Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da lazimin ta.




***** ******* ***********

Shigowan sa kenan cikin gidan nasa, tun gama shari'an gaba ɗaya suka wuce gidan su sai yanzu yadawo, ahankali yabuɗe ɗakin nasa yashiga, aje komi yayi tare da cire kayan jikin sa yawuce cikin Toilet wanka yayi sannan yafito, ko mai be shafa ba yaɗauko kayan sa ƙaramar riga fara da dogon wando robber shima fari yasaka, fitowa Parlour yayi yazauna saman 3sitter, wayoyin sa da suke kashe duk ka biyun yaɗauka yakunna, saƙonni ne suka soma shigowa, sai da suka gama gaba ɗaya sannan yasoma buɗe wa yana gani, duk yawanci Abokan sa ne da waɗanda yasani suke tayasa murna, be fi guda goma yabuɗe ba yamayar da wayan ya'ajiye tare da kwanciya yana ɗaura hannun sa ɗaya saman fuskar sa yalumshe idanun sa, ya ɗau tsawon awanni yana ahaka, babu abinda yake yi sai tunani, sai da yaji kiraye-kirayen sallan Magriba kafin yamiƙe a kasalance yashiga Toilet ɗin dake parlour'n yaɗaura alwala yatafi masjid.




*** ***** **** ****

*BAYAN KWANA BIYU*

A kwana biyun nan sosai jikin Saleema yayi sauƙi, don haka aka sallame su suka koma gida, gaba ɗaya Ummi tahaɗa su tana basu kulawa kasancewar har alokacin itama Halwa sosai take fama da jikin ta, laulayi ya sako ta gaba ko abinci sai anyi dagaske take ci, gaba ɗaya ta rame sai haske da tayi, komawar su gida ma sai da Ummi tasake saka mata Drip sabida yawan aman da take yi.

Yanzun ma kwance take saman gado, duk ta ƙudundune jikinta cikin bargo tana ta rawan ɗari, Saleema kuma na zaune gefen ta tabuga uwar tagumi tana kallon ta, fuskarta ya nuna damuwa sosai kamar tayi mata kuka, cikin tsananin tausayawa tace

"Wai meyasaka baza'a cire cikin bane? Kina shan wahala da yawa.."

Ummi da shigowar ta ɗakin kenan taji maganar da Saleeman take yi tayi saurin katse ta

"Kull.. kar in sake jin kin bata wannan shawaran, bakisan haramun bane zub da ciki? Bana son in sake jin kin faɗa mata hakan kinji ni?"

Gyaɗa kanta Saleema tayi tace "Toh Ummi".

Zama Ummin tayi tana ajiye Coolarn da tashigo dashi tare da plate tace

"Tashi kici abinci Halwa, Faten wake ne nasanya akayi miki nasan zakiji daɗin sa kinji? Tashi maza kici".

Saleema tace "to Ummi kawo in zuba mata".

"Ai har dake zakici, in kun gama sai kusha maganin ku ni zan tafi asibiti, sannan nasaka Larai tayi muku Farfesun kayan ciki, shima sai kuhaɗa dashi kuci, ni natafi ku kula da kanku sosai kunji?".

Gyaɗa mata kai sukayi, daga nan ficewa tayi bayan Saleema tayi mata "adawo lafiya". Tana fita Saleema tabuɗe Coolar'n tazuba musu Faten waken da yaji nama sai tashin ƙamshi yake yi, kallon Halwa da har yanzu take kwance tayi tace

"Tashi muci".

Sai kuma ta'ajiye abincin a ƙasa tana matsowa kusa da ita tataimaka mata tasauko, zama sukayi a ƙasa suka soma ci, Halwa bata wani ci sosai ba tamatsa gefe tana ɗan sakin nishi, Saleema kallon ta tayi tana shirin yin mata magana sai taga tasoma kwarara amai, dasauri tamatsar da abincin tamiƙe tana riƙo ta ganin tana shirin faɗuwa, sai faman sannu take mata kamar zatayi mata kuka, sai da ta amayar da duk wani abinda ke cikin ta sannan tatsakaita tana numfarfashi cike da galabaita, taimaka mata Saleeman tayi suka shiga Toilet tawanke jikin ta kafin suka fito, zaunar da ita saman gadon tayi takoma Toilet ɗin taɗauko kayan Moping tawanke wajen tare da sharewa, sai tadawo tazauna tana kallon Halwan da itama tazuba mata idanu tana jingine jikin gadon, murmushi tasakar mata cikin sanyin murya tace

"Na.. go..de".

Waro idanu Saleema tayi tana mata alama da hannu "na mene?"

"Bansan da me zan saka miki ba, kin taimaki rayuwata sosai, kin zame min ƴar uwa alokacin da narasa kowa nawa, sannan kin kawo ni gidan ku kin maishe da ahalin ki ahalina, wlh bansan da bakin da zan miki godiya ba, haƙiƙa bazan taɓa manta ki cikin rayuwata ba, daga yau kece komi nawa kuma insha Allahu zan ɗauke ki ƴar uwa kuma wacce zata maye min gurbin ƙawata Zainab".

Runtse idanun ta tayi jin hawaye na son zubo mata, Sai kuma tabuɗe tana murmushi tace

"Daga yau bazan sake kewarta ba tunda har nasami madadin ta".

Riƙo hannun ta Saleema tayi itama tana murmusawa tace

"Ki dena faɗan haka, Ni nayi ne duk sabida Allah, sannan naji daɗi da kika ɗauke Ni ƴar uwa ƙawa, dama na daɗe ina jiran ranan da zan sami tawa ƴar uwan, sai gashi Allah yabani ita har gida".

Sai kuma tasaki dariya har haƙoran ta suna bayyana, tamiƙe tsaye tana faɗin

"Bari in amso mana ferfesun sai ki ƙara ci tunda kin amayar da wannan da kikaci, ina zuwa".

Daga haka fita tayi dasauri, bata jima ba tadawo ta'ajiye musu a saman gadon, sai taɗauko maganin Halwan dake ajiye a kan drower tadawo tazauna, nata tabuɗe taɓalla tasha tare da korawa da ruwa, sai takalli Halwa tana sakar mata murmushi tace

"To kema kici sai kisha maganin ko?"

Gyaɗa kanta tayi tana saka hannu tashare hawayen da suka sulmiyo kan kuncin ta batare da Saleeman tagani ba, bayan ta ɗan ci kaɗan sai tasha maganin sannan taci gaba taci, Saleema kuwa cire hannun ta tayi tana yin gyatsa tare da faɗin

"Alhmadulillah Ni dai na cika cikina, saura ke".

Kallon juna sukayi sai suka saki dariya gaba ɗayan su

"Kinsan me?" Cewar Saleema tana shafa cikin ta

Girgiza mata kai kawai tayi tana kallon ta

Cikin sakarci irin na yaran masu kuɗi tace "Idan kin haihu ko Ni zaki bama Baby, Ina son shi ni zan kular miki dashi, zamu riƙa wasa tare in koya masa karatu da komi da komi, kinji zaki bani ko?"

Saurin sauke kanta ƙasa Halwa tayi tana jin hawaye na zubowa daga idanun ta, sai tayi saurin tare hannun ta tasharce shi, hannu itama Saleeman takai tana sharo mata hawayen cikin sanyin murya tace

"Kuka kike yi? Ni ce ko? Kiyi haƙuri Don Allah".

Ɗago kanta tayi tana kallon ta tare da girgiza mata kai, still tana hawayen tace

"A'a ba don ke nake yin kukan ba, kawai na tuna da gida ne, ina matuƙar kewar su Mama, ina matuƙar kewar su sosai.."

Sai tafashe da kuka, nan da nan jikin Saleema yasoma yin rawa sai itama tafashe da kukan

_"Bamu san ya zamuyi ba idan muka rasa Saleema, muna tsananin ƙaunar ta ni da mahaifinta, kuma ita kenan gare mu ita kaɗai ce mallakin mu, amma kuma Allah ya ɗaura mata ciwon da muke ganin koda yaushe zamu iya rasa ta, a kullum burin mu shine mu saka ta farin ciki.."_

Tunawa da maganganun Ummi ne yasaka Halwa saurin katse kukan ta tana kallon Saleeman da ita har yanzu bata dena nata kukan ba, dafa kafaɗunta tayi cikin murmushi tace

"Menene na kuka ke kuma? Kinsan da cewa baki da lafiya don Allah ki dena kar wani abu yasame ki".

"Taya kike tunanin zan dena bayan na ganki cikin ƙunci? Ina matuƙar tausaya miki idan natuna labarin ki, bana jin daɗi ko kaɗan idan naganki cikin damuwa".

Dariya Halwa tayi tace "to na daina ai, kuma Ni ina kuka ne sabida farin ciki, farin cikin na sami ƴar uwa me ƙaunata, wacce take ƙaunar abinda zan haifa tun kafin yazo duniya, insha Allahu idan har nahaife shi na baki shi kyauta, daga lokacin kece mahaifiyar duk abinda zan haifa".

Itama dariya Saleema tayi tace "wayyo naji daɗi sosai, bari su Ummi su dawo zan sanar musu, amma kuma kinsan me Yakamata in saka masa a suna?"

Girgiza kanta Halwa tayi tana dariyan shirmen Saleema, wani lokacin in tana abu tamkar ƙaramar yarinya, kuma duk sangarta ne da yayi mata yawa, sai da ta ɗan yi tunani kana tawashe baki tace

"Idan mace ne zan saka mata sunan Ummi, idan kuma na miji ne sai in saka masa Abbana".

Murmushi Halwa tayi tace "hakan yayi".

Matsowa sosai Saleema tayi kusa da ita kana tace "yauwa yanzu ya jikin naki dasauƙi ko?"

Gyaɗa mata kai tayi, duk da tana jin ciwo amma bazata iya nuna mata ba coz yanda taga tana nuna damuwarta sosai

"Ok bari in baki labari, zan baki labarin school ɗin mu tare da ƙawaye na".

Labarin tasoma bata suna ta dariya kamar basu ba, kuma duk kan su idan kakalle su zaka gane ba ishashshen lafiya ne dasu ba, sai dai ƙarfin hali kawai da suka ara suka yafa, daga ƙarshe ma barci ne yaɗauke su sakamakon maganin da suka sha akwai na barci aciki.












_Allah Sarki wannan shi ake cewa gamon jini, Allah yahaɗa mu da masu son mu fisabilillahi._❤️🙏🏼
[10/1/2020, 1:46 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```


.

*CHAPTER 34*


Kwance take saman gadon ta daga ita sai ƴar shimi fara ƙal, sai jan wando robber da yamatse ta sosai wanda da kaɗan yawuce gwiwarta, wayan ta dake ajiye saman gadon ne tasoma ringing sai tajawo tana kallon screan ɗin wayan, ganin sunan HONEY yafito ɓaro-ɓaro yasaka tayi peacking call ɗin tana kangawa a kunne, shiru tayi tana sauraron sa sai kuma ta'ajiye wayan tamiƙe tsaye tana ɗaukan Red colour Jaket ɗin dake ajiye saman gadon tasaka, Jaket ɗin irin me buɗaɗɗen gaba ne sai Belt da aka saka a iya tsakiya wajen cikin ta, iyakan cinyan ta yatsaya mata, sai taɗau Facing cap shima Red tasaka tafito, Ahmad ne kaɗai yake zaune Parlourn yana kallo takalle shi tace

"Idan Mami tafito kasanar mata nafita wajen Sharif".

Ahmad yace "ok".

Fita tayi tanufi inda yake tsaye jikin motan sa, tun fitowan ta yake kallon ta yana murmushi har ta'iso wajen

"My beautiful girl". Yace hakan yana sake faɗaɗa fara'ar sa

Ɗan cije laɓɓanta tayi tana kallon sa itama cikin murmushi tace "ya kake?"

"Lafiya, kefa?"

"Lafiya lau". Tayi maganar tana jingina da motar itama kamar yanda yayi, sai dai facing juna suke yi

"Kinsan me?".

Girgiza kanta tayi still tana kallon sa

"Kullum sai in riƙa jin ƙaunar ki na ƙara zauta Ni, har yanzu nakasa sabawa da yanayin da nake ji a kanki".

Sai ya ɗan yi murmushi yana shafa kwantaccen ƙasumban sa yaƙure ta da ido yace

"Na ƙosa Kausar kikasance mallakina, ina ji ajikina kamar in ban yi dagaske ba zan iya rasa ki".

Kallon da take masa ne yasauya zuwa mamaki, amma sai batace komi ba taɗauke kai tana jin zuciyar ta na bugawa, kiran sunan ta Sharif ɗin yayi, sai taɗago kai kawai tana kallon sa

Yace "har yanzu baki bani amsa ba akan maganar da mukayi dake".

"Wace magana kenan?" Tatambaye sa cike da rashin fahimta

Murmushi yayi yace "har kin manta maganar da mukayi lokacin da zamu dawo Nigeria? Haba Dear yakamata ki bama zance na muhimmanci, Ni nayi miki alƙawari wlh zan bar ki kici gaba da aikin ki koda munyi aure, be kamata mu zauna muna ɓata lokaci ba bayan kinsan da cewa mun fahimci juna, kuma iyayen mu sun san komi, to me muke jira?"

Shiru kawai tayi tana sauraron sa har sanda yadasa aya, sai kawai tasaukar da kanta ƙasa tana tunani, gaba ɗaya murmushin dake fuskarta ya ɓace, sai damuwa da yamaye gurbin

"Kausar".

Saurin ɗago kai tayi takalle sa

"Wai me ke damun ki ne? Na kula gaba ɗaya kin sauya yau meke faruwa?"

"Ban jin daɗi ne Honey".

"Eyya shine baki sanar min ba? Kinsan bana Son abun da zai dame ki, yanzu meke miki ciwo?"

Yaƙe tayi tana kallon sa tace "kar ka damu kawai gajiya ne yahaddasa min ciwon kai".

"Eyya sorry, kije gida to sai muyi maganar awaya, Allah yasawaƙe kinji?"

"Ameen".

Sake sallama sukayi sannan tajuya tatafi, shi kuma yabi bayan ta da kallo har sanda tashige, ajiyan zuciya yasauke yana buɗe motan sa yashiga yabar gidan

Ita kuma tana shiga parlour tawuce ɗakin ta dasauri, akan gadon ta tafaɗa tana sauke numfashi, shiru tayi na ɗan wani lokaci kafin tajawo wayan ta tana latsawa, Numban Khalil talalubo sai tatsaya kawai tana kallo, daga ƙarshe sai tadanna masa kira, har yatsinke be ɗauka ba, akaro na biyu ma da takira be ɗaga ba sai tayi jifa da wayan tana kifa kanta tare da rufe idanu, kamar an tsikare ta kuma sai tamiƙe tafito parlour, har yanzu Ahmad ne kaɗai zaune, ficewa kawai tayi shi kuma yabi ta da ido.

Tana fitowa gidan su ta'isa bakin Gate ɗin gidan Khalil tasoma nocking, Me gadi ne yaleƙo da kansa yana ganin ta yabuɗe mata, murmushi tayi masa tace

"Yana nan ko?"

"Eh yana nan, yanzun nan yadawo".

Shiga tayi tanufi cikin gidan, tana isa tasoma nocking sai dai shiru babu amsa, ta ɗan jima a wajen tana tunani sannan kuma sai tasaka hannun ta tamurɗa handle ɗin ƙofan yabuɗe, shiga tayi tana kallon parlour'n, babu kowa sai plasma dake aiki shi ƙadai, kan kujera tasamu tazauna sannan tasoma sallama

Khalil dake cikin ɗakin sa, fitowan sa kenan daga wanka yajiyo sallaman ta, ya gane ko wacece don haka kawai yaci gaba da shiryawan sa, bayan ya gama ne yafito parlour'n yasami wuri yazauna yana kallon ta, murmushi tayi masa tace

"Ashe kana lafiya? Na kira wayan ka naji shiru baka ɗauka ba shine nashigo in duba ka".

Shima murmushin yayi mata yace "sorry ban jiba ne, to ya aikin naki?"

Still tana murmusawa tace "alhmadulillah, kai fa?"

Sai ya ɗan kwaɓe fuska sannan yace "ba daɗi".

Dariya tayi sosai tana kallon sa yayinda shima ɗin ita yake kallo yana sakin murmushi, sosai take jinta cikin farin ciki ganin ta tare dashi

"Yunwa nake ji ko zaki dafa min abinci irin na ran nan?"

Tsayar da dariyan nata tayi tana kallon sa da murmushi a face ɗinta tace

"Me zai hana, ko me kake so zan yi maka ai".

Sai tatashi kuma tana faɗin "kabani mintuna 20 yanzu zan gama maka".

"Ok to muje nima in tayaki ko na koya nima".

Kausar taji daɗi sosai ganin yanda Khalil yasaki jiki da ita a yau ɗin, atare suka gama abincin suka zubo kuma sukaci tare, duk kan su in kakalle su zaka gane suna matuƙar farin cikin kasancewar su tare, duk abun da ɗaya yayi sosai yake burge ɗayan, Kausar ba ita tabar gidan ba sai bayan la'asar.



***** ***** ***** ****

"Zainab wai yaushe zaki dena wannan kukan ne? Tun sanda Halwa tatafi kullum cikin kuka kike yi, ko kukan naki ne zai dawo da ita?"

Shiru Zainab tayi sai dai har yanzu hawaye basu dena zuba cikin idanun ta ba

Umma tace "ki tashi kije ki ɗiba ruwa kiyi wanka tunda yanzu kin zama ƙazamiya wankan ma kin dena".

"Umma Ni har yanzu na kasa yarda da abinda Mama da Nura suka faɗa mana, ta ya Halwa zata tafi tabar su lokaci ɗaya? Ya za'a yi Halwa tatafi batare da ta sanar min ba? Tunda muke da ita ban taɓa jin Halwa tayi maganar dangin mahaifin ta ba, ta ya zasu ce don sun zo ganin ta zata bi su tabar su?"

Sai kuma tafashe da kuka, cikin kukan take cewa

"Wlh Umma ƙarya ne, ƙarya suke yi suce Halwa tazaɓi dangin Mahaifin ta akan su, zuciyata takasa yarda da abinda suka faɗa, suna nufin kenan fa tatafi bazata sake dawowa ba? Ni na tabbata sai dai in wani abu ne yafaru amma Halwa baza ta taɓa tafiya ba".

"To don ubanki tunda baki yarda dasu ba sai kiyi tayi, ko kuma kibi ta inda kikasan tatafi". Umma tafaɗi hakan a zafafe domin Zainab ɗin tasoma kai ta maƙura akan zancen Halwan

Tashi Zainab ɗin tayi tashige ɗakin ta batare da tasake furta komi ba.




October 2020.
[10/19/2020, 7:48 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```


.

*CHAPTER 35*


Dad da Mom da Nazeefa ne zaune saman dainnig table suna yin luncing, baka jin ƙaran komi sai Spoons, ita Nazeefa kanta na ƙasa daƙyar take cakalan abincin, don har yau bata saba dasu ba, gwara-gwara Mom in suna tare su biyu.

Sameer ne yashigo cikin parlour'n yanufo su yana faɗin "wow nazo a sa'a domin yunwan nima nake ji".

Mom da taɗago kai tana kallon sa tace "ba daga gida kake bane?"

"Eh naje wajen Friend ɗina ne, kuma daga nan muka wuce Hospital shine nabiyo ta nan".

Gyaɗa kai kawai Mom tayi tamayar da hankalin ta ga abincin ta

"My Dad barka da rana". Sameer ɗin yafaɗa yana dafa glass table ɗin da hannayen sa

Dad kaɗa masa kansa kawai yayi sakamakon ya sanya abinci a baki

sai lokacin Nazeefa taɗago kanta tace "sannu da zuwa Yaya".

Sameer ɗaura hannun sa yayi akanta yana kallon ta yace "Yauwa ƙanwa ta, abinci kike ci ne haka babu tayi?"

Murmushi Nazeefa tayi tana Sad da kai ƙasa, zama yayi gefen ta kana yace

"To nima yi saving ɗina in tayaku".

Plate tajawo tasoma saving ɗin shi

Dad yace "Sameer yau wai ya naji wayan Ibrahim be shiga lafiya dai? Kuma ban gansa ba kwana biyu".

Ɗago kai yayi Sameer yana kallon sa yace "Dad wlh ban sani ba, nima dai tun yesterday rabona dashi kuma bamuyi waya ba".

"Ok ƙara try Numban sa kaji yanzu".

"Ok Dad".

Wayan sa yaɗauka yasoma kiran Khalil, ringing ɗaya tashiga but babu answer, sai da yayi two missed calls kafin Dad yace masa "yaƙyale sa haka". Abincin su sukaci gaba da ci, kamar 5mint kuma sai ga wayan tana ringing, Khalil ɗin ne yakira, ɗauka Sameer yayi zai miƙa ma Dad sai yace masa

"Ɗauka kawai kace masa ina kiran sa yanzu yazo yasame Ni".

"Ok Dad".

Peaking call ɗin yayi yace "Hello ɗan ƙanina".

Khalil dake zaune bakin gado daga shi sai gajeren wando yaɓata fuska yana cewa "Bro bana so fa nace maka".

Ɗan dariya Sameer yayi kana yace "ok na daina, kazo Dad na Kiran ka".

Ɗan jimm Khalil ɗin yayi kana yace "ok ga ninan".

Daga nan kashe wayan sukayi ya'ajiye tare da miƙewa tsaye yanufi wajen sif ɗin kayan sa yafito da wanda zai saka, bayan ya shirya as usual cikin ƙananan kaya farar riga da blue jeans, yasanya brown cover shoes yanufi gaban looking glass yabuɗe locker yafiddo car key yafice, a cikin ɗaya daga cikin motocin sa kalan ruwan zuma yashiga, be cika hawa motan ba sai yaga dama, yanzun ma yau yafiddo ta yasaka aka wanke masa, yana isa bakin Gate yadanna hon aka buɗe masa Gate ɗin yafice, ahankali yake tuƙin nasa har yakai gidan nasu yafito yashige cikin gidan, a lokacin su Mom sun dawo saman kujerun parlour'n suna zaune suna hira, in kaɗauke Nazeefa da bata wajen ta shiga ɗakinta

Lokacin da ya'isa cikin parlour'n bayan ya gaishe da iyayen nashi zama yayi kusa da Sameer dake zaune kan Two sitter

Dad yace "yauwa ina maganar mu da muka yi, shin ka samo matar da zaka aura?"

Shiru Khalil yayi yana kallon Dad ɗin batare da yace komi ba, haka zalika su ma kallon sa suke yi suna son suji me zai faɗa, ganin shirun nasa yayi yawa Mom tace

"Auta kayi shiru, ko har yanzu baka samu matar bane?"

"Ai kuwa idan be samu ba Ni sai in nema masa tunda naga abun nasa yana ɗaukan sa da wasa ne". Cewar Dad kenan

Khalil kuwa shafo gashin kansa yayi yajuya kai yana kallon Sameer Wanda shima ya kafe shi da nashi idanun yana kallon sa, alama yayi masa da ido sai yakau da kansa yana kallon Dad ɗin yace

"Dad na samu".

"Masha Allah haka ake so, yanzu yarinyan aina take kuma ƴar wacece?"

"Suna zaune a Jan Bulow, mahaifinta sunan sa Alh. Ahmad Sofana".

"To Alhmadulillah insha Allahu zamu je zuwa gobe ko jibi don gwara ayi a huta".

Mom washe baki tayi tace "My Son na tayaka murna, Allah yatabbatar da alkhairi".

Murmushi kawai yayi yana faman sosa kai, Sameer kuwa ɗan bugun kafaɗan sa yayi yace

"Congratulation My Lil Bro Allah yasanya alkhairi Allah yasa ayi damu, Burina dama kenan naga auren ka gashi komi yakusa zuwa".

Mom itama cikin farin ciki ta karɓe zancen da cewa "wlh kuwa ai nima nafi kowa son ganin wannan ranan, amma Auta mene sunan surukar tawa? ya kamata kasanar min tun yanzu in sani sannan kakawo min ita in ganta don in tabbatar da cewa ka dace da yarinyan ko kuwa".

Dariya Dad yayi yace "kai uwar yara wannan zumuɗi haka? Ai sai ki bari komi yakankama tukuna ko?"

Itama dariya tayi tace "Uhm baza ka gane bane amma Ni kaɗai nasan irin farin cikin da nake ji, Ni kaɗai nasan me na tanada a auren Autana".


...... ........ ........ .......
Da gudu ta'isa kan gadon ta tafaɗa tana sakin kuka me ƙarfi, sosai take kuka sai kazata yanka ta ake yi, kukan baƙin ciki na jin hiran nasu, bata taɓa tunanin ƙaunar Khalil take yi ba sai a ɗan kwanakin nan tagane, hakan yasaka wani baƙin kishi yaturnuƙe ta jin ya sami wacce zai aura "shikenan yanzu ita ta rasa shi?" Tambayan da tayi ma kanta kenan tana sake kecewa da kuka, duk da tasan yafi ƙarfin ta amma sosai take matuƙar ƙaunar sa fiye da tunanin me karatu, batasan wani hali zata shiga ba idan har tarasa shi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba

Jin motsi kamar za'a shigo tayi saurin tsayar da kukan nata cak tana juyawa takalli ƙofan shigowa, dasauri takuma saka hannun ta tashare hawayen fuskarta dai-dai lokacin da Mom tabuɗo ƙofa tashigo, kallon ta tayi yayinda ita kuma tasad da kanta ƙasa tana murɗe yatsun hannunta

"Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa naga kamar kin yi kuka? Meke damun ki?" Mom tatambaye ta cike da kulawa

Shiru Nazeefa tayi sai kuma tabuɗe baki ahankali cike da rawan murya tace "ba..bu ko..mi Momy, wani abu ne yafaɗa min a idanu".

"Subhanallah sannu, yanzun ya fita ko kuwa?" Still Mom ɗin tasake tambayar ta cike da nuna kulawan ta tana saka hannayen ta taɗago kan Nazeefan tana kallon idanun da suka sauya kala

"Eh ya fita".

Mom tace "ok sannu ko? Allah yakyauta gaba".

"Ameen".

"To tashi yanzu kije Yayan ki na kiran ki zakuyi maganar School ɗin ki da zai saka ki".

Nazeefa ta'amsa mata da "Toh". Kana tatashi tanufi ƙofa, itama Mom bayan ta tabi suka fice atare.





****** ****** *******

A cikin satin ne Alhaji Abdurra'uf tare da abokin sa Alh. Mustapha sai kuma Yayar Mom Alh. Maddibo suka je nema ma Khalil auren Bilkisu, koda suka isa gidan kyakykyawar tarba suka samu wajen ƙanin Mahaifin ta kasancewar a wajen sa take zaune, bayan da su Dad suka gabatar da abinda suka zo nema, Alh. Umar wato ƙanin Mahaifin nata nan yasoma magana cikin dattako

"Alhmadulillah gaskiya naji daɗi sosai da akace kamar ku kun zo neman auren ƴata hakan ya faranta min rai matuƙa, sai dai matsalan da akwai wanda nayi mamaki matuƙa cewa ita yarinyan bata sanar muku ba sannan kuma nayi mamaki kan cewa ta turo wani don yanemi auren ta".

Ɗan jan numfashi yayi yana kallon su yaci gaba da faɗin

"Zan baku haƙuri da cewa mun riga da munyi wa ƴar mu Miji tun tana ƙarama, wanda hakan shine abinda muka saba tun farkon dangin mu wato haɗa auren zumuncin, ina fata zaku fahimce Ni kuma hakan bazai ɓata muku rai ba?"

Alh. Maddibo ne yace "a'a wlh babu komi, ai kayi mana bayanin da zamu fahimta hakan ya gamsar damu, shikenan dama Allah yayi nufin ba matar sa bane Muna godiya sosai".

Alh. Umar yace "ai Ni ne da godiya bisa abinda ƴar mu tayi, tunda da tasanar dashi duk hakan bazai faru ba".

Daga nan dai tashi su Dad sukayi tare da yi masa sallama suka tafi, a hanya Alh. Maddibo yayi musu sallama suka rabu yayinda Dad da Alh. Mustapha

Please Login or Register in order to submit comment