Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai zuba soyayyarsu da bawa junansu kulawa suke yayinda kullum suke cike da farin ciki Sam Hisham ya manta da wasu Wai su Alhaji Saminu abunda ke gabanshi kawai yakeyi , Laurat ma aikinta takeyi cikin kwanciyar hankali inda ta dage sosai wajan taimakawa marasa k'arfi da jikinta da aikinta da aljihunta , wannan yakara Mata daukaka sosai awajan aikinta kowa sonta yakeyi da Yaba kirkinta ,

*************************

BAYAN WATA HUDU

Kwance suke akan makeken gadonsu ta shige cikin jikinshi sosai tana shak'ar k'amshin jikinshi Mai Sanyata nishadi a yanzu , idonta biyu ba bacci take ba saidai idonta a rufe yake kamar Mai baccin , yayin da Hisham ke baccinshi hankali kwance ,hannunta ta Dora saman k'irjinshi a hankali tana shafa kwantaccen gashin Dake kwance luf akan faffadan k'irjinshi Wanda take matukar so sosai , kamar acikin mafarki yakejin hannunta na yawo ajikinshi , a zabure ya farka Yana Kai dubanshi inda agogon d'akin yake , zaro ido yayi ganin har 8 ta gota kamun ya juyo da kallonshi inda take Yana harararta , dariya tafashe dashi tace "to Kuma Ni mi nayi daga tashinka zaka wani fara zubamun harara tafad'a tana munguda mashi bakinta, k'wafa kawai yayi baice komai ba ya tashi yanufi bayi don yin wanka , yayinda Laurat ta rakashi da ido cike da son mijinta juyawa tayi tasake kwanciya don gaba daya batajin karfin jikinta kwana biyun nan dauriya kawai takeyi musamman ma data fahimci abunda ke damunta a matsayinta na Likita ta fahimci tanada shigar ciki , wannan yasa gaba daya yanzu takejin kanta wani iri ga muguwar kasalar Dake damunta da jiri akai akai jiri ya kwasheta sai tayi sauri ta zauna , ciyon Kai kuwa ba'a magana sannan tarasa yadda zatayi ta fad'awa Hisham tanada juna biyu hakanan taji tanajin kunya sosai ,

Bayan ya fito sauri sauri ya shirya cikin uniform dinshi na aiki Wanda suke k'ara fito mashi da kwarjinin da Allah yayi mashi , zuwa tayi gabanshi tafara Sanya mashi agogonshi Wanda tasani bazai iya sawa ba kamar wani yaro cikin Yar dariya tace
"Habibi duk fushin ne haka , janyota yayi ya had'ata da jikinshi ya na kallon cikin idanunta yace ,
"Ai sanin bana iya fushi Dake shiyasa kike mun abunda kikaga dama , tun da asuba na gayamaki ki tayar Dani k'arfe bakwai akwai inda zani shine Kika barni inata sharar bacci kamar kasa , "
"To kayi hakuri Nikaina ban farka da wuri ba bacci Mai nauyine ya daukeni banjima da farkawa ba Nima,"

"Wai kwana biyun nan duk kin canza komai naki ya canza sannan na fahimci kamar ma bakida lafiya Amma kina kokarin 'boyemun , gayamun Mike damunki? Kwantar da kanta tayi a k'irjinshi tana murmushi tace "ni ba abunda yake damuna Habibi",
"Aa ban yarda ba ga jikinki nan da zafi zafi , kina Likita guda Amma kina Wasa da lafiyarki ko ?
"Bafa wani Abu bane Habibi abun farin ciki ne , " kallon rashin fahimta yayi Mata cikin jin kunyar shi tace babynka ne yake wahalar dani kwana biyun nan" ta k'arasa maganar da 'yar shagwa'ba ,

'dagota yayi da sauri Yana fito da idonshi waje cikin had'ewar harshe yace "pls Banda Wasa da gaske kike ? Da gaske kinada cikina ajikinki Laurat ? A hankali ta d'aga mashi kanta tana murmushi wani uban tsalle ya buga kamar karamun yaro tare da dunkule hannunshi Yana fadin yessss kamun Kuma ya zubee wajan yayi sujuda Yana Mai nuna godiyarshi ga Allah sai kirari yakewa sarkin sarakuna tare da fadin alhamdulillah Alhamdulillah Allah na gode maka, Yana dagowa Kuma ya rarumeta da k'arfi ya rungumeta ya rink'a bata kiss Mai zafi kota Ina tare da zuba Mata sambatun so da kauna ,kamar Wanda aka tainkara Kuma sai ya saketa da sauri ya juya yabar d'akin sauri yake kamar yatashi sama don ya Matsu ya gayawa Momma wannan albishir din ,tun a waje yake kwalama Momma Kira , aikuwa da sauri ta fito suka had'u afalonta inda ya shigo kamar daga sama ,yadda taga fuskarshi yasata sauke ajiyar zuciya tana cewa Kai shalele Naga sadda zaka girma Kai Kam wallahi ka tsoratani irin wannan kira haka, shi Bai ma kula da mitar da takeyi ba sai zuwa yayi ya rungumeta Yana cewa "congratulation Momma kin kusa Kai ga jika ,Lauart tana dauke da ciki a yanzu ,yafada cike da doki kamar ya janyo haihuwar yakeji,

Wani irin murmushi ne ya kwacewa Momma Wanda kana kallo kasan na tsantsar farinciki ne , a hankali ta shafa kanshi tare da cewa alhamdulillah Allah mun gode maka Allah ya sauketa lafiya yabamu masu albarka ," kasa amsawa yayi don sai a yanzu Kuma ya kejin kunyar Momma 'Dan Sosa kanshi yayi Yana sakinta daga rungumar da yayi Mata Yana wani sinne Kai ,dariya tayi tace "ja'iri sai yanzu ne zakaji kunyar ai Nikam kariga da ka rainani shalele Ni Bari naje Naga jikin d'iyar tawa dama kwana biyu Naga kamar batajin Dadi Amma sam ban kawo cikine ba Ashe alkhairi ne ,daga haka ta fice daga sashen inda tabar Hisham nan tsaye ,zubewa yayi akan kujera Yana shafa sajenshi farin cikin da yake ciki yasa Yama manta da wani fita Aiki.......

Tunda daga lokacin suke bawa laurat kulawa sosai fiye da zato sun dauki duk wani so da kauna sun d'orashi akan cikin nan komai suka gani na Yara zakiga sun siyo sun ajiye abun kamar hauka , ba momma ba ba uban gayyar ba abin nasu dariya yakeba Laurat sosai , cikinta nada wata shida Hisham yasa ta dauki hotu a wajan aiki a cewarshi shima da zai samu hutun dauka zaiyi su zauna suyi zaman jiran isowar babyn su Bata so ba haka ta hakura don tasan ko momma bazata Bata goyon baya ba indai akan wannan cikin ne ,


.......................................

Wallahi yau rashin mutunci nakeji Kuma duk Wanda tsautsayi ya hau kanshi to ba ruwana Zan sauke akanshi ne cewa Zayyan Yana wani zuk'ar shisha ,
"To oga in hakane mi zai Hana mu saukeshi akan Dan sandan nan Mana , cewar wani daga cikin yaranshi da har yanzu idoshi daya Bai koma daidai ba saboda bugun da yasha a hannun Hisham Wanda ba ranar da bazaiyi maganarshi ba,
"Yes ka kawo shawara junior hakan za'ayi dama inajin haushin Dad yakasa yin komai akanshi yanzu muje mu samu wata hadaddiyar babe mu 'barshe shegiya sai muga abunda zai iyayi tunda yace shi Mai aiki da gaskiya to zamuga ko zai iya kamomu a Karo na biyu yanzu ne zamu fara wasan tsakanina dashi !!!??
"Tunda suka fara magana wani da ake cema wizy yace "taf wallahi wannan aika aikar badani ba ku Kuna ganin yadda bawan allah nan yadda yayi Mana dukan mutuwa badon Allah yasa munada sauran numfashi ba Allah da tuni mun tsufa a lahira don haka nidai nayi nan badani ba wallahi Kuna ganin mutum hannayenshi kamar k'arfe duk duka daya sai kaga stars aa wallahi yafada Yana barin falon dama gidan Baki daya ,

Sauran Kam duk suna bayan Zayyan da haka Suma suka kwasa suka shiga k'atuwar motar da Zayyan ke Hawa suka harba titi,

_________________________


"Inna nagama da komai ga abincin sai kici gaba da dubawa Ni zanje wajan Jamila tayimun kitso nagaji da Zama da kan nan haka , "
" To Mariya bazaki tsaya kici abinci ba tun safe fa bakici komai ba nasan kinajin yunwa matuk'a ki tsaya in kinci abincin sai ki tafi,"
" Aa Inna bazan iya jiraba yanzu Zan dawo don ba Mai yawa zatayimin ba kawai nagaji da Zama dashi ne , "
"To shikenan tunda kin kafe Allah ya tsare sai kin dawo ," "Amin Inna "
"Anty Zan biki don Allah ," cewar Asmau ,
"Ok Asmau zo muje dama banason fita Ni kad'ai , nan suka Sanya hijabansu sukayi wa inna sallama suka tafi ,

Tafe suke a hanya kasancewar akwai Yar tazara tsakaninsu da gidansu Jamila , asmau tana rik'e da kwalbar man kitso sai surutu take zubama yayarta , kamar daga sama saiji sukayi ansha wani wawan birki agabansu Wanda yasasu saurin ja baya cike da razana don harga Allah sun dauka motar bigesu zatayi kamun sugama dawowa daidai tuni na motar sun fito sun sunkuce Laurat sun jefata a mota kamun suka tasheta suka bar wajan cikin matsiyacin gudu kamar guguwa ,

Wata razananniyar k'ara Asmau ta saki kamun tabi motar aguje saidai kamun kace mi ta daina hango motar haka ta juya gida tana wani irin kuka kamar ranta zai fita ta gigice ta dimauce ta fita a hayyacinta Allah ne kawai ya mayar da ita gida lfy...................


*Indai inada masoya Kuma Kuna Yi na kamar yadda kuke fad'a , to in gani ak'asa gsky ta hanyar siyan littafin nan naira 200 kacal ngd sosai da kaunarki gareni my fans*😍😍😍😍

Don Allah don Allah don Allah in bazaki iya wahalar da kanki wajan yimun comment ba to don Allah kirike TNX DINKI KO SITIKA wlh Allah yagani na tsani tnx da sitikan nan πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ *JAMI'IN DAN SANDA* πŸ‘¨πŸ»β€βœˆοΈ

*_KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION_*

*_Wannan littafin na kudi ne a yanzu maiso tamun magana zaku biya 200 only ta account ko katin MTN 07069711327_*

_ina Mai baku hakuri a page din baya nayi mistake wajan sa sunan Mariya sai nasa Laurat mistake ne Mariya aka dauke ba Laurat ba_

πŸ…ΏοΈ_38

................."Subuhanallahi ke Asmau lafiya , mi ya sameki haka kike irin wannan kukan , Ina yayar Taki take ne , "
Gaba daya Asmau takasa magana sai nuni take Mata da hannu cikin ficewar hayyaci Wanda yasa hankalin Inna mummunan tashi cikin wata irin tsawa tace " kiyimun magana Asmau nace Ina yayarki take Kuma mi ya sameki , "
Da k'yar ta bude bakinta cikin hard'ewar harshe tace " ...wasu..'yan ..'yan...yankan..Kai ne suka ..dauketa sun ..tafi da ..ita Inna " ,caraf a kunnen Baba da Yaya sulaiman,da dawowarsu kenan suka tsinci wannan mummunar maganar , a hanzarce Yaya sulaiman ya k'araso inda take kafad'unta ya rik'e Yana girgizata cikin rud'ewa da zancanta yace " ke Asmau ki nutsu Mana kiyi Mana bayanin abunda yafaru , su waye suka dauke ta Kuma garin Yaya ",
Da k'yar ta tsayar da kukanta saidai hawayen idonta sun kasa tsayawa tace
"Muna cikin tafiya har mun kusa Kai gidansu Jamila , daidai k'aton filin nan da ake aiki sai kawai mukaga mota tayo cikinmu sosai ,kamun muyi magana kuma wasu maza suka fito suka dauke Yaya suka sata a mota suka gudu da ita" ta k'arasa maganar tana sakin kuka,

Gaba daya jikinsu rawa yake Banda innalillahi wa inna ilaihin rajiun ba abunda suke fad'a Inna kuwa har tafara kuka inda Baba yayi zaman Yan bori Yama kasa magana Banda girgiza ba abunda jikinshi keyi ,tunaninshi ya tsaya cak da k'yar yasamu yafara maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihin rajiun ,Yaya sulaiman kuwa tuni idanunshi sun kada sunyi jajir ,waye ya dauke mashi k'anwa, mi tayi masu, mi suke nema, mi zasuyi Mata , su waye sukeson su datse masu Dan guntun farincikin da suke ciki , hannu biyu yasa ya dafe kanshi da yakejin Yana barazanar tarwatsewa , kallonshi ya maida ga iyayenshi , inda yake hango tsantsar tsoro da tashin hankalin da suke ciki , wani nauyi yaji ya ziyarci zuciyarshi cikin zafin nama ya juya zaibar gidan ,
Cikin muryarshi da ta dishe lokaci daya kamar Wanda yayi kuka yace "tsaya sulaimanu Ina zakaje "
cikin wani irin raunin murya sulaiman yace " zanje inda abun yafaru ne Baba ko Zan samu wadanda akayi abun a gabansu inyaso daga nan Zan wuce police station nakai report, "
"To shikenan sulaiman jirani muje bazan iya Zama ba muje Allah ya tak'aita Mana wahala Allah ya tsare Mana ita aduk inda take Kar Allah yabasu ikon cuta Mata , nan suka amsa da Amin inda Baba da sulaiman suka bar gidan a hanzarce inda sukabar Inna da hafsat a tsakar gida suna zubar da hawayen tashin hankali,

Lokacin da suka Isa wajan sun iske mutane awajan sosai kasancewar lokacin da abun yafaru yafaru ne aka idon mutum biyu wani tsoho Dake Zama agefen hanyar Yana bara saikuma wani Mai caji da yake can tsallake yanada tazara da wajan saidai kasancewar Yana fesin wajan yasa komai yafarune akan idonshi saidai kamun yayi wani motsi ma tuni motarsu ta 'bacewa ganinshi , wannan yasa aka taru a wajan Ana maida yadda akayi ,

Zuwansu Baba ne tsohon da saurayin Mai caji suke k'ara Gaya masu yadda akayi dakuma Basu shawarar su hanzarta Kai report ko Allah zaisa adace kasancewar Basuyi nisa ba a duk inda suke , nan suka juya suka nufi station din,

Cikin ikon Allah Kuma sai suka nufi babban ofishin Yan sanda ,wato reshen su Hisham ,
Afujajan suka Isa station din kana ganinsu kasan hankalinsu a tashe yake , nan suka bukaci ganin babbansu , kasancewar Hisham Bai nan sai aka kaisu wajan ASP Garba , Saida ya'bata lokaci Mai tsawo kamun yabasu damar shiga inda yake , tunda suka shigo yake binsu da wani kallon rainin hankali don yasan wadan nan dai komi sukazo dashi ba wani abun kirki za'a samu a wajansu ba,

Gaisheshi sukayi ya amsa batare da yabasu izinin Zama ba yace "Mike tafe daku ?
Yaya sulaiman ne ya zayyane mashi duk abunda yafaru , tun fitowar su Mariya har dawowar Asmau da Kuma bayanin da suka samu daga mutane wajan,
Tunda yafara magana ASP Garba ke kallonshi bayan yagama ne sannan ya dubeshi yace " to yanzu mi kukeso ayi maku ne " don wannan matsalar dai kunsan ba k'aramar matsala bace ,
"Hakane sir shiyasa ai muka zo nan ataimaka Mana abincika mana inda yarinyarmu take Kar rayuwarta ta salwanya abanza don Allah yalla'bai cewar sulaiman Yana hada hannuwashi wajan rokonshi ,

Nisawa ASP yayi yace " to shikenan. Insha Allah zamuyi iya bakin kokarinmu ,Amma kamun sannan zaku bada wani Abu asa Mai don kunsan abun nan ba karami bane doli zamu tura Yaranmu kowane sako da lungu na garin nan don ganin mun gano maku yarinyarku don haka zaku bada dubu hamsin na Mai insha Allah yarinyar ku zata dawo cikin aminci

Cikin mad'aukakin mamaki suke kallonshi kamun Yaya sulaiman yace " haba yalla'bai wane irin dubu hamsin Kuma , muna gayamaka an dauke yarinyarmu sannan kana zancan mubaka dubu hamsin ,to gaskiya mu ko dubu goma ta kanmu bamu da ita a halin yanzu ,"
Wani kallo ASP Garba yayi mashi kamun yace to tunda bakasan ya zakayi ba ai sai ku tafi ku jira dawowar tata duk sanda sukaga damar mayar maku da ita ,"
"Haba Dan nan Taya zakace haka don Allah ka taimaka Mana nayi maka alkawarin in aka ganota Zan Nemo maka kudin inbaka don Allah yalla'bai , cewa Baba da duk hankalinshi ya tashi ganin inda yake sa ran za'a kwatar mashi hak'k'inshi a Nemo mashi 'yarshi sai gashi Abu Yana nema yazama kasuwanci , (ya Allah ka gyara Mana k'asarmu😭😭)
Wani malalacin kallo ASP yabisu dashi kamun yace to naji zaku iya tafiya in mun samu wani labari akanta zamu nemeku , daga haka yaci gaba da rubuce rubucen da yakeyi ,

Wani irin haushi da takaici ne suka rufe Yaya sulaiman gefe daya ga tsananin tsoro da fargaban abunda zai iya samun 'yar uwarshi Saidai Babu abunda zai iya Yi wasu hawaye ne masu zafi suka sauko mashi inda yaja hannun Baba suka bar office din zuciyoyinsu na k'una da bugu kamar zasu fasa kirjinsu su fito, Baba kam dauriya ce kawai yake Amma shikad'ai yasan abunda yakeji ,k'irjinshi yakejin kamar zai 'balle gida biyu yasan tabbas ciyon zuciyarshi ne yake neman tashi abunda yayi shekaru rabon da ya taso mashi , bayan fitowarsu rasa inda zasu dosa sukayi , nan suka Kara tabbatar da tabbas talauci mugun ciyo ne don da su din wasu ne da yanzu ko'ina ya dauka da zancan batan yarsu da tuni anfara bincike akai Amma yanzu duba kamar ba Dan mutum ne ya 'bata ba ko dabbar mutum ta 'bata yaci ace an tausaya Masa bare da sukutum Amma wannan *Dan sandan* don rashin Imani har yake zancan subashi wasu makuddan kudade da su kansu Basu mallakesu ba ,
Haka suka rinka yawo a gari Basu nan Basu nan har bayan la'asar zuwa lokacin yunwa da k'ishi ma ya ishesu Babu yadda suka iya doli suka juya gida ,

Nan suka iske Inna kwance zazzafan zazzabi ya saukar Mata tunda suka tafi banda kuka ba abunda yakeyi Khadija ma bayan dawowarta daga aike da Inna tayi Mata tasamu wannan mummunan labarin nan ta zube tana kuka Asmau ma kuka anrasa Mai lallashin wani , acikin wannan yanayin suka samesu ,wani Abu Mai d'acine ya ziyarcesu ganin halin da Inna da yaran ke ciki gashi Suma dauriya ce kawai sukeyi Amma tabbas suna cikin raunin zuciya sosai , kallo d'aya Inna tayi masu tasan Babu nasara a galabaice tace
"ya ake ciki malam ??
Batare daya kalleta yace " sai addu'a Inno addua kawai zamu ci gaba dayi har Allah ya bayyana Mana ita ,munje wajan 'yan sanda yanzu munkai report ki kwantar hankalinki insha Allah za'a ganta lafiya, " cikin k'ok'arin danne kukanta tace " Allah yasa malam Amma inaji ajikina duk inda Mariya take tana cikin mawuyacin Hali, " to Amma malam mi zai Hana mu Kai sanarwa gidan radio ko Allah zaisa adace , "

"Aa Inno ba amfani kai sanarwa gidan radio saboda Mariya saceta akayi bawai 'bata tayi ba , addu'armu kawai take buk'ata a yanzu Inno , yafada cikin wani irin yanayi Mai nuni da karfin halin danne zuciyarshi ne yakeyi kawai , innalillahi wa inna ilaihin rajiun yadda wadan nan bayin Allah sukaga Rana haka sukaga dare ,wuni ranar ba Wanda ya sawa cikinshi komai acikinsu kasancewar dama can abincin Rana ne Mariya ta Dora masu kamun ta fita saigashi ko nuna abincin baiyi ba suka samu wannan mummunan labarin tun lokacin ba Wanda yasake kula da wata tukunyar abinci ,

Washe gari haka suka sake zagayawa tsakanin inda abun yafaru da wasu wurare Dake kusa dasu kamun suka wuce police station , wannan karon ma ASP Garba kawai suka iske nan yake Gaya masu ba wani labari suje sukara hakuri , daga haka yayi shigewarshi office Yana mita kasancewar dama shigowarshi kenan yayi Karo dasu ,

Wani da ake cewa sajen Musa ne yabi bayansu har sunkusa ficewa daga police station din ya dakatar dasu don yayi mugun tausaya masu tunjiya yake tunanin halin da suke ciki kasancewar Yana nan lokacin da sukazo ,

Gefe ya jasu cikin sauri yafara magana yace " kunga wajan can kuje can ku zauna kamun oganmu yazo in yazo zanzo na kiraku insha Allah in kuka ganshi zai tsaya tsayin daka wajan ganin an Nemo maku yarinyarku duk inda take a fadin garin nan ,
Fuska cike da farinciki suka fara Yi mashi godiya da Yi mashi addua , yace "ba komai kudai kuje ku jira insha Allah kukanku ya kare , "


________________________

"Kai maman biyu gaskiya nagaji tun jiya nake Abu d'aya ko tausayina bakyaji jiyafa ko bacci Baki barni nayi ba akan tausar nan, "
Yamutsa fuska tayi cikin yanayin shagwa'ba tace
"To Habibi Ni ma ai bana samun baccin Kuma kana ganin yadda k'afafun nan suka kumbura doli sai Ana daddanamun su kaga tsakanin jiya da yau ai sun rage ko ? "Tayi maganar cikin sigar tambaya ,
"Hmmm Ni Kam Naga d'a da wuya, da hakan ai gara kawai na dauki cikin na haife abuna , Amma a ce kullum banida hutu aiki sai Wanda Kika manta saboda kawai Zaki haifamun baby , "yayi maganar Yana yamutsa fuska kamar zaiyi kuka don harga Allah yagaji tunjiya take wahalar dashi tana baccinta Yana Mata tausa daya daina zata tashi tafara rigimar kafafunta ciyo da yaci gaba sai ta bingire da baccinta tabarshi da aikin tausa ( hhhhhh maganin maza kenan gara araba wahakar ai malam HishamπŸ€ͺ )

Da k'yar yasamu ta rabu dashi wanka yaje yayi yayi Shirin zuwa aiki Saida ya taimaka Mata ya rakata sashen Momma kamun ya fito yanufi motarshi ya shiga inda ya tasheta yanufi office din,


*Daga dai insha Allah free pages sun Kare sai Wanda suka biya maiso ta turo kudinta 200 amma daga wannan page din to na yankeshi sai Wanda ya biya*

*Zan rinka post in nayi yau to bazanyi gobe ba sai jibi Amma zanyi kokari narinka Yi maku page Mai tsawo* ngd mmn Yusuf Mai kayan mata


πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ» *ASLM GANI FA NA SAKE DANNOWA DA SABBIN KAYA MASU SABON SALO*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

*takuce mmn Yusuf Dr mata mai gyaran mata ciki da wake*πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kijiβœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ»

Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka,πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»
*Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*

Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje

Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir

Maganin nono Dana hips
Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar,
Maganin gashi
Maganin hawan jini
Maganin sugar

Sabulun wanka na gyaran jiki
Sabulun dilka na amare
Dilkar amare

Kwallin mallaka (daga ni sai kai)
Maltinar mata
Bobintan mata
Set na lalata gindin kiahiya
Set na ukku bala'i
Set na rantse bakida kishiya,

Kalolin gumba
Kalolin gari
Kalolin matsi
Kalolin sabulan tsarki
Zumar mata
Zumar ridi
Zumar goron tula
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin sabon budurci
Tsumin kankana
Tsumin tabaje
Tsumin makalemata
Shayin mata
Sirrikan mallaka
Dan goshi da mahadinshi
Dan goshi na Mara
Kyallen al'ajabu
Rakumi da akala
Bita zai zai
Dahuwar kalolin kaza zabo zakara
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar zuciya
Dambun nama
Dahuwar yan shila
Yajin mata
Yajin maza domin Karin karfi


*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜‰πŸ˜ wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani ,
Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mataπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°

Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah ,
Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi maganaπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° 07069711327

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko

Please Login or Register in order to submit comment