Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka wuce wajen aikin su.


Bilkisu asalin su Nufawa ne ƴan garin Minna, tana zaune wajen ƙanin Mahaifinta ne anan Katsina, babban Family ne dasu kuma sun saba yin auren zumunci ne, ita kanta Bilkisu akwai wanda aka haɗa ta dashi tun tana ƙarama, sai dai shi ɗin baya ƙasar ne yana zaune can Sudan yana aiki, daga zuwa karatu yazauna har yanzu yaƙi yadawo, Allah ne yasaka mata ƙaunar Khalil har takasa haƙuri dashi duk da tasan zai yi wuya ta aure shi, amma soyayya ya rufe mata idanu kwata-kwata ta manta da cewa akwai wanda iyayen ta zasu bata, kuma nan bada jimawa ba ake tunanin sanya ranan auren nasu.
[10/21/2020, 4:12 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```

_wannan shafin naki ne ZEENAT, ina godiya da yanda kike ƙaunar Littafina, Allah yabar ƙauna_❤️


.

*CHAPTER 36*


Dad na zaune a parlour'n sa Khalil yashigo yazauna kan kujeran da ke Facing Dad ɗin, Dad ce masa yayi

"Ina fata kaji abinda ke faruwa ko?"

Gyaɗa kansa Khalil yayi

Dad yace "yanzu kana da wata ko kuwa?"

"Dad ni Banda wata, ni abar ma maganar sai zuwa nan gaba don ban shirya aure yanzu ba dama".

Kallon sa Dad ɗin yake yi be ce komi ba, sai kuma can yabuɗi baki yace "Ibrahim ba maganar wasa muke yi da kai ba, aure nake so kayi kuma a wannan lokacin na gaji da ganin ka haka, idan har maganar neman mata kake yi to Ni na samo maka, akwai yarinyan Abokina da zaka je kanema domin yanzu mun riga da mun gama maganar da Alh. Mustapha".

Ɓata fuska Khalil yayi yace "Dad meyasaka kake son kabani wacce bana so?"

Murmushi Dad ɗin yayi yace "har yanzu kai yaro ne Ibrahim, ba wai zan maka dole bane amma tunda naga matar ce kakasa nemowa shine Ni nayi maka gwanin ta nanemo maka, kaje wajen ta idan har kun dai-daita kanku shikenan".

Khalil yace "Dad don Allah meyasaka baza'a janye maganar ba? infact ma Ni yanzu bani da lokacin aure sabida zan tafi England yin wani course, kuma One year zanyi acan".

Dad yace "ok kana nufin Adena maganar auren ka har sai kaje kadawo?"

Gyaɗa kansa yayi yana kallon Dad ɗin tare da turo baki, daƙuwa Dad ɗin yayi masa yace

"Kaga naka Ibrahim babu inda zakaje sai kayi aure koda kuwa gobe ne zaka tafi".

Cikin shagwaɓa Khalil ɗin yace " Haba Dad please Mana kabari sai nadawo inyaso sai in auri ita yarinyan da kakeso".

Shiru Dad ɗin yayi yana kallon sa kana yace "ok shikenan, dama itama yarinyan tana karatu kuma dama Mahaifin ta yace min zuwa nan da shekara ɗaya da rabi zata kammala, kaga idan kadawo sai asaka ranan auren hakan yayi?"

Jinjina kansa yayi yace "eh Dad".

"Ok tashi kaje Allah yataimaka, yaushe ne zaka tafi?"

Khalil da yamiƙe tsaye yabashi amsa da cewa "nan da Three weeks".

Dad yace "kana da lokaci ai Yakamata kaje wajen yarinyan kaganta, kuma bana son inji cewa bakaje ba".

Gyaɗa masa kai yayi kafin yayi masa sallama yafice. Koda yafito babu kowa a palrour, kawai ficewa yayi batare da yashiga wajen Mom ba, motan sa yashiga yabar gidan, wayan sa yaɗauka yakira Brr. Tahir ringing biyu yaɗauka yace

"Ango ango".

Ɓata fuska Khalil yayi yace "wanene Angon?"

Dariya Brr. Tahir ɗin yayi yace "ai naji komi wajen Dr. Sameer, yace "min anje nema maka auren Billy".

Tsaki Khalil yaja cike da haushi da zaka gane cikin muryan sa yace "kabari dai kawai Tahir, yarinyan nan ashe yaudarana tayi".

Brr. Tahir yace "bangane ba kamar ya yaudaran ka tayi?"

Daga nan Khalil yasanar masa da abinda yafaru da su Dad da sukaje kana yaƙara da cewa

"Dama abinda nake gudu kenan Tahir tun farko shiyasaka bana son yin soyayya bcoz yawancin matan mayaudara ne, and duk da bana wani son ta but naji haushi sosai ɓata min lokacina da tayi, gashi yanzu taja min Dad ya samo min wata".

"To fa haka akayi? Gaskiya banji daɗi ba kuma Bilkisu bata kyauta ba, amma kayi mata uzuri mana don Ni banga laifin ta anan ba matsalan daga iyayen ta ne, meyasaka baza su bata wanda take so ba?"

Gajeren tsaki Khalil yayi yace "har kana da bakin kare ta anan? Ni Abokin wasan ta ne?"

Brr. Tahir yace "kayi haƙuri kabi abin a sannu, kuma don Allah karka ce zakayi mata wata magana da be dace ba".

Shiru Khalil ɗin yayi don shi yariga da ya rufe shafin ta

"Yanzu to aina yarinyan da Dad ɗin yasamo maka take?" Brr. Tahir ɗin yatambaye sa

Taɓe baki Khalil yayi yace "wai ƴar Abokin sa ne, sai kace suna neman kai dani".

Brr. Tahir dariya yayi yace "kai masha Allah Allah yasanya alkhairi, gaskiya naji daɗin wannan haɗin domin kuwa idan Dad yabiye taka baza kayi auren yanzu ba".

Yamutsa fuskar sa yayi yace "kaga ni zan aje waya ina tuƙi ne sai anjima".

Still dariya Brr. Tahir yayi yace "ok zuwa a anjiman zan kira ka bye".

Daga nan ajiye wayan yayi yaci gaba da tuƙin sa.





**** ***** ****** *******

Ummi ce zaune kan Three sitter Saleema tayi matashi akan cinyan ta, gefe ɗaya kuma Abba ne zaune kan Two sitter suna hira

Abba ne yace "ƴar Baba tashi akwai maganar da zamuyi dake me muhimmanci".

Amsa mishi Saleema tayi tana tashi zaune

"Shin kin tuna Abokina Alh. Abdurra'uf?".

Kallon Abban tayi kana tace "eh Abba nasan shi, ko ba wanda ada kake yawan kai ni gidan ba?"

Murmushi Abba yayi yace "yauwa shi ƴar Baba, kinsan yaran sa ko?"

Gyaɗa kai tayi tace "nasan su Abba".

"To ki saurare ni da kyau ƴar Baba, kinsan Burin mu shine mu aurar dake ga mutumin da zai kula dake kamar yanda muke kula dake, muna Son farin cikin ki Daughter wannan dalilin ne yasaka muka yanke shawara Ni da Mahaifiyar ki mu samo miki Miji wanda zai baki duk wani kulawa, ɗan gidan mutunci wanda zai iya riƙe mana ke bisa amana, akwai ɗan sa Ibrahim Khalil shine mahaifin sa yake nema masa auren ki, Ni kuma ganin haka yasa na'amince but duk da haka sai na tambayi ra'ayin ki, idan har kin amince zai zo wajen ki don ku dai-daita, kiyi tunani da kyau My Daughter don baza mu taɓa baki abinda baki so ba, zaɓin ki shine namu".

Saleema kallon Abban nata kawai take yi har yadire maganar kafin cikin zaƙuwa tace

"Abba wai kana Nufin Yaya Barrister?"

"Eh Shi ƴar Baba".

Rufe bakin ta tayi tana waro idanu cike da wani irin farin ciki tace "Kaiiiii.."

Ummi tace "lafiya Daughter me yafaru?"

Dariya tasaki tana yarfe hannayen ta sai kuma tasake rufe bakin ta tana kallon iyayen cike da tsananin farin ciki, su kuwa kallon ta kawai suke yi suna tunanin "meyasaka ta farin ciki haka lokaci ɗaya?" Muryan ta suka tsinkaya tana cewa

"Anya Abba Yaya Barrister shine Wanda mahaifin sa ke nema masa aure na? Ina mamaki Abba taya?"

Murmushi Abban yayi yace "Ƴar Baba kenan ki dena mamaki ai komi ba yanda Allah baya nuna ikon sa, yanzu menene ra'ayin ki akai? shin kin amince ne?"

Saurin gyaɗa kanta tayi tana me tsananin farin ciki, riƙo hannun ta Ummi tayi tana kallon ta da murmushi a face ɗin ta tace

"Wai farin cikin na menene da alamun dai kina son sa kenan?"

Saleema har ta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi saurin rufewa don baza ta iya yin musu bayanin abinda ke ranta ba, illa tashi da tayi da gudu tanufi hanyan ɗakin su tana ci gaba da dariya, bin bayan ta sukayi da idanu cike da tsananin mamakin ta kana Abba yace

"Ikon Allah wai lafiyan ƴar Baba ƙalau?"

Ummi cike da farin ciki tace "ai inaga Abban Saleema da alamun ƴar mu ta daɗe tana ƙaunar sa ne, domin Ni sheda ne abaya sanda kake yawan ɗaukan ta kuje gidan kullum idan tadawo bata da magana sai na Yaya Barrister, Kai har dai na gaji daji don idan tazauna labarin kenan, to tun sanda tayi ciwon nan sosai aka kwantar da ita asibiti kadena kaita to ban sake jin tayi maganar ba, amma Ni ina da tabbaci son sa take yi kuma ina ganin tana cikin mamakin abun ne".

"Kai amma idan ko hakane zamuyi farin ciki sosai ai dama fatar mu kenan, burin mu shine tasami miji na gari kuma ina da yaƙini ta samu, domin Khalil be da wani matsala yaro ne me tsananin kirki da biyayya na tabbata bazai taɓa wulaƙanta mana ƴa ba, wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin haɗa wannan auren".

Ummi jinjina kanta tayi cike da gamsuwar bayanin mijin ta kana tace "to Allah yatabbatar da alkhairi Allah yasa ayi damu".

"Ameen ameen". Cewar Abba still yana me nuna farin cikin sa

"Amma ina tunanin ba yanzu za'a yi auren ba sabida yaron zai yi tafiya, kin ga har sai ta gama school ma anan, sai kiyi mata bayani yanda zata fahimta".

"To babu matsala ai hakan yayi ma". Cewar Ummi kenan

Daga nan hira sukaci gaba dayi suna tattaunawa akan maganar.
[10/30/2020, 8:51 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```


.

*CHAPTER 37*


Tana shiga ɗakin tafaɗa kan Halwa dake barci, hakan yasaka Halwan tafarka tana kallon ta da idanuwanta da sukayi ja, cike da tsananin farin ciki Saleema tace

"Wayyo Allana yau ina farin ciki sosai kitashi ki tayani murna".

Ahankali Halwan tatashi zaune tana ci gaba da kallon ta tace "me yafaru ne Sister?"

Murmushin da yabayyana haƙoran ta tayi tace "kinsan me Abba yazo da maganar aure na Ni da ɗan Abokin sa".

Waro idanu Halwa tayi tana kallon ta, sai kuma tayi dariya tace "shine yasaka ki farin ciki?"

Gyaɗa kanta tayi tana sake washe bakin ta tace "eh mana abin ne ya matuƙar bani mamaki, ban taɓa tunanin wannan ranan ba, ban taɓa tunanin Ni Saleema ina da matsayin da zai sa ace yau zan zama matar Barrister ba, Mutumin da ko magana ban taɓa samu ya haɗani dashi ba, ada nayi burin ace Barrister ya zama nawa but ko kaɗan babu hanyan da naga yiwuwar hakan, amma yanzu kiji abin mamaki sai gashi lokaci ɗaya Allah ke ikon sa wai ni ce yau ake son haɗa ni dashi, abun sai kace amafarki wlh".

Yanda taƙarike maganar nata ne yaba Halwa dariya, sai da tadara kafin tace "to menene aciki? Ni a ganina banga Namijin da yafi ƙarfin ki ba, kar ki manta kema fa kina da kyau da haɗuwar da ko wani namiji zai yi fatar samun ki, ki dena zuzuta shi da yawa don nasan bazai fi ki da komi ba".

Saleema tace "uhmmm baza ki gane bane Sister, ko wace mace idan har tagan shi zata so yazama shine Mijin ta, ba wai don haɗuwan sa ko kyawun sa ba amma yana da nagartan da idan har kin ganshi kema wlh sai kin so shi, domin bakiga yanda mata suke rushing akan shi bane".

Taɓe baki Halwa tayi tana kallon ta tace "da alamu dai kina son sa da yawa, amma to kina ganin shima yana ciki?"

Zaro idanu Saleema tayi tace "hmm mutumin da ban taɓa magana dashi ba taya kike tunanin yana sona? I Think ko sanina be yi ba".

Shiru kawai Halwa tayi tare da tunanin Nura aran ta

"Burina a rayuwa shine in Sami Miji tamkar Barrister sai gashi shi ɗin na samu, nasan ko baya so na watarana zai ƙaunace ni domin kuwa zan yi duk abinda yake so". Saleema taƙarike maganar tana rufe fuskarta cike da farin ciki

Buɗe fuskar tayi tana kallon Halwa da tafaɗa tunani, sai tataɓo ta tana cewa "Sister lafiya tunanin me kike yi?"

Ajiyan zuciya Halwa tasauke kana tace "Babu".

Murmushi tayi tace "to faɗa min kema, menene burin ki a rayuwa?"

Shiru Halwa tayi tana kallon ta batare da tace komi ba

"Sister kisanar min mana kinji?"

Duƙar da kanta tayi tana murza ƴan yatsun hannayen ta masu tsawo da burgewa kana taɗago kanta tana kallon Saleema da murmushi a fuskarta tace "ada bani da wani buri a rayuwa sama da inyi aure in ganni gidan Yaya Nura amma.."

Shiru tayi tana kawar da kanta kana taci gaba da cewa "amma a yanzu Burina inyi karatu me zurfi in zama lauya ko dan naɗau fansar abinda Haris yayi min".

Ɗaura hannun ta Saleema tayi akan na Halwan tana cewa "meyasaka kike Son ɗaukan fansa? Meyasaka baza ki barshi da Allah ki manta dashi cikin rayuwan ki ba? Idan har kikace zaki ɗau fansa hakan na nufin kenan zaki riƙa tuna sa har zuwa wani lokaci?"

Halwa tace " Ni kaina nayi tunanin barin shi da Allah kamar yanda tun farko nabar shi, amma yanzu wani tunani yazo min arai saboda shigan ciki a gare ni, idan har nahaifi abinda ke cikina dole ne watarana yatambaye Ni "ina Mahaifin sa?" kina tunanin wani amsa zan bashi?"

Taƙarike maganar hawaye na cikowa cikin idanun ta, kana taci gaba da cewa

"Wannan dalilin ne yasaka nayi tunanin na zama lauya don nan gaba na kaisu ƙara kotu domin hakan ne kaɗai zai saka gidan su Haris su amshi abinda nahaifa, baza su taɓa amsan abinda zan haifa ta daɗin rai ba dole sai ta wannan hanyan".

Numfashi taja me ƙarfi still taci gaba da faɗin

"Burina na biyu shine in San meyasaka Yaya Nura yajuya min baya? Ina son in San dalili ina son insan meyasa?.."

Sai kuma tasaki kuka me ƙarfi, cikin rawan murya tace "na.. na kasa yarda cewa Ya..ya Nura zai juya min ba..ya, zuciyata takasa amince wa da hakan.."

Kasa ci gaba tayi da magana dole yasaka tayi shiru, rungume ta Saleema tayi cike da tsananin tausayin ta tace

"Kiyi shiru don Allah Sister ki dena kuka kinji? Ni nan zan taimake ki wajen cika burin ki, in Allah ya yarda zaki cika burin ki, zanyi wa Abbana magana zai saka ki aduk makarantar da kike so a faɗin duniya domin cikar burin ki, please ki dena kuka".

Shiru Halwa tayi tana sauke ajiyan zuciya, ɗago kanta Saleema tayi tasaka hannu tasoma share mata hawaye.





*****

*TWO WEEKS*


Khalil ne zaune ƙasar Roll ɗin parlour'n sa, daga shi sai gajeren wando fari da baƙin t.shirt, gaban sa takardu ne masu yawan gaske yake dubawa, gefe kuma Kausar ne kan kujeran da yajingina bayan sa tana ɓare maggi dake cikin Vowel

A ɗan wannan lokacin sosai suka shaƙu da juna kullum Kausar tana gidan, ita take mishi girki da gyaran gidan, su zauna suyi ta hira kamar wanda suka daɗe da sanin juna, yanzun ma hiran suke yi aciki yasako mata maganar auren sa da zai yi

Ɗan kallon ta yayi yana smile yace "kin kusa hutawa dai duk ranan da akace nayi aure, babu ke babu ɗawainiya dani".

Tsayar da abinda take yi tayi tana ɗago kanta takalle shi, kana cikin rashin fahimta tace "ban gane ba?"

Ɗan taɓe bakin sa yayi yana kawar da kai yace "nan ba da jimawa ba zanyi aure.."

Ɗif Kausar tayi gaba ɗaya tadena jin abinda yake cewa, maggin kawai take ɓarewa amma batasan ma takamaiman a halin da take ciki ba, sai da yagama maganar sa kana yajuyo yana kallon ta, ganin kamar tayi nisa a tunani sai yakau da kansa yaci gaba da abinda yake yi

Ita kuwa sosai tashiga ruɗu da jin abinda yafaɗa, ba don komi ba sai don ƙaunar da tatsinci kanta dumu-dumu aciki tana yi masa

Nocking ɗin da akeyi ne yadawo da ita hankalin ta

Khalil yace "Yes Come in".

Brr. Tahir ne yashigo ciki da sallama, sauke idanun sa yayi akan su yana bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo cike da tsananin mamaki da al'ajabi, Kausar itama shi take kallo sai dai kawai kallon nasa take yi but tunanin ta yana wani wajen daban, maganar Khalil ne kawai ke mata yawo a tsakar kai

"Lafiya katsaya nan? Kashigo mana". Cewar Khalil kenan yana kallon sa

Ahankali Brr. Tahir yasoma takowa yana shigowa, sai da ya'iso wajen yazauna saman sofa kana Kausar tamiƙe tsaye da hanzari tana ajiye Vowel ɗin hannun ta asaman Centre table, kallon Khalil tayi fuskarta babu walwala tace

"Zan je gida".

Shima ɗin kallon ta yake yi cike da mamaki, sai kuma bai iya cewa komi ba in banda gyaɗa mata kai da yayi, ita kuma tajuya tayi hanyan ƙofa dasauri yayinda Brr. Tahir yaraka ta da idanu, sai da tafice kana yamayar da kallon sa ga Khalil yace

"Kai Man ina kasamo wannan Babe ɗin? Shin anya ba idanuna bane ke min gizau?"

"Kamar ya?" Khalil ɗin yatambaye sa yana ɗago kansa yakalle sa






_plz Share🙏🏼_
[11/1/2020, 9:10 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
```NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.```


.

*CHAPTER 38*


Brr. Tahir yace "abin ne da mamaki mace nake gani agidan ka? Taya hakan zai faru? Meye alaƙan ka da ita?"

Gajeran tsaki Khalil yasaki yana kawar da kansa, domin shi a tunanin sa ko wani abun yagani don har ya tsorata shi

"Kayi min bayani mana meye alaƙan ka da ita? Kar dai ace.."

Wani kallo da Khalil yasakar masa ne yakasa ƙarisa abinda yayi ninya, sai yatsaya kawai yana kallon sa batare da ya ɗauke idanun sa akan sa ba, Khalil kuma juyar da kai yayi yaci gaba da abinda yake yi kana yace

"Ba abinda kake tunani bane, maƙociya ta ce".

"Maƙociyar ka?"

Brr. Tahir yamaimaita maganar kamar be fahimta ba, sai kuma yasaki murmushin gefen baki yana cewa

"Kayi min bayani yanda zan gane har yanzu ban fahimce ka ba?"

Tsaki Khalil yaja yana hararan sa, nan dai yabashi labari yanda suka haɗu da alaƙan sa da ita

dariya Brr. Tahir yakece dashi yana cewa "Cab ɗi.. wai dama ka iya sakewa da mata har haka?"

Kallon banza Khalil yayi masa yace "me kaɗauke ni to?"

Ɗage hannu Brr. Tahir yayi yace "No babu".

"Kafaɗa karta kashe ka, ai nasan duk abinda kake tunani".

Shi dai Brr. Tahir dariya kawai yake yi, sai da yagama dariyan sa son ransa Khalil be sake kula sa ba, sannan daga baya yace

"Kasan me? na samo maka shawara, me zai hana kawai kakai ma Dad ita a matsayin wacce kake so tunda naga taku tazo ɗaya".

Idanun Khalil kamar zai faɗo ƙasa sabida kallon da yake yi masa, Brr. Tahir da yabuɗe baki zai ci gaba da magana Khalil yayi saurin katse sa da cewa

"Banso don Allah kadena wannan maganar, ce maka akayi ina son ta? ko ce maka akayi ita tana so na? Babu wani abu da zai haɗa mace da namiji ne sai soyayya? Ni kawai burge Ni take yi ba wani abu ba".

"To ai hakan shi ke kawo ƙauna, don me zata burge ka idan har babu ƙauna aciki?"

Ɗaure fuska Khalil yayi yakawar da kai don bazai iya biye masa ba, kuma yasan halin Brr. Tahir idan yakama abu to baya jin bari

"Uhm Ni kawai shawara nake baka, idan kuma kafison wacce Dad zai baka ai shikenan , ta yiwu ma kaje kaganta batayi maka ba".

Shiru dai Khalil yayi be ce komi ba, amma tunanin maganar Brr. Tahir ɗin yake yi da yayi a ƙarshe

Brr. Tahir yakatse masa tunanin sa da cewa "katashi kashirya mana mutafi, in kuma ka fasa ne sai nayi tafiyana don ina da abin yi".

Miƙe wa Khalil yayi still be ce masa komi ba yanufi ɗakin sa, sai da yayi wanka yashirya cikin wani farin Gezna da yayi masa kyau ainun, yasaka baƙar hula me ƙube tare da baƙin Sandal shoes, babu abinda ke tashi ajikin sa sai sassanyan ƙamshi, car key yaɗauka tare da wayoyin sa yafito parlour, Brr. Tahir kallon sa kawai yake yi ganin yanda yayi masa mugun kyau

"Kai Abokina kaga yanda kayi kyau? Ni namiji kenan ina ga mace ta ganka? wannan wanka gaskiya Amarya dole tabiya mu".

Tsaki Khalil kawai yaja yanufi ƙofa batare da ya tanka sa ba, shi kuwa Brr. Tahir biyo sa yayi yana ta tsokanar sa yana faman dariya

A cikin motan Khalil ɗin suka fita, mintuna ashirin yakaisu gidan Alh. Mustapha, suna yin hon aka buɗe musu Gate don dama gateman ɗin yasan da zuwan su, lokacin da sukayi parcking duk kan su suka fito alokaci ɗaya, Brr. Tahir sai gyara wuyan rigan sa yake yi yana faman doka murmushi sai kace shine aka rako, Khalil kuwa in banda harara da yake aika masa babu abinda yake yi, ahaka akayi musu iso har zuwa Parlour'n Alh. Mustapha inda anan ne aka sauke su, me aiki aka saka takawo musu abin motsa baki, babu abinda suka taɓa sai hira da Brr. Tahir yake jan Khalil dashi, shi kuwa sai latsa wayan sa yake yi ko kula sa be yi ba

A ciki kuwa Saleema ce taci uban kwalliya cikin wani tsadadden less me ruwan toka, ɗinkin riga da sket ne da yayi mata kyau matuƙa, tayi ma fuskarta Light makeup Wanda yaƙara fito da tsantsan kyau ɗin ta, dama Saleema ba baya ba wajen kyawu, Halwa na zaune tana kallon ta har tagama shiryawa tayafa gyale fari ƙal me kwalliyan stone, haka ma flat shoes ɗin da tasaka a ƙafafun ta fari ne, murmushi kawai Halwa take zubawa kafin tace

"Gaskiya kinyi kyau My sister, anya baza ki zautar da Angon nan naki ba yakasa manta ki?"

Washe baki kawai Saleema take yi cike da farin ciki, kana tace "dagaske nayi kyau Sis?"

Halwa tace "wlh sosai kinyi kyau Sister, kuma ina da yaƙini dole ki shiga ran sa alokaci guda, don babu wanda zai ganki be yi fatan ki zamo matar sa ba".

Dariya Saleema tayi tace "Thank you My Sister, bari inje kar suji Ni shiru tunda nace kizo muje kinƙi".

Girgiza kanta Halwa tayi tana murmushi tace "O'o Ni bazan iya zuwa ba, ke dai kawai kije ke kaɗai, idan yasake dawowa watarana sai mu gaisa".

"To na tafi, sai na dawo Sis".

Daga nan fita tayi ita kuma Halwa kwanciya tayi tana sauke ajiyan zuciya cike da tunani a ranta, Saleema tana shiga Parlour'n da sallama Brr. Tahir da yatsare ƙofan da idanu ya'amsa mata yana sakin murmushi, a ransa kawai "masha Allah yake faɗa". Don ba ƙarya Abokin nasa ya dace da zaɓi, Saleema kanta a ƙasa ta'iso tazauna kan sofa me facing nasu, sai tagaishe su alokaci ɗaya tana ɗago kai tana kallon su, dai-dai da shima Khalil ya ɗago kai yasauke idanu kanta suka haɗa idanu, sauke kanta ƙasa tayi cike da tsananin kunya tare da zallan farin ciki, shi kuwa taɓe baki kawai yake yi amma yakasa ɗauke idanun sa akanta, Brr. Tahir kuwa cikin murmushi ya'amsa mata tare da tambayan ta "ya take da ƴan gidan?" Amsa mishi tayi, sai Brr. Tahir ɗin yakalli Khalil dake faman ƙare mata kallo, hakan yabashi dariya yayi saurin ƙumshe bakin sa yana cewa

"To Abokina ga fa Amarya ta iso, Ni bari in fice in baku space don kutattauna ko?"

Sai lokacin Khalil

Please Login or Register in order to submit comment