Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta saki jikinta , don ta kula daga Momma har Hisham basu gama dawowa hayyacinsu ba barinsu su kadai zai iya haifar masu da wata matsalar saboda yawan tunani da damuwar da suke ciki,


Agurguje pls๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„Zan baku agurguje saboda inason mushiga gundarin labarin ne don wannan sharar fage ne kawai kuma sam ba wannan matsalar ce ta rabo Hisham da gida ba cakwakiyar tana gaba๐Ÿ˜๐Ÿ˜


*Bayan wata shida*

Zuwa yanzu komai yazama tarihi Alhamdulillah daga Momma har Hisham sun mik'a lamarinsu ga Allah suna rayuwa cikin farin ciki , saidai yanzu gaba daya Hisham ya canza yakoma shiru shiru sam bayason abunda zaisa yayi magana yakoma miskilin karfi da yaji Momma ma yanzu saidai taga murmushinshi amma badai dariya ba ga wani fad'a da ya taso mashi abu kadan zai kama masifa a haka dai sukaci gaba da rayuwa kuma har wannan lokacin inna Asabe tana tare dasu duk lokacin da tace zata tafi yanzu Momma zata fara koke koke shiyasa yanzu har ta daina cewa zata tafi ,


Dayan bangaren kuwa kkowanne da damuwa dankare acikin zuciyarshi saidai suna kokarin nunawa juna basa tare da wata damuwa ,
Momma tana zargin kashe mata miji akayi saboda wasu dalilai amma takasa gaya kowa batasan yadda Hisham zai dauki al'amarin ba shiyasa taja bakinta tayi shiru ,

Yayinda a 'bangaren Hisham yake ta tunanin ta yadda zaiyi ya shawo kan Momma ta barshi *ya cikawa mahaifinshi burinshi na zama _Jami'in dan sanda_*

Yau ma kamar kullum suna zaune a dining suna karyawa ya d'ago kanshi yace "Momma akwai maganar da nakeson muyi amma don Allah inason ki tsaya kiyiwa abun kyakkyawar fahimta Kuma pls momma karki ce Zaki hanani don Allah ,"

"Ina jinka Hisham gayamun mi kake so , "?

Cikin inda inda yace Momma dama shekaranjiya ne naje na cike Form na aikin *dan sanda* to inatason namaki bayani amma...............baisamu damar k'arasawa ba sakamakon wani irin tari da ya sark'e Momma , a rikice ya debo ruwa zai bata amma ga mamakinshi sai gani yayi tasa hannu ta ture ruwan tareda wurga mashi wani irin kallo wanda tunda yake da ita bai taba ganin tayi mashi koda makamancin shi bane ga wani tsantsar tashin hankali da fushi hade da masifa da ya hango acikin kwayar idanunta ,

Pls momma .............hannu ta daga mashi kamun ta tashi tabar wajan batare da ta ko kalli inda yake ba,.................โœ๐Ÿผ



*Zanyi aike Kano da Zamfara gobe kuma kudin motar kyauta ne maiso ingantattun kayan mata tayimun magana ta pc ngd* 09035027743[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜

_wannan shafin nakine my takwara (Maryam taly) kiyi yadda kk so dashi_๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ


๐Ÿ…ฟ๏ธ_18


.......................sati na zagayowa yafara fita aiki , inda Momma tayi mashi nasihohi masu ratsa zuciya da addu'o'in samun nasara , haka ya fita yanajin wani irin farin ciki a zuciyarshi wanda yarasa gane kona minene , amma tabbas a yanzu yanajin son aikinshi har cikin zuciyarshi ,

Satinshi d'aya da fara aiki DPO Huzaifa Umar ya fahimci irin nagartar da Hisham yake da ita , aiki yakeyi tuk'uru da dukkan gaskiya da amana uwa uba tsantsar k'warewar da yake da ita akan aikin kamar wanda ya jima acikin aikin , wanda ba komai ne ya janyo hakan ba sai tsabar kaifin basira da irin horon da ya samu akan aikin,
Wannan dalilin ne yasa sir Huzaifa ya janyo shi ajiki tare da k'ara mashi k'warin gwuiwa akan yadda yake gudanar da aikinshi , sannan ya damk'amashi case din wasu Criminals da ake nema ruwa a jallo , amma kamasu ya gagara saboda wadan da ake d'orawa akan case din tuni an siyesu shiyasa suka kasa aiwatar da komai akai , sai dai surink'a nuna suna iyakar k'ok'arinsu akai,

Asmy da Jafar da Zubair su Sir Huzaifa ya za'ba a matsayin wad'an da zasu taimakawa Hisham akan case din kasancewar su amitattu a gareshi ,

Cikin ikon Allah kuwa sai gashi acikin kwana ukku kacal Hisham da abokan aikinsa sun samu nasarar kama mutanen da ake nema tsawon shekara biyu amma ankasa kamasu saboda halin nigeriyanci da akeyi a k'asar nan,

Wannan nasarar da Hisham ya samu ba k'aramun janyo mashi farinjini yayi ba a hukumar tasu ta yan sanda, yayinda d'ayan 'bangaren yafara tsonewa wasu ido a hukumar in da suke ganin doli su tashi tsaye don ganin wannan sabon zuwan bai sha gabansu ba a hukumar tasu,

Jin dadin wannan aikin ne yasa sir Huzaifa zak'ulo wasu cases da suka gagari sauran 'yan sandan ya d'ora alhakin bincikensu akan Hisham ,
Sai gashi cikin kankanin lokaci sunan Hisham yayi amsa kuwa a cikin hukumar tasu harma da wajen gari , aiki yakeyi tuk'uru don zak'ulo duk wasu 'bata gari dake cikin garin na Lagos , babu ruwanshi da kudink'a ko muk'amin ubanka duk wanda ya kama da wani laifi to zai gurfanar dashi a gaban hukuma ne ,

Lungu da sak'o suke shiga suna kama masu laifi kamar 'yan fashi da makami , masu garkuwa da mutane, k'ananan 'barayi, masu yiwa mata da k'ananun yara fyade , wadan da sunema yafi tsana akan komai , sai kuma 'yan shaye shaye kamun kace mi tuni labarin *ASP Hisham Abdurahaman* ya karad'e garin na Lagos inda jama'ar gari ke jinjina mashi tare da yimashi fatan alkhairi don hak'ik'a ya kawo sauyi mai d'umbin yawa acikin garin , duk wani iskanci yanzu sai dai ayi shi a 'boye don ya hanawa kowa sakat , musamman 'ya'yan masu kud'i da suke ganin ya shige masu hanci da yawa ,yayinda iyayensu ke ganin cewa ya takurawa ฦดaฦดansu da yawa ,

Acikin kame kamensu ne suka kama yaran su Alhaji Manu su ukku , kolo, kunama, da kuma Goga, sun kamasu ne a lokacin da suke k'ok'arin shigowa da hodar ibilis , duk da kuwa sunyi matuk'ar shirya shirin da yanada wuya agane mi suke dauke dashi , sai dai cikin ikon Allah kallo Daya Hisham yayi masu yaji bai aminta dasu ba wannan yasa yabada umurnin da abuba kayan da suke dauke dasu ,

Da fari sam basu damu ba don aganinsu ba mahalukin da zai gane shirinsu ,

"Sir na duba bakomai aciki gaba daya kifi ne acikin motar , " cewar wani dan sanda ,

Zama Hisham ya gyara akan saman motar da yake zaune fuskar nan tashi ba alamar sassauci aciki yace " ku k'ara dubawa dai"

Nan suka shiga bincikar k'atuwar motar da aka ciko taf da danyen kifi cikin kwalaye ,har zuwa lokacin basuga komai ba , yayinda su Goga keta aikin murmushi don sun san bazasu ta'ba gane komai ba,

Ganin hakan yasa Hisham tasowa da kanshi inda yayi tsaye yana k'arewa kifayen dake cike acikin kwalaye , umurni ya bayar akan a dauk mashi kwali daya ,
Da hanzari Jafar ya dauko ya kawo inda yake , alama yayi mashi da ya bud'e kwalin ,

Ido ya zubama manya manyan kifayen yana kallo , sai can idonshi ya sauka akan wani sirrin zare dake wajan cikin kifin ,
Duk'awa yayi a hankali ya sanya hannu ya ta'ba wajan , ganin da gaske dai alamar dinki yake gani yasa wani daga cikin yan sandan akan ya dauko abu ya 'bare mashi cikin kifin,

Tunda su Goga sukaga hakan cikinsu ya duri ruwa nan fa suka nemi hanyar guduwa sai dai babu dama don tuni yan sandan sun zagayensu da bindigogi tunda suka fahimci kudurinsu,

Aikuwa ana 'bare cikin kifin sai ga ledar hodar ibilis aciki , dukkansu mamaki da tsoro ne ya kamasu ganin wata sabuwar hanyar yaudara da aka samu tabbas wadan nan mutanen suncika hatsabibai , nan sukaci gaba da duba kifayen duk wanda suka bude to zasu samu leda biyu ko ukku aciki , wannan yasa aka rufe motar aka hannuntata ga yan sanda yayinda su kuma su Goga aka wuce dasu CID diret don case dinsu babba ne,


Aikuwa lamarin ba k'aramun d'aga hankalin su Alhaji Musa yayi ba don kayan da aka kama kayane na miliyoyin kud'i , abun yazo masu a bazata don sun riga da sun sakankance akan cewa bawata matsala don sun siye duk wasu jami'ai Da kayan zasu iya biyowa ta hannunsu,

Babban tashin hankalinsu ma shine yaransu da aka kama , kar su bayar da wata masaniya akansu ,

Gaba daya a rikice suke duk da sanyi AC dake falon sai hada zufa sukeyi , Alhaji manu kuwa sai faman shafa sank'on kanshi yakeyi yanajan tsaki gaba daya yarasa abinda zaiyi,

A fusace Alhaji Buba yace " wai tsayama tukunna wane mai tsautsayin ne ma da k'arar kwana har yayi gigin shiga hurinminmu irin haka , mi yake tak'ama dashi ne , lallai sai ya dandana kud'arshi tunda har ya yarda tsautsayi ya sanya shi shiga gonarmu ,
Alhaji Manu ka kira mana Zakari inason sanin wanene mai wannan zarrar acikin hukumar tasu,

Daukar wayar yayi ya dannawa Zakari kira , bugu biyu Zakari ya dauka tare da fad'in " ina kwana oga, "

Bai amsaba yace " nasan kasan duk abunda yake faruwa , wanene shi dami yake tak'ama sannan mi ake ciki a yanzu ,??"

Ajiyar zuciya Zakari ya sauke yace "oga wallahi akwai matsala don in har bakuyi wani abuba da gaggawa to komai zai iya faruwa , don wannan yaron bashida mutunci ko kadan , jiya agaban idona akayi komai sai dai banida ikon hana komai kasancewar yana gaba dani , maganar da nake maka yanzu haka yaranku basu cikin station din Nan tun jiya aka wuce dasu C I D don .............. Katseshi Alhaji manu yayi cikin tsawa yace kai banason maganar banza to ku miye amfanin ku kenan miye amfanin makuddan kud'ad'en da muke baku ne , yazama doli kuyi wani abu inba hakaba wallahi duk sai kun had'u da fushina ,

Gaba daya jikin Zakari ya dauki rawa don an sakashi cikin tsaka mai wuya , cikin rawar murya yace " oga Yakamata fa ka fahimci maganata abun nan fa babba ne sam ya wuce tunaninku , yaron nan wlh ba k'aramun hatsabibi bane sannan ya samu goyon bayan D P O yadda baka tunani duk abunda yakeyi ma da d'aurin gidinshi yakeyi shiyasa baya shakkar uban kowa , sannan duk wani babba da yake cikin jami'a mu sun san da maganar kuma yanzu haka zancan da nakemaka zancan turasu kotu akeyi , abunfa ya wuce inda kake tunani wallahi , shegen yaron nan zuwan jiya jiya yazo duk ya tayar mana da hankali ya shige mana gaba bamuda wani motsi yanzu a hukumar sai abunda ya aikata yanzu haka jiya da dare dan gidan ministan Kudi ya kamo ya sank'ama a cell har yanzu ankasa fitar dashi don kiri kiri oga ya goya mashi baya , yanzu dai ya kamata.....................cikin tsananin 'bacin rai da tafasar zuciya Alhaji manu yace to wai shi wannan yaron dan gidan uban waye haka , waye ubanshi a garin nan , mi yake tak'ama dashi da har zai zo ya ruguzama shirin da muka shafe shekaru munayi ," .......


"Oga ka kuwa san ko waye wannan yaron ? To wannan yaron ba d'an kowa bane sai d'an *inspector Abdulrahaman* sannan yayi gadon kafiya da taurin kai irin na ubanshi kai harma ya zarta ubanshi da muguwar ak'ida ," nan Zakari ya karkace baki yarinka zuba yana fada masu abunda yasani akan Hisham ,

Tun lokacin da Zakari ya ambaci sunan Inspector Abdurahaman daga Alhaji manu har su Alhaji Musa basu sake fahimtar abunda yake cewa ba ,da yake wayar a hans free ya sakata ,

lokaci d'aya sukaji zukatansu sun buga a tare da wata irin fargaba da basu taba jin irinta ba , lokaci daya suka fara sharce zufa ,
Dama inspector Abdulrahaman yana da d'a , ? Kuma har wanda ya girma haka , d'ansa ne kokuma d'an 'yanuwansa , tambayoyin da sukeyi acikin zukatansu kenan, sunjima a haka an rasa wanda zai fara magana acikinsu sai can Alhaji Buba yayi tsaki yace " shima zamu turashi inda muka tura ubansa ne, daga haka ya mik'e ya
Shige cikin wani d'aki , dukkansu da kallo kawai suka bishi duk da suma sun kasa gane abunda ya haifar masu da wannan fargaban , abunda Basu ta'baji akan wani mutum ba,.......



***********************


Da sallama suka shiga gidan , tana tsakar gida tana wanke wasu kwanuka yayinda take taunar cingum k'as k'as tana Yan wak'e wak'enta , duk da taji sallamar da akayi hakan baisa ta d'ago da kanta ba ma bare ta amsa sai wake wak'enta takeyi,
K'wafa Mansur yayi baice mata komai ba yaja hannun Abokinshi Ibrahim suka wuce dakin yayan nashi,

Yana kwance bisa katifa sai ma ka kula da kyau ne sannan zaka san da mutum a wajan saboda yadda ciyon ya cinyeshi gaba daya banda k'aton kai ba komai ajikinshi duk ya yamushe ya k'ank'ance yayinda yake fitar da numfashi da k'yar tsabar yadda yake jin jiki , da sauri Mansur ya k'arasa kusa dashi yana riko hannunshi yace " sannu yaya Haruna ya jikin naka , ? Kayi hakuri yau banzo da wuri ba nima na tashi da ciyon kai ne shiyasa , kamashi yayi ya tayar zaune ya jingina shi da bango sannan ya dauko ledar da yazo da ita, shayi ya hada mashi yabashi yasa sosai sannan ya fara bashi maganinshi , acikin zuciyarshi kuwa Banda tsinema matar yayan nashi ba abunda yakeyi, sai k'wafa yakeyi ,

Ibrahim ma jiki a sanyaye ya zauna daga gefe yana yiwa yayan na Abokinshi sannu da jiki cike da tausayawa, harda yar kwallar shi don Ibrahim akwai tausayi sosai ,

A hankali Haruna yake amsawa yayinda ya kafe Ibrahim da ido yana tunanin a ina yasan fuskar nan ne,

Can Allah yasa ya tuna , aikuwa a zabure yayo kan Ibrahim din da nufin isowa wajanshi amma sai yakasa saboda rashin karfin jiki, yafito Ibrahim yarinkayi da hannu alamar yazo inda yake ,

Da sauri Ibrahim ya karasa kusa dashi , hannu biyu yasa ya rike hannun Ibrahim din yana numfashi da k'yar yafara magana wanda da kyar ma akejin abunda yake cewa ,

"Dan samari kamar nasanka a gidan marigayi inspector Abdulrahaman ko ?"

Gyad'a kawai Ibrahim yayi yana mamakin dalilin shi nayi wadan nan abubuwan don shi kam dama kallo Daya yamashi ya tuna ya sanshi abokin aikin Abban Hisham ne ashe shine yayan Abokinshi Mansur,

Maganar Haruna ce ta katse mashi tunanin da yakeyi jikinshi har wani rawa yakeyi yaci gaba da cewa , " don Allah ina yaron Abdurahaman , dakuma matar shi , don Allah Dan samari ka taimaka kayi mun wata alfarma don darajar Annabi Muhammad SAW kayi duk yadda zakayi don ganin ka tahomin da matarshi dakuma d'anshi anan , akwai buk'atar in gana dasu , abune mai matukar muhimmanci agareni in gana dasu kamun dan sauran lokacin da ya ragemun ya cika don Ni nasan wannan ciyon bai mai barina bane na riga da na yanke kauna da sake taka k'asa sai dai nasani Alhaki ne ke bibiyata wanda inhar ba na rok'i yafiyar wad'an da na cuta ba bazan ta'ba ganin da kyau ba duk da kuwa Ni kaina nasan lokacin yin hakan ya riga da ya k'uremun kuma nasan bazasu ta'ba yafemun ba yayi maganar wasu hawaye Masu dumi da yaji suna gangarowa daga cikin kwamin idanunshi,

"Haba yaya kai kullum bakada magana sai kiran Alhakine ke bibiyarka , bayan kuma nasan duk zafin ciyo ne kayi hakuri insha Allah zaka warke kamar ba kaiba amma Yakamata karage sawa kanka damuwa hakanan kar abun yayi maka yawa yaya , yafad'a kamar zai zubarma da yayan nashi hawaye,

Murmushi mai ciyo yayi yace " bakasan komai akaina ba Mansur Ni azzalumi ne Ni maha'inci ne Ni maciyi amana ne na ci amanar aikina da al'umma ta , sai dai abu mafi girma da na aikata wanda sanadinshi ne na hadu da wannan jarabawar sai gashi babu wan Babu k'ane ban tsira da komai ba sai tarin walana da dana sani, abu daya zakuyi mun shine ku taimaka kuzo mun da wadan nan bayin Allah ko na samu sassauci akan abinda nakeji ajikina , wanda har lokacin hawaye basu daina zuba a idonshi ba,

Daga Mansur har Ibrahim kansu ya k'ulle sun kasa gane zantukan na Haruna , amma ganin yadda ya rikice masu yasa suka mashi alkawarin gobe da safe zasuzo mashi da wadan da yake nema din,
Sai a lokacin ya saki ajiyar zuciya tareda gaya masu don Allah sucika alk'awari,





*Washe gari*

A gurguje yake shiryawa don yau yaso ya makara sosai , bayan ya gama shirin shi tsaf cikin kakin shi na yan sanda wanda yake matuk'ar yi mashi kyau da kara mashi haiba abunka ga farin mutum kuma isasshen namiji mai jini ajika, turare ya dauka yana fesawa sannan ya dauki agogonshi da hularshi ya fito daga dakin , dakin Momma ya nufa , da sallama ya shiga tana tsaka da gyara kayanta da aka amso guga taji sallamarshi ,

Murmushi ta saki lokacin da tayi arba da d'an nata masha Allah son kowa kin wanda ya rasa , har kasa ya duka ya gaisheta kamun ya mik'a mata agogon yace " yawwa Momma doramun agogon nan,
Murmushi tak'ayi tace kai dai shalele ta'bararka tayi yawa wallahi ace har yanzu k'ato da kai ka kasa iya sa agogo kullum sai dai ka bayar a sakama , amma ai duk abbanka ne ya sagartaka da yawa komai sai dai yamaka kamar wani k'aramun yaro,
Murmushi yayi yace kai Momma nikam kullum sai kinyimun jawabi akan saka agogon nan gaskiya zanyi zuciya in koya in huta Nima, yafad'a Yana wani yamutsa fuska ,

"Hmm inda Kanada wannan zuciyar ai da tuni kayi , Ni yanzu dai kazo ka nemi matar aure ko nima na huta da shiriritarka kaje can matarka tayi maka,"

Taf wa zaiyi aure yanzu Momma kofa shekara talatin banyi ba gaskiya ba yanzu ba sai na k'ara girma, "

"Aiko baka isaba don kaji na gaya maka insha Allah kamun karshen wannan shekarar doli kayi aure don banga abunda kake jiraba,"

Jin maganar tafara tsawo yasa yace kinga Momma zan tafi yanzu kiyimun addu'a in nadawo sai muyi maganar , "

Ajiyar zuciya ta sauke kamun tayi murmushi tace *kowa da wannan kayan k'ima yake samu amma kuma sauk'e hak'k'in al'umma da amanar kayan su suke samar da k'ima ta gaskiya karka karya doka sannan kuma karka bari a karya doka fatan nasara shalele adawo lafiya*. Tunda tafara magana yake murmushinshi Mai burgewa kamun yace " Nagode sosai Momma" sannan ya juya yabar gidan,


___________

"Ibrahim wace irin magana kakeyi ne to nikuma miye had'ina dashi naga tun rasuwar Abba ko inuwarshi ban sake gani agidan mu ba , "

"A'a Hisham karkayi saurin yanke hukunci acikin fushi kabari muje sai muji koma minene sannan Ni akwai abunda nake zargi tabbas akwai wani boyayyen abu da yakeson fada wanda kuma ya danganci Abba ne shiyasa yakeson ganawa daku,"


Shiru Hisham yayi na wani lokaci kamun yace " to amma Ni kadai zanje bazan tafi da Momma ba koma minene in na koma zan gaya mata, "

Okey ba damuwa yanzu kagama aikin da kakeyi sai muje don na gayama Mansur cewa ya jiramu ,

Gyada kanshi kawai yayi yaci gaba da duba wasu takardu , duk da haka kawai gabanshi ke faduwa lokaci daya kuma sai yaji bai yarda da wannan kiran ba tabbas akwai wani abu Yakamata ya hanzarta yaje koma minene sai yaji da wannan shawarar ya ajiye aikin da yakeyi yacema Ibrahim "muje"



________________________

Minti 15 sai gasu a kofar gidan, gaisawa sukayi da Mansur sannan yayi masu iso acikin gidan , wanda tunda suka shigo unguwar gaban Hisham ke tsananta bugawa wanda yarasa dalilin hakan,

Wani irin yunk'uri Haruna yayi sai gashi a k'asa ya fad'o daga saman katifar , bai damu da ciyon da yaji ba yayin faduwar don ko yaya bayason abunda zai taba jikinshi ko ina ciyo yake mashi , da sauri duk suka nufeshi suna da nufin kamashi suna jera mashi sannu cike da tausayawa matuk'a , Hisham ma jikinshi yayi sanyi wani irin tausayin shi yakeji har k'asan zuciyarshi ,

Mansur ne yakamashi ya maidashi akan shimfid'ar shi yana cewa " haba yaya miyasa zaka tashi so kake kajima kanka ciyo ne ,

Gaba daya jikin Haruna rawa yakeyi sai hannu yake mik'ama Hisham alamar yanaso ya matso kusa dashi , tasowa yayi yazo kusa dashi ya zauna yana furta "sannu Baba" Allah ya baka lafiya ,"

Haruna kuwa ba komai ne ya firgita shi ba kamar ganin Hisham sanye da kayan *Yan sanda* kuma dauke da babban matsayi , tambayoyine fal a ranshi amma yakasa furtasu saboda yadda bakinshi ke rawa ,sai dai wani bangare na zuciyarshi najin dadin ganin Hisham a wannan matsayin wanda ko ba komai zaifi jin dadin ja da mak'iyanshi ,

Da kyar yasamu yafara magana , aikuwa cikin kuka da rawar harshe yafara neman afuwat Hisham kamar zai duka mashi sai kalma daya yake nanatawa *yaci amanarsu don Allah su yafe mashi* Hisham bai fahimci komai ba hasalima gani yake duk zafin ciyo ne ,ganin haka yasa Mansur cewa "haba yaya ka nutsu kayi mana bayani mana ka sanyamu a duhu bamu fahimci komai akan maganarka ba , su wa kaciwa amana ??

Hisham ya nuna da hannu sannan yashiga basu labarin abunda yafaru tun daga farko har zuwa karshe ,

Tunda Hisham yafara fahimtar inda zancanshi ya dosa jijiyoyin kanshi da wuyanshi suka fara mik'ewa yayinda idonshi ya kad'a yayi wani irin ja mai ban tsoro gaba daya farin idonshi ya tafi , dai dai da jijiyoyin idonshi sun mik'e tsaye hannayenshi kuwa sai wani rawa sukeyi lokaci daya jikinshi ya murd'e duk wata siffar k'rafinshi ta bayyana k'undar hannunshi kuwa har wani irin rawa take tsabar tsananin 'bacin ran da ya tsinci kanshi aciki ,

Ibrahim da Mansur kuwa kamar wadan da aka dasa ko motsi sun kasayi sai ido da hanci da baki da suka saki suna kallon Haruna , yayinda suke jifanshi da wani irin kallo mai tattare da tsana,

K'arar da sukaji itace ta dawo da hankalinsu cikin tsoro duk suka dubi inda suke kiyo k'arar , Hisham ne ya sa k'afa iya k'arfinahi yayi Ball da Haruna wanda saida ya tashi sama ya dawo k'asa wannan yasa ya saki wata razananniyar k'arar da ta karad'e gidan gaba daya , .....................๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™€๏ธ

Mun shiga tara Hisham zai ida gawar da batashi baโ˜น๏ธ๐Ÿ˜‚



*Zanyi aike Kano ,Zariya , Abuja, Kaduna , Lagos Maison INGANTATTUN KAYAN MATAN na yar mutan Sokoto mmn yusup yayi magana a hada da nashi ngd*๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ
[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ_16



.........................zaune suke cikin wani k'ayattacen falo wanda babuce kawai babu acikinshi , ga sanyi AC da wani daddad'an k'amshi na tashi , kowanensu Yana hakimce akan kujera ,kallo Daya zaka masu kasan cewa lalli wad'an nan alhazan sunci sun tada kai da nera suturar jikinsu ma in ka kalla kasan ba k'ananan mutane bane ,

'dayan 'bangaren kuma ,yan jagaliyar su ne a tsaitsaye kowanensu rike da zungureriyar bindiga fuskar nan tasu ba alamar imani ,

Alhaji Manu da Alhaji Musa da Alhaji Buba shahararrun yan kasuwa ne wanda sukayi suna a cikin garin na Lagos har ma da kewayenta, masu kud'i ne na gaske wanda ake damawa dasu suna da kamfanoni shaguna gidajen abinci da gidajen mai da sauransu , duk wanda ya sansu da wadan nan abubuwan ya sansu sai dai ta k'ark'ashin k'asa sud'in sun kasance azzalumai ne ga k'asar tasu don sun kasance manya manyan masu shigo da miyagun kwayoyi kayan maye kala kala

Please Login or Register in order to submit comment