Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

are very stupid , kinsan yanzu 'karfe nawa ne? da zakice zaki mana break fast ,ke har kinsamu damar ma dazaki kwanta kiyi barci batare da kin mana abun karyawa ba .........

Shuru tayi jikinta na rawa , hawaye na zuba a fuskarta .........

'Kwafa yayi yafice ranshi a matu'kar 'bace......

Daukansu yayi ya fita dasu , suka nufi restaurant , suka ci abinci.......

Bayan ga fita wani matsanancin kuka Hibba ta fashe dashi tana me 'kara jinjina hali irin na mahaifinsu , ha'ki'ka badan tana tausayin 'kannenta ba kuma tana tausayawa irin rayuwar da zasu Shiga ba da tabbas sai ta bar gidanan ko ta samu Inda zata huta taji dad'i koda na kwana d'aya ne a rayuwarta......

Kuka tayi sossai ganin kukan bazai fisheta ba yasa ya mi'ke ta nufi kitchen tafara 'ko'karin d'aura musu abincin rana.......

Kwance take a kan gado tana ta tunani , wasu hawaye masu zafi suka zubo mata a fuskarta .......

Ringing wayarta ta farayi , ganin sunan da ya baiyyana akan screen d'in wayar yasata sakin wata ajiyar zuciya ........

'Dauka tayi muryar a sanyaye tace," Asslamu alaikum! wa alaikumu salam shima ya amsa murya a sanyaye......

Hamdiyyah yakamata ki fad'amin abun da ke faruwa ,tun da nazo gidanku naga yanayinki nasan wani abu na damunki ,dan Allah ki fad'amun kin barni cikin damuwa da tashin hankali , sannan kin sa hankalina ya'ki kwanciya, ki tausayama zuciyata dan Allah ki fad'amun menene?

'Ko'karin danne zuciyarta tayi , taja dogon numfashi tace," Faisal , ka tayani da Addu'a Allah kasa kar a rabamu ,domin ala'kata dakai tana daf da rabuwa.......

Wani mummunar fad'uwa gabanshi yayi jin ta ambaci rabuwa , mi'kewa yayi yace," ban gane abun da kike nufi ba , bakyaso na ne ?

Yazakace bana sanka kaidai kawai ka tayani da addu'a , faisal wallahi inasanka , ina 'kaunarka , nidai, addu'arka kawai nake bu'kata ,cewar Hamdiyya tafad'a cikin matsananciyar damuwa..........

Batareda da ta 'kara magana ba tayi saurin kashe wayar wani matsanancin kuka ya ku'bce mata ........

Jin kukanta yasa Ammi tayi saurin shigowa d'akin tace,"ke Hamdiyya meke damunki kika zauna kina ta sharara kuka ke dawa kuma?

Cikin muryar kuka take fad'in," Ammi dan Allah karki rabani da faisal ina sanshi wallahi ,Ammi kiyi hakuri kar ki rabani da shi dan Allah dan Annabi tafad'a cikin matsanancin kuka ......

Wata uwar harara Ammi ta gallamata tace,"shegiya dan ubanki akan wannan matsiyacin kike kuka , shine har ina shigowa da sauri na , to kita kukan ki ke ki ka sani tafad'a had'e da sa da'n yatsanta ta zungure mata kai .......

Wani kuka Hamdiyya ta'kara fashewa dashi ........

A 'bangaren Faisal kuwa jin hamdiyyah ta kashe wayar yasashi furzar da wata iska mai 'karfi , cike da damuwa yace," to me hakan ke nufi ,Kodai mahaifiyar hamdiyya bata sona ne? ganin bashi da amsar tambayar yasa ya tashi yayi wanka ya nufi majalisar su ko hankalinshi zai kwanta .........


Bayan kwana biyu , 'yan matan Alhaji tanim gamji suka tafi gidajansu a cewarsu zasu je hutu za suyi kwana biyu.........

Batare da ya damu ba ya basu ma'kudan kud'i suka tafi........

Ganinsu d'auke da trolley na tafiya yasa hankalin Hamdiyya ya kwanta cikin ran ta take fadi'n," ko ba komai hankali na zai kwanta da zan huta da bakar azaban da nake ci na jwana biyu nan.......

Misalin 'karfe biyar na yamma , Alhaji tanimu gamji yayi wanka yayi shigar manyan mutane, da ka ganshi ka ce mutumin Allah ne .....

Sanye yake da fararen kaya , yasha malum_malum , hannunshi Sanye da farin agogo , ga ha'korin makanshi sanye a ha'korinshi fari sol, takalmin 'kafarshi ma fari Sol ne , ga kuma siririn farin gilashin fuskarshi .......

Kai tsaye ya d'auki motarshi...
bai zarce ko ina ba sai rikkos are'a ......

Tsayawa yayi a daidai bakin layin su Hamdiyya, ya nemi layin ne da taimakon wani mataccen 'kadangaren tsafin shi dake cikin aljihun motarshi.......

Ganin kar a ya 'bata ma kanshi lokaci yasa ya 'kara curo 'kadangaren tsafin.....

kallanshi yafara yi yana wani irin yare mai wuyar fassarawa ,irin nasu na matsafa....
take 'kadangaren yafara komawa jajawur.....

Zaune take a d'aki tana cin abincin , a zabure ta mi'ke ta d'auki hijabinta tafara 'ko'karin sakawa .......

Ganin tana shirin fita yasa Ammi ta kalleta tace," ke miye hakan kin haukace ne ? ko kuma d'an anacen ne yazo naga kin zari hijabi zaki fita?

Cikin sauri tace," A'a Ammi kawai zan d'an le'ka waje ne bazan dad'e ba zan dawo , zan shiga gidansu ikilima ne fa na tuna akwai abun da zan kar'bo ne a gurinta tafad'a tana 'ko'karin fita .......

Cikeda da gamsuwa Ammi tace,"to shikenan kiyi kidawo kar ki dad'e kinji koh? to tace gamida saurin fita ......

Ganin ta tsaye a kofar gida yasa ya tuntsure da wata shu'umar dariya yace," dakyau dakyau Azarfakinzo aikinka na kyau .........

Da sauri ya fita a cikin motarshi ya nufi gurinta .....

Cikin sanyin murya yace," Assalamu Alaikum , yafad'a kamar mutumin arziki .....

Wa alaika salam tafad'a a ta'kaice .......

Amm 'yan mata dan Allah in ba damuwa inaso ki d'an bani lambar wayarki.....

Lambar wayata kuma?kagamu bawan Allah nan ,daga ganina kace na baka lambar wayata , ni ban sanka ban ta'ba ganinka ba kace na baka lambata ?tafad'a had'e da galla mishi wata harara.......

Murmushi yayi daya baiyyana farin ha'korin makanshi da ba ko yaushe yake sashi ba sai in ba yazo neman aure ba.....
kallanta yayi yace," Amma ai yanzu kin ganni ko , so zaki iya bani ai ?

Turo baki tayi tace," uhmmm ni ban da waya to.......

Murmishi ya'karayi yace," baki da waya? Ehhh tafad'a had'e da juya kanta gefe .......

Okay d'an jirani pls inazuwa ,yafada' gamida yin sauri ya nufi gurin motarshi ya bud'e , aljihun motar ya curo wata sabuwar waya a kwalli , 'kirar infinix hot ten (pro).....

Gurinta ya nufa , ya mi'ka mata wayar yace," to gashi dan Allah ki kar'ba , akwai sim card da komai da komai a cikin ......

'Karema wayar kallo tayi tace," A'a wallahi hazan kar'ba ba nagode ,nima inada tawa ......

Amma fa ke kika cemun baki da waya yanzu kuma kince kinada ita , kinsan dai ba kyau 'karya ko? yafad'a had'e da murmishi a fuskarshi ......

Tsaki taja tace," Msstt sai kayi ai , ni ka ga tafiyata , tafad'a gamida shigewa gida.......

Da kallon mamaki ya bita , yayi murmishi , had'e da nuna alamun ko in kula ya juya ya Shiga motarshi ya bar layin......

Gida ta shiga cikin fushi had'e da yin mita ......

Da kallon mamaki Ammi ta bita tace," ke kuma fa? Kedawa? Ko ikiliman ce ta 'bata miki rai ,kika shigo kike ta mun mita?....

Cuno baki Hamdiyya tayi tace," Ammi inama naje gidansu ikiliman , ban ma je ba , wani 'katon mutum ya tare ni a kofar gida wai na bashi lambar wayata , kin ganshi ne ? wani 'kato dashi? Kuma bissa ga dukkan alamu cewa zaiyyi yana sona, ta cigaba fa fad'in," kuma ma kinsan miye , har wata babbar waya ya curo ya mi'ka mun wai tunda nace ba ni da waya wai in kar'ba inyi amfani dashi .......

Tunda Hamdiyya ta fara magana Ammi bakinta yake a bud'e.....

Cikin Sauri ta katse Hamdiyya da fad'in," yanzu kin ba shi lambar taki? kuma ina wayar take? Kuma yanzu ina mutumin yake ?

Cikin nuna Alamun rashin ko in kula tace,"tab ni ban bashi ba , kuma ban karbi wayar ba , ni shigowa gida nayi na barshi tsaye a gun , inaga ma ya shiga motarshi ya tafi abinshi .........

*MUJE ZUWA*

*ZAKU IYA FARA BIYAN(PAYMENT) KUDINKA DAN NASAKU A PAID GROUP*

*DON NEMAN 'KARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTU'BATA AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386347*

*DAN ALLAH KU DINGA MUN SHARING MUN*

*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
*&*
*VOTE*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*

🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 11&12*

*Kiyi haƙuri rashin jina kwana biyu matsalan wayana ne ,amma yanzu koma yayi daidai inshallahu*


Tunda Hamdiya ta ke magana Ammi take kallonta baki buɗe.....

Wata uwar harara Ammi ta gallamata , ta rafka uban salati tace la ila ha illallahu muhamaddu rasullillahi Sallallahu alaihi Wasallama, ohhh ni ƴasu yanzu a marran nan ka haifi ɗa mai baƙin ciki ƙiri- ƙiri , eh Lallai Hamdiyya na yarda wallahi Allah bakya ƙaunata kwata_kwata, kullum burina kenan a ce Allah ya baki gidan hutu mu huta amma ke sam baki ga wannan ba , Ashe ke ba ƙaramar muguwar bace Azzaluma, hmmmm Lallai Hamdiyyah ,Ammi tafaɗa gamida taɓa baki......

Murya na rawa Hamdiyya tace," wallahi Ammi in kin ganshi ya kusan haifaina, Ammi wallahi bana sanshi , Ni bai mun ba , wallahi bazan iya ko soyaiyya dashi bare na aure shi ba , ke kin ga shi ne , ni kam Faisal nakeso......

Wani gigitaccen mari Ammi ta sauƙe mata a fuskar ta tace wallahi tallahi matuƙar Faisal ba kudi yayi ba wallahi ke dashi har abada , babu ke babu auren shi , kinji na gaya miki , banda iskanci , dan ubanki ana miki kwaɗayin inda zaki huta shine zakije ki jawo ma kanki ƙarin talauci , to ki sani bazaiyuyu in sai da akuya tazo tana ci mun danga ba kinji na faɗa miki, Banda shashanci irin naki me Faisal yake dashi da har zai aureki....

Tsugunnawa Hamdiyyah tayi a ƙasa fuskarta na fitar da ƙwallon haɗe da sakin wani matsanancin kuka tace," Ammi,Ammi dan Allah dan Annabi Ammi karki mun haka , Ammi wallahi inasan Faisal , banasan rasashi ,Ammi dan Allah kiyi haƙuri kar ki rabani dashi....

Cikin faɗa tace," Hamdiyya , wallahi bazaki sani rantsuwa a banza ba , nafaɗamiki kiyi kukan jini ba na ruwa ba , Ammi tafaɗa haɗe da zungure mata kai gamida tafiya ta bar gurin .....

Da sauri Hamdiyyah ta miƙe ta nufi cikin ɗakinta da gudu cikin matsanancin kuka, tana me matuƙar tausayi kanta.....


Misalin ƙarfe takwas na dare hibban ta gama komai tasamu ƙannenta abinci sukaci daga bisani suka kwanta sukayi barci saɓanin ita da take kwance tana tunani iri-iri cikin ranta haɗe da ƙwalla.....

Tashi tayi ta fita falo ta juya hoton dake maƙale a bangon ɗakinsu....

Ganin hoton yasata sakin marayan kuka , haɗe da ƙura ma hoton kallo , cikin muryar kuka tafara magana tana faɗin , waiyyo Allah na , waiyyo Allah na , mommy , mommy kin tafi mommy kintafi kin barmu,kin barmu cikin azababbiyar rayuwa tafaɗa cikin matsannancin kuka....

Kuka sossai takeyi gudun kar ta tashi sauran ƙannenata a barci yasa ta ɗan tsagaita kukan haɗe da yin wata hanmma Alamar barci.......

Wani barci ne yayi a wun gaba da ita.......

Misalin ƙarfe sha biyu na dare Alhaji tanim gamji yashigo gida bayan ya biya gurin hutawanshi da mata....

A wannan ƙaramar yana so ya huta sossai hakan yasa bai ɗaukko kowa sun zo gidanshi da ita ba ......

Bayan ya shigo cikin gidan kai tsaye ya nufi ɗakinshi...

Ganin wutar ɗakin su Hibba a kunne yasa yaja dogon tsaki gamida da faɗin wannan yarinyar bataji tasan dokar gidan ba'a kunna wuta amma sai da ta kunna yau ko , zanga abun da take yi da yasa bata kashe wutan ba .....

Ɗakin ya shiga kai tsaye ...

Buɗe kofar ɗakin yayi , ganin hoton matar yasa shi zaro ido a firirgice , gani yayi tanayi mai gizo kamar tana zaro mishi ido , ga idon ta sunyi jajir.......

Wani ihu yasa , hakan yasa Hibban firgita da sauri ta farka daga barci da takeyi tamiƙe .....

Nuni yakeyi mata da hannu , da sauri Hibba ta juya ganin hoton yasata miƙewa ta tashi tayi saurin juyashi, tana me tsananin damuwa da tsoron karya dokar mahaifinta , tasan yau dinnan ta shiga uku ....

Da sauri ya juya yafita da gudu ya shida cikin ɗakinshi......

Kai tsaye ya haye gadonsa yana numfasawa , fuskar matar na yawo a cikin idamuwashi ......

Duƙunƙuna yayi a bargo yanata haɗa zufa......

Duk inda ya juya sai yaga tana yi mishi gizo......

Cikin tsananin damuwa Hibba tace," ohhh na shiga uku na , ya akayi na manta da hotonan a hana bayan nasan daddy bayaso ya ganshi a daidai.....

Da sauri ta tashi ta koma falo tana tunani yanda zasu wanye da mahaifinta gobe da safe , da haka har barci ɓarawo yayi awun gaba da ita .....

A daren Alhaji tanim ganji baiyyi barci ba domin gizo fuskar tayi ta mishi kamar zai zauce , Allah Allah yayi gari ya waye .......

Ana kiran sallar Asubah yayi sauri ya tashi , yayi wanka ya fita ......

Jin ƙarar mota yasa Hibba faɗin to ko ina Daddy zai tafi da Asuban nan oho .....

Ganin bata da amsar tambayar yasa ta cigaba da aikin dake gabanta kamar yanda ta saba .......


Kai tsaye gurin
hutawanshi (guest house ) dinshi ya nufa ....

Cikin sauri masu kula da gidan suka ƙara so , suka risina haɗe da gaisuwar ban girma ....

Batareda ya kula kowa ba ya nufi cikin gidan ya kwanta a tanƙashashen gadonshi yana numfashi ........

Waya ya ɗaukko ya dailiing number Mikeal, da sauri Mikeal ya ɗauki waya cikin girmamawa yace",Yes sir , ka kawo mun wine mai ƙarfi wacce zata sakani barci yanzunnan, yafaɗa a taƙaice gamida kashe wayar ya koma ya kwanta.....

Cikin ƙanƙanin lokaci Mikeal ya shigo da wine katan ɗaya , yana ajiye wa ya fita batare da ya ce komai ba ........

Bayan Mikeal ya fita yayi saurin miƙewa ya ɗauki wine din ya buɗe ya kafa a baki ya fara shanta kamar mayunwacin zakin da ya shekara bai ci abinci ba , sai da yasha kwalba uku , ya haɗa uban zufa , ga rinannun idanuwanshinan suƙara yin jajawur, take ya yi wurgi da kwalbar ƙarshe wani barci mai nauyi yayi awun gaba dashi ......


Tsaye Faisal yake a ƙofar gidansu hamdiyyah , ganin ya gaji da tsayuwar yasa ya koma ya zauna a dakalin da suka saba zama.....

Ƙara gwada lambar ta yayi amma shiru baya tafiya , ganin wani yaro yazo wuce ta ƙofar gidan yasa yayi saurin faɗin kai yaro! ƙarasowa yarin yayi yace,"ina wuni? Lafiya ƙalau Faisal ya amsa , yaci gaba da faɗin , dan Allah kashiga gidan kace ana sallama da Hamdiyah , to yaron yafaɗa gamida shiga gidansu Hamdiya .....

Assalamu alaikum yaron Yayi sallama , wa 'alaika salamu , wai ana sallama da Hamdiyya yaron yafaɗa ....

Da saurin Ammi ta ƙaraso cikin murna da farin ciki tace," Alhamdulillah , Allah Nagode maka inaga mutumin ranar ne ya dawo kai masha Allah , kallon ta Ammi ta mayar kan yaron tace," kai yaro inji wa? wani ne dai bansan suna shi ba ...

To jeka kace inji wa? Ammi ta faɗa , to yaron yace gamida komawa waje ......

Cikin ɗaga murya Ammi ta fara faɗin ,"ke ke hamdiyyah yarinyar kirki fito maza ki ɗauki gyalenki kije inaga mutumin ranar ne ya dawo maza ki fita, Ammi ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe labilan ɗakin hamdiyyah. ....

Kwance take idonta na kallan sama tana ta tunanin Faisal cikin ranta .....

Cikin tsawa Ammi tace," ke dan Ubanki kina jina damaa maza ɗauki hijabin ki ki fita ana sallama dake inaga mutumin ranar ne ya dawo ....

Cikin faɗuwar gaba hamdiyyah tace," Ammi dan Allah kibar ni wallahi kaina ciwo yake mun tafaɗa murya a sanyaye.....

Kutumar Ubanki keda ciwon kan maza tashi ki fita kinji na faɗa miki ....

Bayan yaron ya koma gurin Faisal yafaɗa mishi abin da Ammi tace , nan Faisal ya shiga tunani cewa ace Faisal ne ko kuwa ya ɓoye sunanshi?

Ganin ɓoyewa baida wani amfani yasa yace," kaje kace inji Faisal .....

Faɗa sossai Ammi take yima hamdiyya,....

Sallamar yaron ce ta katse ta da faɗan da takeyima hamdiyya....

Leƙowa Ammi tayi fuskar ta cike da Annuri tayi saurin cewa yaro wai inji waa? wai inji Faisal yafaɗa cikin Alamun ko in kula.....

Take Annurin dake bayyane a fuskar Ammi ya gushe , wani ashar ta mulmulo tace," kaje kace mishi bazata zo ba in bai bar ƙofar gidan ba wallahi zaiga yanda zanfito inyi dashi .....

Juyawa yaron yayi fita .....

Tunda Hamdiyya taji yace Faisal tayi saurin miƙewa ta tashi a ɗan ƙaramin gadonta .....

Cikin kuka tace," Ammi dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri ki barni naje naga Faisal ko sau ɗaya ne dan Allah .....

Wata harara Ammi ta gallamata cikin tsantsan ɓacin rai batare da ta kulata ba ta shiga ɗakinta abunta......

Wani marayan kuka Hamdiyyah ta sake ta zube a ƙasa gwanin ban tausayi .....

Koda yaron ya isar wa da Faisal sakon shuru Faisal yayi batare da yace komai, miƙewa yayi daga bisani ya tashi ya tafi jiki a sanyaye ......


Bayan su Ajmal sun dawo daga school kai tsaye suka nufi ɗaki suka cire uniform suka ci abinci sukayi sallah suka fito da home work dinsu kamar yanda suka saba ......

Zuba musu ido hibba tayi tana kallansu kasancewar bata iya koya musu ba , dan ma ba laifi yaran suna da ƙoƙari,da kansu sukeyin Home work ɗin saɓanin hibba da bata iya ba ......

Ƙarfe huɗu tafara ƙoƙarin ɗaura musu abincin dare bayan tagama wanke musu uniform da socks da sandals ɗin su ......


Misalin ƙarfe goma na ɗare Abban su hibba yadawo gida tare da karuwar da zata tayashi kwana ... ..

Leƙa ɗakin hibba yayi yaga wutar a kashe hakan yasa kai tsaye suka nufi ɗakinshi da karuwar tashi ......

Washe gari Hibba ta tashi da Asuba kamar yanda ta saba ......

Jin Alamun ihu mace da kukan sangarta da numfarfashi yasa hibba tayi saurin toshe kunnuwanta , ta nufi ɗaki da sauri , domin kuwa ba yau ta saba jin irin ƙananun ihun nan ba domin ko da bata sani ba tasan cewa ana aikata wani abu ne da yake sa matan kukan daɗi.....

Ko da ta shigo ɗaki kuka ta tuntsure dashi tana me kyamatar irin wanan rayuwa tasu.....

Gudun Kar ƙannenta Susan halin da take ciki ne yasa ta gimtse jikinta ta tashi ta fita ta cigaba da aikinta batare da ta ƙara bi ta hanyar ƙofar daddyn nasu ba.....

Misalin ƙarfe bakwai da rabi tagama shirya ƙannenta nan take ta rakasu suka tafi school .....

Bayan tadawo ta cigaba da aikinta kamar yanda ta saba ....

Break fast ta ɗaura musu gudun kar tajama kanta matsala yasa tayi musu ta ajiye musu duk abun da zasu buƙata akan dining, tana ajiyewa ta cigaba da aikinta daga bisani tayi wanka ta shiga ɗaki barcin wahala yayi gaba da ita .....

Bayan Alhaji tanim gamji da karuwar shi sun fito kai tsaye suka nufi kan dining suka fara yin breakfast , chips da kwai ya gani kasancewar yana san chips hakan yasa batare da ɓata lokaci ba suka fara ci ....

Bayan sun gama suka koma ɗaki suka cigaba da aikata Alfashansu........

Bayan sun gama sukayi wanka ya ɗauketa suka fita ........

Misalin ƙarfe shaɗaya Hibba ta farka wani zazzaɓine ya rufeta ,jikinta na karkarwa , ga azababben ciwon kai da ciwon jiki, da ciwon ciki dake damunta.......

Daƙyar ta iya daure wa ta miƙe ta sha magani , lallaɓawa tayi ta koma barcin ......

Misalin ƙarfe daya da kwata su Ilham suka dawo , buga ƙofar sukafara yi shuru hibba bata buɗe ba ......

Kamar a mafarki taji ana buga ƙofar a rikice ta miƙe ta lalubo ƙaramar wayar da take gefenta ta duba taga ɗaya da talatin da biyar , nashiga uku shine abun da ta iya furta wa ....

Tashi tayi da kyar hannunta na riƙe da kanta kamar me layi ta tashi ta fita ta buɗe musu ƙofa .....

Cikin tsamin baki Ilham tace," Anti hibba munata buga ƙofa baki buɗe mana ba, tafaɗa kamar me shirin yin kuka ....

Kuyi haƙuri wallahi banjiku ba ina kwance ne bansan lokaci har ya ƙure haka ba ................


*MUJE ZUWA*

*ZAKU IYA FARA BIYAN KUƊI KU DAN ADDING ƊINKU A PAID GROUP*

*DAN NEMAN ƘARIN BAYANI ZAKU IYA TUNTUƁATA AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386347*

*DAN ALLAH KU SHARING MUN*

*COMMENTS*


Please Login or Register in order to submit comment