Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"amma kinji kunya wlh, ƙatuwa dake shine kika sheƙo hanya da gudu ga mutane ko kunya ko?"


"To Aunty ki tsaya mana kiji me yakoro Ni, wlh Umma ce tatakura min akan maganar Nuran nan shiyasa na'ari na kare nayo nan".


Dariya Murjana tayi tace "kai wlh Zainab baki da dama, to Ni wai meye laifin Nuran nan kullum kina wahalar dashi? Magana dai taƙi ci taƙi cinye wa".


Taɓe baki Zaituna tayi tace "kema dai kya faɗa, bata da hankali Zainab ko kaɗan, wai inace duk kina wannan abun ne don Halwa?"


"Aunty baza ki gane ba wlh, nifa gaba ɗaya tun sanda yasoma nema na natsane shi, wlh koda ba batun Halwa aciki Ni bazan iya auren sa ba, kullum idan yazo min da nacin nan nasa kullum sake jin tsanar sa nake yi araina". Zainab tayi maganar cike da baƙin ciki


"Aiki ya ganki". Zaituna tafaɗa tana ci gaba da ƙullin ta


Murjana tace "kiyi ma kanki faɗa don Allah, ko wace mace tana burin tasamu masoyi me ƙaunarta amma ke kin samu kina wasa da damar ki, wlh Nura yana son ki tunda kikaga yana jure wulaƙancin nan naki, Zainab babu batun yaudara anan ki karɓe shi hannu bibbiyu tun kafin lokaci yaƙure miki, dama ce tazo miki har gida, idan kuma kikace zaki tsaya tunanin wata to zaki rasa wannan damar taki, ki duba magana ta".


Numfashi Zainab taja, baza su taɓa gane abinda take nufi ba, ita tayi alƙawarin wlh sai dai gawan ta za'a kai gidan Nura amma baza ta taɓa auren sa ba, koda kuwa Halwa ce tazo da kanta tace ta'aure shi, amma a yanzu tarigada ta ƙudurta ma kanta dole ne tasamu saurayi tayi aure ko Allah zai sa yabarta, ada dai bata da burin aure yanzu amma tunda taga abun yazo da haka tasan komi zai iya faruwa


Yanzu ma baza ta koma gidan ba sai dare, sai dai idan ta koma Umma tahaɗiye ta


Hannu tasaka tasoma tayasu ƙulla gishirin batare da tasake cewa komi ba


Su kuma tuni sun sauya zancen ma sun ci gaba da hiran su da suke yi.





.

*__________________________*

*BAYAN WASU WATANNI*

A halin yanzu Saleema tasake samun ciki a karo na biyu, kamar dai wancan haka tasha baƙar wahala watan shi ɗaya yafice bayan da tazubar da jini sosai kamar baza ta rayu ba


A wannan lokacin ne kuma tasan matsalan ta, tayi kuka kamar baza ta dena ba, har sai da iyayen nata sukai dana sanin faɗa mata sabida gudun tashin ciwon zuciyarta


Ita kanta Halwa ta taya ta kukan kuma ta tausaya mata sosai


Sai da tayi jinya na tsawon sati biyu a asibiti kafin a sallame ta



Tun daga ranan kuma Khalil yasoma bata maganin hana ɗaukan ciki batare da sanin ta ba, ita a ganin ta duk cikin drugs ɗin da aka bata ne a asibiti tunda wani lokacin shi ke bata magungunan, kuma bata taɓa saka wa aranta zai iya cutar da ita ba bare tayi tunanin wani abu, sosai yake matuƙar tausaya mata baya son tasake shan wahala kamar yanda tasha a baya, duk da yana son yara amma hakan shine mafitan da zai iya taimaka mata idan har yana tausayin ta


A sannu a sannu rayuwa taci gaba da tafiya, tun Saleema na damuwa da matsalan da take fama dashi tunda itama tana ƙaunar yara har dai tacire komi a ran ta, ta buƙaci a dawo mata da Husna taci gaba da riƙe ta amma firr Ummi taƙi tunda har yanzu jiya iyau take, yau lafiya gobe ciwo, kuma Ummi tayi tayi takawo mata ƴar aiki but Saleema ta baɗe ma idanun ta toka akan baza'a kawo mata ƴar aiki ba, ita ta saka a ranta duk ƴar aiki tana ƙwace Mijin matar gida ne, shiyasa take jin tsoron a kawo mata ƴar aiki watarana taƙwace mata miji, anan Ummi tace "to tunda baza ta yarda akawo mata me taimaka mata ba dole tahaƙura da rainon Husna har sai taji sauƙi", ba da son ranta ba haka tahaƙura


Khalil na iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya taimaka mata ainun, a haka zaman su yaci gaba har zuwa wani lokaci, kuma har a lokacin soyayyar Halwa na nan cikin zuciyar sa sai dai ya binne abun aransa tunda babu yanda zai yi


Ita kanta Halwan abun da take ji akan sa ne har yanzu takasa sakin jiki dashi bare su saba, ko magana zata iya ƙirga iya adadin da yataɓa shiga tsakanin su, sau tari idan tayi tunanin komawa gidan Saleema don ta tayata zama sai ta fasa, bata son ko kaɗan abinda zai sa su haɗa hanya, duk da har yanzu batasan menene musabbabin abinda yasa take jin haka daga gare shi ba, amma ita a ganin ta nesa dashi shine kwanciyar hankalin ta


Har yanzu kuma bata taɓa tunanin yin saurayi ba duk da kuwa ansha biyo ta, amma a ranan farko take taka ma mutum burki


Ummi kanta sai da tazaunar da ita akan tadena koran samari auren nata shine abunda yadace da ita, amma ita Halwa abinda take hangowa tabon da ɗa namiji yayi mata a rayuwa, ta tabbata ko wanene zai so ta idan har yasan da Husna wacce tahaife ta bata hanyar aure ba to zai tafi yabarta, bata son taba ma namiji yardan ta a karo na biyu, tunda wanda yafi kowa sanin ta a duniya kuma yafi kowa sanin me zata iya aikata wa ya juya mata baya akan hakan, tayi imani ko waye ma hakan zai mata, shiyasa maganin kar ayi kar a fara, ta yarda zata ci gaba da rayuwan ta ahaka har ƙarshen numfashin ta, idan har ba Nura bane yadawo gare ta to bata jin zata iya auruwa


A yanzu haka ta shiga aji na biyu, babu abinda tasaka a gaba sai karatu, ko ƙawaye taƙi yarda tayi har yanzu, sai dai mutunci kawai da take yi da wasu daga cikin ƴan ajin su


Har yanzu har gobe tana tunawa da ƙawarta Zainab, sau tari tana tunanin zuwa koda gidan su ne, amma kuma hakan na nufin kamar ta tona ma kanta asiri ne duk ranan da takoma wajen waɗanda suka santa, kuma hakan na nufin zubar da mutuncin su Baba kamar yanda suka guda tun farko, wannan dalilin yake saka wa tafasa zuwa.



.


*____________________________*

Baku tambaye Ni labarin Haris ba?


Tunda baku tambaya ba nima bari in ƙyale KU, byeeee👋👋👋 sai ajiman ku ko in CE sai gobe.😅🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️








_kar ku manta don Allah 🙏🏼ku danna Vote sannan kuyi comments don jin ra'ayoyin ku, na gode._
[11/24/2020, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Eight*

________🎓Haris ɗan wani babban attajiri ne ɗan siyasa, yanzu haka yana riƙe da kujeran Minister, shi ɗaya ne ɗa wajen iyayen sa duk da iyayen Familyn su ɗaya ne kuma babban Family ne dasu


Ya taso cikin gata sosai, babu abinda yarasa a rayuwan sa, wannan dalilin ne yasa yake taka duk wanda yaso yakuma hukunta duk wanda yake ƙi, sabida yana da ɗaurin gindin mahaifin sa don ko kaɗan baya ganin laifin sa


Haris yana da son mata da yawa sannan kuma yana da farin jinin ƴan matan, su da kansu ƴan matan suke kawo kansu wajen sa don yayi amfani dasu yabiya su kuɗi, duk da sau da dama suna kawo kukan su akan ya taimaka ya aure su amma shi a ganin sa babu macen da ta'isa yaso ta, shi dai kawai ya san mata a wajen sa su biya masa buƙata ne yajefar dasu don basu da wani Amfani


Ana cikin haka kwatsam yazo giftawa ta hanyar makarantar su Halwa yakusa bige ta, tun a lokacin da yaganta yakamu da tsananin kaunar ta har yana jin koda zai yi aure to babu shakka ita zai aura, duk da alokacin mafi rinjaye na zuciyarsa sha'awar ta ce, amma kuma ita kaɗai ce yake iya mata kallon wacce zata iya kasancewa matar sa anan gaba


Sai dai abinda be sani ba Halwa ta mutu a ƙaunar Nura a lokacin, duk da alokacin yaso yanuna mata kuɗi da gadara, amma da yaga yarinyan tana da taurin kai babu yanda zai yi yasame ta sai yakoma yana bin ta talalama


Sai kuma tsautsayi yagifta a ranan da Halwa tamare shi, wannan dalilin ne yaɗau alwashin sai yayi mata abinda baza ta taɓa mantawa dashi ba, domin kuwa tunda yake babu wanda yataɓa taɓa masa lafiyan jiki



A lokacin babu abinda be sani akanta ba, har soyayyar da suke yi da Nura ya san komi sabida yana da yaran da suke bibiyan masa ita


Abu na farko da yasoma yi shine neman Nura, har gida aka kawo masa Nura kuma yafaɗa masa buƙatarsa, a lokacin Nura be amince ba sai da yaji kuɗi Miliyan uku da yayi masa alkawarin zai basa in dai zai sadaukar masa da budurcin Halwa, shi a ganin sa idan har yakawar da sha'awar Halwa aransa to tabbas duk wani soyayya da yake mata zai gushe, wannan dalilin ne yasaka yanemi aikata mata fyaɗe bayan ya nemi taimako wajen Nura


Shi kuma Nura babu musu ya amince, a ganin sa idan har yasadaukar da budurcin Halwa akan wannan zunzurutun kuɗin be faɗi ba, kuma hakan yana ganin dama ce tazo mishi da zai yi kuɗi batare da yasha wahala ba, sannan yarigada ya saka ma ransa shi zai auri Halwa ɗin yarufa mata asiri tunda SHINE SILA, kuma shine zai ɗau alhakin duk abinda zai same ta don yarage girman laifin sa


Take nan ya amince sannan suka shirya yanda za'a yi har Halwa tazo hannun Haris, kamar yanda kuka gani abaya


Duk wannan abinda yafaru da Halwa da haɗin bakin Nura, sannan kuma lokacin da yaji maganar ciki hankalin sa yayi mugun tashi duk da alokacin yana tunanin bazai iya auren macen da yasan ba ta tare da mutuncin ta ba, anan ne dabara yazo masa har yanuna shi be san da maganar Fyaɗen da akayi mata ba don kawai ya yakice ta ajikin sa


Haris kuma tun sanda yayi mummunan aika-aikan nan yakoma Abuja kasancewar acan yake aiki, yana kula ma mahaifin sa da ƙaramar Companin sa da yabuɗe na Shinkafa, amma me tunda yakoma sai yazamana bashi da sukunin zuciya, ƙaunar Halwa tayi masa bakeke a rai ta hana sa saƙat, be taɓa tunanin sonta ya kai haka ba sai da yayi nisa da ita, ya so yadanne yajure ko zai manta da ita amma hakan ba me yiwuwa bane


Dole yadawo gida don ganin ta ko yaji sanyi a ransa, lokacin watan sa biyu acan kuma a lokacin tuni Halwa tayi wajen two weeks da barin gida


Dawowar sa da jin abinda yafaru wajen Nura hankalin sa yayi ƙololuwar tashi, yayi baƙin cikin koran ta da sukayi da cikin sa ajikin ta, ya sake shiga damuwa matuƙa, haka ya bazama neman ta ko Allah zai sa adace, domin ya rigada ya ɗau alwashin muddin yaganta zai aure ta kuma su raine abunda zata haifa, yana matuƙar son ta bazai iya rabuwa da ita ba, har Gombe can dangin mahaifin ta sai da yaje amma akace bata zo ba, su ma alokacin suka ji abinda yafaru, sai dai basu wani damu ba tunda Mama ta faɗa musu cikin Shege tayi suka koro ta nan ashe bata zo ba, su aganin su hakan ma da tayi yadace tunda ko tazo su ma ɗin korata zasu yi don baza su iya riƙe ta da abun kunya ba


Rayuwa ta sauya ma Haris matuƙa ya shiga damuwa sosai akan rasa Halwa wanda har sai da yakwanta ciwo, kullum bashi da buri idan ba yahaɗu da ita ba, a haka iyayen sa suka tilasta masa auren ɗaya daga cikin dangin su, domin su a ganin su idan har yasamu mata hakan zai dawo masa da nutsuwar sa, duk da dai basu san musabbabin abinda yafaru ba amma sun san cewa akan mace yashiga wannan halin, tunda be da abin faɗa sai sunan ta


Be musa musu da auren ba tunda shima hankalin sa baya jikin sa, ahaka akayi auren Amarya Zubaida tatare a gidan auren ta, da daɗi babu daɗi haka tazauna dashi tunda dama ita tana matuƙar ƙaunar sa, haka rayuwa taci gaba da tafiya har komi yalafa ma Haris duk da har yanzu ƙaunar Halwa na ransa sai dai yanzu ya cire duk wani damuwa aran sa ya dawo daidai yaci gaba da aikin sa, sai dai yaƙi komawa Abuja acewar sa anan Katsina Yakamata yazauna yayi aikin sa koda Allah zai haɗa sa da Halwa, baya son ko kaɗan yayi nisa da garin duk da be san cewa tana nan ko bata nan ba


Haka shekara ɗaya da watanni yashuɗe Zubaida bata taɓa koda ɓari ba, gashi burin iyayen sa su samu jikoki masu yawa tunda shi kaɗai Allah yabasu, hakan sosai yaɗaga musu hankali har shi Haris ɗin don shima yana son ganin yaran sa, don haka suka soma ziyartan asibiti amma sakamako ya nuna lafiyan su ƙalau lokaci ne be yi ba


Ana cikin haka Mahaifiyar Haris tasake ce masa yayi aure domin ita bata yarda matsalan ba daga wajen Zubaida yake ba, shi kuma Haris ko kaɗan baya ƙaunar tara mata da yawa don haka yabijire mata duk da kuwa ba wai yana son Zubaida bane amma suna zaune lafiya sosai sabida kyautata masa da take yi


An kai ruwa rana kafin Haris yayarda aka yi masa aure, don iyayen nasa duk sun goyi bayan ƙara auren nasa tunda suna son suga jikokin su nan kusa, duk da kuwa shekara biyu kenan da auren


Haris ya rigada ya sa aransa duk sanda yahaɗu da Halwa idan har zata aure sa to tabbas sai ya rabu da duk matan nasa tunda shi a tsarin sa mace daya yake so, sosai yaji daɗin cikin da tatafi dashi, kuma hakan yasa ya gane cewa shi ɗin yana haihuwa Allah ne be kawo ba, bashi da buri a yanzu illa yaga abinda tahaifa masa, ƙaunar ɗan nasa da be taɓa gani ba tuni ya shiga ransa sosai


Da maganar ƙara auren nasa da auren be fi wata biyu ba akayi komi aka gama, Amaryan sa Fahima ta tare a sabon gidan da mahaifin shi yagina masa tare da Uwar gida Zubaida


Itama dai tunda tazo ɗin bata taɓa koda ɓatan wata bane, har sanda itama tashafe shekara ɗaya curr kafin Allah yabata Ciki, zo kuga murna wajen Familyn baki ɗaya don kowa ya ƙosa yaga yaran Haris, iyayen sa babu wanda yakai su murna, haka akai ta tattalin Fahima da ɗan tayin cikin ta


Sai dai tunda tasamu cikin babu lafiya, yau suna asibiti gobe suna gida, yana watanni uku tayi ɓarin sa wanda har sai da aka dangana ga asibiti saboda yanda take zuban jini ta fita hayyacin ta gaba ɗaya, haka aka ɗauke ta ranga-ranga aka nufa Hospital da ita duk hankalin su a tashe.




______________________

A wannan lokacin itama Saleema ashe ciki ya shiga jikin ta, duk yanda kaso da dabara Allah idan yariga yaƙaddara abunsa to babu yanda zakayi, duk maganin hana ɗaukan cikin da Khalil yay ta bata amma a banza gashi ta samu shigan ciki har na wata ɗaya kamar yanda idan yakai hakan take ɓarin sa wannan ma karon hakan tayi, sai dai na wannan karon yafi na kowanne baƙin wahala


Tunda aka kai ta asibiti suke sintiri su ji me zai biyo baya amma babu likitoci babu alamun su, sai da akayi kamar mintuna 30 kafin suka fito suka nemi jini, tana buƙatar jini leda huɗu saboda ta bala'in zub da jinin ta


Haka aka ɗibi na Khalil dana Abba, sai aka siya ɗaya duk aka saka mata, su kansu Likitocin basa tunanin ma ko zata iya rayuwa a yanda take, ko numfashi bata yi sai da taimakon Oxgyen


Likitan ta yarigada yayi ma su Abba bayani dole sai an juya mata mahaifa sabida idan taci gaba da samun ciki to ƙarshe rasa ta zasu yi har abada, yanzu ma basu da tabbacin ko zata iya rayuwa.



Can ɗakin da aka kwantar da Saleema, su Ummi ne suka shiga tare da Halwa, gaba ɗayan su hawaye suke yi, yanda suka ganta tamkar matacciya hankalin su ya daɗa tashi ainun, Halwa kasa jurewa tayi tarufe bakin ta tafita dasauri cikin ɗakin, wani lungu tasamu tasoma gurzan kuka kamar zata shiɗe, kuka sosai take yi na tausayin Saleema



Haris lokacin yashigo asibitin kawo ma Matar sa abubuwan buƙata tare da abinda zasu ci, tunda a ranan kwanan ta biyu a asibitin kuma har tasamu sauƙi ana saka ran sallaman su yau ko gobe


Tunda yashigo idanun sa yasauka kan Halwa da tahaɗa kai da gwiwa tana ta sharɓan kuka, sosai yaji babu daɗi aran sa, haka kawai kuma yaji yana son ganin ko wacece yasan damuwar ta, sai kallon ta yake yi kamar yaje sai kuma yashige cikin asibitin yanufi ɗakin da aka kwantar da matar sa


Ƙanwar Maman Fahiman ce take jinyan ta, su biyu ne a ɗakin


Yana shiga suka gaisa ya'ajiye kayan da yazo dashi, tunda yazauna yarinyan da yawuce tana kuka ita ce tahana zuciyarsa sukuni, daga ƙarshe sai yamiƙe yafito don zuwa wajen ta yatambayi abinda ke damunta.
[11/24/2020, 9:03 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

_Wannan shafin naku ne masoyana na cikin group ɗin Khaleesat Haydar, na gode da nuna soyayyar ku gare Ni, Allah yabiya._❤️


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Nine*

________🎓Yana zuwa wajen sai dai babu ita, ya dudduba amma be ganta ba don haka yakoma cikin ɗakin da aka kwantar da Fahima, dama kawai don ta tsaya masa a rai ne but tunda yaduba be ganta ba sai be sake tuna ta ba har yabar asibitin.



____________________
Halwa tana tashi a wajen komawa ɗakin tayi, sai dai tana zuwa bakin ƙofa kunnuwan ta suka jiye mata maganganun Abba dake faɗa ma Ummi matsalan Saleema ɗin, sai kawai tazame nan ƙasa tasaki kuka me sauti, daga inda take zaune tana jin kukan Ummi itama don takasa jurewa, sai da Abba yayi ta rarrashin ta yanuna mata zata iya damun Saleema idan bata dena kukan ba tunda an ce kar suyi hayaniya da zai dame ta, hakan yasa Ummi tarage kukan ta takoma kukan zuci da hawaye



Abba ne yafito yatarda Halwan anan ƙasa tana nata sharɓan kukan, gaba ɗaya idanunta sun rine sun kumbura suntum wanda kallo ɗaya zaka yi mata katabbatar ta jima tana kuka yanda har fuskarta sai da yakumbura


"Subhanallah.. Daughter me kike yi anan? Kukan me kike yi?" Yatambaye ta yana saka hannu yaɗago ta


Halwa bata iya bashi amsa ba sai ƙara sautin kukan ta da take yi, duk da kuwa ta toshe bakin ta da Hijabin ta hakan be hana an ji fitan sautin kukan ta ba


Dafa kanta Abba yayi cike da ƙarfin halin sa yace "kiyi shiru kinji? insha Allahu ƴar uwanki zata samu sauƙi ki dena kuka haka nan".


Ya daɗe yana rarrashinta kafin yabuɗe mata ƙofar ɗakin yabata umarnin tashiga, shi kuma yajuya yatafi.




Tana shiga taƙarisa gaban gadon inda Ummi ke zaune ta tasa Saleema agaba tana zirarar da hawaye


Gefen gadon taɗan ɗofana mazaunan ta tana kallon Saleeman itama, wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta sabida tausayin ta, lumshe idanuwan ta tayi tabuɗe su akan Ummi da har yanzu ko ƙifta idanu bata yi, cikin rawan murya tace


"Yanzu shikenan Ummi.. baza ta haihu ba? Meyasa za'a juya mata mahaifa? Meyasa baza'a nema mata magani ba? Don Allah.. kar ayi.. gaggawan wannan..aikin". Taƙarike maganar nata cikin tsananin rawan baki da jan numfashi


Itama Ummi numfashin taja cike da sanyin murya da idan kaji zaka san tana cikin matuƙar damuwa tace "Ni kaina bansan wani irin ciwo ne wannan dake damun ta ba, sai dai sun tabbatar mana akwai wasu tsirrai a cikin mahaifan ta da baza su taɓa bari ta raini ciki ba, sannan kuma mahaifan ta babu ƙarfi ko anyi mata aiki ba lallai ne asamu nasara ba".


Halwa tace "Ummi idan har za'a iya dashen cikin ajikina Ni zan iya rainon mata, zan haifa mata idan har zata ga ɗan ta a duniya, a shirye nake in sadaukar da komi nawa don samun farin cikin ta".


Ummi kallon Halwa take yi kamar bata gane me take nufi ba


Sai Halwan tasake cewa "Ummi ki duba magana ta, idan har Saleema tasan da cewa an juya mata mahaifa hakan na nufin baza ta ƙara haihuwa ba to zata shiga matsanancin damuwa, kuma kinsan tana da ciwon zuciya idan hakan yayi tasiri zamu iya rasa ta, tunda ina da hanyan taimakon ta zan rainan mata cikin in haifa mata sai in bata yaron ta".


"Halwa idan har na amince za'a yi hakan Mahaifin ta da Mijin ta ba lallai su yarda ba, bansan me zan faɗa musu ba".


Daga maganar Ummin sai suka yi shiru gaba ɗayan su suna tunani


A lokacin ne Mom suka zo ita dasu Dad har da Khalil dasu Sameer, gaigaisa wa akayi tare da tambayan me jiki?


itama Halwa tagaishe su suka amsa cikin farin ciki, daga haka bata ƙara cewa komi ba tana jin su suna maganan su, daga baya su Dad suka fita ɗakin yarage daga Mom sai Ummi sai ita Halwan, har sai da likita yazo kafin suka fito waje


Sai dare ita Mom tatafi gida lokacin Khalil ya dawo sai yatafi da ita


Ita kuma Halwa sai da Larai takawo musu abinci sannan suka koma tare


A ranan Ummi ta kwana ne da maganganun Halwa a ranta, sosai tahau tunanin neman mafita, daga ƙarshe kuma tayanke shawaran zata soma tuntuɓan mijin Saleema da maganar idan ya amince tasan sauran babu matsala


Da sassafe Khalil ɗin shi yasoma zuwa, Ummi batayi ƙauron baki ba tafaɗa masa komi da kuma taimakon da Halwa tace zata yi ma ƴar su


Khalil shiru yayi kawai yana sauraron Ummi har sanda tagama maganar ta, lokacin hawaye kawai take yi


Sai tausayin ta duk yakama sa, shi kansa zai so hakan sabida tsananin tausayin Saleema dake ransa, yasan da cewa idan har taji komi zata shiga wani hali sosai, ba abu ne me sauƙi ba ace baza ka taɓa haihuwa ba bare kuma fa waɗanda suke son ƴaƴan, yana matuƙar tausayinta ta yanda Allah yajarabce ta da cututtuka kala-kala, gwara shi namiji ne yana da damar da zai iya ƙara aure yahaihu da wata matar, idan har hakan shine maslaha to ya yarda zai taimaka mata, idan tasamu ɗanta ko guda ɗaya ne hakan zai sanyaya mata ranta, sannan ma ba wai wata daban ce zata rainan masa cikin ba Masoyiyarsa wacce yake matuƙar ƙauna aransa ne zata raini cikin, ko babu komi zai yi farin ciki da hakan


Don haka koda yanuna ma Ummi ya amince tayi farin ciki sosai, su biyun suka nufi office ɗin Doctor sai suka bar Halwa don alokacin tarigada tazo


Sun jima suna tattaunawa, duk da shi doctor ɗin ya nuna musu kuskuren yin hakan tunda musulunci Bata yarda da hakan ba, amma kuma duk kansu sun rigada da sun san hakan mafita kawai suke nema, ba don komi ba sai dan taimakon Saleema, sun manta da cewa haka ƙaddaran ta yake, sai dai sun san idan da lafiyan ta lau ba ta ɗauke da ciwon zuciya tabbas haka nan zata ɗau ƙaddaran ta


Kasancewar

Please Login or Register in order to submit comment