Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tuni sun saka kuka sabida halin ruɗe wa


"Ku taimaka min.. ku taimaka min na ɗauke ta". Matar tasake faɗa cike da rawan baki


Daƙyar suka ɗaga Halwa suka nufi motan da ita suka saka ta daga ita har Trolly ɗin ta, matar taja motan suka bar wurin


Direct asibiti suka nufa, dayake sananniya ce wajen Likitan sai yasaka Nurse suka amshi Halwa batare da bincike ba akayi Emargency Ward da ita


A reception suka zauna zaman jiran fitowar likitan


Mintuna kamar 20 yafito yanemi Matar tabiyo sa, bayan sun zauna a Office ɗin sa yasoma mata bayanin abinda ke faruwa


"Ba wani abu bane yasame ta sai buguwa da tayi akanta wanda hakan yaja mata dogon suma, amma da yardan Allah zuwa gobe zata iya farka wa".


Wannan bayanin na likita shi yakwantar wa matar da hankali, daga nan suka tattauna sannan tafito tasami ƴan matan ta suna jiran ta


Tambayan ta suka hau yi har yanzu suna zub da hawaye don ba ƙaramin tashi hankalin su yayi ba


Kallon su tayi cikin kwantar musu da hankali tace "ya isa haka babu abinda yasame ta illa buguwa da tayi akanta".


Atare suka sauke ajiyan zuciya suna faɗin "alhmadulillah".


Murmushi tayi kafin tace "to yanzu yakamata ku koma gida inyaso Ni sai in zauna da ita don baza mu tare anan ba, kuma ban ce ko waccen ku takira Daddynku tafaɗa masa ba don kar hankalin sa yatashi kuna jina?". Matar Taƙarike maganar da jan kunnen ta


Gyaɗa mata kai suka yi atare suna cewa "to Mami".


"But Mami ki bari Ni zan kwana da ita mana tunda ba wani abu me wahala bane". Cewar Safina tana kallon Mami ɗin cike da son amincewar ta


"Ok to bari mutafi gida Ni da Nafisa, but ki kula bana son rawan Kan nan naki kinji Ni? Idan da akwai matsala kiyi kiran Doctor".


Safina tace "to Mami insha Allahu".


Daga haka babu abinda suka sake faɗa illa wuce wa ɗakin da aka kwantar da Halwa da suka yi, basu fi mintuna goma ba Mami da Nafisa suka fito suka bar Safina a wajen ta.




_sai muce Allah yabaki lafiya Halwa._
[1/5, 12:58 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

_Fateema Zahra, Hauwa Ali, Wanka Yakubu Isa, Munir Y Abdullah, M. Bintu Thank You for the loving My Book._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Twenty Five*

________🎓Washe gari da sassafe Mami tadawo Asibitin da breakfast, Safina na gaishe ta ta'amsa tace mata


"Yauwa to tashi kije yi maza Drever na jiranki ki koma gida ki shirya kar kuyi late, ki tabbatar kinyi breakfast kafin ki tafi ko kuma ki ɗiba ki tafi dashi kina jina?"


Murmushi Safina tayi lokacin da tamiƙe tana ɗaukan gyalen ta


"Mami sai kace wata yarinya haka kawai sai inje da Breakfast school?"


Hararan ta Mami tayi tace "Ni dai na faɗa miki kuma na bada sallahu idan ma baki je dashi ba Nafisa zata faɗa min, ai na faɗa miki daga yanzu na dena baku kuɗi, wuce ki tafi kar in saɓa miki uwar shiririta".


Turo baki gaba tayi tafice batare da tasake cewa komi ba


Ita kuma Mami zama tayi idanun ta akan Halwa wacce ko motsi ba ta yi tun jiya tana nan ayanda take, an naɗe mata kai da bandage sabida ba ƙaramin rauni taji ba



Ajiyan zuciya kawai Mami take sauke wa cike da tsananin tausayin Halwa, kawai aranta tunanin yanda aka yi matashiyar yarinya kamar wannan tafito gidan iyayen ta da tsakar dare take yi.



Tana nan zaune wajen ƙarfe 09:00am na safe sannan ne Halwa tafarka, don haka tamiƙe da hanzari takira Doctor coz tunda tafarka ɗin tabuɗe idanun ta bata sake motsawa ba, duk sannun da tajero mata taƙi ta amsa ta


Doctor da yazo yadudduba ta yatabbatar bata da wani matsala sannan yace aba ta abinci taci sai tasha magani



Sai da yafita kafin Mami tasoma haɗa mata abin kari, bayan ta gama takalle ta kamar yanda Halwan tazuba ma matar idanu tamkar me neman wani abu ajikin ta


Murmushi tayi mata tace "tashi kisha kinji?"


Halwa batace komi ba tayunƙura tagyara zaman ta, duk da babu abinda ke damun ta amma sosai kanta ke mata ciwo daƙyar take iya motsa shi, amsar Cup ɗin tayi tariƙe da hannu biyu ta kasa sha


Sai da matar takula da ita kafin tace "af na manta baki wanke baki ba ko zaki fi jindaɗin sha".


Amsar Cup ɗin tayi tamiƙo mata ruwa, sai da tawanke bakin kafin tamiƙa mata Tea Cup ɗin, sannan alokacin tasake ciko mata Plate da Arish da soyayyan ƙwai ta'ajiye mata akan gadon, sai tatashi tafice don tabar ta tasake


Tana fita Halwa talumshe idanunta, aranta kewar gida kawai take yi tare da tunanin makomar ta a yanzu, bata dena tunanin ba take ta tsoma bakin ta tana shan tea ɗin zuciyarta duk babu daɗi


Ta jima ahaka batare da tasan awani hali take ciki ba, har Mami tadawo tatarda ita ahaka ko rabin Cup ɗin bata yi ba, babu ma abinda tataɓa acikin Plate ɗin


Mami kallon ta tayi tana nazartan ta, kafin kuma tatamke fuska cikin serious face tace "har yanzu baki ci komi ba ashe? Bana son shashanci Yi maza ki cinye ki bani Plate ɗin da kofin".



Kallo ɗaya Halwa tayi mata ta tabbatar matar ba ta ɗaukan raini, nan da nan taji tsoron ta ya kamata ta batare da tayi mata musu ba tayi yanda tace mata tamiƙa mata Plate ɗin kamar yanda tabuƙata



"Good kinyi kyan kai". Mami tafaɗa bayan ta amsa ta ajiye sannan tafice



Da kallo Halwa tabi ta tana tunanin ita kuma wannan matar daga ina? Menene haɗin ta da ita? Ita dai tasan an bige ta to ko dai ita ce tabige ta ɗin?".



Tana cikin wannan tunanin ne suka dawo da doctor, magani yaba ta bayan ya tambaye ta "ko akwai abinda ke damun ta?"


Dayake Halwa jin ta take yi tamkar a ƙaya musamman yanda matar nan tanuna mata sai taji ta ƙosa su raba hanya, don haka tace masa babu abinda ke damun ta


Hakan yasa Doctor ɗin ce ma Mami zuwa anjima za'a sallame ta.




Ƙarfe 02:35pm. Safina da Nafisa suka kawo abincin rana, ganin Halwa ta farka ga jikin ta dasauƙi hakan ya faranta musu rai sosai musamman ma Safina, kasancewar ita akwai ta da son mutane ga fara'a ba kamar Nafisa ba, hakan yasa lokaci ɗaya tashige ma Halwa tana ta janta da Surutu


Itama Halwa sosai tasaki jikin ta zuwan su ba kamar ɗazu ba duk da kuwa ba magana take yi ba iyakan ta murmushi da bin Safinan da kallo me zuba mata surutu.



Da yamma aka sallame su suka taho gida, babban gida ne dasu me kyau sosai, kai da gani kasan ba ƙaramin kuɗi ne da me gidan ba


Suna isa Safina taruƙo mata hannu suka yi ciki, ɗakin su takai ta tahaɗa mata ruwan wanka tashiga


Itama Nafisa sai gata ta shigo da Trolly ɗin Halwa ta'ajiye mata tafice


Safina na zaune bakin gado tana jiran Halwa har tafito, murmushi tayi mata tace


"Aunty ga kayan naki nan sai ki shirya ina zuwa". Taƙarike maganar tana miƙe wa cike da zumuɗi


Gyaɗa mata kai Halwa tayi tare da mata murmushi, har tafice tana kallon ta kafin tazauna gefen gadon tana zuba tagumi, ta ɗau lokaci ahaka har Nafisa tashigo ɗakin batare da ta sani ba, sai da tataɓa ta kafin taɗago kai dasauri tana kallon Nafisan, ko kaɗan ba wai ta gane ko wacece acikin su ba duk da kuwa taji sunayen su tun a Hospital, but tsananin kaman da suke da juna baka banbance wacece Nafisa wacece Safina, iyakan dai a fuska idan kakalli Nafisa zaka iya shaida ta sabida bata da fara'a ko kaɗan, miskila ce na ƙarshe saɓanin Safina ko yaushe haƙoran ta awaje suke


Murmushi Nafisa tasakar mata ganin yanda tatsare ta da idanu tana son tantance Nafisa CE ko Safinan



"Ki taso Mami na kiran ki". Tafaɗa ahankali tana juyawa tayi hanyan ƙofa


Ɗan numfashi Halwa taja batare da ta ɗauke kanta daga kallon Nafisa ba har tafice, yanda tanuna mata ɗin tuni ta gane ba Safina bace



Miƙe wa tayi tabuɗe kayan ta taciro riga da skert na atamfa kalan Baby pink sai ratsin Milk da aka yi amfani dashi wajen zanen Flower jefi-jefi, bayan ta gama saka wa taɗau siririn gyale baƙi tayafa akanta sabida bata saka ɗan kwalin kayan ba sannan tanufi ƙofa tafice



Suna zaune gaba ɗayan su a falo, Halwa da tafito ƙasa tasamu tazauna cikin sanyin muryanta tayi wa Mami sannu


Amsawa tayi idanun ta akanta kafin takalli su Nafisa tace "ku tashi ku bamu wuri".


Babu musu suka tashi, sai ma suka yi ƙofar fita suka fice gaba ɗaya


Juyo da idanun ta kan Halwa tayi tace "yauwa so nake yanzu ki faɗa min abunda yasa kika baro gida, ayanda nafahimta da nazarin da nayi miki hasashe na ya bani kin baro gida ne sabida wani dalili naki hakane?"


Halwa da kanta ke ƙasa ta kasa ɗago kai bare ta'amsa mata, sosai matar take bata mamaki da kuma yanda halin ta yake, kai da gani kasan ba ƙaramin jarumar mace akayi a wajen ba, dakakkiyar mata me tsananin kwarjini da baiwa..


"Kinyi shiru ina magana? bana son ina maimaita ma mutum magana biyu kinji Ni?"


Dasauri Halwa tagyaɗa mata kai cikin tsananin shakkar matar da yakamata tun ganin ta da tayi


"Ki buɗe baki kiyi min magana ba gyaɗa kai nace kiyi ba".


Cikin rawan baki Halwa tabuɗe baki tasoma sanar mata da abinda take buƙatar ji a wajenta, iyakan abinda tasanar mata tafito gida ne sabida anyi mata aure da mijin ƴar uwanta, ganin tanuna kamar bata ji daɗi ba shine ita kuma tabi wannan hanyan don guje ma auren".


Jinjina kai Mami tayi idanun ta kafe kan Halwa ɗin, cikin kausashshiyar murya tace "wato kin zaɓi guduwa ne don kawai ƴar uwanki bata ji daɗin wannan haɗin ba? Kin nemi ki baro iyayen ki sabida ki faranta mata ko?"


Cikin zub da hawaye Halwa tasake duƙar da kanta, cike da raunin murya tace "nayi hakan ne kawai saboda farin cikin ta, Ni bazan so in shiga rayuwanta ita da mijin ta ba, sannan zan so takasance cikin farin ciki ko dan ciwon da take fama dashi".


Shiru ne yabiyo bayan maganar ta illa shashsheƙan kukan ta dake tashi


Wajen shuɗewar mintuna biyar kafin Mami tace "shin ke kina son Sa ko kuwa bakya son sa?"


Baki na rawa tace "Ina son sa".



Murmushi Mami tasaki tana kaɗa ƙafafuwan ta, sai da taja lokaci kafin tace "shikenan yanzu abinda Yakamata zuwa gobe zan maida ki gida saboda babu ta yanda za'a yi in barki kibi duniya akan wannan banzan dalilin naki, idan yaso in namayar dake sai in faɗa musu su raba auren tunda baki son zama dashi, kinga babu ke babu guduwa kenan, tashi ki wuce na sallame ki".



Jiki a sanyaye Halwa tamiƙe takoma ɗakin su Nafisa, tana shiga tazauna kan gadon tana ci gaba da tsiyayar da hawaye kamar an kunna famfo


Ba wai maganar mayar da itan bane yaɗaga mata hankali, jin cewa zata faɗa a raba auren ta da Khalil, ita ji take yi a yanzu ta gummaci tatafi da auren sa tayi ta yawo da araba auren, hakan zai saka zuciyarta tayi sanyi daga zugin da take mata na tsananin ƙaunar sa da take yi, auren Khalil akanta shi zai sa duk inda taje takasance cikin farin ciki, ko babu komi zata mutu da auren wanda tafi ƙauna fiye da ranta a yanzu ɗin atare da ita.



Ita kuma Mami murmushi tayi lokacin da Halwan tashige ɗaki, sosai aranta ta tausaya mata domin tunda take bata taɓa ganin irin wannan sadaukarwan da Halwa tayi ba, kina son mutum amma sabida farin cikin ƴar uwanki ki zaɓi rugujewar rayuwan ki gaba ɗaya akanta, gaskiya samun me hali irin Halwa da wahala, tana da kyakykyawar zuciya matuƙa, tana iya sadaukar da komi nata akan masoyi


(Hmm nace Mami don ma bakisan sauran sadaukarwan da tayi mata bane)




Mami tana zaune da ƴaƴan ta biyu Nafisa da Safina masu shekaru 16 a duniya, twins ne su kuma daga kansu bata sake haihuwa ba, mijinta babban soja ne sosai yana aiki a Kaduna


Baza ku gasgata maganar nan da ake cewa matar Soja itama Soja bane sai kun haɗu da Mami, Kai in taƙaice muku tsaurin idanun Mami da dakakkiyar zuciyar ta ta ninka na mijinta da shine ma Sojan, bata da tsoro ko kaɗan gata macece me tsayawa akan komi da yashafe ta da tsananin jarumta, bata nuna gazawar ta a komi, tana da fara'a sosai sai dai ba ta yin sa sai a inda yadace, shiyasa Nafisa a halayya ita taɗauko, sai dai ita Mami ba wai miskilanci ne da ita ba dakakkiyar macece da bata ɗaukar raini koda yaushe, wannan dalilin ne zaka ga tamkar bata cika wasa ba


Yanzu haka ita ma'aikaciyar gwamnati ne me amsar zunzurutun albashi don babba ce sosai a wajen aikin su.


*WASHE GARI*


Wajen ƙarfe 10:00am. Mami tasaka Halwa tashirya



Dama tuni su Nafisa sun tafi school, Safina har da kukan ta jin cewa a yau ɗin Halwa zata tafi, domin sosai jinin ta yahaɗu da Halwa ɗin a kwana ɗayan nan da tayi agidan, ta ɗauke ta tamkar babban Yayarta wacce suka fito ciki ɗaya shiyasaka tasaki jiki sosai da ita, taso Mami tabar su yau dai rana ɗaya kar suje school atafi dasu kai Halwa gida, amma ina Mami taƙi yarda, daga ƙarshe ma sai da tayi kamar zata mangare Safinan kafin tatafi school da kuka



Ita kanta Halwa sosai taji ƙaunar Safinan aranta, sai bata ji daɗin yanda Mami tayi ɗin ba, sai dai bata da bakin magana iyakan nata idanu ne domin wargi ma wuri yaka samu



Bayan Halwa tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na Baƙin yadi da zanen Flower da aka yi da dack orange Colour, fitet ne rigan sai tayi Rolling da gyale me ruwan madara irin me taushin nan sosai ya rufe mata har bandage ɗin kanta


Janyo jakan tayi tafito Parlour inda Mami ke zaune tana jiran ta, kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kai tana ci gaba da latsa wayan nata


Ita dai Halwa tana nan tsaye a waje ɗaya ko ƙwaƙƙwaran motsi bata iya yi


Kamar shuɗewar mintuna goma kafin Mami tatashi tayi wa Halwa nuni da hannu alamun su je



Gaba Halwa tayi dasauri tana jan Trolly ɗin ta, koda tafita sai da tajira Mami ɗin takullo ƙofa tazo tasame ta kafin su ƙarisa wajen motan


A lokacin har me gadi ya ƙariso wajen yana kai gaisuwa wajen Mami



Amsa masa kawai tayi tana buɗe Boot



Dasauri yanufi wajen Halwa yana ƙoƙarin amsar jakan nata don yasaka mata a Boot ɗin, but Mami tatsai dashi da faɗin



"Ƙyale ta tasaka da kanta Ali, je kabuɗe min Gate".


"To Hajiya". Yafaɗa dasauri yana nufan Gate ɗin


Ita kuma Halwa saka Trollyn tayi sannan Mami tarufe suka shiga motan, sai da taja motan zuwa bakin Gate ɗin kafin tatsaya tazuge glass ɗin tana kallon me gadin tace



"Ali idan su Nafisa sun dawo kace musu su duba keey ɗin a inda nasaba ajiye musu, sannan kafaɗa musu su tabbatar sun tafi islamiyya yau bazan dawo ba sai zuwa dare".



"To Hajiya insha Allahu zan faɗa musu, Allah yadawo dake lafiya".



"Ameen ya Allah". Tayi maganar tana maida Glasses ɗin tarufe sannan taja motan taƙarisa fice wa.



.












_To ga fa Halwa za'a koma gida Fans, ko me zai faru?_
[1/5, 2:40 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Twenty Six*

________🎓Kamar yanda Halwa tafaɗa mata address ɗin gidan su Saleema can tanufa, a cikin motan babu me magana, ita dai Halwa kallon hanya kawai take yi tana kitsa abubuwa aranta da tunanin abinda zai faru idan takoma..



Ƙaran horn ɗin da Mami ta danna ne yadawo da ita hayyacin ta, takai duban ta ga Gate ɗin lokacin har me gadi ya leƙo don ganin wanene, be buɗe musu ba sai da yazo har wajen motan yayinda Mami tasauke Glasses Motan


Har ya buɗe baki da ninyan yin magana sai yahangi Halwa, cike da tsagwaron murna da al'ajabin ganin ta don zuwa yanzu har ma'aikatan gidan sun san abunda yafaru duba da yanda iyayen gidan nasu hankalin su yake a matuƙar tashe da halin da Saleeman ke ciki



Washe baki yayi yace "Hajiya Halwa ke ce?"



Murmushi tayi masa cikin sanyin murya tace "eh Yusha'u".


"Masha Allah bari in buɗe muku ƙofan to". Yayi maganar yana nufan Gate ɗin dasauri har da haɗa wa da gudu


Yana shiga yabuɗe musu Mami taja motan zuwa ciki


Har wajen motan me gadin yabi su bayan da yamayar da Gate ɗin yarufe, anan ne suka gaisa da Mami itama Halwa tagaishe sa sannan sukai ciki


Halwa ce agaba don haka ita tabuɗe ƙofan tashiga da sallama a bakin ta


Ummi dake zaune saman kujera ta riƙe waya a hannu tana latsawa, kallo ɗaya kayi mata zaka hango tsantsan damuwar da take ciki


Sallaman Halwan shine yasa taɗago kai sabida jin muryan da bata taɓa zaton ji ɗin ba a halin yanzu, dasauri tamiƙe ganin dai itan ce zuciyarta cike da zallan mamaki tare da wani irin murna


"Halwa.." takira sunan ta idanun ta akanta don tama kasa motsawa


Murmushi Halwa tayi takalli Mami dake bayan ta, sai kuma tasad da kanta ƙasa


Mami gaba tayi zuwa cikin parlour'n hakan yasa itama Halwa tabi bayan ta, sai da suka zauna kafin Ummi tasake samun bakin magana


"Halwa ina kika shiga ne? Ina kika shiga kika bar mu cikin neman ki?" Tayi maganar tana dawo wa kusa da Halwan tare da riƙe mata hannu



Hawaye Halwa tasoma yi, cikin rawan baki tace "don Allah ku gafarce Ni Ummi nabi son Raina na tafi na barku amma bazan sake ba".


Washe baki Ummi tayi tana rungume ta cike da tsantsan murna, bakin ta sai faɗin "baki yi mana komi ba Halwa, baki yi mana komi ba wlh.."


Mami dai tana kallon su batare da ta furta komi ba


Tsawon mintuna biyu kafin suka nutsu har Halwan dake yin kuka


"Ummi tace tunda kika tafi Saleema taƙi lafiya, kullum cikin neman ki muke yi, yanzu ma haka tana nan ɗakina ta kwanta tana barci".


Zumbur Halwan tamiƙe tana shirin nufan ɗakin Ummi sai taji saukar muryan Mami tana faɗin



"Oh baza ki gabatar dani bane zaki tafi ki bar ni? Tunda anga uwa dole ki manta dani". Ta yi maganar ne fuskarta yalwace da murmushi



Juyowa Halwa tayi sai dai bata kai ga magana ba Ummi tariga ta da cewa



"Don Allah kiyi haƙuri wlh murnan ganin ta ne yaɗauke min hankali sam gashi ko gaisawa bamu yi ba".



Murmushi Mami tayi tace "babu komi ai".


Sannan suka gaisa kafin Mami ɗin tace "ina son ganin mahaifin ta idan babu damuwa sabida maganar da nazo dashi".


"To babu komi bari in Kira sa". Cewar Ummi tana ɗaukan wayan ta.



Halwa ita tuni ta shige ɗakin Ummi ganin sun manta da ita, koda tashiga Saleeman na barci kamar yanda Ummi ɗin tafaɗa, tunda tasauke idanun ta akan Saleeman hawayen ta suka sake gudu wajen fitowa, toshe bakin ta tayi ahankali tasoma takawa zuwa gadon, sai da tazauna sannan tasaka hannun ta tana shafa mata saman goshin ta cike da tsananin tausayin ta, wuni biyu kacal yasa ta wani irin mugun ramewa kai da ganin ta kasan tana jin jiki



Kasa riƙe kukan ta tayi tasoma shashsheƙan kuka duk da kuwa tana dannewa kar yafito fili



Sai dai hakan be tasiri ba don tuni kukan nata ne yatashi Saleema, ahankali tabuɗe idanun ta akayi Sa'a sai tasauke su kan Halwa da hawaye suka cika idanun ta har bata iya gani sosai sai ta rage su da hannu



Kallon ta kawai Saleema take yi batare da ta motsa ba


Sai Halwan tasakar mata murmushi cikin rawan baki tace "ƴar uwa.."


Lumshe idanuwan ta tayi tasake buɗe su akanta amma kuma bata da alaman motsawa, tsira mata idanu kawai tayi tana tunanin ko dai mafarkin da take yi ne a yanzu bata farka ba?


Sake kiran sunan ta tayi cikin sanyin murya tana cewa "Ya jikin naki?"


Sai da tasake ɗan ƙif-ƙifta idanun nata ta yanda zata tabbatar ba mafarki take yi ba, ganin dai har yanzu tana ganin Halwan sai tayi saurin tashi zaune idanun ta akanta takai hannun ta tana taɓa ta


Hakan sai yaba ma Halwa dariya don ta gane me take nufi tana kokwanton ita ce ko ba ita ba


Murmushi tayi taruƙo hannun nata da take shafa mata jiki tace "ƴar uwa Ni ce fa, na dawo gare ki ne".



Sai kawai Saleeman tafashe da kuka tana rungume ta, cikin kukan take faɗin


"Don meyasa zaki tafi ki bar ni? Kina tunanin zan iya ci gaba da rayuwan farin ciki ne bayan kin tafi? Ƙaunar da nake miki shine zai hana Ni samun farin ciki a rayuwata, wlh da baki dawo ba bazan taɓa yafe miki ba".


Itama Halwan kuka take yi sosai zuciyarta cike da tsananin rauni, tabbas tayi nadaman tafiya, da yanzu Mami Bata dawo da ita ba shikenan haka zata tafi tabar ƴar uwan ta cikin damuwa na rashin ta, abun da taguda ashe shine zai faru, tayi nesa dasu don farin cikin Saleeman amma kuma tafiyan nata yazama barazana ga rayuwan ta, ko kaɗan bata taɓa tunanin hakan ba, tabbas ƙaunar da Saleema take mata ya wuce tunanin ta


Sun jima ahaka kowa yaƙi sakin ɗan uwan sa, kuma basu fasa yin kukan ba sannan babu wani kalma da tasake shiga tsakanin su



Ummi ce tashigo ɗakin, ganin su ahaka sai tasaki murmushi tare da saka hannu tana share ƙwallan da yacika mata idanu, ahankali tataka wajen su cikin farin ciki tace


"To ya isa kukan haka kunji? Tunda komi ya wuce Allah yasa kin dawo sai mu gode waa Allah".


Sakin junan su suka yi yayinda Saleema takasa dena kukan


"Please sis ki dena kukan mana kar ki saka inji na tsani kaina mana, domin idan wani abu yafaru dake bazan taɓa yafe wa kaina ba".


Murmushi Saleeman tayi duk da hawayen basu dena zuba a idanun nata ba


Ummi tashafa kanta cikin jindaɗi da ganin ƴartan ahalin lafiya, sai takalli Halwa tace "muje kiyi sallama da Baƙuwar tamu zata tafi".


"To Ummi". Halwa ta'amsa mata tana tashi tsaye


Dasauri itama Saleeman tamiƙe tana jeho ma Halwan tambaya akan wacece? Don tuni Ummi tayi gaba ta fice


Ataƙaice Halwa taba ta amsa da faɗin "wacce tadawo dani ne".




Abba da Dad ne zaune a parlour'n suna sake sallama da Mami, kafin kuma su ɗunguma gaba ɗaya da Ummi dasu Saleeman suka je raka ta zuwa wajen motan ta, anan suka sake sallama yayinda Ummi take sake mata godiya tare da faɗa mata insha Allahu zasu har gida su sake mata godiya


Itama Halwa godiyar tasake mata tare da bata saƙon gaisuwa zuwa wajen su Safina


Har sai da tabar gidan sannan suka yo cikin gidan, Ummi tasoma yin gaba tabar su nan


Har zasu shige su ma suka jiyo ƙaran buɗe Gate, a tunanin su ko Mami ɗin ne sai duk suka waiga, saɓanin haka sai suka ga motan Khalil na shigowa ciki


Ahankali Halwa tajanye idanun ta daga kallon motan tabuɗe ƙofan tashige


Saleema da bata san da shigewar ta ba tajuyo da murna zata yi mata magana sai kuma taga wayan babu ita, murmushi tayi tagyara tsayuwar ta tana jiran isowar sa.



A ciki kuwa Halwa na shiga

Please Login or Register in order to submit comment