Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali zasu fara ciwo in sun kwanta jinya suyi fari fat Alamar babu jini a jikinsu , bayan ƴan kwanaki kuma sai su mutu, hakan ya matuƙar ɗaga ma Mutane hankali ,suna me mamakin yanda suke jinya iri ɗaya daga baya kuma sai su mutu , wannan dalilin ne yasa mutane suka fara tabbatar da raɗe_raɗin da ake faɗa na cewa Alhaji tanim ne ke sadaukar da jinin su wa ƙungiya.......

Gaba ɗayansu sai da suka rasu bisa sadaukar da jinin su da akayi ..........

Sossai Alhaji tanim ya gawurta , kuɗi suna shigo mishi sossai kasancewar baya taɓa karya dokar ƙungiyar su, wannan dalilin ne yasa suma suke zubar mishi da kuɗi sossai domin dan ya sadaukar da mutum a gurin shi ba abu ne mai wahala ba.......


Zuwa yanzu Alhaji tanim yayi suna sosai ya gawurta ,kuɗaɗɗenshi sunyi yawa matuƙa........

Harkarsu bata tsaya a iya Nigeria ba har da ƙasashen ƙetare, musamman kasar Indiya , nan ne inda tushen kungiyar su take........

Tunda Alhaji tanim yayi kuɗi yake busha sha sossai da kuɗi , yake kuma kashe wa ta hanyar da bata kamata ba ,da zaran yaji sha'awar kwanciya da mace to fa minti kaɗan za'a nemo mishi Ita yabiya buƙatarshi ...........

A Lokacin da yake da shekaru talatin , A lokacin ya nufi garin Zaria, inda ya auri matarshi ta farii.........

Ana nan ne ƙaddarar haɗuwarsu da Asiya ta kasance wato mahaifiyar Hibba.......

Ganinta yayi zata tafi islamiyya ,ko da ya ganta nan ya tsayar da ita ,ya kuma ƙwallafa ran mallakar ta ko ta halin yaya ne , da taimakon ƙadangaren tsafin da yake tafe dashi........

Cikin Sa'a kuwa ta tsaya batare da ɓata lokaci ba ta kwatanta mishi gidansu yaje .........

Ga mamaki iyayen nata suka karɓe shi hannu bibbiyu ........

Cikin ƙanƙanin lokaci aka tsaida magana , bayan ya turo iyayenshi na ƙarya suka tambaya mishi aure, batare da ƙwaƙwaran bincike ba aka fara shirye-shiryen aure ..........

Watanni hudu akasa bikin inda......
Bayan watanni huɗu aka ɗaura aure ya ɗauki Amaryar shi ya nufi garin Asaba da ita.......

Ko da ya kaita a wani katafaren gida ya ajiye ta mai kyau da tsaruwar gaske.........

Hakan yasa Asiya ta dan tsorota ganin irin katafaran gida da tsaruwar gidan da kuma girman gidan ..........

Ya zuba mata komai na rayuwa babu abun da babu a cikin gidan , ya kuma shaida mata cewa ta sakata ta wala tayi duk yanda takeso a gidansa........

Sai dai wani ɗaki da ya nuna mata cewar ko yananan ko bayanan bai yarda ta buɗe dakin ba , cikin bin umarnin mijin nata ta amincewa haɗe da bin umarnin shi ..........

Abun da ya ɗaure ma Asiya kaii ba koma ba sai rashin ganin danginsa da bata taɓayi ba , zuwa yanzu watan su biyar amma babu wani da taɓa zuwa gurinta , daga nata dangin har nashi, hakan ne yasa ta ɗan fara mamaki da tsoro da kuma tunanin , ita kadai take rayuwa a cikin gidan daga ita sai halinta..........

Yakanyi sati uku baya garin , zai ajiye mata kuɗaɗeɗe masu yawa, Kafin ya tafi , sai dai ta zauna ita kaɗai tayi ta tunani, duk da kuɗaɗɗen da yake Ajiye mata amma sam basa gabanta , bata da bukatarsu , domin Babu inda take zuwa balle ta ga abun buƙata da zata yi da kuɗin .........

Bayan watanni tara Asiya ta haifi ɗiyar ta mai suna A'isha sunan mahaifiyar Asiya lnda akayi mata laƙani da Hibba..........

Toh sai Alhaji tanim yayi ɓarin kuɗi duk da cewa mutane ɗaɗɗaiku ne suka halarci sunan daga mokotansu sai matan abokanan harƙallarsu duk yanda Asiya taso ya mata bayani cewar lna dangin shi sam yaƙi mata ƙwaƙwaran bayani akan hakan badan ranta yaso ba ta haƙura ta barshi, kasancewar in tayi mishi magana yanayi faɗa sossai bayason ta dinga mishi maganar ,da haka ta yi shuru ta zuba mishi idanu ........

A haka take zaune da ɗiyarta Hibba inda take samun kulawa sosai ta ɓangaren mahaifiyarta saɓanin maihaifin ta da bai fiye kula da ita ........

A gurguje

A haka Rayuwar Asiya take tafiya cikin takura da ƙunci, babu fita ko da ƙofar gida ne ,haka rayuwa take tafiya mata cikin tsanani da takura .......

Zuwa yanzu kam ma tafara sabuwa da mugayen ɗabi'un halin Alhaji tanim , a gabanta zai yi waya da ƴan mata ko a jikinshi, sai dai ta kalleshi kawai ta girgiza kai, kasancewar mace mai haƙuri da juriya .........

Duk yanda taso ta gano sana'arshi sam yaƙi bada ƙofar ta gano haka, duk yanda taso tambayarshi sam yaƙi bata amsa,dan kanta ta barshi ta zuba ma Sarautar Allah ido.........


Bayan shekaru biyu Asiya taƙara haifar ɗiyar mai suna Nafisa , inda ake yi mata laƙabi da Nihal ............


*Muhadu a next page*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 55 & 56*

"Bayan Asiya ta haifi Nihal duk damuwa suka taru sukayi mata yawa , Abubuwa suka fara damunta, kewar gida ya dameta , ga damuwar zaman kaɗaici , ta bangare guda kuma ga rashin sanin takamaime sana'ar mijinta , domin tana ɗan lura da wasu abubuwa , takanyi mamakin hanata shiga wannan ɗakin da yayi , kuma taci alwashin shiga ta gani koma menene , hakane yasa tafara tunanin shiga ta duba ɗakin ........

Da zarar Asiya tayi yunƙurin zuwa duba ɗakin sai kuma tsoro ya kamata sai ta fasa , haka tacigaba da rayuwa tamkar akuyar ɗaure........

" Bayan shekaru biyu ,A lokacin Hibba nada shekara uku a duniya ,ita kuma Nihal nada shekara ɗaya da rabi , sossai yaran suke shiga cikin damuwa , basu shaƙu da mahaifinsu ba , dan wataran yakanyi wata biyu zuwa uku bai waiwayo gida ba , haka yasa Asiya rama matuƙa tafara danasanin auren , duk da cewa takan yi tunanin yama akayi ta aureshi , domin ji take tamkar ba aure tayi , hakan ne yasa ta kuɗiri niyyar cewa a ranta ƙaddarar tace haka , haka tacigaba da haƙuri haɗe da juriya a zaman gidan.........

Zuwa yanzu dai lokacin ne ake shirye_shiryen sadaukar da jinin Asiya ,a cikin ƙungiyar su Alhaji tanim , domin yace a wannan karan zai bayar .........

Zaune take ,tana ta tunani cikin ranta , kamar an zabureta ta mike ta ƙudiri aniyar cewa sai ta duba ɗakin da mijinta ya hana shiga koma mai zai faru ya faru , wala Allah nan zata gano asalin sana'arshi ......

Cike da karfin hali ta fara neman keyn ɗakin , cikin sa'a kuwa ta sameshi , bayan ta sameshi ne ta nufi ɗakin kai tsaye , ta sake key , nan da nan kuwa ɗakin ya buɗo.......

Duk da cewar tsoron da takeji bai hanata fasa shiga cikin dakin ba , kutsa kanta cikin ɗakin tayi ,ɗakin yayi duhu sossai , gefen bangon ta kunna nan da Nan wuta ta kunnu a ɗaki , *innalillahi wa'inna illaihir raju'un* shine abun da bakinta ya iya faɗa , kayaiyyakin tsafin ne burjiki , kwarya cike da jini , ga wani skeletal an ƙulleshi a jikin bango , abubuwan tsafin ne burjiki cikin ɗakin ,ta ɓangare ɗaya kuma ga kayukan mutane .........

Nan Danan jikin Asiya yafara rawa tafara tsorata matuƙa , cikin sauri ta dawo ɗakin, da sauri ta ɗebi ƴan kayansu , ta rike ƴaƴanta da niyyar gudawa ......

Ga mamaki wani Irin jiri taji yana neman yarda ita , riƙe kanta tayi ta runtse idanuwanta bakinta na faɗin *innalillahi wa'inna illaihir raju'un*, Neman guri tayi ta zauna , ga Wani zazzaɓi da ke barazanar lulluɓeta, sossai Hibba ta tsorata da ganin halin da mahaifiyarta take ciki duk da cewar bata da wayon sanin ko menene.......

Mama meyasa meki , Hibba ta tambayeta cikin tsananin damuwa ,duk da cewar Hibba yarinya ƙarama ce amma tana da wayyo matuƙa , da sauri ta tashi ta ɗaukko mata ruwa ta Fara ƙoƙarin bata wai ita a dole ko zata tashi.........

Itadai Asiya kallon yaran kawai takeyi , cikin ranta tane me fargaba da tsoron wani hali zata barsu , domin kuwa ji takeyi Tamkar mutuwa zatayi , ta kasa ɗaga ko da ɗan yatsanta ne , sai bin yaran da kallo kawai da takeyi ..........

Take ta fara wata irin shaƙuwa , gaba ɗaya Fatar jikinta ya koma fari fat kamar takarda , idonta ya koma kore , tacigaba da numfarfashi , har zuwa sanda indonta ya kakkafe alamar ranta yabar gangar jikinta *innalillahi wa'inna illaihir raju'un*........

ƊanJijjiga ta Hibba take yi sossai tana faɗin,"mommy!! mommy!! mommy !!!! Amma Ina ido akkakkafe , Nihal ko sai kallon ikon Allah takeyi, kasancewar bata san komai ba.......

Kuka Hibba da Nihal ɗin suka fara ganin har yanzu mahaifiyar tasu bata tashi ba , dukkan su kwanciya a jikinta sukayi , sukayi luf,suna Ajiyar zuciya har barcin wahala yayi awun gaba gwanin ban tausayi.......

Misalin ƙarfe tara na dare Asiya ta fara sandarewa , a lokacin su Nihal har sun farka daga barcin , fuskokin su sunyi jajir sun kumbura tsabar kuka , ga yunwa da tafara damunsu , musamman ma Nihal da take shan nonon, nan da nan jikinsu ya ɗauki zafi sossai zazzaɓi yafara lulluɓesu , wani barcin Azaba ne yasake kamasu ..........

Misalin ƙarfe ɗaya na dare Alhaji tanim yadawo gida , ko da ya dawo yaga halin da suke ciki. Cikin sauri ya ɗauki Asiya ya sata a cikin ɗakin Asirinshi , bayan yasa ta ne , ya canza shigarshi zuwa ta ƙungiya , zuwa jajayen kaya da baƙi , nan ya ɗauki wata Irin wuƙa mai Kamar kadaa ya fille Mata kanta dashi .........

Ba tsoro ba imani ya ɗauki kan ya saka a cikin bayan motarshi ya rufe , bayan ya rufe yadawo cikin gidan , ya ɗebi duk wani kayan buƙata da yasan zai buƙata ya kwashe , hoton Asiya da yake maƙale a jikin bangon ɗakin Alhaji tanim ya ɗauka, badan komai ba sai dan bin umarnin ƙungiya , cikin ranshi ma yace," gara na ɗauka ko ba komai yaranan zasu san mahaifiyarsu , bayan ya ɗauka ne ya ɗebi yaran nashi da suke ta sharar barcinsu ya zuba su a mota ya ja motarshi ya tafi ..........

Kai tsaye a wani hotel ya sauƙa , kasancewar hotel ɗin sun san da zuwanshi sukayi mishi yi maza suka tarbeshi , ya nufi ɗakinshi da yasa ba kwana........

Abinci ya tarar daban_ daban a ɗakin , nan ya tashi Hibba da Nihal yafara basu abincin, amma sam sunki ci , kuka sosai suka fara , Hibba na faɗin," Daddy Ina maman mu, dabara yayi mata yace," ok mamanku ta nanan zuwa kici Abinci yanzu kinji ko ? To Hibba tace tafara cin abincin , ya ɗaukko Nihal yabata yoghurt tayi saurin karɓa tafara sha ........

Bayan sun ci sun koshi suka kwanta suka fara barci...........

Washe gari da safe , Alhaji tanim ya biya ma 'aikaciyar hotel ɗin kuɗi masu yawa kan cewa ta kula mishi da yaransu na tsawon kwana biyu , kafin yaje yadawo , ba musu kuwa ta yarda ta karɓi yaran hannu bibbiyu , tayi alkawarin kulawa dasu , sakamakon tausayi da suka bata , inda yayi mata ƙaryar cewa mahaifiyar su tayi yaji ne kuma babu inda zaikai su , danginshi basa garin Nan kuma shi ma'aikaci ne bazai yuyu ya tafi ba tare da izinin ba ,kuma bazasu barshi ya tafi ba .......

Sossai ta tausayama su Hibba , ta kuma Aminta da kulawa dasu ........

Koda Alhaji tanim ya tafi ,kai tsaye indiya yanufa dan ya basu kan Asiya zasuyi tsafe_tsafensu dashi kai *wa'iyazubillah* batare da damuwar koma ba ya basu suka ji daɗin hakan kuma ........

Bayan kwana biyu ossai su Nihal da Hibba suka saba da ma'aikaciyar hotel ɗin , a ƴan kwana biyun nan , inda take basu kulawa daidai gwargwado .........


Bayan kwana uku yadawo , ganin yanda ta kula da yaran sosai yasa Alhaji tanim bijiro mata da maganar aurenta , ya faɗa mata cewar aurensu ya rabu tsakani shi da mahaifiyar su , a cewar shi tafiyan da yayi ya je ayi sulhu ne abin bai yuyu ba , gashi har an rabu ..........

Sam bata ji daɗin rabuwar su ba,sai dai dalilin yaran ta aminta da auren shi , ko dan ta kula da yaran ma , sossai yaji daɗin haka. ..........

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci suka fahimci juna , yasamu iyayenta aka tsaida biki wata ɗaya , bisa ga yarjejeniyar cewa zaiyyi mata komai na buƙata , sossai suka amince da hakan ...........


Bayan wata ɗaya aka yi aure , Alhaji tanim ya auri bahijja , inda ya ɗauketa zuwa garin bayelsa............

Yanda rayuwar Asiya ta gudana a gidan Alhaji tanim haka Rayuwar bahijja ma ta tafi, inda bahijja take ƙoƙarin kulawa dasu Hibba sossai tamkar yaran da ta haifa da cikinta.........


Itama bayan watanni tara Bahijja ta haifi ɗan ta namiji wato Ajmal, haka Ajmal suke rayuwa da Hibba da Kuma Nihal cikin rayuwa me cikeda kunci , tun Hibba na tambayar mammanta zuwa yanzu har ta gaji ta daina , saɓanin Nihal da bata da wayon sani , a tunani ta bahijja itace mahaifiyarta ......

Bayan shekaru biyu , Bahijja tasake haifan ɗanta wato Mujahid .........

A lokacin da Mujahid yayi watanni takwas a duniya a lokacin ne Alhaji tanim yasake auren murjanatu wato mahaifiyar mujahid da mufida, mazauniyar Garin Borno ,...........


Ba laifi sunyi zaman Amana sossai ,sam basu ɗauki kishi da zafi ba , dama ance in da kaji daɗi nan ake kishi , dalilin zaman kuncin da akayi sam kishi bai damesu ba ,sudai sun zuba ma Sarautar Allah ido kawai

watanni shida zuwa bakwai da auren murjanatu , bahijja ta mutu , itama ya sadaukar da jininta ma ƙungiya......

Sossai murjanatu tashiga damuwa sossai akan mutuwar bahijja , ba yanda zatayi ta ɗauki hakuri da juriya ,ta Kuma bita da addu'a da kuma alkawarin kula mata da ƴaƴanta , Amana,wannan ce sakaiyyar da zatayi mata kawai kenan ..........

Haka Rayuwa ta ci gaba da tafiya da Murjanatu, yau suna wannan garin gobe suna wacan, da zaran ya kula da mutane sun fara saka mishi ido to fa zai tattara inashi_ inashi yabar garin , haka yasa murjantu tafara zargin shi sossai itama .......

A lokacin da ta shekara biyu da rabi , a lokacin ta haifi Mujahid da mufida , a lokacin ne ya bijiro mata da maganar auren Nafisatu ƴar Asalin garin lafiya.........

Batare da damuwa Komai ba tayi na'am da abun........

Nafisatu itace mahaifiyar Jawad, a lokacin kuma da ta haifi Jawad a lokacin ne murjanatu itama tace ga garinku , a lokacin itama ya sadaukar da jininta wa ƙungiya , sossai hankalin nafisatu ya tashi , inda itama tsoro ya kamata , ta fara ɗawainiya da yara biyar , da taimakon Hibba, take aikace aikacen gidan .........

A lokacin da Jawad ya shekara ɗaya a lokacin ne itama ya sadaukar da jininta ta mutu........

Ya rage su kaɗai ne a cikin gidan , Inda Hibba take da a shekara takwas a duniya , tafara koyan komai tun bata iya ba Kasancewar su kaɗai ne a gidan dolenta ta iya.......


bayan wata ɗaya ya auri zainab, ƴar Asalin garin Adamawa , bafulatana ce mai kyan gaske , cikin lokaci ƙanƙani ya auri ta , bayan ya aure ta ne ta samu cikin illhama, cikin da ta ɗauki son duniya ta ɗaura mishi , ko bayan Ilhama ta fito duniya haka soyayyar ta ci-gaba dayawaita, sossai take ƙaunarta , kamar tasan baza tayi rayuwa mai tsayi da ita ba ..........

A gurguje

Alhaji tanim ya auri ƴan mata bayan zainab sunkai biyar , daga garuruwa daban_daban, matan sun zauna da zainab sunyi zaman kishi ,sai dai babu wacce ta taɓa haihuwa a cikinsu , dalilin maganin hana haihuwa dayake basu su sha ko sunaso ko basa so, a cewar shi yaran sun isheshi ...........

Dukkaninsu su sun rasu , sai zainab kaɗai tayi saura , abun na matukar bata mamaki sossai , inda mutane suka fara zargin cewa zainab ce mai kashe su sanadiyyar kishi , itadai ta fauwwalawa Allah komai , domin ita kanta abun na damunta .........

Dalilin da yasa Alhaji tanim bai sadaukar da jinin ba , ba komai bane yasa sai dan kyau da take mishi da kuma tsantsar ƙaunar da yake yi mata, wannan dalilin ne yasa yakasa sadaukar da ita , yake zaune da ita ...........

Bayan shekaru uku , a wannan karan ne ƙungiya suka buƙaci cewar jinin zainab suke da buƙata, sossai hankalin shi ya tashi domin kuwa yazama dole ya sadaukar da ita ,ba dan yaso ba haka ya sadaukar da ita , itama ta mutu tabar Ilhamanta ........

Tun bayan rasuwar zainab Alhaji tanin bai sake aure ba , domin kugiya sun ɗaga mishi ƙafa ,domin ya sadaukar da mutane sosai ba kaɗan ba , da wannan dalilin ne yasa ya ɗan dakata da auren, yacigaba da neman matan barikin shi , wannan kenan ..........


Abun da masu karatu baku sani ha , duk matan da Alhaji tanim yake aura ba yin kansu bane suke zama dashi ba , da taimakon tsafinshi, yake rufe musu baki da kuma iyayensu , sannan kuma dazaran mace ta shigo gidan to bazata taɓa iya buɗe baki tace zata fita ba ko da bada Sanin shi ba, Hakan ne yasa yake yin duk abun da yaga dama dasu .........

Wannan kenan ,taƙaitaccen Tarihin Alhaji tanim gamji kenan...........

Cigaban labari .........


*Muhaɗu a next page*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 57 & 58*

"Bayan harɗo yagama basu labarin munanan halayen Alhaji tanim , da kuma baƙar Azabar da Hamdiyyah da su Hibba suka sha a gidan , sossai hankalin su ya tashi matuƙa , kuka suka dingayi kamar an aiko musu da sauƙon mutuwa , Mallam Musa ma ƙarfin hali kawai yayi , amma zuciyarshi ta matuƙar taɓuwa sossai , haƙiƙa sun matuƙar jinjina mugayen halayen Alhaji tanim gamji matuƙar gaske , suna kuma jin wata irin tsanarshi , haɗe da Allah ya tirr da halinshi , da bin shi da munanan addu'a, haushin kanta Ammi ta dinga ji matuƙa , tana me tsanani da takaici da danasanin haɗa jiki da ɗiyarta tayi da Wannan kazamin mutum, Kuma marar tausayi da imani , sossai Ammi ta kara jin haushin Kanta , domin koma menene ita ta janyo , da bata dage ta aureshi ba , da kuma son abun duniyan ta , da yanzu haka bata kasancewa ba, dan haka ba ɗauki laifin duk ta daura shi akanta .......

Sossai harɗo yacigaba da nunar musu illar aurama yarinya Wanda ba taso, da kuma wanda ba'a san Asalinshi ba, ya kuma shaida musu cewar dole Alhaji tanim zai girbi abun da ya shuka ko da ta ɓangaren ƙungiyar su ne .......

Sossai harɗo yaja musu kunne haɗe da nasiha mai ratsa zuciya ya kuma shaida musu cewar yabar jikinta kwata_kwata domin abun da ya kawo shi jikinta ya gama , ya kuma yi alƙawarin bazai sake dawowa jikinta ba , sossai sukayi mishi godiya daga bisani Hamdiyyah ta rufe idonta , ta yi wata attishawa mai ƙarfi, nan take ta fara buɗe idonta , ta tashi a hankali.........

Sannu suka farayi mata , dukkanin su hankalinsu yayi kanta suna son ganin halin lafiyarta , ganin yanda duk suka nufota suna kallonta tace," Lafiya kuwa kuka sani a gaba kuna kallo na , meyafaru ?? Shuro ko wannensu yayi sai kallonta da sukeyi ,suna karayi ma Allah godiya daya kuɓutar musu da ɗiyarsu........

Kallon Ammi Hamdiyyah tayi tace," Ammi ina su Hibba , ko har yanzu suna barcin ne? Kaɗa kai Ammi tayi tace," ehh suna barci , kema ko zaki dan kwanta ne kiyi barcin ne ???A'a Hamdiyyah ta faɗa tacigaba da faɗin,"Ammi ku faɗamun wai miye yafaru ne ?buɗe baki Ammi tayi zatayi mata magana Mallam Musi yayi saurin dakatar da ita ta hanyar faɗin,"ammm ba komai bane Hamdiyyah , Aljanin da yake jikin kine ya hauro, yabamu labarin irin ƙalubalen da kika fuskanta a gidanki , sannan ya kuma faɗamana dalilin shigarshi jikinki , sannan kuma ya ƙara tabbatar mana da cewa shine ya ɗaukeki ya kai ki can wata uwa duniya , ya ɓoye ki , shi yasa muka nemeki muka rasa ki kwata_kwata..........

Shuru Hamdiyyah tayi tunanin abubuwan da suka faru da ita ta shiga yi, cikin tsantsar mamaki ta zaro ido tace,"baba yanzu kenan dama

Please Login or Register in order to submit comment