Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda aka budewa Hisham k'ofa Amna na tsaye saman bene tana hangen shigowar motar , ganin batasan motar waye ba yasa ta kafe motar da ido, ba k'amun bugu k'irjinta yayi ba lokacin da tayi arba da daurarriyar fuskar Hisham Mai cike da fushi da kwarjini, ,idonta ta lumshe tasake budewa akan kyakyawar fuskar shi, duk da dare ne Amma tarr take hango fuskarshi saboda kwayayen lantarkin da suka haska gidan kota Ina fess tamkar Rana ,a hankali ta furta wow tana kallonshi har lokacin da ya nufi sashen mahaifinta , atake ta yanke cewa tabbas tasamu mijin aure irin kalan da takeso kenan miji na nunawa sa'a son kowace mace ,don tafiyarshi kawai ta Isa ta nuna mata shidin jarumin namiji ne ,kiss tayi ta hura mashi Wanda shi baimasan tanayi ba har yayi shigewarshi ,aguje ta juya daga inda take tafara saukowa daga benen tana k'walawa mom Kira,


"Kai matsiyaci ubanmi yasa ka shigomin gida kuma har nan cikin falo na ,da izinin ubanwa kayi wannan gangancin, lallai tsagerancinka yayi yawa Amma Zan nuna maka naka kadan ne,"yafada Yana huci da mamakin ya akayi suka tsira bayan su yaran sun kirashi sun tabbatar mashi da cewa suna hannunsu a d'azu,

Batare da Hisham yayi magana ba yafara tafiya , kukerar da ba kowa ya janyo ya zauna ya Dora k'afarshi daya akan daya ya kallensu a dak'ile yace,
"Minene dalilinka na son shiga rayuwata minene a tsakaninmu da kakeson ka 'batamun Rana Mai matukar muhimmanci a gareni , ? Kasan wahalar da nasha kamun nasamu yarinyar nan kuwa yafad'a Yana jujjuya hannunshi fuskarshi Sam bazakace Yana cikin damuwa ba Kuma magana yake hankali kwance kamar baisan girman abunda yake aikawata ba, yaci gaba da cewa , Anya Kai kasan girman soyayya kuwa , ? Soyayyar da nasha wahala kamun nasameta shine kukaso ku wargaza tare da dukkanin burina a Rana d'aya ?? Ku a tunaninku hakan zai yiwu cikin sauki , hmmm yayi wani murmushi na tura haushi kamun yaci gaba da cewa , a gaskiya da wani abu yasamu matata da bazance ga abunda Zan aikata ba wannan yasa nazo nayi Jan kunne da fatan za'a kiyaye , "

"Kai yaro ka iya bakinka tun kamun ka tsinci takalmanka a hannu bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane yanzu sai nasa a 'batar dakai daga duniyar ma Baki daya , matsiyaci dan talakawa kad'ai har kanada k'warin gwuiwar shigomin gida ka gayamun magana to wallahi sai Naga uban da ya daurema gindi aduk fadin k'asar nan da har kake iya kallon idona ka gayamun magana,"

"Ok badai zaka janye ba kenan , ? Cewar Hisham ,yaci gaba da cewa to shikenan idan zaka turo yaran naka yakamata kasan irin wadan da zaka tura , ba ririn wadan da ka tura yau ba , kaje ka turamun wasu Yan koyo sunsa fad'an ko wani armashi baiyi ba mrtss ,Kuma wallahi wallahi kajawa d'anka kunne idan har yasake aikata abunda ya aikata wlh zakuyi Dana sanin sanina da kukayi wannan shine gargadina na karshe a gareku , na barka lafiya, "
Yafada Yana juyawa

"Idan yak'i kiyayewar fa mi zakayi ?
"Banason na fad'a maka abunda zanyi ne ai ,"
" To shikenan kaje kayi duk abunda zakayi nikuma a lokacin Zan iskeka har office Dinka da takardar k'arin girma ,"

Murmushi Hisham. Yayi yace "to godiya nake ranka ya Dade , fatan alkhairi, yafada Yana sarama Alhaji Saminu kamun ya juya ya fita har lokacin da murmushi a fuskarsa Wanda a zuciyarshi sam ba haka bane wani irin zafi da Kuna yakeji mussaman in ya tuna kukan Laurat da maganganunta ,

Fitowarshi tayi daidai da zuwan Amna wadda takasa hakurin har ya fito ta biyoshi , ganin murmushin fuskarshi yak'ara dulmiyawa da ita wani irin narkewa zuciyarta tayi da sonshi yayinda ta kankame hannayenta ajirji tareda lumshe ido tana shak'ar k'amshin turarenshi , har yazo ya giftata batasani ba da sauri ta bude idonta tabi bayanshi da Dan gudunta don yanayin tafiyarau ba daya , sanye take da mini siket Baki sai farar Riga wadda takamata sosai da kadan ta rufe cibiyarta , kanta ba dankwali sai dogon gashinta da yazubo har bayanta Amna kyakykyawa ce ajin farko kana ganinta kaga bafulatana sannan tana kamanni da Zayyan sosai kasancewar duk mahaifiyarsu suka biyo,

Har ya bude motarshi ya shiga ta k'araso tana haki hannu ta d'aga mashi cikin muryarta Mai Dadi tace HI 👋🏻 kallonta yayi a d'age take ya hango tsantsar kamanninta da Zayyan , maida kallonshi yayi ga shigarta Yana mamaki Wai a haka diyar musumai ce mrtssss tsaki yayi kamun yayi ribos da k'arfi Wanda Saida Amna ta Fadi saboda yadda ta jingina da motar , bai ko bi ta kanta ba yabawa motarshi wuta yabar gidan , inda yabar Amna cike da tsananin begenshi a zuciyarta Sam bataji haushin abunda yayi Mata ba saima burgeta da yayi Kuma taci alwashi sai yazama mallakinta ko Ana ha maza ha Mata , (tofaaaa😅aiki yasamu Mata)

Hisham Bai koma bi takan Laurat ba kamar yadda itama ta shareshi saidai takasa fadawa kowa abunda yafaru,kamar yadda yabata umurni, Allah yagani tana k'aunar Hisham fiye da tunaninta Wanda batasan lokacin da zuciyarta ta afka haka ba wannan yasa takasa fad'a don in Abbanta yasani wallahi tsaf zai Hana auren nan ,sai dai tasan tabbas rayuwarsu na cikin hadari in akaci gaba da tafiya a hakan, , (Ashe duk burgar banza ce🤣🤣)

A yau Assabar aka daura auren Laurat da Hisham Akan sadaki 50k taro yayi taro manyan k'asar sunzo sosai mussaman manyan jami'ian Yan sanda, da Governor da tawagarshi Mataimakin governor ne dai baizoba😂anyi shagali sosai inda bayan d'aurin aure maza suka dunguma hotel din da aka Kama don yin liyafa yayinda wajan Mata suka zarce da yinin biki , k'arfe 8pm aka fara gudanar da dinner wadda ta k'ayatu sosai saidai amarya da ango sun Sha kunu kowannesu cike yake da Dan uwanshi, k'arfe 10pm aka tashi daga dinner din inda aka wuce da amarya gidanta ....................✍🏻


*To alhamdulillah ,masoya da abokan arziki inason in shaida maku cewa littafin Jami'in dan sanda yakoma na kudi sakamakon rashin comment da bana samu daga wasu sai Yan k'alilan don haka duk maiso tabiya 200 nasata a paid grp Kuma insha Allah zakurinka samun post akai Kai don musamu mugashi da wuri Wanda dama rashin comment dinne ke.dakatar Dani daga typing Koda yaushe, maiso tamun magana ta wannan number. 07069711327 WhatsApp kad'ai pls , Banda Kira , zaku turo ta account kokuma katin MTN ngd sosai Allah yabar kauna*

*Mmn Yusuf*
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍✈️ *JAMI'IN DAN SANDA* 👨🏻‍✈️

*_KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION_*

*_wannan littafin na kudi ne a yanzu yakoma na kudine saboda wasu dalilai maiso tabiya 200 ta karanta 07069711327_*


🅿️_36

.........................Masha Allah gidan amarya ya had'u iya had'uwa komai a tsare kana kallon gidan kaga gidan 'yan Boko Sam ba wata kwamacala aciki komai an ajiyeshi inda yadace , 'Yan kawo amarya sai yaba kyau da tsarin gidan sukeyi , ahaka suka nufi sashen da akayiwa momma acikin gidan don damk'a Mata amanar amarya Lauratu ,

Sanye take da wani Cotton less bak'i Mai adon fararen duwatsu sai Wal Wal sukeyi , anyane Mata kanta da farin gyale Mai masifar kyau takalminta da Jakarta ma farare haka sarkarta da awarwaraye Masha Allah tayi kyau har tagaji ga uban k'amshin Dake tashi a jikinta Mai masifar Dadi da shiga Rai , a hankali sukayi sallama abakin k'ofar Fallon , amsa Masu akayi da Basu izinin shigowa , wata k'anwar Abbansu ce rik'e da hannun Laurat a hankali take Jan hannunta har suka k'arasa gaban momma sannan ta zaunar da ita ak'asa kusa da k'afafun momma nan suka shiga gaisawa da gabatar da amarya , falon na momma cike yake da 'yan tarbar amarya su Inna Indo da wasu daga cikin dangi da sukazo daga sokoto sai kawayenta wanda mafi yawansu matan abokan mahaifin Hisham ne ,
Anyi masu tarba ta mutunci sosai Inda momma ta janyo Laurat ta d'orata akan kujerar da take zaune ta rungumeta tace " kudaina wani wahalar da kanku na cewa kunbani amanar Lauratu ,don Lauratu ba a matsayin sirika zata zauna Dani ba amatsayin 'ya take a wajena , Allah yagani inason 'ya mace sai gashi Allah Bai baniba yanzu kuwa gata nasamu ta sanadin 'Dana don haka karku damu Laurat tana tare da mahaifiyarta fatanmu dai Allah yabasu zaman lafiya da zuri'a masu albarka , dukkansu da Amin sun amsa cike da farincikin kalaman Momma , sannan sukayi masu sallama tareda mik'a amarya sashenta sannan sukabar gidan ,

Zaune take ita kad'ai a tsakkiyar gado ta lullube kanta da gyalenta har fuskarta kamar dai yadda akasan amaryar hausa fulani, gaba daya zuciyarta a hautsine take , Tama rasa tunanin da zatayi , tunda abun nan yafaru komai nata ya canza tayi sanyi sosai kullum cikin zullumi da fargaba take ,tunani take Anya kuwa tayiwa kanta adalci , Anya Bata Sanya kanta a had'ari ba ,auren Wanda ake farauta ido rufe takowane fanni , wata zuciyar tace Mata _aa Laurat bakiyi ganganci ba hasalima auren mutum kamar Hisham abun alfaharinki ne mutumin da ya tsaya iya gaskiyarshi yake yiwa k'asarshi aiki yake yak'ar azzaluman cikinta Wanda yakawo sauyi sosai acikin garin nan , Wanda da Babu irinsu to da k'asar mu tak'ara shiga garari fiye da Wanda take ciki a yanzu , Kuma Allah Yana bayan Mai gaskiya insha Allah Babu abunda zai faru sai alkhairi, kiyiwa mijinki kyakyawan fata Kuma ki tayashi yaki Akan makiyanshi sannan ki k'arfafa mashi gwuiwa akan aikinshi_ , jinjina Kai tayi tana amanna da wannan shawarar ta zuciyarta insha Allah zata cire komai ta kula da mijinta Kuma duk Wanda ya ta'ba Mata miji to sai inda karfinta ya kare , don tasan ba abunda mutum ya isa ya yayiwa wani mutum sai dai in dama can kaddararka a hannunshi take,

Wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali taji suna shigarta duk wani tsotonta da fargaba sun fice Mata fitttt ( haba kokefa jaruma Matar jarumi🤣🤣🤣)

Dirin motoci ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi , ai take wata sabuwar fargaba ta shigeta tana tunanin ko ya zata kwashe da wannan Dan rainin hankalin oho,
Hisham ne da abokanshi su hudu Wanda sukayi mashi rakkiya , duk da yace bayaso haka nan suka nace Saida suka biyoshi, wajan Momma suka fara shiga suka gaisheta inda Inna Indo tashiga tsokanar Hisham Ana dariya Bai tanka Mata ba sai harara da yake banka Mata , momma tace "kaci gidanku Hisham uwar tawa kake harara ne , "
"Barni da Dan banza Inka matsamun yanzu sai naje na dauke amaryar Inga ta tsiya , " wani murmushi yayi yace inkin fasa ban gode maki ba, " duk dariya suka Sanya ganin yadda yayi maganar nan dai sukayi masu sallama suka nufi sashen ango da amarya , suna shiga ya tsayar dasu anan falo yace " to Masha Allah rakkiyar ta Isa haka don wallahi Babu k'aton da zai kallemun Mata abanza , ku ajiyemun ledojin anan kuyi tafiyarku nagoda sosai Allah ya huta gajiya,

Dukkansu Baki suka saki suna kallonshi dayan yace " tooo lallai ma mutumin nan mu zaka Kora don kaga mun gama maka wahala ko , Ibrahim Yana dariya yace kunga ku barshi kuzo muje muma Allah ya kaimu mu Rama , "
"Amin" hisham yace Yana turasu Akan sutafi yarufe k'ofar , yazid yace " to Allah dai ya shiga tsakaninka da wannan amaryar irin wannan daukar hankali karkaje ka halaka Yar mutane shiyasa Ni da 'ya ta bazan bawa tuzuru ba wallah ,
"Eh naji dai kutafi Allah ya kiyaye hanya ,hakan suka fita suna dariya shikuma ya kargame kofa,

Duk rigimar da sukeyi tana jinsu , tana mamakin wai wannan wane irin Hali gareshi ne mutane suzo maka lalura amma kana wani korarsu , to Allah ya kyauta ,
Sallamar shi ce ta katse Mata tunanin ta inda zuciyarta taci gaba da bugawa , da kyar ta amsa sallamarshi cikin sanyin muryarta,
A hankali yafara nufo inda take yanajin wani irin farinciki Wanda Bai taba Jin irinshi ba hannayenta ya zubama ido yadda suka Sha kunshi ja da Baki Wanda ya kwanta lif akan fatarta Zama yayi kusa da ita Yana cewa "Kinga bude fuskarki nagani don Ni ba wani Baki da Zan siya yafada Yana kumshe dariyarshi don son ya takarota , aikuwa yayi nasara don take tafara cika tana batsewa saidai batace komai ba Kuma Bata bude fuskarta ba, hannu yasa ya yaye Mata mayafin , take yafara tasbihi ga Allah acikin zuciyarshi yayinda wani sihirtaccen k'amshi ya bugi hancinshi Wanda har Saida ya lumshe idonshi da k'arfi Yana Kara bude kofofin hancinshi Yana shakar k'amshin , (hmmm turaren mmn mamah kenan karku Bari abaku labarinshi😋) sake bude idonshi yayi ya sauke akanta Wanda tuni idanun nashi sun lumshe sosai Yana Kare Mata kallo , ba zato saiji tayi ya fisgota ya had'ata da jikinshi yabata wata kyakyawar runguma inda ya Dora kanshi akan wuyanta yanajin kamar ya shige cikin jikinta saboda yadda k'amshin jikinta ke fisgarshi , mutsu mutsu tafara zata kwace zuciyarta na bugawa Amma takasa don ba karamun riko yayi Mata ba har tagaji tayi luf ajikinshi yayinda zuciyoyinsu ke bugawa fiye da misali, sun Dade a hakan kamun ya dagota a hankali cikin kunnenta ya ce

" ke tashi ki ciyar Dani kizo mu kwanta bacci nakeji,"
zaro ido tayi waje tana mamakin kalamanshi kamar ya ta ciyar dashi Kuma, Wai wannan wane irin ango ne Allah ya hadata dashi itakam , wato itace ma zata ciyar dashi a maimakon shi ya ciyar da ita lallai wannan ko acikin Yan rainin hankali shi oga ne , kwace jikinta tayi taja baya tana gunguni , baiji abunda take Fadi ba yakula bakin tsiwar ya mutu yau,

"To tunda bazaki ciyar Dani ba to Ni Bari na ciyar dake Amma kisani Ni bazan ciyar da ke.abanza ba doli sai........ Bai karasaba ya saki wani munafukin murmushi , kamun yace je kiyo alwala muyi nafila , batace komai ba ta tashi tanufi bandakin inda ya Rakata da ido Yana dariyar mugunta, bayan ta fito shima shiga yayi yayi alwala ya fito inda yajasu sallar raka'a biyu sukayi inda yayi Mata tambayoyi Akan addininta Kuma alhamdulillah tabashi amsa yadda yakamata , daga nan yaje falo ya dauko masu kayan da su Ibrahim suka siyo masu , bayan ya ajiye yakoma kitchen ya dauko filet da wuk'a sai kofuna biyu ya dawo har lokacin tana inda yabarta a zaune , nan yazuba masu gasasshen nama Wanda yaji Hadi sosai sannan yazuba masu fresh milk nan yafara Bata abaki tun tana kin ci har tafara amsa Bata wani ci da yawa ba tace ya isheta , aikuwa nan ya birkice Mata akan doline itama tabashi abaki kamar yadda yabata , cikin matukar kunya da nauyi tafara bashi Naman yanaci Yana korawa da milk bayan sun Gama ne ta tattare wajan sauran kayan tasa a frij , duk da yaso su watsa ruwa Amma hakan ya gagara saboda wata irin masifaffar sha'awa data taso mashi Wanda har yake mamakin dama yanada sha'awa irin hakane aikuwa nan yayiwa Lauratu daukar jarirai ya nufi gado da ita.

Hakika Laurat taga soyayya wadda Bata taba tunanin zata samu makamanciyarta ba , Bata taba kawowa ranta Hisham Yana kaunarta har hakaba Tasha ruwan kalamai har tarasa inda zata sasu ,gaba d'aya ya gigitata da salon soyayyarshi Wanda har hakan yasa ta iya jurema bukatarshi batare data nuna gajiywa ba gefe daya Kuma hawayen farinciki takeyi da adduar Allah ya basu zaman lafiya,

Hisham ma Yana cikin farinciki sosai don ya tsinci kanshi a yanayin da Sam baiyi zato ba ,wannan yasa yaji duk duniya bayan momma yanzu ba abunda yakeso kamar Laurat yanajinta a kowane sako da lungu na jikinshi , haka ya kwana yana sallah Yana mika godiyar shi ga Allah da irin baiwar da yayi mashi don tabbas matarshi Yar baiwa ce,

Kasancewarta Likita yasa tun a Daren tabawa kanta duk wani taimako da ya dace da,

WASHE GARI

K'arfe 9 Momma ta Aiki Aisha Yar wajan Baffansu Hisham ya kawo masu breakfast dinsu , lokacin Bata tarar da kowa a falonba sai kawai ta ajiye akan table tayi tafiyarta , sai wajan goma saura suka farka daga nauyayyen baccin da kwashesu bayan sallar asuba , wanka sukayi suka shirya cikin shadda iri d'aya kalar sararin samaniya inda akayiwa Hisham dinkin da gayu ke yayi a yanzu anyi mashi kwalliya da zare kalar blue mai duhu inda hularshi da takalminshi ma suka Zama blue Mai duhu yayinda fuskarshi ke fitar da wani irin annuri na anganci, gimbiyar kuwa doguwar Riga aka Mata wadda Tasha fentwork blue yayinda gyalenta da takalminta suka kasance kalar aikinta , Masha Allah ga sihirtaccen k'amshin jikinsu daya hade Dana juna kana kallonsu kaga ango da amarya Wanda suka dace da junansu , ahaka suka fito falo ,nan suka karya sam_sama kamun suka nufi sashen Momma don gaida ita da bakin da Basu Gama tafiya ba,

Tunda suka doso falon Momma ke zuba murmushi bakinta yakasa rufuwa sai Masha Allah take fad'a , sallamar su CE ta ankarar da mutane falon isowarsu aikuwa nan aka yayyabesu Ana yabawa da kyawunsu ,har k'asa suka durkusa suka gayarda Inna Indo da Matar Baffansu inda sauran yaran suka gaidasu sumu , kamun suka mike suka nufi inda momma take wadda Sam takasa dauke idanunta akansu , Laurat zata duka momma ta tarota da sauri inda tahadata da Hisham ta rungume tana maimaita kalmar alhamdulillah,

Laurat nauyi da kunya hade da soyayyar Matar ne suka cikata , cike take da farinciki sa'ar sirika da tayi tun jiya da aka kawota Taji kalaman da tayi akanta take Jin kanta sakayau tanaji aranta bazatayi missing mahaifiyarta ba tunda tana tare da momma , sunjima a sashen har Saida Yan uwan Laurat suka fara zuwa ganin daki sannan ta koma 'bangarenta inda Hisham ya fita wajan abokansa badon yaso ba ,


BAYAN SATI BIYU

Soyayya ruwan Zuma , wata irin soyayya ake gudanarwa tsakanin Hisham da Laurat tuni sun cure sun Zama Abu daya sunajin in Babu dayansu dayan bazai iya rayuwa ba , hakama tsakanin momma da Laurat zamansu abun sha'awa komai Bata Bari momma tayi tana Bata girmanta sosai Inda kullum momma ke Kara alfahari da ita tare da Taya Dan ta murnar sa'ar Matar da yayi , a yau Monday hutunsu ya kare zasu koma aiki , inda. Hisham ya siyawa Laurat mota Yar karama Mai shegen kyau don zuwa aiki , ahaka sukaci gaba da gudanar da aikinsu hankali kwance Wanda so da yawa kamun su dawo momma ta dafa masu abinci basuda matsalar komai , duk da Sam Laurat batason yadda momma ke wahalar da kanta wajan Yi masu aikin abinci tafiso tabari idan ta dawo ita sai ta dafa masu ...............fatan alkhairi Laura Hisham😍😍😍


*Hmmmmmmm tana k'asa tana dabo*

*Masu bukatar wannan littafin su biya 200 nasasu a grp don daga next page bazan sake turashi ko inaba sai Wanda suka biya*
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍✈️ *JAMI'IN DAN SANDA* 👨🏻‍✈️

*_KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION_*

*_Wannan littafin na kudi ne a yanzu maiso tamun magana zaku biya 200 only ta account ko katin MTN 07069711327_*


🅿️ _37

......................Bafa zaka samu yadda kakeso ba ta wannan hanyar , abun ya dauremun Kai sosai a binciken da nayi na gane cewa yaron nan yanada d'aurin gindi sosai ga manyan k'asar ciki kuwa harda shugaban k'asa wannan yasa yake duk wani bura'uba ak'asar nan , yanzu haka naji rad'e rad'in cewa za'a kara mashi girma zuwa babban matsayin na I.G na Nigeria Baki daya ,mi kake tunani in hakan ta faru ?baka tunanin hakan zai iya kawo Mana cikas sosai a harkar kasuwancin mu ,? kawai duk yadda zakayi kayi ka kashe yaron nan gaba daya kowa ya huta don zamanshi a raye ba k'aramar barazana ne ga rayuwarmu ba , dama dai kasan nasan bawai saboda abunda yayi wa yaronka kakeso ka dauki fansa akansa ba kawai ka la'be ga sabara ne kana Harbin barewa don haka yakamata muyi Mai yiyuwa gaskiya komai Yana gaf da lalacewa, cewar Alhaji Ilyas babban Dan kasuwar da akeji dashi a fadin garin na Lagos Kuma abokin kasuwancin Alhaji Saminu Wanda Allah ne kad'ai yasan tsakaninsu Amma tabbas duk abunda suke kulkawa to ba na alkhairi bane , lokacin da Hisham yazo gidan Alhaji Saminu Alhaji Ilyas Yana d'aya daga cikin wad'an da ya tarar dasu a falon tun daga lokacin yafara bincike Mai tsauri akan Hisham don ason samunsu shine Susa a saukeshi daga kan muk'aminshi inda halima a aikinshi gaba d,aya , sannan su wulakanta rayuwarshi kamun su aikashi inda ba'a dawowa Wanda hakan zai K'ara tsoronsu a zuciyar sauran Jami'an Dake son shige masu hanci da kudundune ,

Tunda Alhaji Ilyas yafara magana yake zagayen falon hannayenshi goye a bayanshi , cikin tsananin fushi yafara magana
"Aa Alhaji Ilyas bazan taba kasheshi a yanzu ba doli saina wahalar da rayuwarsa baisan wanene Saminu ba da Bai shigo har cikin gidana ya gayamun magana ba bayan yagama zautamun yarinya yanzu gaba d'aya yadda kasan mahaukaciya haka Amna ta koma akan doli shi takeso Ni kuwa Dana barta da wannan tsageran yaron nafison Naga gawarta , yasha shigarmun hanyar harkokina Wanda baida masaniyar nawa ne wannan yasa nake daga mashi kafa saboda banason a fahimci abubuwana sai gashi tsautsayi yasashi taba yarona wannan yasa na fake dashi don daukar fansa don a Yan watannin nan ba k'aramar Aasara ya jazamun ba, don haka tabbas sai nabi duk wata hanya da yakamata nabi don kuntata rayuwarshi ,sai nasa yayi mutuwa dubu kamun yayi daya kwakkwara, muje zuwa Hisham ya furta hakan cin tsawa da huci,

Girgiza Kai Alhaji Ilyas yayi yace aa abokina kawai kayi yadda nace don wallahi Dan hakin daka Raina shi yake tsone maka ido kayi maganinshi tun kamun lokaci ya kure maka , don haka Ni Zan tafi kayi tunani, " daga haka yabar gidan shakatawar Dad din inda mafi yawa anan suke gudanar da duk wani abun da ya shafe kasuwancinsu , (ko wane irin kasuwanci ne wannan 🤔)

Sanye take da wando fari iya gwuiwa sai karamar Riga Mai hannun bes red ,tana zaune a k'asa ta had'a kanta da kafafunta inda dogon gashinta ya barbazu a saman kafadunta da fuskarta kuka take kamar ranta zai fita lallashin duniya mom tayi akan ko breakfast ta tashi tayi Amma Taki , tsawon sati biyu kenan tana cikin wannan halin tun lokacin haduwarta da Hisham acikin Daren ta gayawa Daddyn ta shi takeso aikuwa take ya zabga Mata wawan Mari in da ya tabbatar Mata da ko maganar wannan yaron yasake ji daga gareta to sai ya kusa kasheta agidan , a yanzu babbar damuwarta Bai wuce na rashin sanin inda zata sake saka wannan saurayin a ido ba hasalima batasan wanene shi ba a Ina yake ya sunanshi duk Bata sani ba wannan yasa kullum take cikin kunci da koke koke a tunaninta Dad dinta zaiji tausayinta ya Nemo Mata shi tunda tasan tabbas shi yasan wanene tunda har gashi yazo inda yake,


Zuwa wannan lokacin Zayyan da abokanshi sun warke rass ,Kuma ba abunda ya sauya a halayensu saima abunda yayi gaba yanzu Dadyn Zayyan ya siya mashi wani dank'areren gida acan kusa da gidan gonarahi ba abunda Babu aciki na more rayuwa nan suke shek'e ayarsu , bin Mata Kuma kamar bunsura kullum cikin Tara Mata suke a gidan suna abunda sukaga dama ,ga Dan banzan shaye shaye, yanzu sai yayi sati biyu Bai lek'a gida ba Kuma har wannan lokacin Yana nan da tunanin hanyar da zaibi don daukarwa kanshi fansar abunda Dan sandan yayi mashi tunda yaga kamar Dad yakasa,

________________________


Su Hisham Kam yanzu hankalinsu kwance ba abunda yake damunsu ,

Please Login or Register in order to submit comment