Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hanani bacci yazama doli na yak'iceki koda Ke mayya ce to ni nafi karfinki banza masifaffafiya kawai ,mrtsss yak'ara jan tsaki a haka ya gyara kwanciyarshi yafara salatin annabi a hankali kamun kace mi bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi,

_______________________


Washe gari da wuri ya shirya ya nufi office ,yana zuwa ya nemi ganin Wanda ya wakilta don kula da tsohuwar da aka bige jiya, inspector Sale , yana shigowa ya Sara mashi tare da cewa good morning sir , "morning " yace mashi yaci gaba da tattara wasu takardu saida yagama ya dubeshi da kyau yace "ya jikin matar nan kuwa da sauk'i ? sannan ansamu wani Dan uwanta ne ? "

"Jikinta da sauki sir Allah ya taimaka bata wani ji ciyo sosai ba yar kurkurjewa CE kawai sai buguwa da bayanta yayi sosai amma da sauk'i , ansamu yan uwanta yanzu haka kuma likitan yabada tabbacin nan da kwana ukku zasu sallameta tunda jikin da sauk'i ,
Ajiyar zuciya yayi yace "to Alhamdulillah anjima zanje naduba jikin nata , Allah yakara tsare gaba , Sale ya amsa da amin , bashi takardun yayi yace zaka iya tafiya ga wannan ka kaiwa sajen Abubakar shi yasan inda zai kai ," "OK Sir yes sir ya Sara mashi ,maimakon ya juya ya tafi sai kuma ya tsaya yana yan soshe soshe , kallonshi Hisham yayi tare da d'age mashi girarshi d'aya yace da matsala ne ??"
Cikin in ina yace "am dama maganar yaron nan ne tun jiya mahaifinshi Ke zarya anan Ashe wai d'an alhaji Kabir naira ne to shine suketa zarya anan , " ya k'arashe maganar a sanyaye ganin wani mugun kallo da ogan nashi yayi mashi cikin kaukausar murya yace "to sai akayi Yaya ? Karka sake zomun da. Wannan maganar banshirya ganinsu ba zaka iya tafiya , cikin jin haushin ogan nashi ya juya tareda cewa sorry sir yafita daga office din yana mai tsinewa Hisham don yaso samun kudin da alhaji kabir yamashi alkawarin zai bashi inhar yayi masu kokarin da aka basu Berlin yaron.


Sai misalin k'arfe 4 na yamma yabar office din yanufi asibitin da aka kwantar. Da matar nan tareda insfector sale ,
A hankali suka murd'a hannun gambun suka shiga ciki ,

tsaye take tana wasu rubuce rubuce akan file. Din matar , k'amshin turarenshi ne yafara yi masu sallama a d'akin , kamun ya shigo bakinshi dauke da sallama, d'ago kan da laurat zatayi ne idonta yafad'a cikin nashi , gaba dayansu saida zuciyoyinsu suka buga kamun suyiwa junansu kallon ido cikin ido ......................kai nagaji don Allah sai kuma gobeπŸ™„πŸ™„πŸ™„


JAMIIN DAN SANDA FANS 2 BAKU COMMENT YAKAMATA KU GYARA DON WALLAHI ZANKAI INDA ZAKU BUKACE LITTAFIN NAN AMMA BAZAKU SAMU BA HAKAMA GRP DIN *MMN YUSUF FANS* ZAN CINCI MASU COMMENT MUKOMA GEFE MUYI ABUNMU TAU KUMA BA YANZU BA SAI LOKACIN DA BAZAKU IYA JURAR RASHINSHI BA NIKUMA ALOKACIN ZAN RAMAπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

*masuyimun comment ngd sosai Allah ya biyaku ya faranta maku kamar yadda kuke farantamun duk wadda tamun comment ina gani kuma inajin dadi saida bazan zamu damar binku dai bayan dai ina gdy ba saboda idona sake ciyo saboda hasken wayar amma ina ganinku kuma inajin dadi ngd sosai*


πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

*takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kijiβœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ»

Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»
*Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*

Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje

Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir

Maganin nono Dana hips
Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar,
Maganin gashi
Maganin hawan jini
Maganin sugar

Sabulun wanka na gyaran jiki
Sabulun dilka na amare
Dilkar amare

Kwallin mallaka (daga ni sai kai)
Maltinar mata
Bobintan mata
Set na lalata gindin kiahiya
Set na ukku bala'i
Set na rantse bakida kishiya,

Kalolin gumba
Kalolin gari
Kalolin matsi
Kalolin sabulan tsarki
Zumar mata
Zumar ridi
Zumar goron tula
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin sabon budurci
Tsumin kankana
Tsumin tabaje
Tsumin makalemata
Shayin mata
Sirrikan mallaka
Dan goshi da mahadinshi
Dan goshi na Mara
Kyallen al'ajabu
Rakumi da akala
Bita zai zai
Dahuwar kalolin kaza zabo zakara
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar zuciya
Dambun nama
Dahuwar yan shila
Yajin mata
Yajin maza domin Karin karfi


*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜ wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani ,
Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mataπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°

Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah ,
Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi maganaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° 07069711327
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§

*MALLAKAR*
*Maryam umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ
*Mutum ce kuwa*
*Minene asalina*
*Husna ko Huzna*
*and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ
*Jami'in Dan sanda*


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍


πŸ…ΏοΈ_25

............................."kaga banason fitina rabu dasu duk Wanda yayi nagari kansa amma har yaushe zanbari ka tsaya wani kula irin wad'an nan mutanen salon ka k'ara 'batamin lokaci don kar kaje ko ? To ba inda.zaka fita don nasan hanyar guduwa kake nema tunda inba haka ba ai yanzu ba'a fagen aiki kake ba ,
Shiru Hisham yayi don maganar gaskiya kowaye acikin motar to ya bashi haushi sannan haka kawai yaji yanason yaga wane d'an iskan ne acikin motar, ba tare da yace komai ba ya koma ya gyara zamanshi tareda rufe k'ofar Wanda a dai dai lokacin aka basu hannu , ai kamun ma suyi wani motsi tuni motar su zayyan ta kutsa a inda aka fara samun hanya sabida wucewar na gabansu take suka wuce da gudu kamar walk'iya suka halba titin , k'wafa kawai Hisham yayi tareda bin motar da harara, sannan ya kunna tashi motar yaja suka dauki tasu hanyar inda sukayi hannun Riga dasu zayyan ,

Tafiyar minti goma sukayi suka k'arasa unguwar su hajiya Sara , unguwa ce ta masu hannun da shuni , unguwar shiru shiru Sam ba hayaniya sai iska mai dad'i dake k'adawa a hankali , Hon sukayi mai gadi ya bud'e masu k'aton get din gidan , a hankali Hisham ya k'arasa inda aka tanada don ajiye motoci , gida ne k'aton gaske Wanda kallo daya zaka mashi kasan cewa an narkar mashi da dukiya mai tarin yawa, kallon gidan yakeyi a hankali yayinda yake mamakin ina Momma tasamo wad'an nan hamshak'an mutanen kuma , πŸ€” dafe kanshi yayi cikin matuk'ar 'bacin rai don shi Allah yagani masu kudin nan basa burgeshi Sam bayason mu'amala da Wanda yasan yafi k'arfinshi don gudun wulak'anci amma shine yau momma zata kawo gidan mutane a matsayin Wanda take tallanshi ai a take yaji zuciyarshi tafara tafasa haka dai ya daure yafito daga motar jiki a sanyaye don ganin Momma ta fita har tayi gaba,

Aguje tafara saukowa daga matakalar benen tsabar Saurin da takeyi har had'a matakala biyu takeyi bakinta kuwa kamar zai yage waja. Kiran Momy Momy Momy, kanajin muryarta zakasan cewa tana cikin matuk'ar doki da farinciki ,
Anan falon k'asa wata hakimar mata ce zaune acikin kujera ,matar k'atuwa ce masha Allah tanada jiki sosai Wanda har k'ibar taso tamata yawa , cikin tsabar sauri tafara cikiniyar mik'ewa tsaye kasancewarta k'atuwar gaske yasa saida takwashe wasu second kamun tasamu ta mik'e duk da tanacikin Sauri kuwa,
Afusace tafara magana " Ke Ke wai kekam wace irin shashashar yarinya ce ,yau kwana nawa kenan ina jan kunnenki akan karki kuskura kiyi mana wannan shashancin naki da kika saba , to ahakan kikeson yace yana sonki gani nan kullum bakida nutsuwa , wallahi in kikayi wasa wannan murd'ad'd'en yaron bazai yarda ya aureki ba don haka garama ki kama kanki da wannan banzan rawar kan naki,"

Turo bakinta.tayi sannan ta murgud'a baki tace "to ni miye laifina nagansu fa sunzo ne ina sama naga shigowarsu shinefa zanje na tarbosu, "
Cikin takaici matar da aka kira da momy ta watsa mata harara tace to uban waye yace kizo tarban nasu ? Oya don Allah maza ki koma kuma karki kuskura kifito har sai na nemiki shashasha kawai, turo bakin tak'ayi kamun cikin jin haushi ta juya ta nufi wani daki dake cikin falon,
Komawa momy tayi ta zauna tana jiran shigowar bak'in nata , da yake akwai tazara sosai tsakanin wajan ajiye motocin da k'ofar shiga gidan,

Da sallama Momma ta shiga falon , cikin farinciki da murnar ganinta momy ta amsa mata sallamar tare da fadin oyoyo hajiya maryam sannu da zuwa sannu da zuwa , cikin farinciki itama momma Ke amsa mata kamun ta zauna a d'aya daga cikin kujerun falon , bayan sun gaisa ne da tambayar lafiyar juna hajiya Sarah takasa hak'uri tace Aminiyata ina d'an nawa yake ne banganshi ba, "

"Hmmm aikin San halinshi yana waje bari na kirashi ta waya nace yashigo,"
"A'a karki kirashi bari na tura *Samra* ta shigo dashi kawai , murmushi momma tayi kamun tace yawwa hakan yayi kirata taje ta shigo dashi, "

Mulmulawa momy tayi da kyar ta tashi tanufi haryar dakin da Samra take , koda tashiga dakin samun Samra tayi gaba madubi sai faman k'arawa face dinta kwalliya take , kuma masha Allah tayi kyau sosai kasancewarta dama can kyakyawa ce saida kwalliyar tayi mata yawa wannan yasa takoma kamar wata aljana tsabar yadda aka fente fuskar nan,

Rik'emata hannu momy tayi tace "to ya isa haka sarkin kwalliya maza kitashi kije ki shigo da saurayin naki yana waje sauran karki nutsu kije kina wannan rawar kan ya rainaki,
Cike da murna ta mik'e tana cewa kai momy nifa da hankalina nasan yadda zanyi agabanshi , bari naje kar ya gaji da jira da sauri ta ra'ba ta gefen momy ta fice daga dakin,

Tun daga nesa yake k'are mata kallo ta k'asan ido tafe take kamar zata kifa saboda wasu shegun takalmi da take sanye dasu masu masifar tsini , Samra doguwa ce irin sosai din nan fara CE tass tanada doguwar fuska mai dauke da dogon hanci da manyan idanu fatare Tass sai d'an k'aramun bakinta Wanda ya k'arawa doguqar fuskarta kyau ,atak'aice dai Samra kyakyawa ce sosai a fuska saidai batada cika irin ta cikakkiyar mace doguwace sosai kuma siririya ce wadda ta tafi samk'am kamar muciya Sam ba gaba bare baya , gata da shegen son saka takalmi mai tsini wannan yasa take k'ara tsawo marar fasali , cikin yan seconni yak'are mata kallo azuciyarshi kuwa tsaki yayi yace " wai wannan abun momma take mun fatan in aura sai kace Wanda ya rako maza duniya , haba , to in auri wannan ince na auri mi, ai da duk wata rashin sa'ar aure ta tabbata a kaina wallahi mrtsssss yaja wani dogon tsaki afili Wanda tsakinshi yayi daidai da isowarta kusa dashi ,

Bakinta kamar zai yage saboda fara'a tace " Dear sannu da zuwa ygd wai momy tace ka shigo daga ciki, "
Kamar ya falla mata mari haka yaji data kirashi da Dear amma dai ya danne jin haushin shi ,ba tare daya kalli inda takeba ya daga k'afarshi yafara tafiya,
Da Sauri ta biyoshi tashiga gabanshi don yimashi jakora , tafiya suke yana k'arewa d'an k'ugunta kallo awa na sauro (injishi )😹 azuciyarshi yake cewa oh Allah mai iko wannan in auren akayi ma ko a ina zata ajiyeni da wannan k'ugu nata kamar na 'yan shila sai wasu dogayen k'afafu haka kamar na barewa wannan da alama ma zatafini tsawo , komai ya tuna kuma sai yayi saurin cewa astagfirullah afili tare da kauda isonshi daga kanta Wanda yayi daidai da shigarsu cikin k'ayataccen falon gidan inda momma da momy keshan firansu ,
Har k'asa ya duk'a ya gayar da Momy , itama cikin jin dadi da murna take amsa mashi gaisuwarshi , daga nan tasa Samra ta rakashi falon bak'i,
Saukar ban girma akama Hisham da momma , inda yan uwan samra maza da mata suka rink'a zuwa suna gaisawa dashi daga nan aka kaishi har falon Daddyn samra suka gaisa , Alhaji usman sahabi yaji dadin ganin Hisham a matsayin surukinshi Wanda yana fatan hakan ya tabbata tabbas yasan da yarsa tagama dace da nagartaccen miji kamar Hisham, bayan dawowarsa ne falon bak'in ya buk'aci ganin Samra zasuyi magana daga momma har Momy rasa Wanda yafi wani murna da farinciki akayi don suna ganin Hisham shima yakamu da son Samra tunda har gashi yanacewa akirata zasuyi magana,

Cikin karad'i da rawar kai da ya zame mata jiki tayi sallama ta shigo , badon yasan darajar sallama ba to da bazai amsa mata ba don haka akwai wani haushinta yakeji musamman da yaga yadda iyayensu suka dauki abun da gaske ,

Samra kam Sam bata damu da yanayinshi ba saima zama da tayi akusa dashi tana yi mashi wani fari da ido tare da cewa "yawwa dear gani ," juyowa yayi ya fuskanceta sosai suka kalli juna ido ciki. Ido , tsuke fuskarshi yayi tamau lokaci daya ya koma ainahin Hisham d'inshi lokaci daya ya juye mata izuwa wani jarumin namiji Wanda kallo daya zaka mashi ka kirashi da suna Jarumin jarumai haibarshi da k'warjininshi ne suka cika mata ido Wanda hakan yasa ta sauke k'wayar idonta daga cikin nashi a hankali zuciyarta na bugawa ga wani tsoronshi da ya shigeta lokaci daya,
Cikin jarumar muryarshi yafara magana yana cewa,
"Ke d'ago kanki ki kalleni ," a hankali samra ta d'ago manyan idonta ta zuba mashi Wanda zaka iya hango tsoro k'arara acikinsu , tsaki yayi sannan yacigaba da cewa " kinga nayi maki kama da shashasha ?? Ko ni sa'an wasanki ne ?" Da mamaki take kallonshi saboda mamkin tambayoyin nashi Sam bata fuskanci abunda yake nufi ba, cikin sanyin murya tace "ni bangane abunda kake nufi ba, " ta karashe maganar da murgud'a mashi baki Wanda yazame mata jiki yin hakan,
Cikin fushi yace "to yanzu ko zaki gane , inason kifita a hanyata Sam bakimun ba kuma bazan aureki ba , don haka inason kisani kuma kisa aranki ni bazan iya aurenki ba don bansan abunda zanci ajikinki ba Ke in banda ma karambani inake ina ni ai wallahi namaki yawa tako ina don haka inason yanzu kije ki gayawa iyayenki bakya sona bazaki aureni ba in kikayi haka to kin taimaki kanki da kanki , "

Cikin tsiwa da rashin kunya Wanda dama can d'abi'arta ce tace "to in kai bakasona ni ina sonka kuma mamanka tana sona don haka sai na aureka in yaso ka kasheni in.............wasu yawu masu kauri ta had'iye da k'yar lokacin da tayi arba da bindigar daya zaro daga cikin k'ugunshi ya nunata da ita kamar zai harbeta da gaske , cikin kakkausar murya yafara magana yace , "zakiyi abunda nace ko bazakiyi ba , ? Kisani in kika kuskura kikace ma iyayenki da mahaifiyata kina sona to sai nafasa kanki da wannan bindigar , kuma banyarda ki gaya masu yadda mukayi dake ba kawai kice masu bakyasona banyimaki ba inba hakaba sai nafasa shegen kan nan naki mai rawar tsiya da wannan bindigar ,ya k'arasa maganar yana gyara kunamar bindigar ,

Ai a firgice samra ta duk'a tanabashi hakuri akan yayi hak'uri bazata gayawa kowa ba kuma bazace tana sonshi ba don Allah yayi mata rai kar ya kasheta ,wani munafukin murmushi yayi ganin plan dinshi yatafi dai dai nan yasata ta share hawayen tareda gyara fuskarta sannna yace mata ta tashi ta tafi , aikuwa kamar jira take kamar walk'iya haka tabar wajan don ta tsorata sosai da lamarinshi dama can samra matsoraciyace ta bugawa a jarida,
Ganin hakan yasa yayi ficewarshi shima daga d'akin yayi waje cike da farinciki , yana zuwa inda yayi parking ya bude motar yashiga yana sauke ajiyar zuciya ji yake kamar an sauke mashi wasu kaya ,

Samra kam jiki na rawa tahiga falon batare data kalli inda su momma suke ba ta haura sama da sauri ta shige dakinta,tana zuwa ta fada bisa makeken gasonta tasaki kuka ,yayjnda maganganun Hisham Ke mata amsa kuwa acikin kunne,

Sukam basu kawo komai ba musamman momma ta Dauka duk kunya ce nan tayiwa hajiya Sara sallama saboda magariba takusa inda hajiya Sara ta rakota har wajan motar Hisham nan suka k'arayin sallama da alkawarin zasuyi magana ta waya komi kenan , suka juyo suka dauki hanyar gida,

Ganin Hisham cikin farinciki da walwala ba kamar yadda suka taho ba yasa momma farinciki a zataonta ya kar'bi tayinta ne ,taso ta tambayeshi amma kuma sai taga bari kawai ta barshi har su k'arasa gida sai suyi magana,
Sunzo daida wani round danja ta koma tsayar dasu , nan take tunanin mortar d'azu ya fad'owa Hisham arai , yarasa abunda yasa yakejin haushin rashin ganin mai wannan mortar , amma ba komai in kare na yawo zomo na yawo watarana za'a had'u don tsab ya rik'e number mortar,

Kamun abasu hannune wani mai mashin yazo aguje Sam baiyi tunanin tsayawa ba haka ya wuce ta gabansu aguje yana wani tuk'in ganganci kamar titin na ubanshi ne Wanda zuwanshi yayi daidai da zuwan wata tsohuwa zata tsallaka titi aikuwa babu zato babu tsammani saiji akayi yayi sama da wannan tsohuwar ta fad'o Tim tareda FASA wata uwar k'ara ,

Cikin wani irin zafin nama Hisham ya b'alle murfin mortar yafita aguje yayi kan mai mashin din nan da yaketa son ya gudu amma mutane aun karamashi cafko wuyanshi yayi yayi gefe dashi yafara zuba mashi mari kamar an aikoshi , Wanda a daidai wannan lokacin ne danja tabasu damar su wuce , nanfa mutane suka fara tafiya yayinda wasu sukayi parking a gefe don ganin yadda zata kaya , tsohuwar kuwa tuni Hisham yabada umurnin akaita asibiti yayinda shikuma yayi waya a station dinsu akan aturo mashi yan sanda su tafi da yaron , kuma har lokacin dukan yaron yakeyi gaba daya ya hada mashi jini da majina,

Adai dai wannan lokacin motar su Lauratu ta sawo kai wajan ganin mutane sosai a wajan ya tabbatar masu da ba lafiya ba , zee ce Ke Jan motar don haka ta gangara gefe tayi parking tana cewa "anty inaga ba lafiya muje muga abunda yake faruwa pls ,

Dafe kanta lauratu tayi cikin jin haushi tace " wai zee sai yaushe zaki daina wannan halin naki nabin diddigi inaruwanki da abunda yake faruwa don Allah ni kija mota muje agajiye nake wallahi ga kaina na ciyo sosai , "
"Haba anty don Allah kibari muje mugani mike faruwa kikasani ma ko wani mai Neman taimakone mu taimakamashi , inkuma bazakije ba ni kijirani yanzu zan dawo bari naga mike faruwa,daga haka batajira cewarta ba ta bude gambun ta fita ta nufi wajan da taron yake ,

Girgiza kai kawai laurat tayi tana mai mamakin halin kanwar tata na shegen ganin k'wam , kamar ba zata fita ba kuma sai taji bari taje ta ganewa idonta tunda zee tasasu tsayawa ,

A hankali ta fito daga motar ta rufe , sanye take da doguwar rigar atamfa kalar sararin samaniya rigar tayi mata cif ajikinta saman rigar kuma farar rigace irin ta likitoci ajikinta sai k'aramin farin gyale da tayane kanta dashi ,fuskarta fayau bawata kwalliya sai farin glass irin nasu na likitoci Wanda yakara haska kyakkyawar fuskarta , a hankali take tafiya tanufi inda ake hayaniyar , zuwanta yayi daidai da wani shuri da Hisham yayiwa gayen nan mai mashin , wani irin zaro idanu tayi cikin jin haushi da tsawa cikin siririyar muryarta ta cewa Hisham " kai wane irin mugu ne kai kam mi yaimaka da zaka mashi irin wannan dukan , wane irin rashin imani ne zakama d'an uwanka musulmi irin wannan dukan , kasan darajar da jinin d'an Adam yakedashi kuwa ko kasan ..............wani irin kallo da Hisham ya watsa mata ne yayi sanadiyar rufewar bakinta batare data shirya ba , lokaci d'aya zuciyarshi tayi wani irin bugu da baita'bajin irinshi ba idonshi yak'ara warewa akanta yanamata wani irin duba mai.......................✍🏻



*wadan da basu comment wlh zanfara cireku ba ruwana GRP din da banawa ba kuma in naga baku comment to zan daina turawa*
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§ *JAMI'IN 'DAN SANDA*. πŸ‘¨πŸ»β€πŸ”§

*MALLAKAR*
*Maryam umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*πŸ‘‡πŸΌ
*Mutum ce kuwa*
*Minene asalina*
*Husna ko Huzna*
*and now*πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ
*Jami'in Dan sanda*


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍


πŸ…ΏοΈ-28

........................."Ke banason shashanci wani irin zai kashe ki kuma , ? "
"Wallahi momy kasheni zaiyi haka fa yace .....saikuma takasa k'arasawa tuno da gargad'in da yayi mata,
" uhumm ina jinki yace mi " momy ta tambayeta ,
"Bakomai momy nidai kawai bana sonshi , " cikin mamaki momy ta tsareta da ido ganin ita ta nace akan tanason Hisham tun ganin farko da tayi masa lokacin da suka kaima hajiya maryam ziyara, wannan yasa cikin hikima ta janyo hankalin hajiya maryam akan su had'a yaran nasu aure don k'ara dank'on zumunci , ta 'boye cewa Samra CE Ke son Hisham din, _anya kuwa yarinyar nan batada aljanu_ ta raya a ranta batare da tasake cewa komai ba ta juya ta fita daga d'akin, direct saman Daddynsu tayi ,

Da sallama ta shiga falon nashi yana zaune akan wani kyakyawan kafen ya kishingid'a da waya a hannunshi yana daddanawa da gani wani yake nema a wayar, zamanta yayi daidai da kara wayar da yayi a kunnenshi , nan yafara magana da Wanda yake kan layin sunjima suna waya kamun suyi sallama ya katse kiran , juyowa yayi ya kalleta da kulawa yace " yadai madam lafiya kuwa na ganki kamar kina cikin damuwa?"
"Hmmm ba doli ka ganni cikin damuwa ba Daddyn samra al'amarin yarinyar nan ne yafara bani tsoro , wai tanacan tana kuka akan batason Hisham bazata aureshi ba , bayan kuma ita tanace akan tana sonshi ,tunani nake anya kuwa yarinyar nan batada aljanu duba da yadda kwata kwata batada mashinshini ban ta'ba ganin wani saurayi ya biyota yace yana sonta ba, tun bata damuwa har tazo tafara damuwa har kuka takeyi akan hakan, to yanzu daga sama tasamu yaro kamar Hisham amma wai tace bata sonshi gaskiya da walakin goro a miya inaga yakamata a nema mata magani in ba aljanu ne suka aureta ba,tayi maganar cike da damuwa,

Nisawa Daddyn samra yayi yace " wannan ai iskanci ne taya zata maidamu kananun mutane bawani aljanu iskanci ne da ta'bara ni nagaji da zamanta a gidan nan don haka bazan bari wannan yaron ya su'buce mata ba tunda ita batasan inda yake mata ciyo ba" yafada cikin jin haushi ,

Mommy ma batace komai ba don Allah yagani itama batason yarta ta rasa wannan Damar ,wannan yasa ta yanke

Please Login or Register in order to submit comment