Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saleema bata sake bari magana ta haɗa su da Halwa ba, yamma na yi Saleeman tace zasu tafi ganin Ummi ma zata wuce wajen aiki, haka suka yi sallama suka fito tare da Ahmad da Larai tahaɗo masa kayan sa tunda Ummi tace baza ta tafi da Husna ba, kuma dama yanzu Husnan ta soma zuwa school ɗin ta ba ma wuni take yi a gidan ba


A cikin mota ma tsit suka yi babu me magana, Halwa ta kasa yin mata magana ne sabida fargaba, ta rasa wani kalma ne zata iya amfani dashi wajen furta ma Saleeman, musamman yanda taga ita kanta bata son kula ta bare kallon ta, sai hakan yasake saka ta damuwa da tsoro cikin zuciyarta


Suna shiga gidan suka fito cikin motan atare, Saleema na rungume da Ahmad tana ƙoƙarin jan Trolly ɗin sa da drever yaciro mata a Boot


Sai Halwa tayi saurin miƙa hannun ta dake faman rawa tace "sister bari in taimaka miki".


Saleema bata ce komi ba tabar mata tajuya dasauri tawuce


Bin bayan ta da kallo Halwa tayi har sai da tashige cikin gidan, ahankali taja ƙafafun ta a matuƙar sanyaye tanufi ciki itama cike da rashin ƙwarin jiki, tana shiga da sallama idanun ta suka sauka kan su ita da Khalil ɗin dake zaune riƙe da Ahmad ajikin sa yana masa wasa, kallo ɗaya kayi masa zaka ga farin ciki tsantsa a fuskar sa wanda ganin tilon ɗan nasa ne yasaka sa wannan tsantsan murnan


Tunda tashigo shima yaɗago kansa yana kallon ta, wani irin kallo yake aika mata dashi me cike da zallan soyayya da nuna shauƙi ga duk wanda yagani


Hakan yaƙara saukar ma da Halwa kasala da mutuwar jiki, idanuwan ta tajanye daga kansa wanda suka kawo ruwa lokaci ɗaya tana ɗaura wa akan Saleema dake wasa da hannun Ahmad


Daƙyar tasoma jan ƙafafun ta bayan tacire idanun ta daga kallon ta tashigo cikin parlour'n, bata ce komi ba tayi hanyan ɗakin Saleeman tashige don ajiye mata Trollyn


Hakan yasa Khalil yabi ta da kallo cike da wani irin yanayi ganin yanda tasauya lokaci ɗaya duk da kuwa be ga hawayen idanun ta ba, amma ya tabbata akwai abinda ke damun ta


"Me yasami Maman Husna naganta ahaka?" Yayi maganar lokacin da yamaida idanun sa kan Saleema


Murmushi Saleeman tayi tace "babu komi wlh me kagani?"


Numfashi kawai yaja batare da yace komi ba yamaida idanun sa kan t.v


Lokacin Halwa tafito tanufi ɗakin ta tashige har da rufe ƙofan da keey, ahankali tazame ƙasa a jikin ƙofan tahaɗa kanta da gwiwa tasoma rere kuka, kuka take yi sosai wanda tatoshe bakin ta da gyalen ta ta yanda babu me jin ta, ita kanta bata san kukan na menene ba, sai dai tasan yana da alaƙa da yanda Saleema tanuna mata, wannan dalilin yasaka zuciyarta take mata wani irin zugi wanda ta san cewa dole ne rabuwar ta da wanda zuciyarta take bege a halin yanzu, alƙawari ne taɗauka kuma dole ta cika shi baza ta taɓa yin sanadin da Saleema zata sake shiga ƙunci a rayuwan ta ba, wanda ta tabbatar da cewa muddun tazauna batare da son ta ba bata jin zata yi farin ciki



Bata tashi a wajen ba sai da aka yi kiran sallan magriba, tamiƙe ahankali jiri na ɗiban ta sabida tsananin kukan da tasha, har gaban ta bata iya gani haka talallaɓa tashige Toilet taɗauro alwala


Sallah tayi tazauna nan bata tashi ba, sai da aka kira sallan isha'i sannan tatashi ta gabatar.




Lokacin da Khalil yadawo daga sallah shi kaɗai yazauna a Parlour, shiru-shiru yana jiran yaga sun fito amma babu wanda yafito cikin su, tashi yayi yashiga ɗakin Saleema nan yaganta zaune tana aikin gyaran kayan Sip da tawargazo gaba ɗaya tana maida wa


"Wai baza ku fito mu ci abinci bane?" Yace da ita lokacin da yaƙarisa gaban ta yana saka hannun sa ɗaya yadogare da Sip ɗin


Kallon sa tayi tace "zan zo amma yanzu Ni dai bana jin yunwa ne sai anjima".


"Ok bari inje ɗaki nima ina da aiki". Abinda yafaɗa kenan yajuya yafice


Yana fita yatsaya yana kallon ɗakin Halwa, shiru yayi yana tunanin yaje ko kar yaje, haka kawai yaji gaban sa na faɗuwa, gashi kuma yana jin babu daɗi ganin yanda tashigo a ɗazu kuma ya san bata sake fito wa ba har yanzu tunda tashiga


Numfashi yaja yanufi ɗakin sa yashige.



*****

Ƙarfe 11:30pm. Lokacin gidan yayi tsit baka jin ƙaran komi


Ahankali Halwa dake zaune a ƙasa jikin gado tamiƙe tasaka Slippers ɗin ta taja Trollyn dake gaban ta shaƙare da kayan ta, cikin sanɗa tafito tana tafiya ahankali har ta'isa bakin ƙofan parlour tasaka hannu tamurɗa keey ɗin tabuɗe tafice


A haraban gidan babu kowa sai hasken lantarki da ya haskaka gaba ɗaya wajen, inda akwai duhu nan take raɓa wa tana bi duk da kuwa zuciyarta cike take da tsananin tsoro, amma abinda take hango wa shine kawai tabar gidan, bata son ko kaɗan tasake kwana a gidan nan


Tana isa bakin ƙofa taci Sa'a babu me gadi, sai dai ya rufe ƙofan ya shige ɗaki ya ɗan kwanta zuwa anjima sai yatashi yaci gaba da aikin sa


Ahankali tasaka hannu tazare saƙatan ƙofan taja Trollyn ta dasauri tafice batare da ta rufo ƙofan ba.


.









_uhmm wlh yau na gaji nasha typing da yawa, nayi muku har gobe ne ku karanta rabi yau sai ku bar rabin gobe😆, Asha karatu lafiya Fans, Ina matuƙar ƙaunar ku._
[1/5, 12:13 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

_Wannan shafin naku ne *Mommyn Teema* tare da *Mmn Adnan/Yusra* ku more da wannan ɗin 👇 ina godiya da ƙaunar ku gare ni._



*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Twenty Three*

________🎓 Washe gari da safe Khalil ne yasoma tashi yay Shirin sa na zuwa Office, dayake yau ɗin yana da aiki sosai don haka da wuri ya shirya be tashi Saleema ba yafito Parlour, yasan cewa Halwa ce ke yin musu girki a yanzu shiyasa yanufi dainning ɗin kanshi tsaye, amma me? abun mamaki babu breakfast ɗin


Tsayawa yayi yana kallon wajen cike da tsantsan mamaki, yasan bata taɓa late ɗin yin musu abin kari ba, musamman da tasan yanzu yana yawan fitan safe sosai


Ganin dai tsayuwar sa babu amfani sai yajuya yashige ɗaki yaɗau briafcase ɗin sa yafito, kasancewar sauri yake yi duk da kuwa yana son shiga yadubo ta ko lafiya sai dai kuma be yi hakan ba yanufi ƙofa zai buɗe yafita, abun mamaki ƙofan abuɗe yagani babu keey, sosai yayi mamaki a ransa yatsaya yana tunani ko dai jiya basu rufe ƙofan bane? shiru yayi yana son tuno wa, tabbas jiya ba shi yarufe ƙofan ba maybe su Saleema sun manta ne, da wannan tunanin yabuɗe ƙofan yafice


Motar sa yashiga yaja yay bakin Gate yana danna horn


Me gadi dake zaune bakin ƙofan a saman benci yayi saurin tashi yawangale masa Gate ɗin yafice



Sai a lokacin Gate man ɗin yasaki wata wawan ajiyan zuciya, tunda yatashi da asuba yaga ƙofan abuɗe yake a cikin ruɗu, yasan dai Khalil baya fita sallan asuba sai idan ta ɗauro, kuma ajiyan yariga kowa tashi agidan bare yay tunanin wani ne yazo yabuɗe, saboda ma yatabbatar da zargin sa sai da yatambayi ma'aikatan gidan duk suka ce masa basu bane, to yanzu jira yake yi yaji ko Oga Khalil zai yi masa maganar wani abun ya faru a daren jiya but ganin ya fita batare da ya tunkare sa da wata magana ba shine yaji dama-dama aransa, domin dai yana da tabbacin ya rufe ƙofan, kuma be sake dawowa wajen ba sabida barcin da yasha jiyan.




Saleema bata tashi ba sai wajen ƙarfe 10:00am. Wanka tasoma yi sannan tashirya cikin doguwar riga na yadi me ruwan kuka, ɗinkin fitted gown ne sannan sai aka yi kwalliya da red stone a gaban rigan, ɗaura ɗankwalin simple tayi sannan tanufi kan gadon taɗauki Ahmad tazauna tasoma cire masa kaya


A lokacin yafarka yana saka mata kuka


Rarrashin sa tasoma yi tana ci gaba da kwaɓe masa kayan, bayan ta gama ajiye shi tayi tashiga Toilet tahaɗa masa ruwa a bawo tafito taɗauke sa, wanka tayi masa tadawo tashirya sa, sai da tahaɗa masa abincin sa taba shi sannan takwantar dashi tafito Parlour


Direct kan dainning tanufa sai dai ganin babu komi a wajen sai taja ta tsaya, shiru tayi na ɗan daƙiƙa kafin tasaki murmushi


Daman tasan za'a rina, Halwa zata shiga wani hali a sabida yanda tanuna mata a jiyan, ita har a zuciyar ta ba wai haushin Halwa take ji ba, tabbas dai taji kishin ta da Ummi tafaɗa mata yanzu tana matsayin kishiyar ta ne, amma kuma abinda yaƙara saka ta damuwa ce mata da akayi an juya mata mahaifa, sosai tashiga wani irin ruɗu da yahaddasa mata jin haushin Halwan a lokacin tare da tsananin kishin ta har takasa haɗa idanu da ita bare tayi mata magana, sai dai kuma ba wai tayi ne don muzguna mata ba tayi hakan ne kawai don samun damar yin tunani da zuciyar ta batare da tafito da damuwar ta fili sosai don su gani ba


A jiya kwana tayi tana sallah sabida gode ma Allah da yakawo mata Halwa cikin rayuwanta, sannan ta kwana tana roƙon Allah yaba su zaman lafiya a zaman da zasu yi, ta sani cewa zuciya bata da ƙashi duk ƙaunar da suke yi wa junan su tunda har kishi yahaɗa su tabbas sai sun ɓata, don itama jiya ba ƙaramin ƙarfin hali tayi ba da danne zuciyarta har zuwa yau ɗin da tatashi sakayau babu abinda ke damun ta, burin ta a yau ɗin tafaɗa ma Khalil yaraba musu kwana su zamto matan sa su duka.


Numfashi taja tana saka hannunta ta sosa goshin ta kafin tanufi ɗakin Halwa, tura ƙofan tayi tashiga da sallama tana wurwurga idanu cikin ɗakin ganin babu ita, bakin gadon tanufa tazauna a tunanin ta ko tana cikin Toilet, sai dai har tsawon shafewan wasu mintoci babu Halwa babu dalilin ta


Miƙe wa tayi tanufi Toilet ɗin tasaka hannu tayi Nocking, jin shiru sai tatura ƙofan tashiga taduba babu kowa, fito wa tayi tana sake bin ɗakin da kallo, a ranta kuma tana tunanin inda Halwa taje, tuna ko tana kichen ne yasaka ta fita tadoshi kichen ɗin, sai dai nan ɗin ma babu ita


"Haa'a to ina taje ne wannan matar?" Tafaɗa a fili lokacin da tafito Parlour tana sake kewaye parlour'n da kallo


Numfashi taja kafin tafice dasauri, Garden ɗin gidan tanufa tasoma dube-dube sai dai duk inda tasan zata iya ganin Halwa agidan ta duba babu ita, hankalin Saleema ya soma tashi sosai, cikin ruɗu tanufi bakin Gate


Me gadi tunda yahange ta yatashi yana muzurai


Tana isowa tambayan da tasoma yin masa sai da hantan cikin sa yakaɗa, amma cikin ƙarfin hali yabata amsa da cewa "wlh Hajiya Ni dai yau ban ga gilmawan ta ba, rabon da na ganta tun jiya da kuka dawo cikin gidan nan".


Goshin ta ta dafe cike da tashin hankali, sai kuma tasake kallon sa tace "to ko ka ga sun fita da Barrister ne?"


"O'o O'o shi kaɗai yashiga motar sa yatai abin sa".



Juyawa tayi dasauri har tana cin tuntuɓe, yanda zuciyarta lokaci ɗaya takawo mata banzan tunanin cewa ta gudu ne hakan yasaka hankalin ta yay mummunan tashi, har tana tuntuɓe tana faɗi wajen isa ɗakin Halwan da mugun saurin ta, Direct gaban Sip ɗin kayan ta tanufa tabuɗe tasoma duba wa babu komi aciki


Dayake ta dawo da kayan ta ɗakin, akwatunan auren ta kuma Khalil ya ɓoye mata a Library ɗin sa.


Wani irin mugun bugawa ƙirjin ta yayi, tana shirin zube wa ƙasa tahangi farar takarda dake kan gadon an danne rabin sa da pilow wanda tun shigowar ta ɗazu bata kula dashi ba, dasauri ta'isa wajen taɗau takardan tana buɗe wa gaban ta na faman faɗuwa, rubutun tabi da kallo kafin tasoma karanta wa



_Aslm alaikum ƴar uwata, nasan zaki ga wannan saƙon ne a lokacin da nayi nisa da rayuwan ku, kar ki damu bare ki ɗaga hankalin ki, Ni naga dacewar barin ku sabida wasu dalilai na, i know zama daku a yanzu be da wani amfani sabida naga kamar ina son shiga rayuwan ki ke da mijin ki, wlh sister bani da ninyan ƙuntata ma rayuwan ki, babu wanda ya tambayi ra'ayina akan aure na da Yaya Khalil, shiyasa yanzu na gummaci barin ku akan nazauna da auren sa batare da son ki ba._


_Abu ɗaya nake roƙon ki kiyi min alƙawarin zaki kula min da kanki, kar ki taɓa saka damuwa a ranki duk inda nake zan rayu ne cikin farin ciki tare da kewar ki a raina, sannan ki roƙa min Mijin ki yasake ni sabida bana son in zauna da auren sa a kaina._


_Allah yaba ku zaman lafiya da ɗorewan lafiyan ki ƴar uwat..."_


Yanda hawayen idanun ta ke sintiri saman fuskarta yasa takasa ganin sauran rubutun, gaba ɗaya ta jiƙe takardan da hawayen ta, kuka tafashe dashi tana zame wa ƙasa tafaɗi, kuka sosai take yi wanda yahaɗe mata da tari sai yi take yi babu ƙaƙƙauta wa, magana take son Yi amma Ina da zaran ta soma buɗe bakin sai takasa furta wa sabida tari da kukan da take faman yi, babu abinda harshen ta ke iya ambata sai sunan Halwan tana wani irin kuka me cike da tsantsan firgici tare da fita hayyaci



Zabura tayi dasauri tatashi tanufi ɗakin ta da gudu riƙe da takardan a tafin hannun ta, wanda tamatse sa gamm ta kasa saki, wayan ta taɗauka tafito Parlour tasoma neman layin Khalil, ringing ɗaya yaɗauka



Kuka tasake fashe wa dashi da ƙarfi tana tattaro numfashin ta wajen har haɗa kalmomin da zata faɗa masa


"Hal..wa.. ta tafi ta gudu.. ta bar ni, ta tafi.. Halwa...".


Kasa ƙarisa maganar tayi sabida wani irin tari me haɗe da gudan jini da yataho mata


Khalil dake zaune kan kujeran Office ɗin sa, tun sanda yasaka wayan a kunne yasoma jiyo kukan Saleeman hankalin sa yay ƙololuwar tashi, tambayan ta yake yi ko lafiya duk da yaji tana magana but ya kasa jiyo me take cewa sai sunan Halwa da take faɗi, dasauri yaharhaɗa kwarmatsan sa yasaka wayan a aljihu batare da ya kashe ba, keey ɗin motan sa ya ɗauka yafito da mugun sauri duk hankalin sa a tashe, sosai yashiga ruɗu da faɗuwar gaba don yasan babu lafiya


Cikin mintunan da basu gaza 10 ba ya'iso gidan.



Saleema na nan zaune a inda take, izuwa lokacin tayi kiran Numban Halwa ya kai sau ashirin but amsan ɗaya ne a kashe yake Numban


Shigowar Khalil yayi dai-dai da sakin wayan da tayi tana sake fashe wa da kuka


Gaban sa ne yafaɗi time ɗin da ya sauke idanun sa akanta yaga jini a bakin ta, ga kuma wanda yaɗiga a ƙasa, cikin kiɗima yatunkare ta dasauri yana duƙawa gaban ta yariƙo ta tare da tambayan ta abinda ke faruwa


Amma ina ta kasa magana illa ƙara Volume ɗin kukan ta da tayi, daƙyar taɗago hannun ta tamiƙa masa takardan dake ciki


Dasauri yasaka hannu ya'amsa yana warware wa sabida yanda tacukuikuye shi duk ya yage, wani irin rawa jikin sa yasoma yi ganin abinda ke ƙunshe a takardan, idanun sa yakai kan Saleema da tuni numfashin ta ya rabu da gangan jikin ta, lokaci ɗaya sai ga hawaye sun cika masa idanu yana zama dirshan a ƙasa tare da dafe kansa da yasoma mugun sara masa, cikin wani irin sarƙewan murya yace



"Why Halwa? Why kike azabtar da rayuwana? Me na miki?"


A dai-dai lokacin da hawayen suka sauka kan kyakykyawar fuskar sa.










.





_kai gaskiya *SALEEMA* kina ganin rayuwa._


_anya baza mu bar Halwa taƙara gaba abinta ba abar Barrister da Saleeman mu? Tunda naga kamar kun fi sonta dashi._


_ko kuma daga nan Saleema tatafi tabar mana Halwan mu da Barrister._


_don haka yanzu ina son jin ra'ayoyin ku, ku zuba min ƙuri'a duk wacce tafi Fans tsakanin *SALEEMA* da *HALWA* to ita ce zamu bar ta da *BARRISTER* sai na ji ku._ 💃💃💃💃💃
[1/5, 12:23 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️


*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*




*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈


*\F.W.A📚/*

```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

```Wannan shafin naku ne masoyana Fhadeela, Fateeymuhammad, Auta Safna, Nana Faruk, Nafisa Ibrahim, Mum Afnan $ Yumna.. kuji daɗin ku da wannan page ɗin domin naku ne kyauta, na gode da ƙaunar ku gare ni.```


*BOOK TWO*


.

_______________________________

*CHAPTER Twenty Four*

________🎓 Jiki na rawa Khalil yamiƙe yanufi Fridge ya ɗauko ruwa yazo ya yayyafa mata a fuska, bata motsa ba sai da yasake zuba mata sosai kafin takawo numfashi alamun ta dawo hayyacin ta, bata buɗe idanun ta ba sai dai hawaye dake fitowa ta cikin idanun suna gangarowa gefen kunnen ta


Kiran sunan ta yasoma yi but taƙi ta amsa masa duk da kuwa tana jin sa, hankalin sa ne yasake tashi yana shirin ɗaukar ta sai wayan ta tasoma ringing, ɗauka yayi ganin Ummi ne me kiran sai yayi peacking


Daga can Ummi ce tasoma magana da faɗin "Hello My dear".


"Aslm alaikum Ummi ba ita ce ba".


"Ok Khalil Kai ne ashe, to lafiya dai ko?" Ummi tafaɗa gaban ta na faɗuwa


"Ummi babu lafiya, Halwa ce tabar gida ita kuma Saleema gata nan akwance har suma tayi sabida tafiyan nata". Yayi maganar ahankali cikin dauriyan murya da dannewar tashin hankalin sa


Cike da tsananin tashin hankali Ummi tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ta tafi kuma me yafaru ne?"


Bata jira kuma amsar sa ba sai tace "gani nan zuwa gidan yanzu insha Allahu".


Wayan takatse tana ɗaukan gyalen ta tayafa tare da jakar ta tafito Parlour


Daidai lokacin da shima Abba ya fito daga nashi ɗakin yana saɓa malin-malin, hannun sa riƙe da takardu, su yamanta shine yadawo ɗauka


Kallon sa tayi yayinda shima yake kallon nata


"Lafiya na ganki ahaka meke faruwa?"


Ummi kamar zata yi kuka saboda tashin hankalin da take ciki tace "Abban Saleema wlh babu lafiya, wai Halwa ce tabar gidan ga kuma Saleema can hankalin ta atashe har suma sai da tayi".


"Subhanallah.. mu je muje gidan". Abba yafaɗa yana yin gaba dasauri Ummi na take masa baya



*****

Shashsheƙan kukan Saleema ne kaɗai ke tashi cikin parlour'n, tana jingine jikin Ummi, Abba kuma na zaune gefen Saleeman sun saka ta tsakiya, yayinda Khalil ke zaune a kujeran dake Facing nasu


Tunda suka zo suke faman rarrashin ta but taƙi yin shiru sai ma ƙara tayar musu da hankali da take yi, musamman yanda suka ga in tayi tari jini ke fita, kuma taƙi tashi akaita asibiti illa nuna musu cewa babu abinda ke damun ta ita Halwa kawai take son tadawo, baza ta taɓa iya rayuwa babu Halwa ba, taɓara dai irin na ƴaƴan gata shi tazauna tana ta musu, yayinda su kuma suke ta faman lallaɓa ta Ummi har da ƙwallan ta, kai da gani kasan ba'a hankalin ta Saleeman take ba


Shi kanshi Khalil tsananin tausayin ta ne ya cika sa, shima yayi rarrashin but taƙi kula sa sai kuka take yi tana surutai


Abban ne yace su koma gida in yaso sai akira Doctor yaduba ta, daga nan sai anemi Halwan ko za'a ganta, don haka suka tattara gaba ɗaya har Khalil da yaɗauko Ahmad yamiƙa wa Ummi suka bar gidan, su sun wuce gida shi kuma Khalil yabi cikin anguwa ko Allah zai sa yahaɗu da Halwa


Idan kukaga Khalil a yanzu zai matuƙar baku tausayi, sosai yashiga damuwa akan tafiyar Halwan, gaba ɗaya zuciyarsa ta kasa sukuni tun sanda ya karanta takardan nan, yana ji ajikin sa ta tafi kenan, wannan dalilin ne yasaka yashiga matsanancin tashin hankali, sai dai juriya da ƙarfin hali da yake dashi hakan yake saka wa baza ka gane a halin da yake ciki ba



Yayi yawo sosai babu inda be je ba wai ko zai ganta, duk da Halwa bata da wajen zuwa but inda be yi tunanin zata je ɗin ba duk ya duba, haka yaƙarishe yawon sa yawuce gidan su, inda anan ne yafaɗa musu halin da ake ciki


Su ma Dad da Mom sun tashi hankalin su matuƙa, anan ne ma Dad ɗin yake faɗa musu labarin Halwan da alaƙan su dasu Saleema


Lokacin da Dad ɗin yagama faɗa musu komi sai kawai hawaye suka ciko idanun Khalil, miƙe wa tsam yayi yafice daga parlour'n yadoshi part ɗin su inda ɗakin su yake na Da


Akan gado yakwanta yana lumshe kyawawan idanun sa, haushi da takaicin kansa kawai yake yi



Meyasaka ya ɗau laifi ya ɗaura wa baiwar Allah batare da yasan musabbabin rayuwan ta ba? Shin meyasaka yamanta cewa ƙaddara irin wannan zai iya samun ta batare da laifin ta ba?


Shin meyasa mutane suke ɗaura laifi ga macen da suka ganta tana rayuwan ƙasƙanci? Shin sun tambaye ta dalilin da yasa har tafito gida take wannan rayuwan? ko kuma sun manta cewa wasu sanadin fyade ne yajawo musu rabuwa da gida akan tsangwama da kyara da ake musu, menene laifin su don ƙaddara ta faɗa musu ake koran su? Shin mun manta da cewa idan suka tafi zasu ci gaba da wannan rayuwan ne ko kuwa su faɗa hannun ɓata gari wani abu yasame su ta sanadiyar mu ne.. Allah dai yatsare mana imanin mu yasa mufi ƙarfin zuciyar mu, ya Allah ka kare mana zuri'armu daga faɗa wa mummunan rayuwa..


Ajiyan zuciya kawai yake sauke wa, ya jima a haka kafin daga bisani yamiƙe yaɗauro alwala jin ana kiran sallah yafice.


Wasa-wasa har dare babu Halwa bare labarin ta


Izuwa lokacin har ƙarin ruwa sai da aka yi ma Saleema, sai da akayi mata alluran barci sannan suka samu sukuni domin yanda tashiga wani hali hakan ya ɗaga wa iyayen ta hankali, babu daman tayi tari sai jini ya fito, gashi Doctor yayi musu bayanin cewa idan har taci gaba da kasancewa ahaka to tabbas akwai matsala domin zuciyarta ta gama kumbura sosai


Abba yaso akai ta asibiti but likitan yace abar ta zuwa safiya idan jikin ya sake tsanani.


Bata farka ba sai washe gari, Ummi ita ta taimaka mata tayi wanka tashafa mata mai tare da saka mata kaya, sabida ko kaɗan bata da ƙarfin jiki bata iya yin komi da kanta, sosai suke ta lallaɓa ta suna faɗa mata kalamai masu daɗi yanda zata kwantar da hankalin ta


Abinci ma abaki Ummi taba ta sannan taba ta maganin ta tasha.




**** **** **** **** *****

Tunda Halwa tafito daga gidan sai tasaka kuka, tafiya take yi batare da tasan inda zata nufa ba, ahankali take jan Trolly ɗin duk da kuwa zuciyarta cike take da tsoro matuƙa ganin yanda garin yaƙara duhu gashi babu kowa sai haushin karnuka, but bata jin zata iya tsaya wa hakan yasaka taci gaba da tafiyan ta tare da danne tsoron ta cikin rai, tafiya ɗaya sai ta waiga ahaka har tafito titi inda anan ne take ɗan ganin motoci suna wulƙa wa


Hannun ta tasaka tasharɓe hawayen fuskarta kafin tanufi titin don ta tsallaka, babu zato tahangi mota tayo kanta duk da kuwa bata san da zuwan motan ba sai ganin ta tayi kusa da ita, ƙwalla ƙara tayi amma ina tuni motan ta bige ta


Dasauri matar dake cikin motan tafito ita da ƴaƴan ta biyu suka yo Kan Halwa


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Matar take faɗa


Yayinda ƴan matan

Please Login or Register in order to submit comment