Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba ,cikin rawar harshe tace "Hisham ka nutsu ka gayamun abunda ke faruwa ko na baka shawarar da ta dace inason ka rink'a sarrafa fushinka kar watarana ka aikata aikin Dana sani Wanda bana fata ,Amma wannan fushin naka yayi yawa in Abu ya dameka karinka maimaita innalillahi wa inna ilaihin rajiun zakaji sauki a zuciyarka kaji"

Daga kanshi yayi alamar amsawa kamar k'aramin yaro , cikin hikima da dabara momma ta samu ya gaya mata abunda yake faruwa , ai kamun ma ya k'arasa tuni momma tafara zubar da hawaye jikinta har rawa yakeyi cikin wata irin murya Mai cike da tashin hankali da bayyanar da zallan tsoron da take.ciki tafara cewa " Hisham ka duba girman Allah ka janye wannan case din , don Allah ka fidda hannuka daga ciki, banason. Kana shiga irin wad'an nan case din Hisham sunfi k'arfinka ,bazaka iya komai akai ba kabarsu duk Wanda yayi na gari kansa , Amma don Allah karka je ka janyomin abunda bazan iya dauka ba kasani Kai kad'ai gareni Kai nake kallo naji sanyi ba uwa ba uba ba miji ba marik'ana ba wa ba k'ani ka tausayamun bazan iya jurar wani abu ya sameka ba tunda kasani ba Imani ne da mutanen nan ba, ba abunda bazasu iya aikatawa ba indai akan take gaskiya ne Kai shaida ne akan mahaifinka ,a irin hakane aka kashe shi idan suka cutar dakai a wannan karon bazan iya jurewa ba don Allah Hisham ,ta k'arasa maganar tana had'a hannayenta da nashi cikin kuka,

Tuni zuciyarshi tak'ara hasala ga kukan mahaifiyarshi da yakejin kamar Ana zuba mashi darma a azuciya cikin sanyi da raunin da zuciyarshi tayi akan mahaifiyar tashi yace " Momma ya zanyi ? Zaluntarsu fa akayi Kuma zalunci Mai matukar girma yanzu shikenan a haka zasu zauna cikin bak'in cikin zaluncin Da akayi masu ..............katseshi tayi da cewa Hisham na k'are magana inason ka janye hannunka a wannan case din , insha Allah Allah zai bi masu hakkinsu Allah ba azzalumin bawansa bane saidai bawa ya zalunci kanshi , da sannu Allah zaiyi Mana maganinsu da sannu zasu girbi abunda suka shuka da hannunsu, "

Batare da ya sake cewa komai ba ya mik'e ya nufi d'akinshi zuciyarshi kamar wuta yanajin in Bai hukunta wadan nan shegun yaran ba bazai taba samun nutsuwa ba Amma doli zai zare hannunshi akan case din saboda Momma , shi ya sani basu isa suyi mashi komai ba saidai zai barsu ne saboda kwanciyar hankalin mahaifiyarshi, alwala yayi ya gabatar da sallar magrib da Isha alk'ur'ani ya dauko yafara karantawa a fili cikin zazzak'ar muryarshi yajima sosai Yana karatun kamun ya rufe littafin ya ajiyeshi inda yake ,yakoma bisa gadonshi ya kwanta , sai a lokacin yaji zuciyarshi tayi mashi sanyi sosai lumshe idonshi yayi da son yayi bacci ko zaiji saukin ciyon da kanshi keyi mashi , a hankali kyakyawar fuskarta tafara yi mashi gizo kamar dai jiya babu shiri ya bud'e idanunshi tare da dafe kanshi hannunshi Yana mamakin yadda ya manta da zancan zuwa wajan yarinyar nan, da sauri ya dauko wayarshi ya lalubo number ta wadda yayi serving da *Likita* bugu biyu ta dauka cikin muryarta Mai sanyi da nutsuwa tace "assalamu alaikum "
Saida ya lumshe idonshi ya bud'e kamun ya amsa mata sallamar tata cikin Jan aji, take ta had'e fuskarta don ta shaida muryarshi shine ya kirata jiya Yana mata rainin wayo,
Cikin wata irin murya da shi kanshi baisan yanada itaba yace " Matar kinga yau Baki ganni ba ko nasan kinyi ta jirana wallahi Sam na manta ne Amma insha Allah gobe Zaki ganni kiyi bacci lafiya "ya k'arashe maganar da hura mata wani sanyayyen kiss Wanda taji iskanshi har a kunnenta Wanda take tsikar jikinta ta shi da sauri ta cire wayar a kunnenta kamun tayi wani yunk'uri ma har ya kashe wayar tashi, tajima tana kallon wayar cike da wani irin yanayi Amma takasayin tunanin komai sai can Kuma tayi tsaki tana mamakin rainin hankalinshi , wai ya manta Kuma a hakan wai sonta yakeyi tsaki tayi tana jifa da wayar tare da k'ara gyara kwanciyarta ,

Hisham kamnan take bacci yayi awon gaba dashi cike da annashuwa Kai kace bashine.yake cikin matsanancin fushi ba a d'azun'

___________________________
WASHE GARI

Sosai ake bawa zayyan kulawa wanda alhamdulillah ya fara jin sauk'i ,kumburin fuskar ma yafara sacewa , Momy sosai take kula dashi Amma Amna ko sau d'aya bataje ta gaidashi ba saima haushin yadda duk Daddyn da momy suka damu akanshi takeji,
Yanzu ma Daddyn ne zaune agefen makeken gadon da Zayyan yake kwance Yana shafa kanshi a hankali tare da k'ara kwantar mashi da hankali akan zai daukar mashi fansa akan duk wani Wanda yake da hannu da ta'ba lafiyarshi , Yana jirane yasamu sauki ta yadda zaiga yadda zaiyi da wannan banzan Mataimakin commissioner din,

____________________________

Tunda yazo office yau yakasa ta'buka komai har na tsawon awa biyu , gajiya yayi da zaman kamun ya tashi yabar office din , direct asibiti ya nufa inda aka kwantar da Safiya ,da sallama ya shiga d'akin , mamanta ce zaune kusa da ita tana rik'e da hannunta sai fisge fisge takeyi tanason cire k'arin ruwan da aka samata , ga wani kuka da takeyi wanda komai rashin imaninka sai ka tausaya mata ,itama mamar kuka takeyi tana rirrik'eta da Bata Baki,tashinta kenan daga alluran baccin da akayi mata d'azu da safe , zuba masu jajayen idanunshi yayi da suka canza nan take a hankali fushinsa na jiya ke dawowa , daurewa yayi ya matsa inda suke kallon maman yayi yace " "saketa Mama, "
"Yalla'bai zata jima kanta ciyo ne"
"Saketa zata daina "
Jin hakan yasa batayi musu ba ta saketa zama yayi kusa da ita yafara mata magana a hankali Wanda ko maman bataji abunda yake ce mata ba , nan take ta nutsu tare da zuba mashi kumburarrun idanunta don gasgata maganar da yake fad'a mata , jinjina mata kanshi yayi alamar hakane , lumshe idonta tayi a hankali wasu hawaye masu zafi suna zubo mata , kamun tayi baya ta kwanta ,mamaki ne ya rufe maman ganin duk irin lallashin da sukeyiwa Safiya Bata ko daga ido ta kallesu Amma gashi cikin yan seconni Hisham ya bi da ita cikin ruwan sanyi , wani girmanshi ne da kaunarshi suka k'ara kama maman sai addua take zuba mashi Yana amsawa da Amin cikin tausayinsu ,lokaci. Da zai wuce ne yake barmata sakon Yana neman Baban safiya a office in ya zo ,to Mama tace mashi kamun suyi sallama ya tafi,

____________________________

Hisham ne zaune tare da Baban safiya da kanenshi office dinshi , da k'yar ya daure yayi masu bayanin halin da ake ciki tare da sanar dasu an kar'be case din a hannunshi yanzu case din Yana hannun manyanshi Wanda shi bashida wani abu da zai iyayi akansu sai yadda sukayi sai dai yayi masu alkawarin abunda akayiwa safiya bazai taba tafiya a banza ba inaha Allah zaisan matakin da zai dauka haka dai yayi ta kwantar masu da hankali ,saidai hankalin nasu yakasa kwanciya sunga samu sunga Rashi tabbas wanna. K'asar tamu abun tausayi ce yanzu shikenan. Talakan Nigeria bashida wani yan cin Kai ??? Kullum sukenan zasu zauna a mulkin mallaka ? Sosai Baban safiya ke kuka da idanunshi tare da adduar Allah yasakama 'yashi yasan in sunfi karfin hukuma ai bazasufi k'arfi. Allah ba, da k'yar Hisham ya lallabasu suka tafi ,cikin rashin jin dadin zuciya yabar office din shima yanufi gida,

_________________

Misalin k'arfe 4 ya isa gida a massalaci yafara tsayawa yayi sallar la'sar kamun ya k'arasa gida , koda yazo ya tarar da momma Bata nan dama ta gaya mashi zataje gidan k'awarta hajiya Hadiza , wanka yayi ya canza kayan aikinshi , cikin wani tsadadden bak'in yadi Mai shara shara ya shirya Wanda ya k'ara haska farar fatarshi yayi mashi kyau sosai bak'in takalmi yasa sai agigonshi fari Mai azabar tsada da kyau , farin glass dinshi ya dauka ya Sanya ,Masha Allah yayi kyau sosai kamar ka saceshi ka 'boye🤪 a gurguje yagama Shirin ya fita ya dauki wata bak'ar motarshi wadda Tasha wanki da guga sai daukar ido takeyi direct unguwar su laurat ya nufa kasancewar tun kwanaki yayi bincike akanta sosai yasan komai akanta sai abunda ba'a rasa ba wannan yakara bashi k'warin gwuiwa akanta don tasamu yabo ita da iyayenta sosai ,

A bakin get din ya tsaya ya dauko wayarshi ya Danna mata Kira , sai wani farinciki yakeji daga can k'asan zuciyarshi ,Yana jin kanshi wani daban don Bai taba zuwa zance ba baimasan yadda akeyin zancan ba ,daga kafadunshi yayi afili Yana cewa ai sai ta koyamun don da alama ita tasan yadda akeyin zancan, har wayar ta tsinke Bata d'aga ba , tsaki yayi ya sake Kira ringing biyu ta dauka tare da yin sallama, cikin lumshe idonshi ya amsa mata sallamar ya Dora da fadin "da bakiyi niyar dauka bane ko kuwa Jan aji ne ? Bai bata damar magana ba yace kifito ki shigo Dani Ina k'ofar gida,

Dam dam zuciyarta ta buga tana mamakin wai wannan wane irin karfin hali yake dashi, kallonta zee tayi tace "lafiya anty, ?"
"Hmm inafa lafiya wani dan rainin hankali ya sakoni agaba gashi Abba Yana nan bansan ya zanyi ba , wai gashi a k'ofar gida ,"
"To Kuma anty bake kikace yazo ba ?"
"Taya zance yazo bayan banko sanshi ba Ni banma San inda yasamu number ta ba wallahi, don Allah ki taimaka kije ki koreshi tun kamun Abba ya ganshi kinsan dai kiris yake jira Dani wallahi ,dariya zee tayi tace "okay to Bari naje Naga ko waye "

"Yawwa my swt.sis don Allah taimaka"
Gyalenta ta dauka ta yafa tafita a hankali ta nufi bakin get din tana dariyar Shirmen lauratu na korar samari ita kam in taga yayi mata wallahi bazata koreshi ba shigo dashi zatayi sai dai duk abunda za'ayi ayi,da wannan tunanin ta k'arasa get din ,bude karamar k'ofar tayi ta fita ,motar ta nufa tana k'wank'awasawa a hankali kasancewar motar Mai duhun glass ce Bata ganin Wanda ke ciki ,
A hankali ya bude motar yafara fito da k'afarshi ,gaba daya zee ta k'ara waro idonta don ganin Wanda zai fito daga motar, fitowarshi gaba daya yasa ta kusan fasa ihun murna ,da k'yar ta danne murnar ta cikin rawar jiki tafara gaisheshi bakin nan kamar gonar auduga don ba karamun ganin dacewarshi da antyn nata tayi ba ,cikin farin ciki tace "sannu da zuwa Yaya anzo lafiya yagida anty tana ciki tace nayi maka iso ,
Murmushi yayi don lokaci d'aya zee ta shiga ranshi rawar kanta na kara bashi dariya , rufe motar yayi Yana amsa mata gaisuwarta kamun yabi bayanta suka nufi cikin gidan ...............nagaji sai gobe🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍✈️ *JAMI'IN DAN SANDA*👨🏻‍✈️

*_MALLAKAR_*

~MARYAM UMAR ABDULLAHI~
( _MMN YUSUF_)
*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*


🅿️_32

......................... Zee na barin wajansu falon Abbanta ta nufa Allah Allah take taje takai masu labari Kuma tanason tayiwa antynta d'aurin talala ta yadda bazata iya dagule lamarinba kamar yadda takeso don takula in ta biye ta tata zatayi masu buk'ulu ne, bayan Kuma duk munafurci ne don ba Wanda zaik'i wannan gayen ,
"Assalamu alaikum" tayi sallama abakin k'ofar falon,
Wa'alaikussalam shigo" cewar Momy , cikin zumud'i ta shigo falon sai washe Baki takeyi ,
"Ke lafiyarki kuwa kike wani washe Baki kamar Mai tallan makilin ," cewa Momy ,
"Ai Momy wani abun alheri ne ya samemu yanzu dai Antyna tayi free ta huta da k'orafin Abba ,"ta fad'a tana dariya tare da kallon Abban , harararta tayi tare da ware hannunshi akanta yace " kinci gidanku Zainabu Ni kike cewa Ina k'orafi rainin naki Kuma yanzu a kaina ya dawo ko "?
Dariya Momy tayi tace oho yau dai anji kanku ai in tanamun shak'iyanci nayi magana kace na takurata ai yanzu gashi nan tafara dawowa kanka,
Murmushi Abba yayi yace " ai bazaji kanmu da uwata ba saidai waccan sarkin rashin jin 'yar Taki , yawwa uwata zo nan gayamun minene yake faruwa , da sauri ta k'arasa kusa da kafafunshi ta zauna cikin zumud'i tafara magana ,
"Am Abba albishirinka Bata jira cewarshi ba taci gaba da cewa , yau dai kayi sabon suruki Abba , Anty Tasamu Wanda takeso wallahi Abba baka ganshi ba ya had'u sosai gashi kyakykyawa ga shi Dan gayu ga nutsuwa Allah Abba in ka ganshi kallo daya zakayi mashi kaji ya burgeka tayi maganar tana washe Baki kamar wata karamar yarinya , daga Abban har Momy dariyar shirmenta sukayi yadda take Abu kamar wata Yar shekara 6 dama zee Kam badai ta'bara ba ,

Momy tace " to Zee basai yayar Taki tana sonshi ba tunda Kiri Kiri yarinyar nan kamar Mai aljanu duk Wanda zaice Yana sonta shikenan batada makiyi sama dashi kawayenta duk sunyi aure Amma ita ko a jikinta duk akayi magana tace ita ba Wanda takeso ,"
"Aa Momy wannan kam tana sonshi sosai don sun kwana biyu suna waya ma kamun yazo Kuma da kanta ta gayamun wannan tana sonshi ai yanzu ma tanacan wajanshi a d'akin Baki ,

To Alhamdulillah Allah ya tabbatar da alkhairi cewar Abba cike da farinciki don Allah yagani zaman yaran nan a gabanshi yafara isarshi shiyasa yakeson ya sauke nauyin da Allah ya Dora mashi ya aurar dasu ko yasamu nutsuwa ,Momy ma taji Dadi sosai sai adduar alkhairi take , nan suka ci gaba da tattaunawa akan maganar suna jiran Laurat ya shigo suji daga bakinta,.

____________________

Hisham Kam cike da farinciki ya nufi inda ya ajiye motarshi ya bude bayan motar ledojine kusan hudu masu k'yalk'yali kowacce shak'e da Kaya ya dauko ya nufi wani Dan saurayi da bazai wuce 20yrs ba Yana can gefe Yana wankin Kaya ,sallama yayi mashi da sauri saurayin ya tsame hannunshi ya nufoshi Yana gayardashi amasawa yayi kamun yabashi ledojin yace " don Allah ga wannan ka kaima yarinyar gidan " to Alhaji wacce acikinsu , Dan murmushi yayi yace pretty zaka kaiwa kace inji *Dan sanda* wasu kudi ya fito dasu yabawa yaron yace wanna naka ne daga haka ya juya yabar yaron sake da Baki da tunanin wacece Kuma pretty??? ,

Tafe yake a mota Yana tuki a hankali wani irin farinciki da nishad'i yake ji Wanda Yama rasa Kona minene , Yana cikin wannan yanayin ne kamar kyaftawar ido aka hasko mashi fuskar safiya acikin idanunshi , nan take yanayinshi ya sauya daga farinciki zuwa fushi mai tsanani ahaka dai yaci gaba da tafiya Yana sauri ya isa gida kamun afara kisan sallah,

___________________________

Yalla'bai kayi hakuri wannan ba abune Mai yiwuwa ba Nima bansan miyasaba bansan kuma daga Ina ne ba Amma tabbas Hisham yanada d'aurin gindi a sama korarshi a aiki ba abune Mai sauki ba sir zai iya haifar da babbar matsalar da bakayi zato ba , don haka kayi hakuri nidai ta 'bangarena ba abunda Zan iyayi da nayi maka kaima kasan wannan sir ,

Wani irin huci Mai zafi Daddyn Zayyan ya fitar cikin hasala ya nuna Wanda suke magana dashi yace ,"karka gayamun maganar banza Mana , wanene Hisham Kuma mi akayi akayishi ubanwa ya tsaya mashi a garin nan, oh Yana da d'aurin gindi wannan yabashi damar ya ta'ba yarona , hmmmm tabbas yayi ganganci duk shegen da ya nemi shiga gonata to ba makawa sai na hanashi jin Dadin rayuwa , naso nasa akoreshi ne daga aiki sannan daga baya na wulakanta rayuwarshi , to yanzu ma bazan barshi ba Zan dauki mataki da hannuna Kuma kaima kasan abunda Zan iya sannan Zan binciko uban da ya daure mashi gindi a k'asar nan ma ba a garin nan ba ya k'arasa maganar Yana dukan table din dake wajan da k'arfi ai kuwa take kayan dake bisa suka watse cikin huci ya Mike tsaye tareda nuna mutumin yace ka jirani kaima Zan dawo kanka , ba Wanda ya isa na sashi Abu yayimun jayayya ,daga haka yabaza babbar rigarshi yabar office din,

wani irin zufa ne ya yankowa mutumin cikin tsananin tashin hankali yafara girgiza kanshi yasan waye Alhaji Saminu Sulaiman yasan abunda zai iyayi , tabbas bazai taba sa hannu a Kori JAMI'I Mai gaskiya da samun irinshi a wanna lokacin yanada wuya ba kamar Hisham saidai Yana tsoron abunda zai iya samunshi ,dafe kanshi yayi da dukkan hannu biyu Yana adduar Allah ya kare Hisham daga sharrin wadan nan shedanun mutanen ,

____________________________

"Kai Mariya karatun nan naki Yana cin kudi sosai yanzu Kuma Ina zamu samu wannan uban kudin ,nikam dama kin hak'ura da wannan karatun kina ganin yayanki Bai aje ba baiba wani ajiya ba duk Dan abunda yasamu akan karatun nan naki yake karewa gashi har yanzu Baki gama ba bare a San ran cin amfani,
Sosai ta fito da manyan idanunta waje cikin sark'ewar murya tace In ajiye karatu fa kace Baba , yanzu wannan wahalar da mukayi sai ta tashi a banza kenan Baba" ta k'arasa maganar kamar zata kuka ,
"To ya zamuyi Mariya haka Allah yaso don nikam bansan a Ina Zan samo maki wannan uban kudin ba , Kuma sulemanu ma bana tunanin a wannan karon yanadasu bare yabaki, "
"Aa Baba bazata dakatar da karatunta ba indai Ina Raye insha Allah sai Mariya ta cika burinta na zama ma'aikaciyar jinya ," cewar Sulaiman Wanda yashigo gidan yanzu ya tsinci zancan da sukeyi,

Duk ido suka zuba mashi jin abunda ya fad'a ,cikin karfin hali Baba yace kayya dai sulaimanu yanzu ma wasu kudin za'a biya Wanda bana tunanin kanadasu bare ka biya Nima don ba yadda zanyi ne shiyasa nace abarshi kawai,

Murmushi sulaiman yayi yace nasan da zancan kudin baba wannan yasa nayi tanadinsu tun kamun a bukacesu ,akwai wani adashen da na shiga tun watannin baya insha Allah nasan zasu Isa abiya kudin makarantar anjima zanje na amsosu insha Allah gobe sai takai kudin,

Daga Baba har Inna Indo Banda addua da sa albarka ba abunda suke yiwa sulaiman suna alfahari da Dan nasu sosai shiyasa suke mashi wani irin so , Mariya kuwa tuni hawayen sun wanke Mata fuska tanajin wata irin kaunar Dan uwan nata da tausayinshi da sauri ta k'arasa inda yake ta rungumeshi cikin farinciki tace "nagode yayana Allah yasaka maka da mafificin alkhairi Allah ya daukaka ka yakara maka budi akan harkokinka ngd sosai Yaya , murmushi yayi yace bakomai K'anwata in nayi maki kamar kaina nayiwa fatana dai ki tsaya ki kula da karatunki Allah yasa adace duk suka amsa da Amin kamun sukaci gaba da tattaunawa,

_________________________

"Hello sir " aka fad'a cikin wata hargitsatstsiyar murya Marar Dadin sauraro , a dayan bangaren akace
"Yawwa big boy kana jina ko , akwai hoton da Zan turo maka tare da adireshen Mai hoton da dik wani abu da ya shafeshi inason kufara bibiyarshi inason sanin komai game dashi acikin kwana biyu kacal don haka banason shirme a aikina kasani , "
"Yes oga za'ayi komai kamar yadda kace Kuma akan lokacin da ka bayar , "
Batare da ya sake magana ba ya kashe wayar , sannan ya tura masu duk wani abunda ya shafi Hisham hotonshi cikakken sunanshi wajan aikinshi da Kuma unguwarsu , bayan ya tura ne yafara zagaya d'akin Yana tunanin irinn hukuncin da zai yiwa Hisham don har yanzu Zayyan baigama warwarewa ba ga k'afarshi da har yanzu yakasa taka ta da kyau saidai yayi dingishi yanajin ciyo sosai in yaga yadda d'anshi ke tafiya sai kace wani gurgu , mrtsss yayi tsaki tare da k'wafa afili yace zamu hadu ne,

(Hhhhhhhhhh nikuma nace wanzam kenan bakaso ga jikinka)

_____________________
Washe gari

Momy ce da Abba zaune a kan dinning suna karyawa bayan sun gama ne ya dubeta yace "Wai momyn Yara ya kukayi da 'yar Taki ne nayita jiran naji kince wani abu Amma shiru itama tun jiya take wasan 'buya Dani ,"
"Hmm Alhaji kenan nayi Mata magana Amma sai wani kwane kwane takemun da alama dai zancan Zee ne itama tana sonshi may be kunya takeji murmushi Abban yayi yace to alhamdulillah kiramun ita naji waye shi inason inganshi sannan nayi bincike akanshi don banason tarayyarsu tayi nisa batare da na Yi bincike akanshi ba , "
"Hakane to Bari na kirata, .............nagaji sai gobe kuma🤪🤪
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍✈️ *JAMI'IN DAN SANDA*👨🏻‍✈️

*_MALLAKAR_*

~MARYAM UMAR ABDULLAHI~
( _MMN YUSUF_)
*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*


🅿️_31

...................Falon da Abbansu ke sauke bak'i ta kaishi sai nan nan take dashi cikin fara'arta da takasa gushewa tace "yawwa Yaya zauna anan zanje na kawo maka ruwa dakuma antyn , "

Murmushi yayi Mai kyau yace " to k'anwata Ina jiranki"
Fita tayi da d'an gudunta tanufi falonsu inda tabar Laurat acan ,
da k'arfi ta turo k'ofar Wanda yasa laurat juyawa da sauri tana kallonta , aikuwa tana shigowa falon tafara tik'ar rawa tanayi tana juyi,tsaki laurat tayi tace "kefa Shashasha ce rawar mi kikeyi , ya tafi ne ko Yaya"!
"Kai anty irin wannan kamu haka kinga kuwa gayen nan wlh ya had'u iyakar had'uwa zakuyi bala'in dacewa dashi Allah anty , "
"Ke bashi na tambayeki ba cewa nayi ya tafi ko Yaya ? Tayi maganar ranta a had'e

"Ya tafi Ina Anty? 😳ta fad'a tana zaro ido ai wallahi ba zamu saki tukunya mukama murhu ba ke kinganshi anty ta Ina zanyi wasa da irin wannan damar da mukasamu ai wallahi wannan ko bakya sonshi to shi Zaki aura don ni yayimun sosai Bari ma nayi sauri na Kai mashi ruwa kekuma ki hanzarta kidan sake Kaya kishafa Yar powder kije Yana d'akin bakin inba haka ba wallahi yanzu zanje na hadaki da Abba kin Kuma San tsaf zan iya" ta fad'a tana wani juya duwawu tayi kitchen don hada mashi abun Sha,

Dafe kanta tayi cikin takaicin kanta da ta tsaya aika zee bayan tasan halinta Sarai yanzu ya zatayi kenan ? Yazama doli ta hanzarta zuwa ta sallameshi tun kafin zee ta had'a Mata bom agidan ,tana nan tsaye tana tunanin abunyi zee ta fito daga kitchen hannunta dauke da wani madaidaicin tire inda ta hado mashi lemu da ruwa da cek ,ta gaban Laurat ta wuce har takai bakin k'ofa ta juyo tace " pls anty don Allah kije ki canza kayan nan kizo kinji wallahi gayen nan yayi bala'in dacewa dake Amma na yarda in kin ganshi baiyi maki ba to shikenan sai mubashi hak'uri, tayi maganar tana wani marairaicewa kamar marainiya ,harara Laurat ta banka Mata da manyan idanunta tace "wallahi ba abunda Zan canza tunda bani na gayyatoshi ba ahaka zanje Kuma ki ajiye kayan nan don ni ba fira Zan je hakuri kawai zanbashi na dawo ,"
" In mayar fa kikace anty Aa wallahi Ni ban iya rowa ba ai bak'onk'a annabinka Ni dai kiyi sauri don Allah,daga haka ta wuce ta barta tsaye ,

K'wafa kawai Laurat tayi kamun ta janyo hijab dinta ta Sanya Wanda da kadan ya wuce gwuiwarta , tana sanye da doguwar rigar atamfa wadda tayi Mata d'ass ajiki ta Kuma bayyanar Mata da shape dinta sosai ,don laurat akwai k'ira sosai komai yaji ajikinta wannan yasa take yawan amfani da hijab da wuya ka ganta da gyale , a sanyaye ta nufi sashen da suke sauke bak'i zuciyarta na bugu sosai , haka kawai Kuma sai naji tana muradin taga wannan isashshen da yake yi Mata magana cikin Isa da gadara kamar wani ubanta,

Tun daga waje tafarajin karad'in zee sai surutu take zuba mashi kamar wata karamar yarinya , haushine yak'ara kamata jin yadda zee ke karad'i cike da zubda aji tsaki tayi acikin ranta tana tunanin irinn hukuncin da zatayiwa zee,

Ciki ciki tayi sallama ta shiga d'akin, da sauri ya d'ago da kanshi ya zuba Mata

Please Login or Register in order to submit comment