Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abincin dayawa ba , hakan yasa bata girka wani ba .......

Haka suka kasance jugunjugun har dare yayi , suka ɗan taɓa Abinci , suna zaune babu wanda yace ƙalla , duk sunyi shuru suna zaune akan kujera , ilhama kuma na jikin Hibba , suna tunanin dawowarta........

Gyangyaɗi suka farayi, nan da nan barci ya kwashe su dukkansu saɓanin Hibba da idonta yake tangararas babu Alamar gyangyaɗawa ma bare kuma barci domin zuciyarta fal take da tunanin Hamdiyyah......

Cikin ƙarfin hali Hibba ta kwashi ƙannen nata ɗaya bayan ɗaya takai su gurin barcinsu ta kwantar da su ta dawo ta zauna gamida shingiɗe wa a kan kujerar tana me tunanin iri_iri cikin ranta ........

A ɓangaren Hamdiyyah kuwa , misalin ƙarfe shida na safe , a lokacin gari bai gama haske ba , wata iska mai daɗi ta ratsata, sossai , daɗin Iskar ne yasa ta farka daga nannauyan barcin da takeyi......

A hankali tafara buɗe ido ta , har ta buɗe su gabaɗaya , ga mamaki sai ta ganta a wani guri saɓanin ƙaton gadonta da tasan ta kwanta akai ......

A firgici ta tashi tana ƙara mutsitsika idonta ko shine baya nuna mata daidai .......

Juya_juye tafarayi tana waige_waige ,ganinta a gadon kara yasata ƙara mamaki matuƙa , *innalillahi wa'inna illaihir raju'un* na shiga uku na me ya kawo ninan ? Shine abun da ta ke tambayar kanta........

Tsoro ne ya kamata matuƙa , jikinta na rawa ta miƙe tafara dube dube hanyar fita a ɗakin .......

Ganin wata ƴar ƙaramar ƙofa yasata nufan gurin kai tsaye .....

Ganin wata ƴar bafulatana a ƙalla zata kai shekaru talatin zuwa talatin da biyar , sanye take da kayan Fulani farare tas , sunkuye take a gindin murhu , ganin matar yasata ƙara tsorata matuƙa tana tunanin abun da yakawota nan , domin ita tasan a gadonta takwanta tun jiya da daddare , Amma yaza'ayi ace ta wayi gari ta ganta Anan , hannun ta tasa a fuskarta ta wanka ma fuskarta mari , a cewarta in ma barci takeyi Yakamata ace tafarka.......

Ganin tabbas eh da gaske ne ba mafarki takeyi ba tsoro ya
sake kamata sossai.......

Juyowa wannan bafulatanar tayi , ganin ta tsaye a bakin ƙofa yasata sakin murmish gamida karasowa gurinta, cikin Muryarta irinta fulani tace,"Sannu da tashi Hamdiyyatu, kin tashi lafiya? Shine Abun da ta tambayeta .........

Ƙasa magana Hamdiyyah tayi saima rawa da jikinta yakeyi , cikin rawar murya tafara faɗin," dan Allah wacce ke , me ya kawoni nan ? Meke faruwa dani? Inasu Hibba , dan Allah ki mai dani gida kar ki cutar dani dan Allah , su Hibba zasu sha wahala su kaɗai ne a gidan , zasu damu sossai in basu ganni ba dan Allah ki taimakeni ki mai dani gida dan Allah , ta ƙarasa maganar gamida fashewa damatsanaci Kuka........

Murmushi bafulatanar tayi daga bisani tace yarinya kiyi haƙuri ki daina kuka , mu shiga ciki zan miki bayani kinji ko kiyi haƙuri ........

Badan Hamdiyyah taso ba ta bita, tana Allah Allah taji yanda hakan ta kasance ...........

*Muje zuwa*

*STORRY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*

*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 37 & 38*

Bayan sun shiga ɗakin ne cikin ƙaguwa Hamdiyyah tace," Dan Allah ki mayar dani gida yanzu haka nasan su Hibba sun damu sossai ........

Murmishi bafulatanar ta ƙara sakewa kafin daga bisani tace," Hamdiyyah ki kwantar da hankalinka wallahi Ni bazan taɓa cutar dake ba, Amanar ki aka kawomin kuma Wanda ya kawomun ke Amana bai bani damar faɗa miki komai ba , har sai ya zo shi da kanshi , kuma ya tabbatarmun a gaban iyayenki zai faɗa duk yanda akayi , sabida haka ina so ki kwantar da hankalinki , kisani Ni ba muguwar bace , ba kuma macuciya bace , nima musulma ce kamarki , sabida haka ina ƙara faɗa miki kar ki damu , anyi haka ne don taimakon rayuwarki kinji ko , ki kwantar da hankalinki wallahi tallahi kinji nayi miki rantsuwa zamanki a wannan gidan rayuwar ki zata shiga cikin bala'i da masifa,babbar barazana ne ga rayuwarki sabida haka ina ƙara jaddada miki kiyi haƙuri ki zauna a nan na wani lokaci ne , zaki koma kicigaba da rayuwarki mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali , ke yarinya ce ƙarama , sannan kwakwalwar ki ma ta yara ce ba komai zata iya ɗauka ba , kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki kinji ko ? Taƙarasa maganar gamida kai hannayenta ta saukesu akan na Hamdiyyah tana ci gaba da bata haƙuri dayi mata nasiha mai sanyaya zuciya .......

Dogon numfashi Hamdiyyah taja , wasu hawaye Masu zafi duka sauƙa akan fuskarta , cikin sanyin murya tace to su Hibba fa , rayuwarsu abun tausayi ce , na zaɓi na zauna dasu ko da hakan zai zama silar ƙarshen rayuwata , yaran abun tausayi ne ,mun riga mun saba dasu , ina kaunar yaran suma suna ƙaunata ,rashina kusa dasu zai sa su shiga cikin matsananciyar damuwa ......

Saurin dakatar da itaa tayi ta hanyar faɗin," Hamdiyyah kafin kizo su kaɗai suke rayuwa, kafin kizo su kaɗai suke zaune a cikin gidansu, nasan dole zasu damu akan rashin ki ,amma kiyi haƙuri naɗan lokaci kaɗan ne komai zaiyyi daidai inshallahu , Addu'a zakiyita binsu dashi har Allah ya kare su akan duk halin da suke .......

Shuru Hamdiyyah tayi gamida sakin wani ɗan marayan kuka tace," to Nagode inshallahu zan ta musu Addu'a har muga Abun da Allah zaiyyi, ta ƙara sa maganar gamida share hawayen fuskar , taci gaba da faɗin,to Anti me suna ki to ??.......

Murmimushi bafulatanar tayi tace," Hmmm sunana ?? Sunana Inna furairah , murmishin yaƙe Hamdiyyah tayi tace Allah sarki .....

Sossai Inna furairah tacigaba da yi ma Hamdiyyah nasiha har Hankalin Hamdiyyh yafara kwanciya , sai dai kuma ta wani ɓangare na zuciyarta cike fal take da tunanin su Hibba ........


Bayan kwana biyu ,ƴan kungiyar su Alhaji tanim ne zaune , dukkanin su sunyi jigun jigun, musamman shi Alhaji tanim .......

Cikin tsantsan ɓacin rai Azarfakinzu yafara faɗin," Tanimu kaɓata mana aiki a karo na farko ,kuma kasani ƙungiya bata ɗaukan Asarar ko ya take , yanzu haka yarinyar nan bata gidanka, duk inda mukayi ƙoƙarin gano inda take sam mun kasa, kasani kungiyaa batasan tausayi ba , ba tasan yafiya ba, sabida haka dole musan abinyi babu abun da ya shafemun da ɓatan ta ,ya ƙara sa maganar gamida yin wani irin huci .......

Tunda Azarfakinzu yafara magana Alhaji tanim ke fitar da wani zufa , idonshi sun kaɗa sunyi jajir ,abun goge zufan dake hannunshi ya Kai kan fuskarshi gamida goge zufar dake fita a fuskarshi yayi ........

Cikin tsantsan tashin hankali yafara faɗin," Azarfakinzu kayimun rangwame , kasan ba'a taɓa samun matsala daga gareni ba , karka manta na sadaukar maka da mutun tara , mutum ɗaya dai bazata gagara ba , bansan inda yarinyar nan take ba , bansan ya akayi har ta fita a cikin gidanan ba ,inaso kayi haƙuri kayi mun yafiya , badan hali na ba .......

Shuru Azarfakinzu yayi kafin daga bisani yaɗago kanshi yace , shikenan zamu ga abu yin, zamu daga maka ƙafa ne badan komai ba sai dan kanayima ƙungiyar hidima sossai , Amma badan haka ba da tabbas sai ƙungiya ta ɗauki ƙwaƙwaran mataki akanka , sabida haka zamu nemi wata hanyar zuwa gobe , kuma duk abun da muka ce kayi dole kayi dan maye gurbin wannan aikin da baiyyuyu ba ........

Nannauyan Ajiyar zuciya Alhaji tanim ya sauƙe gamida faɗin," shikenan Azarfakinzu Nagode sossai , koma ma mene zanyi , Nagode ƙwarai da gaske , da haka suka cigaba da tsubbace tdubbacensu har suka tashi kowa ya tafi .........


A ƴan kwana biyunan Haka su Hibba suka kasance cikin kewa da jimamin rashin Hamdiyyah , badan sun so ba haka suka saka ma zuciyarsu hakuri , kullum cikin maganar ta suna me tunanin halin da take ciki haɗe da Addu'ar Allah kasa tadawo ......


Bayan watan ɗaya abubuwa da dama sun faru , ciki kuwa harda sabawar Hamdiyyah a gidan inna furairah , sai dai kewarsu Hibba da tunanin su da takeyi da kuma tunanin Amminta , haɗe da masoyinta wato Faisal , dayan zuciyar kuma tana me jin tsabar Alhaji tanim cikin ranta.......

Sossai suka shaƙu da juna matuƙa, kasancewar Hamdiyyah nada saurin sabo sossai , kuma Inna furairah ma m janta a jiki sosai kuma tana bata kulawa matuƙa , wannan dalilin ne yasa suka saba sossai tare.......

Tunda Hamdiyyah tazo gidan bata taɓa leƙawa ko waje ba , kuma bata damu da son fitan ba, haka ta ke rayuwarta daga daki sai tsakar gida ita da Innah furairah.......

Sai dai abun da yake bata mamaki Inna furairah Bata taɓa fita da sunan zata siyo wani abu a waje ba, duk abun buƙata akwai shi a Cikin cikin gidan , batare da damuwa da hakan ba ta tattara ta watsar a cewarta koma menene ba ruwanta , ba mamaki kawo mata akeyi in tana barci ko in ta shiga bayan gida, wannan tunanin ne yayi tasiri a cikin zuciyarta.......

A ɓangaren Ammin Hamdiyyah kuwa , Abubuwa duk sun taru sun mata yawa , tunanin ƴar tatace fal cikin ranta , hakan yasa ta yanke shawarar zuwa dubata kota halin yaya.......

Ƙaramar wayarta Ammi ta ɗauko ,gamida da lalubo lambar wata ƴar uwarta wacce suka kai Hamdiyyah ........
Jikinta na rawa tafara kiran layin , bugu biyu ta dauka , bayan sun gaisa ne take mata bayanin komai , nan ƴar uwartata tayi mata kwatancen gidan Hamdiyyah , sossai Ammi taji daɗi , gamida yi mata godiya ta kashe wayar........

Jikinta na rawa ta dauki tsohon gyalenta, ta yafa , gamida fita ta dauki tsohon kwaɗon gidan ta rufe ta nufi gidan Hamdiyyah.........

Bata sha wahalar gano gidan ba , sai dai ta matuƙar tsorata ganin gidan a bayan gari , da tsoro fal cikin ranta ta ƙara sa ƙofar gidan .......

Ganin irin girman gidan yasa Ammin mamaki matuƙa , gamida faɗin," ehh lallai Hamdiyyah ai dole ta manta dani , tunda ana cikin wannan Aljanar duniya ina ko zata tuna dani , to yanzu dai na gano gidan dan ubanta sai na dinga zuwa nima ina dangwalar Arzziƙin tafaɗa gamida sa hannayenta duka biyun tana bubbuga ƙofar gidan.......

A tsakar gida Hibba take ,tana wankin kayansu jin ana buga ƙofar gidan yasa Hibba ta tashi da sauri ta dauko keyn, da gudu ta nufi gurin gate ɗin dan buɗe kofar, tana me Addu'ar Allah kasa Hamdiyyah ce ........

Jikinta na rawa tafara ƙoƙarin buɗe gare din......
Ko da ta buɗe gate ɗin ga mamaki sai ta tarar saɓanin abun da take tunanin , tsayawa Ammi tayi tana kallonta , murya a sanyaye Hibba tace,"ina wuni ? Lafiya Ammi tafaɗa a takáice tacigaba da faɗin," ina Hamdiyyah take ? Je kice mata ga Amminta tazo .......

kuka Hibba ta fashe dashi tace," Amminl Banganta ba , mun dade bamu ganta ba bata gidanan ,muma nemanta mukeyi ........

Zaro ido Ammi tayi gamida faɗin," nashiga uku ina Hamdiyyan ta tafi to ? Babanku yasani ??
Shuru Hibba tayi daga bisani tace," eh bai sani ba ai baya garin kwata_ kwata , kuka Ammi ta fashe dashi tace nashiga uku ina ubannaku ya kaimin ƴata , nasa dai wallahi Hamdiyyah bazata taɓa guduwa ba , Shuru Hibba b
tayi batare da tace koma ba ......

Cikin kuka Ammi ta juya ta fara ƙoƙarin komawa gida tana ta surutai a hanya kamar zararriya.......

Ko da ta tafi bata zarce ko ina ba sai gidan Mallam Musa , da kuka tashiga gidan , batareda da ta gaida kowa ba tafara tambayar ina Mallam Musa ? Mallam Musa dayake kwance yana lazimi ya mike jin Ammin Hamdiyyah a gidanshi , fitowa yayi yace,"Ramatu lafiya kuwa?
Kuka ta sake fashewa dashi ta labarta mishi duk abun da ya faru , tunda ga farko har izuwa yanzu .......

Dogon Numfashi Mallam Musa yaja gamida faɗin," Hmmmm Ramatu to Ni miye nawa ,abu ɗaya zan faɗa miki , duk inda kikasan zaki nemo mana ƴa kije ki nemo mana , sabida ke kikaje kika siyar ɗa ƴarki da hannuki , dan wallahi a wannan karan baki isa ba, domin yanda kike da hakki akanta muma haka muke da hakki akanta , sabida haka kije kinemo ta , in ba haka wallahi sai mun shiga Shari'ah dake, yana faɗin haka ya juya ya shiga ɗaki rai a bace, cike da mamaki ɓatan Hamdiyyah .......

Cikin kuka Ammi tace haba Musa , me yayi zafi haka ? Wacce irin magana ce wannan ? ganin yashiga ɗaki ya barta tsaye a tsakar gida tana ta ɓaɓatu yasata yin, Shuru batare da ta ƙara cewa komai ba ta juya ta fita jiki a sanyayevta cigaba da kukanta.......

Gida Ammi ta koma tadinga rusar kuka tana neman mafita , gamida da shiga tashin hankali matuƙa.........

Washe gari ƴan ƙungiyar su Alhaji tanim ne suka haɗu a gun da suka saba haduwa ...........


*Waiyyo nagaji mu haɗu a next page*

*Muje zuwa*

*STORY AND WRITTEN BY MUM FU'AD*


*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*

*PAGE 39 & 40*

"Mai da hankalinsu dukkansu sukayi zuwa ga Azarfakinzu dan jin abun da zai faɗa......

Mai da kallonshi Azarfakinzu yayi zuwa kan Alhaji tanim gamji yayi gamida fadin," tanimu, duk yanda naso naga na nemo wata mafita dazai maye gurbin Wacce zaka kawo miyi aiki da ita abun yaƙi yayuwa, sai ta hanyar ɗaya zuwa biyu zuwa uku yaƙarasa maganar da kakkausar murya !!!!!

Mai da hankali Alhaji tanim yayi cikin ƙaguwa da rawar jiki yace," ina jinka Azarfakinzu ........

Nan Azarfakinzu ya bushe dawa wata matsananciyar dariya gamida kallon Alhaji tanim yace,"Dole ka zaɓi ɗaya , ko ka sadaukar mana da kanka muyi Amfani dakai , ko kuma mu haukatar dakai in kayi yunkurin barin ƙungiya , sai na ƙarshe ,wanda shine nake tunanin hanyar bada ta dace Kabi , da sauri Alhaji tanim yace , ina jinki mece hanyar faɗamun Azarfakinzu ,kayi amfani da ƴaƴanka ina nufin kayi masu fyaɗe, to jinin da zo zuba a jikinsu shi mukeso ka ɗebi kaɗan ka kawo mana , dashi zamuyi amfani , to wa'innan sune sharuɗan to zaɓi ya rage naka sai ka zaɓi ɗaya Azarfakinzu yafaɗa cikeda rashin damuwa .......

Shuru Alhaji tanim yayi kamar me nazarin wani abu kafin daga bisani ya dago kanshi ya kalleshi da rinannun idanuwanshi da sukayi jajawur yace,"na Amince zan kawo jini, zan aikata wanda kace shine daidai.....

Dariya sossai Arzarfakinzu yayi daga bisani yace yabashi nan da sati biyu , in har bai kawo ba duk hukuncin da ya yanke kanshi daidai ne ......

Cikeda tsoro da tashin hankali Alhaji tanim yace," baza'ayi haka ba , kafin sati biyun ma zan kawo , wannan ba matsala bane nayi maka Alƙawari......

Nan suka cigaba da tsafe tsare su daga bisani duk suka watse .......

Bayan sati ɗaya Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda shirye_shiryen Alhaji tanim na koma ƙasar Nigeria, batareda da fargaba ko tsoron abun da zai aikatawa ƴaƴanshi ba yake shirinshi cikin kwanciyar hankali.......


A ɓangaren Ammi kuwa ,kusan kullum sai taje gidansu Alhaji tanim tana kuka tana tambaya ko babansu yadawo, Amma kullum Amsa daya ce cewa bai dawo ba ......

Sossai Familyn Mallam Musa suka ɗaga ma Ammin Hamdiyyah hankali , hakan yasa ta sake shiga cikin matsananciyar damuwa abubuwa sun taru sun mata yawa , ga wata rama da tayi , duk tazama wata iri , ga rashin kudi a gurinta balle kuma Abinci da zataci ......

Sossai Ammi tashi ga cikin damuwa da tashin hankali , duk ta fita haiyyacinta tazama abun tausayi , tazama tamkar zararriya ,kullum cikin kuka da danasani takeyi .......

Kullum sai Mallam Musa yazo ya ɗaga mata hankali yace duk inda takai musu ƴa su fito da ita , hakan yasa duk bakin Ammi a wannan karan tayi shiru domin koma wani hali ƴarta ta shiga to itace sila , wannan dalilin ne yasa take ƙanƙan da kanta gudun kar Mallam Musa su Kaita ƙara , duk da shima mallam Musa yasa ana bincike sossai ta ɓangaren shi akan Hamdiyyah batare da sanin Ammin ba.......

A ɓangaren Hamdiyyah kuwa sossai take samun kulawa agun Inna furairah,Kullum Burin Hamdiyyah bai wuce taganta a gun su Hibba ba , haƙiƙa ko Amminta bata tunani yanda take tunanin su Hibba, tane me tunanin halin da suke ciki, duk yanda Inna furairah take ƙoƙarin kwantar mata da hankali , sam haka bai hanata kuka da kewarsu ba ......

Wani lokaci takan zama tayi tunanin irin rayuwar ta yanda rayuwa ta koma , kuka sossai take yi musamman in tatuna irin rayuwarta ta baya tana me Addu'ar Allah ya bata ikon cin jarabawarta , sai tayi kuka mai isar kafin daga bisani tayi shiru dan kanta ........

A ɓangaren su Hibba kuwa bayarda suka iya haka suka far sabon da rashin Hamdiyyah , amma kullum suna tunanin ta da maganarta .......

A yau ne Alhaji tanim ya sauƙa a ƙasar Nigeria , kai saye gurin karuwanshi ya nufa kamar yanda ya saba.......

Bayan su gama hutawansu kai tsaye ya kwashe su suka nufi gidanshi .......

Tunda Hibba taji horn ɗin motarshi gabanta ya fadi , tasani cewa yadawo , hakan yasa tayi duk wani abu da tasan yanaso ta kuma kiyaye duk abun da tasan bayaso .........

Ka tsaye suka shigo cikin gida , sam bai bi ta kan su Hibba ba ya wuce ɗakin kai tsaye ........

Washegari , misalin ƙarfe uku na Yammah Alhaji tanim ne zaune aƙaton gidonshi , zaune yake daga shi sai ƴar ƙaramar singlate da karamin boxers, Shuru yayi kamar me nazarin wani abu , kamar a tsinkareshi ya miƙe ya fita , ko da ya fita bai zarce ko ina ba sai part ɗin su Hibba .......

Zazzaune suke suna Assignment ɗin school , Hibba kuma na ninke kayansu da ta wanke jiya , ganinshi a yanda yake yasa Hibba tsorata , gamida sunkuyar da kanta ƙasa ta cigaba da ninkin ta .......

Batare da wani Annuri ko murmushi a fuskarshi ba yace,"ke me kikeyi?? Ya tambayi Hibba cikin isa da ɓacin rai .......

Cikin rawar murya Hibba tace," ninkin kaya nakeyi kana son wani abu ne? Shuru yayi ya bita da kallo kafin daga bisani yace," ba komai shikenan cigaba , yana faɗin haka ya juya ya koma part ɗinshi........

Ko da ya koma zama yayi yayi Shuru ,cikin ranshi yafara saƙe_saƙe iri_iri , cikin ranshi yake faɗin," gaskiya koma menene dole in Nemo mafita , bazan iya zama cikin talauci ko hauka koma in rasa rayuwata ba gaba ɗaya , yazama dole in aiwatar da kuɗiri na akansu , dole in cika Alƙawarin da na daukan ma Azarfakinzu , nan ya cigaba da tunanin shi gamida tsara yanda zai aiwatar da komai ......


Mallam Musa tsaye ne tsaye a kofar gidansu Ammi , Sallama ya Rafka a ƙofar gidan cikin ɗaga murya da ɓaci rai......

Ammi da take zaune a tsakar gida ta rafka uban tagumi majina da hawaye duk sun wankemata fuska tsabar kukan da takeyi , jin sallama ne yasa ta koƙari ta miƙe gamida gyara daurin tsohon zanita daya sha datti, ta miƙe ta fita ........

Cikin Ladabi da ƙanƙan da kai murya a sanyaye Ammi tace," A'a Mallam Musa ashe kaine sannu dazuwa shigo mana .......

Cikin faɗa haɗe da tsawa yafara faɗin",kiyi haƙuri banzo gurinki dan nashiga gidanki ba , nazo ne na tambayeki ki kwatantamun a inda kika siyar da ƴarki , ki kwatanta mun gidan .......

Ɗago rinannun idonta Amma tayi gamida faɗin," Haba Mallam Musa wani irin magana kake haka fisabilillahi yaza'ayi kadinga cewa na siyar da ƴata da hannu na wanan wacce irin magana ce , nima fa abun nan dameni , tunda ko ma mene wannan yarinya ƴata ce tunda duk tsiya ni na haifi Abata saboda haka kadaina irin wa'inna maganganun........

Cikin faɗa da tsawa Mallam Musa yace," Ni bance kimun wata magana ba , ƙarya nayi ba siyar da ita kikayi ba ? Kinasan ƴar Taki kikaje Kika bi son zuciyarki Kika aurar da ita ,ni kar ki ɓatamun lokaci banzo nan dan in tsaya sauraran shirmamamun maganganunki ba da basu da wani Amfani , saboda haka abun da nazo yi shine , ki kwatanta mun inda kikai ƴar ki kika siyar ? Ina ne gidan mijin nata yafaɗa cikin faɗa da tsantsan

Please Login or Register in order to submit comment