Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

narkakkun idanunshi Yana amsa sallamar tata ciki ciki kamar yadda tayi, lokaci d'aya zuciyarta ta buga da k'arfi ganin Wanda yake zaune dama wannan Dan sandan ne yake kiranta,a Ina yasamu number ta to Kuma ya akayi yasan gidansu ne mima yakawo shi to ,?

daburcewa tayi ganin yadda ya zuba Mata idanu ,dama wannan Dan rainin hankalin ne yake kiranta a waya,? Tak'ara tambayar kanta
da k'yar ta tattaro nutsuwarta gudun kar ta bada kanta , had'e Rai tayi don karma yaga damarta a nutse ta k'arasa cikin falon sosai kamun ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna , a hankali take satar kallonshi gefe daya Kuma zee take zubama harara kamar idonta zasu fad'o k'asa ,dariya zee ta fashe da ita tana cewa "kinga anty maida wuk'ar bani na kar zomon ba rataya aka bani Ni tafiyata ma zanyi , "ta juya tana kallon Hisham tace Yayana sai anjima ko afito lafiya cikin murmushi yace to k'anwata nagode sosai kinji don Naga kinfi yayar Taki hankali, da dariya zee tabar falon don taga yadda antyn ke cika tana batsewa,cikin ranta kuwa addua takeyi Allah y tabbatar da alkhairi don itakam Hisham yagama burgeta sosai tayiwa yayarta sha'awarsa,

Jikinta har rawa yakeyi jin yadda idonshi ke yawo a jikinta da k'yar ta daure tace "Ina wuni"
Ajiyar zuciya ya sauke cike da kasala yace "ai na dauka Baki iya gaisuwar bane , " wani kallo ta aika mashi cikin turo Baki tace "mi ya kawoka gidanmu"? Murmushi yayi yace "Matata nazo na d'auka"
"Matar ka ? Wace Matar ka anan , to malam an rigaka sai ak'ara gaba ko zaka dace don na lura Kai ko neman So baka iya ba sai .......shiru tayi bata k'arasa ba ,
Cikin jarumar muryarshi yace " Ina saurarenki saimi ?? Ki k'arasa Mana ,turo bakinta tayi tana magana k'asa k'asa ,murmushi yayi yace "inba tsoro ba ki fad'a Mana ,juyar da kanta tayi gefe tana cewa "pls in bakada abun cewa inason Zan koma ,

"Ina zakije Baki amsamun soyayyata ba ? Taji ya fad'a kamar maiyin rad'a,
"Soyayya ! wace irin soyayya Kuma ai na gaya maka anrigaka yanzu haka saura k'iris a dauramun aure so kayi hakuri pls ,
Har yanzu murmushin yakeyi cikin yanayin tsokana yace "Jan aji zakiyimun bayan Kuma nasan bakida wani mashinshini ai k'anwata zee ta gayamun komai tace kinyi kwantai don haka kawai kibada Kai karkiyiwa kanki asarar santalelen saurayi kamar Ni ,ki Bari na rufa maki asiri nayi wufff dake ,ya k'arasa maganar Yana had'iye dariyarshi ganin yadda ta cika tayi fam kamar zata rusa ihu cikin tsananin 'bacin rai da takaicin zee ta hayayyak'o mashi kamar zata cinyeshi da masifa , d'an mitsitsin bakinta ya tsurama ido Yana kallon yadda yake motsawa komai nata cikin nutsuwa masifar ma sai tayi Mata kyau komai nata burgeshi yake ,tana cikin masifar ne batare data Ankara ba sai jin numfashin mutum tayi a kusa da ita ,da sauri ta waro idanunta waje tare da ja da baya ganin yadda ya matso ta , ahankali yafara tafiya Yana nufota ita Kuma tanaja da baya tare da Yi mashi gargad'i da idanunta da suke cike da masifa,
Ahaka har suka dangana da bangon d'akin hannuwasa yasa ya dafe bangon gefe da gefenta ya zamanata ya Sanyata a tsakkiya , kallon ido cikin ido suke yiiwa juna yayinda wad'ansu kibiyoyi ke fitowa daga idanunsu suna shiga cikin junansu kasa jurewa kallonshi tayi don lokaci d'aya ta nemi nutsuwarta ta rasa wani irin maganad'iso takeji Yana fisgarta daga cikin idon nashi kamar mayen k'arfe , ga kusancin da ya Samar a tsakaninsu wannan yasa takasa wani taka'bu jikinta ya saki sosai ,
"Maimaita abunda kikace , yafad'a cikin wani irin salo Wanda yak'ara narkar da zuciyar Laurat , turo bakinta tayi tana gunguni ,kamun ta d'ago idanunta ta zuba mashi harara , murmushi Mai kyau yayi Mata kamun yaci gaba da cewa " nidai Allah yagani tunda nayi niyar taimaka maki na dauke ki daga gidan nan to bazan fasa ba , nasan Allah zai bani Lada don haka zanje namasu Abbanki da maganar ko ya Kika gani yayi maganar Yana d'aga Mata girarshi daya cikin wani salon da shi kanshi baisan yayi ba Kuma sai hakan yayi masifar Yi mashi kyau , kauda kanta tayi daga kallonshi Jin yadda zuciyarta ta harba da k'arfi tare da kar'ban duk wani sak'o da yake aika Mata Sam takasa samun wata nutsuwa , ga magana tanason tayi Amma Sam takasa wani bak'on yanayi takeji Yana shigarta Wanda ya Sanyaya Mata jiki sosai , murmushi Mai kyau yayi ganin tarkonshi yakama kurciya , janyewa yayi daga kusa da ita ya d'anja da baya Yana dubanta yace " Ni Zan koma don Naga lokacin sallah Yana k'aratowa Amma jibi zanzo na gana da Abba don haka ki gaya Masa ,sannan in kinshiga ciki pls ki turomin k'anwata nayi Mata sallama kinji yafada Yana d'aga Mata hannu sannan ya juya yafara tafiya , har yakai bakin k'ofa yaji tace " in ka tafi basai ka dawo ba don Babana bazai taba baka Ni amatsayin Mata ba ta fad'a a tsiwace don taji haushin yadda takasa yi mashi duk wata rashin kunya da ta kullomashi ,

Murmushin gefen Baki yayi batare da ya juyo ba yace "akan mi fa "?

Cike da gadara tafara taku har tazo Inda yake tace "saboda aduniya kalma daya Tak Abba ya tsana "

"Ko Zan iya sanin wace kalma ce "?

Saida ta rausayar da Kai sannan cikin jin Dadin zata kuntata Masa tace " *Police*
A hankali ya juyo ya zuba Mata idanu Wanda take jikinta yafara tsuma Babu shiri ta duk'ar da kanta k'asa , cikin k'asaita yace Mata "nikuma nayi maki alkawarin sai ya so wannan kalmar fiye da tunaninki daga haka yajuya yabar falon cike da nishadi don ko kadan maganarta Bata razanashi ba a tunaninshi kawai ta fad'a ne don ta Bata mashi rai..........

FATAN KUNYI SALLAH LFY



*HAPPY SALLAH HAPPY SALLAH*
πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

*Dr Mmn Yusuf (likitar Mata)*😍😍😍

*BONONZA BONONZA BONONZA*

*Karku Bari abarku a baya don mace Mai gyara kanta Bata boranci , kayane ingantattun Kuma zafafa ,na sakesu a arha don tayaku murnar shagalin sallah dakuma Amaren bayan sallah Yan Mata da zawarawa uwar gida da amarya ku garzayo ku kwashi rabonku kar ayi babuku, Sam karku Bari wannan damar ta wuce ku karku manta MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI Kuma a Dade anayi sai gaskiya namu ba irin nasu bane kayanmu na musamman ne domin jin Dadin ma'aurata Babu kalan kayan matan da bamudashi kedai garzayo kar abaki labari mmn Yusuf Dr Mata farincikinku takeso*😍😍😍😍

*Ina Amaren da suke k'amas komai a bushe to kuzo nazo maku da ingantattun kayan gyaran jiki Wanda Zaki ciko gaba da baya kuyi d'ass abunku gwanin sha'awa*

*Amaryar dake da matsalar rashin nono ko hips ko siranta yayi maki yawa kike buk'atar kidan ciko to kizo na tanadar maku ingantaccen maganin nono da maganin hips da maganin k'iba ta yadda Zaki kankarowa kanki martaba a wajan oga ,uwa uba SAHIHIN MAGANIN SANYI Wanda yakeda. Matukar muhimmanci ace kowace amarya tafarayi kamun komai don indai kinada ciyon sanyi to duk abunda zakiyi amfani dashi to bazaiyi maki wani tasiri ba AMARE YAKAMATA A KULA KAR AJE AYI TA BARNAR KUDI A BANZA ANA GYARA BAYAN GA SANYI BA'A MAGANCESHI BA*

*Wadda take fama da rashin sha'awa , rashin niima kullum kasanki a bushe to ki garzayo wajan mmn Yusuf Dr Mata Zaki rabu da wannan matsalar da izinin Allah*

*Masu bukatar sabulan gyaran jiki na gani a fad'a masu sa jiki yayi kyau yayi lumi-lumi yayi haske Mai kyau bana bilicin ba yacire maki duk wani tabo ko kurji da yake jikinki ,da shahararrar DILKA Mai maida tsohuwa yarinya ga k'amshi Mai Kama jiki gasa sulbi da santsin fata kamar ta jariri to ku garzayo Kuma ku kwashi rabonku a farashi Mai sauki ,wajan mmn Yusuf Dr Mata Ina sokoto Ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah adade anayi sai gaskiya*

07069711327. Call or WhatsApp

Pls wadda Bata shirya siya ba kar tamun mgn serious pls kibari in kin shirya sai Musa labule πŸ˜‰ banason mu batawa juna lokaci ne ga azumi typing ba dadiπŸ₯±πŸ₯±
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ

*_MALLAKAR_*

~MARYAM UMAR ABDULLAHI~
( _MMN YUSUF_)
*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*


πŸ…ΏοΈ_33

.......................da k'yar ya bude kumburarrar fuskarshi da har yanzu takasa komawa dai sai saboda sambad'e bad'en da yasha Wanda sanadiyar hakan hak'oranshi biyu na gaba suka fita wannan yasa yakoma kamar wani dodo saboda Muni Kuma dama can ba kyaun ne dashi ba yace ".wai oga yanzu haka zamu k'yale wannan banzan Dan sandan bazamu dauki fansa akan shege ba ka duba yadda gayen nan ya mayar Dani, Ni kaina kunyar kaina nakeji, shiyasa ma yanzu Sam bana fita ko Ina jiya bakaga yanda babys din nan su Sumy suka dingamun dariya ba wallahi naji haushi sosai, cewar d'aya daga cikin abokan Zayyan Mai sun junior,
Zaune suke a katafaren falon Zayyan da babuce kawai Babu aciki , Yana zaune akan kujera ya Dora kafa daya Akan daya Yana girgizawa cike da izgilanci yayinda abokan nashi suke zagaye dashi suna jiran umurni ,a hankali ya d'ago da kanshi ya kalli fuskar Junior yace
Kaima kasan bazan ta'ba k'yaleshi ba don ba Wanda ya ta'ba yimun irin wannan dukan da yayimun tunda uwata ta haifeni , yanzu haka bincike nakeyi akanshi sosai , Kuma Dad ma Yana nan Yana bincike akanshi saidai Ni bazan wani jira Dad ba da kaina nakeson na dauki mataki akanshi Amma kamun nan sai naci gaba da lalata yanmatan da bayaso ayi Ina aika mashi dasu har office dinshi sai Naga abunda zaiyi sai na wulakantashi kamun nasa a 'batarmun da shege zai gane ya ta'bo Zayyan wallahi yayi maganar cikin tsananin 'bacin rai da fushi ,
Wani daga cikinsu Mai suna Shams yace "yes sai oga haka nakeson ji babaaa Ni wallahi ma naso ace yanada k'anwa ko Mata billahillazi da akansu zamu sauke iskancinmu inyaso ya hura wuta ya jefamu Allah oga da tsaf zamusa a daure Mana shi Yana kallo muyi masu kaca kaca wallahi Amma ba komai yanzu ma Bata 'baci ba zamu sake aikata fyade ga duk wadda tayi Mana in yaso muzuba mu dashi shege ka fasa , yayi maganar Yana wani cizon Baki irin na cikakkun Yan Daba , daga Zayyan har sauran yaran dariya suka fashe dashi , Junior yace " Kai shams kasan takan tsiya fa Allah har naji haushin da bashida kanwa da munyi mashi abunda har yamutu bazai manta damu ba ,saidai Kash gashi bashida ko daya ,

Wani mushirikin murmushi Zayyan yayi yace " ai yanada mahaifiya ko, Allah Ni ko akanta Zan iya sauke haushina nasan daga lokacin zai hade zuciya ya mutu shikenan basai na walahar da kaina wajan aikawa dashi ba , gaba dayansu suka fashe da wata mahaukaciyar dariya suna Yi mashi kirarin da suka Saba aduk lokacin da yayi wata tabokara irin wannan ,

Mom dake tsaye tun d'azu tana saurarensu ta girgiza kanta cikin matukar damuwa da tashin hankali ta k'araso cikin falon tana cewa
" Zayyan mi naji kana cewa ? Anya Zayyan kwakwalwarka Bata fara juyewa ba kuwa kasan wanene Hisham kuwa to wallahi tun wuri ka fita sabgarshi inba haka ba wallahi bazatayi maka kyau ba ,daga Kai har uban baka da kake tak'ama dashi , ka daina biyewa mahaifinka da wadan nan shashashan abokan naka suna dauraka a hanyar da bazata 'bulle da Kai ba sannan in ................"ohhhhh Mom ya zakizo ki cikamu da surutu ne , ko kinji na kiraki ne ohh wato ma la'be kikemun ko ,to kibari In mun janyo bala'in ai ba akanki zai sauka ba don haka don Allah mom kije Kuma ki daina irin wannan yawar kina bayar Dani agaban abokai haba , Ni Zan gayawa Dad ma ya siyamun gidan da Zan zauna kawai na barmaki nan Dake da wannan munafukar Yar taki , Baki ganniba ma bare kisamun eyes haba,
"Innalillahi wa inna ilaihin rajiun Zayyan Ni kake gayawa wannan maganar , tafad'a kamar zata fashe da kuka , cikin jin haushin kanta da tabiyewa son zuciya wajan za'bar Wanda Bai kamata ta za'ba a matsayin abokin rayuwarta ba tace " shikenan ba laifinka bane laifin ubanka ne da ya daure maka gindi kayi duk abunda kaga dama ,Allah ya shiryeku Baki d'aya daga haka ta juya tabar falon cike da k'unar zuciya,

Tana fita Zayyan yayi tsaki Yana gunguni tare da Harare Harare kamun yace Kai ku tashi mubar gidan nan muje gidan gonar daddy don wannan Matar bazata daina takurani ba ko tausayina bataji Anya ma itace mahaifiyata kuwa yafada Yana k'wafa , aikuwa kamun kace mi sun tarkata sun fice a gidan ,

_________________________

"Assalamu alaikum " tayi sallama cikin shiriritar muryarta ,
" Wa'alaikissalam shigo ki zauna " cewar Abba , kusa da k'afafun Momy taje ta zauna kanta a k'asa tace "Abba barka da hutawa , " kanshi kawai ya d'aga Mata alamar amsawa sannan yace
" Naji sak'onki a wajan k'anwarki tace mun kin samu Wanda kike so harma kun daidaita kanku ko ? to alhamdulillah naji d'ad'in hakan abunda nakeso yanzu shine ki gayamun waye shi inason in gana dashi don sanin asalinshi dayin bincike akanshi ,don haka tunda har kuna waya dashi to ki sanar mashi cewa Ina nemanshi gobe in Allah ya kaimu , Allah yayi maku albarka ya za'ba abunda yafi alkhairi , cike da farinciki Momy ke amsawa da Amin yayinda Laurat tayi suman zaune tana mamakin yaushe tayi da zee akan ta gayawa Abba tasamu miji ne innalillahi Amma wannan yarinyar ta gama da ita , yanzu yadda taga suna farincikin nan ta Yaya zata ce masu ba haka bane , sannan ta yayama zata daga waya ta Kira wannan Dan rainin hankalin tace mashi Wai Abbanta na nemanshi , ai sai ya dauka ma tana sonshi kenan , runtse idonta tayi da k'arfi cikin takaici lallai Zee tayi Mata d'aurin talala yanzu minene mafita ,
"Laurat lafiya dai Ana magana kinyi shiru, "
Zubur tayi tana Yan soshe soshe cikin in Ina tace " ah.. ba..bakomai Abba Zan ..zangaya mashi ,
Jinjina Kai yayi yace "to shikenan Ina jiranshi don indai nayi bincike akanshi Naga ya cancanta da aurenki to bazamu dauki wani lokaci ba indai a shirye yake insha Allah, "
"Allah ya tabbatar da mafi alkhairi Amin" cewar Momy ,
Sum sum sum Laurat ta tashi tabar falon inda Abba da momy sukaci gaba da tattaunawa akan zanca ,

Tunda ta fita daga falon take zuba sauri kamar zata tashi sama direct d'akinsu ta nufa tana zuwa ta banka k'ofar d'akin a fusace ta shiga , da sauri Zee ta juyo Jin yadda aka banko k'ofar d'akin ga bakinta taf da wata k'atuwar alewa tana taunawa kamar zata tsinke harshenta don wani shegen Dadi da alewar ke Mata ,da k'yar maganarta ke fita saboda yadda alewar tacika mata baci tace " haba anty wallahi har kin tsoratani irin wannan dukan k'ofa haka Ina nan zaune Ina cin kayan Dadina Zaki razanani ,haba ai wannan daukar hakki ne wallahi ,

Wata irin harara Laurat ta aika Mata kamar idanunta zasu fado k'asa cikin kakkausar tace " yaushe na ce ki gayawa Abba nasamu Wanda nakeso yaushe mukayi hakan Dake eye , wallahi Zee kifita a idona yanzu ya kikeson nayi da Abba gashi ya kirani Wai na turo mashi shi , to Taya Zan turo shi din ,bayan Babu komai tsakanina dashi kawai Ina zamana kinzo kin sani tsaka Mai wuya saboda neman fitina irin naki ,to ai sai kije ki gaya masu gaskiya don ni ba wani kiranshi da ,zanyi,

A hankali zee ta kwashe kayan makulashen da ta zube a gabanta tana kwasa Wanda duk suna cikin tsarabar da Hisham ya aikowa Laurat dasu ,Wanda ko kallon kayan tak'iyi shiyasa zee ke bikinta son ranta da kayan ,cikin nutsuwa ta mayar da komai inda yake sannan ta tashi ta nufi inda yayartata take janyo hannunta tayi a hankali ta zaunar da ita a bakin makeken gadon su tace "don Allah anty kiyi hakuri ki gafarceni banyi hakan da musgunawa a gareki ba saidon inason kisamu makoma Mai kyau ,duk da bansan halin yayana ba Amma Ina kyautata mashi zato kallo daya zakayi mashi kasan cewa akwai hankali da nutsuwa a tare dashi , hakama kallo daya zakayi mashi kasan cewa shin din Mai ilimi ne ta kowane fanni yanayinshi ma ya nuna haka , Ina rokonki da kiyi hkr ki tsaya ki fahimceshi na tabbatar da Zaki sameshi % sannan kinga Abba ma zaiyi bincike akanshi doli sai ya tabbatar da nagartarshi kamun ya yarda yabashi ke , nasan dai a yadda yake kyakkyawan nan bazakice baiyi maki ba anty don bashida makusa, kota Ina yayi burin kowace mace ne ki zauna kiyi tunani ko don ki farantawa iyayenki don tsakanin jiya da yau suna cikin farinciki sosai pls anty kiyi tunani , daga haka ta tashi ta bar Mata d'akin , tana fita tafara tik'ar rawa ganin yadda maganganunta suka Yi tasiri akan Lauratu,

Shiru tayi kusan minti talatin tana saka da warwara ta hanga ta hango tabbas gaskiya zee ke fad'a Babu wata makusa atare da Hisham Babu macen da zata ce Bata sonshi saboda ya hada komai da mace zata bukata a wajan namiji , ita kanta tasan Bata Isa tace Bata sonshi ba kawai dai gayen ne Dan rainin hankalin Wai harda cewa zai taimaka Mata yayi wuf da ita sai kace wata wadda tarasa masoya ,ta dauki lokaci Mai tsawo tana tunanin mafita don itadai batajin sonshi haka Kuma batajin Bata sonshi , saidai Abu daya ta sani shine Yana burgeta sosai ,( ahaf Zaki dawo hanya ne yarinyaπŸ˜‚πŸ€£)
Tana hakan Zee tak'ara shigowa d'akin ,zama tai kusa da ita tace "yadai anty kin kirashi ne , ? Harara ta banka Mata tace na kirashi nace mashi mi ,dariya zee tayi tace to kwantar da hankalinki na rage maki aiki na kirashi na gayamashi don dama na karbi number shi , wani kallo Laurat ta watsa Mata tace "mi kikace mashi ? Badai kinje kin saki Baki kina zuba zance da Wanda aka tambayeki da Wanda ba'a tambayeki ba kinasa Yana Raina mutane ,
"Aa fa anty nifa nasan abunda nakeyi cemashi kawai nayi Abba na nemanshi gobe daga haka na kashe wayar "
"Kedai Kika sani da shegen rawar Kai mrtss, "
Daga haka tafad'a kan gadon ta gyara kwanciyarta cike da tunanin Hisham ,
_________________________

"Momma Albishirnki "
"Goro fari Tass shalele "
"To alhamdulillah yanzu dai na wuce Gori na samu maki santaleliyar suruka ,yanzu haka ma Babanta ne yake kirana gobe zamu gana kiyi mun addua Allah yasa yabani ita don Ina sonta sosai,"
Kafeshi da ido momma tayi don son gano gaskiyarshi in ba shak'iyancin nashi ne ya motsa ba , musamman da Bata taba Jin yace yanason wata mace ba ,
"Da gaske kakeyi shalele"??
"Allah momma da gaske nakeyi Bari ma na nuna maki hotonta , "
Wayarshi ya dauko ya nono wani hoto na Laurat Wanda an daukeshi ne a asibiti kayanta na aikin asibiti ne ajikinta yayi kyau sosai da alama ma batasan an dauketa hoton ba , ya mik'a Mata ,

K'urama hoton ido momma tayi cike da farinciki tace "Kai Masha Allah shalele Ashe dai ka iya za'be wannan yarinya haka Masha Allah son kowa k'in Wanda ya rasa Masha Allah Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah sarki Samrah Ashe ba rabon ayi da ita bane Allah yabata miji nagari ,wata muguwar dariya ce tazowa Hisham tunawa da fasalin Samrah da yayi a ranshi yace ah toh ak'ara gaba dai da yanzu an shak'amun wannan zar'ben ko inyi Yaya da ita ohoπŸ€”
"Yawwa Momma Ni Zan wuce wajan aiki sai na dawo ,
"To shalele a dawo lafiya Allah ya tsare yabada sa'a "
"Amin y Allah Momma daga haka yasa Kai yabar gidan ,
Direct gidansu Safiya yafara zuwa alhamdulillah yanzu taji sauki sosai sai dai duk yanayinta ya sauya abun tausayi kullum zaka ganta shiru shiru tana tunani sam Bata walwala magana ma sai ta wuni batace kala ba sai yazama doli abun Yana damun iyayenta sosai saidai Babu yadda suka iya sai addua da suke Mata a kullum , gashi makarantar ma anyi anyi Takoma ko zata rage wannan damuwa Amma Taki da anyi maganar ma sai tafara yimasu kuka , wannan yasa mahaifinta ya nemi taimakon Hisham akan yayi Mata magana ko za'a dace ta yarda da maganarshi ganin yadda takebin duk abunda yace mata,


*Banso na tsaya anan ba Sam Amma yazama doli wlh banida lfy ku tayani da addua jiya ma shi ya hanani post banajin Dadi wlh kuyi hkr da wannan*

*Wadan da sukeso daga farko ga link nan a k'asa kuduba ta Wattpad zaku samu ngd sosai*

I think you'd like this story: "JAMI'IN DAN SANDA" by MmnYusuf on Wattpad https://www.wattpad.com/story/269145691?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=MmnYusuf&wp_originator=u5DC1AfUjn3VMvEBRA8AdWZQ%2FFF3m4j3FJj5yG9L%2B7MULqzPeCvhYv%2FmD32Q5erjhTS%2F8%2FwQtAN3lqQl4u0k7nBoC5PhqKfSSTmopPn2C8TGcX0DUDQQBtxZFOZUZVIZ

Ngd
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA*πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ

*_MALLAKAR_*

~MARYAM UMAR ABDULLAHI~
( _MMN YUSUF_) *_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Masu bukatar wannan littafin daga farko su duba wattpad zasu samu ga link din nan k'asa* πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»
I think you'd like this story: "JAMI'IN DAN SANDA" by MmnYusuf on Wattpad https://www.wattpad.com/story/269145691?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=MmnYusuf&wp_originator=VI1NWAufZb0tx3t77W69IEk8v6Q9Hyxe7SN13OW29bnoIlDbsBwOX40OX%2BiagGLOwiWP4bupJY75QC0AYa3IQyOf9C6cNq%2FsfKfEdhq%2FQqp3Wihagg0pTRl7AYJddvQb

πŸ…ΏοΈ_34
...................Zaune suke a falon Abba Yana jiran shigowarshi , hakanan kurum yakejin gabanshi yana fad'uwa yayinda kuzarinshi da k'warin gwuiwar shi yake raguwa , Sam baibi ta kan kayan motsa bakin da aka ajiye mashi ba, zuciyarshi tayi nisa wajan tunanin yadda mahaifinta zai kar'beshi , Sam a Ada Bai dauki maganarta da wani muhimmanci ba sai ma ganin da yakeyi duk cikin son ta 'bata mashi rai ne , Amma miyasa yanzu yakejin fargaban abunda yaji daga bakinta , _"ba abunda Abba ya tsana kamar kalma d'aya , police,_ wannan kalmar ce ke caccakar zuciyarshi da sashi fargaba ,saidai in ya tuna addu'o'in Momma akanshi sai yaji tabbas shine da nasara , Yana haka ya tsinkaye sallamar Abbansu zee cikin kamilalliyar muryarshi Mai cike da nutsuwa da tarin dattako , da sauri Hisham ya mik'e tsaye cikin girmamawa ya amsa sallamar sannan ya durk'usa har k'asa ya gayar da Abban ,
Cikin fara'a Abban yakamo hannunshi ya tayar dashi zaune kamun yakamo hannunshi sukayi musabaha yayinda yake amsa mashi gaisuwarshi ,sannan ya zauna Akan kujera inda Hisham ya zauna akan kafet din dake malale a wajan ,
"Aa Hisham hau kujera ka zauna Mana "
"Cikin yin k'asa da Kai yace "aa Abba nan ma ya isa ai , nan suka sake gaisawa kamun Hisham yayi shiru Yana jiran yaji ta inda Abban zai fara,

"To Alhamdulillah naji dadin ganinka a matsayin Wanda yakeson auren 'ya ta saboda a kallo d'aya naji na gamsu da yanayin nutsuwarka da Kuma tarbiyar ka Amma duk da hakan inason sanin waye Kai ,? Asalinka dakuma aikinka inyaso daga baya Ni sai nakarasa bincike akanka kamar yadda addini ya koyar ,don haka Ina saurarenka ,"

Jinjina kanshi Hisham yayi yace hakane Abba Kuma hakan da kayi shine dai dai , ni asalin Dan sokoto ne aikine ya kawo mahaifina wannan garin na lagos......nan dai ya fad'a mashi Dan takaitaccen tarihinshi da Kuma matsayin aikinshi ,

Cike da mamaki Abban yake kallonshi yace " kana nufin kai d'an wajan Asp Abdulrahaman ne ,?ikon Allah girman Dan

Please Login or Register in order to submit comment