Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kale bi a Yarinyar nan, ni banga wani abun burgewa a tare da ita ba, amma kai ta wani ɓare ɓare a kanta"

Wani ɗan fito Sadik ya ja, me cike da rainin hankali yai gaba abunsa ya nufi ajinsu Farhan"

Nas yace "ƙyale shi, nasan abunyi, nasan dole ze haɗa mata birthday ai, tunda kuɗin banza gareshi be san cuwon su ba, da wannan damar zamuyi amfani musa shi a hanya"

Amin yace "what a good idea, shi banda wawanci ma, wannan 'yar talakwan kawai ya sarara ya watsar da ita, ko wani abun yai mata ba mataki zasu iya ɗauka ba, amma ya kankane ya hana kowa wai shi Aurenta zeyi"

"Bar banza za muyi maganinsa ne"

Ya na zuwa ya tarar da Farhan ta cika tai fam tana zumɓura baki, Lilly na mata dariya.

Yana zuwa ya kaɗa paper a fuskarta, ta miƙa hannu zata karɓa amma ya ɗauke yana murmushi.

Yace "ke yanzu birthday ɗin naki ya kusa, amma baki gayamin mu fara shiri ba"

"Ni ba wani shiri, ni bana wani birthday fa"

"Wannan karon zaki fara, hall zamu kama ƙarami ai shagali kamar ana bikinmu"

"Dan Allah ka bari, base anyi ba fa, ni a gida baza'a barni ba ma"

Tsuke fuska Sadik yai yace "in dan gida ne, ba matsala zan san yadda za'ai a fitomin da ke, amma sekin zo gurin nan, in kuma ba kya so ne ki gayamin"

Ɗago fararen idanunta tai ta sa a nasa, amma ta kasa sake musa masa se shiru da tai ta sunkuyar da kai.

"Idan ina Magana, ko ince ayi abu kina mun gaddama, I will....."

Se kuma yai shiru, ya juya ya fita.

DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
07063065680.

[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:   🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN. 
   





                         29

Bayansa Farhan ta bi da kallo, ta na shakkar bijirewa abunda ya ke so, da kuma hatsarin aikata wani abu ba da izini ko sanin iyayenta ba.

Muryar Lilly ce ta dawo da ita hankalinta.
"Haka kurum, zaki mana sagegeduwa, ai nasan in dai ya sani akwai shagali na gasken gaske, dan Prince akwai son harkar girma"

Ita dai Farhan ba tace uffan ba, se tsunduma kogin tunani da tai.

Haseena kam tsaki ta ja, dan ta tsani duk wani abu da ya danganci Farhan, haushin ta take ji nesa ba kusa ba.

"Fatima Hakeem Yola, lambarki ta fito" cewar class captain ɗin su Farhan.

Lilly tace "lambata ta fito a ina? Me nayi?"

"Sir Nazir ke nemanki"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, kashina ya bushe nasani"

Kwashewa da dariya Yasmin tai tace "kaga 'yar iskar ƙarya, ke da kike cewa zaki dinga abun da zaki ɗaga masaa hankali, se kuma gashi kin tsure dan ance yana kiran ki"

Hararta Lilly tai tace "ke dalla ƙyaleni, ni mutumin nan wasu lokutan tsoro yake bani wallahi, gashi jarababbe"

Class rep yace "to yanzu zaki je ne ko kuwa?"

Murguɗa baki tai tace "wallahi ba zani ba"

"Au ba zaki ba, idan ya zo ya ritsaki fa?"

"Wallahi ba zanje ba, fecewa zan gida, sedai komai za'ayi ayi, haka kurum"

Suka dinga yiwa Lilly dariya, ta ɗauki jakarta ta bar ajin gaba ɗaya.

Ko da aka tashi daga Makaranta, ba wanda ya nemi wani a tsakanin Sadik da Farhan, sedai ta tafi gida tana ta zullumin abunda Sadik ɗin ke shirin yi, tana tsoron iyayenta su gano, bata san wani irin hukunci zata iya fuskanta ba.




"Nana wai shirin me kike yi ne haka?"

"Inna kin manta ne, babar 'yar ajinmu ce fa ta haihu yau suna, nace miki zamuje, bana tambayeki ba kika ce kin barni ba?"

Inna tace "ai na manta ne, kuma baki tunamin ba, se ganin ki nai kina shiri kawai dole in tambaya ai"

"Ai na gayamiki kin manta ne"

Inna tace "Allah ya taimaka"

Nana ta cigaba da shafe shafen hodarta tana shiryawa.

Inna na aiki a tsakar gida, sega ƙawayen Nana sunyi sallama.

Inna ta amsa musu tana ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya. Daga bisani tai musu nuni da ɗakin da Nana take.

Kai tsaye suka nufi ɗakin suka shiga.

"Ahh su Nana 'yan mata irin wannan ado haka?"

Nana tai fari da ido tace "to a garin nan idan ban ado ba waze yi?"

"A'a ba wanda zeyi ta Jamilu ba da kanki a sare, ai idan muka wuce ta hanyar gidan me unguwa ya ganki seya rikirkice"

"Wallahi kuwa, dan mun haɗu ɗazu na kai niƙa yace min ina Nana? Nace masa kina gida amma da yamma ta layinsu zamu wuce zamu suna, ina ga ma yana nan a bakin layin yana jiran mu"

Nana tace "ke Hannatu, kama kanki, ni ba sa'ar wannan yaron bace"

Hannatu tace "ke! Jamilun ne yaro?"

"Eh mana ban da ya rainawa kansa hankali ni zece yana so?"

"Ke Nana shikenan kowa yana da saurayi amma banda ke?"

Nana tace "To Alawiyya meye dan bani da saurayi? Ke nifa wallahi ɗan Birni zan aura insha Allah, amma se nayi karatu me yawa, in auri saurayi ɗan gayu ɗan birni"

Hannatu tace "eh lallai kin ɗakko da zafi, ko da yake kuna da 'yan uwa a Birni ai"

Alawiyya tace "Amma ki tsaya ku gaisa da shi, kinga ba daɗi wulaƙanci"

Ɗan shiru Nana tai tana tunani, dan harga Allah ta na son taji ance ita ma ta na da suarayi, ta na son sanin me ake ji a soyayyar idan ana zance me ake cewa?"

Ba ta kuma cewa komai ba ta tashi, ta ƙarasa shirinta suka fito tsakar gida.

Nana tace "Inna zamu tafi?"

Inna ta kalleta tace "zaku tafi ina kenan?"

"Haba Inna, ɗazu fa nace miki ga inda zamu"

Inna ta ƙare musu kallo tace "ba inda zaki"

Saroro Nana tai tana kallon Inna, Cikin rawar murya Nana tace "Inna meyasa? Na tambayeki fa kince kin barni"

"Yanzu kuma nace ba zaki ba"

Ƙwalla ta taru a idon Nana tace "Inna meyasa ba zani ba?"

"Saboda na isa, kin wuce kin ban guri ko senai fatali da ke a gurin nan? Ku kuma maza ku kama hanya ku tafi"

Sumi sumi suka nufi hanyar fita daga gidan.

Nana kam da gudu ta bar tsakar gidan tana kuka, ta rasa wace irin rayuwar takura ce haka, wasu lokutan gani take kamar Inna ba ta ƙaunarta Saboda yadda take takuramata, da hanata sakewa.

Su Alawiyya na fita suka fara gulmar Inna.

"Taɓ Hannatu, dama haka kakar Nanan take, wannan mata anyi jarababbiya, ji yadda ta koremu"

"Hmm kedai bari, shiyasa Nanan ma gata nan jarababbiya, wallahi idan nice ba zan yadda da wannan abun ba, ai kakata ce ba uwata ba"

"Wallahi kuwa balle kuma ni"

Suka tafi suna cigaba da tattauna maganganun su.

Nana da mayafinta, da jakarta da takalmin ta duk a tsakar ɗakin ta watsar da su tana kuka.

Inna ta shigo ɗakin, ta kalli kayan da ta watsar ɗin, ta kalli in da Nana ta dunƙule ta na kuka tace "dan ubanki zaki tashi ki kwashe wannan kayan da kika zubar ko sena saɓa miki? Ni zan miki Magana ki min zuciya ki zubarmin da kaya a tsakar ɗaki, kiyi kukan jini ma tashi daga gurin nan ko in haɗa miki jikinki yanzun nan, mara ɗa'a kawai"

Nana tana share hawaye, ta miƙe ta shiga tattare kayan da ta zubar ta maida su mahallin su, ta cire kayan jikinta, ta ɗakko masu datti ta saka dan ita ma ta ɓatawa Inna rai, ta ɗakko hijjabi ta saka, ta tafi turakar Hakimi tai kwanciyarta.

Inna tai banza da ita bata tanka mata ba, ta cigaba da hidimomin ta.

Ko Abinci dare Nana ta ƙi ci, Inna kuma ba ta takurata taci ba.

A haka Hakimi ya dawo ya tarar da Nana, taci kukanta ta godewa Allah, tana kwance tai shiru a ɗakinsa.

"Subhanallah shalelen ba lafiya ne?" Yai Maganar yana taɓa goshinta.

Girgiza masa kai tayi alamar a'a.

"To meyafaru?"

"Inna ce" tai maganar tana fashewa da kuka.

"Me Innar tai miki?" Kasa Magana Nana tayi, se cigaba da kukanta da tai"

Hakimi yace "shikenan, ya isa dena kukan haka share hawayen.

Suna cikin haka Inna ta shigo ɗakin, ɗauke da kwanukan kayan Abinci.

Kallo ɗaya tai musu, ba tace komai ba ta ajiye ta cigaba da harkokin ta, yasa Nana a gaba suka ci Abincin su tare.

Seda ya tabattar ta ƙoshi, sannan yai mata umarnin taje tai sallar isha'i ta kwanta.

Hakimi ya saba da irin wannan rigimar ta Nana da kakarta, dan haka be takura akan se ya san meya haɗa su ba.

Har washegari Nana ta shirya za ta tafi makaranta, amma ba ta wani shiga sabgar Inna, saboda a ganin ta ta gama dizga ta a gaban ƙawayenta.

Tun da Lilly tai ido huɗu da Sir Nazir a gurin Assmebly gabanta yai mummunar faɗuwa, dan tasan tai masa laifi gagarumi, Allah kaɗai yasan yadda ze da ita.

Ga mamakinta ko kallonta be sake yi ba, balle yai mata Magana ya shareta.
Ita ma share shin tayi, sedai ƙirjinta na ta dukan uku uku.

Aka watse daga gurin Assembly, suka nufi classes ɗin su.

Farhan na tafe sannu a hankali, taji an riƙo hannunta ta baya, cikin hanzari ta waiwaya zaton ta Sadik ne, se dai ba kamar yadda tai tsammani bane.

Salma ce ƙawar Nasreen wanda suke a Ss3, wanda ta gansu tare da su Nasreen ɗin ranar da Nasreen ɗin tai ɓari.

Murmushi taiwa Farhan tace "Farhan ko?"

Farhan ta jinjina mata kai alamar eh.

"Dan Allah in ba zaki damu ba, ina son ki zama sister na a school ɗin nan,  if you won't mind"

Saroro Farhan tai tana kallon Salma.

"Anyway, idan an fita break ki zo Class ɗin mu ina son ganinki please"

Farhan ta jinjina mata kai, ta juya ta tafi tana tunanin ita kuma wannan meye haɗinsu, da zata wani ce ta na so ta zama sister ɗin ta?.

A ɗarare Farhan take gudanar da al'amuranta na yau, kasancewar ta na cikin period ne, wanda wannan shine karonta na biyu da farawa, gaba ɗaya ta kasa sakin jikinta, ga shi ƙasan cikin ta na ɗan mata ciwo kaɗan kaɗan, wani lokacin kuma ya ɗan tsananta takura mata.

Ga wata uwar kasala da ke damunta, babban abunda yake ɗaga mata hankali be wuce yadda take jin ƙirjinta wani iri ba, zafi zafi ciwo ciwo, ba ta san wa zata gayawa ba, tafi tunanin ko Cancer ce ta kamata, gaba ɗaya ta kasa gane kanta.

Ana musu lesson amma zuciyarta fal tunani daban daban, a ranta take addu'a idan mutuwa za tai Allah ya nuna mata ta auri Sadik kan ta mutu.

Har aka fita break tana wannan tunane tunanen.

"Yau kuma tunanin me kike yi?"

Firgigit ta dawo hayyacinta, ta kalli Sadik dake kusa da ita a zaune.

"Bakomai"

"Bakomai kamar yaya? Kin san lokacin da na shigo?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a.

"Ke kin ma yi min laifi ko ki neme ni balle ki bani haƙuri ko?"

"Lefi kuma?" Ta faɗa a ɗan shagwaɓe kamar za tai kuka.

"Eh laifi mana, na yimin gaddama"

"Ba fa haka bane, ni tsoro nake ji a gida kar ai min faɗa"

"Zam bi hanyar duk da ta dace, ba wanda ze san anyi, kawai za'a ɗan yanka cake ne aci a sha, mu tayaki murna shikenan fa"

Sunkuyar da kai tai ba tace komai ba.

"Ko dai haryanzu ba kya so ɗin"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Yarinya kin taimaki kanki, da faɗa za muyi"

Ɗan murmushin gefen baki tai, dan ita yanzu halin da take ciki ne yafi damunta, na wannan ciwace ciwacen da take fama"

Idanunta ne suka kuma sauka a hannun Sadik, a ido kawai fatarsa abun sha'awa ga wannan gargasar ta jikinsa da take burgeta.

A hankali ta ɗauke idonta daga kallon hannun nasa ta ɗaga kai ta kalleshi, karaf sukai ido huɗu yace "me kike kallo a hannuna?"

Mamaki ne ya kamata, dama yaga hannunsa take kallo.

"Ni ba hannunka nake kallo ba fa"

"Yanzu kuma ƙarya nake kenan?"

"Wai kai komai nayi lefi ne" tai maganar kamar ta rushe masa da kuka.

Cikin kwaikwayon muryarta yace "kawai ina son in dinga tsokanar ki ne"

Littafin gabanta ta ɗauka ta kwaɗa masa a hannu, ya cigaba dai mata dariya yace "naga hannun nan kamar wani abun kike kallo a jiki, bari in ciro miki shi sosai ki gani" ya kama botir ɗin gabar rigarasa ze fara ɓallewa.

Zaro ido tai ta ja da baya daga kusa da shi, tana kallonsa dariya yai yace "ke da shagwaɓar ki, da tsoron ki, duk ba sa ɓuya, tashi muje ki rakani shop"

"Ni ba zani ba banda lafiya"

"Ke kullum ba ki da lafiya ne? To sekin rakani"

"Ni bana son bi ta wajen SS3 ɗin nan"

Yace "meyasa?"

A ɗan marairaice tace "Kasan wani abu kuwa?" Sadik yace a'a sekin faɗa.

"Kasan wannan Salma ɗin ta SS3?"

Yace "eh na santa"

"Ita ce wai tace wai tana so in zama ƙanwarta, idan aka fita break wai inje"

Take ta ga annurin fuskar Sadik ya ɗauke, wani gumi ya tsatstsafo a goshinsa, cikin kaushin murya yace "meya haɗa ki da ita?"

"Ni ba abunda ya haɗani da ita, kawai ranar na gansu a toilet ne, wai wata ba ta da lafiya, Nasreen wai cikinta ya faɗi, naji tace ina burgeta shine yau tai min Magana"

"Cikin waye ya faɗin?" Ya tambayeta yana tsareta da idanunsa.

"Wai cikin Nasreen ɗin" ta faɗa cike da rashin wayo.

"I hope ba abunda sukai miki?"

Ta girgiza kai "ba suyi min Komai ba"

Be jirata ba ya tashi fuuu yai waje, hakan ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba.

Kai tsaye SS3 ya nufa, hakan yai daidai da fitar malami daga ajinsu.

Ba shakka, ba komai ya kutsa kai ya nufi gurin zaman Salma.

Kallo ɗaya tai masa tace "lafiya ka zo ka tsaya min a ka haka kamar wani ɗan sanda?"

Dukan benci yai da ƙarfin gaske, sannan ya nunata da yatsa yace "kashedi na zo nai miki, nasan kin san Farhan, to idan kuna rashin mutuncin ku da ɓata yaran mutane, ku kiyayi abunda yake nawa, Farhan is my Asset, don't Cross your limit, kince kina son ta zama ƙanwarki, to ta gayamin, wallahi da wasan wasa kika kuskura wani abu ya sameta, wallahi tallahi I will show you what am capable of doing na gaya miki"

Miƙewa tsaye tayi tace "kai ɗan saurara, kar ka gayan maganar banza, idan kana wa saura hura hanci da tunƙaho karka kuskura kaimin, ni ba sa'ar yinka bace, shekara nawa na baka kamarni zaka zo kace za kaiwa warning?"

Nasreen cikin sauri tace "ke Salma, namiji ne fa wallahi akan 'yar nan ze iya yi miki illa, akan kuɗin vanacula ɗinta ranar ba kiga tijarar da yai min ba"

Mubarak babba ne yace "calm down Sadik, dan Allah kayi haƙuri ka manta da ita kawai, insha Allah ba abunds ze samu beb ɗinka"

"Na rantse da Allah, da wasa ita da gangs ɗin ta sukaiwa Farhan wani abu senai musu illa wallahi, Ita ɗin tawace nikaɗai, nasan suwaye ku nasan abunda kuke aikatawa, kar ku kuskura shashancin ku yazo kan yarinyar nan, ba ruwana da 'yar kowa a makarantar nan, nima ban yadda a taɓa abunda yake nawa ba"

Da ƙyar Mubarak ya fidda Sadik daga ajin nan, sannan ya dawo ya kalli Salma yace "ke baki da hankali, wannan yaron kamar ta masa Asiri haka yake wannan zafin kan akanta kamar matarsa, babansa yana da ɗaurin gindi a ƙasar nan, zaki iya jawa kanki masifa"

"To shine se ya zo kaina yana min hauka?"

"Kibi komai a sannu, bake kaɗai ba ni kaina Yarinyar nan tarko zan mata, dan wallahi ta burgeni, shi ba ya tsaya sokonci ba, ze ga tsiya sena watsa rayuwar yarinyar uban kowa ya huta"

Tace "Aikuwa sedai ya mutu, dan nima zan cigaba da bibiyarta.

Ita kam Farhan sam bata san ma wace wainar aka toya ba tana fama da kanta.

Ba tsammani sega Sir Nazir ya shigo ajinsu, kuma alhalin a ranar kwata kwata ba su da lesson ɗin sa.

Gashi kowa yana tsoro balle suyi Magana, dan da wani malamin ne bore za suyi suce su ba zasu saurari lesson ɗin ba.

Lilly tai ɗaiɗai ta cire jacket ɗin ta, ta ɗora ƙafafuwan ta akan benci, tana cin shawarma, hatta ɗan ƙaramin hijjabin jikinta ta naɗe shi baya, tana ciye ciyenta.

Yana shigowa ta sauke ƙafafuwan ta tana raraba ido, yayin da cikinta ya dinga wata uwar ƙara kamar ya ɓaci.

Ya shigo hannunsa ɗauke da litattatafai, ya juya ya fara rubutu akan board, ita kuma tai maza ta cigaba da cin shawarmar ta, yana juyowa sukai ido huɗu.

Bece mata komai ba, ya cigaba da abunda yake, ɗaya bayan ɗaya ya dinga raba musu litattafan su, da yazo kan Farhan har seat ɗinta yaje ya ajiye mata, ya kalleta yace "Congratulations, you got the highest score in my Assignment, And your note and digrams are well drawn And label, clap for her please"

Raf raf raf. Suka tafa mata.

Ya kalleta yace "yadda kike brilliant ɗin nan Allah ya shirye ki, yasa ki dena biyewa wancan ɗan iskan yaron kuna lalacewa"

Dumm haka ƙirjinta yai mata, dan maganar ta daketa, ta rasa meyasa yake son dizgata haka a gaban 'yan ajinsu.

Shi kam ko a jikinsa kamar beyi Komai ba.

"Fatima Hakeem, stand up and explain the assignment i gave you"

Gaban Lilly ya faɗi, ta miƙe tsaye tana zazzare idanu, dan ita ta manta sam akan me ma ya bada Assignment ɗin.

Ta kai mintuna uku ba tare da tace komai ba.

Cikin tsawa yace "Am talking to you my friend"

Ba ta san lokacin da tace "Ni i have no idea on it" tai maganar tana hararsa ta gefen ido.

"Wow you have no idea on it, na bada Assignment ba kiyi ba, ba ki submitting littafin ba, nace ki zo kin ƙi zuwa, na shigo class kin cire riga, kina ciye ciye, bagidajiyar ina ce ke?"

Shiru tai ta sunkuyar da kai.

"Oya bring out your notebook let me check"

Tana zumɓura baki ta ɗakko littafin ta miƙa masa.

Sannu a hankali ya dinga buɗewa yana dubawa, ba uwar da takeyi a littafin ba ta note ba ta Assignment.

Ya ajiye littafin ya kalleta yace "Follow me to my Office, daƙiƙiyar banza da ta wofi, ba abunda kika iya, sedai ku dinga burga kuna hura hanci iyayenku n kashe maƙudan kuɗi, ana kawoku a manyan motoci amma kanku bakomai, hopeless girl"

Ƙunƙuni ta shiga yi, tana ƙoƙarin ɗaukar jacket ɗin ta, amma yai mata wata razananniyar tsawa, ba shiri tai waje da gudu.

Class rep yace "taɓ she kashin wata ze bushe yau"

Yasmin tace "Wallahi kuwa dan babu alamar imani a idonsa"

Yana fita Sadik ya shigo ajin su Farhan, tai mamakin sake ganinsa, yai mata alamar ta biyo shi.

Ba musu ta tashi ta bishi, kan barandar ajin su Farhan suka tsaya, ya kalleta yace "Farhan"

Ta amsa da "Na'am"

"Ba ke babu wannan 'yan SS3 ɗin, duk wadda ta kuma samunki da zancen wai ki zama sister ɗin ta ko makamancin haka, ki sanar dani Please"

Farhan tace "to ni dama ba saninsu nai ba, wai amma meyasa kace haka?"

"Babu wani abun kirki da ke tattare da su, galibinsu 'yan lesbian ne"

"Meye lesbian?" Ta tambaye shi tana kallonsa.

Lallai Farhan Yarinya ce, ba ta san ma'anar kalmar lesbian ba.

"No karki damu, ba ta da wata ma'ana kawai dai ki kiyaye kinji Babyna, ke tawace nika ɗai Please Farhan watch your self in this school, ni I thinks you are quiting this school as soon as possible, da na samu admission, insha Allah zamuyi Aure mu tafi tare, ba zan iya barin ki a makarantar nan ba"

Ajiyar zuciya ta sauke tana ɗan kallonsa.

"Anjima da yamma zanje in duba hall ɗin da za'ai birthday ɗin nan, ko kina da wani zaɓi ko ra'ayi?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Ni bana son wannan girgiza kan, talk to me"

"I have no choice, duk abunda kai shikenan"

"Ok to shikenan, I love you Baby"

Murmushi tai tana jin yadda zuciyar ta ta karɓi kalmar da ya faɗa ɗin, ta juya ta koma Class.

Nana kam da taje makaranta kasa haɗa ido tai da su Alawiyya, saboda yadda aka dizgata a gabansu, suka dinga yar mata da ƙananun maganganu, sedai duk iya faɗan Nana ba ta kulasu ba ta share su, ta cigaba da sabgarta.

Inna tana ankare da ita harta dawo daga Makaranta, ba ta sakin jiki ta kula Inna.

Har ɗaki Inna taje ta tarar da ita, ta ƙare mata kallo sannan tace "Nana gaba kike dani dan na hanaki bin ƙawaye ko?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"Ƙarya nai miki kenan? Ke 'yar ƙanƙanuwar ki dake har kin san ki fifita ƙawayenki a kaina? Wato ƙawayen ki sunfi mahimmanci a kaina ko? To wallahi duk ranar da suka kuma zuwa gidan nan gurinki, dogari zan saka yai musu dukan tsiya, daga ke har su ɗin, shashasha mara hankali kawai"

Wani malolon takaici ne ya tsayewa Nana a rai, ta rasa wannan wane irin abu ne haka, amma tai shiru tana kumbura wuya.

Lilly kuwa Suna zuwa Office ɗin Sir Nazir ta tsaya kyam a tsaye, a hasale yai mata tsawa "On your knees"

Ta kalleshi sororo "Sir knees kuma?"

"You Are asking me? Ba ki ji me nace ba ne?"

Abun da ba ta taɓayi a makarantar ba, haka ta durƙusa akan gwiwowinta, tana cuna baki.

Ya samu guri ya zauna, ya kunna System ya shiga sabgogin sa.

Tun tana tunanin abun na ƙare ne har ta sare, ƙafafunta suka dinga rawa, duk da AC dake Office ɗin amma ta haɗa gumi, farar fatarta tai jawur, gwiwowinta suka dinga mata wani irin raɗaɗi.

Cikin rauni tace "Please Sir am sorry"

Banza yai mata ya cigaba da aikinsa.

Maimaita abunda tace tayi, Amma ya ɗago ya kalleta yace "kika kuma yin Magana, sena sa bulala na zane miki jikinki"

Yadda yai maganar ba alamar wasa, yasa ta karaya ta fashe da kuka.

Amma babu alamar mutumin nan ze ƙyaleta, ta dinga kuka tana shesheƙa, amma yai banza da ita.

Haka nan yaji zuciyarsa na bugawa da Sauri sauri, tana ƙara sautin kukan bugun zuciyarsa na ƙaruwa, amma ya dake.

Ji yai kamar numfashi yana neman gagararsa saboda tsanantar bugun zuciyar, ya kalleta yace "for now ki tashi ki tafi aji, amma kullum idan aka fito break, ba ki da break, nan zaki zo ki kwafe note ɗin nan gaba ɗaya, kuma kiyi Assignment da duk diagrams ɗin fa baki ba, tashi ki ban guri fitsarariya kawai.

Miƙewa tai a hankali ta shiga jan ƙafarta, saboda yadda su kai mata tsami sosai, jin su take kamar ba'a jikinta ba.

Da ƙyar ta sauka daga kan benen, ta na ta shesheƙar kuka, tamkar za ta shiɗe.

Sedai tana tafe a hankali tana jan ƙafar, kan ta kai ga ajin nasu ta faɗi a hanya!.

A garzaya a buɗe AREWABOOKS, Ai following Ayshercool, RUƊIN ƘURUCIYA ya kusa komawa kan manhajar AREWA BOOKS.

Domin gyara Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:       🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN

Please Login or Register in order to submit comment