Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haushin momin Tata,
Mom kam in da sabo ta saba da rashin girmamawar da yaran ke mata , har fiye da haka ba tasha zaunar dasu tana yi masu nasiha akan rayuwa amma kullum kamar Kara zugasu takeyi ,ajiyar zuciya tayi tace "addu'a ita kadai ce mafita,

"Dad kudi nakeso kabani"
"Mizakayi da kudi son?"
"Dad gidan rawa zan bude nawa na kaina don a yadda nake babban yaro Yakamata ace inda nawa gidan rawa na kaina ,"
Dan jimmm Dad yayi sannan ya nisa yace ,
" Bawai zan hanaka bane ko banason baka kudin a'a , ina tunanin kana ganin babu matsala yin hakan bayan kasan inada burin zama gwamna anan gaba , kasan halin mutane yakamata ka dinga sanin abinda zakayi saboda idon mak'iya don kasan idan har nasamu kujerar Gwamna to kai kanka ka haye wanda ina fatan daga gwamnan na koma d'ane kujerar shugaban kasa, kaga shikenan k'asa tazama tamu sai yadda mukayi da ita wannan shine babban burina a rayuwa kuma nafara ganin nasara tunda nafara tsallake mataki na farko wanda zai sharemun hanyar da zanbi wajan ganin na cika burina,"

Wata irin dariya Zayyan yayi yace "kai Dad har k'asa na hango kaina a villa wallahi , amma dai Dad Ina bukatar kudin nan gaskiya don nayiwa friends Dina alk'awarin Zan gina mana gidan rawa , kuma bazan fasa ba don ba girma na bane magana biyu ,kawai kabamu zansan yadda akayi sunana bai bayyana ba zamuyi komai a sirrance, "
"Ka tabbata?"
"Yes Dad"
"Okay nawa ne kudin?"
"5million ne Dad"
"To shikenan anjima zakaji alert kasan don kai kawai nake neman kudin don haka ba abunda zaka nema ka rasa my son,"
Wani tsallen dadi Zayyan ya buga tareda rungume mahaifin nashi yana cewa ina sonka Dad don kai kadai kake sona bari naje wajan friends Dina mufara tsara yadda zamuyi aiki,"

Cikin murmushi da jin dadin ganin yadda dan nashi ke farinci yace "ok son "
Aguje ya fito daga part din yana ihun murna inda yabar Mom anan ya sameta ko kallonta baiyi ba yayi ficewarshi .

_________________________


Unguwar gwangulori,

Malam jibirin haifaffen garin Lagos ne duk da Asalin iyayensa yan Birnin Kebbi ne ,cin rani ne ya kawo mahaifinshi garin na Lagos har daga baya ya gidandance inda ya aure matarshi Inna Suwaiba , wadda ta kasance yar uwarshi ce , malam jibirin shi kada ne dansu a duniya har lokacin da Allah yayi masu rasuwa,

Malam jibirin talaka ne sosai wanda kullum sai yafita ya nemo sannan za'aci a gidansa ,da matarsa daya Inna Hauwau , yaransu hudu Sulaiman shine babba sai Mariya dake binshi sai Hadiza da shema'u auta,

Yara ne da suka samu tarbiya sosai daga wajan iyayensu , dukkansu masu nutsuwa ne kuma sun iyama talaucinsu ,
Duk da talaucin da suke ciki malam jibirin yayi iyakar k'ok'arinshi na ganin ya'yan shi sun samu ilimin zamani dana boko ,
Alhamdulillah yanzu haka sulaiman ya haษ—a degree dinshi tun shekarar data gabata sai dai halin da ake ciki na Nigeriyanci yasa har yanzu bai samu aiki ba sai dai bai zauna haka ba don dama yana dan taba ษ—inkin tela to Alhamdulillah yanzu ya kware sosai kuma yana samu dai dai gwargwado da wannan sana'ar yake samu yana tallafawa iyayenshi dakuma karatun k'anenshi,

Mariya ma tagama secondry inda sukayi had'a k'arfi da k'arfe suka sama mata admission a makatar koyon aikin jinya , wanda shine babban burninta a rayuwa taga ta zama ma'aikaciyar jinya, haka ta dage sosai tana karatun ta cikin kwanciyar hankali don burinta baiwuce tafara aiki ba don ta tallafawa iyayenta itama don nauyi yayiwa yayanta yawa shikadai ko shima zai samu saukin wani abun,

"Assalamu alaikum Inna sannu da gida "
"Yawwa mariya andawo kenan "
"Eh Inna na dawo yau kam munjima sosai gashi na kwaso rana da yunwa sosai wallahi , Allah yasa dai akwai abinci a gidan," tayi maganar lokacin da take zama akan tabarmar da Inna ke zaune ,ajiye jakar litaffanta tayi a gefe tare da fadin wash Allah wallahi yau najigata sosai,
Inna ta tabe baki tace to ai ke kikaji zaki iya ba yadda banyi dake ba akan ki yarda a tsaida Ranar aurenki da wannan yaron Nura yaro mai
mutunci da nutsuwa kika k'i kikace ke karatu zakiyi ai sai ki daure don ba abunda yake samuwa abanza batare da ansha wahala ba bare ilimi ,"

Kai inna kullum sai kinyi maganar Nura a gidan nan nifa ban ce bana sonshi ba amma dai ina zai iya jirana to don inasha Allah sai nacika burina, "
"To Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" cewar Inna don itakam sam bata wani son karatun tafinson ta fitar da miji tayi aure,
"Sannu da dawowa Anty , "
Yawwa khadija , dauko mun abincina naci don Allah yunwa nakeji sosai "
"To anty ,
Bayan tagama cin abincin ne ta d'ibi ruwa a rijiya taje tayi wanka don samun saukin zafin da takeji,bayan ta fito ne ta tarar Babanta ya dawo nan ta zauna sukaci gaba da fira gaba daya,

___________________________

Zaune suke a babban falon mahaifinsu , gaba dayansu a tsure suke suna jiran abunda mahaifin masu zai yanke a kansu , mussaman ma *Lauratu* duk da sanyin AC da fankokin dake katon falon hakan bai hanata zufa ba kamar an watsa mata ruwa tsabar rud'anin da take ciki don tasan Mahaifin nasu bashida wasa ko kadan sannan yana da tsauri akan ra'ayinsa tana gudun abunda ,zaije yazo karfa garin sanya tayi saken da za'ayimata sakkiyar da babu ruwa ,

Ummi kam sai kallonsu takeyi yadda suke tsuma kamar wadan da aka gurfanar a gaban alk'ali , sosai suka bata dariya amma ta danne don kar su kawo masu wargi,

Gyaran murya Abban yayi ya dubi yayan nashi bayan ya ajiye jaridar dake hannunshi ya ce " ya mukayi daku ???
Saida gabansu ya fad'i musamman ma Lauratu don Zainab kam da dan sauki sauki don itakam tasamu mafita , cikin inda inda Zainab tafara magana, "am dama dama yaya Nasir yace zai turo magabatansa wajanka tayi maganar cikin rawar harshe dakuna kunya,

Daga Abba har ummi murmushin farin ciki sukayi kamun su mayar da dubansu ga Lauratu cikin daurewar fuska Abba yace "kefa?"
Cikin daburcewa tafara magana kamar zatayi kuka tace "don Allah Abba kayi hakuri kadan k'aramun lokaci wallahi har yanzu bansamu wanda yayi dai dai da rayuwata bane amma.........cikin daka tsawa yace " rufemun baki shashasha mai kunnen k'ashi , wato ke duk maganar da za'a maki ta bayan kunnenki take bi ko ? Tun yaushe nake baki lokaci amma har yanzu kin kasa zuwa da magana daya k'wak'k'wara ,to bari kiji in gayamaki wallahi nagaji da zama daku a haka ba aure daga nan zuwa wata daya in baki kawo Wanda kk so ba zan zaba maki duk wanda yayimun da kaina kin kuma Sanni bana magana biyu don haka ya rage naki ko kiyi amfani da damar ki ko kuma kibari ta su'buce maki ,ku tashi kubani waje , har rigegen tashi sukeyi sum sum sukabar falon ,

Alhaji Abubakar mainasara kenan da iyalanshi , matar daya Hajiya Sa'adatu wadda suke kira da Ummi sai yaransu biyu Lauratu da Zainab wadan da sukadai suka suka haifa ,
Lauratu babbar likita ce a babban asibitin acikin garin na Lagos tanada shakara 28 a duniya sai k'anwarta Zainab mai shakara 27 aduniya kasancewar shekara daya ne a tsakaninsu itama tagama karatu ta ma'aikaciyar banki ce

Asalin Alhaji Abubakar mainasara bafulatanin Sokoto ne aiki ne ya kaishi Lagos amma duk yan uwanshi suna Sokoto ,hakama Hajiya Sa'adatu ,
Lauratu da Zainab kyawawane sosai irin na asalin fulanin Sokoto
Lauratu doguwar mace ce sosai tanada dan jiki amma ba sosai ba Allah ya zuba mata kyau najiki dana fuska , don duk abunda namiji keso a jikin mace to Lauratu ta hadashi , komai nata cif cif yake gwanin sha'awa , tana samun masu sonta sosai amma ita sam auren baya gabanta aikinta kawai tasa a gaba , hakama k'anwarta Zainab wannan yasa Abban ya bude masu wuta sosai akan su fitar da mazajen aure , shine Zainab ta gabatar da Nasir wanda ya kasance dan yayar Ummu ne dama yajima yana son zee sosai amma taki bashi dama sai a wannan karon da taga Abba na neman ya aurar dasu ga koma waye takuma san halinshi idan har ya fada tofa bazai taba canzawa ba,

Hawaye ne suka zubo a fuskar Lauratu cikin matukar damuwa ta ษ—ora hannunta akai tareda fadin na shiga ukku tayaya zan kawo miji a cikin wata daya kacal............................naso yafi saidai wlh hannu ya rike๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚



Ilove You wujiga wujiga masoyan mmn yusup inayinku over ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜inajin dadin comment dinku sosai Allah yabar kauna๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ

*Zanyi aike zafafan kayan mata Kano da Katsina maiso tamun magana* 09035027743
[6/12, 8:24 PM] Mmmm Yusuf: ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง *JAMI'IN 'DAN SANDA*. ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ”ง

*Mallakar*

*Maryam Umar Abdullahi*
(Mmn Yusuf)

*Marubuciyar*
*Minene Asalina*
*Mutum ce kuwa*
*Husna ko Huzna*
*And now*๐Ÿ‘‡๐Ÿป
*Jami'in d'an sanda*


*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*_wannan littafin sadaukarwa ne ga daukacin kainuwa writers Ina alfahari da k'unguyar kainuwa da mutanen cikinta Allah yak'ara Mana k'aunar juna son so fisabilillah_*๐Ÿ˜๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ_23


........................."idan fa bakiyi da gaske ba wallahi Abba zai baki mamaki anty ,kinga dai yayi ta baki lokaci amma har yanzu kin kasa kawo mutum daya acikin samarinki , kuma kinada su bare kice babu wanda yake sonki , "
Yamutsa fuska tayi cikin matukar damuwa tace , " bazaki gane bane zee nifa wallahi gaba daya banida tsarin aure a yanzu sannan wadan nan samarin nawa Ni ba wanda nakeso acikinsu gaba daya basumun ba narasa yadda zanyi gashi ga dukkan alamu a wannan karon Abba bazai dagamun k'afa ba" tayi maganar kamar zata fashe da kuka,
Dariya zee tayi tace "kina bani mamaki anty idan har kikace babu tsarin aure a rayuwarki , shin abunda nakeson na sani shine auren ne bakiso gaba daya ko kuwa akwai lokacin da kike ganin Yakamata kiyi auren , ? Yakamata dai kisani ita rayuwar mace ฦ™alilan ce kinada shekara 29 bakiyi aure ba sai yaushe zakiyi ? Yakamata dai kiyiwa kanki fada dai don ita mace babu lokacin da ya dace tayi aure kamar lokacin da ake yayinta ake sonta rashin yin haka kuwa yanasa akai lokacin da zata rasa manemi duk kyauta da matsayinta kuwa sannan................"ke ya isa don Allah karki cikamun kunne da iyayinki na banza ki barni da abinda ya dameni, dariya zee tayi tace "bawani anty kawai dai bakison gaskiya ne amma dai kiyi tunani don wallahi Abba a shirye yake daya aura maki Koma wanene ,cikin damuwa tace " wannan shine abinda yake tsoratani yazama doli na fitar da daya daga cikin manema na tun kamun Abba ya fitarmun da kanshi ,"
Cikin zumud'i da jin dadi zee tace "yawwa anty don Allah ki fitar da Abdul wallahi duk yafi wad'an da suke zuwa wajanki sannan zakuyi matukar dacewa da juna wallahi ,"
"Nikuma bai mun ba zee don haka bazan za'beshi din ba mutum.sai shegen girman kan tsiya da jin shi wanine mrtsss ,daga haka ta tashi ta shige toilet

________________________

Tun bayan abunda yafaru gaba daya halayen Hisham suka canza , mutum mai fara'a wasa da dariya yanzu yakoma kamar wani dodo tsabar daurewar fuska yanzu ko Momma Bata cika ganin dariyarshi ba ,gaba daya ya mayar da kanshi busy aike yake yi da dukkan karfinshi ba dare ba rana ,baya ragawa duk wani azzalumi duk wanda yakama da wani laifi to fa sai ya tabbatar da an hukuntashi koshi waye , saboda jajircewarshi da aiki da gaskiya yasa yayita samun k'arin girma daga wannan sai wannan har inda yanzu Allah yasa aka mashi *mataimakin commissioner* na wannan yanki , yaji dadin wannan muฦ™amin sosai don yanzu yak'ara samun damar da zaiyi yak'i da azzalumai lokaci yayi da Yakamata su samu canji acikin wannan garin na Lagos , Alhamdulillah komai na tafiya yadda yakeso kuma cikin ikon Allah cikin kankanin lokaci ansamu canji mai yawan gaske a jahar sai sambarka , wannan jajircewar tashi ba k'aramun farinjini ya janyo mashi ba ga talakawan garin don yanzu duk wanda aka zalunta matukar ya kawo kukanshi a hukumar to kuwa Hisham zai tsaya tsayin daka wajan ganin ya kwatar mashi yancinshi, wanna yasa ya samu daukaka sosai fiye da tunani, dayawa zakaga unguwanni sun lika fotunanshi saboda tsabar yadda suke sonshi da kaunarahi,
Momma najin dadin yadda dan nata ke gudanar da aikinshi dakuma irin daukakar da yake samu amma acan k'asan zuciyarta kullum cikin tsoro da zullumi take don tasan doli ne d'an nata yayi mak'iya da yawa wad'an da basason gaskiya da ci gaban kasarsu , saidai tana mashi addu'a sosai tasan ba wanda ya isa yayi mashi wani abu sai da izinin Allah,

Abu daya ke damunta dashi shine rashin yin auren shi , tayi magana da fushi har tagaji amma har yanzu kullum maganar sa daya ce bai tashi yin aure ba sai lokacin da ya dibama kanshi, tasha hadashi da yayan k'awayenta amma yana guje masu duk wadda aka kawo mashi sai yace bata mashi ba , tarasa yadda zatayi dashi ,

Yauma kamar kullum yana zaune a dinning Yana karyawa ta fito daga dakin ta zama tayi kusa dashi tace "shalele da karfe nawa zaka dawo yau ?
"Cikin muryarshi mai cike da jarumta ya amsa da cewa " sai dare zan dawo Momma yau inada ayukka sosai a office, "
"To koma dai minene inason ka dawo da karfe hudu akwai inda zaka rakani kuma saura kak'i zuwa kaga abunda zan maka,
Dafe kanshi yayi cike da damuwa yace ohhhh Momma rakiya fa nikuwa ina zan rakaki sai kace wani mace , nasan dai bazai wuce gidajen k'awayenki ba kiyi hkr zan turo direba ya kaiki kinji,"
"Karma ka fara kai nakeson ka kaini kuma doli ne kazo kaji na gaya maka, "
Kamar zaiyi kuka ya amsa mata da "to" don yasan tatsuniyar gizo bata wuce k'ok'i kila takoma nema mashi wata yarinyar ne shiyasa takeso tajashi suje ,shi kam yaga ta kansa kullum Momma cikin talansa take sai kace yarasa masoya gashi sai ja mashi raini takeyi wajan yara ฦ™anana , 'bata fuska yayi cikin shagwabar da shi kanshi baisan yayita ba yace "amma Momma saboda Allah haka zakiyi ta talla ta sai kace narasa mai sona kuma ............."kai rufamun baki kullum maganarka daya ce baka rasa masoya ba nikuma banga alamar hakan ba don haka bazan gaji da nema maka ba kuma wannan karon in har kawatsamun k'asa a ido nikadai nasan abunda zanmaka kaji na gaya maka tunda har yanzu kai bakasan cewa ka girma ba a matsayinka ai bai kamata ace bakada mata ba don aure shine cikar mutuncin kowane mutum , baice komai ba haka ya ajiye abincin da yakeci ya tashi yabar gidan,
Momma kuwa bata damuba don tasha alwashin komai zaiyi a wannan karon bazata daga mashi k'afa ba bakomai ne yasa takeson yayi aure ba saidon wannan bakin halin da ya daukama kanshi mutum kullum fuska a hade kamar hadari ba wanda yake ganin damanshi ita kuma tafison ya dawo ainahin Hisham dinshi mai sakin fuska da dariya da tsokana sam ta tsani wannan sabon halin nashi wanda take ganin idan har yayi aure matar zata taimaka mashi wajan canza shi ya dawo kamar da,

_________________________


Gaba dayansu a buge suke yau sunsha sunyi tatil sai raye raye sukeyi mata da maza kuma abun takaici abun tausayi dukkansu yara ne sosai da bazasu wuce 22 to 25yrs ba abin karin bak'inciki da takaici mafi yawansu 'ya'yan mu na hausa Fulani ne ,mafi yawansu ya'yan manya ne masu kudi da masu mulki , iskanci suke kala kala acikin gidan rawa wanda ya kasance mallakin Zayyan ne,

Shikuma shaid'anin yana gefe akan wata kyakkyawar kujera irin ta sarakai ya hakimce , mata biyu ne a gefenshi sai faman shafashi sukeyi suna sumbutarshi tako ina ba kunya ba tsoron Allah yayinda yan korenshi ke gefenshi suna k'ara zugashi da yi mashi kirari irin wanda yakeso ,

Sun shagala sosai ba zato ba tsammani yan matan nan sukaga Zayyan ya hankadesu da k'arfi har saida suka fad'i , daga yan matan har abokanshi da sukaga abunda ya faru ido suka zuba mashi da mamakin ko lafiya,
Yamutsa fuska yayi cike da shak'iyanci yace "abokai nifa yau ranar ta mussaman ce agareni ina bukatar abunda zai sanyani nishadi sosai , wani daga cikinsu yace " wane irin nishadi kake nema da ya wuce wanan ne babban yaro , ai babu wani nishadi da yafi wadan nan kayan da ka ture kawai kabada kai ka kwashi rabonka Baba,
Tsaki Zayyan yayi yace " kai nifa yau wallahi babbar harka nakeso kota wane hali ,wad'an nan duk tsaffin hannu ne yau sabuwa dal aleda nakeso gaskiya......wani irin ihu suka sanya suna dariyar shak'iyanci da yi mashi kirarin da suka saba idan ya tafka wata ta'asar ,

Yan matan kuwa wani irin haushine ya kamasu musamman ma surayya wadda ake kira da sury yar minister ce Allah ya jarabeta da mugun son Zayyan Wanda ba komai ke rudarta akan shi ba irin tsananin kyaun da yake dashi , kuma a sanadin soyayyarshi ne ta samu kanta a wannan halin shine mutum na farko daya fara saninta 'ya mace kuma bayanshi bata kula kowa amma ta kula tuni ya jefata kwandon shara tunda yasamu abunda yakeso yakewulakanta ta ,cikin jin haushi kamar zatayi kuka tace "haba dear abunda kakemun ka kyauta kenan miyasa kake wulakanta Ni ne bayan kasan irin son da nake maka, abunda kakemun yayi yawa dear yakamata karinka tausayamun , Ina tsananin sonka da kishin ka amma nakula kai sam bakama san inayi ba , kasan bakincikin da nakeji aduk lokacin Dana ganka da wata mace , wannan kaskar ma don narasa yadda zanyi da ita ne na barta tana ra'barka amma daga yau zan fara daukar mataki akan duk shegiyar da na koma ganinka tare da ita wallahi "tayi maganar a haukace tana nuna d'ayar budurwar dake kwance har yanzu tun da Zayyan ya tureta , ita kam sama sama ma take jinsu don gaba daya Zayyan ya daga mata hankali wanda batajin zata iya hakura dashi , tashi tayi tana layi takoma nufo inda yake , cikin fitar hayyaci kamar wata zakanya ta far mashi da salon wasanninta ,tsabar rashin kunya sam bata damu da mutanen dake wajan ba sai kokari take tasamu abunda takeso gaba daya tsabar jaraba yasa takasa control din kanta , ba zato ba tsammani sai gani akayi sury ta nufota da kwalba gadan gadan kamun suyi wani yunkuri tuni ta kwada mata kwalbar akai , wata gigitacciyar k'ara yarinyar tafasa ,take kanta yafara fitar da jini sosai , banda ihu ba abunda takeyi ,

Duk mutanen wajan tsai akayi ana kallonsu amma ankasa samun wanda zasu taimaki yarinyar ,shi wanda akayi domin shi ma dariya abun yabashi haka yarinka sakin murmushin shi mai kyau wanda ba k'aramin k'ara fito da ainahin kyaushi yake ba, cikin rashin damuwa sury ta dauki jakanta tayi tafiyarta,
Wata yarinya ce ta k'araso a guje tana tambayar yarinyar da aka fasama kai tana cewa " ke taly mi yake faruwa ne waya maki wannan aiki , arikice take magana da yake batasan abunda yafaru ba fitowar ta kenan daga d'aya daga cikin d'akunan dake wajan ita da saurayinta ta hango k'awar tata a wannan halin kuma kowa ya zuba mata ido anrasa wanda zai taimaka mata,

Kamata tayi tayi hanyar waje da ita , sanyata tayi a mota taja aguje tabar gidan rawar ta nufi asibiti da ita don ganin yadda tafara layi alamar jinin yafara bugeta,

Zayyan da abokanshi kuwa ko a jikinsu saima dariya da sukeyi ,tashi Zayyan yayi ya dube su yace kunga kuzo muje yau zamu fita farauta don wallahi sai na samo sabuwa dal a leda , ihu sukayi tareda fadin "yau zamu ga mai tsautsayin da zata shigo hanyarmu,hhhhhhhhh,

Fita sukayi suka shiga ฦ™atuwar motarsu suka fice daga gidan ,

***************************

Da kyar ya ajiye ayukkan dake gabanshi ya baro office din ya nufi gida, tafe yake a motarshi sai faman gungini yakeyi gaba daya Momma ta takura mashi akan sai yayi aure shikuma sam baida ra'ayin aure a yanzu shi matan ne ma bala'in haushi suke bashi wallahi ,
Da sallama ya shiga falon ,Momma na zaune cikin shirinta tsaf shi kadai take jira ,ta amsa sallamarshi , gaisheta yayi ta amsa zai zauna kenan tace "a'a karka zauna maza kaje kayi wanka ka ciremun wadan nan bak'ak'en kayan ka nemi manyan kaya kasa kazo mu tafi kuma karka kuskura ka batamun lokaci ,
Baice komai sai yamutsa fuska da yayi ya tashi ya nufi dakinshi,
Wanka yayi ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda ruwan k'asa ya daura hularshi kalar aikin shaddar sai tsadadden takalminshi suma dai kalar aikin shaddar ne yayi kyau sosai daukar agogonshi da farin glass dinshi yayi ya fito daga dakin ,
Hannu ya mik'awa Momma ta Sanya mashi agogo sannan ta tashi suka fita , sai faman washe baki takeyi tanajin dadi , azuciyarta kuwa sai addu'a take akan Allah yasa yarinyar tayi mashi don tasan hali ba yau yasaba bata kunya ba,


*************************

Tafe suke kamar kullum akan titin sai faman shek'a gudu sukeyi kamar zasu tashi sama yayinda music da iface ifacensu ya cika motar , a haka har suka zo wata unguwar talakawa nan suka rage yawan gudun da sukeyi a hankali suka fara bin kowane lungu da sako na cikin unguwar , cikin ikon Allah kuwa Allah ya hadasu da wasu yan mata biyu 'yan makarantar secondry sun taso daga school suna tafiya a hankali suna dan ta'ba fira,
Tundaga nesa suke k'are masu kallo , tuni Zayyan ya k'uresu da ido yana nazarin wadda zai za'ba aciki,
Cak ya tsaida idonshi ga d'ayar wadda ta kasance fara tass kuma doguwar mace ga kallo Daya zaka Mata kasan cewa ta tara abubuwan da duk namiji zai so a wajan mace , cikin wani shu'umin murmushi ya nuna masu ita ,
A take suka kunna motar suka bi bayansu don har sun Dan gotasu k'ad'an, suna zuwa dai dai inda 'yan matan suke suka tsayar da motar , cikin matukar zafin nama da kwarewa suka cafko yarinyar suka turata mota suka shiga Zayyan yaja motar aguje inda sukabar dayar yarinyar na zunduma ihu da kiran a taimaka mata 'barayi ne , kasancewar wajan ba mutane sosai da kyar mutane suka fara taruwa akanta wanda zuwa lokacin ko k'urar motar su Zayyan babu a wajan,....................




๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*SHAHARARRA KUMA K'ASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA _MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TA SAKE ZO MAKU DA KAYATATTUN KAYAN MATA ZAFAFA MASU KYAU DA INGANCI SAYEN DAYA KO SARI INA SOKOTO INA AIKAWA KOWANE GARI A NIGERIA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH KUDAI KU MATSO KAR AYI BABU KU KAYANMU NA MUSAMMAN NE*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป
09035027743
*KADAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA MUKE DASU*

maganin sanyi
Maganin KIBA
Maganin rage tunbi da kiba

Maganin sanyi na maza


Maganin gashi - Yana Sanya tsawon gashi Hana karyewar gashi bakin gashi yana maganin sali kurajen Kai da sauran matsalolin Kai


*Akwai zafafan kayan Mata Kamar jaka*

Gumar Madara
Gumbar gero
Gumbar Jan icce
Gumbar Sha ki matse
Gumbar sa buzu kuwa
Gumbar tada zaune tsaye
Gumbar ridi
Gumbar shinkafa
Gumbar Aya
Gumbar ukku bala'i
Sarauniyar gumba
Da dai sauran kalolin gumbunan da muke dasu

*Kalolin gari*
Dakan jaraba
Kinfi budurwa
Jita salaf
Garin mallaka
Dakan Ni'ima
Bita zai-zai
Sabon budurci
Mai kwamson gyada
Dakan tabaje
Dakan kishiya in bakiyi bani waje
Dakan Amare
Emergency
Dakan sa buzu kuwa
Dakan sha yanzu magani yanzu
Da sauran kalolin da ban fada ba

09035027743 mmn yusuf skt

*Munada kalolin matsi da basuda illah Kuma masu matukar aiki da Kara lafiya ga HQ*

Matsin mallaka
Matsin a Daren farko
Matsin sabon budurci
Danba gigita
Matsin kishiya in bakiyi bani waje
Matsin Dan la'asar
Gam-gam
Matsin kinfi budurwa
Matsin rantse bakida kishiya
Matsin Dan mannau
Matsin k'yallen al'ajabu babban sirri kenan
Da sauransu

*AKWAI*
original Dan goshi ba bugi ba tare da Mahadi shi

Original man ayu
Original man damo da kitsensa
dan goshi sabon salo wanda ake amfani dashi ga mara

*Muna dahuwa Kamar haka*
Dahuwar kaza
Kazar yar gata
Kazar Amarya
Kazar maijego
Ciccibi
Yan shila
Nama
dambun nama Wanda yake jimawa ajiki
Kifi
Da dai sauransu

*Daga gefe Kuma akwai*
1,Maganin kiba maisa cikowa da laushin fata,
2,maganin gyaran nono 3in1
3 na hips mai ingaci dake aiki a cikin sati daya

Kalolin sabulun wanka masu gyara fata da Sanya hasken fata mai kyau
Sabulun tsarki Yana maganin duk wata matsala ta HQ Yana matsi ciki da waje Yana saukar da Ni'ima
Turaren jiki
Turaren daki

Please Login or Register in order to submit comment