Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai ta yarda da cewa zuciyar ta na begen sa bane, wanda bata san cewa tuntuni ta afka kogin ƙaunar sa ba, kuma ko kaɗan bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tunda babu ta yanda za'a yi ta auri Mijin Saleema wacce ta taimaki rayuwan ta, tabbas idan hakan yafaru da ita ta gummaci ta mutu da ƙaunar sa amma baza ta taɓa ba ma zuciyarta damar wannan tunanin mara amfani ba.


Haka kwanaki suka shuɗe wanda har Halwa ta gama jarabawan ta an yi musu hutu


Kwanaki sun ci gaba da tafiya haka satikai yayinda aka tasar ma watanni, gashi yanzu har sun koma hutu sun shiga aji na uku


Ta ci gaba da rainon cikin ta yayinda yake ƙara girma, sosai cikin yake da girman mamaki wanda duk wanda yagani sai ya tausaya mata sabida tsaban girman sa, gashi ya saka ta ta kumbura ainun, kuma tun sanda yashiga wata na tara ta dena lafiya, yau ciwo gobe lafiya, tuni ta jingine karatun ta a gefe har sai sanda Allah yasauke ta lafiya


Shi kansa Khalil yanzu ba ƙaramin tausayi take bashi ba, duk da har a yanzu ba wai magana na shiga tsakanin su bane, idan ko kaji magana me tsawo ya haɗa su sai dai akan cikin ne


Tun farko shi ke kai ta awon cikin har yau kuma be fasa ba, wani lokacin su je da Saleema wani lokacin kuma su biyu suke zuwa.


Yau ma ɗin gaba ɗaya tare suka shirya zasu je asibitin, kasancewar yau ɗin Halwa tatashi jikin babu daɗi sosai, duk da a gobe ne Yakamata su koma Hospital a duba ta amma kuma Khalil ɗin yace su shirya su je yau


Saleema ke riƙe da ita har zuwa wajen motan, tabuɗe mata tashiga daƙyar sannan itama tashiga


Khalil na zaune cikin motan yana kallon su ta cikin mirror, sai da Saleema tarufe motan sannan yasaki ajiyan zuciya yana tada motan yanufi bakin Gate


Me gadi ya wangale masa Gate ɗin yafice da hanzari


Waya Saleema taɗauka takira Ummi


"Ummi ga munan zuwa asibitin".


"Subhanallah.. me yafaru ne ko haihuwar ne?"


Girgiza kanta Saleema tayi kamar tana kallon ta tace "a'a Ummi jikin ne dai babu daɗi shine zamu je".


Ummi tace "to gashi kuma yau ban samu zuwa ba naje duba jikin Sultan baya jindaɗi, amma idan kun ƙarisa sai ki nemi Sister A'isha ta duba ku".


"To Ummi ki gaishe da Aunty, Allah yabashi lafiya".


Daga haka sallama suka yi tasaka wayan a jaka, sannan takalli Halwa dake jingine da kanta jikin kujera ta rufe ido ruf


"Sannu Sister". Saleema tafaɗa kamar zatay kuka



Buɗe idanun ta tayi tasakar mata murmushi tana gyaɗa mata kai don baza ta iya magana ba sabida yanda take ji.


Koda suka isa cikin asibitin Saleema ce tariƙo ta sukai ciki, yayinda Khalil yabiyo su a baya yazauna a reception yana waya da Brr. Tahir


Sister A'isha tayi musu jagora zuwa wajen Likita, an duba ta babu wani matsala kuma ba haihuwa bane, don akwai sauran kwanaki a yanda suka ce musu, illa magani kawai da suka bata, sai ta ɗan kwanta na tsawon mintuna goma sannan suka sallame ta


Sun fito suka haɗu da Khalil ɗin, shi ya'amshi takardan maganin da suka rubuta mata yabar su nan yaje yasiyo sannan yadawo suka fito


Dai-dai sun kawo haraban Hospital ɗin, wani baƙar Mota dake fake a gaban Gate aka zuge glass ɗin, sai jin harbi suka yi wanda yasauka a kafaɗan Khalil dake gaban su yana tafiya, be tabbatar da abinda ke faruwa dashi ba yasake jin wani a setting inda aka sakar masa wancan, idanuwan sa ne suka juye lokaci ɗaya yasulale ƙasa riƙe da wajen, cikin second ɗaya ya dena motsi gaba ɗayan sa


Wanda faɗin nasa yayi dai-dai da kurma ihun da Saleema da Halwa suka yi suka bi shi da idanu da suka firfito dasu waje


Wani irin bugawa zuciyar Saleema tayi tay saurin riƙe ƙirjin ta tana kallon sa, bakin ta na rawa takira sunan sa da ƙarfi wanda yayi dai-dai da zubowar jinin bakin ta, sai kuma tasulale ƙasa tafaɗi babu alamun numfashi


Kuka Halwa tafashe dashi, tayunƙura tabi Saleeman ƙasa tana girgiza ta, lokaci ɗaya itama numfashin ta yaɗauke tafaɗi warwas sabida tsananin firgita da tayi


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".


Gaba ɗaya jama'ar wajen sun hargitse sai salati suke saka wa, masu kuka nayi masu guduwa nayi, ƙalilan mutane ne sukayo kan su Khalil dake yashe a ƙasa babu rai a jikin su.


Baƙar Motar nan wanda a cikin ta aka yo harbin tuni sun arce a tsiyace.
[12/6/2020, 9:59 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Seventeen*

________🎓 *2 Hours Ago*


Suna zaune gaba ɗayan su a reception sun yi cirko-cirko hankalin su duk a matuƙar tashe, babu abinda suke tsimaye yanzu sai fitowar doctors su san wani hali suke ciki


Ummi da Mom sai faman share hawaye suke yi domin labarin abinda yafaru da yariske su ba ƙaramin girgiza su yayi ba


Fitowar Babban doctorn da ya jagoranci duba Su Khalil yasaka suka nufe sa gaba ɗayan su suna jera masa tambayoyi ko wannen su yana tare da fargaban amsar da doctor ɗin zai bayar


Likitan be ce komi ba illa ce musu da yayi su bi sa Office


A tare Dad da Abba tare da Sameer suka bi bayan sa yayinda su Mom suka kasa haƙura suka take musu baya


Bayan sun shiga sun zazzauna likitan yacire Glasses ɗin sa yana saka Handkerchief yashare zufan goshin sa sannan yadube su ɗaya bayan ɗaya yasoma da faɗin


"To alhmadulillah zamu ce tunda komi ya zo da sauƙi ba kamar yanda muka yi zato ba, duk kan su suna da rai, kuma munyi nasaran cire masa harsashin dake jikin sa insha Allahu nan da kwana biyu zai iya farfaɗo wa, sannan..."


Sai yasaki numfashi yana ci gaba da faɗin


"Ita kuma Saleema gaskiya matsalan ta babba ne, domin sanadiyar hakan zuciyar ta tayi wani irin razana wanda yahaddasa mata matsala ainun, kuma hakan ya saka Zuciyar ta tana barazanar bugawa wanda Allah ne kaɗai yatsare be kai ga bugawan ba, but.. yanzu ta shiga Coma farfaɗowar ta sai ikon Allah.."


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ummi tafaɗa tana fashe wa da kuka, a tsaye take sai taja da baya tajingina da bango tana kuka kashirɓan jin halin da ɗiyarta mafi soyuwa a gare ta take ciki


Su kansu su Dad hankalin su yayi matuƙar tashi musamman Abba da yacire hulan sa cikin tashin hankali, babu abinda yake yi sai salati, sosai zuciyar sa ta taɓu da halin da yaji ƴar sa a ciki, sai dai ƙarfin hali da ya ara ya yafa ma kansa yayi juriyar hana kansa kuka


Shiru ne yaratsa a tsakanin su gaba ɗaya babu wanda ya'iya buɗe baki a cikin su


Girgiza kansa Doctor yayi cike da tausayin su yace "haƙuri zaku yi haka Allah yaƙaddaro, am.. ita kuma ɗayar Allah ya sauke ta lafiya duk da dai itama sakamakon gigitan da tayi jinin ta ya matuƙar hawa, sai dai muyi fatan samun lafiyan ta".


Kallon likitan suke yi don basu fahimci me yake nufi ba


"Yanzu ana duba lafiyan Babyn ne kasancewar be yi kuka ba, amma da zaran sun fito zaku ji bayani".


"Doctor Wai me kake nufi?" Cewar Sameer yana kallon sa da mamaki


Shima dai Doctor ɗin kallon sa yayi a rashin fahimta yace "me kenan kake magana akai Docta?"


"Likita maganar Halwa muke maka kuma mun ji kana maganar haihuwa?" Cewar Abba da yatari numfashin Sameer dake shirin magana


Cikin Ummi ne yayi ƙululu tuna abinda ke shirin faruwa, sam ta manta da cikin Halwa ɗin sai yanzu da ake maganar, gashi ba wancan likitan bane da yayi musu aikin bare yarufa musu asiri


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".


Rufe baki tayi kukan nata yatsaya cakk tana sauraron abinda doctor ɗin ke faɗi cike da nunkuwan tashin hankalin da take ciki


Hannun sa yahaɗe waje ɗaya yana kallon su yace "too Ni dai ina muku magana ne akan ita ɗayar yarinyan wacce suka zube tare da ɗiyar ku, tana da juna biyu kuma ta haihu ɗa namiji, wannan shine maganar da nake muku".


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.."


Gaba ɗaya suka faɗa a lokaci ɗaya, yayinda Abba yaƙara da faɗin


"To taya? Ta ina zata haifu bayan bata da juna biyu wannan wani irin abu ne?" Yayi maganar yana kallon Ummi da a yanzu hawayen fuskarta suka ci gaba da kwaranya


Ita kanta bata san me zata iya faɗa a yanzu ɗin ba amma kuma ta san dole ne kowa yasan abinda ke faruwa


"Kun ga yanzu ba wannan maganar zamu tsaya yi ba, mu je mu duba ta mu ganin ma idanun mu wataƙil ba ita ce ba". Dad yafaɗa yana tashi tsaye


Gaba ɗaya miƙe wa suka yi suka fito, da jagorancin doctor ɗin suka isa ɗakin da aka kwantar da Halwa wanda har a lokacin bata farfaɗo ba sabida alluran barcin da aka yi mata, sai dai kuma a lokacin an dawo da jaririn nata an ajiye sa kusa da gadon ta yana kwance sai wutsil-wutsil da ƙafafu yake yi yana ƙwalala idanuwa, baya kuka sai dai hannu ɗaya da yasaka a bakin sa yana ta gwagwiya


Shigowar su sai gaba ɗaya idanun su yasauka akan yaron wanda a lokaci ɗaya suka nufi gaban gadon, Mom CE tasaka hannu taɗago shi tana kallon sa cike da zallan mamaki wanda duk kan su haka fuskar su yanuna


Yaron bashi da maraba da Khalil sak kamannin sa har skin ɗin sa, duk da kuwa Halwa itama baƙa ce amma skin ɗin iri ɗaya ne dana Khalil komi nashi yaɗauko


Salati da tasbihi suka saki suna sake kallon yaron cike da tsananin zargin da yaɗar su lokaci ɗaya a zuciyoyin su, wanda kuwa gaba ɗaya sun ɗaura zargin ne akan ɗan Khalil ne wannan, babu ta yanda za'a yi ta raini ciki a gidan sa be san da cikin ba har kuwa ya isa haihuwa, hakan yasake tabbatar musu da zargin su gaskiya ne


Kuka Mom tafashe dashi tana kallon Dad tace "Alhaji kana ganin abinda nake gani kuwa? Khalil.."


Sai kuma tayi shiru takasa ƙarisawa sabida kukan da yaci ƙarfin ta


Al'amarin da yaƙara ta azzara zuciyar Dad da Sameer kenan, domin su ma tunanin da suke yi kenan a ran su na cewar wannan yaron Khalil ne


Gaba ɗayan su shiru suka yi kamar an yi ruwa an ɗauke, in banda kukan Mom da ƙaran fanka babu abinda ke tashi a ɗakin, har ta da Doctor tsayawa yayi shima yana kallon su batare da yasan me zai yi ba


Motsin Halwa shi yafargar dasu daga tunanin da ko wannen su yake yi a ransa


Ummi ce tayi saurin matsawa kusa da ita tana ɗaura hannu saman nata tare da kiran sunan ta


Ahankali Halwan tabuɗe idanu tana bin mutanen dake cikin ɗakin da kallo, kana daga bisani kuma tasauke idanun ta kan Ummi da har yanzu take zirarar da hawaye, lumshe idanun ta tayi sai tabuɗe su cike fal da hawaye, cikin wani irin karyewan murya tare da sanyi sosai tace


"Ummi... Ina Saleema? Bata mutu ba ko? Don Allah kar kice min wani abun ne yasame ta?"


Sai kuma tajujjuya kanta tana kallon ƴan ɗakin kafin tace


"Yaya Khalil.."


Shiru tayi tana zirarar da hawaye sosai kamar an kunna famfo


Likitan ne yamatso kusa da ita yana faɗin "ki kwantar da hankalin ki kinji kinga kina cikin wani yanayin da ba'a son jinin ki yasake hawa, duk kan su lafiyan su lau babu abinda yasame su kinji ko?"


Kallon Ummi tayi, sai Ummin tagyaɗa mata kai


"To yakamata ku bata wuri ta huta ba'a son tana hayaniya, sannan sai ku nema mata abinci taci za'a bata magani".


Likitan yafaɗa kafin yayi musu sallama yafice


Fitowa suka yi gaba ɗayan su suka bar Ummi a ɗakin, daga nan inda aka kwantar da Khalil suka wuce suka ganshi


Yana kwance babu riga an naɗe masa kafaɗa da bandage, tamkar matacce haka yake ko motsi baya yi, numfashi ma sai da taimakon Oxgyen


kuka sosai Mom tafashe dashi har sai da Dad yariƙo ta suka fito shima yana share hawayen sa, duk sun shiga tashin hankali matuƙa baka ma iya bambance wanda yafi shiga wani hali


Saleema kam ma basu samu damar ganin ta ba, domin an hana su ganin ta tunda har a lokacin akwai likitoci akan ta


Basu sake tayar da zancen yaron Halwa ba tunda kowa hankalin sa baya jikin sa duk da kuwa abun na ransu, itama kanta Halwan an sake yin mata alluran barci ta koma sabida har yanzu jinin ta be sauka ba, kuma suna son tasamu hutu sosai tayanda komi zai zama normal


Mutane sun soma tururuwan zuwa inda akai ta zuwa gaishe su, duk wanda yaji halin da suke ciki dole ya tausaya musu, Brr. Tahir ma yazo da matar sa, haka ma su Hakima da Abida drever ya kawo su, Nazeefa ma tazo sai kuka take yi tunda tashiga ganin Khalil, shiyasa Dad yasaka Sameer maida su gida gaba ɗaya, sai aka bar Mom da Ummi tare dasu Dad ɗin a asibiti


Kasancewar dare yayi bayan su Dad ɗin sun gama yin abinda yadace sai suka tafi, aka bar Mom wajen Khalil, ita kuma Ummi da Larai suka zauna wajen Halwa tunda Ita Saleema sun ce basu buƙatar kowa wajen ta, kafin su tafi da daren sai da aka bar su suka ga Saleema ta cikin Glasses, hakan ya ƙara ɗaga ma iyayen ta hankali sosai


Abba kuwa da tashin hankali yakoma gida, a ranan mutane da dama basu runtsa ba yanda suka ga dare haka suka ga rana


Halwa sai tsakar dare ta farka, tunda ta tashi Larai ta haɗa mata tea me kauri tasha, sannnan tace taba ma yaron Nono tunda sai tsala kuka yake yi domin shine ma yatashe ta, amma ina Halwa ko kallon ta bata yi ba bare ta tanka mata


Lokacin Ummi na sallah tana kai kukan ta wajen rabbi domin yaji ƙan ɗiyarta yaba ta lafiya


A karo na ba adadi Larai tace "Halwa ki shayar da yaron nan mana in dai ba so kike yi ya mutu ba, kinsan kuwa tun yaushe ake godo dashi yayi kuka be yi ba sai yanzu? Amma kuma kin ƙi kula sa bayan kuma kin san yunwa ke cin sa".


Kallon Yaron Halwa tayi wanda yake lulluɓe da kayan sanyi hannun Larai ta ƙanƙame shi, numfashi taja kafin ta kawar da kanta tace


"Bazan iya shayar dashi ba, sai dai ki kai ma Saleema shi domin yaron ta ne".


"Ban gane ba me kike nufi?" Larai tafaɗa a matuƙar ɗaurewar kai, dama tunda tazo take neman wanda zai amsa mata tambayoyin ta da suke cin ta arai bata samu ba, sosai tayi mamaki da aka ce Halwa ta haihu, bare kuma da taga yaron sak irin Khalil, kawai sai taɗaura wa zuciyar ta zargin cewa wannan yaron tabbas na Khalil ne, amma yanzu kuma zancen na son Shan banban..


Bata kai ga sake magana ba taji muryan Ummi tana faɗin


"Larai ki bashi ruwa don Allah ki lallaɓa sa yakoma barci".


"To Hajiya". Larai ta'amsa mata cike da ƙullewar kai, sai dai babu yanda zata yi tasake wani tambayan tunda ba'a bata dama ba


Ruwan taba ma yaron sannan taci gaba da lallaɓa sa yana ta ƙananun kukan sa


Halwa kuwa juya bayan ta tayi tarufe idanun ta kamar me barci, amma ina tunani ne fal a ranta na abinda yafaru a yau ɗin, hawaye tasoma zirarar wa tuna yanda taga Khalil ya faɗi ƙasa baya numfashi, take zuciyarta ta wani irin bugawa lokaci ɗaya ta zabura tana ɓarke wa da kuka.
[12/13/2020, 1:09 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Eighteen*

________🎓 Lokacin Ummi taci gaba da sallan ta, sai Larai ne tayi mata magana


"Halwa wai lafiya kukan me kike yi?"


Shiru Halwa tayi taci gaba da zubar da hawaye tare da haɗiye kukan nata


Larai ajiye yaron tayi lokacin yayi barci sai takoma shimfiɗar ta takwanta, babu jimawa kuwa barci yaɗauke ta, to bata san dai ya aka ƙare ba sai washe gari da suka tashi da safe


Lokacin yaron sai ɓaɓɓaka kuka yake yi amma Ummi na gani bata ce Halwa taba shi Nono ba, sai ma ɗaukar sa da tayi tana rarrashin sa, sannan takalli Larai da tasaki baki tana kallon su


"Yauwa Larai ke nake ta jira, don Allah kije yanzu ki amso min madaran sa wajen Sister A'ishah, naji ta shiru bata kawo min ba gashi kuma yana ta kuka".


Larai tace "to".


Sannan tanufi ƙofa tafice


"Itama kuma a lokacin Halwa ta gama cire kayan ta ta ɗaura zani tanufi Toilet don yin wanka


"Halwa kiyi wankan nan da kyau don Allah, yanzu zan zo idan Larai ta dawo sai in taimaka miki".


Gyaɗa kanta tayi tabuɗe Toilet tashige batare da ta furta komi ba.



Lokacin dasu Abba suka shigo asibitin a time ɗin ne kuma ƴan sanda suka zo, don haka basu shigo ɗakin ba sai da suka gama da Police ɗin, sun zo yin bincike akan harbin Khalil da aka yi


Bayan duk sun yi abinda yadace sai Dad dasu Brr. Tahir suka bi su can Station ɗin kamar yanda suka buƙata


Abba ne kaɗai yashigo ɗakin


Halwa na zaune saman gado tana shan tea, sai Ummi dake zaune kan kujera riƙe da jaririn tana sake bashi madara


Sallaman Abba ne yasaka duk suka ɗago kai suna kallon sa sannan suka amsa


Shigowa yayi ciki yana kallon Ummi fuskar sa da tsananin mamaki


"Ina kwana Abba". Halwa tafaɗa kanta a ƙasa


"Lafiya lau ƴa ta ya jikin naki?"


"Alhmadulillah".


"Masha Allah haka ake so Allah yaƙara lafiya".


A laɓɓa ta amsa masa da "ameen".


Ummi ma gaishe sa tayi tana goge ma Yaron baki wanda duk ya ɓaci da madara


Abba kallon Yaron yasake yi sannan kuma yamaida idanun sa kan Ummi yace "ya naga kina bashi wannan abun bayan ga mahaifiyar sa? Meyasaka baza'a shayar dashi ba?"


Shiru Ummi tayi bata bashi amsa ba


Yayinda itama Halwa tasake duƙar da kanta ƙasa tana sauraron Abban


"Ɗiya ta me yafaru da baki shayar dashi ba ake basa madara?"


Ummi ce tayi magana


"Abban Saleema akwai abinda nake son faɗa maka dama, amma kuma na bari ne sai mun samu nutsuwa, Halwa baza ta shayar da yaron ba sabida ta ba ma Saleema ne, kuma gashi ita bata da lafiya bare ta shayar dashi".


Idanuwa Abba yafid do waje yace "ban gane ba me kike nufi?"


Shiru Ummi tayi ta rasa ma me zata ce


Abba kallon ta kawai yake yi na wani lokacin kafin yajuya yafice


Ajiyan zuciya Ummi tasaki


Lokacin ne kuma su Mom suka yi sallama ita da Nazeefa suka shigo


Amsa musu Ummi tayi tana kallon su


"Sannu da zuwa Hajiya".


Murmushi Mom tayi tana aza idanun ta kan Halwa kafin ta'amsa, sannan suka gaisa a mutunce kafin tatambayi lafiyan me jiki


Ummi tace "alhmadulillah ga ta nan jiki ya wartsake".


"Allah yaƙara lafiya".


"Ameen ameen, ya shima Khalil ɗin?" Ummi tatambaya



Numfashi Mom taja kafin ta'amshi Yaron tana cewa "to dasauƙi dai za'a ce, Allah yarufa asiri gaba ɗaya yakuma basu lafiya gaba ɗaya".


"Ina kwana Momy". Halwa tafaɗa tana ajiye cup ɗin hannun ta


Da fara'a Mom ta'amsa mata tana ƙara wa da


"Ya jikin naki?"


"Da sauƙi".


Mom tace "to Allah yasawaƙe yaƙara muku lafiya".


Nazeefa ma sai a lokacin ta gaishe da Ummi


Itama ta'amsa cikin fara'a tana tambayan ta School ɗin ta



Daga nan shiru ne yagibta a tsakanin su


Nazeefa ita dai idanu kaɗai tazuba ma Halwa tana faman kallon ta, jiya da ita takwana a ranta, musamman yanda aka ce ita ce Maman yaron nan me kama da Khalil, duk da dai bata taɓa ganin ta ba amma a fahimtan ta tasan cewa itace ƴar uwan Saleema wacce take zaune da ita, har yanzu mamaki yaƙi barin ranta yanda aka yi yaron ta yake kama da Khalil, sannan kuma ita ba aure ne da ita ba, kuma har yanzu taƙi yarda da zuciyar ta akan cewa Khalil zai iya aikata mummunan wannan zunubin da ranta ke kitsa mata


Itama Mom yaron kawai tazuba ma idanu tana kallo, ta rigada ta yarda a ranta tabbas yaron Khalil ne wannan, sai dai bata so tayi maganar ne yanzu sai idan hankalin kowa ya kwanta duk da kuwa zuciyar ta a matse take da son sanin gaskiya


Tabbas ba'a shedan ɗan yau, bata taɓa tunanin Khalil zai iya aikata mummunan aiki irin wannan ba, a jiya tayi kuka sosai akan wannan al'amarin, har abun ma yafi tada mata hankali a bisa ciwon Khalil ɗin, yanzu tana ji tana gani an haifa mata jika shege


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tafaɗa a ranta tana ɗauke idanun ta kan yaron zuciyar ta cike da ƙunci


Numfashi taja kafin tamiƙa ma Ummi yaron tana faɗin


"Bari muje, dama zan koma gida ne sai anjima in dawo".


Amsar yaron Ummi tayi sannan tace "to Hajiya sai kin dawo".


Sallama suka yi daga nan suka fice ita da Nazeefa.



*****
Da yamma aka sallami Halwa kasancewar yanzu babu wata matsala dake damun ta, lokacin da zasu tafi Abba ya zo don haka shine yace su haɗo kayan su yakaisu


Halwa ta so taje duba jikin Khalil da Saleema amma babu hali, gashi har a lokacin ba'a basu damar sake ganin Saleeman ba


Lokacin da suka isa gida Halwa tawuce ɗakin ta kai tsaye, tana shiga ta'ajiye Yaron saman gado sannan tazauna tana riƙe kanta dake faman sara mata sakamakon kukan da tasha daga jiya zuwa yau


Husna ce tashigo ɗakin kasancewar ƙofan a buɗe yake, gaba ɗaya jikin ta da kayan ta ta ɓata shi da garin Flower, har ta a fuskarta zuwa gashin kanta dake ɗaure da Ribom duk Flower ne


Tunda tashigo Halwa take bin ta da kallo batare da ta motsa daga inda take ba


Ita kuma Direct wajen Halwan tanufo tana yarfe hannayen ta tana faɗin


"Mammaaa.."


Tana washe baki da ƙananun haƙoran ta guda shida da tamallaka



Gaban Halwan ta'isa tana miƙa mata hannu alamun ta ɗauke ta


Ita kuma ta zuba mata idanu wanda a baɗini tunani take yi don hankalin ta baya wajen Husnan


Ganin dai ba ɗaukan ta zata yi ba sai tajuya tafice tana sake kiran


"Mammaaa.."


Fitowar ta yayi dai-dai da fitowar Larai daga ɗaki tana kallon ta tazaro idanu tare da nufo ta tana cewa


"Ke.. ke.. ke haka kikai ma jikin ki wannan ɓarnan? Kai Husna ba kya ji yanzu ji be yanda kika ɓata jikin ki, da alamu dai kin zubar min da flowern nan?"


Ɓangale baki Husna tayi tana ƙyalƙyale mata da dariya


Ɗaukan ta Larai tayi tace "mu je in sauya miki kayan tunda kin ɓata".


Ɗan ƙaramin hannun nata taɗaura saman fuskar Larai ta damalmala mata da flowern da yaɓata mata hannu


Ita kuma Larai sai tacafko hannun tasaka a baki tana dariya


Still Husna ƙyalƙyace wa tayi da dariya tana janye hannayen ta


"Ƙaniyar ki, yarinya sai rashin jin tsiya, ke ko muje in sauya miki kayan inga kuma kin sake ɓata wa".


Daga haka tashige cikin ɗakin ta da Husnan a hannu tana mangare mata ƙeya.





Halwa na zaune a inda take har yanzu tasoma jiyo hayaniyan Abba da Ummi, abinda bata taɓa ji ba tun zuwan ta gidan, hakan yasa sosai tayi mamaki tayi shiru tana kasa kunne don jin abinda ke faruwa


Izuwa yanzu muryan Abba ake jiyo wa sosai yana ɗaga murya, duk da kuwa ba ta fahimtan abinda yake cewa amma tasan faɗa yake ma Ummi


Bata motsa

Please Login or Register in order to submit comment