Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsawon sokonni biyar yana faman kallon ta kafin yace


"Wai ina Mahaifin yarinyan nan?". Yaƙarike maganar yana aza idanun sa kan Saleema


Shiru tayi tana sad da kanta ƙasa, ba ta jin zata iya sanar masa haƙiƙanin gaskiya kuma bata san me zata ce masa ba a yanzu


Ci gaba da danna Lapton ɗin sa yayi be sake ce mata komi ba, sai can kamar mintuna biyar yasake jeho mata tambayan


"Ina Mahaifin yarinyan nan nace?"


Yanda yayi maganar ne a kausashe yasa hantan cikin ta ya yamutse, batasan sanda bakin ta yafurta "sun rabu ba".


Cakk yatsaya da abinda yake yi yajuyo yana kallon ta


Itama ɗin shi take kallo cike da tunanin meyasaka yake son sanin Mahaifin Husnan bayan ada be taɓa tambayan ta ba?


Kau da kansa yayi yaci gaba da aikin sa


Ita kuma ajiyan zuciya tasauke sannan tagyara takwanta tana tunani aranta


"Shin meyasa nake son kawo zargi ne acikin auren mu? Meyasa zuciyata take son kawo min abinda zai hargitsa min rayuwa? Shin menene abun zargi anan?"


Kwanciyar ta tagyara tana kallon sa, ahankali kuma tafurta "Allah na tuba Allah ka cire min zargi araina".




Aikin yake yi amma maganar Saleema ke kai kawo cikin ransa, duk da yaji sanyi ta wani gefe nasa amma kuma yasan cewa mafarkin sa bazai taɓa zama gaske ba


A haƙiƙanin gaskiya zuciyar sa ta kamu da ƙaunar Halwa tun ranan farko da yaganta, amma taya zai iya mallakan ta bayan ita ɗin ƴar uwa ce ga matar sa?



Har Saleema tayi barci yana nan zaune yana latsa Lapton ɗin sa duk da kuwa tunani ne cinkushe aran sa wanda yahana sa jindaɗin aikin


Daga ƙarshe ma tashi yayi yashige toilet yaɗauro alwala, fitowa yayi yazauna a bakin gadon yana kallon Saleema dake maƙale da Husna, sosai yake mamakin yanda take ƙaunar yarinyan


Ya jima a zaune awajen yana kallon su, amma azahiri tunani ne aransa wanda har yasoma haddasa masa ciwon kai


Kwanciya yayi yaci gaba da tunanin, yafi mintuna 20 kafin yamiƙe yatashi yasoma jero nafilfilu ganin hakan shine kaɗai mafita a gare shi, domin ko kaɗan ayau ɗin baya jin barci zai iya ɗaukar sa.

.








*Plz Share and Vote*

_More Comments more typing._
[11/13/2020, 11:10 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Three*

________🎓Washe gari ƙarfe 07:30am. *BRR. IBRAHIM KHALIL* yagama Shirin sa na zuwa office


Yau yayi shiga na Red colour suit, sai na cikin kuma whiter ne, necktie ɗin sa da Belt ɗin wandon sa baƙi ne, yayi kyau sosai sai tashin ƙamshi yake yi, sosai kwarjinin sa da cikan halittansa suka sake fitowa ainun


Be tsaya yayi breakfast ba duk da kuwa Saleema tuni tatashi tayi masa, haka yafice sabida yana sauri




Aiki sosai yake dashi a office, gashi kuma zasu je wani waje shi da Brr. Tahir


Sai wajen 12:00pm. Yagama sannan suka tafi.


Ƙarfe :2:30pm. Suka gama yanufi gidan su


Yana yin horn me gadi yazo yabuɗe masa, shiga yayi da motar ciki yayi parcking yafito yarufe murfin motan yashiga gidan


Mom na zaune a parlour tana cin Fruits tana kallon tashan African t.v ana wa'azi tajiyo sallaman sa


Fara'a tasaki tana amsa masa sallaman kafin taɗau Remote tarage t.v n


Ahankali yatako cike da gajiya yazauna gefen ta sannan yagaishe ta


Murmushi tayi tana shafa kansa ta'amsa masa tana tambayan Saleema

Sai da yayi releasing akan kujeran kafin yabata amsa da "lafiyan ta ƙalau Mom".


"Masha Allah haka ake so".


Sai da tagutsira 🍌 Bananan hannun ta kafin takalle sa tace "ko asawo maka abinci?".


Gyaɗa kansa kawai yayi yana jan numfashi


Mom har ta buɗe baki da ninyan kiran ƴar aikin ta sai ga Nazeefa ta fito daga ɗakin ta riƙe da plate a hannun ta


"Yauwa Nazeefa sawo ma Yayan ki abinci".


Nazeefa da idanun ta ke kan Khalil ta'amsa mata da "Toh". Sannan tagaishe da Khalil ɗin


Idanun sa shima akanta ya'amsa mata



Kichen ɗin tanufa zuciyarta cike da ƙaunar sa, sosai yau ɗin yasake mata kyau fiye da ko yaushe, domin ta ɗan jima rabon da tagan shi, ko da yazo gidan ita tana makaranta a lokacin


Fitowa tayi riƙe da plate da spoon aciki, taƙariso ta'ajiye masa kan Centre table bayan ta ɗan matso masa dashi, zuwa tayi tazauna can kujeran dake Facing nashi taduƙar da kanta tana satar kallon sa


Shi kuwa abincin sa yaɗauka yana ci yana sauraron hiran Mom da take yi masa akan Yayan nasa Sameer



Ko kaɗan bata gajiya da kallon sa, da ace zata kwana tana kallon sa to baza ta taɓa gajiya ba, a kullum ƙaunar sa sake wanzuwa yake yi a zuciyar ta, ta rasa yanda zatayi tacire sa aranta, bata da damuwa a ko yaushe sai nasa, burin ta kullum tasami hanyar da zata mallake sa duk da tana ganin abu ne me wahala ta same sa, amma baza ta cire rai ba da ikon Allah sai Allah ya mallaka mata shi, koda kuwa zata kasance matar sa ta huɗu ne to zata zauna dashi in dai zai aure ta..


"Nazeefa lafiyan ki ƙalau kuwa tunanin me kike yi?"


Maganar Mom yadawo da ita hayyacin ta, dasauri taɗago kanta tana kallon su


Mom ce kaɗai idanun ta ke kanta, yayinda shi kuma yake cin abincin sa hankalin sa kwance


Cikin daburce wa tace "Mom ban ji bane".


"Yayan ki ne ke magana".


Nazeefa sauke idanun ta kansa tayi tace "Yaya me kace?"


Sai alokacin yaɗago fararen idanun sa yana kallon ta, hararan ta yayi yace "ban sani ba".


Bata san sanda tayi murmushi ba sabida yanda yayi maganar har hararan sai kace wani mace


Mom ma sai da tamurmusa don itama taga sanda yayi hararan, cikin murmushin tace "ayi mata afuwa mana Auta wannan harara haka?".


Ajiye abincin yayi yana kallon Nazeefan da tasauke nata idanun ƙasa yace "meyasa baki taɓa zuwa gidana ba?"


Hannun ta tamatse waje ɗaya cike da fargaba taɗago kanta tana kallon sa tace "Yaya makaranta ne yahana Ni zuwa".


Hararan yasake aika mata dashi cikin ɗaure fuska yace "makarantan ne zai hana ki zuwa gidana?"


Mom tace "ai nima nayi godo da ita taje amma taƙi zuwa wlh, Ni bansan meke damun Nazeefa ba yanzu, ko ranan Saturday ɗin nan sai da nasake yin mata magana".


Nazeefa sad da kanta ƙasa tayi kamar zatayi kuka, ko kaɗan bata son zuwa gidan Yayan nata ba don komi ba sai don kishi, baza ta iya juran ganin sa da wata ba idan har ba ita ba


"Je ki shirya kizo mu tafi, ki haɗo da kayan makarantan ki don kwana zakiyi, idan kin wuce makaranta kya dawo nan".


Tashi tayi batare da tace uffan ba tanufi ɗakin ta, tana shiga tacire riga da skert ɗin jikin ta tasaka dogowar riga baƙi da yasha stone masu ƙyalƙyali, sosai take son dogoyen riguna shiyasa ma Mom Ko da ɗinki zata bada ayi mata, dogayen riguna take saka wa ayi mata, tunda ko anyi mata sauran ɗinkunan bata saka wa sai taga dama


Ɗan ƙaramin jaka taɗauka tasaka kayan makarantan ta sannan taɗau school bag ɗin ta tafito


Ko kaɗan bata murna da zuwa gidan Yayan nata, sai dai sauƙin ta ɗaya zata riƙa ganin sa yanzu



Tana fitowa Khalil miƙe wa yayi sukai sallama da Mom sannan yayi gaba Nazeefa tabiyo bayan sa bayan itama tayi ma Mom ɗin sallaman.



*_____________________*

A mota babu me magana cikin su, tun sanda yatambaye ta karatun ta be sake magana ba, hankalin sa na ga titi har suka iso gidan


Bayan yayi horn me gadi yabuɗe masa yasaka motan ciki, yana parcking suka fito atare, yana gaba tana bin sa a baya sai bin gidan take yi da kallo, komi an sauya ba kamar sanda tataɓa zuwa ba


Suna shiga babu kowa sai Husna dake wasa a ƙasa


Wajen ta Khalil yawuce yaɗauke ta yana saɓa ta sama yana mata wasa


Sai Nazeefa tasaki baki kawai tana kallon su


Sai shine da yajuyo yaganta har yanzu a tsaye yace "tsayuwar me kike yi kuma?"


Sai alokacin tadawo duniyar tunanin ta tasamu wuri tazauna


Shi kuma yawuce ɗakin Saleema da Husna a saɓe a wuyan sa


Yana tura ƙofan da sallama yahange ta zaune kan stool tana shafa Lipstick a bakin ta, tayi shiga cikin riga da skert na ɗan kanti, farar riga me gajeren hannu sai jan skert me ɗan faɗi tare da tsagi ta baya, kayan sun yi mata kyau gashi kuma sun ɗauki white skin ɗin ta, kanta da ɗan siririn ɗan kwali da taɗaura be gama rufe mata tsakiyar kai ba


Amsa sallaman tayi tana juyowa takalle su


Sosai tayi masa kyau yatako wajen yana kallon ta batare da yace komi ba


Sannu da zuwa tayi masa tana murmusawa


Ya'amsa mata still yana kallon ta kafin yace "kin yi kyau matata".


Rufe fuskarta da tafin hannayen ta tayi tana ɗan sakin dariya me sauti kafin tace "Nagode Mijina".


Shima sai yayi dariyan yana sauko Husna yariƙe ta sosai a hannun sa sannan yace "ga ƙanwata nan nazo da ita zata kwana gobe zata tafi".


Miƙe wa tayi ta'amsa mishi da "Toh". Tanufi ƙofa, shima yabi bayan ta


Suna fitowa idanun ta yahaɗe dana Nazeefa, har yanzu dai bata san wacece ita agare su ba duk da kuwa tasan ba ƙanwar Khalil ɗin bane, amma ta danganta hakan da ƙila ƴar uwansa ce


Zuwa tayi da fara'an ta tazauna


Ita kuma Nazeefa ganin Khalil shima yazo ya zauna ne tasaki fuskarta itama sannan tagaishe ta


Saleema ta'amsa mata tana murmusawa sannan tatambaye ta Mom? Ita kuma tabata amsa "tana nan lafiya tace agaishe ki".


"Yaya ko in kawo maka abincin nan ne?" Saleema tayi maganar tana kallon Khalil da yatasa Husna gaba yana faman mata wasa


Girgiza mata kai yayi batare da ya kalle ta ba yace "no sai nayi wanka zuwa anjima zanci".


Sannan yamiƙe tare da Husnan yanufi ɗakin sa


"Ƙanwata taso muje kici abinci". Saleema tafaɗa tana kallon Nazeefa da tabi bayan Khalil da kallo


Murmushi taƙirƙiro tana kallon Saleeman tace "a'a Aunty Alhmadulillah sai da naci abinci kafin na taho".


"Haba dai ko ɗan ruwa ne ai kya sha, bari in kawo miki".


Tashi tayi tanufi wajen Fridge


Nazeefa taraka ta da kallo, sosai take mamakin yarinyan da tagani don bata da masaniyar zaman ta agidan, har Mom ma itama sai daga baya tasani, sai kuma tataɓe baki aranta tace "to Ni ina ruwana".


Saleeman tadawo riƙe da
Drinks da taɗauro saman plate ta'ajiye Mata a gaban ta kan Centre table sannan takoma tazauna tana faɗin "bismillah".


Babu musu Nazeefa taɗauka Robbern Fanta tabuɗe tazuba cikin glass cup ɗin da tahaɗo mata dashi, tana sha suna kallo batare da ɗayan su ya sake magana ba tunda babu sabo ko kaɗan a tsakanin su



Suna nan zaune har Khalil yafito, da alamun yayi wanka ne don ya sauya kayan sa cikin shiga na ƙananan kaya wanda sukai ma jikin sa kyau sosai


Duk kansu kallon sa suke yi cike da tsantsan ƙauna


Shima dai kallon su yayi sai ya'aza idanun sa kan Saleema yaɗan ɗage mata gira ɗaya yace "My dear na wuce masallaci, ga ƴar ki can tana barci".


Murmushi Saleema tayi tace "to adawo lafiya".


Gyaɗa kansa yayi yanufi ƙofa yafice


"Ƙanwata muje in Kai ki ɗaki".


Maganar Saleema yakatse mata tunani, cikin son kawar da abunda yatokare mata maƙoshi tamiƙe da jakanta tabi bayan ta


Ɗakin ta takai ta sannan tafito tanufi ɗakin Khalil, anan ita tayi sallan ta kafin tadawo parlour


Alokacin shima Khalil ya dawo har ya zauna saman dainnig yana latsa wayan sa


Wajen tanufa tasoma saving ɗin sa sannan tajuya zata tafi


"Ke kinci abincin ne?"


Juyowa tayi tana kallon sa sannan tagyaɗa masa kanta tana murmusawa


Be ce komi ba yaɗau spoon ɗin yasoma cin abincin sa



Nazeefa tunda tagama Sallah tazauna nan kan sallayan taƙi tashi, sai ma zuba tagumi da tayi ta'af ka tunani


Bata sake fitowa ba har dare


Koda Saleema tashigo tayi mata maganar tafito Parlour ko zata fi jindaɗi, sai tace "a'a nan yayi mata".


Juyawa tayi kawai tabarta takoma parlour taci gaba da kallon ta don shi tuni Khalil ya shige ɗakin sa yana faman aiki a Library ɗin sa



Daga karshe da tagaji da zaman sai tanufi kichen tayi musu girki me sauƙi, taliya tadafa da raguwar miyan ta na jiya


Sai da tagama komi taje tajera a dainning table, lokacin har an kira sallan magriba


Ɗakin Khalil ɗin tanufa tashiga ciki, alokacin ya fito daga Toilet bayan ya ɗauro alwala, kallon ta kawai yayi yafice dasauri


Ita kuma tanufi kan gadon inda Husna ke kwance tarigada ta farka tana ƙananun kukan ta, ɗaukan ta tayi tanufi ɗakin ta da ita


Shiga tayi da sallama a bakin ta, kallon Nazeefa dake sallah tayi tawuce cikin Toilet


Kayan Husna tacire tawanke mata kashin da tayi sannan tayi mata wanka tafito taɗaura ta kan gado, sai takoma taɗauro alwala tadawo tagabatar da Sallah


Nazeefa na zaune akan kujera tana faman kallon Husna dake ta mutsil-mutsil cikin towel da aka nannaɗe ta dashi tana son cire wa tasauko


Har Saleema ta'idar da sallan ta tamiƙe tasoma shirya Husnan, ta kula Nazeefa ba me son yin magana bane shiyasa itama taƙyale ta batare da ta kula ta ba, amma abinda yadace tana tambayan ta


Har tagama abinda zatayi tafito Parlour tazauna tana ma Husna wasa tana kallo


Sai bayan isha'i sannan Khalil yadawo gidan



Suna zaune kan dainning shi ya ɗaura Husna ajikin sa yana cin abinci yakalli Saleema da itama take saving nata yace


"Ina Nazeefa ne?"


"Tana ɗaki tana sallah nayi mata magana yanzu zata fito.."


Bata rufe baki ba nazeefan tafito taƙariso wajen tana gaishe da Yayan nata


Amsa wa kawai yayi yaci gaba da cin abincin sa


Itama zama tayi tayi saving kanta tasoma ci, can kuma taɗago kanta tana kallon sa yanda duk yabada hankalin sa kan Husna ko abincin ma baya ci sosai


"Yaya wai wannan yarinyan wacece?" Tayi tambayar tana ci gaba da kallon sa


Daga shi har Saleema suka ɗago kansu suna kallon ta


Sai da yakau da kansa gare ta kafin yace "Ƴata ce".


Bata sake cewa komi ba taci gaba da cin abincin ta sai dai zuciyarta haushin amsar da yabata take ji


Ita kuwa Saleema murmushi kawai tayi tana kallon Khalil ɗin cike da ƙaunar sa, sannan taci gaba da cin abincin ta


Shi yasoma tashi yanufi ɗaki


Kamar ana tsikarar Nazeefa tana ganin ya shige itama tamiƙe tanufi parlour


Saleema dai bata ce mata komai ba illa kallo ɗaya da tayi mata taɗauke kanta, sai da tagama tattara komi takai kichen sannan tanufi ɗakin ta


Wanka tayi tasanya kayan barci sannan taɗau abubuwan da zata buƙata tare dana Husna tafito tana kallon Nazeefa dake zaune tana kallo


"Ƙanwata koda akwai abinda kike buƙata ne?"


Sai alokacin Nazeefa taganta ma, kallon ta kawai take yi cike da tsananin kishi, tasan tunda tagan ta da shiri ɗakin Khalil zata tafi


"Kenan ko hiran daren ma basuyi sai su shige ɗaki?" Tatambayi kanta tana ci gaba da kallon Saleeman cike da tsantsan haushin ta


Ita kuma Saleema ganin tayi shiru sai tabuɗe ɗakin Khalil kawai tashige abunta aranta tana jinjina wulaƙacin yarinyan, ko ba komi ai ita Matar YaYanta ne bare ma ta girme mata sosai don aƙalla zata bata shekaru uku ƙwarara


Tana ganin ta shige itama tatashi tanufi ɗakin Saleeman zuciyarta kamar zata tarwatse, har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙoshin ta.



Sai Khalil ne daga baya yafito yakashe t.v n yakulle ƙofan Parlourn yakoma ɗaki.



Washe gari ƙarfe 07:20am. Ya riga ya gama shirin sa har breakfast yayi sannan yafita


Lokacin itama Nazeefa tafito da shirin ta na makaranta tana rataye da school Bag ɗin ta tare da jakan da tasaka kayan da tacire, fuskarta duk babu walwala idanunta sunyi luhu-luhu kamar wacce bata samu ishashshen barci ba



Saleema dake kakkaɓe parlour'n taɗago tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace "Ƙanwata har kin fito?"


Itama Nazeefan murmushin tayafa ma fuskarta sannan tace "eh Aunty Ina kwana?"


"Lafiya lau kin tashi lafiya? Ya baƙunta?" Saleema tasake yin maganar da fara'a


"Alhmadulillah".


"Ok ga breakfast ɗin ki kizo kici".


Nazeefa tace "a'a bazan iya cin komi ba, zan tafi Aunty sai kuma wataran in na sake dawowa ki gaida yaya".


Saleema kallon ta kawai take yi cike da mamakin ta, sai kuma dai batace komi ba ta'amsa mata sannan tabata saƙon gaisuwa wajen Mom


Tana kallo Nazeefan har tafice sannan taci gaba da aikin ta



Drever yaɗauki Nazeefa yanufi da ita school ɗin su.
[11/16/2020, 6:56 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Four*

________🎓 *TWO MONTHS AGO*

A cikin wannan watannin abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da soma zuwan Halwa makaranta, tayi farin ciki matuƙa


Da farko Saleema ce ma Abba tayi yakaita Abroad tayi karatun, har Abba ya amince amma Halwa ita tace sam bata son tayi nesa dasu dole aka barta anan Katsinan


Tunda tasoma zuwa school ɗin babu ruwan ta da kowa harkan gaban ta kawai take yi, kuma sosai take gane karatun tunda shi tasaka a gaba


Duk da kuwa mutane da dama suna sonn ƙulla alaƙa da ita amma taƙi yarda musamman ma maza da yawancin su suke nuna suna son ta, wannan dalilin ne ma yasa take saka niƙap, da zaran drever ya kawo ta zata ɗau niƙap ɗin ta tasaka, idan kuma yazo ɗaukar ta sai ta shiga motan sai tacire


Har yanzu ta kasa manta tabon ɗa namiji cikin rayuwan ta, ta kasa manta abinda Haris yayi mata, sannan takasa manta abinda Nura yayi mata duk da kuwa har yanzu zuciyarta na mishi uzuri


Ko kaɗan ta tsani namiji yanuna yana son ta sabida tarigada ta cire soyayya cikin ranta


Zuwan ta gidan Saleema sau biyu shima daƙyar taje don aranta ko kaɗan bata son sake haɗuwa da Mijin nata da yatsaya mata arai yaƙi gushe wa, sau tari tana tunanin sa sai taji gabanta ya faɗi kuma tarasa me yasa, sai dai tana ƙoƙarin yakice sa aranta musamman ganin ta dena tuna sa gaba ɗaya, sosai take mamakin haɗuwa da cikan halitta irin Mijin Saleema, sai yanzu tagane abinda Saleeman tahango atare dashi har tamutu a ƙaunar sa haka, domin samun irin sa sai wanda yake da babban daraja wanda kuma yakai


Zuwan da tayi gidan duk sun haɗu amma gaisuwa kaɗai ke haɗa su, shima daga nan ko kallo baya sake yin mata har kuwa tatafi


Don shima a nashi fannin sosai yake son cire ta aran sa musamman yanzu da yasan matsayin ta a wurin shi, yana auren ƴar uwan ta, ko kaɗai baya son abunda zai kawo saɓani a tsakanin zaman sa da matar sa tunda yana jindaɗin zama da ita ainun


Amma abinda akace zuciya na so babu me iya raba ta da shi, bare shi da ya jima a ƙaunarta tun lokacin da be san ita ɗin wacece ba, a kuma kallo ɗaya da yayi mata, sau da dama yana mamakin irin Wannan soyayyan, har zama yake yi yayi ta tambayan kansa "wai dama ana soyayya irin haka daga kallon farko da akayi wa mutum koda kuwa baka san ko shi waye ba? Koda kuwa bakasan zaku sake haɗuwa ba?" A yanda take zuwa masa a mafarkin sa ne yake basa mamaki, kullum idan har be yi mafarkin ta ba to zai yi tunanin ta, idan har zata zo mishi kuma a mafarkin tana me kuka ne tana neman taimakon sa, ya kasa gane irin wannan mafarkin musamman yanzu da yaganta cikin gatan ta.





*______________________*

A fannin Nazeefa ma tana nan tana ta fama da son maso wani, ta ari damuwa duk ta yafa ma kanta, yanzu abun har yakai ko karatun ta bata maida hankali a kanshi



Mom tayi mitan sauyawan ta har ta gaji amma taƙi faɗa mata abinda yake damun ta



Wannan halin da take ciki kullum idan taje makaranta bata kula kowa ko ajin ma sai taga daman shiga, da zaran taje zata wuce bayan makarantan inda ɗalibai ƴan Pramary suke wasa taɓoye anan tazauna tayi ta tunanin ta


Ƙawarta Haneefa ita take damun ta kullum tafaɗa mata damuwarta, ta kai ta kawo ma har faɗa sukayi akan ƙin faɗa mata da tayi, daga ƙarshe dai Haneefa da taga fushin bazai kai ta ko ina ba sai tadawo tana rarrashin ta don tasanar mata damuwarta, daƙyar dai Nazeefa tabuɗe baki aranan tasanar mata tana yi tana kuka kamar ana yankan naman jikin ta, har wani rawa jikin nata yake yi sabida tsaban yau komi ya kai mata maƙura


Haneefa na zaune gefen ta tana bin ta da idanu cike da tsananin mamakin ta, bata hana ta yin kukan ba har sanda tayi ma'ishi tafitar da duk ƙuncin dake cikin ranta, sannan ne tadafa kafaɗan ta da hannu ɗaya tace


"Ban taɓa tunanin akan ɗa namiji bane kika shiga duk wannan damuwar Nazeefa, sabida ɗa namiji kika dena shiga aji kika dena mayar da hankalin ki kan karatun ki duk a sabida ɗa namiji? nayi mamaki wlh ƙawata duk kyawun ki kizauna kina ma ɗa namiji kuka".


Shiru Haneefa tayi tana jan numfashi tare da tsare Nazeefan da idanu


Ita kuma Nazeefa alokacin ne taɗago kanta tana kallon ta da rinannun idanuwan ta tace "baza ki gane a halin da nake ciki bane Haneefa, zuciyata tariga da ta mutu a ƙaunar sa, nayi duk iya abinda zanyi don in cire sa araina amma na kasa, wlh ji nake yi kamar in mutu saboda yanda nake ji a kansa, bana jin zan iya auren wanin sa idan bashi ba, bazan taɓa zama da kowa ba sai shi, tun bansan meye so ba zuciya ta takamu da mahaukacin ƙaunar sa har sanda nagane, gashi yanzu yayi min ratan da samun sa babban wani aiki ne agare Ni".



Dariya ma abun yaba ma Haneefa, sai tasaki baki tana yi


Hararan ta kawai Nazeefa tayi tana ɗauke kai cike da haushi


Tsai da dariyan Haneefa tayi tace "ƙawata kenan kin faɗa da yawa, Ni kuwa zan so ganin wannan Jarumin me babban matsayi a wurin ki, amma fa idan har kina son samun sa to ba wani babban aiki bane a wurin ki ƙawata sai dai idan kece baza ki bi hanyan da yadace ba, Allah na tuba don yana da mata sai kice yayi miki nisa?"


Kallon ta kawai Nazeefa take yi kamar idanun ta zasu faɗo ƙasa har sanda tadire aya kafin taɗaura da nata


"Wace hanya ce tadace da zanbi don samun sa? Kina ganin har akwai sauran hanyan da zanbi Ya Khalil yakalle Ni a matsayin Masoyiya?"


"Ƙwarai kuwa, me zai hana ki faɗa ma Mahaifiyarsa tunda ita tabuƙaci haka, na tabbata wlh zata share miki hawayen ki tunda tana ƙaunar ki".


Shiru kawai Nazeefa tayi don tasan baza ta taɓa iya faɗa mata ba, to taya shi Khalil ɗin zai kalli maganar? Abinda take tunawa kenan, ba wai faɗan bane.. matsalan ta na ga Uban gayyar".


Maganar Haneefan ne takatse mata tunanin ta, taɗago tana kallon ta cike da wani irin kallo me wuyan fassara, bakin ta har rawa yake yi wajen cewa


"Baki da hankali ne wannan wani irin shawaran banza ce? No bazan taɓa iya aikata hakan ba, idan kuwa nayi masa haka tabbas na zama butulu, tabbas idan na aikata hakan mutane zasu zage Ni sannan zasu la'ance ni tunda ban riƙe maraicina ba.."


Sai kuma tagirgiza kanta cikin kuka tace "bazan taɓa iya aikata masa haka ba, wlh gwara in mutu da in je wajen boka in cutar da wanda yataimaka min".


Haneefa cikin son nuna mata abunda take nufi tace "ƙawata ki gane mana hakan shine kaɗai mafita kuma hanyan da zaki samu zuciyar sa..."


Ɗaga mata hannu Nazeefa tayi tace "ya isa bana son ji, Kar ki sake min irin wannan maganan".


Tana faɗan haka tamiƙe tawuce tabar Haneefa nan zaune baki

Please Login or Register in order to submit comment