Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kafe ta da nasa idanun.

Ta daidaita nutsuwarta, ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta fara rero karatun Alqur'ani cikin muryarta me daɗin sauraro, take gurin yai tsit kamar babu wata halitta a gurin, se muryar Farhan da ke tashi a gurin.

Ayoyi goma ta karanta na farkon suratul Yusuf, sannan ta rufe da addu'a, tana idarwa akai mata kabbara, seda Sadik ya dinga wasata kafin ya miƙa ragamar assembly ga malamin da ke duty a ranar.

Ta sha yabo ma daga gurin malamai, saboda yadda tai karatun cikin nutsuwa, bayan an watse daga Address, maimakon ya tafi ajinsu, se ya tafi ajinsu Farhan.

Ya sameta a gurin zamanta yace "Weldon dear, gaskiya kin iya karatun Alqur'ani sosai Masha Allah, you have a nice voice"

Se taji kalmar dear ɗin nan ta ɗan mata girma (😂😂 kun sanmu hausawa wasu lokutan)

"Ya naji kinyi shiru, ba zaki ce komai bane?"

Sunkuyar da kai ta kuma yi, kamar wata amarya, Sadik yace "shikenan, tunda ba zaki Magana ba, I love Your voice, in am fito break zan zo"

Ai take gabanta ya faɗi, he loves her voice kuma? Allah yasa wani be ji me yace ba, love kuma? Wannan ya fiye rigimar tsiya.

Sadik yana zuwa aji, Nasir yace "wai ina ka tafi ne?"

"Na je Jss2 ne"

Amin yace "wai uwar me kke a ajin nan da kake yawan zuwa,, kamar me zuwa neman wani abu?"

yace "Wallahi gamo  nai a ajin"

"Wane irin gamo kuma?"

Prince yai wani ƙasaitaccen murmushi yace "a very beautiful Young beb, ban san meke damuna ba, se dai ina son kasancewa kusa da ita ko yaushe, in dinga kallon kyakykyawar fuskarta ɗauke da ƙasaitaccen murmushin ta"

Nasir yai tsaki yace "ji banza, meye haka se kace wani a hausa film, malam ba fa acting ka ke ba, real life ne, kai ka fiye shirme wasu lokutan"

"Ba shirme nake ba Nas, i think am in love with that beautiful creature"

Amin ya kwashe da dariya yace "kaga wata asara, kuma da 'yar Jss2? Yaran da duk ƙwailaye ne,  maimakon ka samo wata zazzafa duk matan school ɗin nan ka rasa ina zaka samo budurwa se Jss2 dan ci baya, duk matan Senior classes ɗin nan, wanda suka amsa sunan su mata, dan tsuya se  a Jss2?"

Prince yace "ba zaku gane ba ne"

Nas yace "wait, wacece a cikin Jss2 ɗin?"

"Farhan, Yarinyar da tai karatun Alqur'ani a assembly ground"

A tare Amin da Nas suka ja tsaki.

Amin yace "dan Allah meye abun so a wannan Yarinyar? Wannan kwata kwata yaushe aka yayeta daga shan Nono aka kawo ta makarantar?"

Nasir yace "taɓɗijan, a part from sexy eyes banga meye abun burgewa a wannan Yarinyar ba, gata wata kidahuma, kullum tana aji da littafi kamar al huda huda, kullum kanta a ƙasa kamar munafuka, tana kallon Mutane ta ƙasan ido, da an tashi ta zumbula wani uban hijjabi kamar wata me da'awa ta ɗau jaka dunkum dunkum kamar 'yar 419, she don't even look romantic at all"

A fusace Sadik yace "zanci ubanka Nasir, bana son wulaƙanci a haka nake sonta, ka sake faɗan wani rashin hankalin a kanta, zan fasa maka baki"

"Allah ya baka haƙuri, Allah ya bar wannan ƙauna, ta shiga sahun tarihi fiye da Romeo and Juliet, ashe zaka iya yin budurwa Prince?"

Tsaki Prince yai ya tashi ya bar ajin gaba ɗaya, saboda yadda suka sashi gaba da iya shege.

Sadik ya sa Farhan a gaba, duk inda ya san ze ganta se yaje, shi babban abunda yake damunsa da Farhan rashin magana, gashi taƙi sakin jiki da shi sosai, ko abu ya bata ba zata karɓa ba.

Wataran ya ritsata an tashi, ta  ɗau jakarta zata tafi gida, ta jiyo muryarsa yace "sweet heart"

Da sauri ta waigo, dan tantance  da wa yake, kasancewar ba ita kaɗaice a gurin ba.

"Da ke nake Farhan, yau ban ganki ba, Ina kika shiga ne?"

Waige waige ta shiga yi taga ko su ake kallo, amma taga ba wanda ya damu da su, wannan kalma haka me nauyi da ba'a jinta se a bakin mayan samari da 'yan mata kuma masoya, amma ya kirata da ita a cikin jama'a.

Ya ƙaraso inda take tsaye yace "Akwai abunda ki ke nema ne?"

Ta girgiza masa kai, yai ajiyar zuciya yace "yau Friday shikenan ba zan sake ganin ki ba se Allah ya kaimu Monday?"

Sunkuyar da kai tayi, tana wasa da yatsunta.

"Farhan kalleni"

Ta ɗago ta kalleshi ta mayar da kanta da sauri ta sunkuyar, saboda yadda yai mata kwarjini.

"Farhan, ban taɓa budurwa ba, amma am feeling something different on you, ina sonki Farhan!"

Se da ta de na ji na wasu ɗan lokuta, wannan gingimemiyar kalmar, wai yana sonta, taji kamar ƙasa ta tsage ta shige saboda yadda kalmar tai mata dirar mikiya.

"Ya naga kamar kina tsoron wani abu ne? Ko dai ba kya sona ne"?

Tai shiru ba tace Komai ba "shikenan, muje se mu sauke ki a gida"

Da sauri ta girgiza kai tace "Za'amin faɗa a gida"

"Ok, to mu fita gate ɗin tare"

Ba zata iya yi masa musu ba, amma Jerowar da sukayi da Sadik ji take tamkar ta zura da gudu, wannan ai rashin kunya ne, yadda suka jero tare, amma shi ko a jikinsa.

Har ta koma gida juya maganar Prince take, wai yana sonta, shi ko nauyin kalmar be ji ba, ta shiga fargabar kar a gida a gane, wani yace yana son ta dan ta san za ta sha faɗa, dan haka sai tai ta ƙoƙari ta manta da Sadik, amma bata cikakken mintuna ashirin kalmar Sadik na yana sonta be faɗo mata a rai ba.

Tun da Sadik yace yana son Farhan, suke 'yar ɓuya, ba ta yadda su haɗu saboda nauyinsa da take ji, idan kuwa suka haɗu har ya gama surutunsa ba zata tanka ba.

A hankali tun tana jin nauyinsa, saboda yawan haɗuwa da suke da zuwa gurinta da yake, yasa ta fara rage jin nauyinsa, take ɗan sakin jiki da shi.

Gefe guda tana fuskantar tsangwama daga wasu ɗaliban, saboda yadda Prince ke ji da ita, ga kyawawan yara da suka fita komai suna crushing a kansa, amma ya je ya liƙewa Farhan.

A hankali ɗalibai suka dinga gane alaƙar da ke tsakanin Prince da Farhan, kasancewar he is very popular a makarantar.

Shaƙuwa ta fara shiga tsakani ta da Prince, ya zamana idan ma be zo inda take ba, da kanta za ta je ajinsu Sadik dan ta ganshi,

Dawowa tai daga dogon tunanin da ta tafi, tana tunanin meye mafita akan yadda zata shawo kansa ya haƙura.

Dan gaskiya she's ready to do anything dan taga Sadik ya dena fushi da ita, yanzu idan ya dena kula ta fa? Ko ya canza budurwa ya za tayi?!

Ji tai gabanta ya faɗi, da tai tunanin Prince ya canza budurwa.





YANZU AKA FARA, SALON NA DABANNE.

DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
AYSHERCOOL
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️



                               5_6

Da sauri Farhan ta miƙe, ta kwaso Uniform ɗinta, taje ta wanke ta shanya.

Ta na cigaba da tunanin, ya zata shawo kan Prince ɗin ta.

Prince kam shima abun duniya ya ishe shi, ya rasa abunda yake masa daɗi, ya dinga jujjuya maganganun su Nasir, ɓangare guda yana jin yadda zuciyarsa ke ƙara jin son Farhan.

Maganganun su Nas na kiransa Yaro, tabbas sun ɓata masa rai amma hanyar da suke ɗora shi a kai, ba me ɓullewa bace.

Miƙewa yai zaune ya kalli agogo, har huɗu da rabi, tunda ya dawo be fita daga ɗakin ba.

A hankali ya tashi ya shiga toilet yai wanka, ya fito yai sallar la'sar, sannan ya shiga cikin gida.

Abun dai da baya so, mutane na ta shiga suna fita a gidan, saboda shriye shiryen bikin Yayansa.

Yatsuna fusaka yai ya shiga falon, ya nufi ɗakin Mother.

Yana shiga ta ɗago ta kalle shi tace "Autan, i have been looking for you since, where have you been ne?"

"Mother ta ya zan shigo, duk an bi an cika mana gida, kamar an fara bikin, mutum da gidan su a hanashi sakewa"

Tai murmushi tace "Ai Arziki ne abun farinciki ya samu brother ɗin ka, an zo taya mu murna, sedai kayi haƙuri, da anyi bikin an gama shikenan"

Prince yace "Da anyi nasa se nawa kuma"

Mother ta kalli Sadik ta ɗan buɗe baki tace "sannu, kai fa baka da kunya wasu lokutan, a beg go carry your food and eat"

"Mother dagaske fa nake"

"Zan make ka, tashi ka bani guri, ka ci Abinci ka ɗau litattafnka ka karanta, bana son shirme"

Bin mahaifiyarsa yai da kallo, yana mamakin yadda suka ɗaukaki boko, ashe akwai daru a gaba, dan gaskiya baze iya zaman jiran wai se ya gama wata jami'a ba.

Ya ɗau Abincinsa ya zauna yana ci a bedroom ɗin, amma tunanin sa na kan wani abu daban.

"Auta, ya naga baka cin Abincin? Meke damunka ne?"

"Bakomai" ya faɗa a taƙice, da ya kammala cin Abincin a nan ya bar kwanukan, da gurin yai gaba abunsa.

BQ ya koma ya sake kwanciya, abun duniya duk ya dame shi, a gaskiya shi baze yadda da wanan aƙidar bokon ba, haka kurum wannan ai cutar mutum ne, ace wani seka yi master's tukuna.



"Nana! Nana!"

"Na'am Innar mu"

"Au da kina jina nake ta faman kiranki  kika min banza?"

"A'a, na amsa fa"

"Ai kin san ni ɗin kurma ce da ban ji ba ko?"

Ta girgiza kai alamr a'a.

Inna ta ɗan ƙureta da ido sannan tace "Ni kin ma yi wanka tukuna yau?"

Tura baki Nana tayi, jin Inna zata fara halin tace "nayi mana"

"Amma kayan jikin ki masu datti ne ko?"

"A'a jiya fa na sasu daf da magariba, kuma na cire na sa na bacci"

'wai ke wace irin yarinya ce me azababben taurin ka ne? Nace miki idan ki kai wanka ki ka sa kaya masu datti, da kinyi wanka da baki ba duk ɗaya jikin ki baze fasa wari ba, haka idan ki baki wanka ba ki ka sa kaya masu kyau shima ba zaki dena wari ba, amma kin kasa ganewa kinfi so kullum in ta yaƙi da ke ina maimaita miki abu ɗaya"

"Haba Innarmu, wallahi bana wari, kayan fa ba datti su kai ba, kuma ko gumi ban ba"

"Zaki wuce kije ki canza kayan ne, ko sena sa miki abun duka? Kije ki cire wannan kayan, ki ɗebi ruwa kije ki sake wanke hammatarki, ki kama ruwa ki wanke fusakarki, ki shafa mai ki canza wannan kayan bera ƙazama"

Nana kamar ta ɗora hannu a kai ta ihu, Inna a duniya idan ba ta takura mata ba bata samun nutsuwa.

Taje ta ɗebi ruwa tana kumbure kumbure, taje ta wanke jikinta, ta fito zata zira kaya, amma Inna ta kuma cewa "ba zaki bar ruwan jikin ki ya tsane ba, ki shafa ruwan alumun ba a haka zaki maka kaya a jikinki? Shiyasa nan da nan kike gumi, ki fara ƙari"

Haka Nana ta shirya a gaban Inna, tace shafa kaza a nan, goga wancan a nan, su nayi Nana na zumɓura baki.

Seda ta canza kaya ta shirya tsaf tai kyau, Inna tace  "yawwa ko ke fa, yanzu kije gidan Rabin kuka, ki ce ina gaisheta, ta baki saƙon nan ki kawomin, kuma ki sauri ina nan ina jiranki"

Nana tace to, ta saka takaliminta ta fita, har taje ƙofar soro na farko, Inna ta ƙwala mata kira Nana ta dawo.

Inna tace "na kira ki ne in sake jadad da miki, bake  ba Zuwa inda ban aike ki ba, kije ki karɓomin saƙo kawai ki dawo, ban da faɗi ba'a tambayeki ba, ko tsoma baki a abunda ba ruwanki, kinji na gaya miki ko?"

"Eh naji"

"Yawwa maza jeki"

Nana ta juya, Inna tace "banda kula mazan da baki sani ba, wanda ki ka sanin ma tsakanin ki da su gaisuwa, kinji ba?"

"To" Nana ta faɗa cikin ƙosawa.

"To Allah ya kiyaye, ban da bi ta Majalisar maza, a tafi ana saka hannu a hijjabi, in ba haka ba, 'yan abubuwan nan da suka fara fitowa, wani ze taɓa ya gudu, kuma idan kika bari wani ya taɓa ba Aurarki yai ba, a haka zasu zauna, harki mutu ba zasu kuma fitowa ba, tun da ba kya alkinta su"

Nana a ranta tace 'Allah ya kiyaye suƙi fitowa har in girma, shikenan ba zan zama 'yan mata ba taɓ"

Inna na shirin kuma ɓaro wani abun, Nana tai waje abunta, dan ta gaji da wannan takarar ta Inna da bata ƙarewa se kace karatu.

Ko da taje gidan da aka aiketa, ta shiga da sallama.

Cikin wata siriryar murya wata ta amsa tace "waye?"

Nana tace "Nice innarmu ce ta aiko ni"

"To shigo mana"

Nana ta shiga ɗakin da sallama, suka gaisa da wannan budurwar, ta girmewa Nana sosai, Nana tace "ina maman take?"

"Ta shiga dubiya, nan maƙota yanzu zata shigo ki ɗan jira"

Nan Nana ta zauna tana jiran dawowar wadda aka aiko ta gurinta. budurwar ta tashi ta ɗebi ruwa a bokiti ta tafi wanka.

Tana shiga banɗaki Nana ta miƙe, taje gaban gadon dake ɗakin, ta ɗau wata brezia dake kan gadon, taje gaban mudubi, ta saƙala ta a haka ta kalli kanta a mudubi tace

"Ohh ni Allah, Allah ka nuna min lokacin da zan fara saka wannan abar nima, wai da anga iyayi, ai ko a makaranta da ba kowa zan kula ba,taku ɗai ɗai zan dinga yi, in dinga yiwa kowa gani gani, Allah dai yasa nima nawa suyi girma, Innar mu ta saimin"

Seda ta gama sakarcinta ita kaɗai, sannan ta ajiye ta nemi guri ta zauna.

Tana zama babu daɗewa sega matar gidan ta dawo, tana shigowa taga Nana ta faɗaɗa murmushin ta, Nana ta durƙusa ra gaisheta, sannan ta faɗa mata saƙon Inna.

Rabi ta ɗakko wata leda, ta bawa Nana tace "gashi nan ki riƙe da kyau, ko hanzarta ki koma, kar ta ga kin daɗe"

Nana tace to, ta karɓi leda tai waje, tana daf da barin layin gidan, ta ga wata Budurwa tana ta zance a ƙofar gida, saurayin yana kan babur, ita kuma tana tsaye, yana mata magana tana murmushi haɗe da Rufe fuskarta.

Cak Nana ta tsaya tana kallonsu, so take ta fahimci meyake gayamata haka da yake sata wannan nishaɗin, take murmushi haka.

Nana ji take kamar ta janyo girma, abubuwa da yawa suna burgeta, a hakan nan ma a 'yan ajinsu akwai masu saurayi, amma tasan idan Hajiya Inna ta san tana da saurayi, se ta dafata ta sha romonta saboda terere da faɗa, gaba ɗaya se jama'ar ciki da wajen gidan sun san meyafaru, amma ita har ga Allah tana son jin me ake ji a tsakanin saurayi da budurwa.

Haka ta tafi tana tunanin ko yaushe itama za tai saurayin nan taji me ake ji haka oho?.

"Hajiya Nana 'yan mata!"
Jin abunda aka faɗa yasa ta waiga da sauri, wani Jamilu ne ɗan me unguwa, ita ko magana bata haɗa ta dashi, saboda yawan kashedin Inna ba kowa take kulawa ba a maza, saboda gani take da taje gida Inna zata gane.

Tsayawa tai sororo tana kallon Jamilu, ya ƙarasa inda Nana take yace "ba gaisuwa?"

Nana tace "ina wuni?"

"Lafiya ƙalau 'yar gidan Hakimi, daga ina haka?"

"Inna ce ta aikeni"

"Masha Allah,ya Innar da kowa da kowa?"

"Lafiya ƙalau"

Jamilu yace "muje, dama nima gurin unguwar taku zani"

Cikin Zare ido tace "A'a, haka kurum aje a gaywa Hakimi ko Inna an ganmu a tare,amin faɗa gaskiya a'a"

Jamilu yai murmushi yace "ba wanda ze gaya musu, ai gaisawa kawai muke"

"A'a to ai na gaisheka ba shikenan ba?"

"Nana manya, wai yanzu ajinki nawa ne?"

"Ina ruwanka da ajina?"

"Bakomai, kawai tambayarki nai"

Ta ɗan murguɗa baki tace "ni gaskiya ka ƙyaleni, kar Inna ta gane na kula maza a waje"

Yai murmushi yace"Shikenan na ƙyaleki, yadda ki ke so haka za'ai, kyakywar jikar Hakimi da duk garin nan babu Tamkar ta a gata ko kyau"

Nana ji tai Jamilu ya wani Mugun fasa Mata kai, tace "dan Allah dagaske kake?"

"Sosai, dagaske nake, ke me kyau ce Nana"

"Amma Inna take cemin bani da kyau"

"Wasa take miki, amma kyawunki ya wuce a misalta ma"

"Kai amma naji daɗi, bari in sauri in tafi kar tace na daɗe"

Ta rungume ledar ta, ta zumbuɗa da gudu, dan kar Inna tace ta daɗe.

An fara kiraye kirayen sallar magariba, sannan Nana ta faɗo a guje, Inna ta kalleta tace "lafiya, kike wannan gudun haka?"

Numfashi ta dinga saukewa sannan tace "Gudu nai dan karki ce na daɗe"

"Au gudu Nana, haka kika ratso cikin mazan gidan nan da wannan uban gudun haka? Ke komai naki cikin hauka da hauma hauma ba nustuwa ba komai kamar rainon maza"

"Allah ya baki haƙuri, ga kayanki nan"

Ta ajiyewa Inna saƙon ta tai ɗaki abunta.

Bayan sallar magariba, Nana tana cin tsiren da Hakimi kan sa a kawo mussaman saboda ita, tace "Innar mu, dan Allah dagaske na fi matan ƙauyen nan kyau?"

Yatsina baki Inna tai tace "Wane maƙaryacin ne ya gaya miki haka?"

"Ba fa maƙaryaci bane, Jamilun gidan me unguwa ne"

"Me ya haɗa ki da Jamilun gidan me unguwar har ya gaya miki haka?"

Gaban Nana ya faɗi tace "wallahi ba abun da ya haɗa mu, kawai gaisheshi nayi"

"Daga gaishe shi ya fara ce miki kinfi kowa kyau? Dama idan na aike ki gurinsa ki ke tafiya ko?"

"Na shiga uku, wallahi ni bana zuwa gurinsa kawai a hanya muka haɗu, yace ban gaisheshi ba, wallahi bana zuwa gurinsa, kuma wallahi ban tsaya  ma a kusa da shi, yace ze rako ni gida naƙi"

Nan da nan hawaye ya wanke fuskar Nana.

Inna tace "Naji ya isa haka, kin san me nake so dake?"

Nana ta girgiza kai, "ban hana ki hulɗa da mutane ba, ko ki gaida mutane ba, ba haka bane, ina jiye miki sharrin mutanen zamanin nan, mussaman ke da RUƊIN ƘURUCIYA, Yake ɗibar ki.

Komai lokaci ne da shi Nana, idan lokaci yayi dole ko ina so ko bana so in barki ki kula samari, a lokacin da nake sa ran ki mallaki hankalin kan ki, kin sai daidai kin san ba daidai ba.

A wannan shekarun naki, za'a iya amfani da ƙanƙantar shekarunki, da rashin wayo gami da RUƊIN ƘURUCIYA a cutar da ke, su maza ba tabbas ne dasu ba, wataƙila ma abunda yasa ya tsaida ke wannan 'yan abubuwan na ƙirjinki yake kallo"

A razane Nana ta kalli ƙirjinta, tai maza tasa hannu ta rufe ƙirjin ta, tare da gwalalo idanuwan ta waje.

Inna tace "eh mana, kuma idan baki wasa ba wataran taɓawa zeyi, kuma ki ka bari ya taɓa ba ke ba Aure, ba haihuwa kuma ba zasu cigaba da fitowa ba"

"Wayyo Allah na shiga uku, amma dai yanzu zasu cigaba da fitowa ko, ai be taɓa ba"

"Eh to ba tabbas, amma dai ki kula, kuma kita istigfari ko zasu fito, maza ki ɗau carbi, ki shiga saƙo kiyi ta Astagfirullah".

Jiki a saɓule, Nana ta cire hannunta daga ledar tsire ta koma gefe, ta ɗau carbi.

Inna ji tai kamar ta tuntsure da dariya, Nana ta nutsu tana istigfari, Allah ya karɓi tuban ta.



Farhan kuwa, ana kawo wuta ta tashi ta goge Uniform ɗinta, gaba ɗaya zuciyarta da tunaninta suna kan yadda za tai da Prince.

Washegari da sassafe, Farhan ta shirya, ta shashafa turare, ta kints da wuri tai sallama da Ummanta, ta tafi makaranta.

Ana buga jiniyar Assembly, Farhan tana cikin 'yan gaba gaba na fitowa gurin Assembly.

Suka tsatstsaya a filin assembly, ta dinga rarraba ido amma ba ta hango Prince ɗin ta ba, ji tai kamar ta je ta tambayi abokansa ko ya zo?.

Gaba ɗaya ta kasa samun nutsuwa, ba taga Prince ɗinta ba, Nazir ne yazo wucewa ta kusa da Farhan, se waige waige take, ya kalli Farhan yace "what are you looking for?"

Kallon sir Nazir tai ta ɗauke kai, dan haushin Sir Nazir take ji.

Yace "ba Magana nake miki ba?"

Ɗan sunkuyar da kai tayi amma taƙi magana, tsaki Nazir yai ya wuce ta.

Har aka kusa gama Assembly, ba Prince ba dalilinsa, hankalin ta duk yaƙi kwanciya, babban burinta shine tai tozali da Sadik.

Har aka kammala assembly, aka fara tafiya classes, Sadik be shigo ba, jiki a sanyaye take ƙoƙarin barin assembly ground ɗin.

Ba tsammani ta hango shi ya shigo, cikin bossy walk ɗin sa yake tahowa, hannunsa ɗaya goye da ƙatuwar jakarsa, ya cake comb a kansa, su Nasir ne suka je inda yake, suka fara gaisuwar su irin ta samari.

Farhan kuwa tsayawa tayi ta zuba musu ido, karaf idon Prince ya sauka a na Farhan, amma cike da jarumta ya kauda idonsa kamar be ganta ba.

Suka zo suka wuce ta gaban Farhan suna hira, Nas yace "Prince beb ɗin can fa saboda kai ta tsaya, kuma ka wani basar"

"Na sani, amma dole in nuna mata mahimmancin soyayyata a tare da ita, zanga wa zata fifita tsakanina da wancan a jawon"

Dariya suka kwashe gaba ɗaya su kai class.

Farhan gaba ɗaya jikinta tai sanyi, shikenan Prince ya dena sonta, tun da har ze iya ganinta ya share ta haka? Kenan ya dena sonta?.

Jiki a sanyaye ta tafi ajinsu, jinta take tamkar mara lafiya, wai yau ita Sadik ya gani amma ya share, ko meyasa ta biyewa maganganun Sir Nazir oho?

Haka ta nufi ajin nasu, sedai tsayuwar da tai a hanya, tana zuwa ta tarar da Sir Nazir har ya shiga.

Gabanta ya faɗi, amma ta dake ta shiga ajin, aikuwa ya ƙureta da ido.

Hakan yasa ta ɗan dirirce, "from where are you?"

"Assembly ground" ta bashi amsa.

"Ni zaki wa ƙarya? Tun yaushe aka baro Assembly ground ɗin? Kin dai tafi gurin wancan banzan yaron mara tarbiyya ko?"

Da sauri ta ɗago ta kalli Nazir, ta msida kanta ƙasa tana sake haɗe rai.

"Wuce kije ki zauna, mara jin Magana kawai, ki cigaba da biye masa zan gauraya dake ne"

Yana ɗauke kai ta murguɗa baki, taje ta nemi guri ta zauna.

Ya ɗau marker, yaje kan White board ɗin, ya rubuta date da sunan subject ɗin, sannan ya zo ƙasa ya rubuta Adoloscent period, ya ja layi sannan ya juyo ya kalli 'yan ajin.

"Today's lecture we are going to talk about adolescent period, but let me warn you guy's, if any body among you misbehave, i will mercilessly deal with that person, hope i made myself clear?"

Suka amsa da yes sir.

"Can anyone among you tells me a little he understand about this topic?"

Gaba ɗaya ajin sukayi shiru, ba wanda yace komai.

"So non of you ever heard this word before?"

Nan ma shiru suka yi, Farhan ya kalla da ta ƙurawa guri ɗaya ido ko ƙyaftawa ba tayi.

"Hey!" Ya daka mata tsawa.

A razane ta dawo hayyacinta tana kallonsa.

"Meke damun ki ne?"

Ta girgiza masa kai tace "Nothing sir"

"Oya stand up"

Ba musu Farhan ta tashi tsaye, Nazir yace "what do you understand by Adoloscent period?"

Sunkuyar da kai tayi, tai masa shiru.

Yai maganar juyin duniya amma taƙi, magana.

"Farhan, I don't know what you are turning to, you are gentle and so obedient before, amma yanzu gaba ɗaya kin canza, kin zama me taurin kai da rashin ji, a haka zaki lalata rayuwarki da tunanin iska da shirme, sit down senseless child"

Farhan tana zama se hawaye, ta rasa me ta tsarewa sir Nazir da take damunta haka ya tsaneta, bayan yasa Sadik yana fushi da ita, amma ya gza dena binta da miyagun kalamai.

"Kamar yadda ku ka gani a allo na rubuta, Adolescence is the period of transition between childhood and adulthood. Children who are entering adolescence are going through many changes (physical, intellectual, personality and social developmental). Adolescence begins at puberty, which now occurs earlier,than in the past, due to environmen and the kind of food we eat.

Shi Adolescent period, lokaci ne na tashen balaga, lokacin da mutum ke canzawa da ga yarinta shiga mataki na girma.

Yaran  da suka shiga matakin balaga, suna fuskantar sauye sauye a halittar jikinsu, yanayin mu'amalar su, tunaninsu da kuma hange.

A baya a kan samu jinkiri, kan yara su shiga matakin tashen balaga, sedai a wannan zamanin yara na shiga matakin balaga ne a

Please Login or Register in order to submit comment