Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaman jiran sa


Shi kuma sai da yayi wanka sannan yafito da alwalan sa, doguwar riga kawai yazira suka ta da Sallah, har suka idar yayi musu dogon addu'a inda daga nan kuma yafice zuwa kichen yaɗauko Plates da Spoon yasake kazan da Saleema taba shi, sai da yagama dai-dai ta komi sannan yayi wa Halwa magana akan tasauko su ci, don ita tuni ta haye kan gado tana lissafi cikin zuciyarta, tayi mamaki da ganin abinda ke gaban sa wanda hakan yatabbatar mata ya shirya ma daren, duk da ko kaɗan bata ji ƙamshin ba sa'ilin da yake sake wa illa motsin leda da take ta faman ji kuma bata yi tunanin dashi yazo ba


Babu musu tasauko duk da bata jin yunwa, amma kuma zuciyarta bata ba ta shawaran musa masa ba ko dan faranta masa da take son Yi, domin kuwa ta ɗau alƙawari faranta masa sosai a daren nan ta yanda zata nuna masa godiyar ta a duk kan komi da yayi mata kuma yana shirin sake mata wajen ƙwato mata haƙkin ta


Bata wani ci ba, shima haka ɗin, ita ta tattare komi zata kai kichen yadakatar da ita yakwasa yamayar


Kafin yadawo har ta shiga ta wanke bakin ta, yana shigowa tana fitowa sai tanufi kan gado tahaye



Shima ɗin Toilet ɗin yashiga, babu jimawa yafito yanufi gaban mirror, anan yagama shafe-shafen sa tamkar wani mace, sai da yabi ko ina nasa da turaruka kafin yakashe wutan yanufi kan gado ya haye...



A wannan dare Khalil da Halwa sun raya sa ne cike da farin ciki da annashuwa, tare da soyayya me tsayawa a rai ga duk kanin su, wanda tuni ko wannen su ya sanar da ɗan uwansa sirrin dake cikin ransa batare da sun an kare ba, har gabanin asuba kafin suka yi barci manne da juna tamkar zasu maida junan su ciki. 🤦🏻‍♀️🙄




*****
Washe gari a makare suka tashi dukan su, don lokacin ƙarfe 07:38am. Ne, Sallah suka gabatar a gurguje, suna idarwa Halwa tasake nannaɗe wa akan gadon don barci ne sosai a idanun ta tunda basu samu sun yi ishashshe jiya ba


Khalil kuwa shirin Office yayi a gaugauce Cuz lokaci ya ƙure masa, gashi babu daman zama agida tunda yana tsaka da soma wani Shari'a ne aiki yayi masa yawa sosai


Koda yagama shiryawa wajen gadon yanufa yasakar wa Halwa kiss a kumatu sannan yaƙara mata a goshin ta, yashafa kanta yana murmushi ganin yanda take yamutsa fuska tana gyara kwanciyarta,


Sosai idan tana yamutsa fuska take masa kyau ainun, ya kula hakan ya zame mata ɗabi'a ko da yaushe sai tayi


Gyara mata Bargon yayi yasake rufe ta yafice dasauri riƙe da briafcase ɗin sa, ɗakin Saleema yashiga sai dai babu ita ciki, har Toilet ya leƙa be ganta ba don haka yafito Direct yanufi kichen


Tana ciki kuwa tana haɗa musu Breakfast, daga ita sai doguwar riga iya cinya da gajeren wando baƙaƙe, sai hula me raga-raga shima baƙi tasaka a kanta, kasancewarta fara sai kayan sukai mata kyau suka sake haskata sosai



Ƙamshin turaren sa shi yasanar da ita zuwan sa, juyowa tayi dai-dai lokacin da ya'iso gaban ta idanuwan su suka haɗe waje ɗaya yayinda suka sakar wa juna murmushi


Ita tasoma gaishe sa, ya'amsa mata cikin fara'a yana janyo ta jikin sa, sannan yatambayi lafiyan ta da yanda tatashi


Murmushi tayi cike da tsananin ƙaunar sa aranta ta'amsa masa da "alhmadulillah Mijina, da fatan ƴar uwata tana ƙoshin lafiya?"



Sai da ya ɗan ja numfashi idanun sa na kanta yace "Lafiya ƙalau tatashi, but yanzu ta koma barci ne".


Narke fuska tayi tace "amma kuma baka yi Breakfast ba zaka tafi?"


"No sauri nake yi ina da aiki a Office in naje zan yi a can, ki kula min da kanki, Allah yamiki albarka".


Yamatso da bakin sa yasakar mata kiss a libs ɗin ta, har ya janye bakin sa sai kuma yamaida yahaɗe bakin su yayi socking na tsawon sokonni biyar kafin yajanye bakin sa, idanun sa yazuba mata yana kallon ta yayinda talumshe nata idon cike da tsananin shauƙi


"I Love You so much". Yafaɗa ahankali still yana kallon ta


Buɗe idanun ta tayi suka shige cikin nasa, yau ne ranan farko da ta iya juran kallon cikin idanun sa har na tsawon wasu mintuna batare da ta janye ba, tsantsan farin ciki ne yacika ta har takasa motsawa bare tasauke idanun nata har tafurta wani kalma


Murmushin sa me kyau yasaki yana saka hannu yaja hancin ta domin sosai yagane bata cikin tunanin ta a lokacin


Ɗan ƙifƙifta idanuwan ta tayi kafin tace "I Love You too My husband".


Sai kuma takau da kai tana murmusawa


Hannun sa yaɗago yakalli agogo kafin yasake kallon ta yasakar mata Peck a goshi yace "na tafi Byeee ki kula kinji".


Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace "Allah yatsare yadawo da kai lafiya".


"Ameen". Ya'amsa ta yana juyawa yafice dasauri



Ta daɗe tsaye a wajen tun fitan sa batare da tayi yunƙurin yin wani abu ba, in banda murmushi babu abinda take sakar wa, sai da tagaji don kanta kafin tajuya ga Ruwan zafin da take tafasawa, lokacin tuni ya tausa har ya gaji, dasauri tazuba citta da kanumfari a ciki, sai tasaka Lipton taƙara ruwa don ya gama ƙonewa, rufewa tayi taci gaba da sauran aiyukan ta


Cikin mintuna ƙalilan tagama komi sannan takwashe takai kan dainning, daga nan ɗaki tawuce tasillo wanka tashirya cikin jan atamfa me ratsin ruwan hanta, ɗinkin doguwar riga me hannun fanka, sosai rigan tabuɗe daga ƙasa kuma tayi mata kyau ainun, sai taɗaura ɗankwalin normal tayi Light makeup da yaƙara fito da ita sosai


Parlour tanufa da waya a kunne suna gaisawa da Ummi da takira ta.


Bata daɗe da zama ba itama Halwa tafito, har tayi wanka ta shirya cikin ƙananun kaya 🍑Baby Peach colourn riga da Skert, rigan me santsi ne da dogon hannu da aka saka bottles, tana da coller sannan kuma shara-shara ne domin har farar Vest ɗin da tasaka a ciki ana gani, skert ɗin kuma me Robber ne me ƙaramin tsagu ta baya dack peach colour, sai tasaka baƙin ɗankwali taɗaure kanta tare da zagaye gashin ta da ta taufke a tsakiyar kai


Masha Allah tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, sai dai ta saka Powder da kazal a idanun ta, fuskarta sai fitar da annuri yake yi tana ƙyallin amarci, kallo ɗaya kayi mata zaka san tana cikin farin ciki da walwalan da yakasa ɓoyuwa a face ɗin ta.



Lokacin da ta'iso Saleema ta gama wayan takalle ta tana murmushi tace "Ƴar uwa kinyi kyau sosai wlh, wannan ƙamshi da kike yi haka kowa yaganki ya ga Amarya?"


Dariya Halwa tayi lokacin da tasami wuri kusa da ita tazauna tana faɗin "kai Sister ban da sharri".


"Wlh dagaske nake yi, baki ga sai shaining kike yi ba, halan baki kalli madubi bane?" Saleema tasake faɗa tana tsatstsare ta da idanu ta sigan tsokana


Hararan ta Halwa tayi tace "Uhm to Ni dai ban gani ba gaskiya".


Saleema tace "to ina ga idanun ki ne, amma dai bari Barrister yadawo sai ya bambance mana gaskiya, yanzu tashi muje mu yi Breakfast dama yanzu nake Shirin kiran ki".



Tashi suka yi suka nufi wajen dainning ɗin inda Halwa tuni ta sauya hiran nasu.




Da rana da Khalil yadawo be jima ba yasake fita, sabida yace musu akwai abinda zai je yayi ba zai dawo ba sai dare, don haka su kaɗai suka zauna suka buɗe shafta suna ta hira


Da yamma sai ga Larai ta kawo Husna da Ahmad, Murna wajen Saleema kamar me, tsaban murna har rawa ta dinga yi tana shilla Ahmad tana cafewa shi kuma yana wangale mata wawulan bakin sa


Ai itama Husna sai tasaka mata kuka akan ba'a ɗaga ta ba



Me su Halwa zasu yi ita da Larai in ba dariya ba, sai suka koma tonon Saleema ɗin ganin yanda take ta nishi daƙyar taɗaga Husna dake mata kukan taɓara tana cewa "ita be ishe ta ba a ƙara ɗaga ta" yarinyan sai uban wayau kamar me


Shi dai Ahmad tunda aka kwantar dashi kan kujera wasan shi yaci gaba da yi don be san ma me suke yi ba



Basu bar Larai ta tafi ba sai da takai musu har magriba sannan tawuce gida.
[1/19, 6:29 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Twenty Nine*

________🎓 *ONE WEEK AGO*


Suna zazzaune akan dainning table suna yin breakfast wayan Haris tayi ƙara, sai da yakai Cofin shayin sa baki yakurɓa kafin yakalli wayan, ganin sunan Dady yafito ɓaro-ɓaro sai yayi saurin ajiye Cup ɗin yana kai hannu yaɗauki wayan tare da yin peacking yana karawa a kunne


"Aslm alaikum Dady.."


"Eh Dady ban fita ba but yanzu zan fita".


"Ok to".


Cire wayan yayi daga kunnen sa yaɗau tissue yana share bakin sa, be ce komi ba sai da yamiƙe yajanye kujeran da yatashi sannan ya dube su yace


"Ni zan wuce but bazan dawo ba yau sai zuwa dare insha Allahu sabida akwai inda zan je".


Miƙe wa Zubaida tayi don ta rakasa, yayinda Fahima tayi masa adawo lafiya tana ci gaba da breakfast ɗin ta


Har bakin ƙofan Parlour takai sa kafin tamiƙa masa briafcase ɗin sa suka yi sallama yafice


Mota yahau sai Family House ɗin su domin amsa kiran Dady da yayi masa.


Bayan ya shiga da motan sa tanƙamemen gidan nasu wanda yakasance me tsananin kyau da burge wa, duk da iyayen sa kaɗai ne agidan ada, but a yanzu Daddyn nasa ya dawo da ƙannin sa biyu da iyalan su suna zaune agidan, kasancewar su kaɗai Allah yaba ma iyayen su that's why mahaifin Haris ke ji dasu sosai, shiyasa da yadena siyasa a yanzu sai yagina wannan tanƙamemen gidan kuma yayi musu umarnin dawowa kowanne da nasa Part ɗin.


Fitowa yayi a motan yanufi cikin gidan, koda yashiga parlour'n; Daddyn sa ne da Mamyn sa zaune cikin damuwa, shi kansa Haris da yashigo ya tabbatar ba lafiya ba ganin yanda sukai tsamo-tsamo fuska duk babu walwala, gaishe su yayi suka amsa masa


Dady ne yadube sa fuskan sa da damuwa yace, "Haris".


"Na'am Dady". Ya'amsa masa ahankali yana kallon sa


Numfashi yaja kafin yace, "wacece Halwa?"


Wani irin bugawa gaban Haris yayi jin sunan Halwan, still sake tsatstsare Dadyn da idanu yayi ya kasa furta komi


"Kayi shiru ina magana?"


"Alhaji na fa faɗa maka kamar yarinyan nan ce da yayi haukan son ta har yakwanta a Hospital". Cewar Mamy idanun ta na kan Dadyn


Jinjina kansa Daddy yayi kafin yaɗauki Envelope ɗin dake kusa dashi yamiƙa wa Haris batare da yace uffan ba


Hannu na rawa Haris yasaka hannu kamar zai amsa sai kuma yatsai da hannun nasa yana cewa "Dady menene?"


"Abun da ka shuka ne yake son bibiyan ka Harisu, ashe dama Ciki kayi wa ƴar mutane har da rabon ɗiya atsakanin ku? To ka amsa gashi nan sun maka ka a kotu domin ƙwato mata haƙƙin ta".



Amsar Envelope ɗin yayi yaciro yasoma warware wa, sai da yagama karanta abinda ke ciki kafin yakalli Dad idanun sa cike fal da hawaye, ba komi yasaka shi shiga wannan yanayin ba sai famo masa gyambon da akayi, hakan na nufin cewa da rabon yasake ganin Halwa a rayuwarsa?


Murmushi yasaki me haɗe da hawaye, gaba ɗaya tsaban farin ciki ya kasa yin magana


Sai da Mamy tace, "Haris kayi magana mana kayi shiru, shin cikin ka ne ko kuwa?"


Cikin zumuɗi yakalli iyayen nashi yace "Wlh nawa ne, yarinyan da nake ta nema shekara da shekaru yau sai gata zan same ta cikin sauƙi, don Allah Dady kafaɗa min aina take yanzu inje inga ɗiyata, ina son ganin ta Dady har yanzu ina ƙaunar Halwa araina, Please Dady kashige min gaba wajen nema min auren ta, na yarda Wlh zan aure ta in dai sabida hakan ne zasu kai Ni kotu".


Baki sake suke bin Haris da kallo ganin yanda yakoma kamar zautacce


"To kai ban da abun ka ina zan ga yarinyan tunda ba ita ce tazo takawo takardan ba? daga kotu aka aiko don haka sai mu jira zuwa nan da Monday ɗin kamar yanda aka rubuto, yanzu abinda zaka yi kaje wajen Brr. Musbahu kuyi magana Idan nadawo zuwa gobe sai mu san abun yi".



Marairaice fuska Haris yayi yace, "Dady please asan yanda za'a yi anemo gidan da suke wlh bazan iya zama har zuwa Monday kafin in gansu ba".


Mamy tace, "To ya kake so ayi ne Haris? Kabari mana zuwa goben kamar yanda Daddyn ka yafaɗa, Ni kaina tun kafin naga yarinyan naji ƙaunar ta araina, wlh Ni farin ciki nayi gwara da suka miƙa case ɗin Court adawo mana da Jikar mu kusa damu tunda cikin naka ne".


Washe baki Haris yayi yace, "Ai Mamy nasan da cikin tun sanda iyayen ta suka kore ta, kuma na neme ta but ban same ta ba SHINE SILAN ciwo na".


Girgiza kansa Dady yayi yace "na ga alamu ko kunyan mu baka ji Haris, don baka ji nace zan hukunta ka ba ko?"


Sunkuyar da kansa yayi yana sosa ƙeya fuskar sa cike da murmushi Mamy ma na taya sa


"To je ka wajen aiki lokaci na ƙure wa, amma kasamu ku haɗu da Brr. Musbahu kaji ko?"


"To Dady". Haris ya'amsa masa yana miƙe wa tsaye


Sallama yayi musu yafice dasauri yana duba agogon hannun sa.



Maida idanun sa ga Mamy yayi yana cewa "kin gani ko? Abinda muka ja wa kan mu kenan silan sangarta yaron nan, da yanzu ban dena siyasa ba shikenan haka za'a ɓata min suna".


"To ya zamu yi Alhaji? yaro ne ka haife sa yanzu baka haifi halin sa ba, Ni ina ga ko da bamu sangarta sa ba dama zanen ƙaddaran sa ne haka, gashi abinda muka rasa muna fatan samu ashe da rabon zamu samu, wlh Ni har na ɗebe tsammani akan zan ga yaran Haris".


Murmushi Dady yayi yace "ban da abun ki duka-duka nawa Haris ɗin yake don be samu haihuwa ba har yanzu zaki cire tsammani? Ni ina ga saboda saka ran da muka yi ne shiyasa muke ƙosa wa, tunda dama matar sa ta taɓa ɓari bare muyi tunanin shine me matsalan, yanzu tunda yace "har yanzu yana ƙaunar yarinyan" kinga sai mu aura masa ita tazauna da ƴar ta, kin ga haɗo min kayana in tafi kar inyi late".


"To shikenan Alhaji Allah yasa mu dace dai". Tayi maganar tana miƙe wa don bin umarnin sa.





**** **** **** ***** *****

Abun zai baku sha'awa zaman Halwa da Saleema, sun ɗau kansu tamkar ba Kishiyoyin juna ba, kamar yanda kuka san suna zaune a baya haka yanzu ɗin ma suka ci gaba da zama da junan su, su kansu suna manta cewa Miji ɗaya suke aure bare har suyi kishin juna, ƙaunar da suke wa juna ƙauna ce ta tsakani da Allah



Shi kansa Khalil yana matuƙar alfahari dasu da jindaɗin kasancewar su mata a gare shi ganin yanda suka haɗa kansu fiye da Da, komi tare suke yi basu banbanta komi a tsakanin su, baza ka taɓa gane wanene me girki ba sai idan dare yayi wajen kwana, shine Khalil zai shiga ɗakin wacce take dashi, gyaran gida, girki, komi da komi tare suke yi, zaman su sai son BARKA, sai dai muyi musu fatan ɗaurewa ahaka. 😅



Yau ma Halwa ce tatambayi Khalil ɗin zuwa gidan su, domin tayi ƙudurin zuwa musamman don ganin Mama da kuma Zainab ƙawar ta, akoda yaushe suna ranta shiyasa yau tatambaye shi




Khalil be yi mata musu ba ya amince, duk da yaso yabi su sai dai aiki sunyi masa yawa, ga cases da yake dasu ciki kuwa har da nata, yanzu be da lokacin zama agidan ma



Saleema cewa tayi zata bi ta don haka suka yi shiri tare, kaya iri ɗaya suka saka, Jan Material Less ɗinkin riga da Skert, har da Gyalen da suka saka White colour da takalmin ƙafafun su iri ɗaya ne



Tubarakallah Masha ALLAH sun yi kyau matuƙa, kallo ɗaya kayi musu zaka san hankalin su akwance yake, in banda ƙyalli da ɗaukan ido babu abinda suke yi



Kasancewar yau Saturday Husna bata je school ba don haka har dasu aka shirya cikin kayan su masu tsananin tsada wanda yayi musu kyau ainun, duk wanda yaga yaran sai sun bashi sha'awa



Saleema da kanta tayi musu dreving, Halwa tazauna gefen su tana riƙe da Ahmad, yayinda Husna take zaune a baya.



Tunda suka shiga anguwan nasu Halwa take baza idanu tana kallon lungu da tsaƙo na cikin anguwan cike da tunano rayuwan ta na baya, har sanda suka kai ƙofar gidan su, gidan da tayi rayuwa aciki tare da sauyawan ƙaddaran ta


Numfashi tasauke lokacin da Saleema tatsai da motan dai-dai ƙofar gidan, fitowa suka yi gaba ɗaya yayinda Saleeman taɗauki Husna dake ta faman tsalle-tsalle



Gidan suka nufa suka shiga ciki da sallama


Wata matashiyar yarinya ne zaune tana haɗa lagwani a risho ta'amsa musu sa'ilin da taɗago kanta tana kallon su



Su ma dai kallon ta suke yi, yayinda Halwa taɗauke kanta daga gare ta tana bin gidan da kallo, gaba ɗaya an sauya gidan da sabbin abubuwa, musamman face_face da akayi wa gidan da kuma penti da akayi wa ko ina na gidan wanda ada babu shi..



Maganar budurwan ce tadawo da Halwa cikin tunanin ta tamaida idanun ta kanta, but aranta kuma tana mamakin wacece yarinyan don ita tasan ba cikin dangin su take ba bare kuma na Baba


"Ko dai matar Yaya Nura ne?" Tatambayi kanta aranta



"Ku shigo mana kun tsaya anan". Budurwan tayi maganar lokacin da tamiƙe tana share hannayen ta ajikin zanin ta



Shigowa suka yi suka nufo ɗakin da tanuna musu wanda ada ya kasance na Baba ne, shiga suka yi da sallama budurwan na biye dasu, sai da suka zauna tukun tasake fita tashiga ɗaya ɗakin, babu jimawa sai gata da ƙaton Jug cike da ruwa aciki, ajiye musu tayi tana faɗin


"Bismillan ku".



Babu wanda yayi ƙoƙarin ɗauka yasha a cikin su illa haɗa baki da suka yi wajen cewa "alhmadulillah mun gode".



Yayinda Halwa taƙara da faɗin "don Allah baiwar Allah wajen Mama muka zo".


"Mama kuma? Ai babu Mama gidan nan gaskiya, ko dai Aunty Zulaiha?" Yarinyan tafaɗa idanun ta akan Halwa


Girgiza mata kai tayi tace, "ina nufin masu gidan nan na asali, but kin san yaya Nura amma?"



Shiru yarinyan tayi tana tunani, sai kuma tagirgiza kanta tace, "a'a gaskiya sai dai kunyi ɓatan kai ne, nan daga Ni sai Auntyna da Mijin ta muke zaune anan ɗin, kuma shi sunan sa Aƙilu ne ba Nura ba, babu wasu kuma dake gidan nan, amma dai abinda nasani Mijin Aunty Zulaiha siyan gidan yayi, to ban sani ba ko waɗanda kike neman su ne suka tashi kenan?".



Murmushin yaƙe Halwa tayi bata iya cewa komi ba


Ganin haka yasa Saleema tace, "to don Allah ko kinsan inda suka koma?"



"Wlh ban sani ba".


"To shikenan bari mu tafi mun gode". Cewar Saleema tana miƙe wa tsaye


Itama Halwa tashi tayi suka fito waje, takalman su suka saka suka yo wajen gidan



"To yanzu ina zamu je?" Saleema tayi tambayar time ɗin da suka iso jikin motan su


Kallon ta Halwa tayi fuskarta da alamun damuwa tace, "wlh ban sani ba, Allah yasa ba wani abun bane yafaru dasu wlh hankali na ya matuƙar tashi, Nasan babu yanda za'a yi su siyar da gidan su in dai ba wani abu bane ke faruwa".


"A'a ki dena faɗar haka, babu komi insha Allahu ki cire komi aranki kinji ko?"


Murmushi Halwa kawai tayi tana sake rungume Ahmad dake hannun ta


Saleema tace, "To ko dai zamu tambayi maƙota ne?"


"A'a muje gidan su Zainab Nasan zamu ji komi acan idan ma wani abu ya faru ne".


Motan suka shiga suka nufi gidan su Zainab da babu nisa da nan ɗin, Saleema nayin parcking suka fito suka shiga gidan suna doka sallama tun daga zauren gidan


Umma na cikin ɗaki ta'amsa musu sallaman tana fitowa, duk da ta kalle su but bata gane Halwa ciki ba illa maraba da tayi musu tace musu "su shigo daga ciki".


Sai da suka zauna taba su ruwa sannan suka gaishe ta


Ta'amsa cikin fara'a tana sake duban su


"Sai dai ban gane ku ba wlh, ko dai wajen Zainab kuka zo?"


Murmushi Halwa tayi tace, "laa umma Halwa ce fa, baki gane Ni ba?"


Sake kallon ta da kyau Umma tayi sai kuma tace, "oh ikon Allah Halwa kece? Wlh ban gane ki ba ko kaɗan gaba ɗaya kin sauya min, Allah Sarki ashe da rabon zamu ganki?".


Still Murmushi Halwa take yi, tasake gaishe da Umman


Ta'amsa mata cike da fara'a tana bin ta da idanu


"ALLAH Sarki tamkar ba ke ba abin ki, waɗannan yaran naki ne?" Umma tayi maganar tana kallon Husna da talafe a jikin Halwan, yayinda Ahmad ke kan cinyan ta shima kwance


"A'a Umma ga mahaifiyar su nan". Halwa tayi maganar tana nuna Saleema


Jinjina kanta Umma tayi tace "Masha Allah to Allah ya raya su ta farkin Gaskiya".


"Ameen Umma, Ina Zainab ko bata nan ne?"



"Ai Zainab tayi aure kusan watanni bakwai kenan".



Halwa cikin tsantsan farin ciki tace, "Umma yanzu Zainab tayi aure ashe? Allah Sarki ashe bazan ga auren ƙawata ba?"



Umma na murmusawa tace, "ai kam Zainab tayi aure, ai dayake babu nisa da nan ɗin da gidan ta, sai in saka yara ma sukai ki idan zaki je".


"To umma amma naje gida ban ga su Mama ba, ko wani abun ya faru ne?"


Umma tace, "ai su Mama sun tashi tuni, ai ba anan anguwan ma suke zaune ba, Nura ya sai musu sabon gida, ashe baki sani ba?"


Murmushi Halwa tayi tana gyaɗa mata kai, kafin kuma tace, "eh umma ban sani ba wlh".


"To kin tafi can Gombe kin ɓoye ba dole ba, ina ga kema har auren kinyi bamu da labari ko?" Umma tafaɗa cike da fara'a


Still Murmushi Halwa tayi bata ba ta amsa ba



Sai Saleema ce taba ta amsa da "Eh umma itama tayi aure ai".



"Allah Sarki to Allah ya sanya alkhairi, bari inje maƙota in Kira yaro sai yakai ku gidan Zainab ɗin". Umma taƙarishe maganar tana tashi tafice.
[1/20, 4:52 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Thirty*

________🎓 A ƙofar gidan da Zainab take aure Saleema tafaka motar ta ta kamar yanda yaron da Umma tahaɗo su dashi yace musu, fitowa suka yi tare da sallaman yaron suka shiga cikin gidan, sallama suka yi duk kan su wanda yajawo fitowar Mahaifiyar Aliyu daga ɗaki


Amsa musu tayi cikin fara'a tare da musu maraba


Halwa ce tayi mata bayanin wajen Zainab suka zo


"Allah Sarki, to ku shiga tana nan ai, ku bi tanan ne ga hanyan sasan ta nan, sannun ku da zuwa". Still tayi maganar cike da fara'a tana sake musu sannu


Inda tanuna musu nan suka shiga, a bakin ƙofar ɗakin suka yi sallama


Zainab dake zaune a tsakar ɗakin ta, ta baje ƙafafuwa da ɗan ƙaramin cikin ta da be wuce watanni huɗu ba, yanzu ne ma yake shirin shiga na biyar ɗin, dayake ta taɓa yin ɓari, yanzun ma

Please Login or Register in order to submit comment