Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai iya gigita tunanin goga,

DA sauri ya fitar da wayarshi ya kira alhaji manu , a hankali ya Fara magana ,
"Maigida akwai matsala fa , yanzu haka inspector Abdurahaman ya shiga wajan da aka kulle goga ana gana mashi azaba ,yakamata kayi wani abu don in har yajima aciki to komai zai iya faruwa , "

Daga can 'bangaren da sauri alhaji manu ya mik'e tsaye batare da yace komai ba ya tsinke wayar da sauri , sannan yafara kiran wata numbar ,
Daga can 'bangaren aka dauka tare da cewa "hello"
Hello sir yakamata kayi wani abu yanzu akace wannan mayen nacan ya tsare goga da tambayoyi,

"What? Okay zan san abunyi yanzu , aka fad'a daga d'ayan 'bangaren sannan ya kashe wayar ,kiran inspector Haruna yayi sunjima suna magana kamun sukayi sallama ,

*****

Tsaye yake ya tsare Goga da manyan Idanunshi masu rikita marasa gaskiya , kallo daya Goga yayi mashi jikinshi yafara rawa saboda tsabar k'warjinin da allah yayi mashi , sun jima suna kallon kallo a tsakaninsu kamun a hankali Goga ya sadda k'anshi k'asa don sam yakasa jurar kallon shi zuciyarshi sai d'al-d'al takeyi ,

Takowa yafarayi a hankali ya nufi inda aka daure Goga yayinda duk wani taku da zaiyi daidai yake da bugawar zuciyar Goga , yana zuwa kusa dashi ya tsugunna dai dai wajan kanshi dake lilo yasa hannunshi da damk'i sumar kanshi ,hakan yayi daidai da kiran wayarshi da akayi , ganin wanda yake kan layin ne yasa ya mik'e da sauri tareda k'ara saita kanshi sannan ya dauki wayar,
"Hello sir " ya fad'a , bansan abunda aka ce mashi ba sai k'amewa yayi tareda cewa "okay sir " juyawa yayi da sauri ya fita daga wajan , barin office d'in yayi gaba d'aya ya dauki motarshi yabar station d'in,

Ajiyar zuciya Goga yayi cike da jin dad'in tafiyar gayen nan (kamar yadda suke fada mashi) yayi imani wannan aikin oganshi ne don haka duk da yanashan matuk'ar wahala to zai k'ara dagewa don yasan bazasu ta'ba barinshi a hannun police ba doli zasu fitar dashi,


Sai misalin k'arfe 11pm ya kamo hanyar gida ................✍🏼

*kuyi hkr banso na tsaya anan ba amma aiki yahana nayi maku da yawa amma insha Allah Gobe zanyi maku*



*KWANCIYAR SAMUN CIKI*



🅰️kusan kowanne namiji lokacinda yayi inzali yana fitarda kwayoyon halitta sama da 1,000,000 saidai yayinda allah ya kudira za'a samu ciki dayane ke shiga mahaifa don zama dan adam amma duka sauran zuba yakeyi,






🅰️kwai yanayin kwanciya kuma wanda lokacinda na miji yayi inzali baya shiga mahaifa harma wasu suna daukan hakan amatsayin tazarar iyali wato mace ta hau kan namiji yayinda yake kwance wannan lokacin maniyi yakan dawo amma wannan be ingantaba don ana samun kuskure,






🅰️kusan kashi tamanin cikin dari (80%) na mata nan take maniyi ki zuba daga jikinsu koda kuwa wacce irin kwanciya akayi da zaran namiji yayi inzali to zataga maniyin yana zuba wasu kuma matan sai daga baya wannan kuma baya hana mace samun ciki domin lokacinda allah ya hukunta samun cikin to kwayar halittar zata shiga,







🅰️mma fa wasu daga cikin mata namiji yakanyi inzali amma babu wani abu dake zuba wajenda ta tashi kamar babu abinda akayi wannan yana zubane lokacin fitsari saidai kalilan ne daga cikin mata masu wannan baiwar,



kankantar gaba bayada nasaba da rashin samun ciki domin masana sun tabbatar indai gaban namiji zai shiga da 2 inch tana iya samun ciki koda kuwa bata gamsuwa dashi saidai idan ya gaza haka ne to wannan baya cikin maza masu al'aura bazaiyu mace ta samu ciki ta dalilin saduwa dashi ba,






🅰️n tabbatar mace ko namiji akwai mataki da ciwon sanyi zaikai inda zai hana samun ciki, kamar ita mace zai hana maniyin namiji shiga mahaifarta, yayinda shi kuma namiji maniyinsa zai tsinke sosai ya zama kamar ruwan famfo har ma kwayoyin halittarsa su mutu bazaiyi ya bawa mace cikiba,

*Muhadu a gobe insha Allah*🥰
[6/12, 8:20 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻‍🔧

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*👇🏻
*Jami'in d'an sanda*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍



🅿️_13


..................zaune ya tadda Momma akan darduma tana karatun Alkur'ani , da sallama yak'arasa shiga falon fuskarshi dauke da murmushi , saida takai aya sannan ta d'ago da kanta cikin yanayin fara'a ta amsa sallamar tashi tareda yi mashi Barka da zuwa ,

Amsawa yayi yayinda yake zama kan kujera , tashi tayi taje ta ajiye Alkur'anin acikin wata loka sannan ta dawo inda yake , duk'awa tayi a hankali tafara cire mashi takalmin k'afarshi tare da safa ta ajiye gefe sannan ta gyara zamanta tafara matsa mashi kafafun ,lumshe idonshi yayi a hankali lokaci daya yaji duk wata damuwarshi ta yaye duk zafin da kanshi ya dauka wajan aiki sai gashi a hankali yanajin kamar bashiba ,

A hankali ya furta " miyasa har yanzu bakiyi bacciba , ba nace ki daina tsayawa jirana har wani lokaci baki kwanta ba bayan kinsan cewa kinada buk'ar hutu sosai ,"

"Hmmm kai ma dai Abban shalele kasan cewa bazan iya kwanci ba tare da naga dawowarka cikin gidan nan ba koda kuwa zaka kai karfe biyu na dare , sai dai idan na tabbatar da bazaka dawoba kana aikin dare wannan ne kawai zaisa na kwanta amma in dai nasan zaka dawo to kuwa doline in jiraka ko karfe nawa zaka kai,

Murmushi Abba yayi yanajin wani son matarshi na K'ara ratsa jijiyoyin jikinshi saboda irin yadda take tsananin bashi kulawa kamar wani yaron goye , duk da shekaru sunja har gashi sun ajiye saurayi amma sam hakan baisa ta daina bashi kulawa kamar yadda tasaba ba kullum zaka samesu cikin farinciki kowanensu kokari yakeyi yaga ya farantawa d'an uwansa , rik'o hannunta yayi yace zo muje kiji wata magana ,
Murmushi kawai tayi ta kama hannunshi ta mike suka nufi bedroom din Abba ,

Ba k'aramun faranta ran junansu sukayiba a wannan dare wanda bazai taba gogemasu ba acikin kundin tarihin rayuwarsu , darene da suka faranta ran juna kamar zasu had'iye juna , sunajin wani irin farin ciki kamar wasu sababbin aure , har karfe 2:30am idonsu biyu sai daga bayane suka tsarkake jikinsu sannan suka fara sallar nafilfili , sai da sukayi sallar asuba sannan suka kwanta bacci ,aikuwa bacci mai nauyi ne yayi awon gaba dasu , da yake weekend ne shiyasa suka shari baccinsu hankali kwance ,

Misalin k'arfe 9am yunwa ta fito da Hisham daga dakinshi don dama shikam sam baya wasa da cikinshi , direct dinning ya nufa , amma mi sai ganin table din yayi wayam ba komai akai , d'an 'bata fuska yayi don Allah yagani matsananciyar yunwa yakeji, turo dan bakinshi yayi gaba kamar wani k'aramun yaro yafara k'unk'uni yana cewa
"Oh wai tsoffi ma sun iya soyayya dubi har yanzu wai Momma bata dora girki ba ko sai yaushe zamu karya yau? Yayi maganar Yana rik'e ha'ba , "

"In kaji haushi kaima sai kayi auren ai "

Yaji an fad'a a bayansa , juyowa yayi yana d'an sosa kanshi yace "Barka da safiya Abba an tashi lafiya"
"Lafiya qalau son an Gama tsegumin mu ?"
Dariya Hisham yayi yace to ai Abba.... bari dai kawai yafad'a Yana dariya "

"Shak'iyin yaro ai da ka fad'a kawai tunda ka mayar damu wasu sa'anninka , yanzu dai maza ka shiga kitchen ka sama mana abunda zamuci don Maryam tana bacci kuma baza'a tasheta ba sai ta tashi da kanta"

Turo baki Hisham yayi kamar zaiyi magana sai kuma yafasa ya tashi ya nufi kitchen din Yana Dan babbuga k'afa k'asa K'amar wani k'aramun yaro,
Da kallo kawai Abba ya bishi yana murmushi , tsakanin Maryam da Hisham baisan wayafi so ba yana masu wata irin soyayya mai matukar zafi , don a halin yanzu bashida wanda ya kaisu sune duniyar shi yana fatan Allah ya tsare mashi su ya kauda idon mak'iya daga kansu don ya sani sosai ake bibiyar rayuwarshi kawai Allah ne bai basu Sa'a akanshi ba har yau ,

Hisham kuwa sai mita yakeyi a kitchen don yunwa yakeji sosai cikinshi sai k'ugii yakeyi, dankali ya soya da k'wai ya dafa ruwan zafi ,sannan ya dauko sauran farfesun da Momma tayi masu jiya da dare ya d'umama sannan ya kwaso kayan ya kawo kan table Hisham ya iya kalolin abinci sosai kasan cewar duk lokacin da Momma zatayi aikin tare dashi takeyi yana tayata , tun yana k'araminshi har kawo yau indai yana gida to zaka sameshi tareda Momma yana tayata aiki , wani lokaci ma har shara da wanke wanke shi yakeyi kamar wani mace
,har wannan lokacin Abba yana zaune Yana duba jarida ,
Juyowa yayi da sauri jin yadda k'amshin abincin ya bugi hancinshi , dama shima yunwar ce ta tayar dashi daga bacci , murmushi yayi yace "sannu da aiki Son Bari na taso na cika cikina ,"

Dariya Hisham yayi yace " Abba bazaka jira Momma ba yau kai kadai zakaci abincin ne,"

"Babu ruwanka d'an sa ido " cewar Abban lokacin da yake zama kan kujerar , dariya kawai Hisham yayi baice komai ba yafara zuzzuba masu dankalin da wainar kwai tayi kyau har tagaji sai kamshi ke tashi, sannan ya haɗa masu tea suka fara karyawa , sunaci suna dan ta'ba fira da wasa da dariya in ka gansu sai ka dauka abokai ne ,

"Sannunku wato kuna nan kuna karyawa kun manta dani ko" cewar Momma da tun dazu take tsaye tana kallonsu cike da so da kauna tana alfahari da mijinta dakuma d'anta kallonsu kawai yana sanyata cikin farinciki ,

Da sauri duk suka kalli inda take , taci kwalliya sosai tayi d'as abunta kai bazakace ta ajiye kamar Hisham ba , tashi Hisham yayi ya riko hannunta yana cewa "zo muje Momma ki karya Abba ne yace wai mu k'yaleki muci abunmu,"
hararshi tayi bata ce komai dagashi har Abban dariya sukayi mata , gaida Abban tayi sannan Hisham ya gaisheta daga nan ya hada mata nata abincin tafara ci , haka suka gama cin abincin suka koma kan kujerun falon suka zauna sunata fira cike da annashuwa , haka suke ko yaushe kowaye yazo gidan sai wannan family ya burgeshi saboda yadda suke matukar bawa junansu kulawa kullum zaka samesu cikin farinciki da wasa da dariya,

Kallon Hisham Abba yayi yace Son anfara siyar da form na *aikin dan sanda* har na siya maka ma na mantashi a office Amma gobe zanzo dashi sai ka cike ko? Yayi maganar Yana kafeshi da ido,

Tunda yafara maganar banda kallon Abban ba abunda yakeyi acikin zuciyarshi kuwa mamakin dalilin Abba na kafewa sai ya gajeshi da aikin *dan sanda* yakeyi ,miye acikin aikin inbanda wahala kullum sukenan basu nan basu nan wajan kama tantiran masu laifi duk don su samu k'asarsu ta gyaru kamar sauran k'asashe amma abun yana tashi a banza ,duk girman laifin da mutum zai aikata ga hujja da kwararan shaidu kiri kiri amma hakan bazai hana manyan mu shige da fice don ganin an saki wannan mai laifin ba saboda duk wani babban laifi da ake aikatawa mafi yawa zaka samu da hannun manyanmu aciki , haka kwanaki kiri kiri a unguwar su aka kama wani matashin saurayi da yara sama da biyar ya sacesu yana shirin hallakasu aka kamashi amma abun takaici ko sati baiyi ba aka rufe case din aka sakeshi, to in irin haka na faruwa tun farko miye amfanin kamashi kenan taya za'a samu wani cigaba ,in hakane miye amfanin aikin ma gaba daya ,shi wannan abun naci mashi rai sosai ba komai yasa yake k'in aikin *dan sanda* ba saidon wallahi in ya shigeshi abubuwan da zasu faru ba masu kyau bane don duk wanda ya kama da aikata babban laifi irin na kisa ko fyade bare kuma satar yara wlh zai iya kashe mutum komai za'ayi sai dai ayi , wannan dalilin ne yasa yak'i yarda ya karbi tayin Abba don bafa zai iya dagawa kowa k'afa ba , yayi zurfi acikin tunanin da yakeyi gaba daya idonshi sun kada sunyi jajir ga jijiyoyin kanshi duk sun tashi sunyi rida rida gaba daya fuskarshi ta sauya tayi jajir alamar ranshi ya ɓaci matuk'a, gefe daya Kuma wani irin tausayin Abbanshi ne ya kamashi , ya tsaya kai da fata yana aiki bisa gaskiya da amana duk da burin samun cigaba ga k'asarsu amma kullum abun k'ara ta'bar'barewa yake ,

Hisham yanada hakuri da fara'a uwa uba wasa da dariya to ammafa yanada matukar fushi idan ranshi ya ɓaci komai zai iya aikatawa , shiyasa yake dannar zuciyarshi ba kasafai yafaye bari wani abu ya bata ransa ba,

Gaba daya iyayen kallonshi sukeyi suna ganin yanayinshi sun san ran yan maza ya 'baci shiyasa ba wanda ya sake mashi wata magana ,

A hankali ya tashi baice komai ba yabar falon dama gidan baki daya,

Ajiyar zuciya suka sauke a tare , cikin sanyin jiki Momma tace " wai Yaya miyasa kakeson sai yaron nan yayi aikin nan na police miyasa bazaka rabu dashi yayi abunda yakeso ba , Ni banga abunda yake cikin aikin ba wanda har zakayi ma danka sha'awar shiga ciki banda tashin hankali miye aciki , Ni wallahi ko kai da zaka taimakeni da ka ajiye aikin nan , "

Murmushi kawai Abba yayi yace " to shikenan uwar gida daga yau bazan sake yiwa danki wannan maganar ba tunda naga kamar kinfi sonshi dani"

Dariya tayi tace "daka kyautamun kuwa Ni da zaka taimaka ma da har kai ka ajiye aikin da zanyi farinciki marar misaltuwa,

"Hmmm bazaki gane ba Maryam kanki kawai kika sani shiyasa amma idan har jami'ai masu gaskiya sukace su ajiye aikinsu saboda tsoron abunda zaije yazo to ta Ina kk tunanin zamu samu ci gaba , ai daga lokacin kasarmu zata kara shiga rudu da tashin hankali kowa zaiyi abunda yakeso tunda babu wanda ,zai taka masu birki , amma idan har muka jajirce sai kiga zuwa gaba komai yazama tarihi mun koma kamar sauran k'asashen da sukaci gaba wanda akullum haka muke fata , "

To shikenan Abban shalele Allah ya dafa maku ya shige maku gaba ya tsare ku daga dukkan sharri na mutum da aljan , "

Ameen my dear haka nakeson ji , yanzu zan dan fita zanje office ne akwai inda zamuje da inspector Haruna tun jiya yake damuna amma bazamu jimaba zamu dawo insha Allah,

"To shikenan.allah ya tsare ya dawo dakai lafiya , "
"Amin amin ya Allah ki lallasarmun dan lelen naki kamun na dawo nasan yayi fushi Dani sosai ,

"Ba ruwana wannan tsakaninku ne ta fada tana dariya"

Har ya kai bakin kofar sai kuma ya dawo janyota yayi jikinshi ya sumbaci goshinta kamun yamata wani irin kallo sannan ya daga mata hannu yasakai ya fita ,

Tajima tsaye a wajan kamun tayi murmushi ta koma cikin falon direct kitchen ta nufara tafara kokarin hada masu abincin rana,


***********************


Sama da minti 30 suka shafe suna tafiya akan titin , yayinda inspector Haruna ke tukin motar Abba kuma na gefenshi yana karanta jarida , a hankali ya ajiye jaridar ya d'ago da kanshi ya dubi inspector Haruna yace " wai Haruna ina muka nufa ne , Ni nakasa gane inda zancanka ya dosa , shi wanda kace ya kiraka d'in akan muzo zai bamu wani sirrin kana da tabbacin ba tarko ya had'a mana ba , in har yanada gaskiya mi zai hana ya samemu a office a maimakon yace mu muje musameshi , "

"Ai ranka ya dade ya gayamun cewa bayason yaje ofishinmu ne saboda duk wani motsinshi ana sane komai zai iya faruwa dashi idan har akasan cewa yabada wata masaniya akan su Alhaji Musa, wannan yasa nace to ya bari mu zamuzo wajanshi sai muyi magana,

Wani banbarakwai Abba yaji zancan don gaba daya baiji ya gamsu da bayanin Haruna ba , d'an musk'utawa yayi yace "koma dai minene banajin akwai alkhairi a tafiyar nan ,ina ji ajikina kamar wani tarko ne kawai , "

Jin hakan yasa gaban Haruna faduwa da kyar yasamu ya daidaita nutsuwarshi gudun karya ganoshi , yasan waye Abdurahaman mutum ne mai saurin fahimtar abu ko yaya kake da rashin gaskiya to zai iya ganoka ,

"Cikin inda inda yace to ranka ya dade ko mu juya ne ? tunda kanajin tsoro"

"Ba tsoro nakeji ba jikina ne yake bani babu alkhairi a tafiyar nan amma muje Allah ya shige mana gaba, "

Ajiyar zuciya Haruna ya sauke don yaji tsoron kar yace su koma ,

Shiru ba wanda yakoma magana acikinsu har wani tsawon lokaci , har suka zo inda suka shirya kulla-kullarsu ,

Suna zuwa daidai wajan wani waje mai tudu da rafi waje ne da gefe da gefen titin suke da gangara sosai suna zuwa dai dai wani icce wanda dama dashi sukayi alama ba zato ba tsammani sai gani Abba yayi inspector Haruna na kokarin bude murfin motar bayan kuma ga motar tana gudu , kamun ya bude baki yayi magana har Haruna ya bude gambun motar yafad'a waje aikuwa kamun kace mi yafara gangara lokaci d'aya ya haɗawa kanshi jini da majina kamun ya bugi wani katon dutse dake wajan lokaci daya ya some a wajan,

Abba kuwa ganin fitar Haruna ba k'aramin daga mashi hankali yayi ba ga motar na gudu cikin tsananin zafin nama yayi wata sufa sai gashi a kujerar mai tuk'i duk a kokarinshi na ganin ya tsayar da motar , kamun yayi hakan kuwa tuni wata k'atuwar mota ta nufoshi gadan gadan bai ankaraba sai ganinta yayi ta nufoshi aguje , ganin tana daf da k'arasowar wajanshi ne yasa ya runtse idanunshi da sauri tareda ambatar *La'ilaha illallah muhammadun Rasulullah* kamun k'yaftawa ido wasu hawaye Masu zafi da k'una sun wanke mashi fuska , duk da yana cikin wannan bala'in saida ya hango fuskar tilon danshi dakuma salihar matarshi , aikuwa kamun yagama dawowa duniyar da ya tafi tuni motar nan tabi ta kanshi ta take sannan direban ya dawo ya bugi motar da k'arfi tuni itama motar ta fara gangarawa gefen titin .........................✍🏼



*Sanarwa sanarwa sanarwa*

*Daga yau littafin jami'in dan sanda yakoma na kud'i saboda rashin comment dinku sam bana samun kwarin gwuiwa akan book din nan bansani ba ko salon labarin ne baimaku ba to zan sani a yanzu in har Kuna tare da wannan littafi ga mai bukata zata iya neman ta wannan numbar 09035027743*

Kudin littafin 200 ne kacan 🤝🏼




*SIRRIN WANKIN MARAH*👩🏻‍🦰👩🏻‍🦰



🅱️abbar hanyar samarda ni,ima ta hanyar aiki da abincin gargajiya na gida, wanda shidai wannan tsumin asalinsa wanke mara yake musamman mata wadanda ni,ima ke basu matsala ta sanadin toshewar mara, wanda zakaga mace tasha tsumi, da garin ni,ima masu kyau amma ta kasa ganin ni,ima da wuri, to ackin hanyoyinda akebi don samarda ni,ima harda wanan hanyar wanda ta inganta koda mace tanada ciki zata iya amfani dasu, anaso asha sau biyu wato safe da yamma, a wuni daya,









🅱️abban abunda zaki fara shine ki wanke aya sannan saiki jika sai kuma kisamu gyada danya, saiki zuba musu ruwa kadan wanda adadinsa be wuce lita dayaba, daga nan saiki gurza kwakwa aciki, ki saka kanunfari kadan, saiki yanka lemon tsami daya sannan ki bari su jika saiki markada, sannan ki tace, acikin ruwan zaki jefa mazar kwaila koda dayane wato rabin kifi amma babba, shikenan ki jira dan wani lokaci tana jika kin kammala.









👨🏻‍🔧 *JAMI'IN 'DAN SANDA*. 👨🏻‍🔧

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*👇🏻
*Jami'in d'an sanda*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*😍😍



🅿️_13


..................zaune ya tadda Momma akan darduma tana karatun Alkur'ani , da sallama yak'arasa shiga falon fuskarshi dauke da murmushi , saida takai aya sannan ta d'ago da kanta cikin yanayin fara'a ta amsa sallamar tashi tareda yi mashi Barka da zuwa ,

Amsawa yayi yayinda yake zama kan kujera , tashi tayi taje ta ajiye Alkur'anin acikin wata loka sannan ta dawo inda yake , duk'awa tayi a hankali tafara cire mashi takalmin k'afarshi tare da safa ta ajiye gefe sannan ta gyara zamanta tafara matsa mashi kafafun ,lumshe idonshi yayi a hankali lokaci daya yaji duk wata damuwarshi ta yaye duk zafin da kanshi ya dauka wajan aiki sai gashi a hankali yanajin kamar bashiba ,

A hankali ya furta " miyasa har yanzu bakiyi bacciba , ba nace ki daina tsayawa jirana har wani lokaci baki kwanta ba bayan kinsan cewa kinada buk'ar hutu sosai ,"

"Hmmm kai ma dai Abban shalele kasan cewa bazan iya kwanci ba tare da naga dawowarka cikin gidan nan ba koda kuwa zaka kai karfe biyu na dare , sai dai idan na tabbatar da bazaka dawoba kana aikin dare wannan ne kawai zaisa na kwanta amma in dai nasan zaka dawo to kuwa doline in jiraka ko karfe nawa zaka kai,

Murmushi Abba yayi yanajin wani son matarshi na K'ara ratsa jijiyoyin jikinshi saboda irin yadda take tsananin bashi kulawa kamar wani yaron goye , duk da shekaru sunja har gashi sun ajiye saurayi amma sam hakan baisa ta daina bashi kulawa kamar yadda tasaba ba kullum zaka samesu cikin farinciki kowanensu kokari yakeyi yaga ya farantawa d'an uwansa , rik'o hannunta yayi yace zo muje kiji wata magana ,
Murmushi kawai tayi ta kama hannunshi ta mike suka nufi bedroom din Abba ,

Ba k'aramun faranta ran junansu sukayiba a wannan dare wanda bazai taba gogemasu ba acikin kundin tarihin rayuwarsu , darene da suka faranta ran juna kamar zasu had'iye juna , sunajin wani irin farin ciki kamar wasu sababbin aure , har karfe 2:30am idonsu biyu sai daga bayane suka tsarkake jikinsu sannan suka fara sallar nafilfili , sai da sukayi sallar asuba sannan suka kwanta bacci ,aikuwa bacci mai nauyi ne yayi awon gaba dasu , da yake weekend ne shiyasa suka shari baccinsu hankali kwance ,

Misalin k'arfe 9am yunwa ta fito da Hisham daga dakinshi don dama shikam sam baya wasa da cikinshi , direct dinning ya nufa , amma mi sai ganin table din yayi wayam ba komai akai , d'an 'bata fuska yayi don Allah yagani matsananciyar yunwa yakeji, turo dan bakinshi yayi gaba kamar wani k'aramun yaro yafara k'unk'uni yana cewa
"Oh wai tsoffi ma sun iya soyayya dubi har yanzu wai Momma bata dora girki ba ko sai yaushe zamu karya yau? Yayi maganar Yana rik'e ha'ba , "

"In kaji haushi kaima sai kayi auren ai "

Yaji an fad'a a bayansa , juyowa yayi yana d'an sosa kanshi yace "Barka da safiya Abba an tashi lafiya"
"Lafiya qalau son an Gama tsegumin mu ?"
Dariya Hisham yayi yace to ai Abba.... bari dai kawai yafad'a Yana dariya "

"Shak'iyin yaro ai da ka fad'a kawai tunda ka mayar damu wasu sa'anninka , yanzu dai maza ka shiga kitchen ka sama mana abunda zamuci don Maryam tana bacci kuma baza'a tasheta ba sai ta tashi da kanta"

Turo baki Hisham yayi kamar zaiyi magana sai kuma yafasa ya tashi ya nufi kitchen din Yana Dan babbuga k'afa k'asa K'amar wani k'aramun yaro,
Da kallo kawai Abba ya bishi yana murmushi , tsakanin Maryam da Hisham baisan wayafi so ba yana masu wata irin soyayya mai matukar zafi , don a halin yanzu bashida wanda ya kaisu sune duniyar shi yana fatan Allah ya tsare mashi su ya kauda idon mak'iya daga kansu don ya sani sosai ake bibiyar rayuwarshi kawai Allah ne bai basu Sa'a akanshi ba har yau ,

Hisham kuwa sai mita yakeyi a kitchen don yunwa yakeji sosai cikinshi sai k'ugii yakeyi, dankali ya soya da k'wai ya dafa ruwan zafi ,sannan ya dauko sauran farfesun da Momma tayi masu jiya da dare ya d'umama sannan ya kwaso kayan ya kawo kan table Hisham ya iya kalolin abinci sosai kasan cewar duk lokacin da Momma zatayi aikin tare dashi takeyi yana tayata , tun

Please Login or Register in order to submit comment