jini suyi aiki dashi Shuru _shuru bai karaso ba , hakan yasa suka fara tunanin ko bai samu bane ?........

Sossai ran Azarfakinzu ya ɓaci, cikin ɓacin rai yafara faɗin," gaskiya mutumin nan yana ɓata mana lokaci da yawa , dole mu ɗauki mataki akai , na farko mun bashi aiki bai yuyu ba , to wannan ma munji Shuru , dole mu ɗauki mataki akan Alhaji tanim ya faɗa cikin tsan_tsan ɓacin rai , Shuru sauran sukayi suna jiran hukuncin da zai yanke .........

"Bayan kwana biyu Hamdiyyah ce zaune tana Bama Hibba' Nihal, da mufeeda abinci , a hankali suke cin abincin kasancewar bakin nasu ba daɗi , ga Azabar da suke sha.......

"Cikin sanyin murya Hibba tace,"Anti nikam Ina ilhama take ? Ko ba' a ɗakin nan take ba ????

Shuru Hamdiyyah tayi tana me tsoron faɗa mata , murmishin yaƙe Hamdiyyah tayi tace uhmm Kinga hibbatuna ki ci abinci tukuna kinji ?
Shuru Hibba tayi ta kaɗa kanta alamar to , Nihal da mufeeda suka bita da kallo kawai ..........

" Bayan sun gama cin abincin ne , daidai Lokacin likita ya shigo ya sake duba su ,kafin daga bisani ya fita .........

Bayan ya fita ne Mallam Musa da baba mariya da Ammi suka shigo cikin ɗakin........

"Sossai suka ji daɗin ganinsu , tunda har sun iya cin abinci .......

" Ganin yanayin jikinsu ne yasa Mallam Musa faɗin," Yakamata ma ace munemi sallama , naga jikin nasu yafaru sauki , idan mun koma gida hankalin mu zai fi karkata guri ɗaya sai a san yanda za'a ɓullowa Al_amarin ko ?????

Gaba dayansu suka gamsu da shawarar Mallam Musa hakan yasa suka yanke shawarar zuwa gurin likita dan neman sallamar.........

Haka kuwa akayi , Mallam Musa ya nemi sallama a gurin likita, likita ya koma ya duba su , yace," za'a iya sallamarsu zuwa gobe dan Jikin na nasu da sauƙi ba laifi , sossai Mallam Musa yayi mishi godiya daga bisani Mallam Musa ya koma ya sanar ma da Human right cewa za'a yi sallamar gobe , nan Human right Suka buƙaci cewa in anyi sallamar akawo musu yaran , cikin rashin gamsuwa da Maganar mallam Musa yace," shi yanaso a bar mishi yaran in ba damuwa ko dan halin da Hamdiyyah take ciki akan matsananciyar soyaiyyar yaran , da haka sukayi rubuce_rubuce bisa ga sharaɗin cewa zasu dinga zuwa duba su akai _akai har suga abun da Allah zaiyyi , da wannan Mallam Musa yayi na'am cike da farin ciki ......

Washegari misalin ƙarfe biyar na Yamma akayi musu sallama me , kai tsaye gidan Mallam Musa suka rankaya suka nufa........

"Sossai su Hibba suka ji daɗin ganinsu Ajmal suma su Ajmal ɗin haka , itadai Hibba tana ta zuba ido dan ganin Ihlam amma shiru babu ita ba labarin ta .........

Kasancewar Hibba yarinya ce mai matuƙar wayyo , hakan yasa ta fahimci cewa Ilhama bata duniya , kai tsaye Hibba ta kalli Hamdiyyah cikin tsantsar mai da hankali da sanyin murya tace," Anti nasan cewa Ilhama na ta rasu ko ? Domin in har Ilhama na duniya to dole zan ganta , tunda duk naga sauran ƴan uwana , Yakamata ace na ganta , tafaɗa idonta cike fal da hawaye , har hawayen suka sami Nasarar zubo mata a idonta ........

"Ƙoƙarin haɗiye kukan dake barazanar zubo wa a fuskarta Hamdiyyah tayi ,gamida ƙokarin tattaro dukkanin dauriyanta da karfin hali tace," eh Hibba Allah ya karɓi ran Ilhama , kiyi haƙuri ki bita da addu'a kinji , dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji kar ki damu kinjiko ?

"Kuka ne ya kuɓuce mata , cikin muryar kuka take faɗin," nasani nasan Ilhama bazayi rai ba , domin wannan baƙar Azabar Ilhama na baza taɓa iya ɗauka ba , shikenan ya kashe mana ilham Allah ya isar mana ,mugu Azzalumi ,Anti Allah bazai bar babbanmu , ta ƙarasa maganar gamida fashewa da matsanancin kuka gamida faɗawa jikin Hibba taci gaba da kukan ............

"Sossai kowa a gurin Hibba ta bashi tausayi ,sai da kowa yayi ƙwalla, duk yanda Hamdiyyah taso daurewa ta kasa sai da tayi kuka itama tana me ƙara jin soyaiyyar yaran cikin ranta , ta ɗayan ɓangaren kuma tana jin wutar tsanar Alhaji tanim na sake ruruwa cikin ranta , haƙiƙa da zata ganshi tsaf zata halakashi har lahira ,domin ya cancanci ya mutu , mutuwar ma ta wulaƙanci, sossai take jikin tsanarshi ........

"Rarrashin Hibba suka dingayi , amma sam takasa daina kukan , sai da taji kanta na ciwo, dan kanta ta haƙura tayi shiru ........

"Abinci Baba mariya ta kawo musu , basu Hamdiyyah tayi suka ɗan ci kaɗan Hamdiyyan ma ta ci kaɗan tayi sallar magriba da isha'i ........

"Kallon ta Ammi ta yi tace," to Hamdiyyah ki tashi mu tafi ko sai gobe mu dawo ko ? Zaro ido Hamdiyyah tayi gami da faɗin," ina ɗin Ammi ?????

"Cikin rashin fahimta Ammi tace," gida mana l!! hmmmmm Hamdiyyah tace," gamida maida kallonta zuwa ga Ammi tace," Ammi wallahi bazan je ko ina ba , ina nan tare dasu Hibba , yaushe zan iya tafiya na barsu taɓɓinjan , ai bazan iya ba , kiyi haƙuri ki tafi ke kawai , nikam ina nan , maganar da tayi sai da taso ba su Baba mariya ɗariya.......

Dogon numfashi Ammi taja gamida faɗin," to fa , To ai shikenan sai ki zauna nikam barin tashi in tafi sai da safe , nan Ammi tayi musu sallama ta tafi cike da mamakin irin son da Hamdiyyah take ma yaran .........

"Bayan Ammi ta tafi ne baba mariya ta basu ɗaki daya mai gado biyu , da Hamdiyyah da Hibba da kuma Nihal da mufeeda suka kwanta , sai ɗayan su Ajmal suka kwanta su uku , gwanin ban tausayi , da haka har ɓaci yayi awun gaba dasu ...........

" Washe gari da safe , Hamdiyyah tayi musu wanka dukkaninsu , Baba mariya Kuma tayi musu abun karyawa, suka karya ,suka sha magungunan su suka ɗan koma barci , kasancewa har yanzu bawai sun warke ba ne ..........

""Misalin ƙarfe biyu Ammin Hamdiyyah tazo , nan suka gaggaisa shima mallam Musa ya fito , suka gaisa daga bisani tafara faɗin," to Alhamdulillah , kullum munayi ma Allah godiya , akan duk wata Ni 'ima da yayi mana , haƙiƙa wannan abu da yafaru ba komai bane sai ikon Allah , kuma duk abun da Allah ya ƙaddara ma bawa to fa sai ya kasance , to Hamdiyyah mun nemeki duk inda muka san zamu sameki amma Banu ganki ba , cikin hikimar Allah Kuma da taimakon Allah sai gashi kin dawo garemu babu zato babu tsammani , kuma dawowarki yayi daidai da jarabawar da ta sami waƴanan yarannan , to inaso ki faɗamun ya akayi haka? Wani irin zama kikayi a gidan aurenki , sannan ya akayi kika bar gida faɗamun, domin abun akwai matuƙar ɗaure kai a ciki kingane ko , to ina jinki ???

"Shuru Hamdiyyah tayi kanta ta saukar kasa hawaye suka fara fita daga idonta , kafin tayi saurin sharewa cikin rawar murya tafara faɗin," haƙiƙa tun randa na tsinci kaina a cikin gidan duk wani farin cikina ya gushe , zuciya ta ta shiga cikin bakin ciki da damuwa , wallahi tallahi baba na shiga matsanancin tashin hankali da wahala da Azaba , nan Hamdiyyah ta fara bada labarin duk zaman da tayi a gidan , bata ɓoye musu komai ba , bata kuma ƙi fadan komai ba , haka ta bada labarin duk irin zaman da tayi a gidan , tunda tafara bada labarin take kuka har taƙarashe labarin , idonta suka kukkumbura........

Haƙiƙa har Mallam Musa sai da ya zubarma da su Hibba da kuna Hamdiyyah hawaye tsabar tsanani tausayi , su ,Baba mariya da Ammi Kuwa kuka ba'a magana , dan harda majina , tsabar tausayin su Hibba da Hamdiyyah........

Wani irin ciwon kai Hamdiyyah taji ya ziyarceta lokaci ɗaya, Wani dan karamin ihu tasa take ta faɗi sumammiya a ƙasa ..........

"A rikice su Ammi suka dagota cikin tashin hankali sukace Hamdiyyah Hamdiyyah lafiya kuwa?????

*To mu hadu a next page*

*Am very sorry for the late update*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*

🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*PAGE 51 & 52*

*Dan Allah kudinga mun Uziri rashin posting kullum abubuwa ne sai a hankali , am very sorry*


"A hankali ta buɗe idanuwanta ta farka ta buɗe idanuwanta , tana yi musu wani irin kallo.......

"Kallanta sukayi gamida faɗin," Hamdiyyah sannu ko? Menene lafiya ko??

"Cikin murya irin wacce batata ba tafara magana kamar haka",_Assalamu Alaikum_ jin baƙuwar murya wace ba irin ta Hamdiyyah ba yasa duk suka kalli juna cike da tsantsar mamaki , wa 'alaikumu Salam suka amsa a tare haɗe da kallon juna.........

"Nan aka ci gaba da cewa,"_Da farko sunan harɗo , Ni ba mutum bane face Aljani........

"Nan take duk suka tsorata sunan jiran ganin ikon Allah .........

Nan ya cigaba da faɗin," gaskiya ni ba Azzalumi bane , kuma Ni Musulmi ne kamar ku, ba na shiga jikin Hamdiyyah bane dan na cutar da ita ba , sai dai na shiga ne dan in bata kariya , duk da nasan cewa duk wani kariya daga gurin Allah yake .......

"Sossai suka yi mamaki matuƙa , baki buɗe suke kallon ikon Allah .......

"Nan Harɗo ya cigaba da faɗin,"mutunci da imani da tausayin da kuma uwa uba Addini da riƙo da addu'a da take dashi ne ma har yasa na shiga jikin ta dan taimakonta, hakiƙa tun lokacin da ta shigo gidan Alhaji tanim nake biye da ita, yarinyar tasha wahala matuƙar wahala , domin da badan Allah ya taimaka ba , da yanzu an sadaukar da jinin jikinta wa ƙungiyar shi mai gidan nata, daf suke da ɗaukan rayuwarta........

"A tsorace suka zaro ido , cikin tsantsar tashin hankali da damuwa , suka ce *innalillahi wa'inna illaihir raju'un* shine abinda bakunansu ke iya furtawa .......

" Nan Harɗo yacigaba da faɗin," kunyi ganganci kuma kunyi laifi , kuma kunyi wawauta da kuka ɗauki ƴarku kuka Bama wanda bakusan Asalinsa ba, baku san sana'arshi ba sannan baku san wanene shi ba ,baku kuma san Ahalinshi ba , to wannan babban kuskure kuka tafka , kuma kun cutar da Rayuwar wannan yarinya .......

"Wani kallo Mallam Musa ya wurgama Ammi , wanda ya ke nuni da cewa kingani ko ? Da sauri Ammi ta kawar da kanta gefe , idonta ya kawo ƙwalla , tayi saurin haɗiyewa , tana n?me jin tsanar kanta haɗe da tsantsar nadama da kuma da nasani , zuciyarta cike fal da tausayin ɗiyar Tata .........

" Nan Harɗo yacigaba da faɗin," shin ko kunsan wanene shi , da har kuka ɗauki ƴarku kuka bashi, haƙiƙa da kunsan ko wanene Alhaji tanim da ko kallonshi baza ki so yi ba balle har kuji sha'awar haɗa zuri'ah dashi , kunsan shi waye ???


To masu karatu nasan kuma za kuso jin wai wanene shi Alhaji tanim gamji ɗinan ne? .........

Ku biyoni a next page Dan jin wanene shi ?

*Ku yi manage da wannan pls*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 53 & 54*

"Shin wanene Alhaji tanim gamji ?????

"Alhaji tanim haifaffen garin katsina nane .......

Sunan mahaifinshi
Haruna gamji , sai kuma mahaifiyarshi Gwaggo salaha..........

Alhaji tanim ya taso cikin wata irin ƙazamiyar rayuwa , wanda hakan ya samu tushe ne daga mahaifinshi ............

Shine ɗa na farko a gurin Alhaji Haruna , sai ƙannenshi su uku, Maza biyu sai mace ɗaya ..........

Alhaji Haruna mutum ne maras imani maras tausayi uwa uba ga bala'in son abun duniya da kwaɗayi , hakan yasa sam baidamu da abun da yaran za su kawo ba ko da kuwa ta wacce irin hanya ce zai karɓa.........

Tun Alhaji tanim yana ɗan ƙaramin yake dan kananun sace_sace , kasancewar shi mai son yaga yayi kuɗi da son tara abun duniya .........

Duk a cikin yaran Alhaji Haruna shine babba kuma shi ne ya ɗauki ɗabi'ar babansu , sanan shine ya ɗauki hali na rashin imani da tausayi ........

Rayuwarshi sam babu Allah a cikinta tun yana yaro , ko wasa yara suka shigo gidansu to fa sai yayi musu mugunta da har sai yaro ya kwanta a asibiti , ko da kuwa ma a hanya yaga yara sai yayi musu mugunta , haka ne yasa duk yaran layin suke tsoronshi matuƙa , da zarar ya fito layin to fa yara zasu fara guduwa , inda har iyayen yara suka kai ƙarar shi gurin mahaifinshi ,babu abun da Alhaji Haruna ke mishi , baya ɗaukan kowane mataki bare kuma har yayi mishi faɗa ,sai cewa dayake ya haifi jarumin ɗaaa........

Hatta mahaifiyarshi ma tsoron yi mishi magana takeyi domin duk abun da zaiyyi sai dai kawai takalleshi ta zuba mishi ido gudun muguntar da zaiyyi mata .........

Domin matuƙar tayi mishi faɗa ko kallon banza to fa sai yayi mata muguntar da sai ta wuni tana zubar da hawaye , a cewar shi ɗaukan fansar fadan da tayi mishi bare kuma duka .........

Haka ne yasa bata taɓa shiga safgoginshi ko lamurran shi ba........

An kai shi makarantu ta fi a ƙirga duk suna kiranshi ,hakan yasa ya daina zuwa makarantar ƙwata_ kwata ya cigaba dabi kwararo_ kwararo yana kananun sace_ sacen shi ..........

Duk abun da zaiyyi sai dai mahaifinshi yayi ta murna ya na ikirari shine jarumi cikin ƴa ƴanshi , shikuma kanshi na ƙara fasuwa yana jin daɗi ........

A lokacin Alhaji tanim nada shekaru ashirin da Shida a duniya mugayen halayensa suka sake baiyyana suka sake fitowa , yazama cikakken tantiri mai sace_sace , duk ya addabi unguwar shi , ga bin mugayen abokan da suka fishi hatsabibanci da lalacewa ..........

Ƴan uwa shi kuwa duk basa kulashi kwata_ kwata musamman ma ƙanwar shi , Kasan cewar neman yi mata fyaɗe da yayi,hakan yasa mahaifiyar suta raba tsakaninsu, dazaran yashigo cikin gidan ko me ƙanwar take da gudu zata tashi ta shiga ɗaki tsabar tsoron da take mishii ........

A gurguje

A kullum mugayen halayen Alhaji tanim ƙara fitowa suke , abubuwan dayake ya ƙara taɓarɓara, baya kallon kowa da gashi , hatta mahaifin nashi da ya ɗaure mishi gindi, hakane yasa duk kowa yadaina kulashi , duk da cewar yana watanni Biyar zuwa shida batare da ya waiwayi gida ba , yana ɗaukan lokaci mai tsayi .......

Cikin hakane yasake haɗuwa da gurɓatattun abokanai.......

Kasancewarshi mai son kuɗi , hakan yasa abokinshi sukayi mishi tayin shiga ƙungiyar shan jini, bayan sun tabbatar mishi dacewa zasu samu kuɗi sossai, batare da wani tunani ba yayi saurin aminta da na'am da abun......

Hakan kuwa akayi kai tsaye suka nufi garin baburawa , batare da ɓata lokaci ba aka gindaya musu duk wasu sharruɗa kuma suka bi suka yarda da sharruɗan.........

A gurguje

Alhaji tanim dai sai da ya sadaukar da jinin duk ƴan uwa shi ,da iyayenshi a dalili ƙungiyar su ......

A

Please Login or Register in order to submit comment