Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, bata jira cewarsa ba ta juya ta koma cikin gida da saurinta,

Yana ganin ta juya yabi bayanta da harara dama tuni yayi zargin hakan shiyasa ya biyo mata ta bayan gida , tsaki yayi yace shashasha ai wallahi ko 'yar Dan uwanki ce baki isa kijemun da ita gida ba bare kuma yarinyar da baki had'a komai da ita ba, indai samu ayi auren zakisha mamaki na , ina sonki sosai amma sam bazan yarda kijemun da wata yarinya ba don Ni ba mahaukaci bane , daga haka ya ka'ba rigarshi ya nufi gidansu cike da murnar zai mallaki masoyiyarshi,


.........................................

"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un , Amna mizan gani haka , shaye shaye a gidan nan , mikikeso kija mana agarin nan , kina kallo an tsayar da ubanki a matsayin *d'an takarar gwamna* amma shine kikeso ki janyo mana idon mak'iya , yanzu mi kike tunani idan har abokan adawarshi suka san da wannan abun da kika tsiro....

Ko kallon momy batayi ba sai dakinta da ta nufa tana tangand'i hannunta rik'e k'ananun kwalabe har ukku tana sanye da riga da wando wanda suka matseta sosai suka fitar mata da surar jikinta kanta ba d'ankwali sai dogon gashinta da ya kwanta har gadon bayanta,

Fisgota momy tayi cikin tsawa tace wai ba magana nake maki ba ...........cikin Muryar maye tafara magana tana cewa
" Indai abunda nake zai sa azzalumi mijinki ya fad'i a wannan za'ben to wallahi yanzu na fara , kuma inaso kisani sai nayi ajalin mijinki da hannuna da wannan hannun nawa tana magana cikin matukar maye wanda har baka fahimtar abunda take cewa sosai daga nan ta zarce da wasu irin surutai da momy takasa tantance abunda take cewa ,
Dafe kai momy tayi zuciyarta kamar zata fito waje tsabar tashin hankalin da take ciki...............✍🏼




*Zanyi kokarin ganin nadinga maku post akan lokaci saidai ba lallai kusamu typing din da yawa ba saboda abubuwa sunmun yawa inkuma da yawa kukeso to zan dinga yi duk bayan kwan biyu*
[6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻‍🔧

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*👇🏻
*Jami'in d'an sanda*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍



🅿️ -9


......................da murnarshi ya shiga gidan da sallama , Inna talatu na tsakar gidan tana surfe ta amsa mashi,

"Inna daka akeyi ne"?

"Eh Nura , daga ina haka kai da kace yau bazaka dawo da wuri ba"?

"Sosa kanshi yayi yana 'yar dariya yace Inna Dama wajan Baba nadawo Allah yasa bai fita ba"

"A'a bai fita ba yad'an zagaya ne"

Suna haka sai ga malam Buba , gaisheshi Nura tak'arayi da jiki kasancewar yana fama da zazza'bi shiyasa ma yau bai fita ko ina ba ,

"Nura mi ya dawo dakai kuma yanzu kai da kace zakayi nisan kiyo ? "

"Wallahi Baba akan maganarmu da Hajar ne naje mun daidaita kanmu yanzu insha Allah baza'a sake samun wata matsala ba shine nakeson ka aika wajan Baffanta ak'ara sa mana rana insha Allah yanzu ba abunda zai koma faruwa tuni na shawo kan matsalar ,

"Ka shawo kan matsalar kamar yaya , ai wallahi ni nagaji da gafara sa banga k'aho ba , Ni dama ban yarda da wasu aljanu ba iskancine kawai , to inaso kabude kunnenka da kyau kaji daga yau ba kai ba wannan yarinyar nariga da nagama magana zamu had'aka aure da 'yar uwarka Dije ranar juma'a in Allah ya kaimu za'a kai kud'in aure. Don haka kar ink'ara jin maganar wata Hajara kaji na gayamaka , kai inbada ma kake wani sakarai har yaushe zakaje ka d'ad'd'agowa kanka gandamemiyar budurwa kamar wannan , ga yara 'yan mata masu tasowa amma ka bige da neman wata hajar , to ban yarda ba dama can kasan Ni bawai inaso had'in bane don dai ubanka ya kafe ne kurum yanzu kuwa bazan yarda ba , cewar Inna cikin masifa ,
Inna talatu masifaffiyar macece ta bugawa a jarida , wannan yasa Malam Buba yake matuk'ar tsoronta sam baya iya taka Mata birki duk abunda zatayi tazama itace mijin shine matar , dama can batason wannan had'in na Nura da Hajar malam Buba ne ya kafe har yasamu ya shawo kanta ta yarda , yanzu kuwa ganin abubuwan dake faruwa yasa ta yanke shawarar hadashi da yar k'anwarta Dije ko yanaso ko bayaso

Tunda tafara magana zufa ke ketowa Nura ta ko ina , cikin tsananin tashin hankali yace " don Allah Inna karkimun haka kimun rai wallahi inason Hajar sosai kuma namaki alkawarin ba abunda zai koma faruwa kuma" ............cikin masifa tace " son nata ya dade bai kasheka ba to wallahi bazaka aure ta ba dama can ba sonta nakeba Dije zaka aura kaji na gaya maka, daga haka ta kwashe hatsinta ta nufi inda suke ajiye ruwa ta zuba tafara wanke surfen tanata zabga mita ,

"Baba kanajin Inna abunda take cewa amma kayi shiru bakace komai ba, yafad'a kamar zai fashe da kuka, "

Kayi hakuri Nura , jiya ba k'aramun tashin hankali na fuskanta ba daga wajan talatu akan maganar nan ,nayi iya yina amma ta kafe kadai san halinta Sarai in takafe akan abu , ni wallahi babbar damuwata ma shine Baffah Ja'in bansan abunda zance mashi ba nayi nayi ta yarda ko don na fita kunyar Ja'in Amma tak'i kayi hakuri kamata biyayya Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, "

Hawaye Masu zafi suka wankewa Nura fuska, wani irin zafin Hajar yakeji sosai ,don a ganinshi duk ita taja mashi da yanzu anjima dayin auren su , haka ya tashi jiki ba kwari ya fita daga gidan ,yanufi inda ya baro dabbobinsu tare da abokan shi,


Haka kuwa akayi ran jumu'a aka kai kudin auren Nura da Dije ,
Su Innar Hajar sai kawai ji sukayi ankai kudin auren Nura , Inna kuwa ta shiga damuwa ba kad'an ba ,don bata da babban burin da yafi taga auren Hajar kodon ta huta da tsegumin mutanen garin ,

Baffah kuwa ko a kwalar rigarshi sam bai wani damu ba saima addu'a da yayi akan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi,

Uwar gayyar ma bata wani damu ba sai cewa tayi Allah ya raka taki gona,


........................................


Afusace ya shigo gidan kamar zai tashi sama , momy na zaune a falo tabuga uban tagumi tanajin duniyar na juya mata , tabbas abunda suka shuka ne suke girma , ta rasa Babban d'anta yanzu kuma tana nema ta rasa 'yar ta wadda ita kadai ta rage mata a yanzu ,

"Ke Hindatu Ni zaku tozarta a garin nan , Ni zaku zubarwa da mutunci , wato kin had'a baki da 'yarki kunason kuga bayana ko ? Inba hakaba tayaya ina matsayin da takarar gwamna a jahar nan amma kiyi saken da zaki bar 'yarki tafad'a wannan halin , duk wani wajan iskanci za'a sameta a wajan ya kikeson mutane gari su lalleni in sukasan cewa 'yata Yar k'waya ce , sannan abokan adawata kinsani inhar suka san da wannan matsalar to na kade har ganyena , yanzu takai har office ake iskoni ana gayamun abunda yarinyar nan keyi a garin nan to wallahi kija mata kunne inba haka ba wallahi daga ke har ita sai kunyi dana sani , kindai san waye Saminu sulaiman daga haka ya juya fuuuuu yabar falon,

Hawaye ne suka zuboma momy tanajin zuciyarta kamar zata fashe tsabar bakin ciki a hankali tace ya Allah wannan wace irin masifa ce daga wannan sai wannan , doli zan dauke Amna daga garin nan har zuwa wani lokaci inba hakaba komai zai iya faruwa tasan halin mijinta Sarai zai iya kawar da duk wani mahaluki da zai kawo masa cikas daga cikar burinshi na zama gwamna

Amna kuwa bata ma san yanayi ba tana daki kwance sai sharar bacci take daidai da takalmin kafarta bata cireba shekara biyu kenan da tajefa kanta a wannan halin sanadin k'awarta Lawisa , tun bayan da ta babbatar da cewa tarasa masoyinta da gaske ta d'auki damuwar duniya ta ɗorawa kanta kullum ciki kuka da damuwa take , wanda har hakan ya haifar mata da ciyon zuciya mai tsanani, da wannan damar k'awarta Lawisa tayi amfani wajan cusamsta ra'ayin yin shaye shaye acewarta kayan maye sune kawai zasu taimaka mata wajan kawar mata da duk wata damuwarta ,


.........................................


Alhamdulillah yanzu jikin Baba yayi sauki sosai , zuwa wannan lokacin sun fawwalawa Allah komai sunci gaba da gudanar da al'amuransu na yau da kullum , duk da ada Baba yaso subar garin gaba daya saboda yadda yakejin garin yamashi k'unci da zafi , sai da k'yar Yaya sulaiman ya shawo kanshi akan ya hak'ura ya barwa Allah tunda in sun bar garin basu san inda zasu nufaba , wannan yasa ya hak'ura doli don ba yadda zai yi sai dai har wannan lokacin bayajin dad'in zaman garin abubuwan da suka faru baya sun kasa gogewa a zuciyarshi,


.........................................

Acikin wannan lokacin ne wata annoba ta shiga ruggar su Baffah Ja'in , inda dabbobinsu suka rink'a mutuwa kusan kullum sai sun rasa wasu daga cikin dabbobinsu , wannnan abufa ya tashi hankalinsu matuk'a , gaba daya yan ruggar sun d'aga hankalinsu , kunsan Fulani da shanu🤣
Acikin sati d'aya sai gashi sun tafka asara mai yawa , sunyi iya bincikensu don sanin abinda ke faruwa da dabbobinsu amma basu gano komai ba ,
Wannan yasa manyan cikinsu suka yanke shawarar tashi daga garin gaba daya ,

Asalin su Baffah Ja'in fulanin yawo ne basuda takamammen wajan zama , duk inda suka ratsa sukaga cewa wajan zai masu to zasu yada zango a nan nawani lokaci , wani wajan sai suyi shekara d'aya wani biyu wani ma bazasu wuce wata shida ba yadanganta da yanayin wajan idan yayi masu , kuma a haka duk inda suka yada zango in wata daga cikin 'ya'yansu ta samu mijin aure a garin indai har sun yarda da tarbiyyar shi to zasu bashi auren yarsu kuma ahaka in lokacin tashinsu yayi zasu tafiyarsu su barki to fa daga nan sai dai in kunada rabon koma ganawa da juna tunda basuda takamammen wajan zama , saidai zasu sanar da mijin ainahin inda tushen su yake kodon wata rana,
Duk inda sukaga yamasu to kowanensu zai d'ibi iya inda yakeso yakafa yar bukkarshi babu zancan wani zagaye gida da sauransu saidai suna bawa juna tazara a tsakaninsu ,

Duk inda suke sauka basu ta'ba jin dadin zama ba kamar wannan jejin ba, duk kuwa da irin yadda dajin keda had'ari amma sukam sosai sukejin dadin zamanshi saboda jejine mai yawan fadamu da k'orsmu ga Ni'ima ,

Babu wani waje da suka ta'ba dad'ewa irin dad'ewar da sukayi a wannan wajan Amma bullowar wannan al'amari yasa doli ungulu zata koma gidanta na tsamiya,

Nan suka yanke shawarar nan da kwana ukku zasu yi hijira daga wannan nahiyar zuwa wata ,

Lokacin da Baffa ke sanar da ahalinshi sun shiga tashin hankali ba kadan ba don sunyi sabo da garin ba kadan ba ,
Sai dai duk tashin hankalin da sukeji bai kama k'afar wanda *Hisham* ya tsinci kanshi aciki ba , yaji wani gingimemen tashin hankali wanda ko lokacin da zai bar mahaifarshi baiji irin shi ba , tuni abubuwan da suka wuce suka fara dawo mashi tuni kanshi yafara juyawa yayinda idon shi suka k'ank'ace suka shige ciki bayan wani irin ja da sukayi kamar an watsa mashi barkono ,

Miyasa rayuwa take zo mashi da abubuwa marasa dad'i ne irin wannan yarasa kowa nashi lokacin da yake da buk'atar taimako Allah ya had'ashi da Baffah da iyalanshi ,a yadda suka daukeshi har mantawa yake da cewa sud'in ba 'yan uwanshi bane ya sakankance dasu sosai sai gashi ƙaddara zata koma shiga tsakaninshi da farincikinshi a karo na biyu , hawayene masu zafi suka gangaro daga kyawawan idanunshi yayinda numfashin shi har sark'ewa yake tsabar tashin hankali, ashe da yake ta cewa zai tafi yabarsu ashe bazai iya aikata hakan ba , bai tabbar ba sai yanzu da yake ganin ƙaddara zata rabasu yanaji kuma yana gani,

Sai da gaban Baffa ya fad'i lokacin da ya kalli yanayin Hisham , shi kanshi tunda suka yanke wannan hukuncin yake cikin matukar damuwa da tashin hankali akan Hisham , shine kadai ne damuwarshi tunda in da sabo sun saba da irin wannan tashin to amma abun damuwar shine ya rayuwar Hisham zata kasance ya rabuwarsu zata kasance,

A hankali Baffa yafara bashi baki yana nuna mashi muhimmancin yarda da ƙaddara don yasan a wannan lokacin doli zasu rabu yaci gaba da cewa "ina tausayinka sosai Hisham ina tausayin irin rayuwar da kakeyi ,nasan ba k'aramun abune zai raboka da gida ba acikin irin wannan yanayin , amma ina maka addu'a da fatan alkhairi a rayuwa , sunjima suna tattaunawa shida Baffah duk da Baffa ne kawai ke maganar wanda shima k'arfin hali ne kawai yakeyi , Hisham kuwa sam yakasa magana ma wani irin shock yakeji gaba daya jikinshi rawa yakeyi ,

Gefe daya Kuma habu da Halliru ne sai faman hawaye sukeyi basu taba damuwa da tashin su daga wani wajan zuwa wani wajan ba sai a wannan karon saboda Hamma Hisham ,gaba daya sun d'aga hankalinsu, gefe d'aya kuma *Hajar* ce ta haɗa kanta da gwuiwa kuka take har na fitar hankali saboda ta tabbatar da yanzu kam zata rabu da Muneeba da gaske kuka take har muryarta ta dashe Inna tayi lallashi har ta gaji, ga Muneeba zaune kusa da ita ganin Hajar na kuka yasa duk ta damu takasa sukuni sai ma kukan da itama tafara ahaka bacci ya kwasheta ajikin Hajar duk ta mak'alk'aleta ,

Kallo Daya Hisham yayi masu yaji wani abu mai kama da tausayi ya daki zuciyarshi da k'arfi , wani tausayin Hajar da 'yar shi ne ya daki kirjinshi ya tabbata da zasuyi kewar juna sosai musamman ma munee yasan kamun ta saba da rashin Hajar zata wahala sosai wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa Sam baiso 'yarshi ta shak'u da kowa ba don kar wani lokaci hakan ya zame masu barazana ,

Dare yayi sosai amma basuda niyar tafiya su kwanta Baffa ne yayi karfin halin yimasu magana akan suje su kwanta zuwa safe zasuyi magana , haka kowa ya tashi jiki a sanyaye suka nufi makwancinsu ,

Gaba daya haka zuciyoyin wadan nan bayin Allah suka kwana cikin matukar damuwa ga wata irin kewa da sukeji tun basu rabu ba,

Hajar sam batayi bacci ba tsabar kukan da takeyi saidai akai akai zata dauki fitila ta haska fuskar Muneeba sai ta jima tana kallonta saikuma ta fashe da kuka,


Kwance yake sam yakasa runtsawa zuciyar shi kamar zata fito waje idonshi kuwa banda tsiyayar da hawaye ba abinda yakeyi ,
*Yanzu haka zaku rabu da Baffah batare da yasan waye kai ba , duk irin wannan hallaci da yayi maka tabbas Baffah ya cancanci yasan ko kai waye* wani sashe na zuciyarshi yayi mashi wannan tambayar ,

Da sauri ya zabura ya tashi zaune Yana fad'in tabbas *Yakamata yasan waye Ni doli zan bashi tarihina kamun rabuwarmu*.................✍🏼
Nagaji sai gobe🤨🤨🤨




09035027743


*MAYUKA MASU KARA NI,IMA*



🅰️ farkon shekarun balaga na kowacce mace musamman dai dai lokacin da take fara al'ada, tana fara ganin ruwa wanda ake fadawa ni,imar mace, yana dan yauki kadan haka zalika yana kama da ruwa dan danonsa kuma kamar an hada sugar da gishiri, ruwan yana iya canjawa kodai daga matsalar ciwon sanyi ko kuma wanda ake cewa dattin mahaifa, ko kuma yanayin maganin ni,ima da mace tasha kalarsa ya canja, haka zalika dandanonsa, wannan ni,ima kenan a takaice.


🅰️ na samun mayuka wadanda kasashen turawa ke sarrafawa wadanda ake matsi ko kuma sha, wanda suke tatso ni,ima ajikin mace da wuri kodai haka kawai ta zama da danshi ko kuma lokacin sha'awa, amma a bangaren mayuka daga magungunan muslinci akwai wadannan da suma ana amfanin dasu ta wannan fannin wato maganin ni,ima kuma anashan cokali biyune safe da yamma, mayukan da ake hadawa waje daya sune kamar haka
1 man ridi
2 man zaitun
3 man kwakwa
4 man habbatussauda



*Daga taku mmn yusup mai kayan mata*🥰🥰🥰
[6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻‍🔧

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*👇🏻
*Jami'in d'an sanda*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍



🅿️--10



..................Asubar fari salla kawai yayi ya nufi gidan Baffa , zuwa lokacin har jiri ke d'ibanshi , ga wani zazzaɓi da yake ji,

Kasa shiga gidan yayi saboda har yanzu garin da sauran duhun asuba , shi kanshi yasan bai kamata yazo yanzu ba sai dai kawai yakasa hak'ura ne ,ji yake kamar idan ya jima baizo ba zaizo ya tarar basa nan,
Zama yayi a wajan gidan inda ya haɗa kanshi da gwuiwa yama rasa wane irin tunani zaiyi,
Yashafe fiye da awa a wajan sannan Allah ya kawo Baffah ya dawo daga masallaci shida su Habu,

Har suka k'araso wajanshi baisani ba don yayi nisa cikin tunanin rayuwa ,
Dafashi Baffa yayi yace
......."Hisham wane irin tunani kakeyi hakane , so kake ka haifarwa kanka da wani ciyo ne, "

Firgigit yayi yana kallon Baffa ,
........"bansan da zuwanku ba Baffa ina kwana,"
...."lafiya qalau Hisham , miyasa ka zauna anan ai da sai ka shiga gida ko"

Shiru yy baice komai ba , daga nan su habu suka gaisheshi sanna suka dunguma suka shiga gidan tare,

Inna na gindin murhu tana hada wutar da zata dama masu kunu dashi sukayi sallama suka shigo,
Gaishe da Baffa ina tayi kamun su Hisham su gayar da ita,
Zama sukayi akan tabarma d'aya duk sunyi shiru kowanensu da tunanin da yakeyi , sai can Hisham ya numfasa yace

"Inason magana dakai Baffah,

Kallonshi Baffa yayi yace " lafiya dai Hisham ? Ko akwai abunda yake faruwa ne ,?"
"Bakomai Baffah kawai dai inason kasan koni waye , inason ibaka *labarina* ne inaji baidace mu rabu a haka ba batare da kasan ko ni waye ba , duk da banida niyar sanar da kowa asalin waye ni tunda na tsinci kaina a wannan sabuwar rayuwar to nayi kudurin bawanda zai san koni waye to amma kai naji inason na gayamaka asalina da abunda yaraboni da asalina yayi shiru sakamakon tuna abubuwa da yawa da suka faru dashi,

Murmushine ya bayyana akan fuskar baffa , cikin farin ciki yace
" Tabbas najima inason sanin ko kai waye Hisham , sai dai banason takura maka ne shiyasa ban sake tambayarka akan abinda ya raboka da gida ba , zanyi matukar farin ciki idan har kabani labarinka,

Tashi Baffa yayi yashiga cikin yar bukkarshi sannan ya umurci Hisham da ya biyo bayanshi, tashi yayi yabi bayan Baffa ,
Habu da Halliru harma da Inna Sam basuji dadin hakan ba don sun so suma suji labarin Hamma Hisham,
Ganin hakan yasa Inna taci gaba da aikin hada kayansu yayinda habu da Halliru suka fita wajan da dabbobinsu suke don duba lafiyarsu ,
Hajar kuwa tana cikin yar bukkarsu itada Muneeba wanda bacci yayi awon gaba da ita saboda rashin baccin da batayiba jiya , sam batasan wainar da ake toyawa ba,

A hankali ya bud'e bakinshi yafara magana yana cewa,

" *Mun kasance* yan asalin garin Sokoto acikin garin shuni , mu Fulani ne mahaifiyata da mahaifina duk yan Sokoto ne ,mun kasance bamuda yawan zuri'a sosai saboda k'arancin haihuwa da dangin mu suke dashi tun tali-tali mahaifina da mahaifiyata yan uwan juna ne auren zumunci aka masu , mahaifiyata ita kadaice a wajan iyayenta wanda Allah ya masu rasuwa tun tana yarinya , a hannun mahaifin Abbana ta girma ,

Kakana malam Muhammad yanada matan aure biyu kuma dukkansu yan uwansa ne da yake basu cika auren bare ba a zuri'arsu , Inna Habiba itace uwargida sai Inna Indo , akwai zaman lafiya sosai a tsakaninsu da fahimtar juna,

Inna Indo itace tafara haihuwa a gidan , inda haifi d'anta mai suna Abdullahi , Abdullahi nada shekara 4 itama Inna Habiba ta haifi danta inda yaci sunan Abdurahaman , yaran sun tashi cikin tarbiya da kaunar junansu ,

Abdullahi nada shekara 14 inda Abdurahaman yakeda shekara goma alokacin ne rikon mahaifiyata ya dawo hannun malam Muhammadu saboda rasuwar iyayenta wanda suka rasa ransu ta hanyar gobara da ta tashi a gidan nasu kamun a kawo masu dauki har wutar taci jikinsu sosai kwanasu daya Allah yamasu rasuwa,
Alokacin tanada shekara 4 a hannun Inna Habiba take zaune
Malam Muhammadu yayi kokari sosai wajan tsayin daka don ganin yaran nashi sun sami ilimin arbiya dana boko,

Bayan wasu shekaru alokacin *Maryam* wato mahaifiyata tazama budurwa sosai alokacin ne daga Abdurahaman har Abdullahi suka nuna suna sha'awar aurenta , ganin hakan yasa Malam Muhammad yabata za'bi a cikinsu , kai tsaye ta za'bi Abba na wato Abdurahaman ,
Abdullahi da mamansa sunji haushi sosai wanda har saida takai Abdullahi baya shiga duk wata harka da ta shafi Abbana , ya dauki karan tsana ya dora mashi , kishi yake dashi sosai *wannan shine mafarin lalacewar kyakkyawar alak'ar dake tsakanin mahaifina da yayanshi Abdullahi*

Bayan wani lokaci akayi bikin Abbana da momma na a Nan cikin garin Sokoto suka fara zama, shekara d'aya da aurensu akayi bikin Abdullahi da matarshi Asma'u wadda suke kira da Nana , wadda ta kasance 'ya ce ga abokin malam Muhammadu,

Abdullahi kasuwanci yakeyi ,yana yawon garuruwa kuma Alhamdulillah yana samu sosai , yayinda Abbana ya dage akan karatun shi wanda bashida burin da yafi ace yazama *dan sanda* (police) bayan gama karatunshi bai jima ba aka daukeshi aikin dan sanda kamar yadda ya karanta , inda ya fito da matsayin inspector, yayi farin ciki sosai hakama iyayenshi , inda yafara aiki gadan gadan, cikin gaskiya da amana , Abbana ya kasance jajirtaccen Jam'i, mai kishin k'asarsa , wanda gaskiyarsa tasa yayita samun karin girma a wajan aikinshi , inda daga baya aka mashi transfer zuwa Lagos,

*Mafarin duk wata matsala*

Saida Momma na ta shekara 7 sannan Allah yabata ciki na , kuma har wannan lokacin suna zaune a Lagos a unguwar *Small lando*

Sunyi matukar farin ciki da samun wannan cikin nawa ba kadan ba , tun a lokacin suka dauki son duniya suka dorama cikin saidai cikin na bata wahala sosai ,duk wata kulawa da take buk'ata to tana samu daga Abdurahaman sosai yake tsaye wajan ganin ya bata kulawa , ahaka har cikin ya isa haihuwa , a wata safiyar jimu'a bayan masallaci Allah ya sauke Maryam inda ta haifi danta fari tass dashi ba abunda ya baro na mahaifinshi , Abdurahaman yayi murna da farinciki a wannan rana kamar ba gobe , haka yayita sadaka ga mabukata , gefe daya Kuma wata irin soyayyar danshi ce ke shiga lungu da sako na zuciyarshi, ranar suna yaro yaci suna *Hisham* bayan sati Daya da suna Abdurahaman ya kwashe mai jego tareda dansu suka nufi Sokoto , acan ya barsu ya koma wajan aikinshi , da niyar in tagama wanka zaije ya dawo dasu,

Bayan sari ukku,

Alokacin satin Maryam biyar da haihuwa tana samun kulawa sosai tayi bul-bul abunta itada baby ran Alhamis kwatsam sai Inna Habiba ta tashi da ciyon ciki , wasa wasa sai gaba abu keyi tun tana daurewa har ta sanarma da Inna Indo , kamun zuwa wani lokaci inba Habiba tafita daga hayyacinta sai mirkususu take , babu shiri Inna Indo ta aika a kirawo malam ,
Maryam kuwa tuni hankalinta in yayi dubu to ya tashi hawayene kawai ke zuba a idonta ganin yadda uwar mijinta kuma uwarta ke cikin mawuyacin hali na ciyo,

Lokacin da malam yazo har tafita daga hayyacinta sam bata gane wanda yake kanta , arikice Yakamata suka nemo taxi suka nufi babban asibin garin wato asibitin daji , kasancewar akwai nisa sosai tsakanin shuni da cikin gari yasa kamun suzu har Inna Habiba ta suma ,
Suna zuwa aka wuce da ita emergency, Basu wani dau lokaci suna dubata ba Allah yamata rasuwa ,

Ba k'aramun gigicewa da rudani Inna

Please Login or Register in order to submit comment