Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, nan kawun Hamdiyya yafara faɗin,' to ke Ramatu da kika kama kika turomun wannan mutumin inason in miki tambaya ɗaya , Kinga dai Kamar yanda Hamdiyyatu take ɗiyarki haka nima take ɗiyata tunda ƴar ɗan uwana ce to gaskiya kafin ace mun Amince da wannan mutumin yanada kyau ace an yi bincike mai zurfi akanshi gaskiya , sannan Abu na biyu Ni a matsayina na uba a gurin Hamdiyyah zan tambaye ta ko tana sanshi ,domin in bata sanshi gaskiya baza'ayi mata dole ba , sai abu na uku yanada kyau a samu lokaci ayi komai a tsanake kar muyi gaggawa ko ba haka ba ?

Tunda yake maganar Ammi take yi mishi wani irin kallo kafin daga bisani tace," gaskiya Mallam Musa kana da matsala wallahi , inji dai wannan yarinyar ƴaa tace, kuma bazan taɓa zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba , ai gaka gata sai ka tambaye ta ai ko tanaso ko bataso , sannan maganar bincike, Ni ai yariga yafaɗamun komai , duk inda yake da zama da iyayensa da kuma aikin shi da sana'arshi duk nasani, sai kuma maganar da kake ce wa wai ayi komai a tsanake , yoo kai banda abunka mallam Musa in Allah ya kawo mijin mai za'a jira , maganar nan dai duk ka barta kawai , Ni dai a matsayinka na ƙanin mahaifinta kawai ka yarda su turo ayi komai a wuce gurin ,Ni banga abun da za'jira ana ɓata lokaci akai ba .......

Shuru Mallam Musa yayi daga bisani yaɗan numfasa gamida kallon Hamdiyyah yace," Hamdiyyatu tsakaninki da Allah kinasan wannan mutumin dan kwanakin baya naji ance kuna soyaiyya da Faisal ɗan gidan Mallam Sani , to Ni abun da ya ɗauremun kai bam san da wannan mutumin ba , Amma ace lokaci ɗaya ya fito neman auranki gadan_gadan , bayan kuma nasan akwai wanda yake neman ki , saboda haka ki faɗa mun gaskiya .......

Shuru Hamdiyyah tayi idanuwanta yafara kawo ruwa , ƙoƙarin haɗiye hawayen da ke barazanar zubo mata a ido tayi , ido ta kai kan mahaifiyarta ....
Nan Ammi tayi mata nuni da ido ta ɗan ɗaga kanta Alamar tace Eh....

Nan Mallam musa ya gyara murya yace,"ke nake sauraro ina jinki!!

A hankali ta ɗago kai Alamar ehh , ganin yanayin ta yasa Mallam Musa sakin murmishi yace," hmmmm Hamdiyyatu tsakaninki da Allah kike faɗamun kuwa? kaɗa kai taƙara alamar ehh ......

Murmishi yaƙarayi irin nasu na manya yace," Hmmm to shikenan tashi kije Allah yayi miki Albarka ,Ameen ta Amsa dashi ,gamida tashi jiki a sanyaye ta bar ɗakin......

Bayan ta fita nan Mallam Musa ya kalli Ammi yace," Ramatu nasaki sarai wallahi , Anya ba tursawa yarinyar nan kikayi ba kuwa akan ta amince da auren nan? wata uwar harara Ammi ta galla mishi tace," bangane ba me kake nufi da wannan maganar ?

Murmusawa yaƙarayi irin nasu na manya yace," Hmmm Ramatu ni ba yaro bane , wallahi daga yanayin yanda ta amsa mun nasan ba'asan ranta bane , dan Allah ina roƙonƙi karki jefa rayuwar ƴarki cikin mawuyacin hali , karkiyi mata abun da za'a zo daga baya ana danasani , in kinsan yarinyar nan bata san aurenan gara a haƙura har Allah ya kawo mata wanda ranta ya aminta dashi amma kar ayi mata dole .......

Cikin faɗa Ammi tace," wai kai wani irin mutum ne ? Inji dai ai a gabanka yarinyar nan ta amsa ? an faɗa maka banfika santa bane da zaka dinga faɗamun haka ? kaga ba fa dole sai ka karɓa auren yarinyar nan ba ,ga jama'ah dayawa a gari , dama ganin kai ne ƙanin mahaifinta yasa na turoshi gurinka, amma inba haka ba mai zai sa na zo gurika , zaka yarda ko bazaka yarda ba ?

Kaɗa kai yayi , yana me jinjina hali irin na Ramatu yace," shikenan Allah ya tabbatar da abun da yafi Zama Alkhairi , zanyi bincike akanshi in anga ba wata matsala sai a tsaida maganar aure.....

Kai wallahi kana da matsala yoo wani bincike za'ayi ne wai , kaga nifa nariga nace ya turo iyayenshi gurinka kawai, ya kawo sadaki ayi komai a wuce gurin kawai , meza'a jira ......

Cikin rashin fahimta yace," wai ke meyake damunki ne? Naga da Alama mutumin nan ya bi ya siyeki da kuɗi ko, binciken ne baza'ayi ba, Bayan haka Manzo Sallallahu alaihi wasalam ya koyar mana cewa ayi bincike kafin aure , Amma zakice baza'ayi ba ? Cikin faɗa ta hayaiyyaƙo tace," ehh na faɗa na kuma bawani binciken da za'ayi.......

Shikenan Ramatu na yarda ayi yanda kikeso , Amma wallahi kisani duk abun da ya biyo baya Babu ruwana , sannan ki kuka da kanki na faɗa miki,duk sanda kikayi niya iyayen nashi sai su zo su sameni in yaso sai ayi duk yanda kikace , yana faɗin haka ya tashi ya fita , gamida yi mata sallama .......

Mita Ammi tadinga yi daga bisani ta tashi , gamida kiran Hamdiyyah suka tafiya gida ......

Masifa sossai Ammi tadinga yi ma Hamdiyyah acewarta ita taja har ya gane yake farfaɗamata magana , ita dai Hamdiyyah bata ce komai ba......

Bayan sun koma gida ne ,Ammi ta kira Alhaji tanim, cikeda da zumuɗi take shaidamishi cewar ya turo, iyayenshi,cike da zumuɗi yace," To to Alhamdulillah , za su zo jibi in badamuwa......

Cikeda gamsuwa Ammi tace," eh badamuwa Allah ya kaimu jibin , godiya yayi mata daga bisani ya kashe wayar cikeda farin ciki .......


Ƙaramin gidane mai ɗauke da ƙaramar ƙofa , ginin gidan ginin laka ne , duk gidan ya tsufa .....

Motar Alhaji tanim gamji ce ta faka a ƙofar gidan,kai tsaye ya shiga cikin gidan ......

Ga mamaki wani ɗan Dattijo da a ƙalla zai kai shekaru hamsin zuwa hamsin da biyar a duniya, da ka ganshi kaga tsohon banza zaune yake a ƙaramar taburmar dake ƙaramin tsakar gidansu , yana taunar goro , ɗayan hannunshi kuma riƙe da sigari yana zuƙa....

Ganin Alhaji tanim yasashi washare bakinshi da duk ya ɓaci da sigari da goro , da murmishi a fuskarshi yace," A'a sannu da zuwa Alhaji ,yau kaine tafe a gidan namu , Ehh nine ya faɗa a taƙaice , washere baki ya ƙara yi yace," yoo inji dai wani auren ne naka ne ya kuma tashi , dan kuwa in ba neman aure zamuje maka ba nasan ba ganinka nake ba, batare da ya amsa mishi ya kalleshi yace", biyoni mota Alhaji tanim ya faɗa a taƙaice , ai dole dole na biyo ka yafaɗa gamida ƙoƙarin tashi ya bishi a baya .....

Shiga cikin mota sukayi , nan Alhaji tanim ya gyara zama ya karkato ya kalli dattijon yace,"harɗo kana jina da kyau? Yanda aka zaba za'ayi sa dai a wannan karan yasha banban da sauran domin wannan kawunta nada matuƙar tsauri kuma bashi da san abun duniya , inaso ka nemo manyan mutane , wanda baza su bamu kunya ba , wanda zasu mlnuna Dattaku sossai, sannan banaso azo a samu wata matsala , karka lalata mun aure! Karki lalata mun aure!, Wannan karan Yakamata ku kula dakyau , yanzu kafaɗi nawa kake da buƙata? kuma nawa kake ganin zai isheku , wanda zaku siya manyan kayan da zakusa , da kuma motocin da zaku haya da kuma sauran abubuwan buƙata ......

Cike da fariin ciki harɗo yace,"Allah ya taimake ka ai ba yau aka fara harkar nan ba , kuma bamu taɓa saɓa yanda ka faɗa mana ba ,wannan ba wata matsala bace, kana ganin mutane kamar nawa zan hayo?

Nazari Alhaji tanim ya fara kafin daga bisani yace," eh to ina gani karmar mutum uku zasuje ko? Sai kai na huɗu, nawa kake da buƙata?....

Ehh to kaga zamu nemi motoci Masu tsada , kuma kaga dole mu nemo abu mai tsoka muba masu hayin mota ,cewar harɗo .....

Saurin dakatar dashi Alhaji tanim gamji yayi ta hanyar faɗin," harɗo Ni bance ka tsaya mun lissafe_ lissafe ba kai sai kace yau muka fara wannan harkar kawai kafaɗamun nawa ne zai isheku komai da komai .....

Washe baki harɗo yayi yace," to inaga ko dubu ɗari biyu ma zaiyyi ,sai musiya manyan kaya na Alfarma da zamu saka .....

Cikin nuna Alamun ko in kula Alhaji tanim ya curo maƙudan kuɗaɗɗe a Aljihunshi ya miƙa ma harɗo yace," ga wannan dubu ɗari biyar ne ka tabbatar komai ya tafi dai_dai, wasu kuɗin ya ƙara curo yace," wannan kuma sadaki ne ......

Jiki na rawa harɗo yasa hannu ya ƙarɓa fuskarshi cikeda farin ciki , yana faɗin," ai Alhaji bakada matsala inshallahu za'ayi komai ma fiye da yanda kace, cikeda jin daɗi Alhaji tanim yace," to shikenan , sai abu na biyu inaso ka faɗa ma mai ɗakinka itama in da yuyuwar ta shigo wannan safgar sai ta shigo , kace mata zan nemeta in lokaci yaya , inaso zata jaa a Matsayin mahaifiya ta , fattan baza'a samu matsala ba ?

Cikeda da farin ciki harɗo yace," Ah cigaba kenan ai ba wata matsala da zata bayar zatayi duk yanda kace kuma zan mata magana ......

Nan suka tsara duk yanda zasuyi, Alhaji tanim ya tsara duk abun da zai faɗa, daga bisani sukayi sallama Alhaji tanim yaja motarshi ya tafi cikeda farin ciki ......

Tunda Alhaji tanim yasa maganar auren Hibba a gaba ya ma manta da lamuran ƴaranshi , bai damu da sanin halin da suke ciki ba , bai ya zuwa duba su ,duk da cewar ko adaa ɗin ma ba kula dasu yake ba bare kuma yanzu, kamar ko yaushe haka suke cigaba da rayuwar ƙuncinsu .......

Washe gari Harɗo ne cikin wata lafiyaiyyar mota ƙirar venza , zaune yake akan siddin ɗin masu zaman banza , sai mai tuƙa mota , baya kuma manyan mutane ne su biyu duk sun sanya manya_manyan kaya masu tsada a jikinsu , fuskokinsu sanye da fararan sirrin gilashi, haƙiƙa harɗo sun ɓadda kama matuƙa ,faka motar sukayi daidai ƙofar gidan Mallam Musa kawun hamdiyyah, fitowa sukayi daga bisani suka shiga cikin gidan........

Zaune Mallam Musa suke a ƙatuwar taburma, Mallam habu ne a gefe wanda yake ƙani ne shi a gun kakan Hamdiyyah , sai ɗaya gefen gashi Mallam Ahmadu ne wanda yake cikakken amininshi .......

Shigowa sukayi cikin yanayi irin na na manya Alhazawa , kai kace da gaske Alhazawan gaske ne, nan kuwa tsoffafin najadu ne......

Tarba ta mutunci sukayi musu daga bisani duk suka samu guri suka Zazzauna......

Shidai Mallam Musa kallonsu kawai yakeyi , domin haka kawai ya ji jikinshi bai aminta dasu ba,da ganin yanayinsu yasa ya kasa sakin jiki dasu , nan suka yi gaisuwar irin nasu na manya daga bisani suka yi duk abun da zasuyi suka bada sadaki Naira dubu dari uku.....

Ganin kuɗaɗɗen da suka bayar da sunan sadaki yasa Mallam Musa faɗin,' bayin Allah ai ba siyar da ƴar mukayi ba da zaku kawo wannan kuɗi yayi yawa .......

Murmusawa harɗo yayi yace," kayi haƙuri amma haka yaro yabamu mukawo , sabida haka kayi haƙuri ku karɓar , ba'a mai da hannun kyauta baya, Ai mace tafi ƙarfin miliyan ɗaya ma domin kuwa darajar mace ya wuce misali, saboda haka kuyi haƙuri ku karɓar kawai ......

Nan su Mallam habu da Mallam Ahamdu suka saka baki , Mallam Musa ya karɓar badan yaso ba .......

Harɗo ne ya ɗan ƙara numfasawa daga bisani yace," to sai kuma muna ɗan neman wata ƴar Alfarma a gurinku , to wani alfarma kenan? Cewar Mallam Ahmadu,muna jinka , in da hali dama inaso a taimaka a yi bikinan nan da wata ɗaya , harɗo ya faɗa bisa umarnin Alhaji tanim gamji .......

Cikeda rashin fahimta Mallam Musa yace," ikon Allah wani irin Alfarma ne wannan ? yaza'ayi kazo da wanan buƙata , in ta ɓangaren ku kun shirya ai mu ba lallai mun shirya ba tunda ƙarfin mu da naku ba ɗaya ba ne ......

Murmusawa harɗo yayi kafin daga bisani yace,"Mallam Musa ai wannan ba wani damuwa bane , babu matsala , dama yace," in faɗa muku wai ku bar komai basai kunyi komai akwai komai a gidanshi basai kun wahalar da kanku ba , Allah ya rufa asiri za'asa komai inshallahu ba wani matsala bane wannan ......

Shuru Mallam Musa yayi kafin daga bisani yaɗan numfasa yace," to gaskiya bana tunanin hakan zai yiyu , amma zamuyi shawara da mahaifiyarta akan haka yanda tace haka za'ayi, zan tuntuɓeta inji inshallahu.......

Cikeda jin daɗi harɗo yace," to shikenan mu zamu koma , tashi sukayi gamida ƙoƙarin miƙewa, gamida yin sallama suka tashi suka tafi....

Bayan sun tafi batare da ɓata lokaci ba Mallam musa ya kira mahaifiyar Hamdiyyah ya shaida mata duk yanda sukayi ......

Cikeda da gamsuwa da farin ciki Mahaifiyar Hamdiyyah tace," A'ah Alhamdulillah , masha Allah ,ai hakan ma yayi , ƴarinya tayi goshi , wato komai zaiyyi , shikenan kaga an hutaccemu ma shikenan , Ammi ta faɗa cikeda farin ciki .......

Numfasawa Mallam Musa yayi kafin daga bisani yace," amma Ramatu kina ganin hakan yayi kuwa? Gara ma ayi ma yarinyar nan ko Babu yawa kodan mu siya mata mutunci , amma haka za'akai ƴar babu komai ??

Sallati Ammi ta rafka daga bisani tace," Musa ,baƙin ciki ƙarara zaka nuna mun fisabilillahi?, kaga Allah yayi ma ƴata nasibi shine zaka ce wai A'a dan kaga kai naka ƴaƴan ba'a musu haka ba , to nidai wallahi yanda yace haka za'ayi tunda ai shi yace ba wai roƙanshi mukayi ba , Shuru Mallam musa yayi daga bisani ya ce," to shikenan Allah ya rufa asiri , ga kuɗin sadakin ƴarki sai kizo ki ƙarɓa , yana faɗin haka ya kashe wayar cikin ɓaci rai .......

Murna sossai Ammi tayi game da faɗa ma Hamdiyyah duk yanda akayi , ita dai Hamdiyyah batace komai ba sai Binta da kallo da tayi , domin tayi ma kanta Alƙawarin bazata ƙara cewa komai ba a sha'anin bikin duk yanda mahaifiyarta tayi shikenan......

Tun biki ya rage saura sati Alhaji tanim ya ƙara gyara gidanshi , inda ya gyara ɗayan part ɗin yasaka komai na buƙatar rayuwa , ya kashe kuɗi sossai a sha''anin bikin , hakan kuma sam bai dameshi ha , a cewarshi biyan buƙatar yafi dogon buri......

Ganin ana gyara yasa su Hibba suka tabbatar da cewa Abbansu zaiyyi aure , murna sossai suka dinga yi, domin ko ba komai zasu samu Abokiyar tayin hira kuma , aiki zai ragun ma Hibba , Addu'a suka dingayi suna me Allah Allah akawo musu Amaryar......

A ɓangaren ƴan uwan jin auren sukayi a sama , babu shiri duk suka taho cikeda mamakin auren .....

A gurguje

Bayan sati ɗaya A yau Asabar ne dubbanin jama'ah suka shaidai ɗauri auren Hamdiyyah Auwal sa'ad tareda Alhaji tanim gamji......

Haƙiƙa duk wanda ya kalli Hamdiyyah sai ya tausayamata , domin da ka ganta zakasan bata cikin haiyyacinta domin ta ƙara lalacewa ta rame , matuƙar ka ganta bazaka taɓa cewa itace Amaryar ba , domin babu Alamar hakan a tattare da ita. duk yanda taso dawo da hankali ta ,ta gagara , duk yanda Ammi tayi akan ta dinga nuna farin cikinta akan auren amma ta gagara domin daidai da ƙwayar zara bata da buƙatar auren , dan kanta haka Ammi ta rabu da ita ........

Misalin ƙarfe biyar na Yammah lafiyyaiyun motoci suka faka a ƙofar gidansu Hamdiyyah ......

Nan aka fito da Hamdiyya data ke ta sharar kuka kamar ranta zai fita , dan kuwa hawayenta har ya ƙafe tafara numfarfashi , haƙiƙa ba komai ne ke sata kuka ba ,sai tuna wa da take da gaske ita zatayi aure ba tare da masoyinta Faisal ba , haƙiƙa Amminta ta cutar da ita , sai dai kuma ta wani ɓangaren takan tuna da cewa mutum baya tsallake wa ƙaddararshi , domi kan haka Allah ya nufa Faisal bazai zama mijinta ba ,kuma tunda biyaiyya tayi Allah zai bata ladan hakan , da wanan tunanin take ɗan jin sanyi a cikin ranta ......

Ita ko Ammi ko a jiki ta illa murnar da take tayi Hamdiyyah zata shiga cikin daula .......

Nan aka kai Hamdiyyah gidanta , kowa ya watse , akabar daga Amarya sai halinta, inda take ta cigaba da kukanta mai matuƙar tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro , domin tsabar kukan har sai da muryarta ta dashe ......

Su Hibba ko suna ɗaki suna jin hayaniyar mutane , kasancewar mahaifinsa ya gargaɗesu da kar su fito ko ƙofar ɗakin , hakan kuwa sukayi suka kulle kansu a ɗaki, suna jin hayaniyar mutane ........

Misalin ƙarfe tara na dare Alhaji tanim gamji ya shigo gida , hannunshi riƙe da manyan ledodi guda uku yana ta washe baki ......

Ɗakin su Hibba ya shiga ya tarar duk sunyi barci , leda ɗaya ya ajiye musu a ɗaki , daga bisani ya fita , ya nufi part ɗin Hamdiyyah........

Jin ƙarar buɗe kofarshi yasa gaban Hamdiyyah yayi mugun yaɗuwa , ganinshi yasa taji gabanta ya ƙara faɗuwa,wanda bata san dalilin yin haka ba .......

Zama yayi kusa da ita cike da dariyar ƙeta yafara faɗin," Hamdiyyah Hamdiyyah , Hamdiyyah kin shigo hannuna , iko sai Allah , Shuru tayi batare da tace komai ba sai ma sunkuyar da kanta da tayi a ƙasa......

Babbar rigar jikinshi ya cire daga bisani ya ajiye ledodin a ƙasa , ya kalleta yace," bisimillah ki sauƙƙo muci kaza ko?

Jijiga kai tayi , muryarta da take a dashe tace," na koshi.....

Wani kallo ya wurga mata kafin daga bisani yace," kamar ya kin ƙoshi? A'a ki faɗi gaskiya dai , kizo muci kawai......

Kaɗa kai tayi alamar A"a ,A zafafe ya miƙe ya jawota kusa dashi ya kifamata wani gigitaccen mari yana faɗin,' How dear you Zaki dinga challenging dani , common saƙƙo kici ......

Cikeda mamaki Hamdiyyah take kallansu muryarta na rawa ta sa hannu a fuskar tace," kayi haƙuri zanci ,amma me nayi maka zaka mareni? batare da ya jira cewarta ba ya yago kazar yafara danna mata baki , nan ta fara ƙoƙarin kwacewa tana haɗiyewa da ƙyar......

A zafafe ya tashi ya cire babban rigar shi , ya cire ta cikin , jikinshi na rawa ya cire wando jikinshi ya rage daga shi sai singileti da dogon wando .....

Gani shi haka yasa Hamdiyya jikin ta ya fara rawa jikinta ya fara rawa ,tafara fitar da hawaye tana jiran ganin ikon Allah .......

Gadan_gadan ya nufe ta , ya fincike mata gyalan jikinta , ya jawo rigar ta da ƙarfi da tasa rigar yagewa , nan ya wurgamata kan gado , yafara ƙoƙarin rabata da siket ɗin dake jikin ta , wani irin kuka Hamdiyyah takeyi mai matuƙar tausayi , da kyar kukan nata yake fita kasancewar muryarta da ta riga da ta dashe , wani irin jinjjiga tafarayi tafara ƙoƙarin shiɗewa .......

Batare da ɓata lokaci ba Alhaji tanim ya raba Hamdiyyah da duk wani kaya dake ilahirin jikinta , jikinshi na rawa idonshi ya kaɗa yayi jajir, da zarar ka ganshi zakayi tunanin ba 'a haiyyacinshi yake ba .....

Ganin yanayin shi yasa Hamdiyya ƙara tsinkewa da lamarinshi , jikinta ya ɗau rawa ,ganin abun takeyi tamkar a mafarki ......

Nan ya hau kanta gadan_gadan ya mata wani mummunan shigar da yasata sakin wani razanannen ihu ,tunda tayi wannan ihun ta komar da kanta bata ƙara sanin inda kanta yake ba.......

Tunda Alhaji tanim ya shiga Hamdiyyah yake abu ɗaya ba ƙaƙƙautawa , yakai aƙalla a wa uku a kanta, wa 'iya zubillah , bai damu da sanin halin da take ciki ba sam , jini ne ya ɓata ko ta ina , yaɓa ta jikinsh, ya kuma ɓata kan gadon , ganin jini kaca_kaca yasa hankalin shi ya dawo jikinshi ......

Ɗagata yayi batare da da damu da halin da take ciki ba ya nufi toilet ya wanke jikinshi ya dawo kan gadon ta gefe ya kwanta, barcin gajiya yayi awun gaba dashi harda munshari ..........

*TOH ANAN ZAN TSAYA SAI KUTARA A PAID GROUP DAN JIN CIGABA LITTAFIN GUGUWAR ANNOBA , KAR KU MANTA ,YANZU LABARIN YA FARA , YANZU AKA FARA WASAN SHIN YA RAYUWAR* *HAMDIYYAH ZATA KASANCE A GIDAN ? SHIN WAYE ALHAJI TANIM GAMJI?, SHIN MECECE MAKOMARSHI???* *WACECE HAMDIYYAH , SU WAYE HIBBA , WANI IRIN RAYUWA HIBBA SUKAYI DA IYAYENSU , TO SAMUN AMSAR TAMBAYAR NAN SAI KUN BIYA NAIRA ƊARI BIYUN KU KACAL DAN CI GABA DA KARATUN LITTAFIN GUFUWAR ANNOBA*

*HMMMMMM KAR KU BARI ABARKU A BAYA ƳAN UWA*

*DAN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁATA AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386347*


*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*




*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 21 & 22*

Kiran Assalatu ne ya fargar da Alhaji tanim dayake ta sharar barcinshi hankali kwance........

Batareda damuwa da halin da Hamdiyyah take ciki ba ya kalleta ya taɓe baki ya bushe da wata razananniyar dariya , ya miƙe ya nufi toilet ya ɗaukko ruwa a buta.....

Tsiyaya mata yayi a fuskartar, a razanne ta farka, taja wani dogon numfashi.....

A hankali tafara buɗe idanuwanta ....
Wani irin Azaba taji ya ziyarceta , ta ɗan ƙara runtsa idonta, ganinshi tsaye a kanta yasa jikinta yafara rawa tana karkarwa, idanuwanta na kanshi , zuciyata fal da tsoronshi .....

Idanu kawai ta bishi dashi tana kallanshi , kasa ɗaga ɗan yatsanta ma tayi tsabar azabtar da take ji a cikin jikinta ......

Cikin Wata irin murya yace," ke ki tashi ki gyara gadon da kika ɓata .....
Kasa magana tayi sai bi shi da kallo kawai da takeyi ......

Kan gadon ya nufi ya ɗagota, jikinta na rawa ta runtsa idonta ta na jiran abun da za ƙara aikata mata .......

Ganin zata ɓata mishi lokaci yasa ya yarda ita a kan gadon , ya tashi ya shiga wanka ya shirya.......

Ɗakinshi ya shiga ya ɗebi kuɗaɗen shi masu yawa daga bisani ya ɗauki trolley ɗin shi ya fita , motarshi ya ɗauka bai zarce ko ina ba sai airport.....

Misalin ƙarfe goma jirginsu ya tashi zuwa ƙasar Indiya......

Hamdiyyah kasa

Please Login or Register in order to submit comment