Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yayi ya kwanta akan k'afafunta tareda sake runtse idonshi ,

Ibrahim dake gefe yana kallon su yayi gyaran murya yace " duk abunda kika fad'a Momma kinada gaskiya kuma banga laifinki ba , domin taron wad'an nan mutanen kamar taron aradu da ka ne , hatsabibaine na gaske sannan komai zasu iya aikatawa ga duk wanda yace zaija dasu , to amma hakan bashi zaisa mu zuba masu ido suci bulus ba yazama doli muma muyi amfani da matsayinmu wajan ganin mun kwatowa kanmu 'yanci
A matsayin da Hisham yake kai a yanzu a dakuma matsayina na babban *Lauya* mai zaman kansa zamuyi amfani da wannan damar don ganin cewa mun gurfanar da wadan nan azzaluman agaban koto ,Kuma zamu jajirce don ganin cewa an hukuntasu dai dai da abunda suka aikata ............." A'a Ibrahim bazaku iya ja da wadan nan mutanen ba, ina gudun abunda yafaru abaya ya sake faruwa , bakuda karfin da zaku ja da wadan nan mutanen sunfiku komai tunda suke da abunda zasu iya juya duk wanda sukaso a lokacin da suka so ,.................."a'a Momma Ina tabbatar maki da zamuyi nasara akansu , karki hanamu don wannan jahadi ne zamuyi ko ba don mu ba bakisan iyakar mutanen da suka jefa a hadari irin wannan ba bakisan iya adadin mutanen da suka cuta ba ,tabbas zama da irin wadan nan mutanen ba karamin hatsari ne ga al'umma koba komai harda k'asarmu zamuyiwa aiki, zamu shiga mu fita har sai munga cewa sun fuskanci hukunci daidai da laifinsu insha Allah kuma nasan DPO ma zai mara mana baya sosai,

Tunda Ibrahim yafara magana Hisham ya kafeshi da ido bayako k'yaftawa tuni k'wak'walwarshi tafara aiki lokaci daya wani tunani ya fado mashi a rai , tabbas da wannan hanyar zaiyi amfani wajan ganin sunyi mutuwar walakanci , duk da ba haka yaso ba amma zaiyi amfani da wannan damar don ganin bayan azzalumai ,duk acikin ranshi yake wannan tunanin don har wannan lokacin yakasa bude bakinshi ma bare yayi magana ,


Momma da ta jima shiru batace komai ba , sai can ta sauke ajiyar zuciya tace "to shikenan Ibrahim Allah yamaku albarka Allah ya shige maku gaba , tabbas Allah yana bayan mai gaskiya don haka nabaku goyon baya dari bisa dari ",

Daga haka sukaci gaba da tattaunawa da Ibrahim , Hisham kam baice masu kala ba saima idonshi da ya rufe kamar mai bacci azahiri kuwa tuni ya lula duniyar tunanin yadda zai gudanar da shirinshi cikin kankanin lokaci don bazai iya jure tsawo lokaci batare da ya kawar da wadan da suka shiga tsakaninshi da farincikinshi ba ,

Bayan tafiyar Ibrahim magani Momma tabashi kasancewar har lokacin jikinshi da zafi sosai alamar zazzaɓi ,baijima da shan maganin ba bacci yayi awon gaba dashi don kaso mafi yawa na daga cikin damuwarshi ya sauka kasancewar ya samo bakin zaren,

________________________

Washe gari
Da wuri Hisham ya tashi yayi wanka tareda shirin shi na fita aiki , a falo ya tadda Momma zaune ta buga uban tagumi tana tunanin da ya zame mata jiki , ba abunda yake damunta irin kad'aici ,sosai takeson d'an nata yayi aure kodon ta huta da zaman kad'aicin nan amma taga alamar shi babu ma wannan a gabanshi , ko maganar aure bayaso ayi mashi gashi kuma yanzu yanason sa kanshi a wata sabuwar rigimar itakam da zai yarda da ya rabu dasu da sannu Allah zaiyi maganinsu don zalunci baya taba d'orewa,

A hankali taji hannunshi akan nata , juyowa tayi ta zuba mashi ido ,murmushin karfin hali yayi mata kamun cikin shak'ak'k'iyar muryarshi da bata fita sosai tun jiya yace "kiyi hkr Momma kiyi mana addu'a ba abunda zai faru insha Allah, daga haka ya mik'e yanufi hanyar fita cikin takunshi na cikakken namiji maiji da karfi da k'urciya,

Bin bayanshi kawai tayi da kallo har ya kai bakin k'ofa tace "haka zaka fita bazaka karya ba,"?

Batare da ya juyo ba yace " na koshi Momma," yasa kai yayi ficewarshi ,

Office dinshi yafara zuwa saida ya rage wasu ayukkan sannan ya fito ya nufi office din DPO Huzaifa Umar ,
Da sallama yashiga office din , bayan ya sara mashi ne yabashi izinin zama , gayar dashi Hisham yayi kamun yace "sir wajanka nazo da wata muhimmiyar magana ina fatan zaka goya mana baya ta yadda zamu samu abunda mukeso ,"

Ajiye biron dake hannunshi sir Huzaifa yayi ya zubama Hisham idanunshi yana nazarin shi kamun yace " ok Hisham ina saurarenka ,mi ya faru ??

Duk abunda ya faru tun daga farko har karshe Hisham ya sanar dashi zuwa lokacin idanunshi sun sake rinewa sosai da tsabar fitina da burin daukar fansa,

Tunda yafara maganar DPO ke kallonshi shima idonshi har ya kada yayi jajir tsabar yadda labarin ya ta'bashi , ranshi ya sosu sosai don ba abunda ya tsana kamar irin yadda ake raina *Jami'in dan sanda* abun yana mashi ciyo sosai yadda duk wani abunda zai faru yan sanda sune farkon wad'an da ake nema Don kawo d'auki a wajan , haka zasu shiga duk hadarin waje don ganin sun Bama al'umma kariya amma sukuma mutane basuda abun wulakantawa sai *dan sanda* bashida wata k'ima ko wata daraja a idanun jama'a saboda kawai 'bata garin cikinsu wanda kuma ba duka aka taru aka zama daya ba ,

Yayinda gefe d'aya masu mulki da masu kudi kecin dudduniyar yan sanda masu gaskiya da rikon amana saboda kawai takamar sunada kudi da mulki wanda suke ganin sunfi k'arfin hukunci duk abunda zasuyi shiyasa duk Jamiin da yace zai ja dasu to kuwa zasuga bayansa ne ta hanyar amfani da karfin mulki da kudi wajan saukeshi daga kan aikinshi yayinda wasu ma zasu kaudasu daga doron kasa kamar yadda sukayi akan mahaifin Hisham wannan ba sabon abu bane amma tabbas a wannan karon shima zai tauna tsakuwa don aya taji tsoro indai yana kan wannan kujerar tasa to tabbas sai yaga abunda ya turewa buzu nadi lokaci yayi da zasu tashi tsaye don memawa kasarsu da jami'ansu 'yanci bazasu sake yarda da wani tozarci ko cin zarafin *yan sanda* ba insha Allah,

"Wannan babban al'amari ne wanda doli sai yaje sama zanyi iyakar kokarina na ganin munsamu goyon baya daga sama kuma daga wannan lokacin bazamu sake saurarawa ire-iren su Alhaji Manu ba a garin nan zamuyi fito na fito dasu ai ba wanda yafi karfin hukuma dama can k'yalesu akeyi amma yanzu kam ya isa haka ,"


Cikin tsananin farinciki Hisham yafara mashi gdy duk da har wannan lokacin ba fara'a a fuskarshi amma a maganarshi kawai za'a fahimci yaji dadi sosai ,

File din da ya shigo dashi ya mikawa DPO yana cewa " wannan file din akan cases din yaran da muka kama ne da hodar ibilis to bincike ya nuna mana cewa yaran su Alhaji Manu ne , inaga da wannan damar zamuyi amfani wajan gurfanar dasu agaban alkali , sanna daga baya zan shigo da wannan case din , "

Duba file din DPO yayi da kyau kamun ya jinjina kai yace "eh tabbas kayi tunani kuma cikin ruwan sanyi zasu shigo hannu , amma kamun nan kana buk'atar kwararre lauya wanda yasan aikinsa don hatsabibancinsu yanada yawa inhar bakada kwararan hojjoji to abune mai sauki su juya case din zuwa kanka , sannan Yakamata kasan halin da Inspector Haruna yake ciki kayi kokari kayi control din fushinka akansa don zai mana amfani, "


Ok sir zanyi duk yadda kace , amma maganar lauya inada lauya yanzu haka , Haruna kuma anijima zamuje wajanshi ,"

"To shikenan Allah ya shige mana gaba"

"Amin sir ngd sosai"

Daga haka yabar office din dama station din gaba daya ,

_______________________

Direct office din ibrahim ya nufa inda ya gayamashi duk yadda sukayi da DPO , Ibrahim yaji dadi sosai inda sukaci gaba da tsara yadda zasu gudanar da bincikensu,

______________________

Hisham, Jafar, Asmy, gaba daya sun duk'ufa akan binciken da sukeyi a boye saboda munafukan cikinsu wadan da son abun duniya ya rufewa ido suka sayarda yan cinsu ga azzalumai ,
Cikin ikon Allah komai yana zuwa masu cikin sauki don sam basuyi zaton zasu samu sauk'in bincikensu irin haka ba , yaran su Alhaji Musa sun taimaka masu k'warai wajan basu hadin kai kasancewar ba karamar azaba Hisham ke gana masu ba cikin kankanin lokaci suka fita daga hayyacinsu da sun gashi take jikinsu ke fara rawa,, duk tambayar da zai masu kuwa take zasu bashi amsa har rigegen fada mashi sukeyi , (hhhhhhhhhhh su Goga anji maza)


________________________


A yau sukayi gagarumin shiri na zuwa kamo su Alhaji Musa inda dama can duk wani motsinsu akan idon jami'an tsaro ne don tuni aka sanya masu ido sosai , shiri sukayi sosai sanin cewa su Alhaji Manu da muggan yan daba sosai wadan da suke amfani da muggan makamai wanda suke fatan har su sukama shiyasa tun farko basu kama kowa ba sunason ne su hada masu tarkon da zasu kamasu gaba daya,


______________________

Zaune suke sunyi jugum jugum ,ba k'aramar damuwa suke ciki ba ganin k'aramun abu yana nema yafi karfinsu , sun rasa dalilin da wasu abubuwan ke faruwa dasu , yanzu duk yadda zasuyi wani sirri ko a waya ne to sai sunji maganar ta fita sun rasa wake masu zagon kasa ne , waya shirya ganin bayansu ne ,?? bayan duk wasu kadarorinsu a hankali iftila'i ke fada masu d'ai bayan d'ai , sosai suka fara zargin junasu da cin dudduniyar juna inda suka fara tada jijiyar wuya , sai daga bayane Alhaji Buba ya ankarar dasu akan Yakamata koma minene to subar k'asar kawai har komai ya lafa sai su dawo kuma zasu samu damar da zasuyi nazarin inda aka samu wannan 'barakar, gaba d'ayansu sun yarda da wannan shawarar wannan yasa sukayi shirin barin kasar zuwa Dubai,

Abunda suka tarar ne yayi bala'in daga masu hankali don sun nemi paspo dinsu sama ko k'asa sun rasa , wannan yasa suka hadu gidan shak'atawarsu don neman mafita,

Suna haka suka fara jiyo jiniyar motocin yan sanda tacika wajan , mamaki ne da tsoro suka kamasu lokaci daya ganin inda suke sam ba'a cikin gari bane dajine sosai wanda ba wanda ya san da gidan dagasu sai yaransu , to mi hakan ke nufi kenan ????

Kamun suyi wani yunk'uri har yan sanda sun cika gidan inda suka fara yin gaba da yaransu kamun suma su fito dasu , kallo kallon sunakayi tsakaninsu da Hisham inda suke mashi kallon zamu hadu da kai yayinda shikuma yake masu kallon na gama daku, ahaka aka sanya su a mota akayi gaba dasu ,su Hisham saida suka shiga gidan sukayi bincike kamun suka fito suma suka bi bayansu,

_____________________________

Kotun tacika makil ba masak'ar tsinke , kowa so yake yaga yadda wannan shari'ar zata kaya da mutanen da kowa kema kallon mutanen kirki ashe su din sun kasance azzalumai masu ha'intar kasarsu ta hanyar shigowa da muggan makamai kayan maye da lalatattun magunguna wadan da Allah ne kadai yasan iya adadin rayukkan da suka salwanta a sanadiyar su, jamaar gari sai Allah tsine suke masu ,

Bayan gabatar da shaidu da kwararan hojjoji kotu ta gamsu da cewa Alhaji Buba da Alhaji Musa da Alhaji Manu suna aikata laifukan da ake zargin su akai sannan tabbas hukunci zai tabbata akansu kamar yadda kundin mulkin k'asar ya tanada ,
ana shirin yanke masu hukunci ne Bariste Ibrahim Umar ya mike tsaye ya shigar da k'ara akan kisan Da su Alhaji manu sukama Jami'in dan sanda Inspector Abdurahaman ,

Jin wannan bayanin yasa kotun harmutsewa da hayaniya jin wata sabuwa kuma inji yan caca ,
Yayinda cikinsu Alhaji Musa yayi wata irin murdewa tuni suka fara zare idanu alamar rashin gaskiya gashi dama a tsorace suke da hukuncin da za'a yanke masu sai ga kuma wannan tashin hankalin,

Da kyar aka samu mutane suka nutsu inda aka shiga gabatar da Shari'a yadda Yakamata , su Hisham sun tanadi duk wasu shaidu da zasu bukata don basa son ko kad'an ad'aga shari'ar sunfi son yau yau ayita ta k'are kawai,

Acikin shaidun sun gabatar da record din da shi marigayi inspector Abdulrahaman yayi a wayarshi lokacin da suke mashi barazana ,wanda tuni wayar na hannun Momma sai a wannan lokacin ya tabawa Hisham wayar ,dama kuma tana sane da wannan daukar don a kanta ne ma ta boye wayar,
Sannan sun gabatar da direban babbar motar wanda aka biyashi don ya haddasa hadarin ,

Saikuma yaran da suka taimaka wajan ganin shirinsu ya tafi dai dai ,

Shaidar su ta karshe shine Inspector Haruna wanda aka shigo dashi a keken guragu saboda sam bazai iya tashi ba bare har yy tafiya,

Shi yayiwa kotun cikakken bayani akan yadda suka shirya komai har zuwa lokacin da suka samu nasarar aikata shirinsu yakuma gabatar ma da kotun dun wani recording da ya rink'ayi dasu Alhaji Musa a duk lokacin da suke magana batare da sun sani ba ,

Nan aka bawa magatakarda ya jona ga tv yadda kowa zaiji , aikuwa sai ga muryarsu Alhaji Musa radau lokacin da suke kulle kulle su, da wannan kwararan hojjoji da shaidu kotu ta yanke masu hukuncin Daurin rai da rai agidan kaso tareda horo mai tsanani hade da tarar kudi masu yawan gaske ,haka aka kada keyar su Alhaji Musa tareda direban da wadan nan yaran nasu da Inspector Haruna zuwa gidan maza ,yayinda mutane keta Allah wadai dasu suna tsine masu ,


____________________

A wannan rana Momma tayi kuka mai yawa kukan farinciki Allah ya nuna mata ranar da ta jima tana jira an hukunta wadan da sukayi sanadiyar rabata da farinkinta , sai yanzu tasamu wani abu da yayi mata tsaye a mak'oshi tun lokacin da ta fuskanci kashe mata miji akayi ya fada ,

Hisham da Ibrahim kuwa cike suke da farinki suma duk da ba haka sukaso ba sun so ne a yanke masu hukuncin kisa nan take to amma yanzu ma Alhamdulillah, DPO ma yaji Dadi sosai koba komai sun rage mugun iri,

*BAYAN SHEKARA DAYA*.............✍🏼




*Mun kada labarin su Alhaji Musa ne a gurguje don suna bata mana lkc inason mushiga gundarin labarin ne ,tabbas cakwakiya na gaba wannan sharar fage ne*

*YAKAMATA MUSAM WADAN NAN TAMBAYOYIN*👇👇

Miyafaru da Hisham yabar gida
Ina Momma take da Abokinshi ibrahim
Wacce Mariya da ahalinta suwa sukayi mata fyade har tarasa ranta ,
wanene zayyan wacece Amna su waye iyayensu
Wanene Amna keso sannan waya kashe zayyan
Wanene Baffah da ahalinshi
Ya makomar Hisham da Muneeba idan su Baffa suka tafi suka barsu
*_tambaya mai muhimmanci shin ina mahaifiyar Muneeba*?????
Miyafaru da ita sannan wace fansa ce Hisham yake cewa zai dauka
Shin zai dauki fansar ne kokuwa zai hakura ???


*Hmmmmmmm akwai rigima sosai a gaba yanzu book ya fara ku taimaka kubani hadin kai wajan yin comment ta yadda zakuci gaba da samun typing akai akai*

Pls ku tayani share🥰
[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻‍🔧

*_domin shiga grp dinmu na Telegram Danna wannan link din_*👇👇👇
https://t.me/joinchat/WBy_jhN2F8-1BJ0z1jtqsQ

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*👇🏻
*Jami'in d'an sanda*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍


🅿️_19

....................cikin tsananin tsoro duk suka zaro idonsu tareda d'ora hannunsu akai🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️ganin irin shurin da Hisham yayi da Haruna wanda k'ara d'aya yayi bai koma koda motsi ba , gaba daya idonsu kamar zasu fado k'asa yayinda cikinsu yayi wata irin murd'awa ,
Hisham kam baima kula da Haruna ya daina motsiba tsabar yadda zuciyarshi da idonshi suka rufe , sai ma k'ok'arin sake dukanshi da yakeyi , aikuwa 360 Ibrahim ya k'araso kusa da Hisham ganin ya daga k'afa zai saike d'auke bawan Allah da wani zazzafan shuri wanda yanada tabbacin in yayi mashi shi sai Allah idan ,zai rayu wannan yasa ya rik'e Hisham gam cikin rawar harshe yake fad'i ,
" Pls Hisham ka dawo cikin hankalinka mana ka tsaya muyi komai a nutse karkayi mana kisan kai pls ,"
Duk maganar da yakeyi sam Hisham baijinshi sai ma k'ok'arin k'wacewa da yakeyi,
Matar Inspector Haruna kuwa tun lokacin da Haruna yabuga wannan uwar k'arar ta rugo aguje zuwa d'akin , ganin abunda ke faruwa ne yasa ta fita aguje tana ihu da kiran ataimakamata za'a kashe mata miji , kamun kace mi har gidan yafara cika ,
Samarin unguwar da zafinsu suka shigo amma ganin Hisham sanye da kayan yan sanda sannan kallo Daya zaka mashi kasan cewa tabbas wannan ,Zaki ne da yake ganiyar farauta duk wanda yayi gigin shiga gabanshi kuwa to tabbas sai dai uwarshi ta haifi wani bashi ba , wannan yasa suka maida wuk'ar suka shiga lalla'ba Hisham da kyar tsoffin unguwar suka samu suka raba Hisham da Haruna wanda baimasan inda kansa yake ba,

Ibrahim ne ya sanya shi mota sannan yaja motar aguje suka bar unguwar don ya tsorata da yanayin abokin nashi tabbas in aka barshi zai iya kashe Haruna , gashi zafin zuciya yasa baiko bari Haruna yabashi shaidun da yace zasu taimakamashi wajan kama wadan nan azaluman ba ,

Mansur kuwa da yayi mutuwar zaune sai yanzu ne yasamu damar iya motsa jikinshi tabbas ya tsorata da muguwar zuciya irin ta yayan nashi , ashe haka yayan nasu yake ashe k
Zai iya kashe mutum sukutum saboda kudi kuma mutumin ma Abokinshi wato shiyasa yake yawan faɗin Alhaki ne ke bibiyarshi ashe shi yasan mugun abunda yake aikatawa wama yasan iya adadin mutanen da yakashe saboda son zuciya gashi nan yanzu wa gari ya waya , ina wadan da yayiwa aikin suke , ? Sun gujeshi saboda yagamayi masu amfani ,
Duk da yanda yakejin zafin shi kanan ya daure yasamo mai nafef suka sanyashi suka nufi asibiti dashi don har wannan lokacin bai farfado ba,


Direc gida Ibrahim ya wuce dasu zuwa lokacin gaba daya Hisham yagama ficewa daga hayyacinshi sam baya gane komai sai wasu irin surutai yake marasa kan gado , don abun ba k'aramun dukan k'wak'walwarshi yayi ba musamman da Haruna yamashi bayanin duk irin yadda suka shirya wannan had'arin gaba daya Abbanshi kawai yake gani a idonshi kamar a gabanshi hadarin ya faru,

Kamashi Ibrahim yayi suka shiga cikin gidan , a falo suka tarar da Momma ,
Tana ganinsu a wannan halin ta zabura a firgice tana tambayar abunda ya faru,
"Lafiya Ibrahim mi yasameshi, tayi maganar a tsorace don ganin halin da d'an nata yake ciki yayi mugun bata tsoro don bata taɓa ganinshi a irin wannan halin ba ko lokacin mutuwar mahaifinshi kuwa ,

Zaunar dashi ibrahim sannan ya dubi Momma cikin karfin hali don shima ba k'aramun tashin hankali ya tsinci kanshi aciki ba yau yace " bakomai Momma ki kwantar da hankalinki ki tofa masa addu'a PLS ko ya dawo cikin hayyacinshi ,"

"Yazaku shigo cikin irin wannan yanayin sannan kacemin ba komai Ibrahim , ?" Tayi tambayar jikinta na rawa,

"Kinga Momma ki kwantar da hankalinki an gaya mashi maganar da ta d'aga hankalinshi ne amma kibari ya nutsu zan maki bayanin komai ,"

Da mamaki Momma ta dubeshi har zatayi magana kuma sai ta fasa ta nufi Hisham ta zauna a kusa dashi tafara tofa mashi addu'o'i , inda daga baya tafara maimita innalillahi wa Inna ilaihin raji'un , a bayyane , a hankali shima yakama yana maimaitawa ,ganin hakan yasa Momma tayi murmushi a ranta don tasan koma minene to yanzu zai samu nutsuwa , aikuwa sai gashi a hankali yafara dawowa cikin hayyacinshi , lumshe idonshi yayi yanajin yadda kanshi ke wani irin sarawa kamar zai cire ga gawata irin k'ishi da yake ji bakinshi ya bushe sosai amma sam yakasa bude baki yayi magana , sun jima a haka sai da suka tabbatar da yadawo cikin hankalinshi sannan suka sauke ajiye zuciya gaba daya ,yayinda Momma ke cike da tunanin abunda yasamu dan nata har yafitar dashi daga hayyacinshi ,

Juyowa tayi ta zubama Ibrahim ido tace "Ibrahim ka gayamun mi yake faruwa , sam karka 'boyemun komai Ni musulma ce kuma nasan ƙaddara mai kyau ko akasin haka nayi imani ba abinda zai samu mutum face da sanin Allah ta'ala , nasan Allah baya ɗorawa bawa abunda bazai iyaba don haka ka gayamun kawai ko na samu nutsuwa a raina,

Hmmmm Ibrahim yayi ajiyar zuciya kamun a hankali ya bud'e bakinshi yace " Momma dama akan Abba ne.....,
Wani irin fad'uwa gaban Momma yayi amma sai ta danne tace " ina jinka wane Abban kenan?"

"Abba dai na nan gidan Momma Abban Hisham , to daga wajan Abokinshi Inspector Haruna muke , bisa dalilin son ganinku da yakeyi keda Hisham , to sai dai Hisham yace bazaije dake ba sai dai yaje shikad'ai inyaso koma minene shi sai ya gayamaki ,
Nan dai yashiga bata labarin abunda ya faru tun zuwansu har kawo yanzu wanda tunda yafara maganar Momma ke kuka sosai har yagama bata labarin wanda zuwa lokacin shima kukan yakeyi saboda yadda yake matuk'ar jin tausayinsu a ranshi yana tunanin in shine wannan al'amarin yafaru dashi ya zaiji ,

Cikin muryar kuka tafara magana ,
"Dama nasani ,najima da sanin cewa kashemun miji akayi saboda kawai an tsani irinsu a k'asar nan duk wani wanda yace zai kawo gyara a kasar nan tamu to za'a waye gari ne babushi a doron k'asa miye laifinsu?? saboda kawai suna aiki akan gaskiya? Ko saboda basa goyon bayan zalunci da azzalumai ,? shiyasa aka za'bi kawarda ire-irensu a doron ƙasa, wannan dalilin ne yasa na tsani aikin nan nashi saboda a kullum cikin barazana yake sun jima suna shirya mashi gadar zare kamar yadda suka jima suna kawarda ire-irensu ak'asar nan"

Tunda tafara magana daga Hisham har Ibrahim ido suka zubamata da mamakin kalaminta , cikin karfin hali Ibrahim yace ,
"Amma Momma kinsan da wannan kuma kikayi shiru babu wani mataki da aka dauka"?

"Hmm wane mataki za'a dauka ibrahim , ko in nayi magana zasu dawomin dashi ne ,sun riga da sun cuceni sun rabani da bangon jinginawata banida kowa sai Allah sai shi da Hisham ,nasan ba abunda za'yi ko na d'aga maganar nan mussaman ma da banida wasu kwararan hojjoji, ko inada hujjar ma bawani amfani don mai kudi shikeda hujja a yanzu akoma minene ,
sannan ina 'boye komai ne saboda Hisham nasani in ya sani komai zai iya faruwa don bazai taba yafe masuba kamar yadda suma bazasu taba kyaleshi ba zasu iya bin duk wata hanya don ganin sun cutar dashi kamar yadda suka cutar da mahaifinshi , abunda kuma bazan iya jura ba a wannan lokacin Hisham shikadai nake kallo naji dadi wannan yasa tun farko na barsu da Allah nasan Allah ba azzalumin bawansa bane ko yaushe ne Allah zai Mana sakkaya in a duniya in a lahira,

Izuwa yanzu kam idonshi ko kalluwa basayi tsabar jan da sukayi kamar jini zaifita daga cikinsu a hasale ya mike tsaye lokaci daya ya kaima wani table dake kusa dashi duka wanda ya kasance na glass ne aikuwa nan take ya tarwatse yayinda lokaci daya hannunshi yafara zubda jini saboda glass din da suka shigar mashi a hannu , wani irin gurnani yakeyi kamar wani zaki cikin kakkausar murya yafara magana ,
"
"Wallahi wallahi duk sai na shirya masu gadar zaren da zata rufta dasu wallahi sai naga bayansu da hannuna yadda suka kashemun mahaifi haka zan bisu d'ai bayan d'ai ina kashesu inyaso nima a kasheni amma tabbas bazan barsu ba , bazan taba barinsu ba *sai na dauki fansa* wannan alkawarine,


Dukkansu idanu suka zaro suka zuba mashi don kuwa yanayinshi ya firgita tunaninsu kallo Daya zaka mashi ka tabbatar har cikin zuciyarshi ne zai iya aikata abinda ya fad'a ga hannunshi na zubar da jini sosai amma bai kulaba kamar ma ba a jikinshi ciyon yake ba , wani irin tsoro ne ya daki zuciyar Momma lokaci daya ta fashe da wani irin kuka kamaun tafara magana ,

"Hisham indai Ni na haifeka to tabbas ban yarda ka dauki hukunci da hannunka ba ban hanaka neman hakkinka ba amma bata wannan hanyar ba idan kuwa har kace zaka dauki hukunci a hannunka to kuwa bazan taba yafe maka .........daga haka ta juya tayi shigewarta d'aki tana gunshek'ar kuka gaba daya sun tado mata da mikin mutuwar mijinta ga kuma

Please Login or Register in order to submit comment