Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, shi zai ganosu duk inda suke a garin nan yasan aikinshj fiye da tunaninka sannan yana aikishi ne bisa gaskiya da amana uwa uba *Kishin k'asa* Wanda ba kowa keda wannan ba kai dai kuje Ku kai report a hannunshi kuma karku kuskura Ku sanar da wani daga cikin police din dake hukumarsu har sai kun Ganshi da kanku sannnan Ku sanar dashi inba haka ba komai zai iya faruwa don mafi yawansu masu kudi suke yiwa aiki karshenta in baka iya kama barawo ba shi yakamaka , "

Gyaran murya d'ayan mutumin yayi Wanda k'ani ne ga mahaifin safiya , yace , mun gode sosai likita tabbas zamuyi amfani da shawararka don inhar ba 'a kamo azzaluman nan ba aka hukuntasu to bazamu ta'ba jin dadi ba doli su fuskanci hukunci daidai da abunda suka aikata ,ni dama banida niyar k'yalewa wallahi sai inda k'arfina ya k'are , nan dai likitan yaci gaba da yi masu bayanin yadda zasu tunkari Hisham da kwatancen inda zasu sameshi cikin sauki ,



___________________________

"Ke wai mi yake damunki ne yarinya kamar mai aljanu , inace da kanki kika dameni akan ba Wanda kikeso sai Hisham ,d'azu ma kamar zaki take kan jariri saboda zumudin zuwansa , shine yanzu zaki wani ce ba kya sonsa , shin shi baice bayasonki ba sai kece zakice bakya sonshi ,to ubanwa kikeso ,wallahi ki dawo hankalinki tun kamun damarki ta kufce maki , don bana tunanin zaki samu mijin da ya kama ko kafar Hisham ne , sha sha sha kawai wadda batada nutsuwa to aure anyi angama bkisani tun da shi yanasonki kuma uwarshi ma tana son..........kuka mai k'arfi Samra ta fashe dashi tana cewa nashiga ukku don Allah momi karku auramun shi wallahi kasheni zaiyi........................✍🏻


*Kuyi hakurin rashin jina kwana biyu yarana suka kwanta asibiti amma alhamdulillah sunji sauki har anbasu sallama saikuma muka shiga bikin yayana shiyasa kukaji shiru*


*AKWAI INGANTATTUN KUMA ZAFAFAN KAYAN MATA NA YAR MUTAN SOKOTO BA ABUNDA BAMUDASHI NA GYARAN AURE KEDAI GARZAYO KAR AYI BABUKE AJIYATA ,

MASU BUKATAR SIRRIKAN MALLAKA MUSAMMAN MASU MAZA MASU MURDADDEN HALI KU GARZAYO ZAKUSHA MAMAKIN YADDA ZAKU DAWO KUNA JUYA ZUCIYAR MIJINKU
MATAN DA SUKE CEWA VASA SAMUN ALKHAIRIN MAZAJENSU KU GARZAYO 💃🏻

*Gareku yan Niger duk maison kayan yar Niger ta yi magana muna aikawa ta hanya mai sauki adukkan garuruwan dake Niger don Neman Karin bayani 07069711327 mmn Yusuf Dr mata*
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍✈️ *JAMI'IN DAN SANDA*👨🏻‍✈️

*_MALLAKAR_*

~MARYAM UMAR ABDULLAHI~
( _MMN YUSUF_)
*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*


🅿️_29

.......…..............."Helloo " tasake cewa jin shirun yayi yawa ne yasa ta yin tsaki tana niyar kashe wayar a hankali cikin jarumar muryarshi yace " karki kashemun waya, " cikin mamakin Mai maganar ta d'ago wayar tasake kallon number tabbas batasan number ba Amma Kuma kamar taso ta gane Mai muryar , maida wayar tayi a kunnenta cikin hasala gundura Mai nuni da an takura mata tace " waye Kai ne miye dalilinka na kirana ?"
Lumshe idanunshi yayi Don lokaci daya muryarta ta hargitsa mashi lissafi , cikin wata kasalalliyar murya yace wanne kikeson kisani acikin biyun , waye ni ko kuma dalilin kiranki ,? A hasale tace "duka biyu nakeson sani"
Murmushi yayi Mai sanyi yace "to mijinki ne uban 'ya'yanki , dalilin kiranki Kuma ni kaina bansani ba Amma kiyi tunani Kila Zaki gano Mana dalilin Kiran, " tsaki laurat tayi cikin jin haushi ta katse Kiran , tana kananun maganganu kamun taci gaba da tunanin da takeyi , ba'ajima ba taji shigowar sak'o a wayarta , tana dubawa taga number d'azu ce kamar bazata duba ba saikuma ta bude sak'on , gani tayi anrubuta *_ba'ayimun tsaki ki kiyaye wannan sannan kishirya tarban mijinki gobe zan iya zuwa kowane lokaci_* tsakin tasake tare da yin cilli da wayar tana fadin aikin banza kawai, nan ta tashi ta nufi falo jin yadda Ammi ke kwala mata kira,

'bangaren Hisham kuwa cike da farincikin jin muryarta yayi bacci Mai cike da mafarkanta gefe daya Kuma cike da tunanin yadda zaikama tantiran nan cikin sauki da hukuntasu daidai da laifinsu
_____________________________

Washe gari

Tun safe laurat ta shirya ta nufi asibiti ko gaisawa da iyayenta Bata tsaya yi ba gudun haduwarta da Abbansu haka ta tafi ko karyawa batayiba ,Zee sai dariya take mata da tsokanarta , Bata tsaya biye mata ba tayi tafiyarta , lokacin da iyayensu suka sauko don yin breakfast Zee kawai suka iske a falon , har k'asa ta duka ta gaishe da iyayen nata cikin fara'a suke amsamata kamun Mami tace Ina laurat ne ko Bata tashiba ,"aa mami ta tashi harma ta wuce hospital,
"Har ta fita fa kikace , shine bazata tsaya mu gaisa ba kamun ta tafi,"
"Taya zata tsaya bayan Kuma mune take yiwa gudun ai zata dawo ta sameni ne, cewar Abba, " Zee cikin danne dariyarta tace "aa Abba Kiran gaggawa akayi mata ne shiyasa , " jinjina kanshi kawai yayi tareda cewa "Allah ya dawo da ita lafiya, zee da Mami suka amsa da Amin,

____________________________
Zaune yake a office dinshi aiki yakeyi sosai yau tun safe Bai huta ba har gashi karfe 4:pm wayarshi ya dauka ya dannawa wata lamba Kira , ba'a jimaba aka dauka tareda cewa "Barka da rana sir ,"ba tare da.ya tsaya amsa gaisuwarta ba yace
"Asmey ya akayi fatan komai na tafiya yadda muka tsara, "cikin ladabi irin na oga da yaronshj ta amsa da cewa " eh sir komai na tafiya daidai yanzu haka suna gidan gonar Mataimakin gwamna Alhaji saminu, "ok aikinki na kyau kici gaba da bin diddiginsu zuwa 5pm zamuzo " cikin Sara mashi kamar Yana ganinta tace okay sir , kashe wayar yayi yafara Kiran number Jafar,

K'arfe biyar a wajen gidan gonar Daddyn zayyan tayi masu , nan suka Danna kansu cikin gidan kansu tsaye , da sauri Mai gadi ya taso Yana tambayarsu mi sukeso wa.suke nema, batareda Hisham yayi magana magana ba ya zagayeshi ya nufi ainahin k'ofar gidan gadan gadan, da sauri maigadin ya yunk'ura zaisha gabanshi Amma mi saiji yayi an rik'e shi ta baya , juyowa yayi zaiyi magana inspector Jafar ya tareshi da cewa *kana tare da Mataimakin commissioner yan sanda* don haka kashiga hankalinka, wani yawu Mai kauri maigadin ya had'iye take jikinshi yafara rawa don mutum ne Mai bala'in tsoron yan sanda , batare da sunbi ta kanshiba suka marawa Hisham baya ,

Zaune suke a babban falon gidan sun baje kayan shaye shaye kala kala akan table Zayyan ne sai abokanshi su biyu sai budurwarshi sury ,sauran abokan shakiyancin nashi basa nan , ba zato sukaga an turo k'ofar falon da k'arfi , a fusace Zayyan ya d'ago kanshi a tunaninshi wani daga cikin ma'aikatan gidan ne ya shigo masu,
Saidai ganin *Jami'an 'yan sanda* yasa shi maida maganar da yayi niyar yi sai wani mugun kallo da yake auna masu na mi kukazo yi don Sam ba alamar razana a fuskarshi , hakama abokanshi kasancewarsu 'ya'yan manya sun San ba abunda 'yan sanda suka isa suyi masu ,saidai sury ta razana sosai don ita Sam babu sanin iyayenta aduk iskacin da takeyi Kuma tana mugun tsoron Daddynta don mutum ne Mai zafi sosai ,

Kallon kallon sukeyi tsakaninsu da su Hisham Wanda tuni zuciyarshi ta kawo mashi iya wuya ganin Dan iskan kallon da suke jifansu dashi Sam ba alamar razana a fuskokinsu, da hannu kawai yayiwa sauran alama da su kamasu , don in yaci gaba da tsayuwa haka agabansu komai zai iya faruwa tsabar tsanarsu da yakeji,
Da sauri yan sandan suka nufesu da nufin kamasu , ko motsi basuyiba sun zubama yan sandan nan ido cike da izgili , sai sury ce tayi yunk'urin guduwa ,Hisham har ya d'aga k'afarshi da niyar barin d'akin , kamar daga sama yaji muryar Zayyan cikin izgilanci da nuna isa da tak'amar shi wani ne yace " Kai d'an gidan uban waye da zakazo har nan ka kama Dan gidan SAMINU SULAIMAN , cak Hisham ya tsaya zuciyarshi kamar zata fad'o k'asa runtse idonshi yayi da k'arfi jin yadda Zayyan ya ambaci mahaifinshi ai kamun kyaftawar ido Wanda duk Wanda yake wajan bazaice ga lokacin da Hisham ya k'araso gaban Zayyan ba kamun ma zayyan yayi wani yunk'uri tuni Hisham ya zabga mashi wani mashahurin Mari Wanda saida gaba daya wajan ya amsa , lokaci d'aya ji da ganin Zayyan sukayi k'aura daga jikinshi luuuu yatafi zai fad'i cikin zafin nama Hisham yakoma taroshi ya watsa mashi wani Marin a dayan gefen fuskarshi nan take ya furzo jini daga bakinshi saikuma yakata tarin wahala yanayi jini na zubar mashi ta hanci ta Baki, a firgice sauran abokan nashi suka matsa wajan yan sandan nan suna Mika masu hannu alamar su kamasu.jikinsu Banda rawar mazari ba abunda yakeyi , sury kuwa tuni ta saki fitsarin tsoro da firgita sai faman kuka takeyi jikinta na rawa tsoro biyu ya shigeta Daddynta da Kuma wannan Dan sandan da take ganin da alama bashida Imani kwata kwata,
Zayyan kuwa lokaci d'aya fuskarshi ta haye tayi sumtum gaba daya kamanninshi sun canza cikin yan seconni , zubewa yayi a wajan Yana maida numfashi don yamakasa yin ihun saboda azabar da fuskarshi da bakinshi ke yi mashi ,d'aga k'afa Hisham yayi zai nausheshi a ciki cikin sauri ASP Jafar ya janye Zayyan Yana cewa " aa oga kayi hakuri Don Allah in kaci gaba da dukanshi zai iya mutuwa wallahi, wani mugun kallo Hisham yayi mashi na zamu had'u kamun ya juya yabar falon gaba daya , mutum biyu ne suka rik'o Zayyan don lokaci d'aya yafita hayycinshi sai layi yakeyi Sam yakasa tsayuwa da k'afafunshi Kuma har lokacin jini nayi mashi zuba ta hanci ta Baki, abokanshi kuwa suna gaba 'yan sandan na biye dasu abaya har inda sukayi parking motocinsu , nan suka dannasu aciki suma suka shiga sukaja sukabar gidan gonar suka nufi station dinsu,

Mai gadi na ganin tafiyarau shida wasu sauran ma'aikatan ai take ya fito daga ma'boyarshi wayarshi ya fito da ita yafara Kiran Daddyn Zayyan, saida yayi Kira biyar ba'a d'auka ba sai Ana shida ne aka dauka , PA dinshi ne ya amsa wayar da cewa Hello , cikin rawar jiki data murya Mai gadin yafara magana Yana cewa " oga ka gayawa Mai gida wasu 'yan sanda sunzo har nan gidan gonarshi sun tafi da Zayyan da abokanshi bayan uban dukan da sukayi mashi sunyi mashi jina jina wallahi sai Allah idan zai ray......... Batare da yak'arasa jin sauran maganar tashi ba ya katse Kiran da sauri ya nufi wani d'aki Yana k'wank'awasawa ,afusace akace waye ne , cikin kwantar da murya PA yace "oga akwai matsala ne yanzu aka Kira daga can gidan gonarka akan wai wasu yan sanda sun je har can gidan gonar sun kama maigida Zayyan da abokanshi wai harda dukanshi sukayi,

a zabure Daddyn Zayyan ya ture karuwarshi dake kwance dare dare bisa jikinshi suna lalabe lalaben juna ,tare da fadin "what wane Mai tsautayin ne Kuma ya shiga gonata a yau , Ashe dama akwai wani Dan sanda Mai k'warin gwuiwar da har zai iya sa hannunahi ya daki Zayyan Kuma yakamashi , nan take idanunshi suka riked'e sukayi jajir tsabar 'bacin rai don Allah yagani ko kuda bayason ya ta'ba jikin zayan da sunan cutarwa , don shi da abu yasamu Zayyan gara shi ya sameshi shiyasa baya ragawa duk wani shege da zai nemi shiga rayuwar tilon d'anshi , cikin kissa da kisisina karuwar ta matsoshi tana cewa "sweet darling mi yake fatuwa ne tayi maganar tana laluban bakinshi wani mugun Mari ya yarfa mata cikin karaji yace "ke bakida hankali ne ko bakiji abunda akayiwa d'ana ba to maza ficemun yayi maganar Yana nuna mata k'ofar "oya maza 'bacemun da gani kamun na canza maki kamanni, cikin matukar gigita da tsoro ta kwashi kayanta ta Sanya tafita daga d'akin jaka da takalmi a hannu ,tsaki yayi kamun ya mik'e ya dauki kayanshi ya Sanya,

wayarshi ya dauka yafara Kiran manyan ma'aikatan *yan sanda* don yaci alwashi bazai taba ragawa duk wanda yayi gigin shiga gonar d'anshi ba , wajan mutum ukku yayi waya dasu kamun ya tashi ya fito daga d'akin direct wajan motocinshi ya nufa inda.yaranshi da securitynshi suma suka shishshiga motocinsu direc yabasu.umurnin su dauki hanyar Lagos , aguje suka bar haraban gidan shak'atawarshi dake garin Abuja suka halba titi
Gudu sukeyi sosai kamar zasu tashi sama don suna matukar tsoron fushin ogan nasu don sun sani bashida Imani ko kadan,


___________________________

Tunda su Hisham sukaje station suka watsa su Zayyan a cell aka k'argamesu kowa yakoma office dinshi , zaman Hisham da kamar minti ashirin sai gashi ya samu Kiran gaggawa daga shugaban hukumarsu Wanda shine shugaba gaba d'aya , bai kawo komai ba ya tashi ya nufi office dinshi , har wannan lokacin babu fara'a a fuskarshi don sosai yakejin kamar yaje ya shek'e yan iskan yarancan da iyayensu ke daure masu gindi suna abunda suka ga dama,

Da sallama ya shiga office din ogan nashi ,k'amewa yayi tare da sarama ogan , kamun yace sir gani ance kana kirana,
Waje ogan ya nuna mashi da hannu alamar ya zauna, zama yayi batareda yace komai ba don ya fahimci ogan nashi kamar Yana cikin damuwa ,
"Am Hisham wad'anne Yara ne kuka kama yau da yamma Kuma suna Ina, "?
Jin wannan maganar yasa Hisham game nan da can cikin tsuke fuska don karma oga yaga damarshi yace "wasu tantiraine da aka kama da laifin yin fyade Wanda yanzu haka yarinyar batasan Wanda yake kanta ba ko ta rayu ko ta mutu , yanzu haka suna cell Kuma insha Allah agobe goben nan zamu makasu kotu don su fuskanci hukunci daidai da abunda suka aikata, ,

Murmushi ogan yayi ganin yadda Hisham kecin magani Yana magana cike da tabbatarwa azuciyar shi kuwa cewa yake saidai kayi hakuri Hisham a wannan karon doli zan taka maka birki don gudun fadawarka wata musiba ,

Shima ogan hade fuska yayi Don ya fahimci Hisham zuma ne saida wuta , yace " Hisham inason nan da minti talatin ka saki yaran nan wannan umurni ne Kuma ba daga gareni ba Nima daga sama na ne , "
A razane Hisham ya d'ago kanshi ya zuba mashi manyan idanunshi da suke dama a rine saboda 'bacin rai ,cikin wata kakkausar murya kamar Wanda yake magana da yaronshi ba oganshi ba yace " akan wane dalili oga ? Ka ko ji abunda na gayama yaran nan sun aikata ,? Sunje sun sace yarinya su biyar suka hadu suka keta mutuncinta sannan ace munkasa daukar mataki ,wane hali kakeson yarinyar da iyayenta su shiga ne , wai har sai yaushe ne masu kudi da manyan masu mulki zasu daina juya 'hukumar jami'ai a Nigeria ne , har sai yaushe Jami'ianmu zasu farga sufara kishin kansu ne , muna da duk wata dama da zamu iya hukunta koma waye Amma miyasa zamu zubar da damarmu mu tsaya wadansu 'bata gari suna juyamu yadda ransu keso mu Kuma saboda matacciyar zuciya da son abin duniya mu tsaya suna takamu yadda sukaga dama suna juyamu kamar waina a tanda ,basa shayin aikata kowane irin laifi saboda suna ganin sun fi karfin hukuma , 'ya'yansu sune 'ya'ya , da an ta'basu zakaji kowa na magana Amma duk abunda zai samu 'ya'yan talakawa ba Wanda zai damu dashi ,sunsa mutane nayi Mana kud'in goro suna zaginmu akan rashin adalcin da mukeyi masu duk wani Mai burin ganin ya tsaya akan gaskiya to ko ta halin Yaya sai anga bayanshi wasu da yawa saboda tsoron rasa aikinsu sun kasa tsayawa suyi aiki da gaskiya kamar yadda sukayi alk'awari wannan wace irin rayuwace shiyasa har yanzu munkasa samun ci gaba a kasarmu ta kowane fanni saboda azzaluman cikinta basu taba Bari muryar masu gaskiya yayi amo har ya amsa kuwar da kowa zaijita , to Ni bazan sakesu ba doli sai nabiwa yarinyar nan hakkinta komai zai faru ya faru, ya k'arashe maganar da huci Mai zafi Wanda yake nuna alamar yakai kololuwar fusata,

Jinjina Kai ogan yayi tabbas yasan duk abunda Hisham ya fad'a gaskiya ne Kuma shima zaiso a hukunta yaran don laifinsu babba ne ,to Amma inda gizo ke sak'ar shi kanshi ba laifinshi bane daga samanshi ne umurni aka bashi wanda rashin bin umurnin kan iya jefasu a wani yanayi ciki kuwa harda rasa aikinsu , a bayan fage kuwa shi kanshi Yana tsoron hatsabibancin Alhaji Saminu tabbas isarshi da ikonshi ba akan Yana Mataimakin gwanna bane kad'ai aa akwai wasu matakai da ya taka Wanda yasa yake tare da manya sosai hatsabibine na karshe sannan bashida Imani ko kadan shi kuwa bazaiso tarihi ya maimaita kanshi ba ,bazaiso Hisham ya fuskance kalubale kamar yadda mahaifinshi ya fuskanta ba, dukda ya yarda da jarumtar yaron da kaifin basirarshi Amma hakan bashi zaisa yabashi damar jayayya da irinsu Saminu sulaiman ba, gyaran murya ogan yayi yace
"Ka fahimceni Hisham Kai kanka kasan bana d'aya daga cikin irin wadan nan azzaluman shugabannin Amma ba isa in Hana Wanda suke sama Dani aikata abunda sukeso ba Wannan umurni ne aka bani Kuma kaima Ina baka umurnin kaje ka sakesu , kayi hakuri inkare na yawo zomo na yawo watarana za'a had'u ne , sannan Ina jiye maka hatsabibancin Alhaji Saminu sulaiman bakasan waye shi ba wallahi ya wuce duk inda kake tunani, sannan zai iya aikata komai akan wannan yaron nashi , in nace komai to Ina nufin komai don haka kaje ka aikata abunda na saka,

Gaba daya zufa ce ke tarfatsomashi jikinshi har rawa yakeyi akan 'bacin rai , tunani yakeyj yanzu ya zaiyi da iyayen yarinyar mi zai ce masu wani kallo zasuyi mashi wani kallo zasuci gaba da yiwa hukumarsu ne , yanzu shikenan wadan nan yaran sunci bulus kenan inaaaaaaa wallahi bazai yuwubaaaaaa da k'arfi ya bugi tabale din kamun ya mik'e ya fita afusace ko Yar sarawar da akema ogan baiyi ba kamar yadda Bai jira izininshi ba yayi tafiyarshi,

Yana fita inda suka ajiye su Zayyan ya nufa , kamar Allah ya aikoshi haka ya hausu da duka da belt dinshi aikuwa tuni suka fara zunduma ihun neman dauki kamun kace mi ya hada masu jini da majina da sauri sauran yan sandan suna rirrikeshi sanin halinshi in ranshi ya 'baci zai iya aikata komai da kyar suka samu suka fitar dashi waje suka sanyashi a motarshi ,da sauri Jafar ya shiga gidan gaba yaja motar da sauri sukabar station din, lokacin k'arfe 7pm , adai dai lokacin ne ogansu ya iso cell din nan yabada umurnin a bud'esu , ganin halin da suke ciki ne yasa yabada motarshi akan akaisu har gida don Alhaji Saminu sulaiman ya tabbatar masu da karsu kuskura ya sanyo k'afarshi acikin garin na Lagos ba tareda an sako mashi d'anshi da abokanshi ba, haka nan 'yan sandan nan sunaji suna gani suka kashe su suka Sanya a mota suka nufi gidan Mataimakin gwanna masu kishin kansu da k'asarsu na bak'inciki da abun yayinda 'bata garin cikinsu ke jin Dadi da farincikin yau dai anyi nasara akan Hisham saboda sunajin haushin yadda ya hanasu rawar gaban hantsi,

_____________________________

Momma na zaune a falo ta idar da sallar magariba kenan tana lazimi taji shigowar mota gidan , tana nan zaune tana jiran taga shigowar Hisham sai taga shiru shiru Bai shigo ba , sai can tafarajin Ana kwad'a sallama abakin k'ofar shigowar falon, haka kawai taji wani irin faduwar gaba Wanda saida ta danne saitin zuciyarta da hannunta kamun a sanyaye ta amsa sallamar tare da bada izinin shigowa , ahankali ya shigo falon har k'asa ya durkusa ya gaisheta a hankali ta amsa gaisuwarshi tana cewa "lafiya dai Jafar ,?Ina Hisham din,? "
"Lafiya qalau Momma oga Yana mota an 'bata mashi rai ne a station shiyasa Yana cikin fushi sosai nayi nayi ya fito daga motar ma Amma yaki shine nace bari na gayamaki ,"
Cikin sauke ajiyar zuciya momma tace to alhamdulillah bari naje nayi mashi magana nagode kaji Allah yayi maka albarka , ai ka kyautamun da kadawo dashi gida Ni bansan inda shalele yasamo wannan bak'ar zuciyar ba wallahi a da dai Sam ba haka yake ba,tayj maganar lokacin da take ficewa daga falon zuwa inda Jafar ya paka motar ,

Yadda Jafar yabarshi haka suka sameshi ya jingina da kukerar motar idonshi a lumshe hannayenshi yayi baya dasu ya tallabe kanshi ,farar fuskarshi ta koma jajir , kallo daya Momma tayi mashi tasan cewa ba k'aramin fushi yake ciki ba tabbas ankai mak'urarshi ne , batare da tayi magana ba ta sa hannunta ta janyo hannunshi dake bayan kanshi , babu musu ya bude idanunshi tareda fitowa daga motar yabi bayanta inda take rik'e da hannunshi kamar wani karamin yaro , haka suka rinka tafiya har suka shige falon ,Jafar dake binsu da kallo ya girgiza kanshi tareda shiga motar yabar gidan shima,

_____________________________

K'arfe 9pm daidai sukayi parking din motocinsu a harabar gidan , har wannan lokacin afusace Alhaji Saminu sulaiman yake , duk da kuwa yasamu labarin tun 7 Zayyan Yana gidanshi da abokanshi harma ankira likitansu yabashi taimakom gaggawa don lokacin da aka kawoshi ko numfashi da kyar yakeyi don ya daku sosai a wajan Hisham ,
Buzun buzun haka ya wuce ya nufi hanyar da zata sadashi da babban falon gidan ,
Ba tare da wata sallama.ba ya afka falon Yana huci ,
Momy ce zaune da Amna momy zaune take ta zuba tagumi cike da alhinin abunda yasamu Zayyan dakuma fargaban irin tijarar da Daddyn shi zaiyi akan hakan , Amna kuwa wayarta kawai take dannawa Sam ba alamar wata damuwa a fuskarta don ita a ganinta wannan shi ya shafa ba itaba batada case da shi,

Ba tare da ya ko kalli inda suke ba yabi hanyar da zata sadashi da part din Zayyan don yasan Yana can,
Kwance ya sameshi Yana bacci gaba daya fuskarshi ta haye ta kumbura sosai sai wasu wurare ajikinshi duk sun farfashe alamar duka , cikin tsananin bakin ciki da takaici hade da rashin Imani da tausayi yafara magana idonshi a juye kamar wani dodo " wallahi na rantse da sarkin dake busa numfashi duk wanda yayi maka wannan gangancin sai ya gwammacewa mutuwarshi da rayuwarshi .......................

*Littafina yakoma na kudi saidai ba yanzu ba sai mungama book 1 don na gaji da Dan kwairo kullum cikin baran comment to zai koma na kudi ehe*🙄🙄🙄🙄🙄 *Amma wadanda sukemun comment sukam zasu samu a kyauta insha Allah*
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: 👨🏻‍✈️ *JAMI'IN DAN SANDA*👨🏻‍✈️

*_MALLAKAR_*

~MARYAM UMAR ABDULLAHI~
( _MMN YUSUF_)
*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*


🅿️_30

..........."innalillahi wa inna ilaihin rajiun, wai Hisham mi yake damunka ne ? Kayi magana mana tun d'azu Ina maka magana Amma ka kasa cewa komai," juyo kanshi yayi ya d'aura akan kafafunta Yana sakin ajiyar zuciya Mai k'arfi, shikad'ai yasan irin zafin da yakeji a zuciyarshi musamman in ya tuno fuskar safiya da Babanta , yanzu wane irin kallo zasuyi mashi tabbas zasuyi zargin an saye shi ne da sa hannunshi,
cikin huci da tsananin takaicin da yake ciki yafara magana Yana cewa " har yaushe sai yaushe k'asarmu zata gyaru sai yaushe za'a daina kashin dankali a k'asar nan , kullum manya su suke danne na k'asa dasu, zalunci yayi yawa sosai a k'asarmu Kuma ba Wanda zai iya daukar wani mataki kullum tsoro da zullumi da mutuwar zuciya su suke k'ara jefamu a halin da muke ciki ,kowa Yana tsoron yayi magana wani abu ya sameshi to shikenan mu a haka zamuyi ta rayuwa kenan talaka bashida wani 'yanci na kansa duk sharar da aka kwasa a zuba mashi , 'a'a bazai yiwu ba bazan zuba ido suci bulus ba doli sai na k'watowa yarinyar nan hak'inta kota halin Yaya wannan alk'awari"............"dakata Hisham" Momma ta katseci cikin sauri don tunda yafara magana jikinta ke rawa duk da Bata fahimci abunda yake magana akai ba , Amma ta fuskanci inda yasa

Please Login or Register in order to submit comment