Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*&*
*SHARE*

*STORY & WRITTEN BY MUM FU'AD*
🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 13&14*

*Kiyi haƙuri rashin jina kwana biyu matsalan wayana ne ,amma yanzu koma yayi daidai inshallahu*

*Dan Allah duk wa 'inda suka biya kuɗinsu su mun magana dan na missing lambobin mutane*

"Kai tsaye suka shiga cikin gidan , da sauri hibba ta shiga kitchen tafara ƙoƙarin dafa musu indomie, duk da jirin dake ɗibanta hakan baisa ta ƙasa yi ba......

"Cikin ƴan mintuna ƙalilan hibba ta gama ta kawo musu sukaci itama ta zuba nata taɗan ci kaɗan daga bisani ta ƙara shan magani ......

Tambayar ta ƙannen suka shiga yi ganin halin da yayar tasu take ciki , daƙyar ta yi ƙarfin hali tace musu bakomai dan hankalinsu ya kwanta........

Bayan Alhaji tanim gamji sun fita da ƙaruwar shi kai tsaye gidan da ya ɗaukkota ya mayar da ita haɗe da bata maƙudan kuɗadde.....

Bayan ya bata ya danna hancin motarshi zuwa rikkos Are'a ......

Daidai ƙofar gidansu hamdiyyah yayi parking ɗin dallelliyar motarshi .....

Waigawa yayi ya hango wani yaro yana tahowa ......

Cikin isa haɗe da taƙama yace,"kai yaro zo!...

Ba musu yazo yace," gani , shiga cikin gidannan kace ana sallama da hamdiyyah , yafaɗa cikin tsantsar ɓacin rai kamar wanda aka ɓatama rai......

Batare da yaron yace komai ba ya juya ya shiga cikin gidan da sallama gamida faɗin,"wai ana sallama da hamdiyyah.....

" Hamdiyyah datake zaune a kujerar tana wanke_wanke tayi saurin juyawa jin ance ana sallama da ita .....

Da sauri Ammi tafito tana faɗin kai !kai! Wannan yaro Allah ya mishi nacin tsiya kai inji wa? tafaɗa gamida kallon yaron , inji wanine a mota a waje .....

Zaro ido Ammi tayi ta fito tana gyara tsohon zaninta tace,"kai yaro maza je kace tana zuwa kaji......

Juyawa yayi yafita ya isar da saƙon cewa wai tana zuwa ....

" Wani murmishi gefen baki yayi cikin ranshi daɗi fal da samun nasara da yayi , duk da dama can yasan cewa dole zasu Amince .....

Koda yaron ya fita cikin tsantsar farin ciki Ammi tace," waiyyo daɗi kinji abun daɗi ko hamdiyyah , inaga mutumin ranar ne ya dawo , kinga! ai bar wannan wanke_wanken zan ƙarasa in yaso sai kije ƙishirya ,kiyi maza ki ɗan shafa powder da ɗan man baki ,maza yi sauri, Ammi taƙarasa maganar tana washe baki .....

" Tashi hamdiyyah tayi fuska a turniƙe haɗe da turo baki , ta miƙe kamar zata fashe dan takaici, buɗe baki hamdiyyah tayi zatayi magana......

"Saurin dakatar da ita Ammi tayi ta hanyar faɗin hamdiyyah in ba
Kinaso raina ya ɓaci bane in miki abun da baki taɓa tunani ba to wallahi tun wuri ki fita banaso inji kince komai ......

"Jiki a sanyaye hamdiyyah ta shiga ɗaki ta ɗauki hijabinta tasaka ta fito ......

"Fitowa Ammi tayi daga ɗakinta hanunta riƙe da wani turare .....

Baki buɗe Ammi take kallanta tace," me yasa kike da taurin kai ne? ina cewa nayi ki ɗan yi kwalliya kisa gyale shine kika wani ɗaukko hijabi kika saka kamar me takaba.....

" Ammi taci gaba da faɗin maza ki koma ki canza kisa gyale kiyi kyau , ai ba tsayawa zaiyyi yana jiran ki ba ko......

Sumi -sumi hamdiyyah ta koma ɗaki....

Cikin faɗa Ammi tace," dan ubanki kiyi maza ki fita mana kina abu kamar ba jini a jikinki ko anfaɗamiki zai zauna yana jiran ki ne?

Badan taso ba ta ɗauki gyalen ta tayafa, ta ɗauki powder tana shafawa hawaye na fita a idonta, mambaki tashafa ta fita kamar zata fashe dan ɓacin rai da takaici.......

"Hungo karɓaa wanan kifesa, Ammi ta miƙamata turaren da ta fito dashi .......

" Ganin zata ɓata mata lokaci yasa Ammin ta faffesa mata da kanta tace," maza jeki a dawo lafiya dan Allah ki sakar mishi fuska kinji ko ?

Batare da tace komai ba ta fita cikin ɓaci rai kamar zata fashe......

"Zaune yake cikin motarshi yana latse_ latsen waya ,cikin ranshi yana tunanin irin rashin mutuncin da zaiyyi mata idan sunyi aure , da haka ya saki murmishi gefen baki yace," yarinya zamu haɗu ne gaba duk ki gama ɓatamun lokaci, ni ba lokacinki zan ɓata ba ni rayuwarki zanɓata gaba ɗaya.....

"" Ganin ta fito yasa yayi saurin buɗe kofa ya saki wani ƙayataccen murmishi yace," wow gimbiyar mata kinyi kyau sossai , amma kin barni inata jira sai dai kuma kwalliyar danaga kinyi yasa na haƙura nasan kwalliyar ce ta ɗauki lokaci , nagode sossai hamdiyyatu ......

Tunda yake magana hamdiyyah take yi mishi wani irin kallo,cikin zuciyarta wani tsananshi na ɗarsuwa , ji take kamar ta shaƙeshi ya mutu, batasan maiyyasa ba tunda ta ganshi taji sam bai mata ba , ji takeyi tsanar shi na ruruwa cikin zuciyarta ......

""Wani kallo ta bishi dashi daya ƙara fito da gwala-gwalan idonta tace," Mallam dan Allah nasan dai kai babba ne kuma ka mallaki hankalin kanka , in har dai ƙwaƙwalwar ka ba ta dabbobi bace Yakamata ace ka fahimci nufina,hausawa sunce labarin zuciya a tambayi fuska , tunda kaga na fito fuskata babu Annuri Yakamata ace kabama kanka amsar cewa babu soyaiyyarka ko ɗaya a cikin zuciyata kuma banaji zanji sonka daidai da na sakwan ɗaya ne , hannayen ta biyu ta haɗa taci gaba da faɗin," dan Allah na roƙe ka karka sake zuwa ƙofar gidanan, kar kasa inyi maka abun da zaka daɗe kana danasani , kai ba yaro bane karkasa girmanka ya zube a banza a hofi , ina fata ka fahimta , taƙarasa maganar gamida sakar mishi wata harara .......

"Dariya yayi yace," okay to shikenan yarinya , amma dan Allah in tambayeki mana ?

Inaji tafaɗa ba yabo ba fallasa .......

" Kallonta yayi yace," amma waye ya ce ki fito bayan alamun sun nuna kamar an tursasaki ne ?

Ina ruwanka, tabashi amsa gamida ɓata rai ....

Hmmm da dai kin daure kin faɗamun ta yuyu faɗa mun yazama silar rabuwa ta dake , domin ni mutumin arziƙi mutumin kirki ne bana takurama yarinya dan ta so ne , shin kina da wanda kike so ne, wanda kuke soyaiyya??

Take idanuwan Hamdiyyah suka kawo ruwa, ƙwalla ta fara fita a idonta ........

Cikin murya irinta tausayi yace," A'a yarinya kuka bai kamaci kyakkyawar fuska irin taki ba , so dan Allah ki daure kifaɗamun kinji yafaɗa cikin tausaya wa kamar gaske ........

"Murya na rawa tace," Faisal!! Faisal!! inason Faisal ,Ammi ta ta rabani dashi tace Lallai bazan aureshi ba , maganar gaskiya itace ta takuramun akai sai na fito gurinka , Alhalin babu san kowa a cikin raina sai na Faisal , tafaɗa gamida ƙarasa maganar da kuka .......

Okay na fahimta kuma na gane , to in badamuwa ko zan iya zuwa naga Ammin taki ?

Zaro ido tayi tace," mai zakayi mata ? Meza kaje kace?dan Allah kabari kawai basai kaje ba ......

Hmmmm dariya yayi yace," A'a kar ki damu , ni nataɓa shiga irin halin da kika shiga a lokacin da nake matashi, kuma na ɗanɗani zafi da raɗaɗin rabuwa da masoyi , shiyasa nake matuƙar tausayama duk wanda ya tsinci kanshi a ciki , saboda haka karkidamu zanje nayimata magana ne ta yanda zata fahimta, har ta amince ta baki zaɓinki kinji ko?

Jiki a sanyaye tace,okay to shikenan amma sai gobe in Allah ya kaimu rai da lafiya sai kazo ko, Nagode sosai , ashe kaima ka taɓa shiga irin halin da nake ciki ?.....

Kaɗa kai yayi yace ƙwarai kuwa..

Cikin tausayawa tace Allah sarki .......

Gyara tsayuwar shi yayi yace to shikenan nagode sossai da wannan damar da kika bani , yaƙarasa maganar haɗe da sakin murmishin gefen baki .......

Kuɗaɗɗe ya curo masu yawa ya miƙa mata yace," gashi dan Allah karki ce bazaki karɓar ba wallahi bana baki bane dan wata manufa kawai naji inada sha'awar miki ihsani ne shiyasa kawai ,dan Allah ki karɓa.......

"Ganin yanda ya marairaice yana roƙonta yasa Hamdiyya taɗanji tausayinshi , inda take mamaki yanda yayi mata sai kace shi ne yake rokonta kuɗin , ganin haka yasa tasa hannu bibbiyu ta karɓa , tace," to Nagode sossai Allah amfana......

A haba bakomai wallahi ,yafaɗa cikin sakin fuska, yanzu ki shiga gida goben zan dawo kamar iwar haka kinji , kaɗa kai tayi alamar to , gamida shiga gida, hankalinta ya ɗan kwanta , tana me murnar samun nasara haɗe da mamakin yanda mutumin yake da fahimta da sauƙin kai , Lallai tayi matuƙar mamakinshi , gashi a ruwan sanyi zai rabu da ita , da haka ta shiga cikin gidan fuskanta ɗauke da farin ciki .....

Bayan Hamdiyyah ta juya zata shiga gida yana ƙare mata kallo , cikin ranshi yake faɗin Hmmm yaro man kaza , Allah sarki yarinya bakisan waye ni ba, bushewa yayi da wata dariya irinta gaggan mugaye , take kuma Annurin fuskarshi ya ɗauke cikin ranshi yake faɗin , Hmmm yarinya kenan , ance miki ni yaro ne ,komai ina amfani da waiyyo dakuma makirci , an faɗamiki zanyi asarar rabuwa dake ne , ai dole ki shigo hannuna , ina
banda ma abun yaro , ji yanda cikin sauƙi na shawo kanta ta amince in Shiga gidan su , dama haka nakeso duk yanda akayi uwarta nada son abun duniya , so nasan shawo kanta bazai taɓa mun wahala ba , har tana iya tsayuwa a gabana ta gaya mun magana , Hmmm Lallai zata gane kuskurenta ,da wannan yayi murmishin samun Nasara gamida shiga cikin motarshi yaja ya tafi .......

Ganin Hamdiyyah ta shigo gida ɗauke da farin ciki yasa Ammi jin matuƙar mamaki, saɓanin kafin tafita......

Washe baki Ammi tayi tace," kowa ya tuba dam Wuya ba lada , kaga yarinya, Ah to,ni nasan za'ayi haka , tunda naga kin shigo da Annuri a fuskar ki nasan en Lallai wannan mutum ya sace zuciyar tilon ƴar tawa , shegiyar Kaya daa har kina mun iskanci wai bazaki fita ba ai gashinan kindawo da farin ciki wallahi ni dama nasan ai za'ayi haka .....

Uhmm Hamdiyah tace," tayi shiru , miƙamata kuɗin hannunta tayi tace," gashi wai inji shi yabani.......

Jiki na rawa Ammi tayi saurin sa hannu ta karɓa tafara ƙirgawa, jiki na rawa tana ƙirgawa,tana rawa , tana gyara zani, cikin matuƙar farin ciki Ammi ta rungume Hamdiyya ta washare baki murna fal cikin ranta tace,"kai kai Allah Nagode maka Hamdiyyah kingani ko? Kinga abun da nake hango miki ko ?, Yanzu ki duba abun arziƙin da ya Bamu , Kinga ko dole mugode Allah ko .....

Ita dai Hamdiyyah shiru tayi batare komai ba , sai kallo datake bin mahaifiyarta dashi .....

Wai gobe in Allah ya kaimu zai to gurinki, Hamdiyyah tafaɗa ba yabo ba fallasa ......

Sake baki Ammi tayi gamida zaro ido tace,"kai Hamdiyyah shi ɗin?

Kaɗa kai Hamdiyya tayi alamar eh !!
A Lallai mutumin nan da gaske yake , Allah yasa auranki zaizo nema Kinga Kuwa shikenan sai a sa muku biki nan kusa bada daɗewa ba kai Allahha Nagode maka ......

Ita dai Hamdiyyah ɗaki kawai ta shiga ta na me jinjina hali irin na wanan mutumin , cikin ranta take faɗin gaskiya yanada kirki babu ruwan shi , inda wani ne yaushe zaiyyi haka, tunani tayi tayi cikin ranta tana me matuƙar tausayin Faisal haɗe da tausayin kanta , domin ko tasan matuƙar aka rabata da Faisal to an rabata da farin cikinta na har abada ........

Murna sosai Ammi takeyi , tana me Allah_Allah goben tayi yazo , Haƙika Allahah na karɓar addu'arta , Hamdiyyah zata shiga gidan hutu .......


Bayan Faisal ya koma gida , kwanciya yayi yana tunani , hawaye na fita ta gefen idonshi ......

Magana ya fara yi tamkar wani yana kallo shi yace,"yanzu rabani da Hamdiyya za'ayi yanzu zambar Hamdiyyah kenan , waiyyo Allah na , Hamdiyyah ina so ki ina ƙaunarki , Allah karkasa na rasa Hamdiyyah , Allah kasa Hamdiyyah tazama matata ,matata ta bar a bada.....

Shuru yayi yana kallon sama , daga bisani ya miƙe a zabure ,ya share hawayen fuskarshi.........

Jikinshi na rawa ya ɗaukko ƙaton trolley ɗinshi ya buɗe drowern kayanshi yafara zuba kaya a ciki .......

Sai da ya cika akwatin da kaya ,da duk wani abun buƙata ,daga bisani ya rufe ,ya ɗauki takarda da biro jikinshi na rawa yafara rubutu kamar haka," _zuwa ga masoyiyata Hamdiyyah , haƙika Ni masoyinki ne na gaskiya , bazan iya kwatanta son da nake miki ba , Allah ya sani ina ƙaunarki ina tsananin sanki , saidai kiyi haƙuri da shawarar da na yanke , Ni Faisal masoyinki na tafi neman kuɗi wata uwa duniya , bazan sake dawowa ba har sai na samo kuɗin aureki ,in nadawo sai a ɗaura mana aure , bawai banda kuɗin da zan aureki a yanzu bane A'a inadashi sai dai nasan mahaifiyar ki taƙi yarda da aure na dake ne saboda bani da kuɗaɗɗe da yawa ,amma yanzu zanje in nemo , saboda haka ki shirya ko wani lokaci zaki iya ganin nadawo matuƙar nasamu abun da nake so , Nagode matuƙa da irin soyaiyarki a garemu , Allah ya barmu tare , ki riƙe mun Alƙawari na karki yarda wani ya ƙwacemun ke , kiyi haƙuri bazaki sake jina ba koda a waya ne , nine naki masoyinki har kullum na barki lafiya......._

Da haka ya nannaɗe takardar ya saka a cikin Aljihu ya ja trolley ɗin shi ya fita ......


*MUJE ZUWA*

*ZAKU IYA FARA BIYAN KUƊI KU DAN NA ADDING ƊINKUNA PAID GROUP*

*DAN NEMAN ƘARIN BAYANJ ZAKU IYA TUNTUƁATA AKAN LAMBAR WAYA KAMAR HAKA 09066386347*

*DAN ALLAH KU SHARIN MUN*

*COMMENTS*
*&*
*SHARE*

*STORY & WRITTEN BY MUM FU'AD*

*🌪️🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️🌪️

*(HURRICANE EPIDEMIC)*

*mallakar👉 zaynerb muhammad kabeer (mum fu'ad)*

*Marubuciyar littafin👇👇👇👇👇*
*mahaukacin kishi*🌺🌺
*Hatsabibiyar mace*🧛🏽🧛🏽‍♀️
*A sanadin kuskurena*💐💐
*And now*👇
*🌪️🌪️GUGUWAR ANNOBA*🌪️🌪️

*Banyarda a canzamun labari na ta wata siga ba batareda izini na ba*

*Kamar yanda kuka sani duk labarai na a gaske suke faruwa( true life) ne to wannan ma hakan yake , sai dai wannan labarin nawa yasha banban da na saura domin yazo da wani salo iri_iri a cikinshi , kudai ku kasance dani , akan farashi mai sauki naira dari biyu kacal 200,*
*Zakuyi iya fara biyan kudin ,ta wanan Account din 1461261429 Muhammad Zainab kabir access bank ko katin waya ta wanan layin 09066386347 sai na jiku*

*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da littafin Na zuwaga member na GUGUWAR ANNOBA fans, nagode sossai da soyaiyyar Ku a gareni, hakika ina sonku son so fisabilillah*

*Haryanzu littafin HATSABIBBIYAR MACE🧛🏽‍♀️🧛🏽‍♀️ nanan akan farashin naira dari biyu 200 kacal maza ku garzayo kusiya, amma akwai promo, duk mai so da wannan GUGUWAR ANOBA 🌪️🌪️ da HATSABIBBIYAR MACE sai ya biya naira dari uku kacal, sai yasha karatunshi kudai ku garzayo kusiya karku bari ayi Baku....🥰🥰🥰💃💃💃💃*

*_______________________*_____________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
بسم الله الر حمن الر حيم
*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*
*ina rokon Allah yasa na fara a sa'a ,Allah kuma ya bani ikon rubuta daidai ,yand na fara lafiya Allah kasa nagama lafiya Ameen*


*FREE PAGE 15 &16*

*Kiyi haƙuri rashin jina kwana biyu matsalan wayana ne ,amma yanzu koma yayi daidai inshallahu*

*Maman Baby da maman Hajjah haƙika comments ɗinku na sakani nishaɗi , da kuma addu'o'inku a gareni , Nagode Allah yabar ƙauna....*

"Fitowa Faisal yayi kai tsaye ya nufi ɗakin mahaifiyarshi......

Gani shi ɗaukeda ƙaton trolley yasa mahaifiyarshi tafara kallon shi baki buɗe tace,"kai Faisal ina kuma zaka je yanzu da ƙaton akwati ??

"Tsugunnawa yaya a gabanta yace," ummah zantafi Lagos ne gun uncle baffaye......

"Cikeda mamaki mahaifiyarshi tace," Hmmm ikon Allah wato daaa anyi_anyi kaje kaƙi, kace ka bazakaje ba ,bazakazafi kabar Hamdiyyah ba , shine yanzu zaka tafi ko yanzu ka haƙura da Hamdiyan ne? Shiru yayi baice komai ba, daga bisani ya miƙe yace," hakane ummah yanzu na canza shawara inason in tafi Lagos ɗin....

Cikin farin ciki ummah tace," to shikenan Faisal Allah ya tsare Allah ya bada Sa'a , ka kula da kanka,sannan ka riƙe amana ina yi maka fatan Alheri.....

. Tashi yayi yace,"Ameen Ummah Nagode sossai sai na dawo .....

Da fatan Alkhairi ta bishi daga bisani ya fita jiki a sanyaye ya ɗauki hanya......

"A bakin layinsu Hamdiyyah ya tsaya inda yaga wani yaro ya miƙa mishi takardar ya nuna mishi gidansu Hamdiyyah yace ya kaima Hamdiyyah....... karɓa yaron yayi ya shiga layin, shikuma Faisal ya juya ya tafi kamar zaiyyi kuka.....

Zaune take tana wanki , da sallama yaron ya shigo Hamdiyyah ta amsa , miƙa mata takardar yaron yayi yace," wai gashi aba ma Hamdiyyah ......

Ga mamaki Hamdiyyah take kallon yaron ,hannu tasa ta karɓi takardar tace," to inji wa? Inji wani ne a waje ya tafi , yaron yafaɗa , okay to shikenan jeka Nagode , juyawa yaron yayi ya tafi .,....

Da sauri Hamdiyyah ta fara buɗe takardar , tafara ƙoƙarin karantawa .....

Karantawa tafara , take yanayin fuskarta ya fara canzawa , jikinta yafara rawa , bakinta na rawa tana cigaba da karantawa , zaro ido tayi a yayin da ta karanta dai_dai inda yake faɗin bazata sake jinshi ba koda a waya ne ,daƙyar ta iya tattaro nutsuwarta ta ƙarasa karantawa ,ƙarasa karanta takardar tayi gamida sakin wani razanannen ihu .......

"Da gudu Ammi da take barci ta fito , ganin Hamdiyyah tsugunne A ƙasa tasa kuka kamar wacce aka aiko ma da saƙon mutuwa yasa Ammi jin matuƙar mamaki tace," kee Hamdiyyah meke faruwa meke damunki ?

Kuka Hamdiyyah ta cigaba dayi tana miƙama Ammi takardar.....

Cikin rashin fahimta Ammi tace," ke banasan iskanci banza ina tambayarka kin wani muƙamin takarda , takardar ce zata bani amsa ?, ko ni iya karatu nayi dazan karanta , shashasha kawai ......

Cikin muryar kuka Hamdiyyah tace," Ammi! Ammi! shikenan burin ki ya cika Faisal ya tafi , ya tafi nemo irin kuɗadden da kikeso , taƙarasa maganar gamida sake fashewa da matsanancin kuka ......

Ƙara haɗe rai Ammi tayi tace," Alhamdulillah Allah Nagode maka , ai garama da ya tafi ko yabarki kuci soyaiyyarku da mai hali, kuma da kike cewa yaje nemo kuɗi ai yanzu kam na gaba yayi gaba na baya sai labari in faɗamiki , wawiya dama akanshi shine kika razanani,ina cikin barci na ina mafarki wai naganki a gidan daula kinata yagar kaza nima nazo kika bani muna sha da lemon kwalba , gashi baki bari na ƙarasa mafarkin ba kika wani tasheni shasha kawai ......

"Ita dai Hamdiyyah tashi tayi ta ƙarasa ɗaki da gudu haɗe da fashewa da matsanancin kuka .....

Tsaki Ammi taja ta shiga ɗakinta ko a jikinta ......

Misalin ƙarfe shaɗaya na ɗare Alhaji tanim ya shigo gida inda ya biya gurin shaƙatawanshi daga bisani ya dawo gida .......

Ɗaki ya shiga kai tsaye , akwatin kuɗinshi ya buɗe , ganin kuɗaɗɗen shi sinyi ƙasa yasa ya tashi ya ɗauki ke ya fita , ya nufi bayan cikin gidanshi ......

Wani ƴar ƙaramar kofa ce a gurin ....
Saka makullin yayi ya buɗe kofar a hankali ƙofar ta buɗu.........

Kai tsaye ya kutsa kai cikin ɗakin......

Wani duhu ne a cikin ɗakin inda ba' ganin komai , hasken wayarshi ya kunna......

Ganin abubuwan da suke ɗakin kaɗai ya isa yasaka tsoro ya ɗarsu a zuciyar mai kallo......

Domin kuwa ɗakin duk an mai rufi da fata , ga kayi kan mutane a gun, wasu sun zama kaurangwal , ga jini ta gefen a wata ƙatuwar ƙaurya , ga kayan cikin mutane ɗanye , kai!wa iyazubillah..........

Haƙiƙa tsayawa kwatanta irin abubuwan da suke ɗakin ɓata lokaci ne .......

Haskawa yayi ta gefe ya ga wani kendir , da ashana , kunna kendir ɗin yayi daga bisani ya kashe touchlight ɗin yabar wutan kendir ɗin.......

Take ya sauya kayanshi ya ɗauki jajayen kayan da suke rataye a jikin angern ɗakin yasa........

Doguwar rigace jajawur sai ratsi_ratsi baƙi ta saman wuyan......

Sakawa yayi daga bisani ya zauna a ƙasa ya ɗauki wata ƙatuwar ƙaurya mai ɗauke da jini a ciki, ya ajiye a gaban shi .......

Take ya sa hannu yana juya jinin, idanuwanshi suka kaɗa sukayi jajir, yafara wani irin yare mai wuyar fassarawa........

Harshen Hausa ya dawoyi yafara magana cikin kakkausar murya da yasa ɗakin yafara amsawa yana faɗin,"Azarfakinzu kifito ka baiyyana akwai matsala ......

Take fuskar wani ƙaton mutum ya bayyana da kakkausar murya yace," meke faruwa ? Faɗi buƙatunka yanzunnan a biya maka shi , domin kaima baka sanya wajan biyamana buƙatar mu ,munajinka ......

Cikin kakkausar murya yace," wannan matar tana takuramun ,tana bani tsoro , tana razanani da idanuwanta , jiya daƙyar na iya barci , ta Addabeni ta addabi rayuwata ,matuƙar naganta sai ta tsora tani , sannan kuma tana hanani sukunin ,duk da nasa an juya hoton amma saidai yara suka juyashi ranar nagani , shine nakeso na tambayeka shin zan iya cire hoton na koneshi gaba ɗaya kawai ??

Take Azarfakinzu ya bushe da wata shu'umar dariya yafara magana da kakkausar murya da zai mazuƙar bada tsoro yace," inaaaaa , bazai yiyu ba ai

Please Login or Register in order to submit comment