Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Faisal ɗin baya kawo abun Arziƙi gidan yasa ta tsanar Faisal matuƙa a cewarta matsiyaci ne shiɗin.....

A haka Rayuwa ta dinga tafiya ma Ammi da kuma Hamdiyyah har izuwa yanzu da Hamdiyyah take auren Alhaji tanim gamji ........

Wanan kenan..


*Cigaban labari*

Washegari da Asuba Hamdiyyah ta nufi ɗakin su Hibba suka fara ƙoƙarin shirya sauran yaran dan tafiya school ........

Cikin ƙanƙanin lokaci suka gama shiryasu suka tafi school, duk da komai Hamdiyyah take ƙarfin hali kawai takeyi , kasancewar zafin da gabanta ke mata , dominda ƙyar ma take takawa .......

Lura Hibba tayi dayanda take tafiyan a daddafe , hakan yasa Hibba faɗin," Anti Hamdiyyah meke damunki ki , naga tun ɗazu kina tafiya da ƙyar ko baki da lafiya ne??

Murmishi yaƙe Hamdiyyah tayi tace,"A'a Hibba ta , babu komai kawai jiki na ne naji babu daɗi, badan Hibba ta gamsu ba ta amsa da to Allah ya ƙara sauƙi , Hamdiyyah tace,"
Ameen .......

Nan Hamdiyyah ta zauna a ɗakinsu Hibba har barcin wahala yayi awun gaba da ita ......

Ko da Alhaji tanim ya gama shirinshi tsaf , bai bi ta kansu ba ya ɗauki keyn motarshi ya fita.....

Jin yafita yasa Hibba jin daɗi matuƙa tana Addu'ar Allah kasa yayi tafiya ne ma kar yadawo , da wannan tunanin itama barcin wahala yayi awun gaba da ita .......



A gurguje bayan watanni biyu , Ammi ce zaune a tsakar gida tana tsintar shikinkafa , tsintar take a zahiri amma kuma sai dai tunaninta duka yana kan Hamdiyyah, kasa ɓoye maganar da takeyi a zuci tayi inda har takai ga ta furta maganar tana faɗin," ohh ni Ramatu !! Ace Tunda kayi ma yarinya aure ace babu ko tsinke bata taɓa aiko mun dashi ba, kuma ma ko ɗan zuwa gaishenin nan bata taɓa yi ba , yoo in ma bata zo ba ai mijin nata dai yazo yaɗan bani kuɗi amma shuri kakeji ......

Dogon Numfashi Ammi taja taci gaba da faɗin," Annya bazan je gidan da kaina ba in ɗebi ne ɗeba ,haba ai nayi kawaici nayi kawaici su basu gani gaskiya inaga da kaina zanje Ni gidan .......

Ta cigaba da faɗin,' kai ko kuma kar dai inyi gajan haƙuri barin in jira nan da watanni uku tunda yanzu watanni biyu ne, Ai wata ɗaya kamar yau ne. Wallahi in basu zo ba Ni da kaina zanje har gidan in ci musu mutunci, haka dai ta dinga mita har tagama tsintar shinkafa ......

Ƙawar Hamdiyyah taka zo taduba inda tayi tayi ta Hamdiyyahtav bari a faɗa ma Ammin ta halin da take ciki amma sam taƙi yarda .....

Matuƙar tazo gidan to sai dai in mijin na gari , domin kuwa in baya gari sai dai tagama bubbuga ƙofarta amma ba halin buɗe wa dan basa ji sam ,kuma wani lokaci yakan tafi da keyi ɗin gidan har indiya ya barsu su kaɗai ......

Duk yanda taso Hamdiyyah tabari A faɗa sam taƙi a cewarta ita tana tausayin su Hibba bazata iya tafiya ta barsu ba da wanan dalilin ne har ƙawar tata ta amince da hakan amma badan taso ba ........

Zuwa yanzu dai Hamdiyyah ta fara sabawa da bakar Azaba gidan Alhaji tanim gamji, Haƙiƙa duk wanda ya kalli Hamdiyyah sai ya tausaya mata domin ta canza tayi baƙi tamkar ba ita ba........

A gabanta zai kawo ƙaruwar ya shiga dasu ɗaki ya kwanta da su tana kallo sai dai ta rufe idonta , duk da ta rufe idonta kunneta sukan jiyo mata ihun so a lokacin da suke aikata Alfashansu , matuƙar tayi yunƙurin Tafiya to fa tashi ga uku dan kuwa da yagama zai ta shi ya mata mugun duka kamar yasamu jaka , domin abun kaɗan zatayi yayi mata dukan tsiya , sai dai tayi ta kuka su Hibba sukata bata haƙuri ........

Bayan yagama kwanciya da karuwan ne shima zai jawo ta ala dole ya kwanta da ita Kuka sossai takeyi domin tana tsoron shigar cuta jikinta , matuƙar tayi mishi gardama haka zai sa su zaneta su tuɓe mata kayan jikinta su wurgata akan gado ya danneta ya biya buƙatarshi a dole , haka tana ihu amma sam bazai ƙyale ta ba .........

Ganin haka yasa karuwan suka fara jin shawa'awar yin maɗigo tare da Hamdiyyah wa'iya zubillah , da zaran yagama da ita zasu fara roƙon shi akan ya Amince suma su ɗan ɗana.......

Shiri yayi kafin daga bisani yaki Amincewa da ƙudirinsu , duk yanda suka so roƙonshi fur yaƙi yarda , badan sun so ba suka haƙora dan ba yanda suka iya.......

Yana gamawa zasu wurgata falo su rufe ƙofar su suyi barcinsu hankali kwance.........

Sai dai Hamdiyyah tayi kuka kamar ranta zai fita , tana me ƙara dana sanin zuwanta duniya ...........


*Hmmmm kuyi manage da wannan*

*muje zuwa*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 33 & 34*

Bayan sati Biyu Alhaji tanim gamji ya koma ƙasar Indiya, don cigaba da gudanar da aikinsu ........

Tsafe _tsafensu sukayi kafin daga bisani Babban su wato Azarfakinzu yafara faɗin," to tanimu gamiji wannan karon aiki yadawo kanka, kasani muna yi maka abun da kakeso , kaima kuma kana yi mana abun da mukeso , mun baka kuɗaɗen masu yawan gaske , kaima yanzu anzo gareka, yarinyar da ka aura kasan ita zaka sadaukar mana domin dama mu muka saka auren , sabida haka ya ake ciki ??nasan Anyi Auren ko? To yanzu muna buƙatarta .........

Wata shu'umar dariya Alhaji tanim yayi kafin daga bisani yace," Azarfakinzu ai kasani aiki na bana wasa ,kuma bana wasa da alƙawarin ka , bana karya alƙawarin ƙungiya , inaaaa!!ban manta ba ,wannan karan itace mace ta ta goma daidai da zan kawo muku , kuma baza'a taɓa samun Matsala ba nayi alƙawari wannan karan ma haka za'ayi , so nake a wahala ta kafin a gama da ita domin ta bani wahala wajan aurenta , babu yarinyar da nasha wahalar kamarta , sabida , kafin ta Amince dani ta ban wahala , sabida haka ita ma yanzu dole mu wahala muma na rama abun da tayi mun nima ......

Take suka tuntsure da wata shu'umar dariya kafin daga bisani Azarfakinzu ya dake ya cigaba faɗin," yanzu abun da za'ayi zamu fara aika mata da mugun Aljanin da zai dinga firgita ta , da zaran ta firgita tayi ihu to shikenan zatafara ciwo , a hankali tana jinya tana jinya mu kuma sai mu dinga zuƙe jininta har ya rage gangar jikin , kaga mungama da ita kenan, a lokacin da kuma ta mutu ina da yuyuwar Amfani da wasu sassa na jikinta to zaka kawo mana ita muyi Amfani dasu ......

A tare suka bushe wata mahaukaciyar dariya mai tsoratarwa da firgitarwa matuƙa ga duk kunnuwan da suka saurareta.......

Bayan sun gama dariyar shuru ya biyo baya kafin daga bisani Alhaji tanim yace," to shikenan angama hakan yayi daidai ....

Nan suka gama tsubbace_ tdubbacensu kafin daga bisani kowa
ya watse ........


Bayan kwana biyu ... Misali ƙarfe goma na dare Hamdiyyah na kwance a kan gado tana barci duk ta baje tana sharar barcin wahala.......

Cikin mafarki ta ne wani mutum ne sanye da farin ƙyalle a jikinshi , fuskarshi bata baiyyana ba sai dai fararen kayan jikinshi, cikin murya irin taraɗa yake faɗin,"Hamdiyyah!!!! Hamdiyyah!! Hamdiyyah!!!! Ki dage da Addu'ar ki dage da addu'ar , kafin daga bisani ya ɓace ɓat...........

Firgit ta miƙa a barcin tana karanta innalillahi wa inna illaihir raju'un , tana miƙewa tafara mutsitsika fuskarta , wata zufa ce tafara karyo mata tsoro duk ya kamata , tunani ta shiga yi shin mafarki ne ko kuma a zahiri ne, to wanene wannan? Dayake cewa ta dage da Addu'a, ko ma menene inshallahu zan dage da Addu'a ......

Jikinta na rawa ta miƙe ta shiga bayan gida ta ɗauro alwala tayi sallah tayi Addu'ointa masu yawa, lokaci ɗaya taji nutsuwa ta zo mata, Tsoron ya kau daga zuciyarta , gadonta ta koma ta cigaba da sharar barcinta hankali kwance .......

Misalin ƙarfe biyu na dare ,cikin wata iriyar murya mai matuƙar tsoratarwa da firgitarwa wa ce tafara kiran Hamdiyyah!!!!!!!!!! Hamdiyyah !!!!!!!!! Hamdiyyah!!!!!! Cigaba da barcinta tayi harda juyi da munshari , muryarce taƙara faɗin,"Hamdiyyah!!!!! Cikeda kuwa da kururuwa murya take ta Ambaton sunan ta ........

Kamar a Mafarki taji ana ƙwalla mata kira......

A hankali ta fara buɗe idonta , cikin Muryar barci take faɗin," *A'uzubillahi minashaiɗanin rajim, bismillahi Rahmanir Rahim,* shine abinda bakinta ke furtawa .......

Waige_waige ta fara tana son saurar ko Kiran da takeji da gaske ....

Takai kusan mintuna Biyu tana jiran ko zata sake ji an kira sunanta , Shuru taji ansake kiran sunanta ba, hakan yasa ta ƙara shafe jikinta da Addu'o'i ta gyara kwanciyarta kafin daga bisani ta kwanta barci yayi awun gaba da ita ......

Haka tacigaba da barcinta batare da tsoro ko wani firgici ba ........

Washe gari da Asuba Hamdiyyah ta tashi ta nufi ɓangaren su Hibba suka yi aikinsu kamar yanda suka saba .......

Tun safe da Hamdiyyah takejin wani ir a jikina ga matsanancin ciwon kai , cikin karfin hali take komai ba tare da tabari Hibba ta gane halin da take ciki ba , duk abun da takeyi ƙarfin hali ne , duk yanda ta so daurewa abun ya gagara ciwon kan ƙara tsananta yakeyi matuƙa, hakan yasa ta nufi ɗakinta ta kwanta ko zata samu sauƙin ciwon kan .....

Ganin Hamdiyyah ta tafi ɗakinta barci yasa Hibba tunanin ko lafiya dan tasan bata tafiya ta barta ita kaɗai ba tare da wani dalili ba Hakan yasa ta bita da Addu'ar Allah yasa lafiya .......


Bayan kwana biyu.......

Abubuwa da dama sun faru , ciki kuwa harda sauyuwar Hamdiyyah , sossai Hamdiyyah take fama da ciwon kai mai zafi, ga ƴan gane _gane da takeyi , sossai Hibba take bata kulawa matuƙa , hankalinsu duk ya tashi ganin halin da take ciki...,...

Da ƙyar take iya komai , kullum sai taji ana ambaton sunanta in tana barci , taimakon ta ɗaya bata firgici ko ihu ,sai dai ta ɗan tsorota haɗe da Addu'a A bakinta , hakan yasa Allah yake taimakonta bata yin ihu ko tsoro akan kiran da takeji....

Duk yanda Hibba taso ta gane wani abu sam Hamdiyyah ta hana , indan Hibba ta tambayeta cewa take babu komai gudun kar ta shiga damuwa .......

Sossai Hamdiyyah ta shiga cikin ruɗani , abun dake faruwa na matukar bata Mamaki ,hakan yasa ta tashi tsaye da Addu'a sossai........

A bangaren Kungiyar su Alhaji tanim gamji kuwa......
Duk yanda Ƴan ƙungiyar su ka kai ga turamata manyan Aljanu akan su razanata dan ta firgita sam taƙi firgita ,a duk lokacin da take tsoro sai ta ambaton sunan Allah , hakan yasa Allah yake kareta ,domin da ta sake tayi ihu shikenan burinshi zai cika akanta, tai makon ta ɗaya tana ƙoƙarin Addu'a ko yaya A bakinta , sossai ta dage da yin Azkar ɗin Safiya da maraice ........

Wasa wasa har ankai sati ɗaya wato kwana bakwai kenan, ciwon kan nata ya kara tsananta harta kai da bata iya ƙwaƙwaran motsi sossai ......

Wasa wasa Har ankai sati biyu Hamdiyyah na fama da ciwon.......

Duk inda ta kalla sai taji kamar mutum a tsaye yana ambaton sunanta ko da safe ko da rana ko da dare , *la'ilaha'illa Anta subhanaka inni kuntu minazzalim* ,shine abun da bakinta ke iya furtawa , da zarar ta fada sai taji anyi shiru .......

Hakan dayake faruwa da ita na bata mamaki matuƙa, ita dai ta barwa Allah koma menene Allah zaiyyi mata maganin duk abun dake faruwa ........

Ƙungiyar su Alhaji tanim gamji kuwa , Ganin basuyi Nasara ba yasa Azarfakinzu ya sake wani sabon shirin akan Hamdiyyah , hakan yasa suka ƙara nemo ƙasungumin Aljanin da zai sa Hamdiyyah ta tsorata matuƙa ........

Kwance take cikin dare tana barci , wani irin hayaƙi ne baƙi ƙirin ya shigo cikin ɗakin Hamdiyyah , take wani irin halitta ya baiyyana mai matuƙar tsoratarwa da firgitarwa.........

Cikin wata kakkausar murya ya fara ambatan sunanta ........

Barcinta taci gaba da yi ba tare da da ta farka .........

Wata irin iskace mai ƙarfi ta taso, take wani farin hayaƙi ya baiyyana a cikin ɗakin Hamdiyyah .....,..

Nan da Nan hayaƙin ya riki ɗe yakoma Mutum mutumin , domin shi ba mutum ba shi ba Aljani ba , fuskarshi dai bata baiyyana ba, sanye yake da farin ƙyalle irin na wancan lokacin ........

Cikin wani irin yare da wata iriyar murya yake faɗin,"kai kai!! Miye damuwarka ne?? meyasa bazaka taɓa barin bil _Adama su huta bane , yanzu me wannan Yarinyar tayi maka da kakeson cutar da ita .?

Wannan bakin Alhaji ne ya buɗe bakinshi yafara magana , wani baƙin hayaƙi na fita a bakin shi yake faɗin," cikin murya irinta doddani yace," yazakazo ka shigarmun aikina, Nima uban gida nane ya aikoni ba zuwan kai na nayi ba , sabida haka babu ruwanka kabari in aiwatar da abun da ya kawoni kawai.......

Cikin murya irinta tsawa yace," karka kuskura ,kar ka yarda ,ka koma kacemusu baza ka iya ba , in kuma kaƙi yarda Ni ɗinan nasan abun da zanyi maka kai ma kuma kasani basai na faɗa ba .........

Take yayi wani irin kuwa da kururuwa cikin ɓaci rai ya yayi wani irin jijjiga ya ɓace ɓat a gurin ........

Nan ɗaya Aljanin ya kalli Hamdiyyah da take ta sharar barcinta, tausayinta ne maƙil ya kamashi , cikin ranshi yake faɗin," zuciyarki nada kyau yarinya , bazan iya bari a cutar dake ba , sabida haka Ni nasan abun yi , yana faɗin haka ya sa hannunshi ya dafata nan take suka ɓace su su biyun da Hamdiyyah da shi ɗin ..............

*Hmmmmm muje zuwa, yanzu wasan yafara*

*Kar kumanta labarin nan true life ne, sai dai ɗan ƙari da ragi da nakeyi a wasu guraren*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 35 & 36*

Washe gari da Asuba Hibba taji Shuru_shuru Hamdiyyah bata fito ba.......
Ganin haka yasa ta yanke shawaz zuwa duba ta ko lafiya , ko kuma jikin nata ne har yanzu .........

Fita tayi da Niyyar zuwa duba ta bayan ta sa musu ruwan wanka ........

Har ta nufi ƙofar ɗakinta wata zuciyar ta raya mata ko ta barta ta huta, ba mamaki barci takeyi yau , tunda ba lafiya ne da ita ba ........

Haka yasa ta juyi ta koma ɓangaren su ta cigaba da aikin ta ita kadai , zuciyarta fal da tunanin Anti tasu ko lafiya.......

Bayan ta gama shirya su Nihal ta kaisu school ,ta dawo ta ƙara sa aikin gidan tas, ta gyara ko ina , tayi musu break fast , ta karya, Shuru tana jiran fitowar Hamdiyyah, duk a tunaninta barcin gajiya da wahala takeyi ga kuma ciwon kai , tunawa da hakan datayi ne yasata yanke shawarar barinta tayi barcin tana me tausayinta matuƙa , tasan tana jin jiki domin dalilin da zai sa Anti Hamdiyyah tayi barci bata fito ta tayata aiki ba to gaskiya babban dalili ne , da wanan tunani ta kara jin garama ta barta kawai basai ta tashe ta ba har sai ta tashi da kanta , Binta da fatan samun sauki tayi zuciyarta fal da tausayinta..........

Hibba ba ta huta ba sai da ta ɗaura Abincin Rana a cewar kar Hamdiyyah ta tashi ta samu aiki tayi ƙoƙarin tayata tunda ita ba ishashen lafiya ba , shiyasa ta kammala duk wani aikace aikace na gidan tana jiran tashinta a barci , hmmmm Abunka da yarinya ƙarama ..........

Misalin Ƙarfe shaɗaya na rana Hibba taga shuru_shuru Hamdiyyah bata fito ba , hakan yasa taɗan dara tsorata tana me tunanin Anya lafiya kuwa ???

Dan jinkirtawa tayi da zuwa dubatan tace zuwa sha biyu in bata fito ba sai kawai ta shiga ta dubata.........

Shuru_shuru Hibba na zaune tana jiran fitowar Hamdiyyah , ganin har sha biyu tayi ne yasa ta tashi a tsorace da damuwa baiyyane a fuskarta haɗe da tashin hankali ta nufi ɓangaren Hamdiyyah ..........

Ko da ta nufi ƙofa dakin ƙirjinta buga wa yakeyi tana tsoron shiga gudun ganin mai zata tarar itadai fatanta Allah kasa tana lafiya .........

Sallama ta fara yi , jin Shuru bata amsa ba yasa ta ƙara tsinkewa da lamari , bubbuga ƙofar ta fara amma shiru ba'a buɗe ba ........

Hannu tasa ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin....
Ga mamaki taga ƙofar ta buɗe , Ajiyar zuciya ta sauƙe ganin ƙofar a buɗe ba'a kulle ba .......

Kutsa kai cikin falon tayi tafara kiran sunanta , Anti !!Anti!! Shuru ba'a amsa ba , hakan yasa ta kutsa kanta cikin uwar ɗakinta tafara dube dube , Amma batga kowa a kan gadon ba ........

Tsoro ne ya bala'in kamata , jikinta na rawa tafara dudduba ko ta in a cikin dakin Amma babu Hamdiyyah babu Alamarta , ƙwala mata kira ta shiga yi kamar zararriyya, ƙara leƙa toilet ɗin ta tayi ko zata ganta Amma inaa Shuru babu labarin ta .......

Sossai hankalinta ya tashi tafara dube dube ba ƙaƙƙautawa ko ta ina bata ganta ba , har inda ma mutum bazai iya zama a gun ba Hamdiyyah ta leƙa Amma Shuru Bata ganta ba .......

Hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka , tana faɗin," shikenan shikenan Ta tafi ,Ta tafi Anti ta tafi waiyyo Allah , cikin matsanancin kuka Hibba kemagana mai matuƙar tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro , cikin kuka ta cigaba da faɗin," Anti Hamdiyyah Ina Kika tafi? Anti Hamdiyyah ki dawo dan Allah, Anti Hamdiyyah na roƙe ki ki dawo , waiyyo Allah na waiyyo Allah , kuka take sossai kamar wacce aka aiko mata da saƙon mutuwa ........

Duk girman gidanan haka Hibba ta zageyeshi tsaf tana dudduba Hamdiyyah , tana kuka .......

Takai a ƙalla Awa ɗaya tana duba ko ina ,amma babu Hamdiyyah babu labarin ta .......

Gajiiyar da tayi da nemanta ne yasa ta zauna a tsakar gidan tana ta sharar kuka tana maganganu masu matuƙar tausayi .......

Sallamar ƙannenta ne ya dawo da ita da matsanancin kuka da takeyi , da gudu taƙarasa gurinsu ta rungume su dukkansu, cikin matsanancin kuka take faɗin,"Anti Hamdiyyah Anti, Antinmu batanan banganta ba naduba ko ina ban ganta .......

Nan danan dukkansu suka fashe da kuka kamar sun haɗa baki .......

Cikin tsamin baki da muryar kuka Ilhama take faɗin," Anti Hibba Anti Hibba kinemo mana Antinmu ina tace bazata tafi ta barmu ba ko ???

Wasu hawaye Masu zafi ne suka zuba a ƴar karamar fuskar Hibba tace," Ihlam bansan inda zan nemo ta bansan inda taje ba bansani ba taƙarasa maganar gameda fashewa da matsanancin kuka ........

Cikin ƙarfin hali Hibba ta rarrashi ƙanen nata , itama tashare hawayenta tace," kuyi Shuru kinji inshallahu Atinmu zata dawo gida kunji ko yanzu muje na saka muku Abinci kunci kunji??

Batare da since komai ba jiki a sanyaye suka bita a baya suna cigaba da kanan kukan su abun tausayi ......

Abinci ta zuzzuba musu Amma babu wanda ya iya ci a cikinsu , daƙyar da lallami Hibba ta sa sukaɗan taɓa Abincin badan ransu naso ba .......

Bayan sun gama cikin ƙarfin hali Hibba ta cire musu uniform ɗin jikinsu ta gyara gurin , ta kai kayan gunrin wanki tafara wanke wa tana kuka , tana tuna Hamdiyyah ,da yanzu ita zata wanke su tace ta huta , domin tunda tazo gidan Hibba ta daina wanki kwata kwata sai yau .......

Kuka sossai Hibba takeyi tana me tunanin Hamdiyyah fal cikin ranta ...,...

Bayan tagama ta zauna ta rafka uban tagumi cikeda jimami......

Daƙyar tasa ƙannenta suma suka fito da homework ɗin sukayi , domin jikinsu duk a sanyaye yake matuƙa, badan sun so ba sukayi Homework ɗin.....

Wunin Ranar Haka suka kasance cikin jimamin rashin Hamdiyyah da tashin hankali ... ...

Hibba kam takasa daina kukan , hakan yasa kanta yafara mata ciwo sossai , ƙoƙarin tsagaita kukan tayi gudun kar ta illatar da kanta ........

Ko Abincin dare bata bi ta kai ba , dan ma akwai sauran na rana Kasancewa basu ci

Please Login or Register in order to submit comment