Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk wani abu da yafaru bayan tafiyarshi Lagos har izuwa yanzu da ya dawo gareta , sosai tayi mishi murna takuma ji daɗi sossai da cigaban da tasamu , kallonshi tayi tace," amma Faisal naji mamaki da har izuwa wannan lokacin bakayi aure ba , duk da cewa yanzu kana da halin auren mace fiye da daya ma ........
Ɗan numfasawa yayi yace," hmmmmm Hamdiyyah Haka Allah ya tsaramun kuma naji daɗin hakan , domin ko ba komai Allah zai cika mun burina na mallakar ki , kuma zan kasance kece mace ta farko da na fara sani , duk da cewar ƴan mata da yawa sun nuna ra'ayin aurena , amma sam ban basu fuskar hakan ba , domin ke kaɗai nake gani a idona , dalilin da yasa banyi aure bake kenan Faisal yaƙarasa maganar gamida sakin murmishi, itama murmishi tayi gamida faɗin," Nagode ƙwarai da soyaiyyar da kake mun Faisal ........

Numfasawa yayi yace," naji abubuwa daban_ daban akan Rayuwar gidan aurenki wasu na yarda wasu banyarda ba , faɗamun ya abun yake menene yafaru .....???

Ƙwallace tafara fita daga idanuwanta tafara dadin," Faisal haƙiƙa nasha wahala , naji jiki matuƙa , na gwammaci mutuwata akan rayuwata, nan Hamdiyyah tafara labarta mishi komai na gidan aurenta bata boye mishi komai ba har rayuwarsu Hibba duk sai da ta faɗa mishi har izuwa yanzu da take zaune gidan Mallam Musa dalilin su Hibba ..........

Bayan tagama shuru faisal yayi har ta kammala zance ta , Wasu hawayen tausayi suka zubo a fuskarshi , haƙiƙa ya jinjina rashin imani irin na Alhaji tanim , ya kuma tausaya ma rayuwar masoyiyarshi da kuma su Hibba matuƙa , hakan yasa tausayin su Hibba ya shigeshi sossai ,yakuma ƙara jin soyaiyyar Hamdiyyah ta shiga cikin ranshi , domin ta hanyar aurenta ne zai wanke mata baƙin cikin da ta kunsa a cikin gidan Alhaji tanim........

"Murya a sanyaye Faisal yace ," Hamdiyyah inaso kiyimun alfarma guda ɗaya , dan Allah dan Annabi in har munyi aure inaso in ɗauki yaran nan gaba ɗaya su mu zauna tare dasu , ciyarwarsu tufatar dasu , makarantar su , komai nasu inaso yadawo wuya na , domin zan riƙesu tamkar yaran da na haifa a cikina , wallahi bansan meyasa ba soyaiyyar yaran ta shiga cikin raina , kuma nasan tausayinsu ne yasa naji soyyaiyarsu , dan Allah a bani su kinji sai mu haɗu dani dake mu kula dasu muhaɗu mu basu duk wani farin ciki da suke buƙata a cikin duniyar nan inshallahu ........

Tsabar tsananin daɗi da murna Hamdiyyah batasan sanda ta rugumi Faisal ba ta fashe da wani irin kuka mai kunshe da dalilai da yawa, cikin kuka tace," bansan da wani irin baki zanyi maka godiya ba , wallahi tallahi kamar kasan yaranan rayuwata ne , banajin zan iya yin nesa dasu kwata_kwata , su ɗin sun zama tamkar jinina , ka gama mun komai matuƙar zaka zauna dani da yaranan , Nagode sossai sossai Allah ya saka da Alkhairi masoyina , yanda kake da burin faranta mun nida yaranan kaima ina roƙon Allah ya faranta maka kaima ..........

"Sossai faisal yaji daɗin haka , rungumar da tayi mishi sai da tasa yaji wani irin shokin a jikinshi , a hankali ya cireta daga jikinshi gudun matsala , ya ce," kiyi Shuru kidaina kukan hakan ya isa kinji yafaɗa cikin tattausar murya irin ta masoya..........

Nan fa suka ɗan fara taɓa hirarsu na yaushe gamo, har sukayi sallama , bisa da yarjejeniyar gobe zai dawo ..........

Jin Shuru_Shuru Hamdiyyah bata dawo ba yasa Baba mariya ta tashi tace," uhmm Ramatu bamuga ta zama ba wallahi tashi zanyi na leƙa yarinya nan nagani ko waye yazo gurinta , ƴarinya tun_tuni kusan fin awa , gaskiya kam Ammi ta faɗa , tashi Baba mariya Tayi da niyyar fita, tsayawa tayi ganin Hamdiyyah ta shigo cikin gida cike da farin ciki ........

Nan su Baba mariya suka cigaba da tambayarta ko waye , nan ta labarta musu komai da duk yanda sukayi da Faisal ɗin , sossai sukayi farin ciki da abun sai ɗan kunya da ta kama Ammi tace," ohh na cima yaron nan mutunci yanzu ga abun da yazo yafaru , gashi yadawo bai gujeta ba yadawo gareta , kaga soyaiyyar gaskiya ,ni wallahi ban ma san ta inda zan fara kallonshi na bashi haƙuri ba, kai ban kyauta ba sossai Ammi taji duk ta tsani kanta domin ta cimma yawon mutuncin ,nan Baba mariya ta cigaba da karfafa mata gwaiwa kancewa ai komai ya riga da ya wuce abun da yafaru ya faru , da haka suka ci gaba da murna da farin ciki musamman Hamdiyyah kam ba'a magana........


Bayan Mallam Musa yadawo ne suke sanar mishi duk yanda Hamdiyyah sukayi da Faisal , sossai shima yaji daɗin wannan lamarin ya kuma bisu da fatan Alkhairi .......


A ɓangaren faisal kuwa ko bayan ya koma gida nan ya faɗa ma Mahaifiyarshi duk yanda sukayi , kasancewar mahaifiyarshi mata ce ma sauƙin kai haka yasa bata wani jaa da lamarin ba ta bisu da fatan Alkhairi da kuma fatan samun farin ciki mai ɗorewa.........


Bayan wasu kwanaki soyaiyya ce mai ƙarfi ta sake shiga tsakanin Hamdiyyah da Faisal hatta su Hibba duk sun sanshi Kuma sun shaƙu domin in fita
zata Hira to dasu zata ɗunguma su fita suyi ta hira suna raha da Faisal , hakan yasa shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu .........

A gurguje

Abubuwan da dama sun faru ciki kuwa har da tsaida ranar auren Hamdiyyah da Faisal da akayi akan watanni biyu , Hmmm murna a gurin masoyan ba'a magana , domin ji sukeyi tamkar su janyo ranar ne tazo, su kasance tare .......

Tun kafin asaka ranar Aure Hamdiyyah ta duƙufa gyaran jikinta tuƙuru ,domin Farantama masoyinta Faisal , domin da taimakon *Mum fu'ad* take aiwatar da duk wani gyaran jikinta kama daga gyaran jiki gyaran HQ da duk wani gyara da amare sukeyi , kunsan *mum fu'ad* ba baya ba wajen sanin sirrikan gyara ciki da waje , haɗe da kula da miji da kuma tsan_tsa iya zaman aure ta ko wani ɓangare ,hakan yasa Hamdiyyah ta koma gidan *Mum fu'ad* da zama dan a gyareta da kyau dakyau saboda burin faranta ma masoyin ta Faisal ........

Tanƙasheshen gida Faisal ya siya musu wanda zasu sakata su wala tare dasu da yaransu wato su Hibba, hmmmm tsayawa faɗin kyau da tsaruwar gidan ɓata lokaci ne, domin gidan yayi matuƙar kyau da tsaruwar gaske .........


Bayan wata biyu a yau ne dubbanin jama'ah suka shaida auren Faisal da Kuma Amaryarshi Hamdiyyah.........

Bayan ɗaurin Aure misalin ƙarfe shida na yamma aka kai Amarya Hamdiyyah katafaren gidanta dake Rayfield, sossai Hamdiyyah tayi kuka musamman tunawa da tayi da rayuwarta sai taƙara fashewa da kuka gwanin ban tausayi.....

Duk yanda Hamdiyyah taso tafiya da su Hibba a ranar sam Baba mariya ta hana , a cewar ta za'a kawo su bayan sun gama cin amarcinsu sai a kaisu ,badan Hamdiyyah taso ba,dole ta amince da hakan........

Bayan ankai Hamdiyyah kai tsaye Faisal ya nufi cikin gidan cikin tsananin murna da farin ciki ..........

Kai tsaye ɗakin Amaryarshi ya nufa , ko bayan ya shiga cikin yin duk wani tsari Abu da addinin musulunci ya tanadar , kafin daga bisani ya aiwatar da sunnar ma'aiki Sallallahu Allaihi wasallam......

Tarawa da faisal yayi da Hamdiyyah wato sex , ya matuƙar kasancewa cikin farin ciki ,domin ji yake tamkar budurwa aka kawo mishi , sossai ya dinga sanya mata Albarka domin ta shayar da shi daɗi matuƙa .......

Bayan kwana biyu Hamdiyyah duk ta damu kan cewa Ita a kai mata su Hibba , Amma Sam Baba mariya taƙi yarda tace sai an kwana biyu , bayanda Hamdiyyah ta iya haka ta haƙura.........

"Bayan sati biyu aka kawo ma Hamdiyyah su Hibba sakamakon nacin Hamdiyya take tayi musu , nan aka haɗa musu kayansu dukkansu aka kaisu , murna a gurin Hamdiyyah ba'a magana sosai taji daɗin ganinsu , shima Faisal yaji daɗin ganinsu matuƙa ..........

"Bayan kwana biyu hmmmm sossai sossai su Hibba suke samun kulawa , walwala farin ciki da kuma Annashuwa duk sun hada , basu da wata matsala ko kaɗan a gidan , kullum cikin farin ciki suke , sai dai kewa Ilhama da sukeyi , ta ɓangaren faisal kuwa kulawa sossai sossai yake ba yaran tamkar yaran cikin shi , makaranta mai tsada Faisal ya saka yaran , haka yasa suka mai da hankali sosai akan karatunsu, sun manta da rayuwarsu ta baya , Faisal da Hamdiyyah sun rike yaran Amana tamkar yaransu na cikinsu , a yanzu ne Hamdiyyah take ɗanɗana daɗin aure , kuma Kullum cikin yima Allah godiya take.......

A gurguje

"Bayan watanni tara Hamdiyyah ta haifi santaleliyar ƴarta mai kama da ita , kulawa sossai yarinyar take samu , soyaiyyar da su Hibba suke nuna mata kuwa ba'a magana, kullum suna manne da ita , shaƙuwa ce mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu........

Bayan shekaru uku Hamdiyyah ta ƙara haifan danta Namiji , shima haka suke kulawa dashi sossai , yaran sun zama Tamkar yaran Mutun ɗaya , babu nuna banbanci ko kaɗan tsakaninsu , kullum cikin kaunar juna da kyautata ma juna suke , kullum soyaiyyar su Hibba ƙara shiga zuciyarta sukeyi , a kullum cikin yima Allah godiya take kan sauyin da yayi mata da kuma canjin dayayi mata ita da su Hibba ,hakika shigowar ta rayuwarsu Hibba Alkhairi ne a garesu , kuma tayi matuƙar jin daɗin haka , domin Allah ne yasa ta shigo cikin rayuwarsu dan taimakonsu .........

A haka suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da walwala da kwanciyar hankali da kuma ƙaunar juna da kuma tausayin juna, Arzikin Faisal kuwa a koda yaushe kara nunkuwa yake Albarkacin rikon marayu da yayi..........

*KUYI HAƘURI DA SOME TYPING ERRORS*


*TAMMAT BIHAMDULLAH*

*ALHAMDULLILLAH!! ALHAMDULLILLAH!!!ALAHAMDULILLAH!!!*


*ALLAH NAGODE MAKA DA KA BANI DAMA DA IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI NA GUGUWAR ANNOBA , ABUN DA NAFAƊA DAIDAI ALLAH KA BAMU LADA , AKASIN HAKA KUMA ALLAH KA YAFEMANA , DA HAKA NAKE CEWA KU ƊAUKI DARRUSSA MASU YAWA A CIKIN WANNAN LITTAFIN , MU ƘARA GINA RAYUWAR MU CIKIN TAFARKI IRIN NA ADDININ MUSULUNCI , MU JI TSORON ALLAH MU KUMA KIYAYEYI SON ABUN DUNIYA DA KUMA RUƊIN SHEƊAN ,ALLAH YASA MUFI ƘARFIN ZUCIYARMU AMEEN SUMMA AMEEN*,

*KAR KU MANTA WANNAN LITTAFIN DA GASKE YAFARU , SAI DAI ƘARI DA ƊAN RAGI DA NAKEYI , DA HAKA NAKE CEWA NA BARKU LAFIYA ,MU HADU A CIKIN SABON LITTAFINA MAI SUNA*

*MATAN GIDA*


*SUBHANAKAL LAHUMMA ,WABI HAMDIK ,NASHADU AN LA'ILAHA'ILLA ANTA, NASTAGFIRUKA ,WANA TUBU ALAILAK ,WA AKIRU DA'AWA NA ANILHAMDULILLAHI RABBIL ALMIN*


*STORY AND WRITTEN BY ZAYNERB MUHAMMAD KABIR (MUM FU'AD JOS)*

*ƊAN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁATA AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386348*

*MA'ASSALAM*👏👏👏

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment