Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanemi ƙasa tazauna tana gaishe dasu Abba duk kunya ya cika ta, su kuwa kamar babu wani matsala suka amsa mata cike da fara'a


Har ta tashi zata tafi Ummi tace mata takoma tazauna


Babu musu tabi umarnin ta


A lokacin ne su ma su Khalil suka shigo


Kusa da ita Saleema tazauna tana riƙo hannun ta gam, duk yanda ka kalli fuskarta zaka san tana cikin tsantsan farin ciki wanda hakan ba ƙaramin faranta ran iyayen nata suka yi ba, dawowar Halwa ɗin ya yaye mata duk wani ciwo da take fama dashi, tamkar ba ita ce take a mawuyacin hali ba ɗazu, har sai da aka yi mata alluran barci hankalin su yakwanta


Shima Khalil a ƙasa yazauna sabida girmama iyayen nasu, idanun sa ƙyam akan Halwa wacce kanta ke ƙasa ta kasa ɗagowa, sosai zuciyarsa tayi masa sanyi da jin labarin dawowarta wajen Dad..



Maganar Abba shi yadawo dashi hankalin sa har yaɗauke kansa daga kallon ta yana sauke ajiyan zuciya, a kwana biyun nan da babu ita har ya faɗa sosai sabida zullumi da tunanin rasa ta har abada, sai gashi kuma ta dawo wanda be taɓa tunanin hakan ba..



Faɗa sosai Abba yayi mata akan abinda tayi, daga ƙarshe kuma yayi mata nasiha me ratsa zuciya inda shima Dad yaɗaura da nasa, sannan yaƙare da faɗin


"Ina ga kamar yanda Hajiya tabamu shawara hakan yakamata muyi, Ibrahim ya sauwaƙe mata kar a sake samun matsala irin hakan, in yaso sai mu haɗa su ita da Sameer".



A razane Khalil yaɗago kansa yana ware idanun sa kan Dad zuciyarsa na matsanancin bugawa..
[1/5, 3:14 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER twenty Seven*

________🎓Kuka Saleema tasaka tana roƙon Dad akan kar araba auren


Murmushi Dad yayi yana girgiza kai cike da mamakin irin wannan soyayyar nasu


"Don girman Allah kar araba auren nan Dady, wlh idan aka raba nima bazan zauna dashi ba dole sai ya sake Ni".


Babu wanda maganar Saleema be basa dariya ba har Khalil kuwa dake a cikin matsanancin ruɗu, a yanda tayi maganar cikin taɓara da sangarta wanda kuma ita iya gaskiyar ta take faɗa tana ci gaba da kukan ta


"Ya isa to ƴata baza'a raba ba, nima wasa nake yi wlh". Cewar Dad yana zuba murmushi


Cak kuwa taɗauke kukan nata jin abinda Dad ɗin yace



Yayinda Khalil yasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya yana sauke kansa ƙasa zuciyarsa cike da tsananin ƙaunar Saleema, lumshe idanun sa yayi batare da ya sake jiyo zantukan da ake yi ba, domin tuni ya faɗa duniyar tunani, sai da Dad yaɗan zungure sa da ƙafa kafin yadawo hayyacin sa yana ɗago idanun sa masu tsananin haske da kyawu yazuba masa


"Tunanin me kake yi ana ta magana kana jin mutane?"


Ɗan wur-wurga idanu yayi ganin Dad ɗin ne da Abba kaɗai a cikin parlour'n, sauke kansa ƙasa yayi yana sosa ƙeya be ce komi ba


Murmushi Abba yayi yace "To Khalil sai kayi haƙuri da duk abinda zaka gani na zamantakewar ku, dama zaman tare zo mu zauna ne zo mu saɓa ne, bare in an haɗa da sha'anin mata, duk abinda zaka ganin kayi ta haƙuri kamar yanda kasaba, Allah yayi muku albarka gaba ɗaya".


"Amin Abba". Khalil yafaɗa idanun sa a ƙasa


Tashi Dad yayi yana faɗin "to Ni dai bari in soma gaba ko?"


"ai jira Ni sai mu koma tare nima ba zama zanyi ba". Cewar Abba shima yana miƙewa



Lokacin su ma su Saleema suka fito sai sukai waje gaba ɗayan su, inda Ummi tayi musu rakiya har waje



Dad da Abba sun hau motar su daban-daban suka bar gidan, kafin shima Khalil yahau nasa yana jiran ƙarisowar su Saleema dake gefe suna magana da Ummi, Saleeman ce tatsaya tana ma Ummi magiya akan gobe a haɗo mata kan ƴaƴan ta adawo mata dasu, yayinda Halwa ke tsaye tana sauraron su tana murmushi



Abun da yasa ma yanzu batace zata tafi dasu ba saboda ita Husna tana school tunda ta fara zuwa, shi kuma Ahmad yana wajen Larai ta tafi dashi gidan su



Sai da Ummi tayarda zata kawo su gobe kafin tasamu sukuni wajen Saleeman, motan suka ƙarisa suka shiga yaja yay bakin Gate yafice bayan an buɗe masa Gate ɗin



Yana dai-dai ta motan nasa akan titi yasauke idanun sa kan mirror yana kallon Halwa dake baya zaune


Itama dai-dai lokacin ta ɗago kai tana amsa wa Saleema maganar da tayi mata suka haɗa ido


Yanda yakafe ta da ido ne yasa tajanye nata tana lumshe su tare da kau da kai gefe, bata sake gigin ɗago kai ba har suka kai gida.




*****

Kusan ƙarfe 05:30pm. Saleema tafito haraban gidan, Sale takira taba shi aike sannan takoma ciki, dayake lokacin Khalil ya fita sabida wani waje da zai je yau ɗin, dama yaso yawuce ne lokacin da yatashi Office sai kuma Dad yakira sa akan dawowar Halwa, hakan ne yasa be je ba sai yanzu da yamma


Ita kuwa Halwa tunda suka dawo sallah kaɗai tayi ko abinci bata nema ba takwanta barci, har yanzu kuwa barcin take yi batare da ta tashi ba


Saleema tayi mitan tashin ta don taci Indomien da ta girka musu amma ina tamkar wacce mayen ƙarfe ke ja sabida barci ko motsi taƙi yi


Yanzu ma da tashigo ɗakin nata kai tsaye gaban Sip ɗin kayan ta tanufa tabuɗe tasoma ciro mata kayan ta, sai da taciro su tsab sannnan tazuba cikin Trolly taja zuwa ɗakin Khalil, buɗe sip tayi tasoma jera mata har tagama sannan tasake fice wa


Nocking door ɗin da akayi yasaka tazarce kai tsaye bakin ƙofan, tana buɗe wa Sale ne tsaye da Ledoji guda biyu da ta'aike sa saƙo


Amsa tayi tayi masa godiya tare da rufe ƙofan tajuya ciki, ɗakin ta takai ta'ajiye inda baza'a gani ba sannan tafito takoma ɗakin Halwa


Halwan na zaune abakin gado tashin ta kenan tana maida ɗankwali kanta da yakwance time ɗin tana barci


"Kasa kin ta shi?" Cewar Saleema tana murmushi


Fuskarta taya mutsa tamkar dai yanda tasaba sai kuma tasaki murmushi tana gyaɗa mata kai kasancewar hamma ya taho mata, hannu tasaka takare bakin ta tana sake waro idanu kan Saleeman dake gaban mirror tana kwashe kayan kwalliyan ta tana zuba wa cikin wani farin kwando


"Sis me zaki yi dasu ne?" Halwan tatambaye ta da mamaki


Bata ɗago kai ba illa amsa da taba ta


"Zan mayar miki ɗakin ki ne, daga yanzu komi naki zai koma ɗakin Barrister ne tunda can ne ɗakin ki ba nan ba, yanzu ke matar gida ce bare ki zauna a ƙaramin ɗaki".



Shiru Halwa tayi bata sake cewa komi ba amma zuciyarta na jujjuya maganar nata, sai kuma tamiƙe ahankali tashige Toilet, wanka tasoma yi duk da lokaci ya ƙure mata sannan sai taɗauro alwala tafito


Gaban Sip tatsaya tana ɗan murza idanun ta da sabulu yashiga wajen wanka, guntun tsaki taja kafin tabuɗe Sip ɗin tana kallon ciki da mamaki ganin babu komi, sai kuma tajuyo tana kallon Saleema wanda a yanzu har ta gama kwashe kayan gaban mirror ɗin tana tattara takalman Halwa a cikin wani kwandon


"Sister yanzu har kaya na kika kwashe?"


"Eh mana baki ji me nace miki bane? Ai daga yau kema zaki fara amsa matar *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* na haƙiƙa, domin yau Amarya ce ke". Duk maganar nan da Saleema tayi tana ci gaba da aikin ta ne batare da ta ɗago ta kalli inda Halwan ke tsaye ta saki baki tana kallon ta ba


Shiru tayi tatsira mata idanu na tsawon lokaci batare da tayi abinda zai fishshe ta ba, sai da tagaji don kanta kafin tanufi ƙofa tafice tayi ɗakin Khalil, tana shiga tasauke ajiyan zuciya ganin babu shi ciki, da sauri ta'isa bakin sip ɗin tabuɗe tazaro doguwar rigan atamfa da tagani asama tare da ɗankwalin shi, Hijab tasake ciro wa tare da under wear tarufe, memakon tasaka a ɗakin sai takuma koma wa can ɗakin inda tabar Saleema har yanzu tana faman aiki, saka kayan tayi tahau kan sallaya tasoma gabatar da sallan Asar da bata yi ba


Lokacin da ta idar tuni Saleema ta gama kwashe mata komi, shigowar ta ɗakin ne Halwa dake zaune kan dadduma har yanzu tabi ta da idanu


Murmushi Saleema tayi tana dafe ƙugun ta da hannu biyu, taƙariso bakin gado tazube tana faɗin "washhh Allahna wlh nasha aiki, kin jini ne tamkar zan rabe gida biyu".


Babu shiri Halwa tasaka dariya tana sake juyowa yanda zata ganta


"To dama wa yasaki? Aikin da babu lada kawai kin saka kanki".


Hararan ta Saleema tayi tana tashi zaune tace "ai in ke baki gode min ba Mijin ki zai gode min, kuma ai taimakon ku nayi ko?"


Dariyan dai Halwa tayi bata ce komi ba, murza hannun ta tayi tana tunanin yanda za'a yi tafurta abinda ke bakin ta, sai kuma tasake kallon Saleeman da a yanzu take ta faman jan hannayen ta tana naushin iska tamkar zata yi kuka, hakan sai yasake ba ma Halwa dariya, ai kuwa tasaka mata dariya


Yayinda ita kuma Saleema tasake kwaɓe fuska tana cewa "wlh sister ki dena min dariya dagaske nake yi baki ji yanda jikina ke min ciwo ba".


Rage dariyan nata tayi tana kallon ta tace "to Sister ai gaskiya nafaɗa miki dama, meyasa zaki yi wannan aikin baki jira Ni na tashi in taya ki ba? Kin san Baki da lafiya amma don Allah kin ɗaura wa kanki abinda yafi ƙarfin ki".


Saleema tace "to ai ke Amarya ce taya zan bar ki kiyi aiki? Bari ma kiji sai kinyi sati ɗaya curr Sannan zaki soma aiki agidan nan don na rigada na amshe komi". Taƙarishe maganar cike da fara'a wanda kana kallon ta zaka san maganar da tayin ya saka ta nishaɗi ne sosai


Halwa har ta buɗe baki da ninyan yin magana Saleeman takatse ta da cewa


"Yauwa yanzu kinga saura abinci zan je in dafa mana shi kaɗai yarage min".


Dasauri Halwa tamiƙe tana faɗin "ki barshi Ni zan yi".


Hararan ta Saleema tayi tana yin gaba tafice batare da ta tanka mata ba


Itama bin bayan ta tayi har zuwa kichen ɗin, duk magiyan da Halwa tayi ma Saleema akan tabar shi ita zata yi but samm taƙi sauraron ta, dole ta haƙura tahau taya ta tana mita


Abinci me rai da lafiya suka shirya cikin awannin da basu gaza biyu ba, sai da suka gama suka kai dainnig suka jera sannan suka zube saman kujera suna taɓa hira, har sannan Khalil be dawo gidan ba.



Sai gab da magriba yashigo, alwala kawai yaɗaura yasake ficewa zuwa masjid, be dawo ba sai da akayi sallan isha'i kamar yanda yasaba akoda yaushe



Suna zaune a parlour'n yashigo da sallama, atare suka amsa masa tare da mishi sannu


Amsawa yayi idanun sa na kan waya, zama yayi yana ci gaba da latsa wayan sa kamar yanda yashigo yana yi


Saleema ce tatashi takawo masa ruwa ta'ajiye masa, ganin hankalin sa baya kansu sai suka ci gaba da hiran su, yayinda shi kuma yake ta latse-latsen wayan sa, ga duk kan alamu abu me muhimmanci yake yi, daga ƙarshe ma tashi yayi yashige ɗakin sa, be fi mintuna goma ba yafito


Saleema da tayi masa maganar abinci sai be amsa mata ba kasancewar a yanzu ɗin ya saka waya a kunne yana amsa Call, da hannu yayi musu nuni su je su ci, sai suka miƙe suka nufi dainning ɗin suka zauna


Kamar mintuna biyar da zaman nasu shima yaƙariso yana jan kujera gefen Saleema yazauna, yayinda suka saka ta tsakiya kasancewar Halwa na zaune ɗaya side ɗin nata


Khalil ɗin be wani ci abincin sosai ba saboda hankalin sa kacokan yana kan waya, Call yake ta amsa wa, daga ƙarshe sai yamiƙe yana jan kujeran baya yawuce abin sa yakoma ɗaki



Ajiyan zuciya Halwa tayi aranta tana mamakin yau kuma lafiyan sa ƙalau? To waya babu ƙaƙƙautawa sai kace wani ɗan Film


Miƙewa itama Saleema tayi tawuce ɗaki bayan tayi mata bayanin zata je tayi wanka tayi shirin barci sabida yau da wuri zata kwanta, duk gaba ɗaya ta gama tara gajiya a jikin ta, kasancewar bata jin ƙarfin jiki hakan yasa aikin yayi tasiri duk yasaukar mata da gajiya


Gyara zama Halwa tayi kan kujeran dainning ɗin, aranta itama tana son taje tayi wankan tayi shirin kwanciya amma tunawa da cewa kayan ta na ɗakin Khalil sai bata yi gigin zuwa ba, Allah yaso ta da wayan ta a hannu sai tayi zaman ta abunta tasaka Game tana yi.


Shi kuwa Khalil tunda yashige zama yayi bakin gado, ya daɗe yana wayan kafin yasauke idanun sa kan agogo, lokacin ƙarfe 10:30pm. Sai yamiƙe yashige toilet yayi wanka yafito, Direct sip ɗin kayan sa yanufa, yana buɗe wa idanun sa suka sauka kan kayan Halwa, mamaki ne yakamasa


Shiru yayi yana tsirawa kayan idanu, ya jima ahaka kafin yarufe yana buɗe ɗaya side ɗin yaciro jallabiya fara da gajeren wando, sai da yafeshe da turaren sa me ƙamshi kafin yasaka yafito zuwa ɗakin Saleema, ko kaɗan be lura da Halwa dake zaune kan dainning ba, tunda yakalli cikin parlour'n yatabbatar babu su sai yashige ɗakin Saleeman a tunanin sa ko suna ciki.


Halwa dake zaune tana kallon fitowar sa da shigewar sa ɗakin Saleeman, hakan yasa tasauke ɓoyayyen ajiyan zuciya don tasan maybe bazai fito ba ya shiga kenan,


Bata san meyasa ba tunda Saleema tayi mata maganar ɗazu sai jikin ta yayi sanyi, komi tana yin sa ne tare da fargaban me zai biyo baya tunda har yanzu bata san makomar ta wajen Khalil ba, "shin zai amshe ta a matsayin matar nasa ne ko kuwa zasu ci gaba da zaman da suka yi ne na baya?" Wannan amsar ne bata sani ba don haka tatashi tanufi ɗakin nashi.


*****

Ƙariso wa Saleema tayi tazauna kusa dashi tana faɗin "Mijina yau fa ƴar uwata ke da kai bani ba?"


Murmushi Khalil yayi, duk da abinda ke ransa kenan amma be san yanda zai ce mata ba Cuz baya son tayi tunanin ko ya ƙosa ne, that's why yabari ko zuwa gobe sai yazauna yaraba musu kwana, sai ma gashi kamar ta fahimce sa take faɗan hakan


Girgiza hannun sa tayi ganin yayi shiru ya tsira mata idanu


"Ko baka ji me nace bane?" Tayi maganar tana faɗaɗa fara'an ta


Basarwa yayi yana taɓe baki yace "naji ki mana Matata, But Ni ba yau nayi ninyan zuwa ba, sai ki bari zuwa jibi inyaso sai in koma ɗakin ta tunda kece babba ai". Yaƙarishe maganar yana kashe mata idanu tare da janyo ta jikin sa


Bata san meyasa ba sai taji farin ciki aranta da maganar nasa, lumshe idanu kawai tayi tana ƙara lafewa a jikin sa, sai dai kuma bata jin zata iya barin hakan domin yau ta tanadar musu ranan nasa ne da Halwa, a ganin ta yau ɗin ɗakin ta yakamata yaje ba nata ba, don haka taɗago tana gyara zaman ta da kyau tace


"A'a Ni dai na yafe wlh, Ni fa na rigada na bar muku ka soma cin angoncin ka kamar yadda ko wani Ango yake yi na tsawon sati ɗaya, haka Shari'a ta yarje mana sannan sai mu raba kwana, bari ma kagani don Ni nayi muku tanadi".


Taƙarishe maganar tana miƙe wa tanufi lungun gadon ta ta ɗaya side ɗin taɗauko ledojin da ta'aiki Sale yasiyo mata kaji da kayan maƙulashe


Khalil dake kallon ta yana ganin ikon Allah har ta'iso ta'ajiye masa a gaban sa tana sake zama sannan takalle sa da murmushi tace "gashi nan na tarban Amarya ne".


Kallon ledan yayi, sai kuma yasaka hannu yaɗago yana duba wa, ɗago ido yayi yana kallon ta


Sai taware masa idanu still tana murmusawa


Be san me zai ce mata ba don haka sai yarungumo ta jikin sa yaɗago ta zuwa cinyan sa tare da haɗe bakin su waje ɗaya


Tabbas yau ya sake tabbatar wa Saleema na daban ce, da ita da Halwa bai san wacce tafi kyakykyawar zuciya ba, duk da Saleema tafi Halwa komi don bazai ce kyawu ne yaruɗe sa ba amma kuma zuciyarsa Halwa take tsananin ƙauna, be san meyasaka hakan ba, a ranan farko da yaganta be san komi nata ba but a kallon da sukai ma juna kaɗai zuciyar sa taharbu da tsananin ƙaunar ta, baya ga haka baya tunanin akwai abinda yaja ra'ayin sa ajikin ta da har yaji yana son ta tunda be san komi nata ba a lokacin, abun dai da zai iya cewa ƙaunar ta kawai daga Allah ne, shine yadasa masa ƙaunar ta a zuciya wanda yake jin sa yana gudana da jinin jikin sa tare da bugun numfashin sa, kullum ƙara jinta aransa yake yi memakon raguwa..



Tunda yahaɗe bakin su Saleema lumshe idanun ta tayi tana sauraron saƙon da yake aika mata dashi, ko kaɗan bata yi tunanin taya sa ba sabida bata son hakan yaɗau lokaci


Ganin dai yana wuce gona da iri sai tajanye jikin ta tana ƙara marairaice fuska ganin yana shirin sake haɗe bakin su, roƙon sa tasoma yi tana faɗa masa lokaci yaja be kamata yazauna anan ba


Daƙyar dai tasamu yabar mata ɗakin don sai da yaƙara ɓata lokaci wajen ta


Yana fita tagyara rigan ta tana faɗawa kan gadon tare da lumshe idanun ta hawaye masu ɗumi suka soma sulmiyo mata, wani irin tsananin ƙaunar mijin ta da kishin sa ne yake nuƙurƙusan ta, amma kuma tasan cewa yanzu ya tashi a nata kaɗai dole sai tayi sharing ɗin sa da wata, ko kaɗan bata jin haushin Halwa a yanzu, idan ma taƙi Halwan da mijinta ai dole sai ya auro wata tunda bazai zauna babu haihuwa ba


Danne zuciyarta kawai tayi taci gaba da rarrashin kanta, sai dai ta daɗe ahaka barci be ɗauke ta ba, sai kawai tatashi taɗauro alwala tasoma raya daren tare da roƙon Allah yaba su zaman lafiya kuma yakaɗe musu sheɗan a zamantakewar su, tare da roƙon Allah ya ƙara mata juriya da haƙuri, domin tabbas ba kaɗan ba zuciyarta tsananin zugi take mata kasancewar ta me fama da ciwo a zuciyan, shiyasa ta kasa jure zafin da take mata har tasaka kuka cikin sallan nata don dai kawai tasamu salama a zuciyar
[1/5, 3:37 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Twenty Eight*

________🎓Yana tura ƙofan Halwa tabuɗe idanun ta, dama tun ɗazu bata yi barci ba tunani ya cika mata zuciya


Jin ya nufo wajen gadon sai tasake Rufe idanun ta tana sauraron bugun zuciyar ta dake sake hauhawa



Ajiyan zuciya yasauke lokacin da ya'iso bakin gadon yasami waje yazauna, fuskarta yake kallo kasancewar Facing ɗin sa take yi kuma da hasken lantarki da yakunna shigowar sa, yasan ba barci take yi ba don haka yace


"Tashi zaune muyi magana".


Runtse idanuwan ta tasake yi, sai kuma ahankali taware su kan bayan sa da yajuya mata, tashi tayi tazauna tana sake jawo bargon jikin ta duk da ba wai ta saka kayan barcin me nuna tsiraici bane, sai dai kasancewar yanda yalafe a jikin ta ana ganin komi, gashi kuma rigan iyakan ƙasan gwiwan ta yatsaya


Shima gyara zaman sa yayi sosai yana fuskantan ta


Kanta a ƙasa tana jiran abinda zai biyo baya, sai dai shiru yaƙi yin magana, ita kuma ta kasa ɗago kai bare ta kalle sa sabida tasan idanun sa na kanta


Zuba mata idanu kawai yayi yana kallon ta, jujjuya maganar da yake son furta mata yake yi a zuciyar sa, sai da ya ɗan ja lokaci kafin yafesar da numfashi yabuɗe baki yasoma magana


"Halwa". Yakira sunan ta a hankali


"Na'am". Ta'amsa masa batare da ta ɗago kanta ba


Hannayen sa yahaɗe waje ɗaya kafin yace "Da farko dai ina so in baki haƙuri agame da zamantakewar da mukayi abaya, sabida yanda na nuna miki halin ko in kula a matsayin ki na Matata, duk da ba wai nayi hakan a son Raina bane, har a cikin zuciyata ina jin zafin abubuwan da nayi miki, don Allah idan na ɓata miki ki yafe min yanzu ina so mu gyara zaman auren mu ne shiyasa nake so mu soma fahimtar juna a yanzu ɗin".



Lumshe idanuwan ta tayi hawayen da suka soma sintiri a fuskarta tun soma maganar sa suka ci gaba da tsiyaya, wani irin sanyi ne yake ratsa ta har cikin zuciyarta, har a yanzu ɗin ma bata ɗago kanta ba tace dashi


"Yaya Khalil wlh baka yi min komi ba, idan ma har kayi min to na yafe maka domin ban taɓa kallon ka matsayin me cuta min ba".


Tattausan hannayen ta yariƙo cikin nasa wanda sai da yasaka suka ji tsigan jikin su ya tashi, domin hakan ba wai ya taɓa faruwa bane dasu, fatar jikin junan su be taɓa haɗuwa waje ɗaya ba


Sauke ajiyan zuciya yayi yana ƙara damƙe hannayen nata, idanun sa kafe akanta duk da ba wai kallon sa take yi ba, sannan yasoma magana


"Duk da bansan cewa kina sona ko baki sona ba but ina me neman alfarma ki bani dama a cikin zuciyar ki, Ni kuma zan koya miki ƙaunata sannan nayi miki alƙwari zan faranta miki da iyawa ta, sannan duk abinda ke faruwa naji komi wajen Dad".


Shiru yayi yana jan numfashi sabida jin wani kishi ya turniƙe shi tunawa da wani banza shi yasoma ɓata wa Halwan sa rayuwa, ɗan daidaita muryan sa yayi yace


"Ina so in ƙwato miki haƙƙin ki wajen tsinannen mutumin da yaruguza miki rayuwa".



Yanda yayi maganar cikin wani irin murya da dole ne kagane tsananin kishin sa, duk da kuwa ya daure sosai wajen dai-dai ta muryan nasa, hakan yasa taɗago kai akaro na farko tazuba masa idanu, bata yi tunanin wai ko wannan maganar yake son faɗa ba koda yace mata yaji komi wajen Dad, cikin sanyin murya tace


"A'a Yaya Khalil abinda yawuce ya rigada ya wuce, duk da ada Ina da burin ɗaukan fansa amma yanzu tuni na cire hakan a raina, Husna yanzu ta zama mallakin Saleema na bata ita har abada.."


Katse ta yayi da faɗin "duk da haka dole ne na ƙwato miki haƙƙin ki, Ni lauya ne ke kuma Matata ce, taya kike tunanin zan iya barin wanda yataɓa yin ma Matata Fyaɗe batare da na ɗau mataki ba? Ba wai mayar masa da Husna za'a yi ba but dole ne Kotu ta yanke masa hukuncin abinda yayi, na rigada na gama bincike a kansa zuwa kwana biyu da yardan Allah zan miƙa Case ɗin kotu".


Wani irin farin ciki me haɗe da kuka ne suka taho mata, ko kaɗan ta kasa ɗauke idanun ta akansa, sai dai ta matse bakin ta gamm ta hana kukan nata fitowa illa hawayen dake ƙara sintiri saman fuskarta tare da murmushin farin ciki dake gudana



Kazalika shima kallon nata yake yi, yayinda yasauya riƙon da yayi wa hannayen ta yana murza mata su a hankali yana jin ƙaunarta na ƙara shiga zuciyar sa tare da ƙara girma sosai, yana son yafaɗa mata sirrin dake ransa sai dai kuma baya son yasanar da ita da baki illa a aikace, don haka yabata umarnin tamiƙe tasauko su gabatar da Sallah kamar yanda ko wanne ma'aurata suke yi


Hakan kuwa yafaru, ita tasoma yin alwalan tafito tasanya Hijab tazauna

Please Login or Register in order to submit comment