Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

,duk wanda yake hark'allar Miyagun kwayoyi to zaka samu a k'ark'ashinsu ya ke ta nan ne suke samun mahaukatan kud'ad'e ,yayinda gefe daya suke shigo da gur'bataccen magungunan asibitin daga k'asashe daban daban ,wad'an da sun kasance masu cutarwa ne ga lafiyar mutum duk wanda yayi amfani dasu a hankali a hankali zasu rinฦ™a kassara rayuwarshi batare da ya sani ba ,su kuwa hakan ba damuwarsu bace tunda biyansu akeyi sunacin dudduniyar k'asarsu,

Ta dayan bangaren kuma suna nunama jama'a cewa su mutanen kirki ne ta hanyar yin sadaka gina masallatai makarantu bada tallafi ga mabuk'ata wannan yasa mutane da yawa suke son su dayi masu kallon mutanen kirki , wanda dama su haka sukeso bawai don Allah sukeyi ba a'a sai don ganin sun kauda idon mutane daga kansu ,
Wannan yasa hankalinsu yayi mummunan tashi lokacin da inspector Abdulrahaman yasan sirrinsu wanda yayi barazanar tarwatsa muguwar manufarsu ,
Har gida sukasa akayi masu kiranshi , batare da wata damuwa ba ya amsa kiran nasu , inda suka bashi mak'uddan kudade akan ya janye idonshi daga kansu sannan karya kuskura ya tona masu asiri inba haka ba kuwa zasuyi duk yadda zasuyi don suga bayanshi ,

, alokacin sam Abba bai wani damu da barazanarsu ba kuma kai tsaye ya gayamasu bazai amshi ko sisinsu ba sannan bazai fasa kai wannan case din kotu ba tunda yanada duk wata hujja a hannunsa , haka nan ya juya yayi tafiyarshi yabarsu baki sake,

Tun daga lokacin suke bibiyarshi tare da yimashi barazana kala kala , da farko sunki kasheshi ne saboda sunason su sani shi da gaske yanada wasu hujjoji akansu kamar yadda ya fada kokuma yafad'a ne don yayi masu barazana , in da gaske ne taya zasusan shirinshi da inda yake da hujjojin,

Sai dai abunda basu sani ba shine abba bashida wata hujja k'wak'k'wara sai goga gashi shikuma goga yaki bada hadin kai dukda irin azabar da ake gana mashi , wannan yasa lokacin da suka gayyaceshi yaje anan ya shirya masu tarko don kuwa duk maganganun da sukayi dashi ya nad'esu tsaf a wayarshi ,

Alokacin da suka samu labarin daukar da Abba yayi ne wanda ita kadai ce hujjarshi yasa suka yanke shawarar kashe shi kawai

Alhaji Manu Yana kan kujera Yana zuk'ar taba duk ya had'a d'an k'aramun gajimare a wajan , meeting sukeyi akan wasu kaya da zasu shigo dasu , do neman hanyar da zasu wuce da muggan makaman batare da wata matsala ba,

D'aya daga cikin masu tsaron k'ofar ne ya shigo ya d'an rank'wafa alamar girmamawa yace " sir kana da bak'o yana waje yace yanason ganin ka ne,"

Saida ya share sama da minti ukku sannan ya dubi security yace "wanene wannan "
"Inspector Haruna ne"
"Ok kace ya shigo "
"To sir" juyawa yayi ya fita daga falon,

A hankali inspector Haruna ya shigo yana wani dudduk'ewa yana washe baki sai faman zabga masu kirari yake yana mik'a gaisuwa ,
Dukkansu ba wanda ya dubi inda yake , tun yanasa ran cewa zasu bashi izinin zama har yafara sarewa ganin sama da 15mnt ba wanda ya kalleshi acikinsu sai faman shaye shayensu sukeyi suna tada hayak'i,
Yawu ya had'iye da k'yar ganin yadda Yan jagaliyar ke yi mashi muzurai kamar wasu zakuna,

"Mike tafe da kai "? Cewar Alhaji Manu

"am am dama Alhaji zancan kud'i da kukace zaku bani ne *Naira miliyan ashirin* to naji shiru har yanzu gashi har anyi watanni , ga wannan ciyon da naji a kaina lokaci da wannan had'arin ya faru ya fara damuna sosai har yanzu fama nakeyi dashi kuma likita ya tabbatar mun da cewa nasamu matsala acikin kaina ne.doli sai anyimun aiki kuma kudin sunada yawa sosai yace rashin yin aikin nan zai iya haifarmun da babbar matsala anan gaba san."..................... "Kai dakata don Allah kazo sai zuba kake sai kace wani Radio , yanzu kai in Banda cewa d'an mahaukaciya ne kai taya kake tunanin zamu baka kudi har miliyan ashirin , ubanmi kamana da zamu baka wannan uwar dukiyar , to kaji da kyau ko sisi bazamu baka ba , inace tun farko munbaka one million to kaje sun isheka inba hakaba abunda yasamu dan uwanka kaima zai iya samun ka, " cewar Alhaji Manu,
Alhaji Musa da Alhaji Buba kuwa ko kallonshi basuyi ba , ganin hakan yasa ya tashi jiki a sanyaye ya fita daga falon , tafiya yakeyi yana hada hanya gaba d'aya sun rusa masa babban burinsa ,tuni ya riga da ya shirya yadda zai gudanar da sabuwar rayuwa idan har suka bashi kudinshi miliyan ashirin kamar yadda suka mashi alk'awari , wani irin tururi zuciyarshi keyi yanajin wani irin bakinciki , d'ayan gefe kuma ga matsalar da yasamu yayin yimasu wannan aikin don saida ya share wajan sati Daya a asibiti sakamakon buguwar da kanshi yayi wanda har gashi hakan ya zame mashi matsala don in ciyon kan ya tashi haka zai koma kamar mahaukaci yana ihu da buge buge tsabar azabar da yakeji , dama shirinshi shine suna bashi kudin zai fita kasar waje amashi aikin sauran sai ya ja jari kawai , don a niyarshi ma zai ajiye aikinshi ne yafara kasuwanci tunda banza ta samu, to sai gashi cikin kankanin lokaci sun rusa mashi komai Kuma bazai iyayin komai ba!!!!

" Inaaaa wallahi bazai taba yiwuwa ba suna nufin sunci moriyar ganga kenan bayan duk irin kokarin dana masu , sannan ga kasadar da nayi wanda gashi nan na hadu da ciyo mai matukar had'ari ga cin amanar abokina da aikina da nayi sannan ace duk wannan ya tashi a banza to wallahi bazai taba yiwuwa ba wallahi koni ko su sai dai ayi mutuwar kasko, " sambatun da ya rink'a yi kenan bayan ya dawo gida ya kulle kanshi a daki , daga baya ma tsabar bacin rai bai san sanda yayi zaune dirshan ba yafara kuka wiwi kamar wani karamin yaro,........



__________________________

"Assalamu alaikum , " yayi sallama tareda d'age labulen falon , Momma ce da Inna Indo zaune suna karyawa , Inna Indo ce kawai ta amsa mashi amma Momma ko kallon inda yake batayi ba , tadai amsa sallamar acikin ranta, sati Daya kenan da yayi mata maganar son shiga aikin d'an sanda ,tun daga lokacin ta dauke mashi wuta , ta daina shiga sabgarshi gaba daya , fushi takeyi dashi sosai , ta yadda zai dauki abun da muhimmanci , tasan Hisham bayason fushinta ko kad'an duk yadda yakai ga son abu data nuna bataso to zaibar abun duk yadda yakeson shi kuwa , amma abunda yake bata mamaki shine yanzu k'iri-k'iri ya kafe akan ra'ayinshi , duk kuwa da irin fushin da takeyi dashi,

Kusa da Inna Indo ya zauna yana gayar da ita kamun ya juya wajan Momma yace "Momma Ina kwana,"
Shiru bata amsa mashi ba , har cikin ranshi yanajin ciyon yadda mahaifiyar tashi ke fushi da dashi amma ya zaiyi tunda ya dauki alk'awarin sai ya cikawa mahaifinshi burinshi,

"Momma izuwa yanzu Yakamata ki fahimceni sam bana kafe akan ra'ayina bane don na 'bata maki , a'a kawai dai inason na cikawa Abbana burinshi ne , kema kin sani Momma sam wannan aikin baya raina amma a haka na ajiye nawa ra'ayin don ganin nayi abunda mahaifina yakeso , ki tuna Momma ko a ranar da zai bar duniya saida yayimun magana akan wannan buri nashi , ai Yakamata ki bani goyon baya , insha Allah ba abunda zai faru sai alkhairi Momma ,

"Runtse idonta tayi yayinda wasu hawaye Masu zafi suka zubo mata cikin Muryar kuka tace " kai yaro ne Hisham har yanzu da k'urciya a tare dakai , sam bazaka iya hangowa kanka abinda Ni nake hango maka ba , sannan indai har Ni na haifeka to inason kabar wannan maganar don sam bazan ta'ba yarda kayi wannan aikin ba , nasanka nasan halinka shigarka wannan aikin zai iya ...................." Haba Maryamu karki yiwa d'anki baki mana miye aibun wannan aikin ne da kike k'iyayya dashi haka , Ni banga abun tashin hankali ba anan , tunda har ya nuna ga abunda yakeso kibarshi yayi aikinshi mana , tunda kinaji yace saboda mahaifinshi zaiyi, shin ke bazaki iya goya mashi baya ba don ganin kin tabbatar da burin mijinki ya tabbata ba akanshi , na tabbatar da in kece kika mutu da irin wannan burin to duk yadda Abdulrahaman zaiyi sai yayi don ganin yacika maki burinki koda baki a duniya haba Maryam kiyi hkr ki bishi da addu'a kawai shi zaifi,

Batare da Momma tace komai ba ta tashi tayi shigewarta d'aki tabarsu anan , tana shiga ta fad'a saman gado tare da sakin wani marayan kuka yayinda kewar mijinta ta dawo mata sabuwa ,
Batason Hisham yayi wannan aikin ne don tana gudun watarana ya binciko gaskiyar abunda ya faru da Abbanshi ta tabbatar da sai ya dauki fansa bazai taba yin shiru ba , in hakan ta kasance tayaya zai iya ja da wadan nan hamshak'an mutane , karshenta shima su samu sharrin da zasuyi mashi , taya zata juri wani abu yasamu Hisham a yanzu shikadai take kalla taji dadi batada kowa sai Allah sai Hisham taya zata bari tanaji tana gani ya jefa rayuwarshi a hadari irin wannan,......


Dukkansu da kallo kawai suka bita lokacin da take shigewa dakin , ajiyar zuciya suka sauke yayinda gaba daya Hisham yaji duniyar na juya mashi kwata kwata ya tsani ganin 'bacin ran mahaifiyarshi ,tunani yakeyi ko ya hakura da aikin ne kawai kamar yadda takeso,!
Wata zuciyar tace zaka iya hakura da burin mahaifinka kuwa wanda ka dauki alk'awarin sai ka cika mashi shi , kawai kaci gaba da lallaba Momma insha Allah zata sauko ta amince , haka yayi ta sake sake a zuciyarshi,

Dafashi Inna tayi tace " karka damu Hisham zata sauko ne kuma nakama alk'awari. Zan shawo maka kanta insha Allah,"

Yawwa Inna Indo dakuwa kin kyautamun sosai wallahi,

Acikin satin kuwa Inna Indo ta samu ta shawo kan Momma da lallashi da wa'azi , a wannan ranar Hisham yayi farinciki sosai , bai zame ko ina ba sai inda ya ajiye form din da yasiya , ya dauko shi ya ciccike komai sannan. Ya dauka ya fita dashi ,

Bayan wata daya komai ya kammala aka tura su makarantar koyon aikin dan sanda inda daga wannan zuwan bazasu dawo ba sai sun zama cikakkun *jami'an tsaron na police*


Wata d'aya kenan da yaje wajansu Alhaji Manu , tun daga lokacin yake shirya masu tuggu kala kala amma yakasa samun nasara akansu saima barazana da suke masa don shekaranjiya har gidanshi suka turo mashi yan daba inda suka kama matarshi da yaranshi suka rufesu a cikin daki shikuma suka tu'beshi suka zaneshi tass saida jikinshi ya farfashe sannan suka mashi barazana da cewa idan har bai dauke idonshi daga kan su Alhaji Musa ba to zasu rabashi da duniyar baki daya ,
Aikuwa ya tsorata da lamarinmu sosai don yasan Daga su har uwayen gidan nasu basu da k'warar imani zasu iyayin komai don ba abunda aka isa ayi masu ,gashi tun daga lokacin ciyon kanshi keson tashi kullum baya bacci yarasa abinda ke masa dadi duniya , sai yanzu yafara nadamar abunda ya aikata ma Abokinshi dakuma cin amanar kasar shi.....................kai nagaji sai jibi kuma...๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ


*Kuyi hkr rashin jina kwana biyu nayi rashin waya ne*

*Please comment and share*๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ



*ZANYI AIKE KANO DA KATSINA ABUJA KADUNA DA ZARIYA MAISON INGANTATTUN KAYAN MATAN MASU KYAU DA INGANCI TAYI MAGANA TA PC KO TA KIRA WAYA NGD 09035027743* ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ
[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

https://chat.whatsapp.com/LdqBkVqx2KX5S37HviKf4U

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ_17

_*BAYAN WANI LOKACI*_

.......................... Cikin ikon Allah da iyawarsa yau Hisham Allah ya cika mashi burinshi kuma burin mahaifinshi , yasamu tsananin horo da sanin makamar aiki wanda duk wadanda sukayi aikin tare gaba daya yasha kansu ya zage ya koyi komai da dukkan zuciya wannan yasa yazama gagara badau kuma zakaran gwajin dafi ,inda ya fito a matsayin *babban Sifeta* na wannan yakin ,

Kyakkyawan matashi dan shekara 28 fari ne tas mai cikar zati yanada tsayi sosai da siffar k'arfi , kallo Daya zaka mashi kasan cewa wannan majiyin k'arfi ne saboda yadda yanayin jikinshi ya nuna , gaba daya jikinshi a murd'e yake irin na Jaruman maza , ba k'aramun kyau yakeyi ba acikin *Kakinsu na 'yan sanda* ga wani irin k'warjini da haiba da suke k'ara mashi ,

Lokacin da Hisham ya shigo gidan sanye da kakinshi na *yan sanda* tsaye kawai Momma tayi tana kallonshi ,yayinda idonta suka cicciko da hawayen farinciki , tsawon lokaci kenan bata danya tilon d'anta a idonta ba , saidai tana mamakin irin yadda yak'ara girma da zama cikakken namiji adan k'ank'anin lokaci irin wannan , gaba d'aya takasa wani motsi ganin yadda Hisham ya rikid'e yakoma sak Abbanshi komai da komai musamman da ya saka wannan kakin,

Shima idon ya tsura mata yana murmushi wanda ya k'ara fito da kyaunsa , ganin halin da Momma tashiga ne yasashi k'arasowa da sassarfa ya rungumeta tareda da sauke ajiyar zuciya , itama ajiyar zuciyan tayi tare da saka duka hannayenta ta rungumeshi ta fashe da kuka , don gaba daya takasa rik'e kukanta Hisham ya tuna mata da mijinta tanajin tamkar mijinta ne ya dawo , gefe daya kuma cike take da farinciki Allah ya cikawa mijinta burinshi sannan d'anta yadawo kusa da ita , jan hannunta Hisham yayi sukashiga cikin dakin wanda har lokacin Momma bata daina zubarda hawayen farinciki ba,

"To miye kuma na kuka Momma ? Inace farinciki zakiyi Allah Yasa na dawo gareki kuma da d'umbin nasarori , "

"Doli nayi kuka Hisham narasa mahaifinka kaikuma kayimun nisa , Inna Indo wata biyu kenan da ta koma gida bayan tayi tayi dani akan nabita can gida amma nakasa yin hakan saboda kai , nikad'ai nake rayuwata agidan nan kewa tayimun yawa sosai yanzu kuwa kuka farinciki nakeyi da Allah ya nunamun wannan rana ka gama lafiya , ina rokon Allah da yayi maka jagora akan wannan aiki naka ka kasance mai nasara akan mak'iyanka ,"

"Amin Amin Momma na" yafad'a cike da shagwa'ba , murmushi Momma tayi tana maijin farinciki ,

"Momma nifa yunwa nakeji wallahi don yanzu sam bana jimirin yunwa " yafad'a Yana wani karya wuya,
"To ai laifinka ne shalele da kayi mana zuwan bazata , da ka fad'a ai da yanzu ancika gabanka da kalolin abinci sai wanda ka za'ba, "
"To ai Momma inason inbaki mamaki ne shiyasa , "
"To naji bari naje na samamaka abunda zakaci kafin nan kayi wanka ka huta sai kabani labarin irin nasarar da ka samu ,
"To shikenan Momma Bari naje nayi wanka nazo,"

Wanka yayi ya shirya cikin farar riga da bak'in wando takalminshi ma bakake sai sumar kanshi da ta kwanta luf-luf kamar ya kafa hula tasha gyara sosai sai kyalli takeyi don ba karamin kudi yake kashewa sumarshi ba, in ka gamshi kamar wani Balarabe ko ba'indiye saboda yadda yakeda cikar suma da sil'bi irin ta fulanin asali,
Zamansa babu wuya sai ga Ibrahim ya shigo gidan aguje jin cewar babban Abokinshi ya dawo , aikuwa nan suka rungume juna cike da tsantsar farinciki da kewar juna, nan suka zauna suna firar yaushe gamo ,
"
"Abokina kaga yadda ka koma kuwa sai kace wanda yake rayuwa a cikin k'ank'ara gaba daya yanayinka da komai ya canza , anya kuwa ka maida hankali kayi abunda ya kaika kuwa , yafad'a Yana dariya"

"A'a banyi abunda ya kaini ba dan rainin hankali , kana kallona kasan ba haka na tafiba duk na rame nayi duhu saboda wahala shine zaka wani ce wai nayi kyau "

"Allah abokina bakaga yadda ka koma ga wata irin murdewa da jikinka yayi irin na asalin jaruman maza gaskiya ina tayaka murna don nasan ba k'aramun rububi zakasha ba wajan yan mata yafad'a Yana dariya ,
"Kai mata suka dama" cewar Hisham , suna haka Momma ta fito masu da daddad'an abinci data girkama Hisham sai k'amshi ke tashi , nan suka zauna sukaci suka k'oshi sannan sukaci gaba da fira ,sunjima anan sannan suka yiwa Momma sallam akan zasuje majalisarsu inda abikansu su gaisa ,

A wannan rana daga Hisham har Momma Basu runtsaba kwana sukayi suna firan yaushe gamo yayinda Hisham ya gayamata irin gwagwarmayar da yasha tareda nasarorin da ya damu da kuma irin matsayin da yake a yanzu , sannan nan da sati Daya zai fara zuwa aiki,
Fatan alkhairi sosai tamashi tareda yi mashi nasihohi masu shiga jiki akan duk halin da gaishiga to ya tsare gaskiyarsa ,


*******************


Har wannan lokacin ba abunda ya canza akan muguwar sana'ar da su Alhaji Musa keyi , komai yana tafiyarmasu yadda suke so don ta kowane fanni sunada yaran dake masu aiki, jami'an tsaron dake masu aiki kuwa bazasu k'irguba , shiyasa suke abunda sukeso alokacin da sukeso , duk wanda yayi yunk'urin shiga gabansu kuwa to tabbas zasu kaudashi ko wanene kuwa , ana wannan yanayin ne aka canza D P O Hamza khamis wanda ya kasance yana daya daga cikin wad'an da suke bawa su Alhaji Musa goyon baya akan mugun abunda suke aikatawa , saboda mahaukatan kudin da suke damk'a mashi , wanda shima dasa hannunshi a kisan Jami'i Abdurahaman , wato Abban Hisham ,

Da farko sam basu wani damu ba tunda suna ganin duk wanda za'a kawo shima zasu siyeshi in yaso sai ya d'ora daga inda Sir Hamza ya tsaya , sai dai mi lokacin da aka gabatar da sabon D P O *sir Huzaifa Umar Abdullahi,* sai kallo ya koma sama don sam wannan ba irin wanda suke tunani bane mutum ne tsayayye mai gaskiya da amana uwa uba tsaye yake akan aikinshi sam ko waye kai ka yarda kashiga komarshi tofa sai kasan ka ta'bowa kanka tsuliyar dodo , mutum ne marar tsoro kuma dan kasada ,
Mutum na farko da suka fara tura masa da nufin ya janyo ra'ayinshi alokacin saida ya karya k'afar mutumin sannan yasa aka rufeshi tsawon sati biyu sannan yasa aka sakeshi zuwa lokacin kuwa tuni ฦ™afarsa ta ru'be banda fitar da ruwa mai doyi ba abunda takeyi ,
Wannan al'amari fa ya tsoratasu matuk'a saidai sun sha alwashin sai sunga bayanshi kota halin k'ak'a kamar yadda sukema duk wani k'aramun k'waron da yace zai kawo masu wargi a harkansu,



*********************,,


Kwance yake gala gala duk ya fita hayyacinshi ,ya rame sosai ba komai ajikinshi sai jijiya da k'ashi gaba daya ciyo ya cinyeshi sai kanshi da yayi wani irin k'ato , idan ka kalleshi doli yabaka tausayi ,

Da k'yar muryarshi ke fita , tun d'azu sai faman k'walawa matarshi kira yake Amma tanajinshi tayi biris dashi sai ma faman jan tsaki takeyi irin ya matsa mata dinan,
Hawayene masu zafi suka zobo mashi ,fitsari yakeji tun d'azu amma matarshi Amina tanajin yana kwala mata kira amma tayi masa banza , bayan duk abinda ya sameshi sanadinta ne , don duk abunda yake samu kanta yake k'arewa duk abunda tagani ko bashida halin siya matashi haka zata yi tsaye tace sai ya siyamata , haka zaije duk yadda zaiyi sai yayi don ganin yasamo kudi yayi mata abunda takeso , don Allah ya dora mashi sonta mai tsanani da wannan take amfani tana juyashi son ranta duk abunda yasamu a gindinta dana yan uwanta yake k'arewa amma shine yanzu don Allah ya jarabceshi take wulakantashi yadda taga dama , bata tausayinshi kokadan ,
Gashi kullum ciyon kanshi k'aruwa yakeyi anyi magani har angaji anzubama sarautar Allah ido , don takai yanzu ko abincin da za'aci a gidan wuya yake masu bare wani kudin magani ,

Kusan kullum sai yayi kuka mai yawa idan ya tuna ya gamu da wannan ciyon ne alokacin da yaci amanar abokinsa , tabbas yasan wannan ciyo nashi *Alhakine* sakayya ce kawai Allah yayiwa Abdurahaman tun ba'aje ko'ina ba , gashi nan shi ya huta ya tafiyarshi shikuma yabarshi cikin tarin sark'ak'k'iya da wahalhalu na rayuwa tareda d'umbin nadama marar iyaka , tunda abun yafaru baikoma lafiya ba inda ciyon yafara yawa ne aka sallame shi awaja aiki acewarsu sai yaji sauki ya dawo to maimakon dauki a'a saima abunda yayi gaba ga matarshi gaba daya ta juya mashi baya ,haka yayita kuka mai ban tausayi , yana tausayin kansa sosai amma yasha alwashin. Sai yasa an nemo mashi iyalan Abdurahaman ya fayyace masu komai tareda neman gafarar su...............โœ๐Ÿผ

๐Ÿ˜ฃ๐Ÿ˜ฃ *yau dai abun bawani armashi wallahi yau banajin typing din sam amma kuyi hkr mutara a page na gaba*๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜‰


*SANARWA*๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
*Ina matan da suke fama da butsarin namiji wato namiji marar sakin fuska namiji masifaffe namijin mai wuyar sha'ani , murdadden namiji dakuma namijin dake wulakanta matarshi ko namijin da kikeso amma baya sonki*
*Ko wanda kishiya tasha gabanki sam mijin baya ganinki sai dai kishiyarki to ku garzayo wajen Mmn yusup mai kayan mata domin samun wani taimako wanda ya kasance ingantacce ne wanda ba bokanci acikinshi sai dai tarin taimako ,idan har aka baki wannan taimakon to insha Allah kekam matsarki tazo karshe zaki samu mijinki a tafin hannunki zai kasance baya ganin kowace mace agabanki zai kasance mai tausayi da jin kai a wajanki , zai kasance mai sauraranki da baki* *lokacinshi akoda yaushe zuciyarshi zatayi laushi akanki duk wani zafin kai nashi to zai sauka da izinin Allah , wannan taimakon 3000 ake badashi wadda ta shirya to tamun magana ta pc ko kuma akira numbar kai tsaye , duk wadda takeso zatamun magana ne sai na mata cikakken bayani akan abun don wannan bayanin nayishi ne kawai a tak'aice, don* *Allah in baki shirya ba karkimun magana mu batawa juna lokaci kibari kin shirya sannan*๐Ÿ™Œ๐Ÿป๐Ÿ™Œ๐Ÿป
09035027743 call or Whatsapp mmn yusup sokoto,*


*Karku manta ba tsibbu ko bokanci acin harkarmu Ayar Allah ce kawai*๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ

*Maison taci gaba da samun wanna littafin akan lokaci ga link Nan tayi join Amma don Allah in baki karantawa karkishi inkuma kinsan bakya iyayin comment nanma karkishiga don Allah*
[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ_20


...................wani irin hucin zafi ya fitar daga bakinshi jin furucin Momma , hannu biyu yasa ya damk'i sumar kanshi da k'arfi kamar zai cireta yana fadin "Miyasa miyasa Momma tuni zuciyarshi ta karye durk'ushewa yayi a wajan tareda fashewa da wani irin kuma mai tsuma zuciya da ban tsoro , kuka yakeyi wanda tunda uwarshi ta haifeshi bai ta'ba yin irinshi ba ,baima san yadda akeyin kukan ba don shi tun yana yaro abune mai wuya kaga hawayenshi bare kuma kukanshi ,

Jin sautin kukanshi ba k'aramun dukan zuciyar Momma yayi ba hankali tashe ta zabura ta bude d'akin ta nufi falon ,

Tana zuwa ta iske Ibrahim na lalla'bashi duk ya rikice saboda ganin irin kukan da Abokinshi keyi wanda har ya zarta hankali dukda ba ihu da kururuwa yake hawayene kawai sai sheshekar da yakeyi wanda takeyi kamar zata tafi da numfashin shi ,

Cikin sanyin jiki ta k'arasa kusa dashi ta sanya hannunta cikin nashi ,d'ayan kuma ta rink'a shafa kanshi dashi a hankali,
Jikinshi yayi zafi sosai hakama kanshi kamar garwashi , haka yake tun yana yaro in ranshi ya 'baci tuni zazzafan zazzaษ“i zai rufeshi ,
Yadda Momma ke mashi yasa a hankali jikinshi yafara rage tawar da yakeyi ya fara samun nutsuwa yayinda zafin zuciyarshi ke raguwa a hankali ,ajiyar zuciya kawai yake saukewa , ganin hakan yasa Momma tafara mashi nasiha mai ratsa zuciya , saida ta kwashe sama da 30mnt tana mashi nasiha da kawo mashi hujjojinta na hanashi abunda yakeson aikatawa ,
Har lokacin baice komai ba sai zamewa

Please Login or Register in order to submit comment