Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutum ba wuya , hak'ik'a nasan mahaifinka sosai munyi Zama na mutunci dashi ,saidai Kai bansanka ba gaskiya , sai dai ta dalilin wannan aikin naka Ina Jin sunanka sosai ,to Amma wani hanzari ba gudu ba Hisham , a hakikanin gaskiya Ni bana ra'ayin irin wannan aikin naka saboda wani dalili nawa tun fil azal Ada gaskiya ba karamun kiyayya nakema ma'aikatan yan sanda ba saboda mummunan halin da suka sanyani bada hak'k'ina ba saboda zalunci da rashin gaskiya, ta dalilin mahaifinka nafara fahimtar tabbas ba duka aka taru aka Zama daya ba mahaifinka yayimun hallacin da bazan manta dashi ba har karshen rayuwata ya bautama kasarshi da jikinshi da aljihubshi dakuma aikinshi Wanda a wannan lokacin samun irinsu yanada wuya sosai Amma mi sai gashi duk abunda yayiwa k'asarshi Bai Hana wasu daga cikin azzaluman Yan k'asar had'a Kai wajan ganin bayanshi ba ,Kuma K'iri K'iri hukumar takasa daukar wani mataki akai har Saida Kai da ya Haifa ka jajirce ka k'wato mashi hak'k'inshi ta hanyar gurfanar da wadanda suka aika mashi hakan agaba kotu hmmm wanna. Abun shi yak'ara Mani tsantsar tsanar da nayiwa aikin Yan sanda , cikin ikon Allah kai kuma sai gashi kazo har ka zarta mahaifinka ayadda kakeyin aikinka cikin gaskiya da Amana nasan bazaka rasa magauta ba musamman ma da ko manyan k'asar nan baka k'yalesu ba ,wannan yasa nake ganin bazan iya baka auren 'yata ba Hisham saboda hadarin Dake tattare da wannan aikin naka _zaka iya bada tsaro ga k'asarka Amma bazaka iya bada tsaro ga iyalanka ba_ idanun mak'iyanka zasu tashi daga kanka ne su barbazu Akan Ahlinka Hisham , tabbas zanso hada iri da Kai don Kai din zinari ne Amma mi hakan bazai samu ba sai in zaka ajiye aikinka na *Dan sanda*

Tunda yafara magana zufa ke ketowa Hisham tako Ina , Abu biyu suka taro suka yiwa zuciyarshi rubdugu , na farko tuno mashi gwagwarmayar da mahaifinshi yayi da irin zaluncin da akayi mashi ,na biyu Kuma zancan da yake ta nanata mashi akan bayason aikinshi , maganarshi ta k'arshe ce ta Sanya zuciyarshi bugawa , tabbas yanason. Laurat Amma zai hakura da ita don a duniya ba abunda yakeso sama da aikinshi ,bazai taba ja baya saboda mak'iya ba, kamar yadda mahaifinshi ya jajirce to tabbas shima Koda zai rasa Ransa bazai taba ja baya ba sai inda karfinshi ya kare Kuma bazai d'agama duk wani azzalumin k'afa ba koshi waye wannan alk'awari ne,

A hankali ya d'ago kanshi ya kalli Abban yace "Abba naji dukkan bayaninka ,duk da bansan dalilinka nak'in Yan sanda ba Amma inaso kasani Abba ba duka aka taru aka Zama daya ba , tabbas a ko Ina zaka samu nagari kamar yadda zaka samu baragurbi aciki ,idan har mukace zamu rink'a tsoron abunda zai faru damu ko iyalenmu to har yaushe k'asar tamu zata gyaru ne bayan a kullum muna barinta a hannun azzalumai ne doli ne mu tashi tsaye mu cire tsoro mu fuskanci kowane irin azzalumi ,Allah Yana bayan Mai gaskiya Kuma shi zai bamu nasara akansu ta hakanne zamu samu wad'ansu masu kishin k'asa su zaburo don son yin koyi damu Suma Wanda ta hakan ne zamu taru muzama tsintsiya madaurinki daya mu yake duk wani azzalumin Dake cikin kasarmu kowaye shi Amma nuna tsoronmu shi yake dakushemu a kowane lokaci azzalumai suna nasara akanmu ,bayan Kuma ba Wanda ya isa yayi maka abunda Allah baiyi maka ba , don haka Abba inason aikina sosai bazan iya barin Aiki na ba Koda kuwa Zan rasa wadda zata aureni ne , idan maganata ta 'bata maka kayi hakuri Abba,

Wani gwaron numfashi Abba ya sauke yace "hakane Hisham kanada gaskiya Kuma tabbas samun irinka a k'asarmu abun alfaharin mu ne ,naji na gamasu da Kai Zan baka auren yarinya ta insha Allah kaje ka turomin magabatanka mu tsayar da magana ,sannan. Baza'a dauki lokaci ba insha Allah inason a hada aurenta Dana k'anwarta zainab ,

Wata madarar farinciki ce tafara kwaranya acikin zuciyar Hisham ,Sam yakasa rufe bakinshi sai godiya yake zubama Abban kamun suyi sallama ya tafi yanajin kowace k'ofa ta jikinshi iskan rahama na shigarshi ,duk da yaso yasake ganin tauraruwar tashi Amma Kuma kunyar Abba da dokin son kaima momma labari ya hanashi ,

BAYAN KWANA BIYU

Bayan kwana biyu iyayen Hisham sukazo gidansu Laurat inda yayyu Abba su biyu suka karbi kudin aurensu tare da Sanya Rana wata ukku masu zuwa , sunga karramawa sosai daga ahalin na Abba inda suka rabu cikin mutunci Ana yabon juna ,

Kamar a mafarkin haka Laurat takejin zancan , lallai ta K'ara girmama girman abungiji Abu kamar Wasa Yana nema yazama gaskiya , Sam Bata kawowa kanta aurenta zai yiwu da Hisham ba saboda tsanar da Abban yayiwa duk wani Dan sanda sai gashi cikin sauki Hisham ya shawo kanshi haka ,yanzu ko ya zata kwashe da wannan Dan rainin hankalin oho , ta bangaren zee da momy kuwa kamar zasuyi mi don murna don dukkansu basa son zee tayi aure tabar yayarta a gida sai doli yanzu kuwa kamar anyi masu albishir da gidan aljanna ,

Bangaren momma ma hakane yau kamar zata take kan jariri tsabar murnar da take ciki ita so tayima a rage lokacin a ganinta wata ukku yayi yawa , Hisham yace."Kai Momma kamar gobe ne fa a wajan ubangiji , Kuma inada aiki sosai agabana inason nafara gyaran gidana sannan Zan Gina maki naki bangaren aciki don bazan iya barinki anan ba gaskiya musamman da mukeda nisa sosai da wannan unguwar , "
"Aa Hisham Ni bazan bika ba nafi son nan Dana Saba gaskiya , "
"Aikuwa bazan barki anan ba momma don haka kawai kifara Shirin tafiya " daga haka ya tashi yayi shigewarshi d'akinshi,

-________________________

"Hello sir , eh sir komai na tafiya kamar yadda kace duk wani motsinshi akan idona yake , yanzu hakama Yana neman aure ne har an tsayar da Rana nan da wata ukku, "
"Good big boy aikinka Yana kyau Kuma tabbas ankai wajan da nakeson akai ,yanzu abunda nakeso da Kai shine kaci gaba da aikinka ,Ni zanyi tafiya ne wajan k'asashe biyar akan wasu business nan da wata biyu Zan dawo alokacin ne Zan aiwatar da kudurina akanshi zanga ta yadda zaiyi auren ai,
"Okay oga angama am oga Ina bukatar na sigari fa ba kudi a hannuna "
"Kwana nawa da nabaku 10million ne kaga banason shashanci kaji ko , Kuma ya maganar wancan aikin Dana saku na Alhaji kabiru fatan dai komai Yana tafiya yadda yakamata , "
"Komai normal oga yanzu haka yarinyarshi tana hannunmu sai mungama razanashi sannan zamu fara magana dashi , "
"Good aikinku Yana kyau yanzu inason duk wata kadara da kuka San Alhaji kabiru ya mallaka inason d'ai bayan d'ai kufara banka masu wuta sannan komai zakuyi kuyi cikin tako Sam karku yarda asamu wata shaida da zatasa agane sa wutar akayi, zakuga alert
" okay sir angama daga suka kashe wayar,

_________________________

Sannu a hankali soyayya Mai k'arfi da shak'uwa suka k'ullu tsakanin Hisham da Laurat ,sosai suke zuba love kamar ba gobe ga tsantsar kulawa da suke da junansu , duk da hakan Basu daina fadan da sukeyi ba don duk lokacin da suka had'u to sai sun raba hali (da alama dai haka nasu salon soyayyar yake, 😉)

AGURGUJE

BAYAN WATA BIYU DA SATI BIYU,

sosai 'bagarorin biyu suke shirye shiryen bikin 'ya'yansu , Baffan Hisham yazo daga sokoto yayan Abbanshi da matarshi dakuma yayanshi sai Inna asabe itama tuni tazo sai faman shirye shirye suke ,

Hakama 'bangaren su laurat Yan uwansu na nesa tuni sunfara zuwa saboda gaba daya kwana goma ne suka rage adaura auren,

A 'bangaren Alhaji Saminu kuwa tuni yagama shirya duk wani Shirin da zaiyi a wannan karon don yaci alwashin bazai taba Bari ayi wannan auren ba hasalima yanaso ne a kashe mashi Hisham din gaba daya aranar da za'a daura mashi auren ko Kuma Daren d'aurin auren, yaci alwashin sai ya kuntata mashi ta hanyar sawa ayiwa amaryarshi fyade a gabanshi sannan shima su aikashi inda baa dawowa,

BAYAN SATI DAYA

Yau saura kwana ukku d'aurin auren ayau narba akayi kamu awani shahararren hotel Wanda ya k'ayatar sosai ango da amarya sun zuba kyau sosai ran jumu'a zasuyi walima Wanda iya Mata ne kawai zasuyi sai assabar da zasu gudanar da dinner ,bayan d'aurin aure,
Da misalin k'arfe 8pm tafe suke a motar da aka tanadarma amarya da ango , wani abokin Hisham ne Mai suna Yazid yake Jan motar yayinda sauran abokan angwaye da kawayen amare tuni suka tsufa a gida sai Yan wadan da baza'a rasaba na kusa dasu , saboda sun tsaya ne Saida sukaga tafiyar kowa sannan ,

Motar dake dauke da Zee da angonta Abdul ne agaba sai motar wasu daga cikin abokan Hisham din ,sannan tasu Hisham itace a k'arshe , tafiya suke a hankali yayinda gaba daya Hisham yake Jin kansa a wani lasalance Wanda ba komai ne ya canza mashi yanayi ba kamar wani irin sihirtaccen k'amshin turaren da yake fitowa daga jikin amaryar tashi yanashiga kowane sako da lungu na jikinshi Yana aika mashi da zazzafan sak'o , tun Yana daurewa har hakurinshi ya Gaza ya janyota jikinshi cikin kasalalliyar murya yace "irin wannan k'amshin haka baby Mai shiga jiki da 'bargo da kinsan yanayin da yake saukarmun da bakiyi amfani dashi a yanzu ba gaba daya ya tayarmun da ........bai k'arasa ba yadora hancinshi akan dokin wuyanta Yana shakar k'amshin da kyau, (hmmmm kadan daga cikin aikin hatsabiban turarruka na maman mamah Yar mutan Niger wadda take zaune a Kanon dabo GRA tanada turarruka masu gigita nutsuwar mai gida ya nemeki ko bashida niya💃💃 08142577927 ga number ta gamai bukata)

Lokaci daya Laurat ta rikice abunda Bai taba faruwa da itaba , mutsu mutsu tafara zata kwace Basu Ankara ba saiji sukayi yazid ya taka wani wawan birki Wanda yasa suka juyo a firgice suna salati , a tunaninsu ma wani suka buge Amma abun mamaki sai gani sukayi mutane sun zagayesu kowannesu sanye da fuskar roba yayinda hannayensu ke rik'e da muggan makamai,

"Hasbunallahu wa ni'imal wakel Innalillahi wa inna ilaihin rajiun shine abunda Laurat da yazid suke fad'a cike da firgici , kamun Laurat ta fashe da wani irin kuka , yazid kuwa muk'ut haka ya had'iye Dan sauran yawun da ya rage mashi , babban tashin hankalinshi shine gaba daya motocin da suke tare sunyi masu nisa sanadiyar gudun da sukeyi bare su San halin da ake ciki ,

Shikuwa Hisham shanyayyun idanunshi da suka Kara shigewa ciki saboda fitina ya zuba masu Yana kallonsu dai bayan dai ,
Cikin wani irin sauti Marar Dad'i d'aya daga cikin mutanen ya buga masu tsawa akan maza su fito waje , kamun ma ya rufe bakinshi yazid da Laurat sunfito jikinsu na mazari cikin mugun tsoron abunda zaije yazo , wata tsawar suka sake dakama Hisham Akan maza ya fito waje ,a hankali ya bude k'ofar motar ya fito shima yanayi masu kallon ido ciki ido, irin kallon nan na Kar tasan Kar,
Babban cikinsu ne ya k'araso kusa da Hisham yace welcome Jamiin Dan sanda JAMI'I Mai gaskiya hhhhhhhh yaudai k'aryarka ta k'are dama can k'yaleka akayi kana tsula tsiyarka saboda baka samu daidai da Kai bane yanzu kuwa ka tabo Zaki alokacin da yake tsakkiyar farautar abunda zaici ,hhhhhhh ango ango gaskiya na tausaya ma malam Hisham , gaba dayansu mutanen suka kwashe da dariya Wanda suke su shida ne Dama saidai kallo daya zakayi masu kasan cewa sudin majiya k'arfi ne sannan Sam Babu alamar Imani ko tausayi a tare dasu , ganin yadda suke babbaka dariya Mai cike da izgilanci da rashin Imani yasa Laurat Kara fashewa da kuka tana rokonsu akan don Allah suyi hakuri karsu cutar dasu ,
K'arasowa babban nasu yayi kusa da ita Yana Kare Mata kallo yace " wow a gaskiya malam Hisham ka iya za'be irin wannan zukekiyar yarinya haka Kai gaskiya zamu more da yawa to irin wannan ai ko oga baice muyi Mata fyade ba to yazama doli mukwashi gara bare Kuma yace muyi , Jin wannan maganar yasa Yan hanjin Lauratu hautsinawa nan take numfashinta yafara sama sama tsabar rud'anin da tashiga da tashin hankali , Hisham kuwa ko d'ar baiji ba sai kallon ukku saura kwata da yake aika masu ......................✍🏻


*Mmn Yusuf Mai kayan mata* 😉😉 *munada zafafan kayan Mata Ina sokoto Ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah maiso PC 07069711327 call or WhatsApp*
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍✈️ *JAMI'IN DAN SANDA*👨🏻‍✈️

*_MALLAKAR_*

~MARYAM UMAR ABDULLAHI~
( _MMN YUSUF_)
*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*


🅿️_35

....................."Kai ku wuce muje ,Kuma wallahi k'wak'waran motsi kukayi sai na tarwatsa kan mutun da bindigar nan , yayi maganar yana fito da bindiga daga k'ugunshi , ai kadan yarage yazid ya saki fitsari a wando ganin bindiga kuru kuru, Laurat ma kasa motsi tayi idonta a waje cikin tsananin firgita take kallon bindigar da marik'inta , tsawar da ya koma daka masu ce tasa Laurat da yazid fara tafiya har suna kusa fad'uwa saboda rawar da jikinsu keyi, Hisham kuwa a hankali yafara tafiya Yana bin bayansu yayinda hannayenshi ke saman kanshi, bayan daya daga cikinsu yagama cajeshi tsaf ya tabbatar da baya tare da wani makami, mutum biyu ne a gabansu biyu a bayansu sai d'ayansu a gefensu na dama d'aya a gefen hagu , sunyi masu k'awanya , da yake wajan wajene da bashida hayaniya ko kad'an saboda k'arancin gidaje da abun hawa Dake wajan ,
Wata siririyar hanya suka bi dasu wadda ta yanka tayi cikin wani Dan k'aramun jeji Dake wajan,

Tuni yaron dake hannunsu na hagu ya shagala da kallon bayan Laurat ganin yadda take tafiya ko Ina na jikinta Yana motsawa , kasancewar doguwar rigar Dake jikinta ta wani yadin material ce Mai rawa rawa anyi Mata dinki dai dai da jikinta irin dai dogayen rigunan da akeyiwa Amaren yanzu wannan yakara taimakawa wajan bayyanar asalin hallitanta ,kallonta yake Yi Yana lashe Baki kamar tsohon maye idanunshi kuwa tuni sun k'ara rinewa tsabar jaraba Allah Allah yake suk'arasa ya far Mata don yasan ba karamar gara zai kwasa ba, Kai sikam gaskiya Yana ganin yafi kowa Jin Dadin wannan aikin da zasuyi,
............duk halin da yake ciki Hisham na kule dashi , aikuwa ji yake kamar Ana tsatstsaga zuciyarshi da wuk'a wani kallon gefen ido yakema mutumin cikin wani irin 'bacin rai na bala'i ,lokaci daya shima idonshi suka riked'e suna fidda wani irin yaji acikinsu ,ga wani k'aton Abu da yazo ya tokare mashi mak'oshi kamar zai hallakashi da k'yar ya had'iye wasu yawu masu d'aci Yana tunanin yadda zaiyi dasu ,
Kasa hakuri mutumin yayi ya d'aga hannunshi zai shafi duwawun ta da suke fisgarshi awar mayen k'arfe duk ta rud'ashi har ya manta abakin aiki fa suke,
.......tuni Hisham ya ankare da abunda yake Shirin yi , aikuwa cikin tsananin zafin nama irin na Wanda yasamu kwararren training ya fisge k'atuwar addar Dake hannun mutumin Dake hannunsu na dama kamun kace mi yakawo hannun wannan gayen Sara , aikuwa Basu ankaraba sai ji sukayi mutumin ya buga wata irin k'ara wadda Saida Dan k'aramun dajin ya amsa kuwa ba karamun razana sukayi da Jin karar tashi a bazata , wannan yasa duk suka juyo kanshi a sittin.kamun sugama fahimtar abunda ke faruwa tuni Hisham yayi wani tsalle kamar d'an biri sai gashi agaban babbansu Wanda shine yake rik'e da bindigar , cikin second yabashi wani uban naushi afuskarshi Wanda yasa shi daukewar wuta na wuccin gadi , kamun yagama dawowa dai dai Hisham ya fisge bindigar ya Kara maka mashi wani nauyayyan naushi a muk'amuk'inshi , take k'aton mutumin ya zube k'asa warwas jini na fita ta hancinshi da bakinshi , duk wannan abun yafaru acikin Yan seconds Laurat da yazid sun rud'e sosai , ganin abunda yafaru ga hannun wannan mutumin Yana reto don k'iris yarage ya guntule hannun, ganin abunda yafaru da ogansu yasa daya daga cikinsu Kama yazid ya d'ora mashi k'atuwar wuk'ar Dake hannunshi a wuyanshi Yana kallon Hisham cikin fusata yace
"Ka ajiye bindigar nan kayi saranda ko yanzu na fille mashi Kai wallahi ,"
Hisham kuwa saitasu da bindigar yayi Yana huci yayinda ya janyo hannun Laurat ya mayar da ita bayanshi , jikinta Banda cira ba abunda yakeyi tsabar rikicewa da rudani yasa ko kukan ma takasayi kana kallonta kasan tuni ta fice a hayyacinta,

Jin abunda mutumin yake fad'a yasa yazid sakin fitsari Babu shiri tuni idonshi sun Raina fata musamman da ya ga yadda Hisham ke tsaye ya saitasu da bindigar Sam bashida niyar sauketa kamar yadda suka buk'ata saima tsananin fushi da yake hangowa acikin idonshi,

Batare d'a Hisham ya kula ba daya daga cikinsu ya jefa mashi wani k'aton dutse a hannunshi Mai rik'e da bindigar , take bindigar tayi tsalle tafadi can nesa dasu cikin ciyayin Dake wajan, aikuwa ganin hakan yasa suka nufoshi su hudu da addunasu da niyar su sassara shi , kamun kace mi wajen ya har mutse Sara da suka suke kawo mashi kota Ina Amma cikin ikon Allah ba Wanda yake samunshi , sun dauki 5mnt ahaka kamun yasamu nasarar kwace addar daya daga cikinsu yafara Kare kanshi da ita , cikin kwarewa da sanin makasar mutum yarinka samun sa'arsu Yana naushinsu agefen wuya kamun kace mi duk sun zube a wajan suna murkususu rik'e da wuya Wanda sukejin kamar ransu zai fita saboda ba karamun naushi yayi masu ba , wayarshi ya fito da ita yafara Kiran yaranshi , ba'a dauki lokaci ba sai ga amintattun yaranshi su Jafar da asmy da sawu mutum hudu ,
Kusa da babbansu Hisham ya tsaya Wanda har lokacin baigama dawowa dai dai ba , k'afarshi yasa ya dakeshi ak'irji tare da buga mashi wata irin tawa yace "uban waye ya aikoku wajena ,?wane Mai gangancin ne yake neman shiga gonata "
Cikin rawar jiki data murya ogan yafara magana a galabaice yace "deputy Governor ne Alhaji Saminu Sulaiman don Allah kayi hakuri yalla'bai, batare da Hisham yace komai ba yabawa yaranshi damar kamasu su tafi dasu ,

nan take suka tarkata mutanen suka sasu a mota sukabar wajan a guje ,

Juyawa Hisham yayi Yana kallon yazid da Laurat da har lokacin Basu Gama dawowa normal ba , dafa kafadarahi Hisham yayi yace "kayi hakuri abokina kuzo muje ,hannun Laurat ya riko suka fara tafiya , binshi takeyi kamar rakumi da akala don Sam takasayin tunanin komai ,motarsu suka shiga wannan karon Hisham ne ya tuk'a motar don ya tabbatar da yazid bazai iya tuki ba a wannan halin, tafiyar kusan minti 15 ce ta kawosu gidansu Laurat Wanda sun tarar su zee tsaye abakin get din hankali a tashe suna tunanin abunda ya tsayar dasu wani ikon Allah Kuma ba Wanda yy tunanin kiransu a waya,

Kallon ta yayi har yanzu a hargitse take yace " yakamata ki sa nutsuwa a ranki don karsu fahimci abunda yafaru , sannan ban yarda ki gayawa kowa abunda yafaru ayau ba kirik'eshi aranki wannan umurni ne ,d'ago kanta tayi ta watsa mashi wani mugun kallo cikin tsiwa da fad'a tace "aikuwa yazama doli na fada don bazan ta'ba gangancin aurenka ba a wannan yanayin Ni ban shiryama mutuwa ba wallahi haka kawai bazaka cajamun tashin hankali ba , inkuwa har ka nace kana Sona to tabbas saidai ka ajiye wannan aikin Naka da Babu kwanciyar hankali a cikinshi , Ina dalili tunda nake ban taba shiga tashin hankali irin wannan ba sai yanzu tarayyata dakai aa wallahi da sake da............."keeee ya isa hakan fita kibani waje karki Kara batamun Rai kinzo kinsa wani shegen Riga da wani figaggen kyale kinsa sai wani kallonki ake Baki barni da wannan 'bacin ranba Zaki karamun wani oya don Allah malama kificemun a mota Kuma Kar Allah yasa ki k'i yin abunda nace ,

Gaba daya wutar Laurat ta dauke gaskiya tayi Mata yawa har takasa cewa komai , tana hango tsananin kishinta a idanunshi Wanda komai zai iya faruwa in taci gaba da Zama kusa dashi , bude motar tayi a hankali ta fita batare da tak'ara kallon inda yakeba tayi shigewarta gidansu da yake su zee tuni sun koma ciki tun lokacin da suka ga isowar motarsu,
Cikin sa'a kuwa ta tarar da ba mutane a falon da sauri ta wuce bedroom din su ,tana shiga tafara cire kayan jikinta tana jifa dasu tana hawaye , toilet ta shiga ta sakarwa kanta ruwa tana kuka Mai cin Rai da anbaton innalillahi wa inna ilaihin rajiun , wannan wane irin bala'i ne k'asarmu take ciki , Wanda manyan k'asar ma sune da kansu suke aikata rashin adalci ga talakawansu yanzu badon Allah ya tsare ba da shikenan hakanan kattin banza zasu keta Mata alfarmarta Wanda tajima tana tanadawa tsayin shekaru bataji ba Bata gani ba batasan tsakaninsu ba saboda kawai rashin tsoron Allah da rashin Imani, tajima a bandakin Saida taji mutane sunfara taruwa a d'akin sannan ta daure tayi wanka ta fito rik'e da kanta Bata kulasu ba tafara Sanya kayan baccinta duk kuwa da maganar da suke Mata tana gamawa ta haye gado ta lullube kanta bayan tace masu kanta ke ciyo,

...............................

Tunda tafita daga motar ya fisgeta a fusace yabar k'ofar gidan yazid sai hakuri yake bashi ,duk da akasan ranshi Sam baiga laifin Laurat ba don ta tsorata ne shi kanshi har yanzu a tsorace yake don har ya sare ga sake rayuwa ,shima gidansu ya kaishi bayan sunyi sallama ne ya juya ya dauki hanyar gidan Alhaji Saminu cike da fushi , (tau fa🙊)

A hanya ya tsaya yayi sallar Isha Wanda dama basuyi ba sannan yak'arasa gidan , Mai gadi ne ya leko Jin Ana hon , bude k'aramar k'ofar yayi yafito ya nufi Hisham Yana zuwa yace " bawan Allah wa kake nema ne ,
"Deputy Governor nake nema fatan Yana nan , "
" Eh Yana nan saidai baya ganin bak'i a daidai wannan lokacin Kuma Bai ce akwai Wanda zaizo wajansa ba don haka kayi hakuri ka koma ko ka kirashi kanemi izini awajanshi, "
"Aa bazan koma ba akwai buk'ar ganin nashi ne a yanzu , kasancewar securityn Jami'in dan sanda ne yasa Hisham fito da l D dinshi ya nuna mashi, take security ya Sara mashi kamun ya juya da sauri ya bude mashi get din gidan ,a tunaninshi wata matsalar ce ta taso ,

Parking Hisham yayi a tsakkiyar filin wajan , Bai damu da inda ya ajiye motar ba ya fito ya doshi wasu ma'aikata Dake d'an nesa dashi , Suma ID dinshi ya nuna masu kamun ya tambayesu inda zai ga maigidan ,
Wani part Mai shegen kyau suka nuna mashi tare da gayamashi Amma Yana meeting ne ,Bai sake bi takansu ba ya doshi part din kamar gidan ubanshi Sam Babu tsoro ko fargaba atare dashi,

Bakin k'ofar ma wasu securitys ne suna ganin ID dinshi suka barshi ya wuce da tunanin k'ila shima Yana cikin masu meeting din,
Baijira komai ba ya bude k'atuwar k'ofar da yake kyautata zaton anan ne suke meeting din don Yana jiyo maganganunsu sama sama ,
Da sauri duk suka juya Jin aturo k'ofar falon batare da neman izininsuba cikin tsananin mamaki Alhaji Saminu Sulaiman ya mik'e tsaye Yana nunashi da yatsa yayinda sauran mutanen ma suke binshi da kallon mamaki da raini ganin yadda ya shigo masu ba sallama bare neman izini gashi ya tsaresu da ido Yana yi masu kallon ukku saura kwata,

A gefe d'aya Kuma

Please Login or Register in order to submit comment