Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, tazuba musu suka fara ci ......


Hamdiyya!!! Wai bazakizo ki samu kije kiyi mana cefanenan bane tun_tuni , ko so kike muyi daren girkiin, inda wannan d'an anacen ne yazo ai da yanzu jikinki na rawa kintashi kin fita, ammi tafad'a tana tsaye a 'kofar d'akin hamdiyyah......

Fitowa waje hamdiyyah tayi tana cuno 'karamin bakinta tace," Kai ammi ke dan Allah komai komai sai kifara sako faisal a ciki ni narasa me ya yi miki da bakya sanshi kuma, ni gaskiya ammi shi nakeso shi zan aura , hamdiyya tafad'a kamar me shirin yin kuka......

Wata harara Ammi ta galla ma hamdiyya tace,"dan ubanki tunda kike dashi yata'ba miki kyautar da tafi ta dubu biyar ne ? Kullum hannushi a ma'ke yake , baya sake miki aljihu ,ni yaushe zan zauna saurayi baya bani abun kirki , shasha kawai , kinbi kin li'ke mishi , tir wallahi , ammi tafad'a tana ta'be baki ......

Haba ammi dan Allah ni fa shi nakeso ba abun hannunshi ba , kuma ni bandamu ba dan baya bani kudi,, domin nasan dan dai baidashi ne , da yana da shi da zai bani kuma......

Saurin dakatar da ita ammi tayi tahanyar fad'in," dallah yimun shuru, tunda bashi dashi basai ki rabu dashi ba , shasha kawai , ammi tafad'a tana shirin shiga kitchen .......

In rabu dashi fa kikace ammi? uhmm ammi kiyi hakuri yanzu dai kawo kudin cefanen sai inje inyi cefenan , hamdiyya tafad'a tana shirin sak hijabinta ........

Wani kallo ammi ta wurga mata tace," dan ubanki karki rabu dashi , tafad'a gamida curo kudin ta gefen hannun zaninta ta wurgamata tace,"hungo ni, kuma kiyi maza kije kidawoo.......

Gigiza kai hamdiyya tayi ta tsugunna ta d'auki kud'in ta fita a gidan gamida fad'in na tafi.....

Shuru tayi ba tare da da ammi tace komai ba sai ma binta da harara datayi.....

Bayan hamdiyya ta fita ammi ta fara mita tana fad'in,"yaro sai shegen naci ,ya rabu mun da 'ya ta ya'ki ,in ba maye ba da tsaurin ido me yake dashi me nasama yaci bare yabama na 'kasa zaizo ya bi ya li'kema 'ya ,haba ,ai inshallahu sai nasan yanda nayi na raba su , inda ma ace yaron nan ri'ke da 'yan canji ne to , amma ko sis bashi da shi zaizo yace yana san 'yata , yoo in banda abun hamdiyya ma ai wallahi tafi karfin wannan yaron , shashashar yarinya kawai, ammi tafad'a gami da Jan dogon tsaki ......

Bayan hamdiyyah ta fita tunanin ta dingayi cikin ranta na halin mahaifiyarta ,tana me addu'ar Allah kar yasa ta rabasu da Faisal .....

Bayan tagama cefenan ta ta dawo gida , nan ta fara 'ko'karin d'aura girkin, tanayi ,ammi nayi ta mata mita akan Faisal , Ita ko hamdiyya shuru tayi batare da da tace komai ba .......


Kwance ilham take tana jijjigan sanyi ,da Alama zazzabi ne ke damunta, tun rana take fama da zazzabi, hibba ta bata sauran maganin , kasancewar saura d'an kad'an ne a cikin kwalbar .. .. ....

Wajejen magriba jikin ilham ya'kara tsananta....

Dudduba gurin magungunansu hibba tafara ko Allah zai sa taga ko da akwai wani maganin , amma cikin rashin sa'a tanema ta rasa duk sun 'kare....

Cikin tashin hankali hibba tadawo fallo tace," mufida d'aukko mun waya na kira daddy na fad'a mishi halin da ilham take ciki ko zai yarda na fita naje na siyo mata magani ....

Tashi mufida tayi ta d'aukko waya tafara dailing wayar daddyn Nasu.....


Kwance suke haihuwar uwarsu da wata ba_indiya suna aikata badala ....

Jin ringing din wayarshi yasashi mi'kewa dan ya d'auka .....

Ganin sunan my children ya baiyyana akan screen din wayarshi yasa ya goge zufar datake zubo mishi yana d'an hakki yace," kai! Hibba to menene?yafad'a fuskarshi cikeda mamaki .......

Matar da take kwance ne akan gadon taja tsaki cikin harshen turanci tace,"wai waye ne muna tsaka da jin dad'in mu zai hanamu , mai yasa baka kashe wayar ba , tafad'a cikin 'bacin rai ....

Juyowa yayi ya kallo ta , shima cikin yaran turanci yace,"am sorry baby , kar ki damu bazan amsa wayan ba yafad'a yana shirin komawa kan gadon .....

Tsinkewa wayar tayi , bayan ta yanke aka 'kara 'kira.....

Sharewa yayi batare da ya 'kara duba wayan ba suka ci gaba da abun da suke......

Jin shuru ba'a d'auka ba yasa hibba ta fashe da kuka tana fad'in," na Shiga uku ilham kiyi ha'kuri kinji daddy bai dauki wayan ba inshallahu zan ki samu lafiya ......

Hannun hibba na rawa tacigaba da trying wayar mahaifin nasu amma Sam bai dauki wayar ba .....


Zuwa yanzu hankalinshi kam baya ma jiinshi domin kuwa bai ma bi takan wayar ba bare ya duba wayar .....

Ganin haka yasa hibba ta tashi ta d'auki hijabinta , ta shiga d'aki ta d'aukki dubu uku a cikin 'katon akwatin da mahaifinsu yake ajiye musu kudi....

Bayan ta 'Debi kudiin , ta kalli nihat tace_" nihat kujira ni karkufito ko tsakar gida yanzun nan zan dawo kunji , tafad'a gamida d'aukan keyn gidan....

Da sauri ta fita cikin tashin hankali.......
bayan ta fita tasama gidan key , gudun kar wani ya shiga gidan...

Cike da damuwa tafara 'ko'karin neman chemist.....

Sai da hibba tayi tafiya mai nisa kafin ta samu chemist kasancewar unguwarsu shuru take .....

Dakyar tasamo chemist , ta hado mata magunguna , kafin daga bisani ta fara sauri had'e da gudu , dan komawa gida......

Wasu matasa ne su biyu suna tangad'i da Alama sun shawu ...
Cikin yanayin la yi suka sha gabanta Suna 'kare mata kallo ....

'Dayan ne yafara nufowa gurinta yana cikin tsananin maye.......

Cikin muryar maye yake fad'in," kaga yarinya kyakyawa ,kuma zazzafa gaskiya yarinya kinmun kyau .....

Cikin matsanancin tashin hibba tafara ja da baya , gabanta na mugun fad'uwa ...

Muryar ta na rawa take fad'in," dan Allah kuyi hakuri , wallahi kanwata na kwance bata da lafiya Ku bani hanya na tafi......

Wata dariya suka fashe dashi suka fara 'ko'karin nufo Inda take...

Da gudu hibba ta juya tafara gudu suna binta, gudu take sossai tana hakki suma suna binta....

Kasancewar unguwar shuru take babu kowa
Hakan yasa babu Wanda ya ganta bare ya kawo mata d'auki .....

Wani layi ta shigo , kafin su karyo layin ....

Wani gida tagani a bud'e tayi saurin Shiga gidan , ta 'buya a bayan kofar gidan......

A hankali take numfashi ,ta to she bakinta da hancinta gudun kar su ji motsinta ....

Idonta ne yayi jaa hawaye na bin fuskarta , tana kara toshe bakinta.......

Duk da hibba na cikin matsanancin tashin hankali, amma hakan bai hana zuciyarta tunanin halin da ilham take ciki ba .......

Wasu hawayene suka 'kara zubo mata a fuskarta cikin ranta ,tana fadin," ko a wani hali ilham take ciki oho......

Nemanta matasan suka farayi ganin zasu 'bata ma Kansu lokaci yasa suka juya suka koma suna tangad'i....

A hankali hibba ta le'ka, cikin tsoro take kallan waje .....

Ganin sun tafi sunyi nisa ne yasa hibba ta fita da gudu .....

Gudu take sossai , zuciyarta na tunanin halin da ilhama take ciki....

Jin ana kiran sallar isha'i yasa hankalin hibba ya'kara tashi matu'ka ......

Ganin ta iso layin gidan nasu yasa hankalinta ya kwanta ..

Nan tayi saurin bud'e gidan tashiga.......

*MUJE ZUWA*

*Zaku iya fara biyan kudinku (payment) dan na antaya Ku a paid group*

*Dan Neman 'Karin bayani zaku iya tuntubata a wanan Layin kamar haka 09066386347*

*DAN ALLAH KUYI SHARING MUN*

*I NEED MORE COMMENTS*

*COMMENTS*
*&*
*SHARE*
*&*
*VOTE*

*STORY & WRITTEN BY MUM FU'AD*

*๐ŸŒช๏ธ๐ŸŒช๏ธ๐ŸŒช๏ธGUGUWAR ANNOBA*๐ŸŒช๏ธ๐ŸŒช๏ธ๐ŸŒช๏ธ

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar๐Ÿ‘‰ zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*
*mahaukacin kishi*๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*Hatsabibiyar mace*๐Ÿง›๐Ÿฝ๐Ÿง›๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ
*A sanadin kuskurena*๐Ÿ’๐Ÿ’
*And now*๐Ÿ‘‡
*๐ŸŒช๏ธ๐ŸŒช๏ธGUGUWAR ANNOBA*๐ŸŒช๏ธ๐ŸŒช๏ธ

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE๐Ÿง›๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ๐Ÿง›๐Ÿฝโ€โ™€๏ธ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA ๐ŸŒช๏ธ๐ŸŒช๏ธ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*

I think you'd like this story: "GUGUWAR ANNOBA" by ZaynerbmuhammadKabee on Wattpad https://www.wattpad.com/story/296961375?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=ZaynerbmuhammadKabee&wp_originator=8jKG72vdfu9MDTwXH8S1wlHtN9A8q5ywRaKt2jqSaJeoViKW0QyqdhJ3SwbBjMfsf8hs%2ButNL8zz%2FlcilxbAJGEyReuqitW717I9zq4yGfAxPP09emV7mABPUUqgrQWV
*_______________________*_____________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู…
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 5&6*

Jikinta na rawa tana hakki ta bud'e cikin gidan ta shiga .....

Da sauri ta Shiga d'akin.....
Ganinta a kid'ime yasa kannen nata suka shiga tambayarta suna fad'in," anti hibba lafiya ?

Murmushin ya'ke tayi musu tace," babu komai , kawai dai inata sauri na dawo ne na ba ilhama maganinta ,tafad'a gamida 'ko'karin d'aga ilham, ta bud'e maganin ta bata.....

Bayan ta bata maganin ta kwantar da ita .....

Jawad ne ya turni'ke fuska kamar me shirin yin kuka yace," Anti hibba yunwa nakeji.....

Innalillahi , kai jawad kiyi ha'kuri wallahi kaina duk yayi zafi na ma manta ban d'aura abinci baa gashi har kusan 'karfe takwas saura , tafad'a gamida tashi ta cire hijab d'in jikinta ta nufin kitchen.....


Bayan hankalinshi ya dawo jikinshi sun gama aikata fasi'kancinsu , Kai tsaye ya nufi gurin wayarshi....

Ganin missed calls goma yasashi matu'kar mamaki ......

Take yafara 'ko'karin dailing number...

Kwance take hawaye Na bin fuskarta , tana tunanin rayuwarsu....

Jin ringing din wayarsu a falo yasata saurin mi'kewa tana fad'in," nashiga uku!!..

Da sauri ta 'karasa gurin ta d'auki wayan....

Murya a sanyaye ta d'auki wayan cikin tsoro take fadi'n," asallamu alaikum daddy......

Cikin fad'a da tsawa yace," ke kuma menene kika damu mutane da kira haka ?

Cikin tsoro muryar tana rawa take fad,"in,"daddy dama ilhama ce bata da lafiya kuma jikinta yayi zafi sossai .....

Saurin dakatar da ita yayi ta hanyar fad'in," to babu magani a gidan ne zaki dameni da kira haka ?

Cikin rawar murya take fad'in," daddy ba haka bane wallahi na duba maganin ya 'kare ne shine dama nace zan kiraka na fad'a maka zan fita siyo mata maganin kuma nayita kiranka baka d'auki wayan ba , shine na fita na siyo mata maganin tasha ....

What!!!ki ka fita?dan ubaki wa ye yace ki fita?
Baki da hankaline banace karki kuskura kifita ko nan da can bane ,in ba kai yara school ba ?

Hawayene suka fara gangarowa a fuskarta tace," daddy ba haka bane wallahi jikinta ne ya tsananta kuma babu maganin ko kad'an a gidan shine na fita na siyo mata , dan Allah kayi hakuri ....

Cikin fad'a yace," amma ranar da mukayi waya ai na tambayeki nace kuna da komai? kikace mun eh , bakice mun bakuda magani ba ai da na aiko muku dashi amma sabida bakida hankali baki iya fad'a ba ko?

To as from now on ba ciwo ba ko menene karki kuskura ki sake fita batareda izinina ba kinji ko ?yafad'a cikin tsawa ......

Ehh naji tafad'a cikin rawar murya .....

Kashe wayan yayi batareda ya kara cewa komai ba ......

Jiki a sanyaye hibba ta koma gadon ta ta kwanta wasu hawaye masu zafi suka zubo ta gefen fuskarta.....

Haka rayuwarmu zata 'kare haka zamu kasance , kai Allah na gode maka , Allah sarki rayuwa kaddara , inda ace ana shawara da mutum tun kan yazo duniya inda yakeso a haifeshi ha'ki'ka da ko ma'kiyina bazan so ya fito a irin wannan gidan ba , wani kuka hibba ta fashe dashi mai cin rai .......

Tashi tayi ta koma falo..

'Katon hoton dake ma'kale a jikin bangaun d'akin, hibba ta 'kura ma ido ,wasu hawaye masu zafi suka zubo a fuskarta .......

Hoton wata mata ce wacce zata kai a'kalla shekaru talatin...

Shafa hoton tayi cikin muryar kuka tana fad'in," ,mommah ! Mommah ! Mommah waiyyo Allah , takarasa maganar gamida fashewa da matsanancin kuka......

Zama tayi a kujera ta rafka uban tagumi tana sa'ke_sa'ke cikin ranta , iri_iri daban_ daban da haka har barci 'barawo ya kamata ......

Kamar yanda ta saba misalin 'karfe biyar ta farka , ta sa musu ruwan wanka daga bisani ta had'a musu abun karyawa , ta tashesu tayi musu wanka , ta basu abun karyawa daga bisani suka shirya ....

Bayan sun gama shiryawa misalin 'karfe bakwai da rabi suka tafi school......

Bayan ta kaisu ta dawo tafara aikin gida tayi wanke_ wanke ,itama tayi wanka daga bisani ta zauna ta tsafe kitson ta da ya dad'e a kanta .....

Bayan tagama tsifar , ta ke ta'kara mai da guda hud'u akanta kamar yanda ta saba .....

Bayan sati d'aya....
Misalin 'karfe biyar na yamma jirgi ya sauka a Kaduna Airport ......

Hotel ya kama , bayan ya kira d'aya daga cikin karuwanshi na garin Kaduna suka kwanta tare da niyyar washe gari ya nufi garin jos....


Wanki hibba take ta fama dashi ,bayan su Nihat sun tafi school ....

Jin ringing d'in wayarsu yasata ta bar wankin da sauri tanufi d'akin ta d'auki wayar .....

Sanin cewa daddyn su ne ya kira yasa ta fad,in," nashiga uku nasan ya kusa dawowa...

Jiki a sanyaye ta d'auki wayar ta kara a kunneta tace," daddy ina wuni ?
lafiya 'kalau yafad'a a takaice, gobe zan dawo gari so kinsan duk abun da ya kamata kiyi sannan kinsan ai abun da zaki dafa ko, kuma kinsan abun da banaso na tarar ko?
ehh tafad'a a ta'kaice .....

Kashe wayar yayi batareda ya 'kara cewa komai ba ....

Wani mummunar fad'uwa gaban hibba yayi ,jikinta na rawa tayi saurin 'karasa wankin ...

Cikin sauri ta cire labulayen falon ta d'aukko jajayen labulaye ta canza , ta'kara gyara d'akin ...

Bayan ta gama ta Shiga d'akinshi ta gyara ,ta share ko ina ta d'aukko wani turaren da ake saka mishi ta bad'e d'akin dashi ...
Jan zanin gado ta d'aukko ta shinfid'a...

Toilet d'inshi ta Shiga shima ta wanke tsaf tasa turaren .....

Bayan ta fito a d'akinshi nan ta dawo fallo ta d'aga ido ta kalli hoton dake ma'kale a jikin bangon falonshi ,tayi saurin juyashi .....

Sai da ta tabbatar komai yayi daidai kafin hankalinta ya d'an kwanta ......

Bayan su nihat sun dawo daga school nan ta ke shaidamusu cewar gobe daddy zai dawo ......

Gaba d'ayansu shuru sukayi, jiki a sanyaye sukace to..

Hatta ilham 'yar 'karama baso take mahaifin nasu yadawo ba bare sauran ....

Wunin ranar haka suka wuni a guda babu wal_wala tsakaninsu .......

Home work kawai sukayi bayan sun gama suka zauna gaba d'ayansu suka rafka uban tagumi....

'Karfin hali hibba tayi ta tashi ta d'aura musu abincin dare.....

Jiki a sanyaye take komai tana me fargabar dawowan daddyn nasu....


Zaune Hamdiyya take tana cin abinci itada mahaifiyarta ...

Jin ringing d'in wayarta yasata saurin tashi dan d'auka ...

Ganin sunan nurul_ aini yasata sakin wani kayataccen murmishin zuciii. ....

Wata Harar ammi ta gallamata dan kuwa tasan ko ba a fad'a ba tasa Faisal ne ....

Nan ta kara wayar a kunnenta tace," Assalamu alaikum...

Tunda Ammi taji yanda tayi sallamar yasa ta 'kara tabbatar da cewa faisal ne...
Hakan yasa ta ta'be baki tana 'kara jin haushi da tsanar Faisal din ....

A 'bangaren Faisal amsawa yayi da wa alaiki salam matata abun alfahari na, gani a 'kofar gidanku yafad'a cikeda farin ciki....

Murmishi tayi tace" okay to ganinan zuwa ,tana fad'an hakan ta kashe wayar.....

Ga kinan zuwa ina ?to billahillazi yau babu Inda zakije cewar ammi tafad'a cikin fad'a ....

Haba ammi dan Allah kiyi hakuri mana wallahi bazan dad'e ba , ammi dan Allah wai me faisal yayi miki ne ? kika tsaneshi haka ? Ubanki yamun nace ubanki cewar ammi, taci gaba da fad'in,"kuma dan ubanki in kikayi wasa wallahi tallahi sai na rabaki dashi har abadah gara ma ki bini a hankali a toh .....

Tsugunnawa a 'kasa Hamdiyya tayi tace," ammi dan girman Allah ammi karkimun haka ,ammi dan Allah dan annabi ki taimakamun wallahi inasan faisal ,ammi in kika rabani dashi bansan halin da zan shiga ba, ammi dan Allah kiyi hakuri kin ga yanzu yanata ta jirani a waje dan Allah ki barni naje mu gaisa wallahi bazan dad'e ba, hamdiyyah ta'karasa maganar kamar me shirin yin kuka.....

Dan ubanki sai kije ai, kuma wallahi kika dad'e da kaina zanzo har wajen na koreshi kinji na fad'a miki ....

Jiki na rawa hamdiyyah ta mi'ke tace," to ammi nagode , tana fad'in," haka tayi saurin fita , ammi ta bita da harar, had'e da Jan dogon tsaki ......

Bayan Hamdiyyah ta fita ...
Ganin Faisal zaune a dakalin gidansu kamar yanda yasaba yasa wasu 'kwalla masu zafi suka zuba a idonta tana me jin tausayin kanta da tausayin Faisal a duk randa aka rabasu .......

Saurin share 'kwallar idonta tayi ta'karasa gurinshi , had'e da 'ko'karin 'kwa'kulo murmishin yake tace," sannu da zuwa, tafad'a tana me shirin zama kusa dashi.....

Murmishi yayi yace," yauwa matata , yau 'yan Jan ajin ne suka motsa da aka dad'e ba fito ba?

'Kwa'kulo murmishin ya'ke ta 'karayi tace," A,a wallahi ka kirani ina cin abinci ne , shine na 'karasa sai na fito kayi hakurii ......

Ganin yanayinta yasa ya fuskanci akwai abun dake damunta ...

'Kura mata ido yayi yana son ya 'kara fahimtar wani abu......

Juyawa gefe tayi , tafara 'ko'karin danne 'kwallar dake barazanar zubo mata a fuskarta ......

Tabbas Hamdiyyah bakya cikin yanayi mai dadi yau dinan ,sabida haka ki fad'amun menene? Meke faruwa? Meke damunki ? Akwai matsala ne? Ya jero mata tambayar lokaci d'aya......

Shuru tayi ,hawayen da suke ma'kalle a idon suka samu damar zubowa a fuskarta kafin daga bisani tace,"faisal akwai matsala .....

Cikin matsananciyar damuwa Faisal yace," matsalar me? Fad'amun dan Allah...

Tunawa da gargadin da ammi tayi mata tayi, tayi saurin tashi tace," Faisal karkadamu zamuyi magana a waya, ni zan koma tafad'a gamida 'karasawa cikin gidan da gudu.....

Kiranta yafarayi yana fad'in," Hamdiyyah! Hamdiyyah!!!
Ganin ta shiga cikin gida yasa shima ya tashi jiki a sanyaye , zuciyarshi fam da tunani iri_iri had'e da matsananciyar damuwa ya tafi ......

Bayan Hamdiyya tashiga gida, daidai lokacin da ammi take shirin d'aukko hijabinta a d'aki dan fita tayima faisal rashin mutunci ....

Allah ya taimakeki , kinga d'aki nan da na Shiga wallahi hijabina zan d'aukko , da na fita kinga yanda zanyi daku .......

Shuru Hamdiyyah tayi ta Shiga d'aki , takwanta a gado wani kuka ya ku'bce mataa....

Yoo ai bakiyi kuka ba sai randa na rabaku nan ne zakiyi kuka da tushe ammi tafad'a tana 'ko'karin kwashe shanya......

Wani kuka hamdiyyah ta 'Kara fashewa dashi zuciyarta cikeda da tausayin kanta .....

Washe gari da safe .....
Bayan hibba ta shirya kannenta sun tafi school ..

Nan ta fara aiki tu'kuru...

Gyara gidan tashiga yi ta'kara sama d'akin daddy nasu turaren , kafin daga bisani ta Shiga kitchen .....

Bayan ta shiga kitchen nan ta bud'e 'kato freezern su dake cikee ma'kil da nama.....

Wani nama ta d'aukko dake ajiye a gefe , ta curo, ta d'eba tafara 'ko'karin tafasashi .....

Kunna d'ayan gas din tayi ta d'aura white rice , tasa su carrot da green beans da piece a ciki ...

'Katan freezern ta bud'e ta d'ebo kayan miyan tafara blanding din su a blander....

Bayan ta gama ta d'aura akan gas tafara 'ko'karin had'a miya ....

Bayan ta gama tafasa naman ta raba biyu kashi d'aya tayi paper meet, kashi d'aya ta ajiye zata sa sa a cikin stew .. .....

Bayan tagama had'awa, nan ta 'kara kunna d'ayan gas din ta fara 'ko'karin d'aura musu nasu abinci , da Sauri tayi tayi ta dafa musu macroni jeloup...

Bayan sun dawo daga school jikinsu a sanyaye, a tunanin su ma zasu dawo su samu daddyn nasu a gida ne .....

Bayan sun cire uniform ta zuba musu macronin sukaci ....

Nihat ta gyara gurin daga bisani suka koma suka nutsu gurin daya duk suka rafka uban ta gumi .....

Misalin 'karfe uku hibba tagama komai , tasa abincin a katon food flask , tasaka miyan ma a flask , daga bisani ta gyara kitchen din , ta goge ko ina .....

Zama tayi tadan Huta jin wani azababben ciwon baya dake damunta, ga gajiya da take fama dashi ....

Misalin karfe biyar na yamma motar ALHAJI TANIM GAMJI ta sauka , *RINGROAD ARE'A*

*To fa!!!!*
*muje zuwa*

*ZAKU IYA FARA BIYA DAN NASAKU A PAID GROUP*

*DON NEMAN

Please Login or Register in order to submit comment