Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

,
"Madam har yanzu ina kan bincike amma har yau bansamu wata alama da zata warwarema zare da abawa ba, "

Dan Jimm tayi sannan tace " to shikenan kaci gaba da sa ido sannan ban yarda da kowa ba duk abunda zakayi kayi acikin sirri,"

"To shikenan Madam ko mi ake ciki zan kiraki,

"Aa Jabir ban yarda da kira ba ni zan kiraka in bukatar hakan ta taso "

"Yes ma"

Daga haka sukayi sallama itakuma taci gaba da dannar laptop dinta,



**************************

Innalillahi wa inna ilaihin raji'un don Allah Malam ka cire damuwar mariya a ranka Shin da wanne kakeson muji da rashin mariya ko da wannan ciyon da yake damunka , sanin kankane wanda ya mutu bazai dawo ba zaluncine anriga an zaluncemu ba abunda muka iya saidai mu barwa Allah,

Tari yake sosai da kyar yasamu ya lafa mashi , yana sauke numfashi ,gefenshi kuma sulaiman ne da Hadiza sai shemau wadda itace k'arama a gidan ,
Cikin galabaita yafara magana yana cewa

" doli in damu Inno sun cuceni sun kashemun 'yata da banida kamarta sun rabani da farincikina ,yarinya mai nutsuwa da ladabi da biyayya , mutuwarta ba shine abunda yake tayarmun da hankali ba kamar sanadin mutuwar tata , saboda zalunci suka rink'a yi mata *fyade* har sukayi ajalinta wannan wane irin rashin imani ne, bazan ta'ba yafe masu ba , kullum burinta tayi karatu mai zurfi amma yanzu sunyi sanadin mutuwarta ba tareda ta cika burinta ba ya karashe maganar yana zubar da hawaye duka yaran kuka sukeyi to bare kuma inno ,

Tunda suka rasa mariya sukayi k'aura da farinciki duk da ba mutuwar ke k'ona masu raiba sai sanadin mutuwar,............โœ๐Ÿผ



*Rashin comment dinku zaisa in ajiye book din nan gsky bana bukatar stecker ko tnx comment kawai nakeso inba hakaba zan ajiye don inada aikinyi zanbata awa ukku ko hudu inyi typing amma bazaku iya bata minti biyar ba kuyi mun comment*๐Ÿค”๐Ÿค”๐Ÿค”


*KI KARANTA ZAKI KARU SIRRIN HUNTU KO NACE GONGOLI*

๐Ÿ…ฑ๏ธabbar ciyawar maganin gargajiya daga yankin kudu masu yamma na yankin afurka musamman kasashen renon kasar faransa, haka zalika wannan magani daya shahara a kowanne fanni musamman wajen tsaftace gaban mace kamar mejego wanda take bukatar kamshin gaba idan kuma matsi akeso ana hadashi da gabaruwa da saiwar kalgo ana tafasawa ana zama acikin ruwan, wannan ya inganta a bangaren maganin gargajiya tun ba yauba, asalin sunansa kuma da yaren faransa GONGOLI



๐Ÿ…ฑ๏ธayanin yanda yake warkarda cututtukan gaban mace kuma ana aiki dashi da lemon tsami da ganyen gwaiba shine ake jikasu su jika sosai ana tsarki da ruwan, baya bari wata cuta ta shiga gaban mace, wannan koda mace tanada abokan zama masu daukeda ciwon sanyi bazai shiga jikintaba domin akwai babbar garkuwa a tattare da wadannan magungunan wanda haryanzu an tabbatar basu da wani illah ga lafiya matukar aka kiyaye aiki dasu,



๐Ÿ…ฑ๏ธangaren shahara da yayi kuma a yanzu ya zagaya duniya ta yanda wadanda basu dashi ayanzu ya iskesu, harma yanzu ana amfani dashi kadai dinsa ta hanyar jikashi da ruwa anasha domin riga kafin kamuwa da cututtuka maza harda mata





๐Ÿ…ฑ๏ธayan wannan ana hada maganin samun ni,ima dashi, da wanke mara yanda ake ana tafasa shi da zobo da kanunfari idan ya tafasa atace ruwan asaka Zuma ko mazar kwaila anasha.


*KU TAYA YARONA ASLAM DA ADDU'A YAU YA K'ONE DA RUWAN ZAFI*๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
[6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง


https://chat.whatsapp.com/J1pyWjlxrS74JrGU3faQE7

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ_7


...................da k'yar suka samu tarin ya lafa mashi , ruwa yaya sulaiman ya d'auko ya bashi ya sha sannan ya d'auko magungunan shi yabashi ya sha , da yake akwai mai sa bacci aciki baijima bacci yayi awon gaba dashi ,
Ajiyar zuciya suka sauke dukkansu yayinda suka tsurawa Baban nasu idanu kowanensu zuciyarshi kamar zata fashe saboda k'uncin da suke ji a zukatan nasu,

Baba Inno tana daga gefe ta zuba uban tagumi cikin matukar damuwa , tarasa yadda zatayi da malam don ganin ya cire wannan damuwar a ranshi amma abun ya faskara , tanajin tsoron ta koma rasa mijinta bayan rashin 'yarta da tayi, saboda abun ya ta'ba malam sosai fiye da tunani gashi har damuwar tana barazana ga lafiyar shi,

Tashi Hadiza tayi tafara yan aikace aikacen gidan inda tayi shara sannan ta dora masu girki ,shama'u kuma ta had'a kwanikansu tafara wanke wa , yayinda yaya sulaiman ya tashi ya fita shagonshi ,
Sulaiman yana sana'ar dinkin tela Kuma Alhamdulillah yana samun abunda yarufawa kansu asiri dashi don shi yake dauke da nauyin gidan gaba daya , rashin lafiyar Baba ne yasa yanzu yarage fita shago saboda shi yake kula da Baban don jikin nashi yy tsanani sosai,


...........................................

"Hello Alhaji "
" Wai kina ina ne tun d'azu ina nemanki "
"Alhaji muna asibiti fa"
"Ke da wa kenan"?

Wasu yawu ta had'iye kamun cikin rawar murya tace "Alhaji Amna na kawo fa ,na gayamaka jikinta yayi tsanani sosai"
"Da izinin wa kika fita "
"Haba Alhaji wai mi kakeyi hakane , *Amna* fa nake gayamaka batada lafiya , ya kake abu kamar wanda baya cikin hayyacinshi , to ina asibiti kuma Ni zan tsayawa 'yata har tasamu lafiya , " tana gama fadin hakan ta kashe wayarta ranta na k'una , tunani take anya mutuwar Zayyan bata taษ“a kwakwalwar mijin nata ba kuwa , duk irin tsananin son da yakewa Amna yau itace kwance rai a hannun Allah amma ko a jikinshi, .......


Alhaji Saminu sulaiman kuwa k'asak'e yayi yana kallon wayar , shi Hindatu ta kashewa waya ,lallai ta aikata babban kuskure kuwa ,daga haka ya fito daga ษ“angaren yanufi harabar gidan , yana fita securityn shi suka taso aguje suka bude mashi mota shiga yayi gidan baya yayinda suma suka shiga motocinsu suka bar gidan aguje,


...........................................

Zaune yake cikin wani k'asurgumin daji ,dajine mai yawan yalwan tsaunika wanda suka k'awata wajan yayinda suka yiwa wajan wata irin rumfa mai ban sha'awa ga iska mai matuk'ar dad'i na kadawa ,
Zaune yake yayi tagumi yanajin wani irin rad'ad'i na zaga karkashin zuciyarshi abubuwa da yawa na dawo mashi acikin kanshi banda burin daukar fansa ba abinda yake cikin zuciyarshi,

kamar daga sama ya hangeta tana nufo inda yake ,kallo Daya zaka Mata ka hango tsananin damuwa da tsananin tausayinshi aciki idanunta,

Da sauri ya mike tsaye yana zaro idanunshi yayinda yake nunata da yatsa a hankali ya furta *Momma*
Murmushinta Mai kyau tayi mashi kamun ta kira sunan da take kiranshi dashi tace *"shalele* "
Da sauri yayi nufin d'aga k'afarshi don zuwa inda take amma abun mamaki sai yakasa koda motsi ne haka ya zuba mata idanu yanason yin magana amma yakasa ,

A hankali tafara magana tana cewa " kayi hakuri Hisham kayi hakuri Allah yana son masu hakuri kuma yana tare da masu hakuri, kabarwa Allah dukkanin al'amarinka shi zai maka sakayya , amma inason kacire burin daukar fansa aranka , ka kula da 'yarka ka kula da 'yarka ka kula da 'yarka.......daga haka tafara ja da baya tana murmushi tare da daga mashi hannu ,
Yanason yy magana amma yakasa yanason yabi bayanta kar ta koma 'bace mashi amma yakasa yanaji yana gani har ya daina hangota yayinda idanunshi ke zubar da hawayen bakinciki, ..... Kamar an sakar mashi baki haka yaji a firgice ya kwala kiran sunanta "Mommaaaaaa"
Afirgice ya farka daga dogon bacci da yakeyi , tuni ya had'a zufa sai maida numfashi yake kamar wanda yayi gudu yajima a haka har yadan yara samun nutuwa a zuciyarshi ,
Yau kwana hudu kenan da yake irin wannan mafarkin , tabbas yazama doli ya kauda idonshi daga mak'iyan shi ya hakura da daukar fansar , duk da kuwa bashida wani buri da yawuce hakan , zai nisanta kanshi da duk wani abun da zai sa ya tuna baya zai dauki yarshi ya nisanta ta da mak'iyanshi, wad'an da yasan cewa matuk'ar suka san cewa Muneeba tana raye to tabbas zasuyi k'ok'arin ganin bayanta , zai tsaya mata zai inganta rayuwarta zai k'yalesu badon yana tsoronsu ba sai don ganin ya tseratar da rayuwar gudan jininshi, yajima a haka yana sak'a da warwara yayinda wani irin fushi mai tsanani ya bayyana akan fuskarshi yayinda manyan idonshi suka k'ank'ance suka shige ciki sosai jijiyoyin kanshi suka tashi yayinda mak'ogoronshi ke kaiwa da komowa yana had'iyar wasu yawu masu matuk'ar d'aci , yanajin numfashi shi nayin sama sosai a hankali bakinshi ya bude yafara karanta _innalillahi wa Inna ilaihin raji'un_ ya dauki akalla 30mnt a haka kamun yafara samun sassauci acikin zuciyarshi,
duba tsadadden agogon hannunshi yayi yaga k'arfe 3:30 na dare tashi yayi ya fito waje ,tsaye yayi Yana k'arewa wajan kallo , fili ne fetal sai bukkokin fulanin da zaka gani tsili-tsili garin yayi tsit , bakajin komai sai tashin kukan tsuntsaye , alwala yayi yakoma cikin bukkar ya tayar da Sallah , haka yarinka jera nafilfili har akayi asuba ,bayan yayi sallar asuba ne ya koma ya kwanta zuciyarshi cike da tunanin ta inda zai fara,


*Washe gari*

Misalin k'arfe 8:30 ya tashi daga nauyayyen baccin da ya dauke shi , wajen da aka dan zagaye mashi da sunan ban d'aki nan ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito ya wanke bakinshi da fuskarshi sannan ya nufi wajan su Baffah,


Suna zaune a filin gidan suna karyawa yayinda Baffa yake gefe yana hada wasu magunguna Hajar na gefe itada Muneeba tana bata d'umamen tuwon da suke karyawa dashi , sai faman wasa take mata suna dariya,

A hankali yayi sallama ya shigo gidan jikinsa duk a sanyaye , amsa mashi sukayi , har k'asa ya duk'a ya gayar da Baffah da Inna , amsawa sukayi cike da farinciki don Allah ya gani suna matuk'ar kaunar Hisham da tausayinshi , sun fahimci mutun ne mai nutsuwa da hankali ga girmama na gaba dashi sannan a d'an zaman da sukayi sun fahimci mutum ne mai gaskiya da rikon amana ga uwa uba Addini,

"Hamma Hisham ina kwana " cewar Habu da Halliru , amsawa yayi tare da tambayar su aikin da suka tafi yi jiya cikin gari , nan suka shaida mashi komai lafiya qalau,

Juyawa yayi ya mayar da kallonshi wajan da Hajar da Muneeba suke wadda yana lura da ita tunda yarinyar taji muryarshi take ta zillo tanason ta rarrafo inda yake amma Hajar ta hanata sai faman matseta Take a jikinta tana 'yan harare harare ,

Yana yin arba da kwanon tuwon da take d'urawa 'yarshi ya had'e fuska cikin tsawa yace

"keeee wai bana hanaki d'urawa yarinyar nan tuwo ba tunda sassafe sai kinsa tayi k'aton ciki ne, sau nawa zan gayamaki bata isa cin abinci ba , ina madarar da ake bata ne"?

Turo bakinta tayi tace to ai itace takeson cin tuwon nikuma 'ya ta tanason abu bazan hanamata ba ta k'arasa maganar tana murgud'a Dan k'aramun bakinta ,

"Ke Ni kike murgudawa baki lallai bakisan waye Hisham ba ina tausayinki ne wallahi da tuni na 'ballaki oya kuma maza ki saketa tun d'azu takeson zuwa wajena amma kin hanata tsabar kin rainani, ko ?"

Shiru tayi batace komai ba sannan kuma bata saki Muneeba ba duk kuwa da irin yadda yarinyar keson k'wacewa taje wajan babanta don ta saba da Hisham sosai tun bata kai haka ba tafara shaida shi,

Ganin batada niyar sakinta yasa Inna d'agowa daga gyaran waken da takeyi cikin harshen fillanci tace
"Wai ke Hajar wace irin yarinya ce miyasa bakyajin magana ne bazaki saketa ba taje wajan Babanta ,

Cikin shagwa'ba kamar zatayi kuka tace
"Innarmu kina gani fa duk abunda nake ma yarinyar nan bata gani kullum tafinson taje wajan Babanta a kaina to wallahi wataran sai na boyeta ma inda bazai koma ganinta ,

Baffa kam dasu Habu Banda dariyar diramarsu ba abunda sukeyi don in da sabo yanzu sun saba da diramar Hajar da Hammanta kusan kullum sai sun raba hali akan Muneeba , saboda Hajar tana kishin Muneeba sosai ko kadan batason taga yarinyar na kula wani indai ba itaba shikuma Hisham yana jin haushin yadda take kanainaye mashi yarinya wani lokacin ma ganinta sai yamashi wahala sai ya zare mata ido sannan take sararawa duk da haka kwana biyu zata dawo da halinta ,

Hakanan badon taso ba ta saki Muneeba aikuwa da sauri ta rarrafa sai wajan Abbanta sai faman washe mashi baki takeyi irin na yara ,
D'aukarta yayi ya rungumeta yana bata kiss a goshi yace *sweet heart* kina lafiya ? dariya kawai take mashi ,

Hajar kuwa sai faman hararar Muneeba take tanajin haushin yadda takema Hisham dariya harda kyalkyatawa,

Wajan da Baffa yake zaune ya nufa ya zauna kusa dashi yace
"Baffah magana nakeson muyi kuma don Allah inason ka fahimceni Baffah , "

"To Hisham Ina saurarenka"
Cewar Baffah bayan ya mayar da hankali shi ga Hisham din,

Sunkuyar da kanshi yayi a hankali yace
"Dama Baffah na yanke shawarar zan bar wannan jejin ne zan koma cikin gari da zama saboda wasu dalilai nawa , ada naso na zauna anan saboda wani kudiri nawa to amma izuwa yanzu na hakura da duk wani burina inason inyi nesa da idon sani ta ko ina don ganin nabawa 'yata ingantacciyar rayuwa, saboda haka nakeson ka fahimceni Baffah ,

Shiru ne ya ratsa wajan da yake duk suna jin abunda yake fada , Habu da Halliru duk sunyi tsuru tsuru jikinsu a sanyaye don sukam harga Allah basa son rabuwarsu da Hamma Hisham don su murna suke sun samu babban Yaya ,

Kamar daga sama sukaji ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya mai saurare cikin siririyar muryarta mai kama da sarewa tafara fadin
"Wallahi Allah sai dai ka tafi kai kadai ,haka kawai kullum burinka ka rabani da 'ya ta ai nariga na ganoka wallahi Allah Baffah saboda Ni kawai yakeson yayi tafiyarshi don baya sona , tayi maganar tana bubbuga k'afafunta a k'asa cike da shagwa'ba wanda gefe daya Kuma take cike da tashin hankali kar Hisham yarabata da Muneeba ,

Inna ce ta harareta kamun tace wallahi in nak'ara jin maganar ki anan saina tattakaki , shashashar kawai , zumbura bakinta tayi tareda kara fashewa da kuka , azuciye ta juya ta shige cikin bukkarsu ,

Duk abunda take Hisham harararta kawai yake ta k'asan ido , yarinyar tana shige mashi hanci da yadawa ,in banda darajar iyayenta da tuni ya Sa'ba mata kamanni don shi ya tsani yaro sagartacce kuma marakunya to ita kuma yakula anan tafi auki ,

Baffah ne yayi gyaran murya ya dubi Hisham yace .........................โœ๐Ÿผ



Wai wacece mariya???

Wacece kuma Amna

Wanene zayyan mi akama zayyan da mahaifinshi ke aikata wasu abubuwan kanshi

Mi ya fito da Hisham daga gidane ???

Su waye mak'iyanshi da suke neman ran 'yarshi


Hmmmmmmm akwaifa cakwakiya mai girma anan gaba kudai ku kasance tare da Ni don jin yadda zata kaya๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜

*Aslm sister fatan kuna lafiya , ina matan aure yan mata masu shirin yin aure harma da zawarawa masu shirin shiga daki to ku garzayo nesa tazo kuma nazo maku da ingantattun kayan mata masu kyau da inganci irin wadan da baku saba gani ba , sayen dai dai ko sari ina Sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah, don neman kafin bayani ku tuntubeni ta wannan number 09035027743 mmn Yusuf Mai kayan mata yar mutan Sokoto sakkwatawa masu maida k'asari zuma*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿผ

*KARKU MANTA KASAITACCIYAR MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI*๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ
[6/12, 8:18 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ_8


......................"aa baza'ayi haka ba Hisham , narasa wane irin mutum ne kai , kacika kafiya akan ra'ayinka , da kai kadai ne to da zan Barka ka tafi duk da muna matuk'ar son kasancewarka a tare damu ,
A iya zaman da kayi damu na tsawon wata ukku acikin wannan jejin na tabbatar ka fuskanci wasu daga cikin abubuwan masu matukar had'ari dake faruwa acikin wannan yankin, saboda haka inhar ka daukeni a matsayin uba to ban yarda kaje ko ina da wannan jinjirar ba kajira akwai lokacin da Yakamata ka tafi in lokaci yayi Ni da kaina zan umurceka da ka tafi ,

A hak'ik'anin gaskiya Baffah bayason tafiyar Hisham ne saboda abubuwa da yawa da suka tsorata shi dangane da Hisham din tabbas Hisham yana buk'atar taimakon shi , don in har yace zai bar wannan jejin a wannan lokacin to komai zai iya faruwa da rayuwar shi , wannan yasa ya hanashi tafiya ,yanaso sai ya gama bincikenshi akan Hisham kamun ya samu hanyar da zai taimaka mashi ,

Kanshi a k'asa yace
"To shikenan Baffah zan zauna anan din Allah yasa hakan shi yafi alkhairi kuma bazan sake maka maganar tafiya ba har sai inkai ka umurceni dayin hakan Nagode sosai Baffah Allah yasaka maku da mafificin alkhairi, ka maye Mani gurbin da narasa a rayuwata Baffah yanzu banida kowa sai kai sai 'ya ta Muneeba , "

"Sai kuma mu Hamma Hisham" cewar habu yana sakar mashi murmushi ,

Shima murmushin yayi yace
"Hakane habu kudin wani 'bangarene na rayuwata kun so ni da dukkan gaskiya alhalin bakusan koni waye ba Nagode sosai ,"

Kamar ancillota haka ta fito tana washe baki kamar mai tallan makilin cikin sassarfa tace yawwa Hamma Hisham ko kaifa amma in kace zaka tafi ai kaci amanata wallahi don nasan mutuwa zanyi in ka daukemun yarinya katafi , yawwa Baffah Gara da ka hana mashi tafiya wallahi , kaga yanzu ba wanda zai rabani da 'yata. Ko *MUNNI* tayi maganar tana had'a fuskarta data Muneeba tana dariya,

Dariya Baffah yayi yace ai nikam zansha kallon duk lokacin da Hisham yace zai rabaki da wannan yarinyar ,

Turo bakinta tayi tace to kai yanzu Baffah sai ka zuba mashi idanu kana kallo har ya rabamu ??? tayi maganar kamar zatayi kuka,
Dariya Habu yayi yace " kekam Allah ya maki son yara irin wannan k'arfin hali haka ai inaga duk randa kika haifi naki ko kallonsu bazaki bari ayi ba,
Halliru yace " ai mu zuwan Hamma Hisham ya taimakemu don in ka kula yanzu yaushe rabon da akawo mana k'arar Hajar akan 'ya'yan mutane da take daukewa tazo nan dasu wanda da yawa wad'anda basu santa ba suke dauka ko cutar masu da yara zatayi , amma yanzu shiru ba ruwa ta da kowa sai Muneeba,
Habu yayi dariya yace "daina yabonta ba'a yabon dan kuturu sai ya shekara goma da yatsa don wallahi indai Hajar ce ko gobe taga yaron da yayi mata sai ta daukeshi , sunjima suna tsokanarta ita kuma tanata yi masu tsiwa don Hajar badai tsiwa ba ,
Baffah da Hisham kuwa sai firansu suke a hankali inda Baffah ke k'ara bashi shawarwari akan zamantakewar rayuwa ,

Yajima agidan har sai da shima ya karya da tuwon Inna sannan ya tashi ya dauki 'yar shi yakoma wajan bukkarshi dama bashida wajan da yake zuwa daga gidan Baffah sai kuwa Bukkarshi inda ya zame mashi matsayin gidan shi , nan zai zauna yayi ta yiwa 'yarshi wasa yau ma hakan ce ta faru zaune suke a k'ark'ashin wata bishiya iska mai dadi Yana kad'awa yayinda Muneeba keta wasanta a wajan sai 'bingila dariya take , shikuma duk inda ta yi yana biye da ita da kallo murmushi d'auke akan fuskarshi yayinda wani 'bangare na zuciyarshi ke matuk'ar tausaya mata , duk da shi d'in ma abun tausayi ne ,

Kamar daga sama yaji sallamarta,

"Assalamu alaikum Hamma Hisham inuwa ake sha ?"

Kauda kanshi yayi daga barin kallonta batare da yace mata komai ba ,

"Oh Hamma Hisham bakada lafiya ne ? Naga kamar kanajin zazza'bi shine nace bari nazo na tayaka zama kar *MUNNI* tayi kuka ba mai kula da ita akusa ,"

Nan ma shiru yamata , dama yasan kwanan zancan zuwa kawai tayi ta dauke mashi Muneeba ,yarasa wace irin yarinya ce mai shegen nacin tsiya ,duk lokacin da taganshi da yar shi tofa duk yadda zatayi sai tayi taga ta dauke ta ,

Ganin har yanzu bai kulata ba yasata k'arasawa wajan da Muneeba ke wasa ,zama tayi kusa da ita ta rink'a yi mata fira tana dariya Muneeba ma sai dariyar take duk da batasan abunda ake ba , ganin kamar hankalinshi baya kansu yasa ta d'aukar Muneeba a hankali ganin har lokacin bai juyoba yasa ta fara tafiya kadan kadan ta bayan bishiyar tabi yadda bazai ganta ba , tana ganin tabar bakin bishiyar aikuwa tuni tafara zuba sauri harda had'awa da gudu ta nufi wajan da suke kiyo da k'awayenta , tana tafe tana aikin dariya ganin tayiwa Hamma Hisham wayo,

Shi kuwa duk abunda take yana kallonta ta gefen idanunshi ya k'yaleta ne kawai saboda ya gane indai ya biye mata to kullum sai ta sakashi ciyon kai,


*Agurguje pls saboda inason mushiga gundarin labarin ne*


Haka rayuwa tayi ta juyawa dasu inda yanzu Hisham yasaba da zaman shi cikin fulanin sosai kuma yanajin dadin rayuwar shi a haka yayi sabo da mutane da yawa a ruggar sosai suke ganin girmanshi da k'imarshi inda yanzu yake da shekara 3 a wannan ruggar , Muneeba tayi wayo sosai kullum zaka ganta mak'ale da Abbanta wanda take kira da *sweety* Kamar yadda shima yake kiranta da hakan wanda ta koya daga gareshi ne,

Duk da yana ganin lokaci yayi da zai bar wannan ruggar amma sam yakasa yin hakan saboda alkawarin da ya daukarwa Baffa dakuma sabon da yayi da Yan k'auyen musamman ma su habu da suke daukarshi a babban wansu,

Hajar yanzu anzama 'yan mata tanada shekara 17 har ana maganar aurar da ita ga saurayinta Nura wanda ya kasance d'a ne ga aboki kuma aminin Baffa ,
Nura yanason Hajar sosai itama tana sonshi saidai son da yake mata yafi wanda take mashi nesa ba kusa ba , tuni iyayenshi suka so a d'aura aure amma da an tayar da maganar shikenan Hajar zata fara tayar da hauka zanga zanga itace suman k'arya itace sambatu da fisge-fisge kamar wata mai aljanu , wanda hakan yasa ake ta d'aga auren ,kuma abunda yake basu mamaki shine da an d'aga zancan auren to shikenan zata koma normal , wannan yasa iyayen ke tunanin ko aljanu ne suka shafeta sai faman nema mata magani akeyi amma a banza , sau biyar kenan ana saka mata rana abun na warwarewa , wannan yasa Nura ya sameta yana kuka da magiya akan ta taimaka ta yarda asa masu rana don shi harga Allah bai yarda da zancan wasu aljanu ba, ta fadi duk abunda takeson yamata alk'awarin zai matashi inhar baifi karfinshi ba


Aikuwa tanajin hakan ta karkace kai ta janyo d'ankwalinta a goshi irin ture kaga tsiyar nan cikin yamutsa fuska tace

" Nifa bawai sonka ne banayi ba a'a auren ne dai bazanyi ba gaskiya don in nayi aure bansan uban da zai kulamun da d'iyata ba wannan dalilin ne kawai yasa kaga duk akasa mana rana zan rinka abubuwan nan bazan bari ba sai an daga bikin ,

Jikinshi na rawa yafara magana da cewa
"Wallahi Allah Hajar in har kin yarda zaki aure ni wallahi na yarda kije da 'yar ki zan rik'e Maki ita Amana Kamar Ni na haifeta" ................... " Da gaske kake Hamma Nura ?? Tafada fuskarta kamar gonar auduga,
Shima cikin fara'a yace "wallahi da gaske nake Hajar indai wannan ne matsalar to ki kwantar da hankalinki,

Cikin tsananin farinciki tace amma naji dadi Hamma Nura yanzu kam kaje ka samu Babanka ka gaya mashi su turo asa rana na amince tafad'a cike da wauta ,
Shima cike da murna yace yawwa Hajarata bari in tafi yanzu da zafi zafi akan daki k'arfe " ,
"tace to Hamma Nura bari naje nima nafara hada mana kayanmu nida MUNNI ta

Please Login or Register in order to submit comment