Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaɗauke kansa yamayar ga Brr. Tahir, be ce masa komi ba hakan yasaka Brr. Tahir yatashi yafice

Shiru ne yabiyo bayan fitan Brr. Tahir, ita Saleema tunani kawai take yi yanda Khalil ɗin yasauya mata sosai fiye da yanda tasan shi, wani irin kyau da kwarjini yasake yi tare da wani irin gogewa yasake ƙiba, kai da gani kasan hutu da kwanciyan hankali tare da kuɗi sun zauna masa, so take yi tasake ɗago kai takalle sa amma ta kasa domin yanda take jin idanun sa masu matuƙar kaifi suna yawo ajikin ta, shi kuwa a nashi fannin zuba mata idanuwa yayi yana ta kallon ta, a haƙiƙanin gaskiya dogon tunani yafaɗa har be san iya adadin mintocin da suka wuce ba, Saleema dai har ta gaji taɗago kanta tana kallon kyakykyawar fuskar sa da yatsare ta da kallo, cikin sanyin murya tace

"Ko in Kira Abokin ka ku fara cin abincin ne?"

Sai alokacin yaɗan ƙifta idanun sa da alamun yadawo tunanin sa, kallon ta yayi yana ɗan jije leɓe, ba ƙarya ayanda yafahimta yarinyan zatayi sauƙin kai, duk da ba wai tayi masa yanda yake so bane kuma ba wai yaji ta a ransa bane, but ta kwanta masa arai kuma zai iya zama da ita a matsayin matar sa, ajiyan zuciya yasauke kafin yace

"Kina lafiya?"

Saleema da har tagaji da shirun nasa tasad da kai ƙasa tana wasa da yatsun ta, jin sassanyan muryan sa me daɗi yasaka ta ɗago kai tana kallon sa kana ta'amsa mishi cikin biyayya da son burge shi

"Nasan kinsan me yakawo ni nan ɗin don nasan an riga da an miki bayani? Any way ni sunana Brr. Ibrahim Khalil Abdurra'uf, ina fata.."

Shiru yayi don be san me zai faɗa ba, ita kuwa kallon sa kawai take yi tana jin yanda muryan sa me tsananin daɗi yake shiga kunnuwan ta, kamar an matse bakin sa sai yace mata

"Me kike karanta a School?"

Cike da farin ciki ta'amsa masa da "Pharmacy".

Gyaɗa kansa yayi sai kuma sai kuma yayi shiru yana ajiyan zuciya, wayan sa yaɗauka kana yaɗago kai yana kallon ta yace "kiyi haƙuri ni ba gwanin iya soyayya bane Thats why ban iya hiran ba".

Murmusawa tayi kawai tana sunkuyar da kai, sosai yaburge ta hakan na nufin kenan be taɓa budurwa ba kamar yanda itama bata taɓa yi ba? Duk kallon da take masa bata taɓa tunanin yana da sauƙin kai irin haka ba

Brr. Tahir yakira yace masa "yashigo". Babu jimawa kuwa yashigo yana kallon su yana murmushi yace

"Har an gama hiran?"

Khalil be basa amsa ba sai miƙewa da yayi yana saka wayan sa a aljihu hakan yasa Brr. Tahir cewa

"To Amarya mu zamu tafi, sai kuma gani na gaba".

"To bakuci komi ba".

"No karki damu next time idan muka zo zamuci yanzu muna sauri ne".

Gyaɗa kanta tayi tana tashi tsaye, daga nan raka su tayi har wajen motan su kafin suka sake sallama tataho gida.








.


_More Comments More post._🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️
[11/1/2020, 9:23 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```


.

*CHAPTER 39*


*AFTER SEVEN MONTH*

A wannan watannin da suka shuɗe abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da haihuwar da Halwa tayi, ta haifi yarinyan ta kyakykyawa me ban sha'awa, sosai yarinyan take kama da ita, sai dai kuma ta ɗakko abubuwa da dama na mahaifin ta wanda idan kakalle ta tabbas zakasan ƴar sa ce, sunan Ummi aka saka mata kamar yanda Saleema tabuƙaci asaka, wato Asma'u suna kiran ta da Husna, duk wani hidima kama daga kan kayan Baby zuwa na uwar Babyn babu abinda Abba be siya musu ba, komi ya wadata su dashi tamkar tana gaban iyayen ta, tun sanda tahaihu kuma Ummi tace "baza ta shayar da yarinyan ba". Don haka da madaran kanti ake shayar da ita, Halwa sosai taji daɗin hakan ko ba komi an ɗauke mata wani nauyi kuma an taimake ta, duk wani hidiman yarinyan Saleema ce me yi, kullum yarinyan tana hannun ta ita take kula da ita, ita take mata komi sai dai wanka da Larai ƴar aikin su take mata, ita kuwa Halwa sai dai taci tasha takwanta hakan yasaka gaba ɗaya tasauya tasake ƙiba tayi kyau gunun sha'awa, dama gashi tana tsaka da jego ne kuma ga hutu da yayi mata yawa

Yanzun ma zaune take agaban madubi tana shafa lipstick a ƙananun laɓɓan ta, fuskarta babu wani kwalliya illa powder da tashafa sannan tazizara kwalli cikin idanuwanta, miƙe wa tayi tana gyara zaman rigan ta, doguwar riga ce na atamfa tasaka Milk and Coffee colour, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau duk da kasancewar ta bata da hasken skin, Halwa irin Chocolate Colour ɗin nan ce me ɗan haske, tana da kyau na ban sha'awa da burgewa, idan har zaka ganta to dole sai ka sake kallon ta coz yanayin ta da komi nata yana da kyan kallo, bata da wani tsayi amma tana da ɗan kauri kaɗan tare da sura me kyau da ɗaukan hankalin me kallon ta, duk da kuwa ita ɗin ba ma'abociyar son cin abinci bane, kallo ɗaya idan kayi mata zaka fassara ta da me sanyi don ko a maganarta ne cikin sanyi sosai zakaji muryan ta, sai dai kuma akwai ta da tsiwa sannan tana da surutu matuƙa sai dai idan bata sami wajen yi ba

Tana cikin ɗaura ɗankwali Saleema tashigo ɗakin, itama ɗin doguwar riga tasaka iri ɗaya da na Halwa har ɗinkin da komi, Ummi taba da aka ɗinka musu wajen kala bakwai lokacin da Halwan tahaihu, itama ɗin sosai yayi mata kyau kasancewar ta fara ce, murmushi tasakar wa Halwa kana tace

"Kinyi kyau Sister".

Murmushi Halwa tayi tana kallon ta tace "Thanks".

"Ok Ina kayan Husna? Larai ta gama mata wankan za'a shirya ta".

"Ban ciro mata ba". Halwa tabata amsa tana saka Room Slippers a ƙafafuwan ta da suka sha lalli ja da baƙi

Saleema wajen kayan Husna tanufa tana cewa "but sai da nace miki ki ciro kafin in dawo fa"

Ƙarisawa kusa da ita Halwa tayi tana taya ta cirowa tace "I'm sorry Sis, ban gama shiryawa bane shiyasa".

"Ok".

Fita sukayi gaba ɗayan su bayan sun gama ɗaukan abinda zasu ɗauka, suna fita parlour Halwa zama tayi akan sofa ita kuma Saleema tawuce da kayan ɗakin Larai, can kuma sai gata tafito ɗauke da Husnan a hannu, an shirya ta tsaf-tsaf cikin kayan ta masu kyau, zuwa tayi tazauna gefen Halwa tana cewa

"Kinga Babyna yau tayi kyau sosai, har carbing mukayi mata".

Halwa kallon yarinyan tayi sai kuma taɗauke kai tana yamutsa fuska kamar yanda tasaba

Kallonta Saleema tayi tace "Yauwa Sis idan nayi aure kema zaki dawo gidana ko? Sai mu zauna tare".

Murmushi Halwa tayi tace "to sai mu bar Ummi da wane? Kinga ke kin tafi dole zasuyi kewarki".

Gyaɗa kai Saleema tayi kana kuma tace "but duk da haka dai zaki riƙa zuwa kina min sati ko fiye da hakan, kinga kuma Ni ban ma iya girki ba idan naje wanene zai min?".

Halwa tace "zaki sami House girl ne sai tayi miki".

Kwaɓe fuska Saleema tayi tace "no bana son ƴar aiki sai dai muje muriƙa yi tare dake".

"To ai nima ban iyaba wlh". Halwa tafaɗa tana dariya

Dariya itama Saleema tayi tace "haba dai? Kice duk jirgi ɗaya taɗauko mu?"

"Eh mana, ko Mama tasaka Ni bana yi har ma ta saba ta dena cewa inyi, sabida Ni dai gani nake yi tunda bana cin abincin to bazan koya ba".

Still dariya Saleema tayi tace "tabb ai kuwa dole mu saka Larai gaba takoya mana".

Ummi ce tayi sallama tashigo

"Oyoyo Ummi". Cewar Saleema tana miƙe wa ta'isa wajen ta

Ummi kuma amsan Husna tayi tana dariya tace "iyeee ga takwarata ga takwara ta".

Sannu da zuwa sukayi mata sannan tazauna tana cewa "Abban ku be dawo ba?"

Saleema tace "ya dawo ya fita ne".

"Ok".

Yarinyan tamiƙa wa Saleema sannan taɗau jakan ta, ita kuma Halwa lokacin tadawo ɗauko ma Ummi ruwa tace

"Ummi ga ruwa kisha".

Murmushi Ummi tayi tace "Yauwa na gode".

Har ta juya Ummi tasake cewa "zo riƙe wannan ledan".

Halwa amsan ledan tayi tana kallo

"Magani ne idan Larai zatayi miki wanka sai ki riƙa Using dashi".

Gyaɗa kai Halwa tayi tana komawa tazauna, ita kuma Ummi miƙe wa tayi tanufi ɗakin ta, sai da tashige sannan Saleema tace

"Menene acikin ledan?"

Kallon ta tayi taɗage kafaɗa alamun bata sani ba, sai kuma tace "ki tambayi Ummi".

Ɗan waro idanu Saleema tayi sai kuma tasaki dariya tace "ai bazan iya bane wlh".

Harara Halwa tayi mata tace "ashe kin sani kenan kike tambaya?"


.

**** ***** ***** ******

Wani irin kallo take masa har sanda yadasa aya a maganar sa sannan tabuɗi baƙi cike da baƙin ciki tace

"Wlh Nura kabani mamaki domin ban taɓa tunanin haka halinka yake ba, har Ni zaka dubi idanuwana kace kana so na? Idan har baka bar mana ƙofar gida ba wlh zan maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba..'

Bata rufe baki ba Nura yace "haba Zainab wai meye laifina anan? me namiki da baza ki so ni ba? Kar ki manta fa wacce kike tunani akanta bata nan don me baza ki bani dama in maye gurbin ta dake ba, wlh ina ƙaunar ki tsakani da Allah.."

Cikin wani irin tsawa Zainab takatse shi

"Dalla kayi mana shiru, duk wani mutunci da nake gani naka wlh ka ɓarar dashi, bari kaji wlh koda maza sun ƙare a duniya Nura bazan taɓa son ka ba bazan taɓa auren ka ba, har yanzu kallon ka nake yi a matsayin saurayin ƙawata kuma Ni bana cikin maciya amana, and nasan da cewa Halwa baza ta taɓa barin ka ba coz nasan irin ƙaunar da take maka, duk inda take a faɗin duniya tana nan tare da kai aranta, idan ma har wani abu kuka ƙulla domin tabar gidan nan to wlh kun ci amanarta".

Wani irin kallo tabuga masa kafin taci gaba da cewa "kasani duk inda Halwa tatafi zata dawo wannan alƙawari ne, anan ne zan tabbatar maka da cewa ita ɗin me ƙaunar ka tsakani da Allah ne ba irin ka ba".

Daga haka tajuya tashige gida batare da tabari yasake furta komi ba, shiru Nura yayi yana kallon hanyan da tabi, ya jima anan tsaye kafin yabuɗe kyakykyawar motar sa yashiga yabar wajen, gidan da yasiya wa iyayen sa yanufa, yana zuwa yadanna hon aka buɗe masa Gate yakutsa motan ciki, bayan yayi parcking yafito yashiga cikin gidan, Mama na zaune a parlour tana faman kallon da tasaba, don tunda suka dawo gidan da zama yazame mata jiki kallon, zama yayi akan kujeran da yake Facing ɗin nata, ita kuma kallon sa take yi ganin yanda duk yasauya face ɗin sa kamar wani abu na damun sa, hakan yasaka tatambaye shi da cewa

"Lafiya Nura meke damunka ka fita cikin walwala kadawo fuska a turɓune?"

Sai alokacin yakalle ta yace "Mama Zainab ce".

Numfashi Mama taja don tariga tasan da zancen, sai da taɗan ɗau lokaci tana ci gaba da kallon sa kafin tace "wai ni Nura meyasaka baza ka nemi wata bace sai ita? Taya zaka zauna yarinya tana wulaƙanta ka amma kaƙi kasauya ta? Ni fa dama hankalina be kwanta da ita ba tunda ita ɗin ƙawar Halwa ce ƙut da ƙut, kuma dama abokin ɓarawo ai ɓarawo ne ban ɗauke tsammanin itama halin su ɗaya ba".

Cike da rashin jin daɗin kalaman Maman nashi yace "Mama don Allah ki dena aibanta ta, Ni nasan Halin Zainab baza ta taɓa aikata abinda Halwa tayi ba duk da kuwa suna ƙawaye, kuma Ni ita kaɗai nake jin zan iya aura sabida ina matuƙar ƙaunar ta tun ba yanzu ba, kawai ki taya ni da addu'a shine nafi buƙata a wajen ki".

Yana ƙarisa maganar nasa yamiƙe yayi hanyan fita, ita kuma Mama tabi shi da kallo har yafice, sai kuma takaɗa kai cike da tausayin ɗan nata a ranta tana masa fatan alkhairi


...... ...... ...... ...... . ..
Tun tafiyan Halwa babu daɗewa Nura yazo ma iyayen sa da zancen zai tafi Legos wani kasuwanci acewar sa bazai dogara da aikin gwamnati ba, dama can yana siye da sayarwa ne na kayan gona, yanda yayi musu bayani akan kuɗin da zai iya samowa hakan yasaka basu wani ja maganar ba suka barsa yatafi, to be rufa watanni uku ba yadawo da zunzurutun kuɗi acewar sa sana'ar da yayi ne Allah ya albarkace sa, iyayen sa sunyi murna matuƙa da samuwan ɗan nasu, acikin lokaci ƙanƙani Nura yayi kuɗi ya buɗe shaguna da yawa ya saka masu kula dasu, kuma ya siyan ma iyayen sa gida me kyan gaske suka koma, sannan shima ɗin yasoma ginin sa inda zai yi aure

Tun dawowar sa yasoma neman Zainab a matsayin wacce zai aura, amma har yanzu ita Zainab taƙi amincewa dashi, shi kuma yaƙi haƙura da ita sabida mugun son da yake mata.





.




_To ya za'a kaya?_


_Plz Kar ku manta kuyi_

*Shere*
*Vote*
*Comments.*
[11/1/2020, 9:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```

_*NANA FARUK* wannan shafin naki ne ke kaɗai, Allah yabar ƙauna🥰_


.


*CHAPTER 40*


Turo ƙofan Mom tayi tashigo cikin ɗakin, Nazeefa dake zaune tsakiyan gado ta tanƙwashe ƙafafun ta tana faman tunani taɗago kai tana kallon Mom ɗin, ita kuma ƙarisowa tayi tazauna gefen gadon tana kallon ta tace

"Meke damunki Nazeefa?"

Nazeefa kallon Mom tayi tace "babu komi Momy".

"Ban yarda ba ki faɗa min gaskiya idan da akwai abinda ke damun ki, gaba ɗaya na lura dake tun da daɗewa kina cikin damuwa, kullum cikin tunani kike kuma kinƙi kifaɗa min abinda ke damun ki, bana son in ganki cikin damuwa hakan na damuna coz Ina jinki tamkar ƴata ta cikina ne".

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana jin hawaye na son zubo mata, idan da tana da daman faɗa mata abunda ke damun ta da tuni tadaɗe da sanar mata, sai dai kashhh baza ta taɓa iya faɗa mata gaskiyan abinda ke cin zuciyarta ba

Dafa bayanta Mom ɗin tayi tace "ki sanar dani kinji Nazeefa zan miki duk abinda kike buƙata idan har ina da halin yi, bazan taɓa barin hawayen ki yazuba ba zan kasance me share miki hawayen ki".

Wani irin sanyi Nazeefa taji acikin ranta tare da wani irin ƙaunar Mom na sake shiga zuciyarta, sai dai baza ta taɓa iya faɗa mata ciwon son ɗanta ne yakamata ba, "to taya?" Hawayen da taji suna son zubo mata ne tayi saurin mayarwa tana ɗago kai takalli Mom cikin sanyin murya tace

"Momy babu abinda ke damuna, idan har akwai kece ta farko da zan faɗa miki sabida na ɗauke ki tamkar ke kika zuƙuna kika haife ni, ki yarda dani Momy babu abinda ke damuna".

Shiru Mom tayi tana kallon ta, sai dai ko kaɗan bata yarda babu abinda ke damun ta ba bcoz ko wanene yaga halin da take ciki dole yatabbatar wa kansa tana cikin tsananin damuwa, sosai take mamakin abinda ke damunta har takasa bayyana mata, amma kuma tayi wa kanta alƙawari sai ta gano ko me ke damun ta kuma sai ta share mata hawaye da iznin Allah, ajiyan zuciya tasauke kafin tace

"To shikenan na yarda dake, amma duk abinda ke damun ki kiyi gaggawar sanar dani ki dena ɓoyewa kinji?"

Gyaɗa kanta Nazeefa tayi sai kuma tace "insha Allahu Momy".

"Ok tashi ki cire kayan makarantan akwai inda zaki raka Ni".

Amsa mata tayi tana tashi tare da saukowa daga kan gadon, itama Mom tashi tayi tafice a ɗakin, sauya kayan ta tayi tasanya doguwar rigan abaya Blue Black, sannan sai tayi Rolling da ɗankwalin abayan, komai bata shafa a fuskarta ba illa flat shoes da tasanya a ƙafafuwan ta, sosai tayi kyau white skin ɗin ta sai sheƙi yake yi kasancewar ta samu hutu har wani ƙiba tayi tare da ƙara girma, fita tayi ta'iske Mom a parlour suka fice, motar Mom ɗin suka hau drever yatuƙa su suka bar gidan.

A wani ɗan madaidaicin gida Drever yasauke su suka fito suka shiga, matar gidan tana zaune a parlour tatarbe su cikin fara'a tare da kawo musu Drinks, sai da suka ɗan yi hira kafin Mom tace

"Yauwa Hajja Turai maganar da muka fara dake a waya ne akan kayayyakin da zaki ɗauko min a London, don haka shiyasa nataho muyi maganar sosai sai ki faɗa min da yaushe zaki tafi?"

Cikin fara'a Hajja Turai tace "ai ina da kaya a ƙasa gaskiya ba yanzu zan koma ba, inaga sai nan da One Month, yanzu abinda yakamata dai sai kiyi min list ɗin komi kibani hakan zai fi, bari in ɗauko miki Littafi".

Miƙe wa tayi tashige ɗaki babu jimawa tadawo riƙe da Littafin tamiƙa mata, Mom amsa tayi tana cewa

"Yauwa sannan kuma zan baki saƙon ƴata ga tanan, itama ɗin kizaɓo mata kayan fitan biki masu matuƙar kyau, acikin gwala-gwalan da zaki siyo min sai ki ɗaukar mata ɗaya, Ni dai ina son ki gwangwaje ta sosai komi yakasance Expensive ne nata".

Dariya Hajja Turai tayi tana kallon Nazeefa tace "ai babu matsala Hajiya Hajara duk abinda kikeso hakan za'a yi, amma ko itace Amaryan don naga kina ji da ita?"

Mom tace "a'a ƙanwar sa ce ai".

"Allah Sarki". Cewar Hajja Turai still tana kallon Nazeefa

Mom tace "don Allah Hajja kaya masu kyau nake so sabida kinsan bikin Autana ne that's why nazo wajen ki, and sai kuma Furnitures ɗina don Ina son nasauya komi na ɗakina".

"Baki da matsala insha Allahu duk abinda kikeso zan yi ƙoƙarin naga na samo miki dai-dai da zaɓinki".

Ita kuwa Nazeefa da tun sanda tazauna tasad da kai ƙasa tana sauraron su, wani irin ƙunci take ji a maƙogaron ta, ji take yi tamkar tabuɗe baki tayi ta zunduma ihu sabida tsaban baƙin ciki, har hawaye sai da tai ta sharewa batare da sun kula da ita ba suna ta tattaunawa, bayan Mom ta gama yin mata list ɗin gaba ɗaya sannan sukayi sallama suka fito, har wajen mota Hajja Turai tarako su sai da taga fitarsu kafin takoma cikin gida

Suna cikin motan Khalil yakira Mom, bayan tayi peacking call ɗin suka gaisa take cewa

"Ɗazu ka kira bana ji ne matsalan network ne, yanzu kuma muna kan hanya ne naje gidan Hajiya Turai".

Khalil da be san ma wacece Hajiya Turan ba sai tambayan ta da yayi "me taje yi?"

Nan take faɗa masa sannan taƙara da cewa "wai kuwa kana kiran surukar tawa don nasan Halin ka?"

Shiru yayi don be san amsan da zai bata ba, shi idan har basu suke masa maganar bikin ba sam mantawa yake yi zai yi aure, kuma ita yarinyan tun sanda yabar ƙasar yamanta irin ta, ko za'a tsare sa da bindiga yafaɗa yanda take bazai iya ba, abinda yasani kawai fara ce ita but kamannin ta ya daɗe da gushe masa, sunan ta ma kanshi be riƙe ba duk da su Mom wani lokacin suna faɗar sunan idan suna waya

"Kayi shiru ko dai dagaske ba ka kiran ta?'

"Ina kiran ta mana Mom". Yafaɗa cike da sanyin murya don shi sai yanzu yasan be kyauta ba tunda ko Phone numbern ta be amsa ba

Daga nan sallama suka yi Mom ta'ajiye wayan cikin jaka, kallon Nazeefa da tatakure a jikin motan tayi idanuwanta a rufe ruf, numfashi kawai Mom taja tana ɗauke kai.


.


*** *** *** *** *** ***

Da hannu biyu tazuba tagumi tana tunani har batasan sanda Mami tashigo tatsaya a kanta ba, sai da tagama ƙare mata kallo kafin takira sunan ta

Firgigit Kausar tayi tana ɗago kai takalli Mamin nata

"Wai ke lafiyan ki lau kike yawan tunani meke damun ki ne?"

Shafo fuskarta da hannun ta tayi cikin sanyin murya tace "babu komi".

"Baza ki faɗa min ba kenan?".

"Mami babu komi fa tunanin aiki ne kawai".

Gyaɗa kai kawai Mami tayi kafin tace "to ki tashi kije Sharif na parlour yana jiran ki".

Kausar kallon Mamin tayi fuska babu walwala tace "Mami kice masa bana nan Ni bazan iya fita ba".

"Wai ke kanki ɗaya kuwa? Wai meyasaka yanzu bakison fita ne idan yazo? Ko faɗa kukayi ne?"

Kausar tace "a'a kema Mami kinsan Da da yanzu ba ɗaya bane, bana son takura ne kawai".

Baki Mami tabuɗe tana kallon Kausar, ita kanta da take Mahaifiyar ta tasan Kausar ta sauya, gaba ɗaya ta dena walwala agidan, sai tashige ɗaki ita kaɗai tazauna su rasa me take yi cikin ɗakin, kuma duk uzurin da zata kawo be da wani kan gado, ajiyan zuciya tasauke kafin tace

"Ki fito ki same sa yana parlour yana jiran ki".

Daga haka tajuya tafice batare da tajira ta bakinta ba

Ita kuwa Kausar ba'a son ranta ba tamiƙe tafito, yana zaune a parlour'n shi kaɗai, gaban sa duk an cika masa da kayan motsa baki amma be taɓa komi ba, shi kansa idan kakalle sa baya cikin hayyacin sa duk ya rame yasaka damuwa a ransa sakamakon sauyawan da Kausar tayi masa, kuma hakan sosai ke barazanan tarwatsa rayuwan sa sabida ba ƙaramin so yake mata ba, kullum ji yake yi ƙaunar ta na sake hauhawa acikin ransa memakon raguwa, ya rigada ya saka ta acan cikin zuciyarsa wanda rabuwa da ita zai mishi matuƙar wahala kuma zai taɓa masa rayuwan sa

Tunda tafito yake kallon ta har taƙariso tazauna akan kujeran dake Facing nasa, cikin sanyin murya batare da ta kalle sa ba tace

"Barka da zuwa".

Murmushi yasaki yace "yauwa gimbiyata kina lafiya?"

"Lafiya lau".

"Kwana biyu ina ta kiran wayan ki akashe na kasa haƙura dole nayi tunanin zuwa yau, shin meke faruwa ne Baby?".

Sai alokacin taɗan kalle sa kana taɗauke kai tace "kashe wa nayi".

Shiru kawai yayi yana kallon ta, sai kuma daga baya yace "wai Kausar ko dai kin samu wani ne kikeson min wulaƙanci?"

Sosai taɗago kanta a wannan karon tana kallon sa, shima ɗin ita yake kallo cike da tuhuma, sun jima suna kallon juna batare da ta sami amsar da zata bashi ba kafin taɗauke kai tare da haɗiyan yamu

"Kinyi shiru ina son insan abun da yasaka kikeson juya min baya Kausar, don Allah ki sanar dani idan wani laifi nayi miki wlh nayi alƙawari zan nemi yafiyar ki".

Sai kuma yayi shiru yana saukowa kan kujeran yayi Neeldown agaban ta yana ci gaba da cewa

"Idan ma kina so in duƙa a gaban ki ne to gani na duƙa don Allah ki yafe min, wlh Kausar ina matuƙar ƙaunar ki bazan iya rabuwa dake ba, dan Allah ki taimaki rayuwata ki faɗa min laifin da nayi miki in nemi gafarar ki". Yaƙarike maganar nasa da rawan murya

Kausar kallon sa kawai take yi don batasan sanda yazuƙuna ba, take taji hawaye sun cika mata idanu sabida tausayin sa, tasan da cewa tana ƙaunar Sharif matuƙa amma yanzu shigowar Khalil rayuwan ta tarasa soyayyan sa a zuciyarta, tayi iya ƙoƙarin ta don taga tayi yaƙi da abinda ke damun ta amma ina ta kasa, ta kasa dawo da ƙaunar da take masa aranta, burin ta yanzu kawai tazama mallakin Khalil, amma tarasa ta wani hanya ne hakan zai faru, tasan da cewa yanzu Khalil yayi mata nisa nisan da baza ta iya samun sa ba tunda yana shirin aure

Wani irin kuka yataho mata batasan sanda tasake sa ba, jikin Sharif har yana rawa wajen matsowa kusa da ita yana tambayan abinda ke faruwa da ita, gaba ɗaya ya shiga damuwa ya rasa yanda zai yi, ita kuwa kukan take yi tana toshe bakinta da hannayen ta, sosai take

Please Login or Register in order to submit comment